Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Huci daga bakinsa


"Sir bana iya magana Idan ina Fushi! , ka kiyayi haduwarmu na Gaba ,Na barka lafiya"


"Aaryaan Dawo " muryan CP yaji ya kirasa Cikin Sanyi ya dawo.


"shiga mota"

Dariya Aaryaan yayi yace

"Sir in shiga mota kuma?, Siyar dani Zakayi?, ko Abinda nayi Na kumayin Laifi ne ?"


"Ko daya Shiga mota muje"

Bai qara musu ba ya shiga CP Dakansa yajasu Suka bar wajen

"Rankashi Dade Mai yasa Ka fara Aikin lada a da ,Sannan yanzu ka zuba ido Ana 6atawa"

"Aaryaan bazaka Gane bane Inspector Haris yana da hadarin Gaske Ni kaina bansan Taya Akayi nazo nan wajen ba ,Infact in takaice maka magana Those corporals dinda ka gani Yarana ne bansan ya Akayi Suka Zama nasa ba"


"Hmmm....to sir taya Akayi ka sanni ne?"


"Na sanka mana Tun kana Yaro Mahaifinka Amini nane a da ,Amintar mu ta tarwatse ne Saboda Tsanar da Matarsa Take Nunawa ga 'Yan Sanda, Nasan komai dangane dakai Harta Aikin 'dan sandan da ka soma duk Da sanina Nasarorin da kake Samu duk da wasu lokutan baka halartar Training Dinda Akeyi mku duk da Taimako na ne......"









*******


A hankali jikina ya fara Motsawa na ware Idanuna Ahankali na kai dubana na kalli hannuna Wanda naji yana mn zafi zafi sai na Ankara ma Qarin Ruwace a jikina


Zumbur na tashi a tsorace ina kallon Gefe inda Janaan ke zaune tana latsa waya Na kuma kai dubana Gefe inda hafsah ke Zaune tana waya .


"Me ya kawoni Asibiti"


Na tambaya A tsorace ,da Sauri duk Suka kai Dubansu Gareni a tare suka hada Baki wajen fadin

"Nyfee kin tashi?"

Rumtse ido nayi da na tuna yanda Akayi har na zo Asibiti.


Ware idona nayi nakai duba ga Hafsah wacce keta faman yi mn Sannu


"Hafseey Yunwa nakeji"

Turo Qofar da Akayi yasa nakai Dubana Ga kofar don Ganin Wanda ke Shigowa.


Junayd ne ya shigo hannunsa Riqeda Ledoji har Guda Biyu Ya Ajiye saman desk Sannan ya qaraso wajena.


"Maman Unborn har kin Tashi? Ya jikin , Nasan kin tashi da yunwa Ga Abinci Na siyo mki sannan ga Magungunan ki Kisha Amma ki farayin Sallah kinji Sulthyn yaya"


Kafeshi nayi da ido ina Maimaita kalmar "Unborn" dinda naji ya Ambata.


"Yaa Ban gane Unborn ba, Dawa Kakeyi ni Jaanu ? "

"Ke mana Bari na kira Yaya na farayi masa Albishir"


Damm Gaba na ya fadi dukda kuwa ban Gama fahimtar inda zancen nasa ya nufa ba Amma na daure nace

"Pitá Krypyá Maat!" (Daddy pls karka Gaya mshi)

Hafsah tayi 'Yar dariya tace

"Tunda tace Kar a gaya mshi kar A kirashin qila so take ya faraji daga bakinta Kun dai San halin Rigimatun namu"

Ta qarashe magana tareda Bawa Janaan hannu suka taafa yayinda Junayd yayi msu Sallama ya fita don Anajiransa Janaan tayi masa Rakiya Ya tafi.

Tana dawowa ta iske har na tada Sallah ta zauna suka cigaba da Gulma na itada Hafsah har Na idar da sallan.


