Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magidanci mai shekarunka ba"

"Me Kike nufi...."


Ban Isa bada Amsar Tambayar sa ba Wayansa dake Kan desk ta dau Ruri , Hannu yasa ya dauka Ganin Sunan Mai kirani yasa Ya Dan Murmusa hadida Karawa a kunne


"Amincin Allah shi tabbata to d Best and Dha Only Adorable Mum in the world...Ameen Mum...Kai Umma .....Gata nan sai faman Raki yakeyi....wlh jikina ne ya Dan motsa ....ameen ...tho gata"

Yana kaiwa nan ya miqa mn wayan
"Umma nah...ina wuni...Alhamdulillah Ai naji sauqi....aa wlh ......Idan nazo me zaki bani?...No a'a ni gurasa nakeso.... Wasan Ba'a rasa Gurasa a Gidan Kanawa... Yawwa Umma mah , gamu nan zuwa yanzunnan ma kuwa.....bye... A shafa mn Kan yarana...this"


Ina gama Fadin haka na miqa masadaga nan Suka Cigaba da hirar su ,Yana gamawa ya dubeni Hadida Kwa6e Fuska .

"Yunwa Ko"

"Eh wlh Muje Gidan Muma tace ta Bar min Gurasa"

Murmushi yayi mai sauti sannan Ya Daga Ni Daga Kan qafarsa da nake Zaune , Ya miqe ya nufi Wajen da ya Ajiye Food Flask bisa sata 'yar qaramar Table ya sauko hadida Plate, Ya dauraye Plate din Sannan ya bude yana fadin
"Ya Zakayi nabar tilon matata da yunwa Ko so Kike umma ta soke ni Ta tuhumeni da Barin diyarta da yunwa?"

Nimmurmshin nayi hade da kauda Kai


"Wlh bazan Ci ba ,qamshin Abincin na irritating Dina ,Please ka rufe ,Muje Gidan umma Zan Ci anan.."


Ganin da gaske nake ba cin Abincin zanyi ba yasa ya Rufe flask din Yana fadin

"Tho ranki shi dade.... ,yanda kikace hakan za'ayi....An daina 6oye cikin kenan"


Dariya nayi sosai hadida Cusa kaina a kirjinsa

"Ya na iya ,Tunda dakanta ta buqaci ganinah?"

Shima dariyan yayi hadida shafa Suman kaina dake tashin qamshi yace

"Yo da meyasa Kike 6oye mata bayan kinsan Ko badade ko bajima zata gani?"


"Kasan ta hanya daya ake samun Ciki, shikenan Ni da daman Mutum ya ra6eni sai Ciki?, haba Ai da kunya Umma ta ganni da qaton Ciki kwata kwata yaushe na dawo da har zanyi wannan Qaton cikin""


"Sorry babe Indai nine saidai Ki daina zuwa Gidan don haihuwa Every 10mounts Tunda na lura mai saurin Chafkan abun na aura"


Da qarfi na kai mashi duka a kirji cikin shagwa6a hadida Turo Baki.

"Kasheni zaakayi kenan"

"Sorry...Rip in adddy"

Ya fada cikin rada. Cikin qanqanin lokaci muka baro Office din zuwa Gida din amsa Kiran da umma ,Muna fita harabar Asibitin Hilaal ya bi bayani mu Shima Gidan umman zashi ,Har zamu Shige motar na hango janaan tana Daga mana Hannu alamar mu tsaya ,Tsayawa mukayi har ta qaraso ,tana qarasowa tace mana itama Gidan Umma zata (Thopa😲) .

