Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da FariNciki duk suka Mamaye 6angare biyun yayinda Suwaiba da Faruq Ke Ta fargaban Abinda zai Biyo baya don Tunda sukaga Innansu ta 6ace basu sake Ganinta ba ,Gashi ko'ina zancensu Akeyi Wai mahaifiyarsu tasa An sace 'Dan Uwan Mahaifinsu ,Manema labarai da 'yan jarida Abin nema ya samu nan aka shiga Yada labarai da jita jita ,da qarya daqarin Da suka saba๐Ÿ˜


***

Yau Kwanaki Hudu kenan Da Kawomu Asibiti Amma Babu Wani Improvement a bayyane amma a badini Komai normal ne.


A hankali ya Fara motsa Hannayensa dake daure da Drip, Sannan ya Fara bude Idanunsa da sukayi masa nauyi Hasken Windown da ya haska idanun nasa ne yasa ya Lumshe su Ahankali daga Bisani ya fara Budesu Cikin nutsuwa Har ya gama waresu Akan DR Habeeb dake Shirin Cire masa drip dindake Daure a hannunsa ,don ya qare.


Idanunsa ya Kai Ga inda Yake harda kayan Dake Jikinsa ,kayan Patent sky blue .


Kallon Dakin yayi Sosai sannan ya maida Idanunsa Ga Dr Habeeb daya Juya masa baya yana Aikinsa.


"Habeeb What the hell Am I doing here? ,Uban me nakeyi anan?"


Kallonsa DrHabeeb Yayi A ransa yace

~Mutum bashida Lafiya ma saiyayi masifa๐Ÿ˜•~


Shuru Dr Habeeb yayi hakan yasa Aaryaan ya Fara tariyo Abinda ya faru dashi ,da qarfi ya Fizge Drip Dinda Ake qoqarin Cire masa ya Miqe tsaye Cikin tashin Hankali da qarfi Yake Fadin

"Ina Matata? ,Where is my wife? ,Kun kasheta ko?, ka gaya mn ina take"

Da sauri Dr Habeeb ya Iso ya dafasa Cikin Calm voice dinsa Yake Fadin

"Ayya sorry Dr ,Situation Dinka baya Buqatar tashin hankali da hayaniya ,you have to calm down"

"Ohhw....don't Tell me to calm down ina Matata take , ka kasheta Ko? ,wlh idan Ta mutu saina Kasheka na kashe Gawarka....ina take?, Habeeb where is my wife?....".


Aaryaan fa ya haukace ya Fita hayyacinsa Daqyar Dr yasamu ya sauraresa kuma yayi masa bayanin Komai dangane da Lafiyata da kuma Qoqarin da sukeyi don Ganin na farfado.


Kallonsa kawai Aaryaan yakeyi da Idanunsa da sukayi jazur kaman Jan Gauta Jikinsa Har rawa yakeyi A Fusace ya miqe ya bar Dakin batareda yace komai ba ,Dr na kiransa Amma ko juyawa Baiyi ba Bare ya sa ran zai dawo.


Yana Fita kai tsaye office dinsa ya nufa Wanda dama Basa ida mukulli Yake buduwa ba , Passcode Yake amfani dashi.

Yana Shiga babu jimawa ya Fito sanyeda LabCoat dinsa kallo 'daya zakayi masa ka fahimci Jikin nasa sai ahankali Qarfin hali yakeyi.


Nurses da sukaga Shigewarsa Office dinsa Kuwa Suka fara Gulma da qananun maganganu Don sun kansu sunsan Kwanakinsa Hudu a Asibiti ko Iya Gane Na tsaye kansa baya iyayi sai Gashi Yanzunnan daga samun lafiyarsa Har ya shiga office ,office Dinda rabonda ya shigeshi ma Har Sun manta.


