Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

بسم الله الرحمن الرحيم...


*_Chapter 9_*

"Da ya kiraki Sai Akayi ya" Malam manseer(HOD) ya fada cikin zaquwa.

"Shine Yace na bashi kaina,in kuma na qi,Zai Cire Sunana a course din gaba daya ko Sai dai ta maimaiawA har 400L, kuma Wlh da gaske yake ko yau Da na duba class list babu Sunana Aciki...." Ina kaiwa nan kuka yafi qarfina (kaman da Gaske🙄)

Ba Malam mansir ba harda Jaanaan zaro ido Sukayi suna Jan Salati
"Innalillahi wainna ilayhirrajiun,Sorry Munayferh, bi'izinillahi sai an bi maki haqqinki,Wannan Cin zarafin yayi yawa,da ba don Allah ya tsare ba Ai da ya Lalata Miki Rayuwa, yanzu Shekarunki nawa ne?"

"Seventeen" na bashi Amsa a taqaice

"OMG,This is child molestation, he molest a child kuma yana neman Yi mata barazana Ga karatun ta!, wannan wani irin Rashin imani ne?, Don't worry Dear Inshallahu zan kai maganar sama Dan wannan case din ba qarama bane,Sai an bi miki hakkinki,Take care of Ur self"

Dadi ya lullu6e ni,Ban iya cewa komai ba,Sai jaanaan da Taketa yi masa godiya,
Zamu tafi najiyo muryanshi yana tambayana "Munayferh Har Yanzu Dad dinku Shuru?, ko kunsami wane bayani dangane dasu ne?"

Ban Amsa mishi ba Dan na tsani Ayi min maganan iyayena, ba Dan zai taimake ni ba da na yarfa mishi magana.

Ganin bazan bashi Amsa ba yasa ya shige office dinshi yana mana Allah kiyaye

Kallo na janaan tayi cikeda mamaki tace "Nayfee, wane lokaci KS ya kira ki office din sa ko dama jiya bayan mun Rabu kin Dawo School Dinnan ne, ?"
Ta fada lokacin da take tada mota

Nace "Aa,ko daya Sharri nayi masa "

"Raunukan Face dinki fa?,kuma kince ba accident kikayi ba"

Kawarda zancen nayi da cewa"Muje Office Din kS,"

Babu musu ta juya Akalan Motar Zuwa Science Complex inda Office din KS yake

Fitowa nayi daga mota daqyar ina Dingisawa na Shiga office din babu ko Sallama ,Ganinshi nayi da wata Student Suna Dan kus-kus🤤,

A Razane Duk Suka dawo hayyacinsu, Student din ta dau Jakarta da mayafin ta ta fice tana Sunkuyar dakai ,Sai da na Kare mata kallo kafin ta fice Dan inna ganta A hanya Gobe Zangane ta ...
Muryar KS naji cikin Hayagaga yana fadin"Ke wace irin mahaukaciya Ce,Ya Zaki shigo Mana babu Sallama ko..."

Hannu na daga mishi"Hey man Kar kamin borin kunya anan, Ba wannan ya kawoni ba, Class list dinda kasa Aka cire Sunana ka tabbata yanda Ka cire Sunan nawa haka Za'a cire Sunanka A jerin ABUlecturers, na fada maka hakan ne Dan Tun wuri ka fara Neman Aikin yi ko dako ne Dan zaifi Rufa maka Asiri" Ban tsaya jin ta bakin sa ba na fice Nasan na Barshi da Takaici da Tunani kalakala......

Ina Fitowa na Sami Janaan Tana jirana a mota ta tambayeni "Me kika gaya masa?"

"I cant Talk anymore, Bakina na ciwo", na fada ina lumshe ido Daidai lokacin da Ya'ya'n cikina Suka Nemi Nasu haqqin.

" Jaan ,Yunwa nakeji"
"Sai kiyi haquri in mun Kai Asibiti kici"
Na Dan yatsine fuska "Janaan kinsan me ya faru dani?"

"Aa saikin fada " Ta bani Amsa cikin Zakuwa Dan ta kosa taji musabbabin Raunukan Danaji

Nace"Yaa Aary ne yadan Ta60 ni Dan na Ari motarsa..........nan na bata labarin duk yanda Akayi Harda Zuwana Kaduna Da Abinda na Aikata Wa Su Suwayba.

