Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Gari jeeoboi Ya koma Sbd Saura Kwanaki biyu su Fara Exams na Tausayinshi ya Kamani Kasancewar Har yanzu baiyi Aure ba ,Ga Hidimar da yayiwa yaran ,Cikeda tausayawa nabashi Shawarar ya Nemi Cousin Dina Fadeelah batada Matsala Nayi masa Kwatancen Inda zai sameta .

Na Lura kaman Bai so ba don Har yanzu Ina Ganin Tsananin Qaunar da yakeyi mn Cikin qwayar Idanunshi ,tafiya MaMa Mahaifiyarshi ta Cigaba da Kula Dani Kasancewar ,Akwai Lokacin da ya rage Mata na Ganin likitan .


Ranar Suna Na za6awa yaron Suna ABUBAKAR SADEEQ Sunan Mahaifin Jeeboi nayi hakan Ne Don Faranta msu gabaki Daya dashi da Mahaifiyarsa ,Sun Riqeni hannu 2-2 Batareda Sun San Matsalata ba Sun Daukeni tamkar 'yar'uwa a lokacin da nake Buqatar 'yan uwa Babu Abinda Zan saka Msu dashi Sai Addu'a Don babu Abinda zAN Basu yakai Dadi da Girman Addu'a.

****

Chan Nigeria Kuwa .


Duk Inda UMMA Ke Tunanin zata Ga Munayferh taje Amma bata ganta ba ,har qasar ta Bari Amma duk inda taje Bata samun nasara Ga Uwar Gayyar a Kwance Munayferh ta naqasata ,bata ta6a tunanin ko zaton Zatayi danasanin Abinda take Aikatawa ba sai Yanzu , Don sosai Alhakin Mu ke binta Dukda an sasanta Su hafsah ta Koma Amma UwarMijinta Bata Qyaleta ba Cin mutuncin Yau daban na Gobe daban Kuma duk Abinda Ke Faruwa Yana dawowa Kunnenta Kasancewar Umman Hilaal Mace Ce Mara sirri , zata Wulaqanta Dan Mutum Kuma taje tana Gayawa Duniya.

UMMA tasan haqqin Ramlah da Munayferh bazai ta6a barinta Ta huta ba , wajibine taje Ta nemi Gafarar Diyarta Ramlah qila hakan zaisa Innocent hafsah kwanciyar Hankali a Gidanta.

Don haka ta Shirya ta nufi Gidan ,(Gidan da Saleem Ya Gina ,Ban gaya Mku ba Ai sun Koma ,Sun bar msu Gida)


Koda taje Cikin Rashin Sa'a bata Isketa a Gida ba ta tafi wajen Aiki, sai Saleem Da Shima dawowansa Kenan Daga Yawo Shida Humdah.


da karramawa ya tarbeta ,ya gaya Mata bata nan sai Da yamma zata dawo UMMA tace Taji ta Amince zata Jirata har ta dawo .

Guri ya bata Ta zauna Kasancewar Humdah Yarinyace Mai son Jama'a gashi batada Qiriniya sai UMMA ta Kirata Tana 'Dan Janta da wasa , UMMA ganin yarinyar take Tamkar 'yar Uwanta UMMIE yarinyar Ta kwaso Kamanninta sak Babu Abinda ta Baki Shiyasa takejin Qaunar yarinyar har Ckin Ranta.


Tun 2:00pm UMMA ke ta zaman Jira har 6:30pm ,lokacin da Ramlah ta dawo Daga Wajen Aiki.


Dirar Motarta a harabar Gidan yasa Humdah Gane Mummynta ta Dawo , Cikin 'yar tafiyarta na Yara 'yan Shekara Daya da rabi ta taka ta Fita Tanayiwa Uwarta ta Oyoyo Cikin Gaurancinta na Yara.

Ramlah ta Dagata sama cikeda murna tana Fadin

"Oyoyo My Princess ,Where is daddy?"

UMMA na zaune tana Kallonsu , Ta share Hawaye Cikeda Tausayin Ramlah , bata samu Kyakkyawar Kulawar Uwa ba ,Gashi Tana Bawa Diyarta Kulawar da Ita bata samuba A lokacinta .