Kai tsaye ward dinda nake ya nufa ,A qofar Dakin ya iske su Daddy ,Ammie, Abdool ,hafsah ,Suwaiba , kakus da Abba Sun zauna sunyi Jugum Jugum .


Suna Ganinshi Suka miqe tareda nufoshi Cikin tsantsar Farinciki da mamaki, amma me? ,Sai ya kawar dakai kaman bai gansu ba yayi Shigewarsa 'Dakin ,Hakan yasa Suka fara tunanin Ko bashi bane Don Zasuyi Mamakin Ganin Mutuminda baisan Wanda Ke kansa ba a mintuna 20 da suka Gabata Yanzu kuma su Ganshi Da qarfinsa kuma da labCoat......


Saida ya Kusa Shigewa Dakin Ammie tasha Gabansa Zatayi magana ya watsa mata Wani irin Mugun kallo Wanda Saida yasa Gabanta Faduwa Batasan Lokacin da tayi bayaba sai kuma ta fashe da Wani matsanancin kuka ,Kakus da Hafsah na Tayata yayinda Suwaibah Tabisu da kallo jiki a sanyaye Daddy kuwa Tunani Yake a cewarsa wannan ba Aaryaan dinsu bane Aaryaan Dinda Suka Sani yana Chan sun barshi Likita na dubashi ,Maybe Wani doctor ne aka samu mai kamarshi.


Abba kuwa da yasan Halin 'Dan nasa Yabishi da kallo kawai Don bazaiji mamaki ba idan Yayi Abinda yafi hakan ,bayan Wanda suka Gani Kwanaki hudun da suka Gabata ?....

Haka dai suka Cigaba da saqe saqensu Har Lokacin da Ummyn Janaan ta Iso ,Suka Cigaba da Jira a tare Suna Dan ta6a Hira Cikin jimami


***


After 4hrs

Wata nurse ce ta Shigo ward din Riqeda Wata qatuwar Leda Mai tambarin NANFAH BOUTIQUE zata Shige Kakus ta sha Gabanta Cikin kuka take Fadin.


"Haba 'Yar nan Ki gaya mana meke faruwa da itane? Ta mutu ko?, 6oye mana Kukeyi ko? ....Don Allah Ku sanar damu in ta mutu ne ,Munada Heart Dinda zamu kar6i wannan Qaddarar ,Idan Gudun Tashin Hankalin mu yasa kuke 6oye mana ne don Allah Ku daina Ku sanar damu Na rantse idan ta Mutu ba zanyi Kuka ba kinji Alqawari Nayi wlh ki gaya mn kinji .....,Kwanaki Hudu kenan fa ko Motsi Ance batayi Wayyo Allahna Wayyo jikalleta ,Daga Dawowanku Sai kwanan Asibiti?, Wannan Al'amarin damai yayi kama? ,Ga jarirai an barsu Babu Uwa babu Uba abin Gwanin ban tausayi"


Ta dan tsagaita tana Sharr hawaye da Gefen mayafinta

"Yarnan baki gansu ba wlh dakingansu Sai sun baki tausayi ,Har qwallah sai kin zubar msu ,Koninan da kike Gani da na jisun fara Kukan nake Farawa ina tausayawa Iyayen nasu da qaddara ta Afko masu a Rana tsaka ,Ni wlh banga Laifin Haleemah da tace ta tsani Aikin 'yan sanda ba, Inbanda Fitina da Neman Cusa kai Cikin bala'i irin na yaron nan inashi ina Aikin 'yan sanda Bayan Gashi yana Aikinsa na Likita Cikin Rufin Asirina Allah amma sbd sakarci da Iya leqe leqe Yajawo Za'a kashe mn Rabin Raina Uwata kuma jikata....."


