Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamakin dama ni matar Aaryan ce?,Toh ya akayi haka?



A mota kuwa kuka nake da iya karfina Ina Roqon Sa cewa nake "DanAllah yaa kayi Haquri, Wallahi Nasan darajar Aure na Rantse na Sani" kuka nakeyi Wiwi Ga yawu ga majina Amma ya toshe kunnensa da Airpod,20mins muka isa Gidan
Abbie dake Low-cost Zaria, Ya danna Horn Mai Gadi ya leqo yana Ganin Motar ya San tawace da Gudu ya Wangale Gate Ya shiga da Motar.


Aaryaan na tsayar da motar yace "Gara Tun wuri ki Goge Hawayen nan naki Ki kame bakinki ki mn Shuru if not.."


Sai ya Tsagaita yana murmushi tareda Cije lips, Nasan Halin shi Idan ya Cije lip to Mugunta ke cinsa, Gara nayi yanda yace in ba haka ba zan wahala ne kawai.


Goge hawayen nayi ina turo baki, yace "idan kika Kara Turo mn wannan bakin Sai Nayi maganin shi" sannan ya bude kofa ya fita nima Fitowa nayi nabi bayansa.



Gidan babu wani Kura amma yayi datti, Saboda anan akayi taron Bikin su Shida Ramlah.

A falo naja na tsaya ina Zaro ido ,Bai tankani ba ya shige ciki babu jimawa ya dawo dauke da Brooms da Parkers ya wurga mn, "Oya dau tsintsiya ki share mn Gidanan Ya fita Fes banason Ganin Even A single sand a nan wajen, na San ko tsintsiya baki Iya Riqewa ba kor ba haka bane?" Ya fada yana kallona.

Kai na gyada mishi Alamar "Eh"

Yace "Wow kinga ni kuma bazan iya zama da Wacce bata iya Aikin komai ba ,So take the broom and Start Sweeping my friend"


Turo baki nayi ina hawaye nace"Babu kyau Shara da daddare fa"

Ya tako daga inda yake yazo inda nake tsaye na dauka Dukana zaiyi shiyasa naqi Matsawa.

Hannuna ya damqa dakyau, Hakan yasani Waro idanu ina kallonsa.

Sai kawai ya fizgi hannuna ya mannani jikin bango shikuma ya min Rumfa,Ban Ankara ba kawai naji ya hgwpbxjkhg๐Ÿคช


Jikina ya kama Rawa saboda Tsoro, banyi zaton Kalar hukuncin da zai dauka kenan ba,ai da ban turo bakin ba.

Ya dau 6mins kafin ya Sakeni



Ai yana Sakina Na, bansan lokacin da na dau tsintsiya na fara Shara ba, Shi kuma ya koma Daki.


Ina Gama Sharar Falon na shiga extra Rooms na Sharesu, Na kwashe datti sannan na koma Parlor na kwanta Rigingine kan 3seater ina maida Numfashi,

Tunda Aka haifeni ban ta6a Aiki mai wahala kalan na yau ba, ko Wacce Amarya Ranar farko ,war haka tana nan ana Rarrashin ta Amma ni Ina nan an Hore ni da Sharar dare๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜‚.


Ina kwance anan bansan ya shigo ba Sai saukar Ruwan da naji saman Fuskata, dagowa nayi ina kallonsa Har ya Sauya kaya Zuwa farar Armless da Blue 3quarter yana Riqe da Gorar Swan.

Ganin naki na tashi yasa ya watso mn Ruwan Bakinsa Saman Fuskata.

A firgice na tashi ina Yatsine Fuska lallai YaaAary ya manta ko Wacece ni ,Shiyasa yake mn haka ya dauka Tsoron shi akeyi๐Ÿ˜, Baisan lokaci kawai nake jira na Rama duk Abin da yayi mn a baya ba, Amma yau ya kaini bango, Sai na Nuna mishi Asalin kalata Dan naga kaman ya fara manta Wacece MUNAYFERH.