Ramlah Dauki Humdah ,Zasu Haye Kan Stairs ,humdah ta Nuna UMMA da yatsa Tana Qoqarin Sanar da ita Zuwanta.


Wani Uban tsaki Ramlah taja tareda sauke humdah Tayo kan UMMA Gadan Gidan ka daukan maketa zatayi ,Amma sai taja ta tsaya Ckin 'Dan Daga Murya Tace .

"Hey Woman what the Heck Are you doing Here?"

Ga mamakin Ramlah sai Ganin UMMA tayi ta durqusa Har qasa Hawaye na Kwaranya A idanunta , Kafin UMMA tayi magana har ta Rigata.

"Womann Abege Get Out of my house Before I lose my Mood on you..."

Cikeda Mamaki UMMA ke kallonta ,Duk Maganganun da Ramlah keyi bata Bari Sun Hada Ido da UMMA ba ,Wani Gefen chann take Kallo.

"Ramlah ni........"


" Ramlo...! I said Out!"

Ganin Ramlah na Shirinyi Mata rashin mutunci tun Kan tasan dalilin zuwan Nata sai ta Miqe tana Share hawaye tareda kakka6e Jikinta Ckin Sanyi da. rawar Murya take cewa

"Ramlah Ina Roqonki Da Allah Don Girman Zatinsa Ki saurareni Koda Sau dayane"


Sai a wannnan Karon Ramlah Ta Kalle UMMA suka Hada Idanu Take Gabanta ya fadi Da sauri ta kawar da Kai Tana Qoqarin 6oye yanayin Zuciyarta a fuska.


Saida ta Tabbata ta Dan natsu sannan Ta Fara Magana Kaman Mai rada

"You Have Nothing to tell me ,am Not ur Inlaw Any more , Am not leaving in Ur Home, Anda am no more Your daughter so What're you trying to tell me.... just Get ur stinky Mouth out of My sight trash...!"


Ta qarashe Da daka Mata tsawa Wanda Babu shiri ta Juya Ta nufi Hanyar Fita Tana share hawaye .



"Ummah Don't mind Her ,Please ki dawo Musa santa"

Inji Saleem da tsawar da Ramlah ta dakawa umma ya Fito dashi.


Juyowa Ramlah tayi ta zabga masa wata Uban harara ta Kama hannun Humdah a qufule zata haye sama ya tareta Ckin sigar Rarrashi yace

"Please Deary Attempt to her ,Remember she Is Still ur mum"

Ya qarashe da kanne Mata Ido 'Daya .


A zuciye tasa hannu ta ranqwashi kansa ya Dafa wajen yana wash

"Wannan Shine Hukuncinka na Kirana Diyar Mare imanin nan......"


Tana Gama fadar Haka tayi Gaba Abinta.























Nima nayi gabasπŸ˜„πŸšΆπŸ»β€β™€οΈ



26decβœπŸ»πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

Na
🀍 *Fahnaan*🀍

Β©πŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…...



*Chapter 88-89*


Saleem Ya Juya Ya nufi inda UMMA ke Tsaye Yace ta Zauna , Yana Zuwa gyada kai UMMA tayi Ckin damuwa , ta koma ta zauna Ranta na Suya.

Sunkai kusan 20mins Kafin su Fito ,Har ta sauya Cikin qananun Kaya , Fuskarta babu yabo babu Fallasa Yayinda na Saleem yake Tamke Kamar Bai ta6a Dariya ba.

Ta gaban UMMA tabi ta wuce Kitchen shi Kuma ya zauna Yana bawa UMMA baki akan Yanzu zata dawo Kuma zata Yafe mata.

Aikam Babu Jimawa Sai gata riqe da Plate din Abinci da Abinsha Mai sanyi , Fuska a Daure ta diresu Gaban UMMA sannan Ta samu Gefen Saleem Ta zauna Tana Turo baki .

Dakin Ya dauki shuru na wasu 'yan daqiqu , banda surutan Humdah Da Qarar TV babu Abinda kake Ji.