"Munafuqar Allah ,Nidai ince wannan Kwadayin Yayi yawa da Anyi magana tace Ita Babu Abinda ya ta6a shiga Tsakani Ina zata Samu Ciki Waya mutu waya tashi ,Gashi ai Anyi walqiya an ganki"


Nima dariyar nayi tareda kai mata Bugu ta kauce tana dariya

"Er Air Nifa har yanzu ban yarda Inada Ciki ba wallahi, Kawai Ina tunanin Irin Cikin TITIN nan ne na maleria Cus serious babu Abinda ya ta6a shiga Tsakanina dashi Illa fyaden da yayi mn har sau Biyu Kunga ni banson Dogon Magana dan Jawo mn Abincin yunwa nakeji"


"A'uzu Jaanu kinji fa Wai Fyade"

Hafsah ta fada Cikin dariya tareda bama Janaan hannu suka tafa

Ni kuwa ko kallonsu ban sakeyi ba na jawo Abinci na faraci A raina kuwa Ina Taya kaina Murnar samun Cikin , Don ni Sosai nake son Yara Shiyasa ma Su Ameer basua Rabuwa da Gidana Dukda kuwa Ammie bata son Yawan zuwansu idan ta hanasu zuwa Saina San yanda nayi nasa Abdool ya kawo mn su ,haka kuma sbd son yaran da nakeyi ne yasa nafi kowa Baqin Cikin Zubewar Cikin Ramlah, baqin ciki na daya da ya kasance Cikin DODO na ne Kuma Wanda ya samu ta Dalilin Fyade haka kuma jinin Umma , Tsoro na daya kar Umma tasan inada Cikin nan bare ta Samu Damar da zata Zubar da Cikin.

"Besty ,Masoyiya? ,Wai da gaske ciki ne Dani?"

Kai suka gyada min Alamar EH

Hafsah ta qara da Gama Result din chan kan table

Tashi nayi da dau Result din na duba da kyau na Tabbatar ba Rubutun Janaan bane sannan nayi Murmushi mai kamada dariya tareda Fadawa kan Bed.

"Wayyo dadi kasheni"

Abinda na furta kenan a bayyane tareda Lumshe idanu na.


Gabaki dayansu Suka kalle juna Tareda dage Girarsu daya Suka fashe da dariya Duk a lokaci 'daya ,Kaman an mintsileni na sauko daga saman Gadon na nufi bathroom na wanko hannu na sannan ba dawo na zauna a qasa ina kallonsu daya bayan daya.


"Besty, Masoyiya ina son Cikin nan ,don Allah karku Fadawa kowa Ko YaaAary din don Allah na Roqeku"

"Meyasa?" Duk suka tambayeni Cikin Fidda idanu waje.


"Saboda inason na haifeshi ,Banason Na rasahi kaman yanda Aunty Ramlah ta rasa nata Cikin"

"Ban Gane ba ,Kinso kice Cikin Aunty Ramlah ya zube?"


"Eh mana.........." Nan na basu labarin yanda Akayi da Hukuncin da Abba ya dauka ,na daura da cewar

"Wlh bazan iya Haquri ba idan Aka Zubar mn da Ciki Shiyasa ma nace haka please kunji"


Hafsah DA Tuni Idanunta suka Ciko da qwalla ta qaraso ta Rungume ni Cikin kuka take fadin

"Eyyerh nyfee .....Haqiqah Umma bata kyauta ba ,Kuma nima banajin dadin Abinda Take mku Kawai Sharewa nakeyi Sbd Itadin Uwa tace bbu Abinda na isa Na Aikata in Baso nake Fushin Allah ya tabbata Akaina ba neryferh ina Ganin Kaman nice kadai A Duniya banyi sa'ar Uwaba ,Kiyi Haquri kinji Inshaallahu komai zaizo Qarshe, mun dau Alqawarin Bazamu Gayawa kowaba Inba ke kika Umurcemu da mu bayyana ba,ki kwantar da hankalinki Amma Ba Alqawarin da muka dauka bane matsala Yanda zakiyi ki 6oye Cikin shine matsala"


"Wannan ba matsala bace , kudai Ku mn Alqawari "


Janaan tace "Munyi mki Alqawari inshaallah bazamu sanar da kowa ba ,Kuma zan fadawa YaaJunayd Karya Shima sanarma kowa "


Sosai naji dadin Amicewarsu ,Hankali na ya kuma kwantawa Sosai..



