Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

2:30pm muka fito daga lectures Nida hafsah da Jannan Muna Dan taba fira Dai dai wurin mai cafรฉ Muka ga Ks daud yana zuba takardu cikin Wani Envelope,

Na kalle Su Hafsah nace "Gafa mutumin mu"
Jannan ta rage murya cikin Alamun rada tace"Ke Lower your voice yana jin mu fa"

"Harararta nayi nace" To yayi ta jin mu mana ni ina ruwa na?, Nasan ko yajini Babu abinda ya isa yamin Wanda ya wuce ya bani CO kuma in CO ne a rigar kowa take, idan ka shigo Uni kafita baka ta6a samun CO ba to ba karatu kayi ba your are just moving around ba karatu kike ba"
A dai-dai lokacin gama kwashe takardun ya juyo yamin wani Shu'umin murmushi Ya kadai kai ya wuce
Kallon da ya min yasa gabana faduwa, Tsoro da fargaba suka dira min a zuciya, Muryan Hafsah naji tana cewa "Yau mun Shiga Uku kashin mu ya bushe ,Nasan wlh babu Mai raba mu da Ks sai Allah" ta karashe magana kaman zata yi kuka

Harararta nayi tare da turo baki gaba " Matsoraciya kawae Wa ya gaya miki hakan?, Nifa yunwa Nike ji , Abege let's Go''

Daga nan babu Wanda ya kara magana kowa da abinda yike saqawa aransa.
A mota ma haka ta kasance kowa yayi shuru babu mai magana duk cikin mu Ganin shurun yayi yawa yasa na Kunna Sauti nace "Jaan kar ki bani kunya mana ban sanki da tsoro ba,Na kalle hafsah wannan Abin itace matsoraciya a cikin mu, koda Mr Ks zaiyi mana Abu bai kamata muji tsoro ba , kin manta yanda mukayi Wa Malam Suleiman Oga lab din mu kenan ?"

Jannan tayi yar dariya "Ni Wa yace mike ina tsoro?, Aa ni Dan naga kinyi shuru ne shi yasa ni kama baki na"
Daga nan fira ta 6arke a tsananin mu har muka isa gida


A falo muka tadda su sunyi jugum-jugum yaya Aryaan yana zaune yana latse latsen waya Ramla kuma tana kallon Tv Umma na tsakiyan su ta wani hakimce a kujera,
Ai bansan lokacin da dariya ya kubce min ba na shiga darawa harda rike ciki, Duk suka waigo suna kallo na harda su hafsah
Ganin na kure su da kallo ina darawa yasa yaa Aryaan fahimtan abinda yasa ni dariya , Ya banka min harara nima na rama harda murguda baki , Ya min Alama da ido zan kamaki yarinya ,
Na karasa na zauna kusa da kujerar su na wage murya ina fadin "Umma nifa ban gane ba kurame kuka zama ne?"

Kafin Umma tayi magana har hafsah ta rigata da fadin "Uhm Umma ki kyale yarinyannan duka take so....,Nifa yunwa Nike ji babu abinci ne a gidan?"

Nace "Food monger, ba yanzu kika gama cin abinci ba?"
Tace "kuka gama ci dai"

Muryan Aryaan ya katse mu "Enough!, Kun Shigo mana gida babu ko sallama balle gaisuwa kun wani ishe mutane da surutun Tsiya"
Hafsah da Jannan suka gaida su niko turo baki nayi nace "Wlh babu uban da zan gaidar,Ai da na shigo da harara aka fara tarya na"
Na kalle Ramla nace "Anty Ga Qawas fa Tazo cin cin-cin ne"

Tace "Ayya Sannu kawarmu ya sunanta"

Nace "Jannan sunanta amma Nida hafsah muna kiranta jaaan",
Wow Jannan nice nameTo sannu barina debo maku
Umma ta tashi ta shige daki nabita da kallo ina ta6e baki
Yayinda Ramlah ta mike ta nufi Daki Dan Dibo mana cin - cin
Na kalle yaa aryaan dake ta faman latse waya nace " Mutun ya wani kanainaye a tsakiyan mata ko kunya bayaji*
Sarai yasan dashi Nike amma sai yayi min banza

Sharenin daya yi ya ta6a ni sosai sai na cire takalma da mayafina na cilla gefen ShiShi ....