Gajiya tayi da shurun Ta katse su da Fadin

"InaJinki da Me kikazo?"

Sunkuyar da kai UMMA tayi a Sanyaye Ta ja Numfashi.

"Dama Zuwa nayi Don Allah Don Girman Allah Ki yafe mn Duk Abinda Nayi mki a baya , na Gane Kuskurena Kuma Inshaallah Kuskure makamancin Wannan bazai sake Faruwaba , nayi mki Alqawarin Zan zame maki Uwa ta gar......."


"Common Woman !....point of Correction, Am not your Daughter!!!!!.... Ni ba diyarki bace"


"Enough Ramlah, Me kikeyi ne haka? ,ki yafe mata mana"
Inji Saleem

"Ramlah Kai tsaye?, Don't Worry Ramlahn Shine Real name Dina ,And For ur Information As From now Kar na sakejin ka Kirani da wani sunan Banda Wannan , Kuma Maganar da Bakaso na fada sai na Fade ta Niba Diyarta Bace!, na qara na Maimaita Ba ita ta haifeni bah!!....Ke Kuma Ki Fice Mn Daga Gida banason ganinki"

Ta qarashe Maganar tana Nuna Mata Hanyar Waje.


"please Ki nutsu Ki kwantar da Hankalinki , Ki zauna kuyi magana Ku fahimci Juna , Wai ma Yaushe Kika zama Tirjajjiyane ?,Ni ramlahn Da na sani bata iya Kafiya ba ,please Ki Natsu ki zauna Deary"

Ya qarashe Cikin sigar Rarrashi. ..


A sanyaye Ta koma ta zauna Sannan Ta dau Ruwan da ta Ajiye gaban UMMA Ta zuba Cikin Cup ta Kur6a Saida ta samu Natsuwa sannan Ta maida hankalinta Ga UMMA waccce Alajabin Maganganun Ramlah ya daureta Ta Kuma kasa Kwancewa.

"UMMA A gaskiya Da Don Ra'ayin kaina Ne da na yafe Miki ,Amma Idan Na yafe Miki a wannan Yanayin Ai kinci bulus ,Mugun Bulus Mah , Yanzu Dai Zan Yafe Mki amma Saida sharadi"

Da sauri UMMA tace

"Na Amince ko wane Irin. sharadi ne"

"Hmmm ...Ba wani mai wuya bane Kasancewar Kece Director din , zan yafe Miki ne kawai Idan Kin dawo mana Da munayferh duk inda Kuka kaita"


"No Ramlahteey Please wannan Sharadin Ai yayi tsauri dayawa , Taci arzikin uwa maanah"

Tsaki Taja ,ta kalle UMMA da ke qame kaman An Jona Mata Shocking tace

"UMMA tsakaninki Da Allah Kin ta6a jin shauqin dake tsakanin diya Da Mahaifiya?"

A sanyaye UMMA ta Gurgiza kai alamar A'Ah

Ramlah ta cigaba da cewa

"Nima haka Ban ta6a jin shauqin Uwa a tattareda Ke Ba , illa shauqin Dangantaka Na Jini Haqiqa 'yar guntun Shauqin nan Shike hanani Rama Muguntar da Kike Mn a baya , Haka Kuma shike qara mki Kwarjini a Idanuna , A duk lokacinda na Kalleki sai naji Kinyi mn Mugun kwarjini , Haduwar Jini Abu ne Wanda yake na daban , Gaba Daya Kinkasa tantance Shaukin dayake tartare da Mahaifiya IFRAH itace Asalin diyarki bani Ramlah ba , babu Wanda yasan wannan Sirrin Dagani sai Mijina Da Kishiharki Aunty salma Wacce itace jagoran tafiyar "
umma kuwa Maganganun Ramlah sunyi matuqar gigiya ta ,Cikeda Tsantsar mamki da Firgici take Kallonta ,Maganar Ta Gaskiyace UMMA bata ta6a jin Shauqin dake Tattareda diya da mahaifiyaba a tattareda Ramlah , maganar da tajiwo Ramlah nayine ta katse Mata tunaninta

"Please Idan Kin Fita Ki Kulle mana Qofa , Guard man Daya muke dashi "

Tana gama Fadar haka tayi Gaba ,UMMA Kuwa galala tabita da kallo har ta6ace .