Abba kuwa A Ranar da na kirashi nace ya sasassauta Hukuncin da ya dauka kan Umma a Ranar Yasa aka shirya mata Visa Cikin kwanaki Uku aka gama komai ya turo akai dauketa Zuwa Denmark inda yake..


Aikam tasha Fa'da kaman zai cinyeta danye Tunda take bata ta6a ganin Fushin sa irin na Ranar ba Don har daga hannunsa yayi Akan ta ya Shahara mata mari ,haka itama kakus ta rufeta da nata fadar


Ranar dai Umma ta banbance tsakanin Aya DA tsakuwa dukda hakan batayi nadamar Abinda ta aikata ba illama tsanar da takeyi wa Munayferh da ya kuma ninka uban wanda takeyi mata a daa kuma kuduri Aniyar Ganin bayan Munayferh da Uwarta wacce take tushen Tsanar da takeyima Munayferhn.



Aaryaan kuwa bayan Faruwan lamarin nan da Kwana Biyu CP Ya kirasa yace an bashi Muqamin Inspector (Qaramin mataimakin CP) ,Ya kuma Cire Inspector Haris akan matsayinsa Saboda yanda yake Amfani da Kaki yanacin Zalin jama'a Dukda huwa hukuma sunsan Da hakan Amma kudin Ubansa yasa Ba'a iyayin komai Akan hakan yayinda Mutane Ke tsoron rasa rayukansu haka suke Amfani da tsoron Don muzgunawa talakawa.


Saboda yanda Aaryaan ya tunkareshi Gaba da Gaba ya tsaida ba na Kashe bayin Allaahn da basuji baa basu ganiba a Ranar ,Yasa aka bashi muqamin Duk wanda duk da kuwa Bashida qualifications na zama a matsayin Cus ko P-Academy bai Gamaa ba Amma CP yace ba Matsala Qualification bai zama dole Sai an samu a rubuce ba ,Kawai Ganin Chan chansa da qwazonsa Yasa Aka Sashi kumaa Suna da tabbacin shi daya zai iya Jada Tsohon inspector Tunda Kudi Suke taqama dashi Shima Aaryaan din yana da Kudi Wa'enda suka ninka naa Uban nasa ba kuma yanada Qarfin Zuciyar Tunkarar duk Wata matsalar da tazo Gabansa.


Sosai yaji dadin hakan Yakuma dau Akqawarin yaqi da miyagun mutane irinsu ,An tsaida nan da watanni Uku masu zuwa Zaije Course Wanda Za'a Rantsar dashi kuma kafin Watanni Ukun masu zuwa Zai kasance tareda CP yana 'Dan nuna mshi Wasu Abubuwan.......


Yanzu dai babu Wata 6oye 6oye Ya kamata Maahaifiyarsa tasan Aikin da yasa Gaba don Ya samu sa Albarkanta Dakuma matansa ....

Ramlah kuwa Tunda Umma tabar Gidan Hankalin ta ya 'Dan kwanta Amma Tana baqincikin zubewar Cikinta a kullum Addu'arta shine Allah yasa Shine mafi alkhayri a wajenta , .


Amma Abinda Yake cimata Tuwo a qwarya Tun randa Cikin Ya zube ,Duk in Aaryaan ya Kusance ta saitayi ta Zubar da jini Sosai abinke damunta Tun tana 6oyewa har ya Gano hakan Dakansa.


Hakan yasa ya Fahimci Alluran da Akayi mata ne yajawo hakan ,Amma duk iya dabarunsa DA taimakon da yayi mata Abin ya faskara don haka ya tuntu6i Abokinsa Wanda Sukayi Karatu Tare a Pakistan Wato Dr Mausouf.

Dr Mausouf yace ya kasa Gane matsalar Amma Suzo Parkistaan din kawai ya dubata Daganan zai iya Gano matsalar Aaryaan ya Amince da hakan don Yanada yaqinin za'a dace Tunda Dr Mausouf Mutumne Mai basira kuma yafishi sanin Wasu Abubuwa Ta Fannin mata.