Manage pls๐Ÿ–‹๏ธ

MASU SHARING A GROUPS GODIYA DUBU A GARE KU


MASU KARATU BASU COMMENT KAR NIKE KALLON KU๐Ÿ˜Ž



MASU ZUBA MIN SHI (COMMENT BA) INA YINKU IRIN TOTALLY A CIGABA DA ZUBASHI๐Ÿ˜









Duk wacce comment dinta tafi burgeni next chapter nata ne๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ



Share
And
Comment

Bye


Fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ
12august2k20

๐Ÿฅขโœจ *UWAR MIJINAH*โœจ๐Ÿฅข
~(Hawan jininah๐Ÿ’”)~


๐ŸคBy Fahnaan๐Ÿค

MARUBUCIYAR:MA'ESHERH (ANNOBA)

๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€

๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA


๐ŸคFahnaan๐Ÿค
ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...





*Chapter 4*

A razane ya mike yana cire earphone din da yasa a kunne , Yana 6ata Fuska kaman wanda yaga abin kyamaYa zuba min Manyen idanunshi,Waenda lokaci guda Suka rine zuwa kalan Jaa sbd tsananin 6acin rai, Nan danan Yan hanjin ciki na suka kada jikina yadau rawa
Yayo kaina zai riko ni ai da gudu nayi bayan Ummah wacce fitowanta kenan daga daki .ina
"Wayyo Umma Kin ganshi ko" su hafsah da Jannan suka sa dariya
Chak ya tsaya yana nuna Wa Umma kayansa da Na jefe shi da takalma(kuma fa wallahi babu Abinda ya sami Rigar๐Ÿ˜ฉ)

Yayo bayan ummah inda nake makalkale ta Ya finciko ni hakan yasa na kwala wata razananniyan kara Wanda yasa shi Rumtse ido da karfi

Cikin Hosky voice dinsa mai nuna alamun gargadi yace" witch!,How dare u step Ur dirty shoe on me?, who hell did u think u are" yaja wuyar Rigata hakan yasa na kara tsurewa na kwala wata razananniyan kara Dan nasan yau na kade a gun yaa aary

Tsawa ya daka mn"Will u Keepshot ko sai na chanza mind dina?,
Batare da ya kalleni ba ya cigaba da cewa "Bazan ta6aki ba haka kuma bazan ta6a kayannan da hannu na ba, cire min shi zakiyi da hannunki , kuma ki wanke minshi fess, inya bushe ki goge min saura ki kona minshi ,kafin 4:00 Inada event dinda zani kuma shi nike so na sa "

Ummah tace"Amma..."
Ya katse ta" Mum karkice komai, yarinyar nan ta raina ni kuma na rantse wlh sai tayi Abinda na sata inba haka ba kuma jikinta yayi tsami" ya kalle ni yace "Oya cire min Dan har jiki na ya fara wari"


Jin yayi rantsuwa babu yanda na iya dole inyi abinda ya Sani in ba haka ba zan chasu kam.....

Ba dai cire Riga bane?, No problem i'll do as he said, na fara takawa ahankali kaman Wanda kwai ya fashe mawa aciki Na isa inda yake tsaye na kalleshi, ya wani yatsine fuska kaman yaga kashi ko abin kyama,
Su janaan kam sun zama Yan kallo, banda kus-kus babu Abinda sukeyi, Umma kam ta nade hannaye a kirji sai faman murmushi takeyi,Wanda ni bansan ma tanayi ba balle nasan dalilin haka.
duk nabi na rude har Nasa hannu zan daga mishi Rigar wata zuciya tace min ~Haba Munayferh ki dawo hayyacin ki mana dan yace ki Cire Rigan da ya6ace shine kika Wani Rude haka?, Idan baki cire ba me zai yi?, Wata zuciya tace duka mana, To wallahi bazan bari ya ta6ani ba kuma bazan ta6a Rigar ba balle nayi Abinda yace~๐Ÿ™ƒ
Na kalleshi fuskarsa dauke da murmushin mugunta, Nima murmushin nayi Na Tofa mishi yawu a jiki, na juya zan gudu , Ya riko ni Nayi tangal-Tangal zan fadi zan fadi ya taro ni na fado jikinsa.
Daidai lokacin Ramlah ta sauko rike da Tray din snacks da drinks
Dam gabanta ya fadi Batasan lokacin da Tray din dake hannunta ya su6uce ya fadi ba.

Karar fashewAn glass cup da yajine yasa ya ankarar dashi ya ture ni nayi gefe kai na ya bugu da bango, Na riqe gurin ina ihu ina kuka Mara hawaye,


Hafsah Ta dagani ta shigar dani daki ina karanto mishi Allah ya isa, janaan ma binmu tayi

Yayinda Umma ta nemi guri ta zauna tana kallon Ramlah da Aryaan, Tana Sonjin irin kalaman rarrashin da zai Suburbudo mata, Ramlah kam kaman ta Gane manufar Umma na Tsere su Sai ta haye sama tana kuka,mai sauti, Hankalin shi yayi matukar tashi, ya yunkura zai bita ummah ta daka mishi tsawa "Ina zaka?,Binta zakayi?,Kayi mata me?,Common dawo ka zauna Johr"ya kalle mahaifiyarsa cikin takaici yasa kai ya fice daga daga gidan gaba daya
Ranar dai plan dinsu da Hilal ya rushe

Washe gari Na shirya ba tare da na jira hafsah ba na nufi skul Dan jiya kwana mukayi tana tsokana ta

Bayan Mun fito daga lectures ne Class rep yake sanarmn Wai Ks daud na kirana, Gabana ya yanke ya fadi kar dai ace shegen malaminnan yasan suna na?

Su janaan suka rakoni har gaban office dinshi babu kowa anan shiyasa muka yi tsaye a bakin kofa muna jiran sa mun dau almost 30mins kafin Yazo ya bude mana office din yace in shigo

Babu musu na shiga, naja kujera zan zauna yace kar in zauna maganar ba na zaune bane batare da nasake kallon shiba naja kujera na zauna na daura kafa daya bisa daya ina kallon sa hannu na rikeda makullin mota ta ina kadawa a hankli cikin magana ta mai kamada Rada nace "Ni bazan iya jure tsayuwa ba gaskiya haka kawae,Just goon tell me me kake son gaya min da har sai nazo office dinka zaka fada min Uhm?"

Yayi murmushn mugunta yana kallona ido cikin ido yace "Your Reg number"

Babu musu na fada mishi yace zan iya tatafiya

Ina Fita ta tarar da su sunyi jugum-jugum suna jiran fitowata, har Riga rige suke gurin tambayata mai ya faru?,

Tsab na kwashe musu duk yanda akayi na kara da cewa "Nifa Tun wuri zanyi Wa tufkar hanci, Zokuji yanda zaayi"
Dukaninsu suka bani kunnensu nayi musu rada A tare suka kwashe da dariya harda tafawa.


Kai tsaye Wani katon chemist din dake kusa da school din muka nufa da mamakin mu sai ga yaa Aryaan da Abokin sa Hilal, mamaki ya kamani,
Me ya kawosu chemist Waye babu lafiya?.

Jaanaan tamin Sign cewa ga mutumin nan fah (bata San na Riga ta ganin shi ba), Ganin basu Ankara da mu ba yasa naja su hafsah mukayi gefe nace mu 6uya har sai sun fita, kar ya ganmu bare ya tambaye mi mukeyi a chemist.

Na rufe baki kenan zan juya Mukayi four eyes dashi yayi min wani miskilin murmushi.

Idanu na rintse "babes wallahi ya ganmu,mun shiga Uku"

muryan shi naji kusa dani yana fadin " Baku shiga Uku ba sai naji dalilin Ku na zuwa Chemist bayan ga skul clinic " yayi magana yana zura hannaye cikin Aljihun wandon shi.


Hafsah tace " Yaa daman... Sai ta kalle ni Na banka mata harara, hakan yasa taja bakinta tayi shuru

"Abinda kazoyi a chemist shi mukazo yi ,mutun in banda saido babu Abinda ya iya mtsww!"

Aryaan ya tsani tsaki, ko wani akayi mawa sai abin ya Sosa mishi rai ballantana ayi mishi, Hilal ya dube shi yana jiran Hukuncin da Aaryan zai dauka Dan shi Shaida ne akan yanda abokin sa ya tsani tsaki bai ya Zane ta a nana din ba babu ruwanshi.

Ga mamakin shi sai yaga yayi murmushi yana Dan shafa gemunsa " Ni wata na dirka Wa ciki nazo siyan maganin Abortion, Kema cikin Gareki ne?"

Hilal ya kwashe da dariya ya kalleni yanda nayi kicin kicin da rai yasan tabbas maganganun sunyi matukar 6ata min rai yace"Don't mind Aary , He's out of his sence, maganin ta6in hankali nazo nema mai"

Dukkanin mu muka sa dariya Amma banda yaa Aryaan Wanda ya hade girar sama da na kasa yana takaicin futucin Abokin sa

Cikin dariya nace " Ai da baayi asarar Neman magani ba Inada maganin Mental Disorder....."






WAYSH๐Ÿ˜ฉ Na gaji fa ๐Ÿ˜ค


See u tomorrow๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š


Dear
Commenters I love You wujiga-Wujiga


Dear sharers
uoy evol i , Backward oya chop this muaah๐Ÿ˜˜๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹



Comment
And
Share๐Ÿ˜—











Fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ


13thAugust


๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...



*Chapter 5*

Hilal Ya kalle jaanaan dake Faman latse waya yace "Wannan fa?, kawar Ku ce?"
Nace "Jaanaan ce fah, baka Santa ba?"

"Eh ,daga yar inace??"
" itama yar kd ce Anguwan mu daya "

"OK, banta6a ganin taba, But she's so cute...,Pretty Damsel"

Nadan Sace kallon jaanaan wacce gabaki daya hankalin ta na kan waya bata ma San munayi ba na ta6e baki "Ba laifi, amma fa nafita kyau"

Ya bude baki zaiyi magana yaji Aryaan nacewa "in ka gama, you can meet me outside" Yana gama fadin haka yayi waje. Hilaal yayi min sallama yabi bayan sa.

Muma muna gama siyayyar mu muka shiga mota na sauke Jaanaan a Off.K mu kuma muka taho gida.
Muna isowa na danna horn har sau Uku Gate-man bai zo ya bude mn Gate ba haushi da takaici suka ishe ni, Na kashe mota na Dora kaina a kan stirring din motana, hafsah ta bude murfin mota ta fita Ta kwankwasa , Gate-Man da fitowarshi kenan daga toilet rike da buta, ya leqo Ta Mini-Space Yana ganin mu da gudu ya wurgar da butar ya wangale mana Gate, Hafsah ta shiga tana Gaida shi cikin Girmamawa.

Nikam na cika nayi fam , kiris nake jira in fashe!, A fusace naja motar Na shiga dashi, Har zan parka a parking inda na saba parkawa, Sai naga Tent dinda Yaa Aary ke parking motarshi wayam, Sai na fasa parkawa na nufi inda yake parkawa na Parka
Ina fitowa naga Gateman tsaye yana jiran fitowana(Allah sarki bawan Allah๐Ÿคค)

Ya durkusa gabana ya hada hannaye waje daya yana fadin "Am very sorry Madam Wlh nadan zaga ne, Ban gama tsarki ba naji hor......." Bai karasa ba Na Daure fuska tare mishi hannu"Enough man!,hang it, duk wannan matsalar kace,Na Riga nayi maka warning Ka jira Hukuncin ka,Tsohon banza kawae mtsw" na sa6a jakana a kafada gaba abina . Direwa ya karayi a gabana Yana hada hannaye alaman roqo "Pls madan ki ban ko wane irin punishment na yarda zan iya jure Wa , Amma banda wanda kika za6a min, inada ulser bazan iya jure yunwa ba har na tsawan kwanaki Uku ,Please Madam ki sausauta min"
Shuru nayi ina jinsa Saida ya dasa aya sannan na kalleshi nace "Ka gama?, Nace ka gama?, OK stand up"
Kaman jira yake ya mike tsaye yana matsar hawaye.
Kallon Agogon Hannu Na nayi 2:47pm. Takaici ya kara turmuke ni yasa na wuce time din cin lunch dina , bansan lokacin da Nasa kasa na shure shi ba nan da nan ya fadi Kansa ya bugu da karfen Tent , Nayi gaba abina. Bai dandara ba ya biyoni da gudu yasha gabana "Madam please help!"
Cikin Zafin rai da kunar zuciya na daga hannu zan wanke tsohon da mari ba tareda na duba girman dattakon sa ba idona ya rufe banaji bana gani,jinayi an Riqe hannu na ta baya, Kamshin turaren sa ne ya tabbatar min da ko waye, na zaro ido Zuciya ta na dukan Uku Uku, Na tattaro dukka karfina Na fincike hannu na nayi ciki a guje .