Harga Allah Na bata dariya, yanda nake bata labarin Kaman ta Sani dole ina Wani yatsine Fuska Alaman Inajin jiki Sosai, Amma kuma Abinda Yaa Aary yayi ya matuqar burge ta kuma ya bata haushi. Dan Ita ma Shaida che Akan Yanda na Rainashi, Mutuminda bayason Raini da yawan magana na maidashi kaman zoben yatsa na, Dukan da yamindai yadan wuce kaida.
Amma Sai ta dake ta hadiye dariyar ta "Subuhanallahi,Allah sarki,Amma dai yaa Aary bai kyauta ba Sannu, Kinga yanda Fuskan ki ta kumbura kuwa?,Sannu kinji"

Haka tayi tamin Sannu har muka Iso Asibitin.

Kamshin turarensa da naji yasa Gabana Faduwa,na Zaro ido "Na shiga uku,Janaan ban makullin motan nan"
Mika min tayi na Amsa Sannan muka Shiga ward din da Sallama.
Zaune yake Gefen Bed yana latse waya
Jin Anyi Sallama yasa Shi dagowa yana kallon mu.
Ya Amsa Ahankali,Idonshi Akaina, Ganin ko kyaftawa bayayi yasa nayi Tunanin ko ya gane Na qara daukan Keyn motarsa ne,Gudun kar ya Shammace ni kaman na jiya ,yasa na juya Zura A guje nayi Karo da mutum kaina ya bugu,

Na Rintse idoTareda Dora hannu A kai cikin Tsoro (Duk Dauka na ya Biyonine ya buga kaina da bango)
"Wayyo Dan Allah yaa Kayi Haquri,Wlh Bazan kara ba" Dariyan da naji anayi yasa na Ware idanu na

Hafsah,Abdool,Umma da Ramlah na gani A bakin kofa Sai Faman Dariya Sukeyi

Baki na turo baki ina Hararar Su "Dariyan fa?"
Basu tanka min ba duk Suka Karasa Shigowa Sami wuri Suka zauna Suna min Ya jiki?, nima Karasowa nayi na sami wuri kusada Abdool na zauna ina turo baki

Aaryan ya Dan kalleni"Keh, ina kika tafi dazun?" Banza na mai Dan ba keh Suna na ba!

"Keh, bakia juna ne?,Nace ina kika je?"

Shareshi na sakeyi ina bude kulolin da Hafsah ta Shigo dashi "Kash,Meyasa kukayi Rice da Safe?,Gaskiya bazanci ba, Haka kawai Mutun ya dinga Durawa ciki Shinkafa daSanyin safiya?"

Muryan Umma naji tana cewa " Ja'ira, kedin me kika iya da har kike da za6in Abinda zakici?,Idan bakici ki koma Gida Ki girka da kanki Dan baki bar mana Ajiyan bayi ba EHE"

Tsaki naja Na cire hijab din jiki na Dan na farajin Zafi-Zafi na Kalle Abdool nace"Tweeny Me kukaci da Safe?,Saida ya Dan Sace kallon Umma Sannan "Ni tea bread And Egg naci,Umma kuma Tea bread plantain Egg and potato taci, Anty Hafsah kuma Irin nawa Aunty Amarya kuma Rice kuma wlh ita ta Girka dukka Umma sai masifa takeyi" Gaba daya dakin Tsit akayi Ana Sauraron bayanin Oga Abdool harya Dasa Aya
Komawa nayi na kwanta Saman Gado ina cewa "Au abincinDaban daban ne? Toh Nima A nemo min Irin na Umma in bahaka ba ,Inqi Cin komai kuma Kusani Ni Amana ce a gare Ku, kuma Akwai hisabi RanarGobe qiyamah,Zaku Gaya ma mahalicci yanda kuka Riqi Amana ta"


"Ke dallah Rufewa mutane baki, kina maganan Amana nawa iyayen naki Suka bari na rikon Amanarku keda munafukin Qanin naki?" Umma ta fada hakan cikin masifa

Turo baki nayi nace"Wlh qani na ba munafiki bane,Kuma kina nawa iyayena Suka bari na kula dani?, Ina ko dukiyar da Mijin naki yake taqama dashi Na uba na ne!,Ni wlh Anemomin Abinda zanci yunwa nakeji" nakarashe magana ina turo baki tareda Wulla Qafa kaman zanyi Kuka.