Haka ta Cigaba da surutai Cikin kuka da qunar rai ,ita dai Nurse tunda taga ta fara kauce hanya tayi Ciki ta kai masa Saqon da ya kira yace a kawo masa



Haka dai suka Cigaba da Zama cikin jimami Har Lokacin sallah yayi daddy da Abba Suka Fice zuwa masallaci yayinda Su Ammie suka Sami Wuri anan Sukayi Alwala suka Gudanar da nasu Sallahn tareda Addu'an samun sauqi Ga Munayferh.



Bayan sun idar da sallah Ammie tace hafsah da suwaiba su koma Gida su dauko Su haseen don A Ragewa Ummie Dawainiya.


Aikam Tana Fita ,aka bude qofar dakin da Aka kawanatar dani ,kakus tabi Kofar da kallo kaman wacce tayi Aike Tana jiran saqo.


Aaryaan ya Fito Riqeda hannuna Na sauya Shiga cikin Wata Gown Cream colour wacce ta kar6eni kuma tayi matuqar yi mn kyau ,Shima haka Sai kace bashi ya shiga Dakin dazun a matsayin Dr bah....***


Su Ramlah kuwa tunda suka Dawo aka ware Msu 6angare daya Suka tare anan ,Umma kuwa Tana Ganin yanda Saleem Ke Wani liqewa Ramlah Gashi Abba bai bata damar sa musu ido ba ,kuma tashin Hankalin dake Gabanta baisa ta fahimci komai ba ,Kunsan dai Har yanzu ba'a gaya mata ba ko?๐Ÿ˜‰ ,Tho ai bata Sani ba kuma Abba kadai yasani .....



Saleem ne Kwance bisa Dogon Kujerar dake qawace a Katafaren Parlon Aaryaan na samartaka wanyake A matsayin Nasu a yanzu ,Ramlah kuwa Tana Kwance a Kirjinsa Idanunta a lumshe hannayenta Duka biyu na bisa qirjinsa tana xagaye qirjinsa Dashi Salon da takeyi masane yasashi Saurin Riqe hannayenta jin Tana Shirin zautar dashi Kallo 'daya zakayi msu ka fahimci Suna Cikin kwanciyar hankali .


A hankali ya matso da bakinsa daidai kunnenta a kasalance ya Furta

"Mayya kawai"

Duka takai masa a qirji Tareda sake Shigewa Jikinsa A shagwa6e tace..

"Idan maita ne Ai kai ka koyar dani Har na iya ,Kaga kai kafini iyawa ma sosai ,Malamin mayyah"

Dariya yayi ya Shafa kanta a hankali Cikin Sigar rada yace

"Wai Waya koya mki magana ne?, Sai kace ba Ramlahn da na Sani Shuru shuru ba "

Itama dariya tayi tace

"Ai duk kai ka koya mn...."

Gehmmm...Aka waniyi banging Qofar aka shigo batareda anyi koda sallama ba ,Wani irin salati Umma ta saki tareda Dafe qirji a Tsorace..


Ramlah kuwa da farko ta tsorata jin yanda Aka Wani Banko qofar ,Amma da taga Umma ce sai ta Dada Shigewa Jikinsa taredayi masa Wani irin salo Wanda yasashi mantawa da inda Yake ko Nace Abinda Ke Shirin faruwa.....








Yaseen baza'ayi wannan Fadar dani ba๐Ÿ˜…



Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ


26novโœ๐Ÿฝ
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
**HAWAN-JINI NA*
~{uwar mijina* ๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._



ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 74*_




A hankali kuma a kasalance Saleem yasa Hannu ya dagata yana Qoqarin rabata da jikinsa Amma sai ta kuma Kanainayeshi ta qamqaneshi tareda Cusa kanta a Qirjinsa.