Muna isa Gidan Muka tarar da motoci Birjik a Gidan babu extra Wajen da zamu parka namu Motar , Dole ya nemi wuri ya parka a waje,Kusan a tare duk muka shiga Gidan yana shigaa kai tsaye Duk sukayi Part din Umma ni kuma nayi part dn Ammie nah


na tarar dasu bisa dinning suna Lunch da sauri na nufesu ina Dariya
Naja Kujerar dake tsakanin Ammie da daddy na zauna Ina gaishesu Gaba daya suka amsa mn Cikin sakin Fuska ,Daidai nan Abdool ya shigo janye da hannun Ameer ,Sadeeq da Haseen Dukkanninsu sunana Sabbin Askin FENDI ,

Cikeda takaici nake kallonsa har ya Iso gareki ,Ganin irin mugun kallon da nake zauna masa yasa ya sha Jikin jikinsa, Da Gudu Sadeeq ya qaraso Wajen hadida Rungume ni yana mn oyoyo ,Nima rungumeshi nayi ina shafe kansa ,Shikam.Haseen Ko kallon Inda nake baiyi ba Sai Wajen daddy da yayi ya rungumeshi Fuskarsa nan a hade ,Ta6e baki nayi a Zuciyata nace
_A jininka yake_
Sannan Na maida Sunana Ga Abdool dake Gaida Ammie

"Abdool ,Uban wa ka Tambayata kafin kayiwa yarana Irin Wannan Arnen Askin?...Ance Maka Su din Irin ka ne ?,ko so kake ka 6ata mn yara?"

Dariya yayi sosai hadida Jan hannun Sadeeq ya miqe Daga Jikina

"Aunty kenan ,Ubansu yayi Wanda yaci Uban namu ma bare Mu tashin yau?"

"Kai Abdool, Ka kiyaye kalamanka kasan Dawa nakeyi"
Cewar daddy

"Daddy ka qyaleshi ya raina ni ne ,Wlh inajin qauye zamu kaika mu amra Maka Lantana ko Kuluwa"

"Ta6 Allah shi kyauta so Kike Nayi Irin Mutuwan Su O'O kenan"

Ya qarashe da jan hannunsu Suka fita waje Don ya Lura da mood din Daddy da Ammie sai watsa masa harara sukeyi.

Maida kallona nayi zuwa Kan Ammie


"Ammie wai Me akeyi a gidan ne?, Naga Motoci duk sun Cika Gidan ne,Kuma ina kakus dasu Ameerah ,Halan yawon da suka saba zuwa Suka tafi ?"

Na gaya ina Fincike Gwangwanin Monster na dauko cup na zuba aCiki.

"No suna Part din UMMAN Ku ,Kuma Nima bansan Abinda Ke faruwa a Chan ba ,nadaiga buhun mutane"

"Thopa Allah dai yasa lpy"
Daddy ya Amsa da Ameen

Na cigaba da cewa

"don tsananin Rowa shine ku kuka ke6e anan kuna da'amy Don kar a gani ace za'aci ko?"

Na fada tareda kai Cup din da na zuba Monster din bakina.

"Munayferh yaushe rabonki da Wannan Gidan hala Kinyi batan hanya ne?"

Cewar Daddy Cikin son 6atar da maganar da na faro ,Nima Rashin Amsan Da zan bada yasa na kauda maganar , Na kalle Ammie daketa faman murmushu nace

"Ammie ya naga Kinyi Fresh ,Kinyi 6ul6ul, haske kai harda qiba? ,kodai Cikine dake?".


Na qarashe maganar da Miqewa gudun Unplanned Ranqwashi.


Aikuwa kaman na sani Rankwashin take shirin Bani na tashi da sauri ina daria na fara takawa don Amsa kiran Umma saida nakai bakin qofa na juyo ina murmushi.

"Ammie yaa Aary yace In gaishe ku zai leqo Anjima ,Tare mukazo yana side _din Ummanshi" .


Nan jura vewarsu ba na nufi part din umma ina sipping Monster dina ina jiwo Ammie tana fadin
"Idan kinje karki sake dawowa"


Ina shiga Side din Umma naji Shuru Ga sani Irin duhun da naRiska anan ,Cikeda tsoro na qarasa parlonta Ina zazzare Dan ni harga Allah tsoron Duhu nakeyi sosai
Mamaki ya kamani da Shiga parlon na tarar shima da Duhu dukda kuwa Rana ne


Cikin qanqanin lokaci Cikina ya duri ruwa kasancewa Ni ba mai son Duhu bace, Tsoro da firgici suka mamayeni Na fasa Kuka ,Gudun kar na juya nayi tuntu6e yasa na Tsaya chak jikina na 6ari ,Cikin kuka nake fadin.

