Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne shiyasa ta ™i Waga kai,
Bai bar wajen ba sai da ya ga ta shige ciki sannan ya ja dogon tsaki yana cewa, "Ni ban taSa ganin ba™auyiyar yarinya irin wannan ba, a haka ne su Daddy suke tunanin haWa Ni da ita, ta saka hijabi sai ka ce zai ka da ita, no I can't, I can't marry this little girl da babu wayewa a tattare da ita ba, infact ma ba budurwa ba, maza nawa suka santa da za a Wauko saura a bani? No, it's not possible, bata yi min ba, she doesn't have what I want, there's no love for her in my heart."
Kamar wani taSaSSe haka ya dinga magana shi kaWai, alamun ransa ne a Sace ya dinga sakin zance, daga karshe ya ciro sigari wanda ya yi wa Soyo cikin motan; ya kunna ya fara zu™a before ya soma jin dai-dai, sai ya ja motan aguje yabar wajen.*****

Koda Madina ta shiga gidan, sai da ta Soye ta sha kukanta sosai sannan ta share hawaye ta shiga cikin falon, sai dai tayi ™o™arin Soye halin da take ciki bata bari su Khairiyya sun gane ba,
Su sai murnan ganinta suke yi ma tunda sun yi zaton ta tafi, hakan ne yasa basu kula da halin da take ciki ba, itama tayi ™o™arin Soye wa ta saki ranta sosai,
Yayinda a zuciyarta abun da Ansar yayi mata ya tsaya mata a rai, ta kasa manta wa, idan ta tuna sai ta ji ™walla sun cika mata ido sabida muzanta ta da yayi

A ranan sai dare aka kwaso kowa aka mayar dasu gidan Daddy,
A washe gari kuma mutane suka fara raguwa sai dangi na kusa,
Tun wannan haWuwar wani abu bai sake hada Madina da Ansar ba, infact ma bata ganin shi sai jefi-jefi daga nesa,
Tunda a lokacin duk su Aunty Hafsah suna nan basu tafi ba, sai da suka ™ara kwana biyu sannan suka tafi, sai yazamana gidan an watse babu mutane daga masu aiki sai mutan gidan,
Ana gobe Madina zata tafi sai da ta ™ara zuwa gidan Khairiyya tayi mata wuni curr, sannan driver ya maido ta gida

Washe gari da safe bayan sun gama karyawa Daddy ya bu™aci ganinta ita kaWai, har falonshi ta bi shi suka zauna,
Sai da ya dube ta sannan ya kirayi sunanta,
Ta amsa mishi cikin ladabi da biyayya kanta a ™asa,
Šan jimm yayi sannan yace, "daughter ina son ki sanar min kin tsayar da wani ne wanda za ki aura a yanzu?"
Shiru tayi sabida maganar ta zo mata a bazata ne, sake du™ar da kanta tayi sosai sabida kunyar da ya kama ta,
Shi kuma sai yayi murmushi yace, "ba wai za ki zauna kina jin kunyata bane Madina, ai already mun zama Waya Ni tamkar mahaifi ne a gare ki, idan har kin Wauke Ni a matsayin Uba ina son ki bani amsa tsakaninki da Allah."
Dakyar ta iya buWe baki tace mishi, "a'a Daddy."

"Babu wanda yake sonki ko yake neman aurenki a gida wanda kike tunanin za ki amince mishi?"
Girgiza kanta tayi cikin kunya ta sake cewa, "a'a babu kowa Daddy."
Shiru yayi kamar yana nazari, sai kuma yace, "ina Wan uwan nan naki da yake son mayar da ke Wakin shi? Har yanzu yana tare da ke kuma ba ki ba shi dama ba? Ko ya janye ne?"
Cike da kunya tace, "eh."

"Ai ban fahimce ki ba Madina, ki buWe baki kiyi min bayani sosai domin ina so nayi magana da ke mai muhimmanci ne, kuma ba bu™atar in tauye miki ha™™inki, idan yana tare da ke har yanzu kuma yana sonki ki yi min bayani in sani?"
Batare da tayi tunanin rashin fadan gaskiyar nata zai haifar mata da wata gagarumar damuwa ba; idan da ta san mai zai nema a wajenta da tun farko ta faWa mishi gaskiya; ta yanda zata guje wa maganar nashi, amma sai ta Soye ta nuna mishi babu wannnan zancen a yanzu