Sosai Taso ta rudashi Amma da ya dago Suka hada ido da Umma yaga yanda Jikinta Ke Wani 6ari sai Wani Kyarma Da takeyi kaman mai Ciwon sanyi ,haka kuma idanun nan sun Fito Waje Ga yanda ta Wani qame kaman kamammiyan Shock

Sosai Kunya ta kama saleem ,Wannan karon da qarfi ya Fizgeta ya Rabata da Jikinsa Tareda zamewa ya duqa Har qasa Jikina 6ari Bakina rawa yace

"Ehmm....uhmm....Ina kwana Umma"

Qarashe maganar yayi daidaida Fasa ihun da Umma ta kurma Cikin Fita hayyaci tayo kansu gadan Gadan Tareda daukan mopping stick dindake Ajiye a Gefe Saboda tashin Hankali Saura kadan ta Kife qasa Cikin Masifa take la'antarsu Tana gayan miyagun maganganu Akansu tareda Auna msu zagi Tana La'antarsu tareda Kai msu Duka Suna Kaucewa ,

Ramlah kuwa Abin ma Dariya ya bata Sai ta daukeshi hakan tamkar Game ,Dariya takeyi Sosai hakan


Umma ta qufula iya qufula ,Haushi ya turnuqeta Ga Zuciyarta dake Bugawa da qarfi da qarfi Tana Barazanar Tarwatsewa ,Bacin rai baqinCiki Qunar Zuciya ,Da Rudani Duk suka dirar mata Suke Barazanar Haukata ta ..


Jiki na rawa ta fice a Dakin ,Idanunta Suka kawo qwalla Tana baqin Cikin hada zuri'a da Ramlah Gashi tazo zata Tarwatsa msu zuri'ah da Fasiqanci Wanda ta gada wajen mahaifanta (Acewarta๐Ÿ™ƒ) ,ta kuma sha Alwashin A yau dinnan Ba sai Gobe ba sai Aaryaan ya saki Ramlah ta fice masa a Gida tareda Saleem ,Kuma Tasha Alwashin Kafin ta fice a Gidan sai ta Gasa mata aya a tafin Hannu taci mutumcinta Ta wulaqanta ta ,Sai duniya tasan abun kunyan da ta aikata da Auren danta akanta ,Kuma bazata Kar6i Humdah a matsayin Jika ba dama chan bata kar6eta ba Gudun 6acin ran Su Abba ne yasa Ta kasayi mata Komai Amma da Mummunar qudurinta akanta harda 'Yayan Munayferh mah ,Kasa tsaye tayi ta kasa Zaune Da ta Lumshe idanu sai ta hango Ramlah Rungume da Saleem ,Kuma Abin mamaki ta kasayi msu komai ,da ta tunkaresu sai Taji bugun zuciyarta na Dada harbawa Zuciyar ta nayi mata Kashedi akan kartaje ,Gani take idan ta sake Yunqurin Komawa Abinda yafi wannan zata Gani , Dariyar da taga Ramlah keyi ya kuma sata cikin Wani tashin hankalin Anya Ramlahn da ta Sani ne kuwa?, Inaaaa ba ramlahn da ta Sani bace , ramlahn da ta Sani a da bata iya hada ido da Mijinta idan Tana Wajen Bare ta Tabashi harda Runguma , Boom ! Da adane Umma ta kama Ramlah da Aaryaan cikin wannan yanayi da dukkanninsu Rayukansu ya 6aci don cin mutuncin da zatayiwa Ramlah saiyafi Cin mutuncin da Akeyiwa Mazinaci Amma abin mamaki sai Gashi ta isketa da Wani Qato amma sai ta kasayin komai ,qarin Abin Haushin shine yanda Ramlah ta nuna Rashin damuwanta Bare taji tsoro illa ma Qara kunsa mata baqin Ciki da tayi.


Kai tsaye Dakinta ta koma ta sha Kukanta Har Saida zazza6i ya nemi ya kamata ,ta rasa Gane Kukan me takeyi ne? Kukan Taya 'danta kishin Wani na Latsa masa mata ko kuma Kukan Ganin Dariyan Ramlah da tayi ne ,Ko kuma Kukan BaqinCikin Ganin Ana Shirin Aikata Haramun A gaban idonta ta Kasa Qwa6arsu ,Ko kuma Kukan tausayawa Makomansu takeyi........


A chan Dakin Kuwa Umma na Fita Ramlah ta zube kan kujera Tareda tuntsurewa Dariya , yi take Tana qarawa Har Tana Shidewa Saida tayi mai isarta taji ta Gaji don Karankanta sannan ta tsagaita Tana maida Numfashi.


Saleem Kuwa harde hannayensa yayi yana kallon yanda take Dariya ,ba qaramin kyau takeyi ba idan Tana Dariya zaiso ace ta kasance Cikin Dariya da walwalah Har Abada ,Saida yaga ta tsagaita kamin ya maida dubansa Gareta Sosai yana nazarinta.

"Babe What Have you done?, ne kike Tunanin Kinyi ne?, Abinda kikayi bai kamata ba Gaskiya, Ki tuna fa Kome tayi She's still Ur mum......"


"Hey...hey malam dakata manah Point of Correction Guy!...My Ex mum Inlaw....Ex mum Inlaw or Ex Mum's sister She isn't my mum and she Can never be okay?...''

Dariya Maganganun nata suka bashi don haka dara kadan Sannan ya matso inda take ya zauna kusada ita tareda riqo hannayenta ya matsasu Cikin nasa ,Cikin killer voice nasa ya fara magana kaman mai rada

" Baby ba'a ta6a chanzawa Tuwo Suna She is ur ex mother Inlaw and Also ur mum's sister ,So she doesn't deserve all these From you ,You need to calm down Kiyi haquri ki share Abinda ya faru a baya ki bari mu fusakanci Gaba Allah yanason masu tawakkali da Yafiya ,ki Yafe Abinda Ya faru ki Cigaba da bata Girmanta Baby please kinji"


Wani Uban tsaki Ramlah Taja tace

"Naji Allah nason masu tawakkali Amma innamal a'amalu Binniyyat , konace na Yafe Mata a iyakar fatar bankine , zuciyata bazata ta6a Goge Abubuwan da suka faru tsakanina da ita ba ,Gara da Allah ya bayyana gaskiya a Lokacin da ya dace domin wlh Har na fara tunanin Rayuwan da zanyi a matsayin Diyar Umma wacce ta sha wahala wajenta a matsayin Matar 'danta Wanda Yake Yayanta Kuma harda rabo a tsakaninsu...."

Sai ta qarashe maganar tareda tuntsurewa da Wata Dariya ta Cigaba.

"This is Crazy dude ,Abin babu ko dadinji Wai Ramlah ta Auri Yayanta Wanda Suke Uwa 'daya Uba daya so irritating mah"


Murmushi Saleem yayi ya lura Yau Ramlahn tasa Tsiwa takeji SHIYASA YA BIYE MATA

"Ramlahty but kin San in ba Don Nurse ba da tuni hakan ta kasance ko?, Ki Godewa Allah ki Gidewa nurse da Suka hana Afkuwan Aikata Abun kunya..."

"Dallah Ni ina Ruwana da wannan matter din?, Ifrah zaka gayawa Wannan Zancen ba Ni ba ,cewa zakayi da badon nurse tayi Tunani ba Da Ifrah da Aaryaan sun aikata Abin kunya ,Abege let's Switch that topic Yaushe zamu koma Gidan mu ne?, Nifa na Gaji da zaman Gidan nan Tunda An fara Shigowa babu Sallama Allah kadai yasan Abinda Za'a Aikata mana Gobe ,Maybe Har bedroom Za'a Rinqa Shigowa ana Investigation Don Ni Nasan halin kayana Wannan ma kadan kenan daga Cikin Aikin mu"


Saleem ya Gane inda Zancen nata ya nufa sai yayi Dariya yace

"Inshaallah immediately ana Gama shagalin Bikin Hafsah da hilaal zamu koma Ko kwana daya bazamu qaraba"


6ata Fuska tayi kaman Zatayi kuka

"Baby Saura 3days fa Ayi Bikin ,kuma kana Maganar har a gama shagalin biki Gaskiya 3days Yayi yawa ....nidai Wallahi Gobe Gobennnan zan bar Gidan nan I can't take it any more , Gara KO Gidan hayane ka samu ka kama mana Ehe Bari ma ka Gani yanzunnan Naje na fara shirya kayana"

Ta fada tareda miqewa ta nufi Upstairs Shikuwa ya bitada kallo har ta kusa kaiwa sama tajuyo ta kalleahi tareda dage masa Gira daya "yadai"

Girgiza mata kai yayi "ki shirya muje mu duba EX Kishiyarki da EX husband dinki"

Murmushi tayi Tareda gyada kai tayi Ciki....


A chan Asibiti kuwa Sosai Su Ammie sukayi Murna da Samun Lafiyar mu ,Amma sai Aaryaan ya Nace Akan mu koma Gida Yanzu Don na tada hankali na Dole sai an kawo mn Yarana na gansu na kasa haquri Hafsah ta dawo Don An gaya mn taje daukosu , babu yanda suka iya da Abinda yafi qarfinsu Haka muka Nufo Gida...



Muna dawowa Umma ta fesawa Abba Abinda ta ta Gani Harda qari wai ganinsu tayi sunayin Babban ๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ ,Abba kuwa ta6e baki yayi yace Saime don Ta ganta da Wani idan ita ta qita Wani yasota sai ya zama laifi? ,mamakin rashin damuwan Abba a wannan Labarin Shine yafi tada mata da hankali ya kuma da'da sata cikin rudani Haka Umma ta wuni Ranar sukuku kaman mara lafiya ta tabbata babu mai Yarda da ita kasancewar Shedar Zina babbar shedace haka kuma da wuya a Gasgata ta Saboda Sanin Da sukayiwa Ramlah kamilace ,koda akazo Cin Abinci daqyar Ummmake Tsakura da sun hada ido da Ramlah sai tayi Mata'yar qaramar Dariya Wata zubin harda Gwalo Abba da ifrah kadai Suke hankalce dasu amma basu tanka ba don basusan mafari ba...


Bayan Mun gama cin Abinci Abba ya sanar dashi labarin da ya girgiza shi Wato an qona mana Gidan mu na Barnawa lkcn da muke LIOS Sakamakon Rashin Amincewan da Junayd yayi Akan ya siyar Musu dawasu Files Wanda ya shafi Case Dinda Yake jagoranta ,sunyi Zaton ya Ajiye Files din a gidane shiyasa Suka qona ,Amma Allah ya taqaita babu Wanda ya rasa Ransa Kuma babu Wanda ya samu rauni ,kuma file din na hannunsa ne....



Aaryaan yayi baqinCiki Sosai , saida daddy Ya Tausasheshi da rarrashi Tukunna ya haqura ya fallawa ma Allah komai ,Yanzu Shikenan Na dawo nan kenan Kona Gama jego Har Ya samu yayi mana Wani Ginin?๐Ÿฅบ



Da Akwai chakwakiya fa ,Ni bazan iya zama tareda Umma ba ,banaso Abinda ya faru a baya ya kuma maimaita kansa.


wani kulawa na musamman yake bani , motsi ba motsi ba sai ya tambayi me nake so ayi, baya rabuwa dani Inba Sallah zaijeba kullum yana taredani harta Wurin Aiki ya daina zuwa Haka kuma maganar Case dinnan ya bari sai qurata lafa , su Ammie kuwa Suna Ganin Rashin Kunya don A Gabansa Yake nuna mn tsantsar Qaunar da Yake mn ,Inbanda jegon da nakeyi da tuni ya daukeni mun bar kd zuwa Gidansa na Zaria , ina ganin gata da soyayya wajen mijina maras misaltuwa, har saida naji haushin kaina na hanasa Kalmar Da ya wahalar dani Ranar fade ,Sosai Aaryaan yake tabbatar man shi'din me 'kaunarta ne ,haka nimahaka ,Sosai Muka Dada shaquwa Cikin Kwanaki Uku kachal ....

Rana bata qarya Saidai Uwar 'diya taji kunya ,inji hausawa๐Ÿ˜




Tho yau aka daura Auren Hilaal Kabeer da Amaryarsa Hafsah Aabaan , daurin Auren da ya samu Halartar Manyan mutane daga sassa Dadama Na qasar nan , haka kuma dukda Yawan jama'an Da suka halarci Taron Hankulan 'yan Gidan bai kwanta ba don basu so mutane dayawa Su halarci taron ba ,Sbd Gudun Sharrin Baqo duba da Abinda ya faru Sati dayan da ya wuce ,harta Dinnern da Aka shirya fasawa akayi ana Gama daurin Aure aka yi wunin biki sannan aka Tafida Amarya Gidanta .


Duk wunin Ranar ina liqedashi , yanzu haka ma muna Garden Kwance Yake akan Grass Carpet Idanunsa na kallon sama yayinda Ni kuwa nake Manne a Jikinsa Ina wasa da siraren Gashin dake Kwance luf a Qirjinsa Ta Cikin rigarsa , A hankali Cikin Jin dadin yanayin Nace

"Yayana da farko sha'anin yau Baiyi dadi ba ,Amma a yanzu sai naji yanayin Ya Bada Wani irin Shauqi Wanda ya haskaka Ranar , yayana inaji a jikina Ranarnan zata kasance cikin kundin qaddarata walau mai kyau walau mare kyau ,Nidai fatana Shin Allah yasa Wannan qaddarar ta zama mai kyau kuma Wanda bazata Raba muba , yayana I Don't Want To Lose You, I Don't Want To Cry With The Memories Of You And I know That I'll Never Leave You zamu kasance tare Har Abada Cikin So da qaunar Juna ,ina sonka mijina..."


Qarar wayana ne ya katseni a kasalance nasa Hannu na daga Batareda na duba mai kiran ba ,Cikin murya Chan qasa Nace....


"Hello"

Muryan janaan naji Tana cewa

"Ke ina kika shiga ne Muketa nemanki Tun dazu, kin bar yara sai kuka Sukeyi ".

Numfashi na Sauke a kasalance Cikin qasa da murya Nace

"Wai yanzu akan wa'ennan Fitinannun yaran kika katse mn jindadin da nake Ciki?, Ba kina da Abinda Zaki basu ba?, Ki hadasu da Little Aabaan (danta Shima yaci Sunan Abba) ki shayar dasu Gabaki daya , kinji Karki sake Kirana ..... Ina tareda ubansu ne"


Ina gama Fadin hakan na kashe wayan ,ina kashewa Wani kiran na Shigowa Dubawa Nayi, Numbern Hafsah ne , a Raina ina tunanin Maiyasa ta kirani a wannan Lokacin ,Yar qaramar tsaki naja tareda Katse kiran na sa Hannu na Shafa Suman kansa

"Bakace komai ba meree Raajaa (My king)"

A kasalance ya Jawoni Jikinsa ya Rungume Yanajin Gabansa na faduwa Zuciyar sa na Raya masa Abubuwa da dama Cikin maganganuna .


A hankali ya bude baki kaman mai jin sanyi ya Furta

"Am speechless Sulthy ,na rasa mai zance miki na rasa mai zan gaya ,If Theres One Joy, One Love.. From Which I Never Want To Part.. Its You sulthy My Very Special Love is with you Sulthy, My World, My Heart, My Life..! all are with you Kece Rayuwa ta kece Farinciki na ,ina tsoron na rasaki Idan na rasaki wlh mutuwa zanyi ..."


Ya qarashe maganar Cikin fuzgar Numfashi Kaman maijin sanyi Tareda Qara Rungumoni Jikinsa ya Qanqame.


"Ohgh Yayana Ka fama mn Ciwona "

"Sorry" ya gaya yana janye Rigar da ta Rufe kafadata daidai wurin Da aka harbeni tareda Shafa Wurin , daidai nan Umma ta zo Wajen da sallama murmushi dauke a Fuskarta ,Tana daukeda Haseen da hasnaah wa'enda keta faman tsala kuka.


A razane Na dago na hada ido da ita nan take Gabana ya yanke ya Fadi dasauri na kawar dakai Gefe Tareda ta6e baki ina Ayyana Rashin Mutuncin da zanyiwa Janaan Don tasan Ban bari Umma Tana Ta6a mn yara amma Don naqi zuwa zata Wani bada mn yara ,salon ta koya msu Rashin Imani da tausayi?๐Ÿ˜’


Aaryaan ne ya miqe a kunya ce ya kar6i yaran Tareda'dan jijjigasu yanayiwa Umma godiya , Umma kuwa Kallona tayi taga yanda na Wani hade Fuska tamkar wacce taga Fir'auna.


Cikin sakin Fuska tace..

"Diyata duk wannan shan mur din fa ?, duk na menene?"


Tsaki naja dai dai Lokacin da Saqo ya shigo wayana daga Hafsah.



๐Ÿ’ฌ"Masoyiya Please Karki Yarda ki hada idanu da Umma cikin Daren nan please "


Tsaki naja na kuma kallon Umma sama da qasa ,Wani qaran saqon da najine yasa na dau wayan a Fusace na duba Saqon



Daga Janaan ce

๐Ÿ’ฌplease besty kar ki Yarda ki hada ido da Umma cikin darennan Koya zakiyi kisan yanda kikayi ki hana idanunki haduwa da nata Please, bestyna Mrs AA. Ummyn Haseen da hasnah , Nasan Zaki Iya its just a gym try please please Kinji......"












Nayi gbas๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ


Manage๐Ÿ˜‘


27nov
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
**HAWAN-JINI NA*
~{uwar mijina* ๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._



ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...




*_Chapter 75*_





Jiki a sanyaye na Dago na kalle Umma dake Shirin barin Wajen sannan na maida Dubana kan wayan fara typing a sanyaye

๐Ÿ’ฌBabe indai wannan game ne da Gaske na Amince Nayi Loosing Don ko a yanzu muna tare Kuma tuni na dade da hada ido da ita ....


Ina Gama Turawa na danna Gefe da niyyar Kashe wayan gaba daya Wani Saqon ya sake Shigowa Saida naja tsaki kamin na duba.

Bank Alert ne Daga companyn su daddy , dama kowane Qarshen Wata akan turo mana kudade daga Kowane Companyn shi ,amma tunda ya tafi Abba yace adaina Har sai Allah ya bayyanashi ,Murmushi Nayi A Raina ina Godewa Allah da ya sake Ara mn Mahaifinnawa a karo na Biyu ,a bayyane nace

"Allah ya bar min kai daddyna ya Qara maka Nisan Kwana da tsawon rai mai amfani ya kareka daga Sharrin masu sharri ,Ya baka Ikon ciyardamu ta hanyar halal Ya Raba Hanyarka da haram ya nisantaka da masu nufinka da haram ya tsoshe maka duk wata hanyar Da zata sadaka da Haram ,Daddyna Allah ya saka maka da Aljannah Firdaus ..."


"Ameen" Aaryaan ya amsa mn murmushi dauke a fuskarsa

A hankali ya Jawoni Jikinsa tareda zaunar dani shima ya zauna tareda daura mn Haseen bisa cinyata ,nasa Hannu na Riqe yaron Sannan ya kwanta tareda

Please Login or Register in order to submit comment