Tsawan da Aaryan ya Daka min yasa na natsu ba tare da na Shirya ba.

"Enough!, Are you Talking to your mate?,Da tsarar ki kike magana?" Na girgiza masa kai Alaman Aa, ya cigaba da cewa "TundaShinkafan ne bakison ci Toh dole Sai kinci Shi,hafsah zuba min Abincin cikin Plate"

"Wlh bazanci ba, kum...." Ji nayi Ya yakico ni na fada jikinsa, Dai dai lokacin da Hafsah ta miqa masa plate Din Abincin hannu daya yasa ya kar6a ya Ruqe ni da dayan Hannun , Ya dibo Abincin cikin Spoon"Oya Open Ur mouth"

"Waiy,Please ka Sakeni Zanci da kaina"

Yasanni Sarai idan nace bazanyi Abu ba to bazajiyi ba, Koda Abinda zanyi na ceton rai ne ,Kara Matsoni yayi jikinsa yayi "Ko ki bude baki ko Ranki ya 6ace"

"Wash bayana ka Fama min Ciwo na"

Ganin ina 6ata mishi lokaci yasa ya janyoni na Fada lap Dinsa Ya Sa kafa ya danne kafa ta ya Riqo hannayena da Hannu daya bai damu da ciwon da ya ke fama mn ba, Haka Ya matse ni ya mn dure ina ihu yana dura mn, da zarar na bude baki zan Tsala ihu sai ya Saka mn a baki, Gashi abincin nada yaji Wayyo baki na zafi 😩, duk nabi na6ata shi da Majina da Hawaye.

Gabaki Dayansu Ido suka Zuba mana banda Ramlah da kanta ke sunkuye tana wasa da Yan yAtsun hannunta ,Umma Sai Faman murmushi take Ganin Ramlah ko dago kai ta kasa yi bare ta kallemu.

Saida ya Tabbata Babu Sauran Abincin da ya ragu cikin plate din sannan ya Sake ni, Aikam Yana Saki na nayi Hanyan Bayi ina Share hawaye ,Sai naji Amai na Taso mn,Da gudu na koma baya na Rungume shi Tare da Shar6a mishi Amai🤮,Duk nabi na 6ata masa Riga, Sai da na tabbata Babu Sauran Abinci A ciki na Sannan na cikashi nayi Toilet ina maida Numfashi kaman wacce tayi Tsere da jemage🤨.

Umma ta Rafka Salati "inna lillahi,Amma Yarinyar nan Anyi, makira, Wato intace batason Abu baa isa A mata Dole ba kenan"Haka tacigaba da sababi Babu Wanda ya kula ta
Jikeda takaici yake kallon jikinsa yana yatsine fuska da ba dan Umma da ta Rantse Akan Shi zai zauna dani HarAsallamo ni, kuma idan ya fita koda nan da kofar Asibitin ne batareda Ansallamo ni ba tom bata yafe ba,

wayansa ya Ciro daga Aljihun Rigarshi Ya latse wani number Ahankali yayi mgn ,So banji me yace ba🥴, 10minutes Tsakani Saiga Doctor ya shigo tareda Wata nurse hannunta Riqe da Leda ta miqa masa ya kar6a ya Shige extra Room Dinda ke Dakin .

Ni kuwa Saida nayi wanka na cire bandages dinda Aka jera min Sannan na fito.

Kallona doctor yayi Yana cewa " Mashaallah Jiki ya warware kenan,inshaallahu,Anjima zaa Sallame Ta"
Jin An Ambace Sallama yasa na zum6uro baki"Doctor ni gaskiya bangama warkewa ba".....




No dogon Turanci
Just comment😇

Bye



Fahnaan

22-Aug
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

بسم الله الرحمن الرحيم...


*_Chapter 10_*

Doctor yace "Calm down Ai kinSami Sauqi,Tunda kina iya Tafiya, Saidai ayi Anyother treatment a Gida, Inshaallahu 1:00pm zamu Sallame ku".

Bance komai ba har ya Gama Bayaninsa ya Fita.

Ganin Duk Sunyi Tsit babu mai magana (Ni kuma na tsani zama Wurinda ba'a magana), yasa na kalle hafsah nace " Ke yau bazaki school bane?"
"Eh, sai gobe"
"Ta6 Ai mu mun je School din Tunda Safe, Har munyi Settling matter da KS dawowan mu kenan ma, ko janaan"Na fada ina kallon janaan

Umma ta sako baki "Qalya kiri-kiri a Filin Allah, ke da ko Takawa daqyar kikeyi ina kika Sami Qarfin Zuwa wani makaranta?"

Katseta nayi ta hanyar daga mata Hannu nace"Umma ni fa ki daina Sako min baki in ina magana Ehey....Wash". Na dafa kaina jin An rankwasheni ,Na dago Dan ganin wanda Ya rankwaahen, Yaa Aary na gani Tsaye yana Gyara Tie din wuyan Rigarsa (Ashe Kaya Nurse Dinnan ta bashi a Leda yaje chanzawa)

Zaro ido nayi na kama baki na "Wlh bada ita nake ba!"
Kwafa yayi ya juya Yana kallon Umma"Mum ya Zaki Ringa Ruba idanu Yarinyar nan tana cha6a miki maganganu San Ranta?, Haba mana, Ni in Shakkar Hukunta ta kike ki barni da ita Duk Randa Ta Miki Rashin Kunya na kamata Saina kusa kashe ta.

Muryan Abdool Sukaji Cikin Dariya yace "ka kusa kasheta ita kuma ta kasheka gaba daya ba" Gaba daya Juyawa Sukayi Suna Kallonshi Ya wani waske fuskansa Na kan wayan da yake dannanwa kai ka ce bashi yayi magana yanzu ba!...

Shima Waskewa yayi Ya juya ga Nurse dinda ke Mopping yace " Nurse Find her Food"
Nurse ta Russuna"OK sir"
Har zata Fita nace"Hey nurse "
Juyowa tayi tana kallo na "Please Find me Green Tea,Fried egg and potatoes, Pls be fast"

Nurse ta Amsa da OK ta fita.


1:30pm Akayi Discharging Dinmu bayan mun dawo ne Umma ta kira Abba take fada mishi Rashin lafiyata,Wai zamowa nayi daga Saman Step stairs😏 (Idan baki San me ya faru ba ki tambaye ni zan fada miki yanda Akayi, bawai kizo kina Zubo mana ehyane ba)😁
Abba yace"munyi waya dazun ta fada mn Zazza6i ne kawai,kuma ta ji sauqi Sosai.....Amma Halima mai yasa kike takurawa Yarannan ne?,Meyasa kika hana Yarinya Saqat a gidan mijinta ne?, Ke haka Akayi miki ne?..............Nan ya Rufe ta da fada ya kuma ce ta dawo Gida yau yau Dinnan Shima ya dawo yana Abuja Gobe zasu karaso in ba hakaba Ranta Sai yafi nashi 6ace.

Bata katse Shi ba dan ta san halinshi in yana fada yafi so A saurare shi har sai ya dasa Aya .saida ya Gama Fadanshi ta bashi Haquri kuma inshaallahu yau Dinnan zata dawo Gida daga nan Sukayi Sallama Ta katse wayan.

Fitowa tayi ta nufi Part dinmu Wanda Tun jiya Aka Gyara mana Nida muka koma NaN.

Hafsah kadai ta gani A falo tana kallo tace"Auta, ina Yar banzan yarinyannan?"
"Ta fita" Hafsah ta bata Amsa a taqaice"
"Toh idan ta dawo ki fada mata ta Yi nasarar Raba tsakanin uwa da Da ta kuma yi nasarar hada Tsakanin Mata da mijiTana Gama fadin haka tayi waje tabar Hafsah da mamakin kalaman Umma (Kodai ta Sami ta6uwa ne?)

Umma kuwa tana Fita dakin Ramlah tayi Ta kara jaa mata kunne akan kar ta ta6a ba ma Aaryan kanta in ba haka ba to zata rasa Mutuncin ta ne kawai a banza A hofi, ta tashi a tutar babu...


******
Nikam Fitan da nayi ,inda na bada Ajiyan motana nayi Na kar6o daganan na nufi Pz nasiyo Wasu Abubuwa Sannan na karaso Gida.
Ina shiga na kwala Wa Hafsah kira ta fito daga bedroom da Alama bacci ya fara Daukan Tane "Hafsah waishin Cikin Attarugu da tattasai wanne ne yafi yaji"
"Mtsww,Dama wannan banzar tambayan Zaki mn kike kwala min wannan Uban kiran?"

"Banzar tambaya ko?,Bakomai"

Ganin kaman raina ya fara baci yasa tace"Duk Sunada yaji Amma inaga kaman Attarugu yafi"

Kallonta nayi da murmushi nace"Thank you So much"

Karasowa tayi tana bude Ledar dake gabana "me kika Siyo mana ne?"

"Attarugu da Tattasai"

Kallona tayi "keko me zakiyi da Attarugu da tattasai?"

"Nothing Fah, Just Pepper juice nake son Hada ma wani First of All ina Abinci na yunwa Nike ji,"

Tadan harare ni"Baki San Hanyan dinning bane?"

"Wlh na Gaji ne please Dauko min"

Mamaki ya kama ta jin yanda nayi magana in a cool voice, Abinda bata ta6aji ba, A ko da yaushe ina buqatar Abu bana Neman Alfarma, Command nake badawa.
Gyada Kai tayi Sannan ta mike ta nufi Dinning ta Dauko Abincin ina ci muna hira.

*****

WasheGari Tunda Asuba na Niqa Tarugu da tattasai na, na tace Sannan na cika mishi Ruwa yayi Tsululu.

Karfe 7:30 naFito cikin Sanda na nufi Part din Su yaa Aary Hannu na Riqe da Empty bottle daKuma Bottle mai kunshe da pepper juice🤪😜

A Dinning naja burki Ganin har An jera kayan kalaci Nadan waiga Ganin babu kowa yasa na bude Katon Jug mai kunshe Da Orange Juice(Wanda na Tabbata na yaa Aary ne,Sbb A kaidan sa kullum kafin ya karya Sai yasha shi sannan zai karya) , na juye A Empty bottle dinda na Riqo,Sannan na Musanyashi da pepper juice,
Takun Kafa naji Abaya na Kaman Ana doso inda nake, Nayi Saurin Boyewa kasan table,

Ramlah ce na hango Riqe da Tray din Jugs and cups An wani ci kwalliya !

~Samun Wuri~ na fada A raina, dai-dai lokacin da Ta Ajiye kan Table ta juya ta koma kitchen.

Saida na tabbata ta shige kitchen din Sannan na fito na bude dayan Jug Din, Black Tea ne a ciki, Shima budewa nayi na zuba Pepper dina Amma kadan Nasa a ciki, Gudun kar ya chanza kala a gane,ina Gama Zubawa na tattara bottles dina nayi waje Raina Fess

8:00pm dot
Ya sauko Cikin Shirinshi na zuwa Office,Sanye yake cikin kananan kaya, logoless Riga Indigo Long Sleeve,Da Dogon Wando Jeans Gashin kanshi yasha Gyara Sai Qyalli yake da daukan ido.

Ramlah ta Dan kalle shi ta kanne mashi ido daya"Kayi kyau"

Yaja kumatunta "Na kai ki?,Ai Kinfi ni kyau" ya fada yana kamo hannunta,suka nufi Dinning Area

Ramlah ta Zuba mishi Orange juice Cikin Transparent Glass Cup, Takai bakinshi,Ya wani wangale baki kaman Mai shirin Hadiye Gida.

Aikam Ganin Ya wangale baki yasa ta Zuba Mishi dayawa,

Wani irin Zabura yayi ya Buge kofin ya fadi kasa,Ya Riqe kirjinshi yana Tari,Idanun shi sun chanza launi zuwa kalar jaa, Gabadaya jiyake kaman ba bakinsa ba,Lokaci Guda ya fita hayyaci sa ga ciwon kirjin da ya dirar masa at once, Da zarar ya bude baki zaiyi magana sai wani Azababben zafi ya Dirar mishi A baki, Da hannu yayi ma Ramlah Nuni da Ta zubo mishi ruwan tea ya kora.
Babu musu ta debo ta zuba a mug, ta miqa mishi tama jera mishi Sannu (cus batasan dalilin Chanzawansa alokaci daya ba haka!).

Yana kaiwa baki ya saki wani irin kara kaman zakiyi kuka, murya na Sukaji Radau ina cewa "............





Masoyan book Dinnan harkullum bazan Gajiya bawurin miqa muku godiyana a gareku, Thank you so much


I love u wujiga² Irin totally😍😍😍


Kumin comments ko naje Strike🤤

Manage pls😍





Fahnaan🖋️

23rd Aug

*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

بسم الله الرحمن الرحيم...



*_Chapter 11 _*

"Nice Nan na"
Daga Ramlah har Aaryaan din Dagowa Sukayi suna Kallona, cikin tsananin mamaki Ramlah tace
"Kece kikayi me?,Me kika yi masa?"

"Juye OrangeJuice nayi na musanya da Jajjagen Attarugu" na fada ina Nuna mata Bottle din juice din ina dariyan Mugunta.
"Yaa Akwai Yaji kor, ko Zaka qara ne?" Na fada ina kara Tsuntsurewa da dariya

Cikin tashin hankali Ya bude baki zai yi magana MaqogoronShi ta Amsa😄,Da Gudu Ramla ta Tashi ta Dauko Ruwan Sanyi A freezer, Ta Kara mai abaki, nan fa ya shiga Antayawa cikinsa, Saida ta tabbata ya shanye Ruwan tas babu Saura, Sannan ta Cire BakinGorar daga Bakinshi

Ina Tsaye bakin kofa Duk Abinda Sukeyi, kar nake kallon Su, Sai faman Darawa nakeyi kaman mahaukaciya Sabon Kamu.

Muryan Yaa Aary naji In his Cool voice yana cewa"Tunda kin Gama Abinda Zakiyi Ki Fitar mana a daki pleasee"

" Ban Gama bah, kasan Dalilin Daya sa na maka hakan?" Bai Amsa ni ba ni kuma oho ban damu ba, na cigaba da cewa.

"Shinkafar da ka dura min A Asibiti, mai yaji, Shine nima na Rama na dura maka Pepper Juice, Naso Ace dukka ka kwankwada Yanda ka Sani Hadiye shinkafar da ban tauna ba, Mugu kawai😒, ke kuma Aunty Ramlah ki fara shirin Shiga Layin zaurawa, Dan in na Fara Rama dukan da yayi min, kashe shine kawai bazanyi ba babu mai Rabani dashi SAi Allah” Ina Dasa aya na juya Har zan Fita Sai na kuma dawowa Naga yanda Idanunshi Sukayi jaa, da Ace ina kusa dashi na tabbata yau Sai dai wata bani ba.
" Yaa Aary look"
Dagowa yayi yana Kallona,na Sa Yar karamar yatsa na A gefen bakina Tareda kanne masa ido daya "Get Ready for my next Target" Na shiga Tari ina bubbuga kirjina kaman yanda yayi Lokacin da yasha Abin, Sannan na juya na Girgiza Masu Hips dina na fice ina dariya.

Ina Fita Ramlah ta matso kusa dashi ta Riqo hannayen shi Cikin damuwa tace"honey,Please ko me Yarinyar nan Tayi maka ka Rinqa danne zuciyar ka,Na lura Yarinyar nan tanada Hadari Sosai, Duk yanda Akayi yarinyar nan Aljana ce, in ba hakaba kome akayi mata Sai ta rama?,ni Tsoron ta ma nike,kar wataran Tsautsayi Ya Afkamin na ta6o ta Nima naji A jiki na"

Aaryaan ya Dan Harareta "Matsoraciya, Shekara nawa kika bata?, you're 24 while She's 17, ba Aljana bace tashen balaga ke dawainiya da ita, zanyi maganinta Ai...."