"Masha Allah alhamdulillah... To dama na ga dacewar in sanar da ke wannan maganar ne wanda mun jima da yin ta, Na tabbata ba ki sani ba, amma Ni yanzu Madina alfarma nake nema in har kin Wauke Ni tamkar mahaifi; ki bani dama in zaSa miki Mijin aure, don Allah."
Wani irin yanayi Madina ta shiga wanda sam ta kasa motsi sabida jin kalaman Daddyn, amma kuma ai bata da zaSi a yanzu face ta amince mishi tunda baza ta iya bijire mishi ba, ya fi karfin hakan a gare ta, su ne mutanen da suka fi muhimmanci a rayuwarta idan aka cire iyayenta, kuma mahaifi ne a wurin Mashkur wanda ko bayan idanunshi baza ta taSa bijire mishi ba, bata da zaSi tabbas domin Daddy ya wuce komai a wurin ta, koda bata so idan ya nemi wani abu a gare ta dole ne ta amsa mishi, wannan ne yasa ta Waga mishi kai alamun ta yarda; yayinda idanunta suka cika da hawaye amma ta kasa bari su zubo, kuma ta ™i Wago kanta bare ya ga halin da take ciki,
Yayinda daddy kuma ya nuna farin cikinsa tsantsa yana ta sanya mata albarka, yace, "insha Allah zata yi alfahari da zaSin da zai yi mata, ta je ta ci gaba da karatun ta bazai mata tilas a yanzu sai an yi auren ba, don haka ta kwantar da hankalinta ta mayar da hankali wajen karatun ta, daga baya zai sanar mata wanda ya zaSa mata sai a yi auren."
Ita dai Madina jin sa kawai take yi amma ta rasa abun da ke mata dad'i, ya nemi abun da ya fi ™arfin shi a wurinta, baza ta iya mishi musu ba dole ne ta amince, amma ita ai bata tashi aure ba, bata son aure domin bata san me zata tsinta a auren ba, sai dai tana ganin dama ita haka Allah ya tsara mata rayuwar, babu wata rayuwar jin dadi a tattare da ita, ita a haka zata ™are rayuwarta daga wannan sai wancan, tana ji a jikinta tamkar wata mummunar ™addaran ne zata kuma fuskanta, duk da ta san Daddy bazai zaSa mata abun cutar wa a gare ta ba, amma ta kasa sukuni, shi auren kanshi shine babban ™alubalen ta tunda bata so, sanadin aure ta ga abubuwa da dama a rayuwarta, idan ta zauna a haka zata fi samun kwanciyar hankali, amma waye zai fahimce ta ya gane abun da take gudu?
Tunda ta koma Waki domin ta shirya kayanta, sai ta shige toilet ta dinga rusa kuka gunun tausayi, ta rasa inda zata saka ranta ta ji dad'i,
Bata da yanda zata yi haka nan zata jira ta ga mai zai faru a nan gaba, but zuciyarta ta Warsu da wani irin tsoro mai wuyan fassara,
Sai da ta ji numfashinta na kokarin Wauke wa sannan ta dena kukan, sai ta fito ta nemi maganinta ta sha sannan ta kwanta na Wan wasu mintina, daga baya kuma sai ta koma toilet Win tayi wanka ta fito ta soma shiri, amma har wannan lokacin zugi zuciyarta take mata

Daddy a fannin shi bai sanar da kowa a game da yanda suka yi da Madina ba, yabar maganar ne sai daga baya zai sanar musu; idan ya kira Ummanta ya faWa mata yanda suka yi

Ansar aka so ya kaita gida, amma tunda ya ji Mummy ta sanar dashi, sai ya nuna ai yana da aiki mai muhimmanci, hakan ne yasa da sauri yabar gidan tun kafin su haWu da Daddy, kuma ya kashe wayansa don kar ma ya kira shi,
Dole sai dai driver ne ya mayar da ita gida,
Amma tunda ta koma ta ™i sanar da Umma abun da ya faru, duk da a yanayin da ta koma sam-sam babu karsashi a tattare da ita, tarin damuwa ne ya nuna a kan fuskartŭ˙˙˙ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~a duk ta sauya gaba Waya,
Umma tayi ™o™arin tambayarta amma ta nuna babu komai, dole ta ™yale ta but tana mata kashedi, "kar ta ™ara ganinta a haka idan baza ta sanar mata abun da ke faruwa ba, ita ta lafiyarta take ji."
Wannan ne yasa Madina ta Soye komai a ranta ta saki fuska tana walwala, sai dai maganar ta daWe tana cin ta a zuciya, irin damuwar da ta shiga shi ya haifar mata da zazzaSin dare, wanda ciwonta ne ya so ya tashi haka ta kwana ta wuni babu lafiya, sai da Umma ta dinga mata faWa sabida ta san dole akwai damuwar da ta saka a ranta ya haifar mata da ciwon,
Dayake har da zazzaSi ne shiyasa tace ma Umman, "wlh babu komai zazzaSi ne yake damunta, dama tun a can Kaduna take ciwon kai."