Asanyaye Saleem ya juyo gareta a sanyaye Ya Fara magana Ckin tausasawa

"Ehmm kiyi haquri UMMA , Ya Kamata Muyi Mata Uzuri kinsan Mace da Ciki sai a Hankali ,Haka Suke Behaving sai munyi Msu Uzuri Amma InshaAllah Zanyi calming dinta Kuma zata sauko Please Kiyi haquri”

A sanyaye UMMA ta share Qwallan dake Manne a gefen idanunta

"Nagode Saleem, Amma da ka Qyaleta inaga Shine zaifi nasan Har na Mutu Ramlah bazata ta6a yafe min ba, domin Kuwa Konice ba Tainci kaina Cikin Halin da ta tsainci kanta Bazan Ta6a yafewa ba ,Kar ka manta faa halina ne yasa Ta kasance a Qarqashin Kulu Ramlah bata ta6a jin dadin uwaba , Haka Kuma ni da hannuna Na zuvar matada Ciki ,Na muzguna Mataa a dalilin baqar hali Irin Nawa ta Kamuda Ciwon HAWANJINI na zame Mata Hawanjini ,Nida na aikata Wa'ennan uban Zunubban taya za'ayi ta sauko har ta yafe mn , Inaga Wannan ba mai yiwuwa bane ,ni na Tafi Zan cigaba Da istigifari da Roqon Gafara har Allah ya Kawo mn Dauki Ckin lamarin "

Ya qarashe Maganar a Sanyaye , ta dauko Jakarta Ta zuge Zip din Ta dauko wata 'yar Chocolate ta Miqa masa

"Ga wannan A Bawa takwarata"

Saleem Yasa hannu ya kar6a Cikeda Tausayinta .

Tana Fita Ramlah ta Fito ,Dama Tana Jinsu ,Chocolate dinda ke Hanninsa Ta kar6a Kafin yayi wani Yunquri har ta Jefar Ta Window

"Wlh Diyata Bazata Ta6acin Abinda ya Fito Daga hannunta ba ,Salon A zubar Mata da 'yar Cikin nata itama?"

"Keh !…Meke damunki ne? ....."


Take ya rufeta da fadar ,Abinda Bai ta6ayi Mata tunda suke tare ,Da yake itama Ramlan Daidai take da kowa yanzu sai Ta wankeshi tasss.


A ranar dau cikinsy babuwanda yayi barcin farinciki... ***

Chan 6angarensu ammie Kuwa Tun Randa Na Kirasu Suka 'Dan Smu Natsuwa At least sun San Ina Raye , Amma tarin da sukaji inayi yayi matuqar Gigitasu Don Haka suka Tashi tsaye wajen Roqon Allah akan Wannaan Lamarin ,Domin shine Maji Roqon bayinsa .


6angaren su Mamy(kulu ) da azzalumin Mijinta , HajiyA larai da sauransu .

An Gurafanar dasu Gaban Kotu An yanke cigaba da tsaresu Har sai an Ga Uwar Gayyar InnaRabi.

**

Karaci


Bayan Arbain na koma nayi settling din Komai na koma makaranta ,Tare nake tafiya da yaran Idan Na isaa Makarantar sai Na Ajiyesu a Baby Creche Idan na Fito na kar6e Su.


Da yike yaran ,Allah ya zuba Msu Farinjini wajen jama'a Sai Na samu Sauqi wajen Rainonsu ,Mutane na 'Dan tayani Da yike Garin ba kalar qasar nigeria bame babu Ruwan kowa da Rauwan wani , Sai nake Jin dadin Zama dasu Koba Komai Sunada Karamci da sanin darajar 'dan Adam..

Tunda na Kira su Ammie na daina Kiransu hasalima so nake na Fara Gogesu A rayuwa na Don Ba Lallai mu sake Haduwa ba , A yanda nakeji Cikin raina dangane dasu , ta 6angaren InnaRabi kuwa ina qare Wanka Na Koma Gidan Jiya ,Ina Mamakin yanda bata ta6a yunqurin Guduwa Ko tseratar da kanta ba , Abinda bansani ba Kuwa A tsarin Gang dinsu Duk wacce ta Fada hannun mace shikenan nata ya qare , tayi surrender kawai ,Domin idan tayi Yunqurin Tserewa tana iya haduwa da bala'inda Idan ta afka Ciki Babu mai iya Hidda ita Har ta qare rauyuwanta , Wnnan dalilin ne ya hana Jami'an tsaro nasara dasu , Domin Mafi aka sarin masu tsaron duk mazane ,shiyasa Ta Cigaba da miqa Wuya domin ta gummace hakan a kan wacce zata afka idan tayi yunqurin ku6ucewa.




*Bayan wasu shekaru*


Haseen neya da Gudu yana Sheqa dariya Hannunsa Riqeda Wata Envelope .


Kai tsaye ya nufo inda nake Zaune Ina kallon news miqa min Envelop din sannan ,Ya fara mgn Cikin harshen hindi wanda suka Saba dashi.

(Fahnaan bata bani daman Rubutowa ba shiyasa zan Ruwaito mku da hausaπŸšΆπŸ»β€β™€οΈ)

"Ummy ,wannan Class teacher dinmuce tace na Kawo miki" .


Ina jin hakan na tabbata Hasanah ta sake Yin halinta ne , dariyan Da Naji yanayine yasa na fahimci dole da Akwai abinda ta Aika domin shi baya Dariya haka kurum ,Komai nashi irin Na ubansa ne harta Kamanninsu miskilanci Da zafin Rai , yanayin Tafiyarsu ma iri daya Murmushinsu Kai komai ma fa sak ne banbancinsu dai Quruciya da Hankali.


Cikin natsuwa na Bude Takardar na Fara karantawa , Kaman yanda na zata haka dinne don Kuwa hasnah ce ta Tsokano Malamarsu Akace dole sai na zo.


Ina Gama Karamtawa na Yaga Takardar na Jefar , na Dubeshi cikeda Takaici Nace

"Ina Hasnan Take "

"Tana waje " ya Bani amsa Cikin yaren hindi wanda Nima dashi na tambayar.


"Jeka Kira mn ita"

Na bashi order, Aikam da gudunsa ya Fita ya dau Almost 20mins kafin su Shigo tareda Ita harda Sadeeq .


A sanyaye ta shigo kanta a qasa cikin tafiya irin ta mai tsoro ta Iso wajena Ta sunkuya tayi kneeling.

Na kama Kunnenta na hagu na Murda Cikin raki ta Fasa Ihu

"Hold your Lips"

Na daka mata tsawa in a serious mood , Irin An zanan uwaar nanπŸ˜‰..



Aikam take ta kama Bakinta Jikina makyarkyata.

"Uban me kika sake Aikatawa A makarantar Ake shirin Korarki?"

Cikeda tsoro Da in'ina Ta fara magana

"Dama....Sonam Ce takeyi min gori wai banida Daddy, shine nayi Reporting dinta , Koda nayi hakan Sai Mrs Murphy ta fara zagina wai Gaskiya ta fada har tana Dungurina ..... Shine , shine... Abin ya bani haushi na .....uhm....na..."


"Kikayi me?" Na fada ciki daka tsawa.


A tsorace ta shiga Zazzare ido , Me su Sadeeq zasuyi inba dariya ba take suka shiga darawa .

Cikin shessheqa ta cigaba

"Shine na je Gidansu , Na iske bata nan Shine Na Rama akan Yarinyarta , na kuma zazzageta nace sune basu da daddy , shine fa da mukazo school yau Aka tarani A assembly kaman yanda suka saba Mrs Murphy tasa Sargent ya zaneni Bakiga hannuna ba Shine da aka Tashi harda aikomin da Wani letter"


Ta qarashe maganar Da turo baki, hannu nasa na buge Bakin

"Ni kike Turowa baki?"