Muryan Shi naji yana cewa"Wa kika barma Wanchan bedroom din?"


Simi-Simi na Wuce na Share Dakin Sannan na shiga Bayin dan dakin nayi Wanka.


Amma Abin mamaki sai Gani nayi babu jini sai Alamar sa, ni dai Nasan nakan Dau at least 5days inayi Amma meyasa Yazo ya gudu a rana daya?, ko dai dagaske YaaAary ya 6ata mn Rayuwa?,Amma meyasa banji Zafi yanda naji ance ana ji ba?, Wata Zuciyar tace kinsan Shi likita ne Kila ya baki Abinda zai hanaki Jin zafi ne(๐Ÿฅบ?).



*Nida Readers (๐Ÿ˜†)*.



Fashewa nayi da kuka Shikenan YaaAary ya Gama dani ya Cutar da Rayuwata .


Shikuwa yana Ganin Shigewana ya Bi bayana ba kallo, ya rasa mai yasa Duk in yana Tareda ni yake mancewa da Kowa a Duniya, Sai a yanzu ya tuna da Wai Ya baro Wata matar a Gida fa๐Ÿค” Gashi dare yayi .


Waya ya Dauko ya tura mata saqo Wai Aiki ya Riqeshi Sai da safe zai dawo.


A lokacin da ya tura Mata saqon Suna dinning ita ,Hafsah da Umma Sun tasa Abinci a gaba suna kallo,Dan Umma tace babu Wanda zaici abincn sai Aaryaan ya dawo ya raba Gardama.


Bayan ta Karanta Saqon ne take Gayawa Umma Abinda saqon ya kunsa ,Amma Fafur Umma tace ita bata yarda ba sai ta kirashi taji daga gareshi, ta ko kirashi Amma fa wayar a Kashe.

Sai tara da rabi na dare kafin Umma ta yarda su ci abincin nan ma Dan kadan ta yarda Ramlah Taci Ahakan ma Wai ta Samu ne,



*******

Ina kwance a bedroom ina kuka mai Tsuma zuciya, Ga Gajiyan Aikin da nayi Ga Baqin cikin Aure ga kuma Yunwan dake qwaqular cikina,Ban San lokacin da ya Shigo ba, na daiji Qamshin Turarensa Kusa dani.


Dagowa nayi ina kallonsa,Yana Riqe da Ledar Apple white, nan take na Hadiye wani Yawo Wanda Nasan na yunwa ce.


Ya Ajiye ledar a qasa,Shima zama yayi a qasa Yace inje in wanko Plates da Spoons da cups harda knife a Kitchen.

Tashi nayi ina yatsine Fuska na nufi kitchen na wanko Na kawo na dire su a gabanshi sannan na koma na zauna saman Gado.


Ya bude ledar da ya shigo dashi ya fiddo wata Lafiyyyar kaza sannan ya Fito da wata takeaway da Wata qatuwar Roba mai kunshe da Fresh Holandia milk.


Waro idanu nayi tsoro ya kuma kamani, Me yake nufi ne?..



Ko kallona baiyi ba Ya zuba cikin Plate a natse ya fara ci yana korawa da Fresh milk



Kallonsa nake yanda yake Motsa bakinshi a hankali Cikin wani irin salo kaman Mace.

Ganin yaci Kusan Rabin Abincin bai min tayi ba bare na sa ran zai tsanmin , sai na bude baki kaman zanyi Magana Amma Gudun karya Hayayyakoni yasa na miqe Saman Gadon na zauna Saman Rug inda yake nasa hannu Nima na faraci..........










Tofa๐Ÿ˜ƒ

Me zai faru???

Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

Wattpad @fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ
7th September


๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 26_*


*narasa bakin da zan godewa masoya wannan littafin sai dai ince Allahu yabar qauna yaqara bani kwarin gwiwar faranta muku ko yaushe ๐Ÿ˜˜*


Hawwa baba

Hawwa'u Adam

Hawwa'u Kwangila

Hawwa ms

Jeedda zubayr


Da dukkan masoyan littafin nan Masu suna Hawwa wannan page din naku neh๐Ÿ˜˜






*LAOS*

Da suka Gudu fado Dakin suna kyakyatawa.


Yarane Sosai Bazasu Wuce Yan Shekaru Biyu bah,Mace da Namiji Suna matuqar kama da juna Sosai, ko ban fada ba Ya kamata Ace me karatu ya Gane y'an Biyu ne๐Ÿ˜‰.

Macen Na Riqe da Tablets Guda Biyu namijin na Binta yana dariya yana ta bashi AbinShi Amma ita Sai wahalar dashi take,Sai tayi kaman zata bashi ya zo Gab da ita take Zamewa .


Suna Haka wata matashiyar mace ta Fito daga daki tana murza ido Alamar daga bacci ta tashi,

Da gudu Namijin dake bin macen ya Ruga ya Riqo hannun ta ya fara kukan Shagwa6a"Ammi tinka Amiya ko!,Ta Tauka mn new tablet tinda Uncle hoody ya bamu " ya fada yana Share kwalla.


Wacce Suka kira da Ammi tayi murmushi Sannan ta Shafa kanshi tace "Shine kake kuka?,Kaifa Namiji ne Can't you be a man?, kaifa Soldier ne!, Oya share hawayenka kaje ka Kar6o"


Yaron ya share hawaye ya wani kumburo baki a dole an ce mai soldier, ya nufo inda Macen ke tsaye,Saida taga yazo Gab da ita ta arce ya kuma fashewa da kuka.


Daidai lokacin da Wani Mutum ya Shigo da Sallamarsa, Macen tayi Wuri da Tablets din kan kujera ta Ruga da gudu ta Rungumoshi tana fadin "Daddy Oyoyo, Oyoyo daddy, ka ciyo mn chaklat kor?".


Shima Ameer ya Rugo da gudu ya Rungume shi yana fadin"Daddy Amiya bata iya kayatu ba, Kuma ai kashe ba'aka Siyawa DumpBaby ba"

Ameerah ta 6ata fuska tace"Daddy walla'i Amiy ne bai iya kayatu ba kuma Uncle Hoody yashe jaijo Anjima, ijan yajo ka taibayeshi"

Ammie dai tana zaune sai faman murmushi takeyi ,Yaranta na matuqar Burgeta, A koda yaushe idan Ameerah ta 6aro Zance Sai ka Rantse wata babbace Sa6anin Ameer da Akoda yake kaman bawanta ,Sai yanda tayi dashi koda yake Yarinyar kenan......๐Ÿ˜‰


Daddy ya Ciro Chocolate daga Aljihu ya miqa msu yana cewa"wanene Uncle Hoody kuma?"

Ameerah ta 6are chocolate ta saka a baki sannan tace"wani sabon Tahfeez uncle ne, bakaji Kiya'an shi ba,So sweat!"


Daddy yayi murmushi,Sannan yaja kumatunta yace โ€Da bakinki anan kaman so Sweat"

Ya Matsa Inda Ammi ke zaune tana kallonsu sai faman murmushi takeyi yace"Ammin Yara ya dai yau ba magana ne?"

Tace"Eh Bakina da Goro "ta fada tana Harararshi ta Gefen ido.


Ya bude baki da niyyan Yin magana yaji an buga Kararrawan kofar.


Da Gudu Ameer da Ameerah Suka shige Dakin su yayinda Ammie ta jawo mayafi ta lullu6e jikinta, Daddy kuma ya miqe ya Bude kofar.



Wani Matashin Saurayi Wanda Akalla bazai wuce Dan Shekaru 30 zuwa 31 ba ya miqawa Daddy hannu sukayi musabaha, Sannan daddy ya buda mai hanya Ya shigo.


Suka Gaisa da Ammie sannan ya Zauna kan Cushion yana Fuskantar su.