Yaya Yunus na zuwa yace, "sai an kaita asibiti an duba ta."
Hakan kuwa aka yi shi ya Wauke su suka wuce asibiti nan kusa, aka yi mata alluran zazzaSi sannan aka bata magani, tunda ta nuna ita zazzaSi ne kaWai a jikinta,
To kwana biyu Madina tana ciwon nan duk da bai yi worst da yawa ba, tana harkokin ta idan dai maganar ta dawo mata ™wa™walwa ne, in ta zauna shiru tana tunani sai ciwon ya dawo sabo,
Wannan ne yasa Umma ta dena barin ta tana zama haka nan, koyaushe suna tare bata bari ta zauna shiru ita kaWai, tunda tana iya yin komai har aiki take saka ta idan babu su Hussaina sun je islamiyya,
To hayaniyar Khalifa ma kaWai ya ishe ta in yana nan

Sati Uku da faruwar hakan suka fara zuwa ABU karatu, duk da su Hassanan ma shekara Waya kenan da gama karatunsu sun riga ta gama wa, yanzu haka suna zuwa makarantar koyon computer ne a nan gomnande ™ofan kibo. Dama shekara Waya ne ake yayewa sun gama da sati biyu kenan suka fara zuwa ABU, but dukkan su ukun kowa fannin karatun ta daban, shiyasa wata rana ma batare suke zuwa ba

Fara karatun Madina sai komai ya zo mata da sau™i, yanzu ta dena damuwa da zancen aurenta da suka yi da Daddy, infact ma yanzu ta soma mantawa, sai daga baya ne Umma tayi mata zancen saboda kasancewar Daddy ya sanar mata yanda suka yi, ita kuma ta ji daWin yanda Madinan ta amince mishi bata yi gardama ba, domin ko mai zasu yi musu baza su iya biyansu da irin alkhairan da suka yi musu ba, tabbas tana ganin Daddy ya isa da Madina fiye ma da hakan, duk abun da ya yanke a rayuwarta zasu amsa da ya™inin bazai taSa cutar da ita ba, bare da Ansar za a haWa su auren ya sanar mata da komai, maganar baya ce har yanzu suna neman alfarman a basu aurenta,
Umma dai bata da bakin magana tunda dama tun a baya ta amince musu, fatanta Allah yasa a ™ulla alkhairi, ta yiwu shi ne zaSin da Allah yayi mata, basu da abun faWa a yanzu,
Sai dai kamar yanda Daddy bai sanar da Madina wane ne zaSin ba? Haka itama Umma tabar zancen sai lokacin yin auren yayi, yayinda take tunanin hanyar da zata bi ta sanar da Yunus wannan al'amarin, domin idan ta ci gaba da Soye mishi ha™i™a zata cuce shi da yawa.
[1/9, 8:18 AM] My Airtel Numb: =ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ
    *RAYUWAR MADINA* =Ĝ§Ü
=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>ĜŬŬ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Ĝß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ĜŞÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A
'ŝ*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 62*
_____A wannan karon sai da Umma ta kira Yaya Haula ta sanar mata da komai; domin ta ji ta bakinta,
Haula ba abun da tace illa fatan alkhairi tunda itama tana ganin kamar babu matsala, sai dai su ci gaba da mata addu'a fatan dacewa da Miji nagari, Allah yasa karshen wahalarta ne yasa zata samu farin ciki a nan gaba,
Umma tace, "Amin dai, don Ni yanzu bani da abun cewa tunda komai na Allah ne, shi ke tsara komai a yanda ya so, in Allah ya yarda Madina baza ta ™ara shan wata wahala a zamantakewar aurenta ba, Allah yasa mu ce gwanda da aka yi, abun da yasa hankalina ya fi kwanciya da zancen sabida gidan mutunci zata je, wlh basu da matsalar komai, shima Ansar Win ina masa kyakykyawar zato duk da dai ba halin su Waya da Mashkur na faram-faram da mutane ba, amma babu ruwansa tabbas ina masa kyakykyawar zato, shi kuma Yunus Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi a gare sa, tunda ita kanta Madina da tana da ra'ayin koma mishi da tuni ta ba shi dama; amma har yanzu basu wani jituwa ta ™i sakar mishi fuska, kinga kuwa ai baza a yi mata dole ta koma gidan shi ba, tunda a yanzu ma ya mayar da Matarsa kawai yayi hakuri Allah ya haWa kowa da rabonsa."


"Haka ne Umma, Ni kaina nayi wannan tunanin gwara dai ta auri Ansar duk da na so ta da Yaya Yunus, amma kinga shi yana da mata; kuma da mai Mata ai gwara saurayin, ta zauna ita kaWai domin muna mata fatan samun jin daWi fiye da yanda muke zato, itama dai ta dage da addu'a shine kawai."
Daga nan hiran kadan suka ™ara suka yi sallama, inda Yaya Haula take ce mata, "zata kira Madinan anjima in sun dawo makaranta sai su sake magana."
Umma tace, "amma fa kar ki sanar da ita wane ne kawai a bar maganar tunda Alhajin ya ce ba yanzu za a yi auren ba."

"To Umma sai anjima."
Daga nan suka sake sallama suka kashe wayan

Yanzu dayake shigan su Madina makaranta; musamman Daddy ya aika musu da wayoyi kowacce nata daban sabida harkan karatun, yanzu sun dena sharing waya,
Dama su tagwaye suna da samarin su tunda suna tsaya wa da saurayi, Umma ce dai ta gargaWe su amsar wayan samari shiyasa basu taSa amsa ba, illa wayan da Baba ya siyan musu gaba Waya suke amfani da ita har Madinan,
Madina dai tana jin dadin makarantar nan tunda tana Webe mata kewa, idan suka fita tun safe sukan kai yamma a can tunda karatun farkon semester ne ana Wiban lectures masu zafi, kuma alhamdulillah dukkansu suna fahimta tunda suna da ™wa™walwa gaskiya, Madina da ta saka karatun a gaba dagewar da tayi sai ta ga komai ya zo mata da sauki, since makarantun da tayi na kuWi ne ta samu koyarwa sosai wanda ya buWa mata ™wa™walwa, sai dai karatun jami'a komin kanka na ja sai ka sha wahala, sai ka shiga zaka tabbatar da cewan akwai bambanci da secondary, dole sai ka sake dage wa don wahalar karatu da yawa yake,
Shiyasa tunda ta fara zuwa ta ™ara kame kanta sosai, musamman da ta ga makarantar babba ce da Walibai masu Winbin yawa, wannan ne yasa da ni™abin ta take zuwa ko kuma ta saka face masks, sai idan an zo musu karatu take Waga wa tunda Malaman basu son ana rufe musu fuska, shiyasa da yawan ´an ajin basu santa ba,
Kuma dama sababbi ne kowa harkan gabanshi yake yi babu ruwan kowa da kowa,
Yau dai sun samu sabon Malamin da ya shigo musu lecture, kafin ya fara sai da ya gabatar da kansa sannan yace musu, "Waya bayan Waya kowa ya fito gaban allo ya gabatar da kansa."
Haka kawai Madina gabanta ya fara faduwa sabida yawan Waliban, har jikinta karkarwa yake yi duk da ba a kawo kanta ba; but haka ta daure ta natsu waje Waya tana kallon masu fita one by one suna introducing kansu,
Dayake tana can baya -baya ne kafin a zo kanta sai Malamin ya dakata tunda duk wanda ya fito sai ya tsaya mishi tambayoyi daga ina yake? Da inda yayi karatu tun daga matakin primary, wasu a yi wasa da dariya a yi raha hakan ya cinye lokacin malamin, tunda dama shine karshe, shiyasa yace musu, "zuwa Monday za a ™arisa before ya fara Waukan su lecture, don yana son ya san sunan kowa, shi haka al'adansa yake, ya fi so yana karatu da fuskar sani yanda zai ji daWin tayar da mutum da sunansa."
Su sun zaci wasa ne da yace musu, "yanzu haka duk sunan wadanda suka gabatar da kansu ya sani."
Sai suka yi ta dariya ´an ajin, sai da ya fara nuna su Waya bayan Waya yana fadin sunan su har da sunan Baban su; wannan yasa suka cika da mamaki kuma ba ™aramin burge su yayi ba,
Yana musu sallama ya fita kowa ya fara fice wa