"A'a Ummie" .

"Muga Hannun naki" na fada ina dagota tareda duba inda Layin bulala ke Shimfide a Jikinta , ko ina Yayi radarada.

Cikin zafin yanda Jikin nata ya tattaso nake fadin

"Wlh babu inda zani , Daga yau ma kun daina zuwa Makarantar Kuma Kotuce zata Rabani da Muguwar Malamar nan Taku, Waya gaya Mata bakuda uba?, Me suka sani akanku?, da yake Jakace batasan Zafin haihuwaba , ji yanda tasa aka Tayar mn da fatar yarinya Fisabilillahi , DUBA FA Ai gara da kika Rama akan diyarta itama taji yanda akeji idan an Ta6a diyar wani...ita sonam Dinda ta fara tada maganar ya Kikayi da ita"


Cikeda jin dadin goyon bayan da ta samu Daga gareni ta fara magana

"Ai wanchan Qaramar Alhakice , kinsan Ba qyaleta zanyi ba , da Break Muka taruata Nida Haseen Muka chaskalata Ko Bhai"

Ta qarashe Maganar da Kallon Haseen Wanda Keta Faman Murmushi tunda yaji za'a Sauya msu makaranta....















Nayi gabasπŸšΆπŸ»β€β™€οΈ

27Dec✍🏻[12/27/2020, 5:54 PM] Fahnaaan❣️: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

Na
🀍 *Fahnaan*🀍

Β©πŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…...



*Chapter 90*

Murmushi nayi Tareda Sake Rungumarta a Jikina

"Hakan Yayi daidai ,amma Ina Tsoron Ranar da Zaki Tsokano Abinda yafi qarfinki "

β€œNo Ummi Ai kinsan Ni bana Ta6a kowa Sai an ga6a ni , Kuma bana ta6o wa'enda Sukafi qarfina"

"Ummie Dazun Munga Uncle Yousuf shida Aunty Fatee "

Inji sadeeq


"Really?" Na fada da Sauri

"Eh Sunce zasu zo Anjima Muyi Msu Preparing delicious"


Murmushi nayi Ina Dubansu

"Me Kuke Tunanin Zamu dafa Msu?"

Hasnah: "Pizza"

Munayferh: No

Haseen : I think We should Just Make pastries.


Munayferh: mr Snack Island No It will take Too much of time


Sadeeq: Let just Cook Rice and Beans

Hasnah da haseen: Boom Abege Keep shut, Rice is too local.


Munayferh: I think The Rice Will be quit better ,Muje kitchen Din.


Na qarashe magana da Nufar Kitchen Din , Yayinda su kuwa suka Tsaya Suna Kallon Sadeeq Wanda keta Faman Murguda Masu baki ,Saida sukaga shigewa na Kitchen Sannnan Suka Zare masa Ido Ckin Gargadi haseen Ya Fara magana

"Kai are we Your mate?"

Yarfe hannu yayi Ckin zaro Ido yace

"What Have I done"

"Ohh You're Asking?, Wlh Idan ka sake Kasa akayi Rice Sai mun Zane ka Kuma kasan halin Mu"Cewar hasanah

"Kaine Qarami a Ckin Mu amma sai wani Ji dakai Akeyi kaman Gold Kome kayi daidaine ,Duk Abinda Akeyi Maka Ka Dinga tunawa We're Your seniors You're 4 while We're 5 "


"Different of One Full year" hasnah Ta qarashe Tana Wani Juya idanu Irin Ga Auntyn nan.


Sadeeq Ya juya Yana Jan tsaki har zai Wuce Hasnah tace

"Who permit you To Go?"

Shuru yayi Yana Kallonsu Ta qasar Ido , Don sauran Idan ya sake Ya furta wata kalma.

"Kaje ka Gayawa Ummie ta yi snack ,We don't need Rice Anymore Go"...


Kaman Jira yake ya Juya ya wuce Kitchen inda nake


Hasnah ta dube Haseen Dake Shirin Barin wurin tace

" I heard You Talking About Age , You should Always Remember cewa Nima na Girmeka With 3hrs ,Am above you All...."