"Good morning uncle And Aunty" Abdool ya gaidasu yana Jan Chair, Suka Amsa mishi cikin Sakin Fuska

"Uncle, wannene Abinci na a ciki?"
"Duk Wanda ka za6a" inji Aaryaan

Aikam Kwadayi irin na Abdool baikai hannu ko ina ba sai kan Pepper Juice😆

__BooM_

~INTERMISSION~

Yau Friday Yau su Abbie zasu dawo so yau Zamu koma Kaduna dan tarbar baqi, Hakazalika yau zan bude su Suwaiba

Tafe Muke a Mota Sai faman Surutu mukeyi, Janaan ke Driving Hafsah na kusa da ita ni kuma ina Sit din baya.
Janaan tace "Aff Babe, kinga na manta nayi Miki ya jiki?, koda yike kinji Sauqi" Duk muka bita da kallon Rashin fahimta.

Nace "Wacece babu lfy kuma?"
Tace"Keman ko kin manta Suburbudan Da kika Sha ne ?,Ranar Saiga Munayferh da Shar6ar hawaye" ta fada tana Rufe baki Dan kar dariyan ta ya fito
Miqewa nayi Na dafa Seat dinda take zaune Na Buge mata baki nace"Muguwa , da kanki anan Tun na haihuwa"

Hafsah tayi dariya Sannan tace "Da kina nan ,Wlh Sai kin fi Shan dariya , ana Zanar ta tana Allah ya isa, mugu kawai,Shi kuma kaman Tunzura shi take tana Allah yaisa yana Zuga mata" Ta fada itama tana kwashewa da dariya

Komawa nayi Seting Sis dinta na Rankwashe ta a ka"Abin dariya, ke meyasa bakiyi dariya a lokacin ba,Yar rainin hankali"

"Lokacin tausayin kine ya Sani Hawaye, Amma deep down Dariya ke cina..." Haka suka cigaba da Tsokanata har muka isa Kabala Costen Kaduna,

Yan Aiki sai kai kawo Sukeyi A harabar Gidan Masu gyare² nayi Masu Share², Masu Wanke² nasu, haka cikin Gida Masu Girke Girke nayi,

Kai tsaye Part din Su InnaRabi na nufa na dau makullin da na jefar ta windown baya, yana nan inda na Ajiye,

Ina Shiga dakin na gansu Gaba dayan Su Sunyi Tsuru Tsuru, Suwaiba na kallon Television Yayinda Umma ke kishingide Tana Gyangyadi , Yaa Umar Ruwan Gora ne A hannunshi yana Sha,Zee kuma tana Shafa mai A kafarta da ya fashe.Sunyi Biji ² Sai kace basu bane Yan gayun nan Masu Aji da iya daukan wanka.

Ganin yanda duk Suka koma kaman Almajirai yasa na Shiga Darawa Ina nunasu da yatsa "Inna,Suwaiba ,zee, yaa Umar ya na ganku wani iri Baku Ganku ba Wlh kaman Ahalin Su mohini na cikin Film din Chintata InnaRabi kinga Fuskar ki kuwa?, yakoma kaman Rubabben Tomato,

Wato Yarinyar nan Ta raina mana Tunani Ashe qalyan jinnu ta mana Ta wahalar damu, tasa zane mana Uwa A gaban mu, ta Ci Uban mu, yanzu kuma tazo tana mana Tambayan Rainin hankali?, Ai in ta San wata batasan wata ba bari na bita A hakan (yaa Umar ke fadin haka a Ranshi)

A zahiri kam murmushi yayi yace " Ai yau kwana mukayi muna Aiki kinsan yau Abba zai dawo"

Nace"Tho, meyasa naga Kofar A kulle?"

Zee ta chafke "Ai ni nasa Zuwaira Kullewa Dan mu Sami damar Gyara dakin inna Sosai"

Nace"Tofah,Meyasa naga Key din a waje?, Kuma Ai dakin nan baiyi kaman an a gyarawa ba, infact Banda Wari da doyi babu Abinda ke tashi Anan" na fada ina Rufe hanci da Bakin Rigana

A Razane inna Rabi ta hayayyakoni kaman zata kamani na zura a guje ina dariya, na Bar part din su na koma Part din Umma Inda na barsu Hafsah

A general falo hango junayd (kanin yaa Aaryaan,tsantsar kamannin Da sukayi ya isa ya fallasa

Please Login or Register in order to submit comment