*****

Yau Watannin mu Biyu kenan da sati Biyu a makaranta haka kuma Cikina na da wata Hudu kenan ,Kuma har ya fara Fitowa.


Rabon da naga Aaryaan tunda na kar6e mota nayi Gaba ,bana komawa Gida Ko weekend a Makarantar nakeyinshi Kuma ko sau daya bai ta6a nemana ba bare ya tambayi ya nake Tunda yana ganin Su janaan Suka komowa duk weekend, Hafsah ce ma kota koma bata kwana achan take dawowa.


Nikuwa dalilin da yasa bana zuwa Gida sbd Wai kar wani ya Ganni da ciki ya kira Umma a fesa mata tasan yanda tayi ta dawo ta Zubar da cikin don Hafsah ta gaya mn tana Denmark tareda Su Abba.


Kuma Anjiman nan ma Zasu Dawo

Ina zaune ina Waya da Ammie na Hafsah ta shigo Tana dariya ban tanka ta ba saida na Gama wayan .



Na kalleta nace "Hafsah lafiyanki kuwa?"

"Lafiya...YaaAary ne ya Kirani Yace In gaya mki Gashinan Zuwa yana hanya ma so ,Ki shiga ki kimtsa Kafin yazo...."


Wani Uban Hararar da na watsa mata yasa ta Kasa qarasa maganar ta Rufe bakinta tana dariya .


Janaan ta fito daga Daki tana fadin " Wai lafiya "

Nan Hafsah ta kwashe ta gaya Mata.



"Aikam wlh baki isa ba, Garama ki tashi ki shirya in ba so kike Mu Shiryaki ta qarfi da yaji ba"

"Jaanu ina wasa dake ne?, Zan 6a66allaki fa"

"Eh naji ki 6a66allani din ,Hafcey Tayani mujata" ta fada tareda Nufar inda nake tajani na miqe ,Babu yanda na iya nasan idan nayi Gardama yanzunnan sai su ce zasu Shirya ni dakansu.



Sosai nayi missing dinshi Amma Tsoro nake Kar Yaga Cikin dake jikina ya Gayama Ummma ta zubars.

Haka na shirya Cikin wata Doguwar Riga baqa mai Flay Tana da Ratsin golden Wanda Ya Fitowa Asalin kyan kayan , na yana kaina da mayafin Rigan Sannan na Dauko wata Jibgegiyar Rigar Sanyi na daura akai.


Dukda kuwa Sanyi akeyi Sosai Amma sbd ya 6oye mn Cikin na saka Sannan na fito ina wani 6ata Fuska a dolee sun takurani .

Ina Fitowa hafsah tace

"Yana waje yace ki fito kiyi masa iso"

"Mtswww....ya ma raina mn hankali, meyasa bazai Kirani ya Gaya mn ba sai ke ?"


"Malama kin manta kinsashi A blacklist ko ya Kira bazai Samu ba mah" Hafsah ta fada tana hararana tareda Jan hannu na mukayi waje.


Janaan na zaune tana kallon ikon Allah bata tanka mana ba har Muka Fita ,Ita Zazza6i ma takeji shiyasa ta ra6e Wuri Guda tana kallon Mu.



Muna fitowa Hafsah ta saki hannuna tayi Ciki Ni kuma na shiga Waige Waigen ta inda zan Ganshi ,chan na hango shi yana zaune kan kujera kusa d Driver Suna Hira.


Yana hangoni ya miqe ya nufo inda nake yana Murmushi, Kallo daya nayi masa Na kauda kai yayi wani Irin fari Ya rame Sosai.


Shima Kallona yake yana mamakin yanda Yaga na Rame yakai Dubansa ga Cikina Wanda nake qoqarin 6oye bayyanar sa Da Rigar Sanyi, dama Chan Tuni Yasan ina dauke da Cikinsa Kuma duk wata Motsinda nakeyi a idonsa Sbd baya Kwana Biyu baizo Zaria ba, sbd Binciken da suka farayi akan Hajiya larai.


Ganin yanda nake ta wani 6ata Fuska hakan ba qaramin bashi dariya yayi ba .