Madina kuwa wayanta ta ciro ta soma kiran Hassana, sabida ta ji ko sun gama nasu lectures Win su wuce tare, sau tari hakan suke yi, sai sun kira juna sun ji in sun gama lectures sai su tafi a tare, wacce bata gama ba kuma ta dawo daga baya,
Lokacin da ta kira Hassanan tace mata, "yanzu zasu fito, ta bata nan da 15mint."
Madinan tace, "ta same ta a department Win su tana jiranta."
Koda ta kira wayan Hussaina ba ta zuwa,
Sai ta sake kiran numban Hassana ta tambaye ta, "ko sun yi waya da Hussainan?"
Hassana tace, "eh Aunty Madina, Wazu ta zo department Win mu tace zata tafi, wayanta babu caji ne shiyasa ta zo ta faWa min, kuma na manta ne ban sanar miki ba."

"To ki yi sauri ina jiran ki."
Kashe wayan tayi tana ™o™arin saka wa a jaka; sai ta ji wata kusa da ita tace, "excuse me. Please don Allah ki ara min wayanki in yi call, My phone has no card."
Kallonta Madina tayi suka haWa ido,
Sai yarinyar tayi mata murmushi,
Itama Madinan murmushin tayi mata ta mi™a mata wayan,
Ta amsa ta saka numban driver Win ta ta kira shi, sai da ta gama wayan before ta juya ga Madinan da yanzu ta rufe face Win ta da ni™ab, mi™a mata wayan tayi tace mata, "thanks."
Kai Madinan kawai ta Waga mata sannan ta buWe jakarta ta saka wayan,
Yarinyar da a shekaru baza ta fi Madinan ba, sai dai itama kyakykyawa ce sosai fara da ita, da alamun yarinyar ´ar masu kuWi ne don wayan hannunta kanta abun kallo ne, ga kayan da ta saka masu kyau da tsada tayi gayunta cikin fakistanin kaya riga da wando; kuma ta yane kanta da ba™in veil face Win ta akwai makeup da yayi mata kyau, da alamun yarinyar kuma tana da fara'a da sau™in kai; shiyasa tace ma Madinan tana son sanin sunanta?
A takaice Madinan ta sanar mata kamar bata so,
Ita kuma sai tayi murmushi tace, "Ni kuma suna na Falak Uthman Al'amin, and yau na fara zuwa, zan so mu zama ™awaye Please idan babu damuwa?"
Sai ta mi™a mata hannunta tana zuba mata murmushi,
Sai da tayi jimm kamar baza ta mi™a mata hannun ba,
Hakan ne yasa Falak tayi dariya tace, "don't worry ina son zama ™awarki ce sabida na ga kina da kyau sosai, kin burge Ni, Please kar ki ce a'a ki amshi ™awance na."
Sai Madinan ta ji kunya sabida ganin sau™in kan yarinyar, kuma tana ganin ba abun ta wulakanta ta bane don daga gani ta fita komai wlh, kyawun ma da take faWi sai take ganin kamar ita ta fita nesa ba kusa ba, ga ta ´ar gayu wayayyiya, wannan ne yasa Madinan ta mi™a mata hannun sabida har a ranta sai ta ji ta yarda da ita,
Manne hannun nasu sosai Falak tayi cike da fara'a tace, "na ji daWin haWuwa da ke sosai."
Murmushi ita kuma Madinan tayi batare da ta iya cewa komai ba,
While wayan Falak Win ne yayi ring, sai ta zare hannunta tana duba wayan, ganin sunan Ammee Win ta ne sai ta amsa call Win cike da shagwaSa tace, "Ammee sai yanzu kika tuna dani ko? Nayi fushi."
Ta kare maganar tana bubbuga ™afa,
Madina da ke kusa da ita tana jin muryan Matan tana cewa, "sorry Auta, yau nayi busy ne a hospital but ban manta da ke ba, ki yi hakuri ga shi na kira ki ai, lafiya me kike so?"

"Ammee bani da credit a wayata, kuma na kasa kiran Yaya A'sim na san faWa zai yi min since jiya ya sa min, kuma Ammee wlh duk su Aisar ne suka cinye min daga na ajiye na koma Waki."

"To Auta yanzu ya kike so a yi?"
ShagwaSe fuska tayi tace, "ki Wan tura min mana Please Ammee, yanzu haka fa ina school an tashi driver bai zo ya Wauke Ni ba, sai aran waya nayi."
Ammee tace, "ok bari in tura miki yanzu, in kin koma ki gaishe min da Mamyn naki."