Ta qarashe Da Tunstsurewa da Dariya.

Tsaki yaja Shima ya Murtuqe Fuska Tamau kaman Bai ta6a Dariya ba, Kai ka Rantse WaNi mugun abu ta gaya mshi

Ya mastso Kusada Ita , Yaja Kunnenta

"Since You Are Above Us All ,Meyasa Idan Mun Zane ki Kike Kuka? , Nida sadeeq Mun fiki qarfi Mune Masu Taya Ummie Aiki , not like You lazy Oaf , Idan Kika sake Cewa Kin Girme Ni sai na hada baki Da Sadeeq Idan Munje sch Gobe mu zaneki"

"Eh Din Ai Ummie ta Ciremu A makarantar"


Ta qarashe Cikeda Tsiwa.

"Are You nagging?"

Haseen ya Yada yana Nufota gadan Gadan ,Aikam ta Arts da Gudu .

Kai tsaye Kitchen Ta nufa inda Nake tareda sadeeq yana Sanar Dani Rashin Mutuncin da sukayi Masa Ina Bashi Haquri Sai gata ta fado itama Ta kawo Qarar haseen da iqrarin da yayi na Dukanta ,Cikeda Takaici na Rufe dukkansu da fada na kuma ce Na 6ata Dasu , SimiΒ² suka bar Kitchen din Suka Koma Parlor suna Gulma na.


Suna Fita na Aza Girki Amma abu kaman Wasa White Rice Kusan 4hrs Bai dahu ba haka Kuma waken Da na Aza shima Bai dafu ba Anda sabo na Saba da asarar Abinci sbd 'yan Biyu ,Babu Shiri Naje dakaina Na rarrashe su Har suka Sauko ,sai a Lokacin na zubar na Kuka aza wani sannan Na Hada Pastries kaman Yanda suka Buqata ,aikam sunji dadin hakan .


Ina Gama Girkin kaman Jira sukeyi na Gamawa sai Gasu sun Iso .

Take Muka shiga Hiraan Yaushe Gamo Kasacewar Munyi hutun semester Next week zamu Koma muyi final Semester Wanda hakan Zai dauke mu tsawon Watanni biyu shikenan Mun gama.

Bayan kowa yaci ya Ture teemah ta dube Hasnah tace


"Hasnah , dazun me kikayi Kuma naga An Baki Letter?"


YoΟ…souf yayi Dariya yace
"Wa'aka Tsokano Kuma"

Take na kwashe msu yanda Akayi da Shawarar da na yanke na Ciresu A makarantar.


Teemah taja Numfashi tace

"Munayferh, Please I THINK yanzu Mun zama Daya Bai kamata ki cigaba da 6oye mana lamurran da suka Shafi rayuwanki ba ,Ya kamata muma musaN WANENE Ubansu , da kuma Asalinki Don Naji kince Ke ba 'yar nan Bace 5years Muma tare ban ta6a ganin Wani naki yazo ,Please Ki gaya Mana ba Don Komai ba ko Dan Halin Rayuwa"


Tunda ta Fara magana Idanuna Ke a lumshe Don Ta Tuna da abubuwan da nake Shirin Mantawa .


Haseen Ne ya dafa ni
"Ummie tears In ur Eyes ?"

Hannu na Daga Da niyyar tabbatarwa Sai hasnah ta Rigani , wai Ashe Hawaye nakeyi .

Hannu nasa na Share Qwallan Sannan Na maido Idanuna Na kallesu 'Daya bayan Daya.

Mun dau 10mins Shuru kowannen mu Zuciyarsa a Tsinke .


"Sunana Munayferh Junayd ,diyaga Shahararren Business man Ne Wanda Africa Suke Jidashi Wato JUNAYD COSTEIN (JY ).

"Don't tell me , ke diyar JY ce?"

Inji YoΟ…souf Ckin Trauma.

Gyada kai nayi Na cigaba da Cewa .

"Ni haifaffiyar yar Zaria Ce Amma a KD na taso........