Aryaan ya kalle Gate-man Wanda gabaki daya ya fice hayyacin sai sharar kwalla yake yi yace " Malam Ali, me ya hada ka da wannan yarinyar"

Malam Ali mai-Gadi yaja majina tare da share gumin Dake karyo masa ya kwashe mishi kaf Abinda ya faru ya kara da cewa "Tun ranar da Tazo nan gidan ta gaya min Dokokin ta na farko kar tayi Horn Sau Biyu ban bude mota ba, idan kuma na qi hukun cina shine bazan ci Abincin Gidannan ba har na tsawon kwanaki Biyu kuma ba fita bare na siyo a wani gun in kuma na fita korana zatayi.

Doka na Biyu kuma idan zatayi aike ni zata aika kuma zata bani Time in na ketare Hukunci na shine bazan Yi Amfani da ruwan Gidan nan ba har na tsawon sati daya inzanyi sallah kam saidai nayi tayammun, in na nema ko akayi ruwan sama na Tara to korana zatayi"

Aryaan ya kwashe da dariya ,cikin dariya ya dafa kafadan Malam Ali maigadi yace "Great hustler VS yar barazana , I wanna ce the end of this play Faah๐Ÿ˜‚"
Gateman ya kasa kunne don jin Horn din DA ake Faman dannawa , ai da gudu ya zura ya wangale gate Motar Aaryan ta danno kai driver yayi parking ya fito da ledoji guda Uku ya mika Wa Aryaan tareda makullin motan.

Ina Shiga na Shige Toilet nayo wanka na sauka kayana zuwa wata baqar jallabiya mai adon Stones na dauro Alwqla na gabatar da sallan Azahar Sannan na fito falo Dan nabawa ciki na hakkinshi.

A takiyar falo na tadda su, duk sun yi tsuru sun kurawa tsarabar da Yaa Aryaan ya shigo dashi ido, jiki na har kyarma yake naje kusa da Umma na zauna nima na kurawa ledojin ido.
Zaro ido nayi Ganin an fiddo Wani katon ledan Vanilla cream Puff pastry , bansan lokacin da na hadiye wani yawu ba(Kwadayi ya motsa๐Ÿ˜œ)
Ya kara fiddo da Awara da doya mai kwai daga dayan ledan ledar karshe kuma beef shawarma duk suna cikin takeaway daban daban ne.

Ya mika ma Umma takeaway mai kunshe da Awara da doya mai kwai, Umma ta amsa cikin fara'a tana sanya mishi albarka,sannan Ya bama Hafsah dayan take away din mai kunshe da beef Shawarma ta amsa tana godiya Ragowar takeaway din mai kunshe da puff pastry kuma ya mika ma Ramlah cikin murmushi ta karma tana godia.
Ganin Angama rabo babu nawa yasa na zaro ido A shagwa6e nace "Yaya Gani fah"
Yace "Uhm?,sai akayi ya?"

Muryan Umma yaji cikin hayaniya tana cewa " Aradun Allah bata sa6uwa bindiga a ruwa, Inye Aryaanu!, Har kayi girman da Zaki Siyo mq matarka Abincin Yan birni ka hada uwarka da Awara da doya?, Anya kasan darajar uwa kuwa? Kasan Allah?, wlh bazanci Awara ba ,ka kwashe tarkacenka kada mata ta cinye" ta fada tana ture Robar takeaway din.

Aaryan ya rike kansa dake Sara Mai cikin taikaici yace "Sorry mum, indai akan puff vanilla ne gashi amma Dan Allah ki fara cin awarar kinsan yana da matukar mahummanci a jikin danAdam ko?,

Umma tayi murmushin jin dadi tace " Allah yayi maka Albarka Aaryaanu yanda kayi min biyayya ka fifita ni akan matarka Allah ya baka waenda zasuyi maka fiye da hakan ma"
Charab na Amshe da cewa "Kema kinsan dai wagga Adduar Iyakarta fatar baki ne kawae ,inba munafurci ba , kin hanasu xrsryjiyeasjkknh๐Ÿ˜œ kinzo kina Adduar Allah ya bashi da?, wane Dan kenan? Shege ko Dan titi?"