Ammie ta miqe Dan ta samo masa Abin ta6awa.


Daddy ya Kalle mutumin A kaikaice yace" Kaman ban Gane Fuskar nan ba,Amma kai Sabon Zuwa ne kor?"


Mutumin yace"Eh,Nine new Tahfeez Teacher din Children naka"

Daddy yace"Ohk, Lafiya kua? Naga basua barin Teachers su Shigo nan Sai ya zama Dole"


Yace"Eh nima satan hanya nayi Amma dai Da farko dai Sunana(_______) ~guess~

Ni Asalin Dan Nigeria ne Dan Hukumar C.I.D ne Bincike ya kawoni nan, kaman yanda Kuka Sani Gabaki daya Yan Gidan nan Yan daba ne, Amma banda ni Na shigo Cikinsu ne Dan Binciken da Nakeyi " ya Tsagaita Yana Fiddo da I'D card Dinshi cikin Aljihun Rigarshi,ya Nuna Musu


Daddy ya Gyada kai ,ya cigaba da cewa"Na Dade ina bincike akan wani case daga Bisani aka turoni nan Amma duk Fanni daya ne,Abinda ya kawoni nan A gurguje inason na taimake Ku ne Saboda Gaskiya Zaman Ku anan Is very Risky,karkuyi tunanin kuna cikin Farin ciki, Komai zai iya Faduwa daku a lokaci daya,Kuma babu Wanda ya damu daku, Please just tell me me yasa aka kawoku nan daga nan zan San Yanda zan 6ullowa Abin" duk maganan nan yayi shi ne a gurguje Da ka ganshi zaka gane ba ya cikin natsuwa.


Daddy yayi Gyaran murya Daidai lokacin da Ammie ta dire Tray na Juice.


Daddy yasa hannu ya dau cup ya zuba Sannan ya Miqa Wa (Baqon), ya Amsa ya kur6a sannan yace"Ina jinka Alhaji "


Daddy ya kalle Ammie yayi murmushi Sannan ya fara magana kaman haka"Ban fiye yarda da Mutane ba Amma na yaji na Yarda dakai 77% Shiyasa zan baka kadan daga cikin Tarihi na .......Sunana JUNAYD YAZEED mahaifina Asalin Dan Nigeria ne yayinda mahaifiyata kuma Yar Sindhi dake tsakanin Qasar India da Pakistan, Mu Biyu iyayena Suka mallaka a duniya,Muntaso Cikin Gata ,Tun ina da Shekaru 20 mahaifina ya daura ni a harkar kasuwanci,Wanda nake dillancin GOLD,diamond,BRONZE da SILVER,Haqiqah Allah ya Albarkaci Sana'ar Sosai shiyasa Tun ina yaro na zama Billionaire,,Nayi suna Sosai a harkar kasuwancin Gold Ko ina ka zaga a kasuwannin Duniya Ka tambayi JY costen Babu 6ata lokaci za'a Nuna maka ni.


Alokacin da Yayana yayi Aure bashida Aiki Nike daukan nauyinsa da na iyalensa,Baiyi Shekara da Aure ba ya Qara Amarya,Still ban Gajiya ba Nike daukar dawainiyarsu, Saida nayi Aure Sannan na tattaro Dukkan Dukiyana na Raba shi Gida Biyu na bawa Dan Uwana Kaso daya Daga ciki,Shima ya Fantama harkar kasuwanci.


Haqiqah ina Qaunar danUwana Fiyeda Zaton mai zato,Zan iya Sadaukar da konawa ne Saboda shi,Kuma na tabbata Shima haka!,



Ba'ayi Shekara daya ba Dan uwana ya Shahara Allah ya Buda Mashi shima,Yama fini Arziqi kuma yayi suna Amma ba kaman ni ba.


A koda yaushe nine na Gaban Goshin Mahaifiyata Shiyasa lokacin DA nayi Aure kaunar da take Nuna mn ya Shafe Matata,Hakan ba qaramin Jagula lissafin Matan yayana yayi ba Suka hau kishi da ita Sai kace itama Kishiyarsu ce.


A Halin yanzu Inada 'ya'ya Biyu achan mace daya namiji daya wato Munayferh da ABDULRAHMAN ,Duk Suna Hannun Dan uwana ne, yaran Sun kasance basuaji Barin ma ta farin Saboda tafi samun Goyon bayan Mahaifiyata da danUwana ,Shiyasa take Sheqa tsiyarsa Bata Ganin Girman kowa a Gidan Harta mu Iyayenta ta Raina mu bata dauke mu da wata mahinmanci ba,Tafi son Dan'Uwana da Mahaifiyata saboda a cewarta sunfi Sonta.


Ba daman Yarinyar tayi laifi Babu mai hukunta ta yanzunnan sai Rayuka Su 6ace.


Akwai babban Dan DanUwana wato Aaryaan shine mutum na farko da ya Fara hukunta ta Har ta fara natsuwa.


Lokacin da ya je Pakistan Karatunsa A fannin likitanci, yana dawowa ya ganta Da Shigar banza Dukda A lokacin bai wani Ganeta ba,Ganin ta Fito daga Cikin Gidan mu Anma Saida ya Hukunta ta hukuncin da ban ta6a tunanin Akwai Wanda zai ta6a yi mata irin Wannan ba,Dan Saida ya zaneta kuma yasa ta tattaro duk qananun kayanta ta qonasu da hannunta,Shiyasa nayi mishi kyautan Gidaje har Biyu manyaยฒ A cikin Garin Kaduna da Zaria,kuma na bashi Company daya daga cikin Companies dna na Nigeria.


Abinda nayi Ba karamin tunzura Zuciyar Yarinyar nayi ba dan Saida ta rama yanda yasata kona kayayyakin ta haka ta Sa shi Qona Company dinda na bashi da Hannunshi batareda yasani ,Saboda Yarinyar Bata barin bashi, daganan Tsana mai tsanani ya kullu Tsakanin Munayferh da Aaryaan.



Akwai wata Rana, Ranarda Bazan ta6a mantawa dashi ba A Rayuwa na Ranar Jumma'a Na dawo daga Masallaci Dama Ranar Wani mutum ya siyar mn da DIAMONDs ,Na saka Shi cikin Akwatin Gold na Adana cikin Motar.


Ina Tafe a mota Sai naga wata Ma'aikaciyar Asibiti Sai Gudu takeyi Jikinta yayi jinajina Duk jini yabi ya 6ata mata Farar kayan dake jikinta da Alama Binta akeyi za'a kashe,Ga kuma wata File a hannunta.


Tana kaiwa wani Guri naga ta Daga wata qatuwar dutse ta saka File din a qarqashi, a lokacin kuma naga Mutanen da Suke Binta Riqeda Adda, Fuskokinsu Rufe cikin Baqaqen masks.



Dama tuni na Farka can gefen hanya,Na Ciro wayana na fara Video coverage, Har suka kasheta basu Ankareda ni Dan ina Dan nesa dasune Amma ina iya Ganin komai,bayan Sun kasheta Suka Yi gaba da Gawar ni kuma na Qaraso inda Na ga ta Daga dutse jiki na Dauko File dinda ta Ajiye.

Na bar wajen jiki na Rawa, ba tareda na duba ko na Karanta Abinda ya qunsa ba,Ina isa Gida na Saka File din cikin Akwatin Gold mai kunshe da Diamonds dinda na Sayo,



Abin mamaki daga lokacin Matar DanUwana ta Biyu wato Rabi da 'ya'yanta suka Fara liqe min Suna shiga harkana Abinda basuayi a baya,Sai daga baya na gane Ashe hankalin su na Gurin Dan Akwatin Gold dinda nake adanawa ne!.