"Ok Ammeena, in na koma zan sake kira muyi waya ma."
Daga nan sai suka yi sallama ta kashe wayan, sai kuma ta soma dariya tana kaWa kai cikin jin daWi, sai ta kalli Madina tace, "Ammeena ne muke waya da ita..."
Bata kai da rufe baki ba ta ji karan shigowar message, tana duba wa ta ga credit na 1500,
Abun mamakin sai Madinan ta ga ta sake kiran wata number tana ™ara ro™on credit Win, ga dukkan alamu wannan Win shine Yaya A'sim da ta gama furta wa,
Daga karshe shima ya sake tura mata kuWi sai kuma ta sake kiran wata numban, tana magiya da faWin, "Aunty Huda don Allah ki tura min credit yanzu, ina school ne kuWina ya ™are kuma zan kira driver ya mayar dani gida."
Aunty Huda ta ce, "to injin tatsa yayi miki kyau, wlh ki dena kira na kina tambayana kuWi tunda Ni ba Sa'an wasanki bane, ki kira sauran da kika raina in ba haka ba zan ci ubanki."
Kamar zata yi kuka Falak Win tace, "kai Aunty idan ban kira ki ba waye nake dashi da zan kira? Don Allah ki taimaka ki tura min daga wannan na dena."
Tsaki ta ja tana cewa, "zan ci ubanki ne kar ki kiyaye Ni ba."
Daga haka kashe wayan nata tayi,
Madina kuwa tsimi tayi tana kallon ikon Allah wajen yarinyar,
Babu jima wa wayanta tayi karan shigowar message, tana duba wa ta ga 1k sai tahau murna tana dariya, ta dubi Madina wacce ta kawar da kanta tace, "ai idan ba a musu haka to wlh baza su bani ba, wadannan dukka yayyina ne, but Ni ´ar Kaduna ne na zo nan ne karatu, ina zaune wajen ™anwar Ammee Winmu."
Sai tayi dariya ta sake cewa, "ni ce ™arama a Wakin mu shiyasa suke ji dani, yanzu ma zan kira Daddyna in sake ro™on sa, ki yi hakuri na cika ki da surutu ko?"
Saurin girgiza kanta Madina tayi tana ™o™arin tashi a wajen tace, "a'a."
Falak tace, "to ba ki bani numbanki ba, kawo wayanki in saka miki numbana."
Babu musu Madina ta mi™a mata don tana ganin kamar yarinyar akwai shegen surutu da gundura, shiyasa ta ™osa ta fice ta barta; sai kace ta tambaye ta ikon Allah,
Numbanta Falak ta saka itama ta Wauki nata, bata ba ta wayan ba sai da ta Wan yi danne-danne a nata, ashe tura mata katin zata yi, sai da ya shiga sannan ta mi™a mata wayan tana cewa, "ga kyautana nan gare ki, nima na saka miki tawa katin."
Idanu Madinan ta zuba mata, sai kuma tace, "amma meyasa ba ki tambaye Ni ba? Ai ban ce miki ina so ba?"

"Haba har sai na tambaye ki? Kyauta na ba ki Please ki amsa domin ™awancen mu."
Sai ta mi™e itama bata jira cewar Madinan ba ta Waga mata hannu cikin fara'a tabar wurin,
Yayinda Madina ta bi ta da kallo har ta Sace mata, sai kuma jiki a mace ta Waga wayan tana duba wa, katin 1000 ta tura mata,
Fita tayi daga class Win ta sake kiran Hassana,
Hassanan tace, "ga ta nan yanzu tana kan hanya ne."
Babu jima wa kuwa sai ga ta ta kariso suka jera suka fita tare, napep suka samu yakaisu har gida


Sun koma babu jima wa Yaya Haula ta kira Madinan,
Sai dai bata Wauka ba sai da ya katse sannan ita ta kira ta suka gaisa suka Wan taSa hira, har Madinan tana cewa, "yaushe za a kawo mata su Abida suyi mata hutu? Yakamata dai ta kawo su nan su zauna ko na sati biyu ne."
Yaya Haulan tace, "ai tana nan zuwa insha Allah bada jima wa ba."
Daga nan ne tayi mata maganar zancen aurenta da Umma ta kira ta ta sanar mata,
Madina kamar zata

Please Login or Register in order to submit comment