Ina gama fadin haka na sunkuce Robar awarar dake Gabanta na kwasa a guje ,Shima biyo ni Yayi yana son kwace awarar Umma!, amma kash kafin ya iso har na shige na sa key, a fusace ya juya zai koma yayi kicibis da Hafsah yace ta kar6o masa awarar Umma karta bari ta dana ko guda a ciki. Ya koma parlour Inda ya tarar da Umma tayi jugum tana Tunanin Furuci na na dazun
Ashe duk abinda takeyi ina sane da ita?, ita ta dauka ni konko ce babu abida na Sani, Lallai zatayi magani na.
***
Koda Hafsah ta kwankwasa kofar ban bude ba Saida na leqa ta Dan karamin Glass dindake tsakiyar kofar .
Ina budewa waya na dake kan dressing mirror ya hau ruri , da sauri na dauka jin Ringing tone dinda na sa ma Abba na ne na kara a kunne ina Dan turo baki cikin Shagwa6a nace"Abiey na sai yau ka tuna dani ko?, Tom nayi fushi"






NO DOGON TURANCI



SEE YOU TOMORROW๐Ÿ˜‰



SHARE
AND
COMMENT๐Ÿ˜’




COMMENTERS I LOVE YOU WUJIGA WUJIGA IRIN EHN๐Ÿ˜‰


GROUPS DINDA SUKA GA NA DAINA MUSU POSTING TAM SUYI BLAMING KANSU...... RASHIN COMMENT NE YA JAWO HAKAN





A CIGABA DA WANKE HANNU๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„

Hope kuna sa nose mask kuma kuna bada Social Distance tsakaninku da wayoyin Ku kafin Ku karanta littafina ko?๐Ÿ˜Œ


Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ





Fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ






Friday 14th August๐Ÿค



.๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 6_*

Daga chan 6angaren Abie yace "Sorry Princess din Abie, kinsan yanayin Network din Garin,Ko na kira Abanza"

Nace "Ba wani nan ,Ka manta damu ne kawae,ni ina Hajiya ta?, Nayi kewar ta"

Abie yace "Jiya Akayi mata Aikin kafa ,tana bacci in ta tashi zan hada ki da ita inshaAllah"

Nadan Shagwa6e fuska nace"Abie na yaushe zaku dawo I Really miss u"

"InshaAllah zuwa next tomorrow zamu dawo ina Auta naa?"

Da kalle Hafsah da ta wani zuba min idanu na kauda zancen da cewa

"Abie Kayi Wa Umma fada Tana Shiga haqqin Su Yaa Arry da yawa.........nan na kwashe masa duk Yanda akayi tsakanin Ranar da Aka kawo Ramlah har zuwa yau dinnan na kara da cewa " in da so Samu ne ma kayi mata fada ta bar mana Gidan mu huta da takuran ta, ta takura mana ta takura Wa Yar mutane" jin yayi Shuru bai ce komai ba yasa na cire wayar daga kunne na naga bai katse ba

nace "Abie kana jina ?"

Yace "Ina jinki princess cigaba"

Nace"Ai na gama"

Yace "Toh ya kike so ayi ne?"

Nace" kawai kace ta koma Gida mu kuma ka Aurar damu mu bar musu Gidan Su ko hafsah? "Na fada tsakani na da Allah ina me duban Hafsah

Abie yayi Yar dariya irin tasu ta manya yace " Yaro kenan, yanzu innace zan Aurar daku kuna da Wanda kuke so ne?"

Nace"Aa kai zaka za6an mana yanda ka za6a Wa yaa Arry"

Yace"Munayferh,You're too young, You're just 17yrs fah"
Turo baki cikin shagwa6a
Nace "Nidai wlh Amin Aure ko In Gudu" ban tsaya jin Abinda zaice ba na katse wayar.

Hafsah ta kalleni cikin dariya Tace"ke yanzu ko Aure Akayi miki ba zama zakiyi ba, Dan na tabbata kina sati zaa koro ki"

"Muguwa,Aniyyarki ya biki" na kalle takeaway din dake gabanta nace nifa bazanci Awara ba, Na tura mata Robar awara na jawo nata dake kumshe da beef Shawarma , ita kam A dadinta, nan ta fara tsakurar awara ni kuma na hambadi Shawarman ta๐ŸŒฎ

Inajin wayana na ruri naqi dagawa, Dan duk a zato na Abie ne, Sai da nga alamun kaman bazaa daina kira ba na dauka ina Saka loman Shawarma cikin bakina Muryan kanina

Please Login or Register in order to submit comment