Sai nasa Aka hada min irin Akwatin Sak Amma ba na Asalin Gold ba,harda Fake Diamond Sannan na saka Empty File a ciki na Adana ,Na Dauko Real one din na bawa 'ya ta Munayferh ta riqe min Amana ,nasanta Duk iya shegenta bata wasa da Alqawari da Amana Shiyasa da wuya tayiwa mutum Alqawari ko kuma ta dau Amanar wani.


Amma Cikin ikon Allah Dukda Rashin son da take Nuna min a lokacin ta Kar6a kuma na tabbata ta Adana a Waje mai kyau,Man karkace na cika zuzuta 'yata , ta chanchanci hakan ne,Abinda yasa na bata kuwa shine Saboda Nasan Har Abada in bani nace ta bani ba bata ba kowa, Ko kasheta za'ayi kuwa, babu Wanda yasan da hakan Harta Wifey" ya fada yana duban Ammie.

Ya cigaba DA cewa"Bayan Shekara daya da bata Ajiyan Muka zonan 'kasar LAOS yawon Shaqatawa da niyyar idan Matata ta haihu Zamu koma Garin mu,Dama a lokacin tanada juna Biyu,Ranar da ta haihu Ranar aka zagayemu da daddare aka Fitar damu zuwa wannan Gidan, babu Abinda babu A gidan,Amma fa akwai tsaro na tashin Hankali,Bansan me mukayi aka kawo mu nanba ,Na dai San ako wane qarshen Wata sai An kawo mn waya ansa na tura 1m Zuwa accounts dinsu Amatsayin kudin Kula damu, Amma ba'a yarda mu riqe waya ba,Saidai Suzo da wayan su idan Zamu tura musu kudin Su saka Sim dina ko a ina suka Samu oho, Muna zaune anan Tsawon Shekaru Biyu kenan, Yaran DA Matata ta Haifa mun sanya Masu Sunan iyayena wato RAHMA da YAZEED muna kiran su da Ameer da Ameerah.


Babu Abinda muka nema muka Rasa daga mu har Yaran namu kuma suna Karatun boko da na islamiyyah duk a Gidannan, basu ta6a fita koda Soron Gidan nan ba saboda tsaro.



Amma akwai Wata rana da Shugaban su yazo yace min in Sallame iyalina su maida su Guda wai Ba dasu suke case ba,Amma fafur taqi amincewa Wai Gani take kaman idan ta koma Kashe ni zasuyi,ni kuma Harga Allah na damu da Nasan hakinda Yarana suke Dukda Nasan Dan'uwana zai kulada Su Iya Gwargwado Amma Tarbiyyansu na Kan Scali Dan Nasan bazasu Sami kyakkyawan Tarbiyya daga Gareshi ba..


Daddy yana kaiwa nan ya Tsagaita yana Duban baqo, baqo ya dubi Agogon bango yace"nagode Sir, bayanenka Zasuyi mana Amfani matuqa, kuma inshaAllahu zan fadawa Shugaba a maida Madam Gida Saboda ta Samu ta kula da 'ya 'yanta nachan ,kuma atleast She can help us with some informations Wanda ya danganci Gidan Dan na fara zargin Wancan matar Yayan naka Rabi take ko waye da sa hannu Cikin wannan Lamarin ,Kuma bayananka zasu taimaka mn wurin Gano Asalin mai gidan nan Wanda bamu sanshi ba haryanzu, nima shine musabbabin Zuwana Qasar nan.... I think time yayi bari na wuce ,Nayi Gabas" ya fada yana Miqewa.



Har bakin kofa Daddy ya Rakashi Sannan ya dawo inda Ammie ke zaune ta zuba Uban tagumi,Tabbas tana Kewar 'ya'yanta Sosai zata so ace ta koma tana kusa dasu ko Dan daidaituwar tarbiyyansu, Amma ya za'ayi yabar mijinta a wata qasa,'kasar da batasan kowa a nan ba?....


Maganan daddy ne ya Fargarda ita daga tunanin da ta shiga yace"Jeederh!, "

ta dago ta kalleshi yace"kin daiji Abinda yace, Am sure he gonna help us ,Shiyasa na yarda na fada mishi,Secret Wanda ba kowa ya Sani ba,Just do as he said,Gobe ki bisu Ku wuce dasu Ameerah, Suma Zasu fi samun Sakewa Fiyeda haka in suna tareda danginsu"


Ammie ta kasa cewa komai ta fashe da wani irin kuka mai Ban tausayi tanaji tana Gani haka zata bar Mijinta A wata kasa ta daban Wanda bata San~ Koda Hanyar nan ba............




Tho bari mu leqa 9ja mana๐Ÿ˜‹




WasheGari

Tun 3:30am na dare na Tashi da wata Matsanancin zazza6i, A daddafe na Miqe na nufi Falor Anan na Ganshi kwance ya Ra6e guri Guda.


Tunawa nayi da Ruwan da ya watsa min Jiya dadaddare ,Sai na nufi Fridge Na Dauko Ruwan Gora mai Sanyi Sosai na Bude murfin Goran ina yatsine Fuska na Antaya mashi Dukka Ruwan a fuska, A gigice ya Farka yana Zaro ido ni kuwa nayi daki da gudu na Sa makulli sannan na zube 'kasa ina maida Numfashi Saboda yanda Zazza6i ke cina....



Nan take barci ya Qara Awon Gaba dani.


Ban Farka ba Sai qarfe bakwai DA rabi na safe A lokacin har ya Fice a Gidan,Nima Na fada Bayi na dauro Alwala nayi sallah.


Fitowa nayi ina dafe da kaina da yakemin kaman zai Tsage Saboda tsananin Ciwo na nufi, Gate nacewa Maigadi ya Siyo mn maganin Sauke zazza6i idan yaaAary ya dawo zan bashi kudin shi, Babu musu yaje ya siyo mn Na Sha, ina mamaki yau Duk rashinson magani na Nike siyan magani akan zazza6i๐Ÿ™‰.

Ina Gamashan maganin na 6ingire da bacci.



_________



Shi kuwa tunda ya tashi yaje masallaci bai dawo ba direct Gidan shi ya nufa Dan Hankalin shi ya fi karkata a chan, Bai ma San Umma na Gidan ba fa๐Ÿ˜„.


Yana Shiga ya kwalawa Ramlah kira"Wifey we're u am back"


Chak ya tsaya Ganin Umma zaune a falo ya wani Hakince a kan kujera sai wani fadi takeyi tana kumburewa tareda Hure hanci๐Ÿ˜Œ













TOH MASU SON SANIN INDA IYAYEN MUNAYFERH SUKE HOPE NA FITO DAKU DAGA DUHU?๐Ÿ‘‚๐Ÿผ


WAI SHIN WANENE WANNAN BAQON?, MEY SUNANSHI?(DUK WACCE TA CINKA ZAN BATA KYAUTAN NAIRA BIYAR)


Waiting for your comments..........

A cigaba da Wanke hannu.


Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ


Wattpad @fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ
8th September.๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 27_*


_*Masha Allahu Hakika jiya naga Ruwan masoya ta koina naji dadi sosai da sosai Ku zage kara himma wajen karatu da comment nikuma zan zaqe wajen Faranta muku Akoda yaushe Allah ya bar Qauna ta har Abada๐Ÿ’–*



Godiya ta musamman Ga Alisha Wacce ta Samu nasarar Lashe Tambayan Jiya, ta fadi Sunan Baqo wato SALEEM tsohon saurayin Ramlah๐Ÿ’–๐Ÿ’–

______________________


Ramlah Jin muryan Aaryaan yasa ta fito da fara'ar ta, saidai Tana isowa falo taja ta tsaya Chak Dan Gaba daya ta manta Umma na Gidan.


Kallon kallo aka shigayi tsakanin Ramlah da Aaryaan.