Muryan Hasnah baki Cikin Rada tana Fadin

"Keh...move kin taka ni"

Sai na kumajin Muryan munayferhn janaan tana fadin

"You guys should keep quiet I think she's here"

Muryan Hasnah na sakeji Cikin Rada tana fadin

"Yeah she's here but she can here is ,Garnny tace muyi Shuru ke kuma kina sani surutu"

A darare na Kira Sunan Hasnah

"Hasnah.... Hasnaahteey were Are you?....anty amiya Ina kuke on the lig....
"

Daidai nan Haske mai hadeda ihun murna hadida saukan Shinning Papers Wandaa saukan ta sama Gefe Guda kuwa Ifrah de ke fesa mn spray. ...


Cikeda mamaki nake bin Ko'ina da kallo ,An qawata dakin Cikin Decoraiions na Red and white ,Chan saman Bango kuwa wani qaton Band ne mai rubutun HAPPY BIRTHDAY MUNAYFERH" Da manyan baqaqe ,


Many an kujerun dakin ma sunana Decorations da red and black ko ina sai tashin qamshi yakeyi ,

Bin kowa da kallo nakeyi har idanuna Suka sauka akan wani qaton Table mai dauke da wani qaton Cake Shima Red and Black , tsari da haduwan Cake din yasa na kasa dauke idona a Wajen Sai kallonshi nakeyi Cikeda mamaki ganin yanda aka qawatashi

Zuciyata cike take da mamakin Abinda ya tarasu Anan Don har yanzu ban samu amsar dalililin da yasa aka qawata dakin akayii mshi wannan uban decorations na Musamman ba ko ina sai Glittering yakeyi Abun gwanin Burgewa .

Gefe guda kuwa su hafsah ,Janaan ,Ifrah ,Humaydah Da Ramlah da ma duk mutanen da suka Taka rawan Gani Cikin abarin nan na hawanjinina Ciki kuwa harda nasal , Hadeeza da Talatu kishiyarta *(Banda Jeoboi ,Fadeelah da abba da mazan suma don basua Kusane) suna zaune ssai faman dariya sukeyi Gefe Guda kuwa dukka yaranmu ne zaune tareda su Abdool suma dariyar sukeyi baki Bude nake bin kowannen su daidanu.

Ji nayi an kamo hannuna koda ban juya na ganshi ba na gane Launin hannunsa.

Cikeda natsuwa da qasaita yajani har izuwa Kujeran da aka tanada sbd ni ..


Ina zama ya ranqwafo saitin Kunnena ya rada mn *Happy Birthday Mere Patnee, we Insinuate these for ur birthday and our 7th anniversary....."



Daidainan wayansa dake Jikin aljihunsa ta dau ruri , Saida ya katse sannan Kiran ya qara shigowa kamin ya daga hadida amsa sallamar da a keyi masa.
[1/5, 5:24 PM] Fahnaaan❣️: "Mashhaalllh ,Me aka samu ?....allah ya rayata.... gatanan....haba Babu komai...
My regards to amaryan qarni bye"


Sannan Ya katse wayan ya dawo kusadani ya zauna ,ya kamo hannuna Cikinn Coolvoive dinsaa yace

"Albishirinki?"

"Goro?"

"Fari ko jaa"


"Fari qal"


"Matar Jibril(jeeboi) ta haihu yanzunnan yake gaya mn"


Wani irin Tsallen murna nayi na rungumeshi daidai nan , Su Kakus da Aunty salmah suka shigo sannan Umma ta mara msu baya hakan yasa babu shiri na raba Jikina da nasa ina Wani irin sunkuyar dakai irin an Girman nan😉 ,Gaba dayansu Suka zauna Bisa 3seater Nima miqeqa nayi Daga Inda nake Zaune na nufi Wajen Umma .

Cikin sakin Fuska nake gaidata Itama amsawa tayi Cikeda tsantsar So hadida kulawa Wanda na Tantancesu Cikin kalamanta.