Amma sai ya murmusa Tareda ware mun hannayen sa Alamar nazo Garshe ,Hararar sa nayi tareda Murguda masa baki.


"Come on Sulthy, please..."


Qarasowa nayi Ina tafiya kaman wacce kazar da Qwai ya fashe mawa a ciki ina Harararsa na fada Jikinsa tareda Sauke Ajiyan Zuciya a lokacin da na shaqi sanyayyan Qamshin Turarensa.


Hannu yasa ya zagaye bayana Cikin jindadin Ganina ,Da qyar na samu ya raba jikinsa da nawa.


Ya kamo hannuna yana Wani Irin Murmushi Wanda ke qarawa Fuskar nan tasa Kwarjini

"Sulthy Bakiyi Fushi Dani ba ko?"


Na hararesa batareda Na bashi Amsa ba.

Ya matse hannuna tareda Fadin

"Allah ya baki Haquri "

" kaima ya baki idan da dadi😏"


Na fada tareda qoqarin barin wajen.

"Okay Sulthy, badon ke nazo ba, nazone Don mu Gaisa da Babyna "


Zaro ido nayi baby kuma?

"Eh cikin da ake qoqarin 6oyewa Likita don kar ya Sani"....

















GA SU UMMA NAN A HANYA FA😘

KUNA GANIN WACE TSIYAR ZA'A KWASHE IDAN TASAN MUNAYFERH NA DAUKE DA CIKI?


YA MAGANAR TAFIYAR SU RAMLAH NE?



SU INNA RABI FA?


WACECE WANNAN HAJIYA LARAI DN?



DUK AMSAR WA'EN AN. TAMBAYOYIN SUNANAN A NEXT CHAPTER INSHAALLAH😘



Nayi gabas🚶🏼‍♀️


31st oct
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: *HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

بسم الله الرحمن الرحيم...


*_Chapter 59_*


Turo baki nayi na hararesa qasa qasa

"Nifa banida Komai"

Sakin hannu na yayi Ya Kamo Cardigan dinda nake Sanye dashi ,nima hannu nasa na Riqe nasa

"Meye haka?, Banson Isknci fa"

"Yoh kin dauka Rigar nan Zai 6oye Cikin ne?"

"Nifa babu Abinda nake dashi, Sanyi nakeji"
Na fada tareda Qoqarin barin Wajen.


Hannu yasa ya Fincike hular Rigar sanyin ta baya ,Wanda yasani komowa da baya batareda na shirya ba.

Kafin na Ankara har ya Zuge zip din Cardigan din.

Nasa tafukan hannaye na rufe Fuska Saboda wani irin Kunyan da ya Ziyarceni.

Murmushi yayi, ya qarasa Cire Cardigan din

"Oya Open Ur Face and Explain Meye Abinnan da ya qarawa Cikin ki Tudu?"

Ganin yanda nake Karkare Fuska na ma kasa bude Fuskar bare na Bashi Amsar Maganarsa.

Hannu yasa ya janye hannuna dake Kan Fuskata Ya Riqe tare da Fadin rataya Cardigan din a kafadarsa .

"Mu Shiga daga ciki nikam na gaji da tsayuwa"

Babu musu na bishi ,A raina kuwa ina baqin Cikin harbo Jirgina da yayi ,Shikenan Qarshen Cikina Yazo.


Muna Shiga Nayi hanyar dakin mu da gudu, Amma Abin Takaici najishi a Garqame

"Kai Kuzo Ku bude mn kofa mana"

Na fada cikin Daka tsawa
"Baza'a bude ba ,Serve Ur husband first"
Inji janaan.


"Ke banson Iskanci fa don Allah Ku bude min"

"Kinsan Allah wlh Cikin babu mai Bude Qofar nan ,Gara ma Kije ki Tarbeshi"


"Kisani Wlh kunci bashi ,Ba'acin Bashina a kwana lafiya Wlh sai kun biya"

"Eh munji Aje chan a Tarbeshi"

Tsaki naja tareda Juyawa na nufi dinning ,Na zuba Masa Abinci Cikin Plate tareda Abinsha.

Na dubeshi yana zaune kan Kujera Ya daura Qafa daya bisa daya Fuskar nan a murtuqe Tamau ,kaman bashi ya Gama Magana Cikin Raha Yanzu ba Hannunsa Riqeda waya yana latsawa.

Tabe baki nayi a raina Kuwa nace

~Mutum Kullum Cikin daure Fuska da ji dakai Saika ce wani Jinin sarauta?🙁 ,Wannan Ai 'ya'yansa sun shiga uku~

Tunowa nayi da cewar akwai Ajiyan 'dan sa a cikina

~Ta6 Wlh saidai a dinga Kwasan 'Yan kallo don bazan ta6a yarda ya Sa ma 'ya'yana ido bah Ehe~

.

Fridge na nufa na dau Goran Ruwa Da Cup ,na tsiyaya Ruwan A ciki na Ajiye a Gabansa.

"Ga Ruwa...Idan ka Gama Ga Abinci Chan akan Dinning"

Da kallon Mamaki ya Bini yana Al'ajabin yanda na Sauya kaman ba Munayferh Mara son Aiki ba ,Komai tayi sai tace ya bata wahala.

Abinda bai Sani ba kuwa nayi hakan ne don su Hafsah Su bude mn kofar ,Nasan Idan banyi serving Dinsa ba For sure bazasu bude mn Qofar ba.


Harararsa nayi na Wuce dakin ina kwanqwasa Wa,

"Tho Ku bude mn ,Na gama"

Na fada kaman zanyi kuka.


"Ki zauna ya gama Chin Abincin ,Sannan ki tayashi hira, Rakashi Ya tafi Sannan ki dawo zamu bude mki kofar " inji janaan

"Ke banza yana jinki fa, zakisa ya Rainani ne ?, please ki Bude mn mana ,Ki bari na shigo , hijab zan dauka Saina Fito kunji My peps"
Na fada cikin marairaicewa

Shuru suka mn basu sake Tanka mn ba, inajinsu suna Darawa Cikin izgilanci sunqi budewa.


Takaici ya kuma Cikani ,na tabbata in banjeba Bazasu bude Kofar ba.

Na juya na nufi inda yake zaune a kan dinning yana latsa waya.

Naja tsaki "tho kaci Abinda zakaci ka tafi mana"

Dagowa yayi ya dubeni Tareda maida Wayan Cikin Aljihunsa.

"Kinci Abinci ne?"

"Ina Ruwanka dani?" Na bashi Amsa a fusace.

"No naji a jikina my baby is hungry So join me Muci tare"

Harararsa nayi tareda zum6uro baki naja 'Yar gajeruwar tsaki.

"Nifa ka fara Cikani da Surutan ka ,Please Eat and Go!"

Daure fuska yayi tareda Miqewa daga Kan Kujeran da yake zaune ya tako inda nake tsaye Ina Huci , Ganin haka yasa ya daure Fuska Kaman bai ta6a dariya ba.

"Ke Ni tsarar wasanki ne?, Muje kici Abinci"

"Na qoshi"
Na fada kaman zanyi kuka.

"Keh , so kike in mki Abinda baki So koh?"

Na Girgiza kai ,yace
"Tho muje"

Muka koma kan Dinning din muka zauna ,Ya deban mun Abincin tareda debowa Ya kai bakina

Na Girgiza masa kai

''Kai ka faraci"

Ganin yanda nayi magana yasa yakai Abincin bakinsa yaci tareda korawa da Ruwa..

Ya dubeni yace

"Amma bake kika Girka wannan Abincin ba ko"

"Me ka gani?"

"Banji Aroman da na sa baji ba maisan Duk ilahirin Jikina amsawa ba"

Dukda bansani ba wannan Girkin Hafsah ne.

Murmushi kawai nayi tareda mayar da dubana Kan Abincin na kafeshi da ido ,Shikuwa ya cigaba da cewa.

"Sulthy Kin iya Girki fa Sosai ,Bakiga na Rame bane? ,tho ai Rashin samun daddadan Abinci mai dadin Dan dano Irin naki ne"

Ban amsashi ba Amma na 'dan Murmusa Still idanu na nakan Abincin

"Tho Yanzu Nasan bazakici Abincin ba kenan ko?"

Sai a yanzu na dago na dubeshi ,Sannan na Gyada masa kai Alamar ~Eh~


Ya cigaba da cewa" tho me zakici?"

Nace "Cheesy"

Zaro ido yayi yace "Meye kuma cheesy ?"

"Cheese balls"

"Ta6 wannan Wanda ake Siyarwa Ten Ten naira?"

"Yawwa Eh shi" na bashi Amsa cikin zaquwa..

Dafe kansa yayi

"Wlh bazan Siyo ba, haka kawai kije ki Haifa mn tsamurarren Yaro Mara Auki Kaman ke Ko nace kaman Fulani?🙄"


"Ni wlh Shi kadai nake jinci" na fada hawaye na zuba daga Idanuna.

"Tho share hawayenki ,Please kiyi Tunani Ki chanza Wani Abun dakaina ma zan Dafa miki Amma banda wannan please Kinji Sulthy"


Share hawayen nayi nace

"Tho Garin Rogo ,Da Quli quli ba sugar da Ruwan Sanyi"

"Ta6di ,Kina Ruwa kuwa So kike ki haifi Yara Marasa jini a Jika?"


Na Girgiza Kai tareda Matse Fuska.

Zaiyi magana wayansa dake Aljihun Rigarsa ta dauki Ruri ya daga tareda Amsa sallamar da Akayi masa ta dayan 6angaren


"Icesmall whatsup ....kai na fasa zuwa fa ,Kacema Haydar ya dakatar da tafiyan Sai Gobe kawai .....yeah ka kasance Cikin Shiri .....Ohhh na manta Amma ganin zuwa yanzunnan kuwa .....okay bye My Regards To Fam"

Yana gama Wayan ya kalleni

"Tashi muje"

Zaro ido nayi
"Ina ?"
Key din motarsa ya Ciro cikin Aljihunsa ya Cilla mn na chafke.

"Ki bude Booth ki Dauko tsarabar Ku"


Cikeda Murna na miqe na Fita ya Bini da kallo ,Cikin da Nake dashi ba qaramin Kyau yayi mn ba, Harta tafiyata ta Sauya zuwa na Masu Ciki.

Babu jimawa na dawo Riqeda Wata qatuwar jaka ina janshi daqyar na Ajiye a Qofar dakin mu na kuma komawa na Dauko dayan Jakar na Ajiye ina maida Numfashi.


Na buga kofar dakinmu


"Tho sai Ku bude kofar "

Shuru babu Amsa hakan yasa na buga kofar da qarfi

"Ke kin cika mana kunni fa"


Ina shirin basu Amsa naji an Damqi hannuna Anyi Hanyar waje Dani ,Bai tsaya Ko ina ba sai inda ya Parka motarsa.


Kallonsa nayi Fuska daure
"Wai ina zaka kaini ne?"

"Airport Zaki Rakani"

Zaro ido nayi kaman zanyi magana Sai na kuma yin shuru.


"Lemme have my key"

"No bari nayi Drive din"

"A'ah My baby zai Sha Wahala".

Harararsa nayi batareda na tanka masa ba ,na bude kofar tareda Shigewa mazaunin Driver .


Shima Murmushi yayi ya shiga dayan 6angaren ,Baiyi zaton Zan Rakashi Cikin Sauqi haka ba ,batareda Nayi masa Musu ba ko naja masa Raiba.


Ni kuwa baqin Cikin Abinda Su janaan Sukayi mn yasana bishi don na Nuna msu Eh da suka wani Kulle kofa sai kace Sunga dodo Ba Cinye ni yayi ba...


Driving nakeyi hankali kwance Yanaja na da hira Nima ina mayar masa da Martani Akai Akai ,Don Ni Tunda nake Dogon magana mai ma'ana ko hira mai ma'ana bai ta6a hadani dashi ba ,Saidai Dogon Magana Mara ma'ana .

"Sulthy ki kaini Gidan mu na lowcost"

"Me zai kaika nan?, muda zamuje Aviation meye hadin mu da Lowcost ?, Ai kaga baya zamu koma kenan"

"Eh wani Abu zan dauka ko bazaki Iya driving din bane ki bani na ja?"


"A'ah " na fada tareda juya kan motar zuwa lowcost🚘

"Yawwa yaya Wa za'a Dauko a Airport?"


"In Munje kia Gansu"

"Okay na fada ina maida hankali na kan titi .

Shikuwa Gaba daya ni yake kallo yana Kallon yanda nake Driving ahankali Cikin natsuwa da kwanciyan hankali.

Tun ina 'Yar Shekara Sha Biyar zuwa Sha Shida na mallaki mota Nawa na Karan kaina Lokacin da na Cika Shekaru Shashida Na Iya driving kuma nake zuwa duk inda na ga dama da mota ,kasancewar A tsarin Abba duk mutumin da ya Haddace Al'qur'ani mai Girma tho yana haddacewa za'a mallaka mashi Motar hawa Duk qanqantansa kuwa.

Ni kuwa Tun inada Shekaru GomaSha Biyu na haddace ,Daddy na ne ya hana A bani ,hakan yasa na tsaneshi a cewa na Baya Qauna na ,Tunda bayason Farin cikina yana daga cikin dalilan da yasa har Yanzu bana son Ayi Maganarsa A gabana.


Saidaga baya Lokacin da sukayi Tafiya zuwa Laos, na nace akan Nifa sai an bani Mota Kaman yanda ake bama sauran in sun sauke Al'qur'ani


Ba'a wanija maganar ba aka bani mota , nace Aaryaan zai koya mn sbd na samu na Rama muguntar da yake mn, Aikam nasha Wahala Wajen shi idan nayi laifi a gida Dazarar Mun fita da niyyar Koyan mota anan yake Cin Ubana kuma idan naje gida na sanar Gobe in mun fita zai Qara mn ,Kuma ba damar nace a chanza mn malami, Tunda Tun farko ni na za6i Abina.





A harabar Gidan na Parka ,yace na jirashi Sannan ya shige Ciki Babu Jimawa ya fito.


Sanye yake Cikin Uniform din 'Yan Sanda kafadunsa Duka Biyu dauke yake da Three Three Ranks Yayinda Fuskar sa ke Sanye da baqin Glass na NO RESPECT ,Kayan Yasha GHETTO na Guga hannunsa Riqeda Police Beret Wanda Gaban Goshin Hular Ke daukeda Tambarinsu na Forces ,Gashin kansa Kuwa Sai sheqi yake Tun daga nesa, Fuskar nan A matuqar murtuqe tamau.

Ya garaso inda na parka motar Cikin tafiyarsa na zaratan maza Masu Jida kansu Cikin izza da isa ya iso har inda nake



Ina Zaune a Motar Ina jiran Fitowanshi ,Ya bude murfin motar , Ya shiga Sannan ya maida Murfin ya rufe...



"Sorry Sulthy na tsayar dake koh"

Dagowa nayi da dubeshi, nan take gabana Ya yanke ya Fadi na dafe kirji da qarfi nace.

"Kai yaya Babu kyau fa ,Wlh idan suka Ganmu Kamamu zasuyi Kuma Babu Ruwansu suna kama mutum Babu mai qwatarsa Sai yayi 5years in prison "

Na fada a Tsorace Don duk a zatona aro Uniform din yayi kaman Yanda Wasu mutanen Sukeyi idan basu so Su biya RoadTax .

Murmushi yayi don ya Fahimci inda zancen nawa ya nufa ya miqa mn Hular dake hannunsa yace in sa masa .

Qin Amsa nayi Na saki baki ina kallonsa

"Ni ba Fake Police bane kaman yanda kike Tunani , Kalle nan kiga"

Ya fada tareda Nuna mn Post dinda ke Dauke da Sunan AA Costen a Jikinsa.


Zaro ido nayi n ma kasa magana

Ya Fahimci Tsantsar mamakin da Nake

Please Login or Register in order to submit comment