"Keh,Me Nake Gani haka?" Umma ta fada cikin Tsawa.

Ramlah tayi hanzarin janye Idanta daga Kallonshi ta maida kallonta Ga Umma wacce take Binta da Kallon tsana,Da hanzari ta Kawar da kai Gefe jiki na Rawa ta koma daki,


Aaryaan ya Sauke Ajiyan Zuciya ya karasa inda Umma ke zaune ya zauna Qasa Gefen kafarta,Sannan ya gaidata,Ta amsa mai ciki-Ciki,Ya Kwantar da kansa Bisa Cinyarta Cikin Shagwa6a yake fadin"Haba Umma,Dama kinzo shine ko ki fada mana zakizo?"

Umma ta Ture kansa da ya aza bisa Cinyarta tace"Tunda MaraAsalin chan ta Mallake mn kai, ta saka Gujeni yanzu ai bana Gabanka,Aaryaan Wai yaushe ka zama haka ne?, har ni zan kira ka kaqi daga min waya Saboda Kar na Rabaka da Rabin Ranka kor, Tho ni da kake Gudu na Dawo Gidan nan da zama Har sai Alhaji ya dawo ,In ka ga dama ka dauketa Ku bar Qasar ne ni kuma bazan Gajiyaba Duk inda kuka Je ,Ku sa a ranku kaman ina Gurin ne Dan Babu makawa sai nazo,Kuma wallahi Tallahi idan ina Gidan nan ko kallon Arziki kayi Wa Yarinyar nan Saina Tsine maka!"


Aaryaan ya dago da Sauri yana duban Umma baki sake, Yana mamakin Rashin Imani irin na Umma,Ya tabbata da Hafsah Ce tayi Aure akae mata haka Sai inda Qarfinta ya qare,tho meyasa zatayiwa Yar wata Akan dalilin da Baitakakarayakaryaba?,Nan danan Tausayin Ramlah ya kamashi Haqiqah tana Haqurin zama da ita maruqah, Tunawa yayi da Munayferh (Amaryarsa๐Ÿ˜‰),ya tabbata Bazata ta6a yarda da Cin mutumci irin na Umma ba,Saidai ayita ta qare..


Muryan Umma yaji ta cigaba da cewa"Ka Kureni da idanu, ko kana tantama ne?,....kai!,Ka kasa kunnenka kajini dakyau idan naji labari koda wasa ka Sake Shiga koda dakinta ne tho ban yafe maka ba...."


Aaryaan bazai iya Jure jin irin kalaman dake Fita daga bakin mahaifiyarsa ba, Shiyasa ya miqe Zubur ya nufi hanyar Fita ba tareda yace mata qala ba.


"Au fita ma zakayi, Dan na isarmaka da Saqon mutuwa ko?" Ta fada cikin karaji,Juyowa yayi ya tako har inda Take idanunnan Sun kada Sunyi Jaa Saboda 6acin rai ya bude baki zaiyi magana, Sai kuma ya fasa ya Dafe kansa dake Sara mshi.


Daidai lokacin Hafsah ta Sauko cikin Shirin Zuwa makaranta, Ganin Umma na kumburewa Ga Kuma Aaryan Riqeda kai yasa ta Gane Umma ta kuma halinta kenan, Da gudu ta karasa inda Aaryaan yake Riqeda kai jikinsa na karkarwa yana tangalยฒ ta Riqoshi zata Zaunar dashi Gudun karya fadi, tamanta idan yana Fushi Baa tunkarar shi,Ta manta idan Yana Baya Ji baya Gani ,

Tana Riqeshi taji Saukar Mari, Yasa kafa yayi ball da ita yana haki ,Tayi Gefe tana Ihu(Daga Taimako?๐Ÿ™„)


Sannan ya tako har inda Umma take Ayau da ba mahaifiyarsa bane a Gabanshi Yau Sai inda Karfinsa ya

Please Login or Register in order to submit comment