"Umma Ina gurasa na? ."
Murmushi tayi hadida shafe fuskata

"Kwadayayya Kice Abinda ya kawoki kenan"

Dariya nayi cikeda Jin nauyinta
"A'ah Umma, Dama ina Son zuwa ..."

"Haka sai kikace na lura bason ganinmu kikeyi ba rabonki da gidan nan har na manta wlhy , ko nayi mki laifine?"


Juya kaina nayi alamar a'ah

"Tho meyasa bakison zuwa kodai nice nakison Gani ko?"

Ta qarashe Cikin rauni, hakan da tayi ba qaramin kunya tabani ba.

Nasa tafukan hannayena na rufe fuska ina Murmurshi.

"Umman Mu kinsan Dalilin da yasa ta daina zuwa Gidan nan kuwa?"

Cewar Ramlah ta fada Lokacin da take zama Kusada Umma.

"A'ah meya hanata zuwa?"

Da sauri na dago ina roqonta da idanu amma don tsabar mugunta Saida ta gaya

"Wai Kunyarki takeji ,Bataso ki ganta tanada Ciki"

Ta qarashe da dariyar Mugunta.


"Aunty Magulmaciya Tunda kin fesa sai Ki tashi ki bar mana Ita ita ,Kije Ki nemi naki"


Janaan Da ta iso wurin ta gaya Tana Ture Ramlah Cikin son zama Kusa da umma.
Ramlah ta riqe ha6a "ohh Masu Uwar mini manja ,Muda bamu dashi Allah ya bamu"

"Ba Ameen ba" ,Na fada ina Yi mata qwalo


Ita dai umma Kallonsu takeyi cikin Burgewa murmushi manne a fuskarta .

Cikin Nasara kuwa janaaan samu ta tureta Ramlah zauna Kusada Umma.

"Umma nima next week ne Birthday dina Zaki hada mn Irin cake din nyfee?"

Wani ubar Harara nace

"Sannu sara Kin dauka matsayina dake daya ne a wajenta da zakice a yi mki irin nawa?"


"Ehwnn..sannu Ai ni nafiki matsayi a wajenta keda kike matar 3k?"


"Inye Lallai ma wannan Yarinyar idan baki sani ba bari na gaya mki, itace Sanadin Auren mu na titi"


Umma ganin Na fara shan corner Gudun kar nayi 6arin baki yasa ta dakatar damu.


"Duk ku dakata ya isa haka ,Badai cake ba?,ku kwantar da hankalinku....zanyi ma gaba dayan ku biyun inshaallah"


Cikeda tsantsar Murna Muka Rungumeta tareda manna mata peck a Forehead Sannan a lokaci guda muka furta.


"Our Mother inlaw is the best Inlaw in the world"


"Ohh na Shiga Uku ni Rahmatu ,Munayferh Mai Zan Gani haka?"
Cewar kakus lokacin da idanunta sukayi Arba Dani .

Cikin sauri na Saki Umma ina kallonta Cikeda mamaki nace

"Ke kuma tsohuwa Lafiya ,Kodai ysufan ne ya Fara Ta6a saman ?"

Na qarashe da Nuna Kai Irin nervously dinnan.

Dariya tayi Wanda ya bayyana Haqoranta Uku da Suka rage Cikin 'yar bakinta a gware take dafa hannayenta tana cigaba da sheqa dariya Wanda yasa na Dan tsargu

"Na shiga Uku Allah na Tuba ,Ni tsohuwa Tunda Allah ya bani tsawon Rai bazai hanani ganin Abin mamaki ba In ban mutu ba Sainaga Dinga ganin Abubuwan Al'ajabi Kala kala , Yanzu uwata ,kwata kwata yaushe Kika dawo Aka kaika Gidanki?, Dududu baki wuce Watanni takwas ba fah Cikinki shafai ,Amma sai gaki yau Da wani qaton tulu a Gaba kaman Amalanke,Ni wlhy da na Fara ganinki har na Tsorata ,Ohni yau naga Aikin Yaran zamani ,in fada miki mu a lokacin Mu ko kinyi aure Sai kinyi sh..."