Tiryan tiryan Na basu Labarina Tun Daga Farko har auren mu na titi Wanda umma ce sanadi Da Qiriniyar da nayi a zamanina Haka kuma Saida na gaya Mata harda Shu'umancin InnaRabi da uma harda hajiya Asiya , da kuma Hukuncin da Na Daukan Akan su Da wanda nake shirin zartarwa akan umma .


Sun tausaya mn Domin kuwa Saida Teema tayi hawaye , kasancewarta Mai rauni.


Ckin sa'a Kuwa Suka Tausaya mn Tareda Yi mn alqawarin karya Wannan Asirin da Hajiya Asiya da InnaRabi sukayi mn. .


Naji dadi sosai , kuma haka muka cigaba da Karatu Kuma Na Sauyawa Yaran makaranta ,kasancewar Shekarar itace Shekarar mu ta qarshe Sai na Dage Don So nake na Samarda Abinda Babu Wanda ya Ta6a samarwa A Qasarmu , so nake na qirqiri element da Abinda Zai Iya sauyawa Mutum kamanni Ya maidashi Sak yanda Su umma suka maidani a 9jeria.



*Nigeria*


Kaman yanda na Umurci Jeeboi Yaje Har Garin su Fadeelah Koda ya Isa Tun Kan Ya kaiga Bayyyana Mata Buqatarsa Aka sanar dashi Anyi mata baiko , hakan yasa ya haqura .


Ana Saura kwanaki Hudu Bikin Allah yayiwa Mijin Rasuwa , Ammie ta Nemi Alfarman Yaruwanta ta roqa A Bata Fadeela Ta Dinga Rage Mata Kewa . , haka kuwa Akayi Fadeelah ta Dawo Wajenta da zama.

Shi kuwa Aaryaan qara Kurmacewa Yakeyi yana qara tsanar Zama Da mutane domin Idan Ya zauna da mutane Jin kansa yake cikin qunci , Hakan yasa ya nesanci Gida Baya dawowa sai qarshen shekara .


Kaman Yanda ya Saba bayan Kowane shekara Yau Ya Dawo Gida Yana Farka motarsa Motar Umar ta danno kai.


Yana Fitowa ya kafe Motar da Idanu har Suka Fito ,Shida Suwaiba Zasu wuceshi ya kirasu , a ladabce suka Iso Gareshi harda Dan rankwafawaa.

Kafe Suwaiba Yayi da idanu Wacce taketa faman Gaidashi.


Da hannu ya Riqo hannunta yana Dudduba Hannunata Zuwa idanunta.


Sake kallonta yayi Don Ya tabbatarda Abinda yake Gani.

Daga Suwaiban Har Umar Sokoko suka Tsaya Suna Kallon Ikon Allah Don basu San Me yake shirinyi ba.


Ckin Murya muryansa Mai Amo yayi maganar da Ta kusa Tsaga Ruhin dukkaninsu gabaki dayansu Su biyun.

"Suwaibah.....you are Pregnant"...


Ya fadi hakan Ne yana Sake kafeta da idanu Don tabbatarda Zarginsa , Aikam Abinda yake Zargi ya tabbata domin ganin Gigicewar da ya gani a fuskarta .....









































Nayi gabas😜



27th Dec✍🏻
[12/28/2020, 9:14 AM] Fahnaaan❣️: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

Na
🀍 *Fahnaan*🀍

Β©πŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…...



*Chapter 91*





Cikeda Mamaki da Gigicewa yake kallonta ,Ganin Abin yake tamkar a mafarki

"So its True , suwaibah You're pregnant?"

Ya fada Cikin shakku kuma Cikeda son Jin Gaskiyar lamarin Daga Bakinta.

Take Jikinta ya Fara Karkarwa Ta Fara rawan Dari gabanta Na dukan Taratara babu Daman Tayi masa Qarya tunda ya ganota sai kawai Ta shiga Hawaye , Umar dake Tsaye Kuwa shima Tausayin qanwar tasane ya Kamashi Don haka Shima Jikinsa a sanyaye yke.


Cikin

Please Login or Register in order to submit comment