Fahnaan:----"Tsohuwa Please Kiyi Shuru in Rufe Littafin nan😢😏"


Gaba dayansu Suka saka Dariya don Maganganun Kakus ba qaramin Dariya ya basu ba.

Da sauri Abdool ya juyo ganin ina shirin Rufewa

"Wait Aunty Fahnaan, Ni baza'a aurar dani bane?, kuma ya kike shirin Rufe littafi batareda Kin bari auty munayferh ta haihu ba?"



Fahnaan:-
"Au na manta , Amma nasan inshaallah nan da few months Nyfee zata haihu Kuma nayi mata scanning na tabbata mace zata haifa tho idan ta haihu Don Allah asa mata sunana(Fateemah)😟, Kai kuma ai tuni na baka humdah......"

Teemah itama ta tareni da fadin

"Hana aunty ,Kin bawa wannan qanqanin Abun yarinya Nifa?,ko so Kike in mutu a gauruwa?"

Dariya nayi hadida Nuna mata hydar Mijin Humaydah
Nace

"Idan zaki iya manage da wanchan"

Daga nan na Arta a Guje don bana son Damben ta ritsaani

Ina Fita naji an kunna wani cool music Mai taken in my feeling waqan Drake Sannan Aka fara shagali🎊🎉. ..






*Alhamdulillah*



godiya ta tabbata ga Allah madaukaki, mai kowa mai komai, mai yadda ya so kan wanda ya so, ko ana so ko ba a so. Gare ka ake neman komai, ba ka neman komai wurin kowa, kowa ke neman komai gare ka. Allah mai baiwa baya gajiya, baya bacci, baya cuta, baya jinya. Allah mai biyan bukatan komai shida baya bukatar komai a garemu , Allah ka biya mana bukata.
Tsira da amincin Allah su tabbata nan ga Rasulu mai haske da daukaka , mai kyawu da martaba, cikakke a halitta a zuci har a jiki Shugaban talikai, cikamakin annabawa Muhammadu dan Abdullah dan Amina fiyayye. Mai kyauta mai sadaka mai tausayi mai kunya. Ba a yi ba baza a yi ba wani taliki kamar sa.
Muna godiya ga Allah da ya kawo mu wannan rana Da na dade ina jira na kawo qarshen wannan Dogon labari.


YaAllah alkhayran dake Cikin wannan Littafin yaAllah ka Albarkace mu dashi ,Ka nesanta mu da sharrin dake Cikin ta .


Godiya ta musammanga mutanen da suke bibiyar wannan Labarin tun daga farkonta har zuwa qarshenta ,Irinsu Aunty hafsee ,Ummu Ayrah ,Sis hawwa baba, Yaseerah , Saudey ,Saratu Garin ,Saleema Bintu ,Fatee takwara k Abdool ,Etc... ya alllah ka biya masu buqatunmu gaba daya ,Masu jinya marasa lfyn mu ya allah ka azurta su da lfy mai dorewa masu 2bodies Ya allah ya saukesu lfy Masu damuwa Aallah ka yaye mana gabaki daya Masu Neman Haihuwa Aah ka Azurtasu da Mafi Alkyari ,Allah ka biya mana Nuqatun mu na alkyari #Ameen.






*#And lastly*

Ina masoyan Littafin Ma'esherh (littafin da na fara na kasa Qarasawa💔😂) ?, Ina farinCikin sanar daku inshallahu zaizo Muku a next novel dina ina nufin zan Shigar dashi Cikin novel din ya zamo abu daya Yanzu nomore littafin Ma'esherh kenan😎.


Sai Mun hadu a sabon Littafina wato ~Maqaryaci~(Fakelife)
Labarin dake dauke da abubuwan dake faruwa a wannan zamanin nmu wato Rayuwan qarya da son Infi wani ,Etc...





Sai.mun hadu kawai







Nayi gabas🚶🏻‍♀️🔚🚶🏻‍♀️🔚

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment