Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miki Albarka Sulthy, Allah ya Baki Aljannah Firdaus Amatsayin Tukuicin Haqurin da kikayi haqiqah Kinyi haquri Sosai Kin jure ,Kiyi haquri kicigaba da Jure qaddararki Wata rana sai labari , inshaallah Sulthy Bazaki sake kuka ba a duniya ,Umma tayi hakan ne don Ta rabamu Wannan ......Sulthy Wasu qaddarorin da kike Gani a Rayuwa da dalili Suke samun mutum ,wannan Qaddarar ta mu kasance tarece .... Ina son ki MUNAYFERH"

Ya qarashe Maganar Cikin Zubda Hawaye Murya na rawa.

"Nima ina sonka YAAAARY ...ina....son.... Ka..."


Na qarashe da rushewa da Wata matsanancin kuka mai tsuma rai.


Da qyar na samu ya Rabani da Jikinsa ya tsura mn idanu Hawaye na bin Fuskar sa.

"Sulthy Mutane Sun Gujeki a dalilin Wannan Fuskar Ni kuma a halin yanzu Fuskar ta fiye mn komai a Rayuwa , Bazan ta6a qyamatarki ba ,koda ace Duk Matan duniya zasu kasance a matsayin masu qafa ke Gurguwace zan kasance Qafarki , idan da Ke makauniyace zan Zame mki Dan jagora , Ni wannan Fuskar ma taimako na yayi dama ina Kishin yanda maza Ke kalle mn Ke. haka kuma muryan nan da aka Sauya mki ba qaramin taimaka mn yayi ba Kinga babu mai jin dadadadar Muryan nan naki Mai sanyaya Zuciya bare Nayi tunanin Dame qwace mn Ke sulthy ina sonki I love you for all that you are, all that you have been and all you are yet to be Kome Zaki zama bazai rage Koda Kadan Daga Cikin son da nakeyi Miki ba, Na bar mki wuqa da nama Ki Zartar da hukuncin da kikaga Dama akan Umma tunda itace mai Laifin na Amince Kiyi mata duk Abinda kikaga dama a matsayin wacce aka cuta...".


Hannu nasa na share Hawayen dake bin Fuska ta a Raina Nace


~Aaryaan da kasan hukuncin da zan dauka da baka bani dama ba , Aaryaan Dakai zanyi Amfani Wurin Hukunta Umma!~


Jin Zafin Jikinsa Nakeji Har tsakar kai na , a sanyaye na dago cikin Rauni Nace

"Meree Raaja ,Are you sick?"


Lumshe idanunsa yayi Tareda sake Rungumoni Jikinsa Batareda Yace komai ba.



*****

Tun bayan Bikin su Hafsah Saleem yayi tafiya Yau Ake sa ran dawowansa ,Yayinda su Umma kuwa suke zune JugumΒ² Suna tunanin Inda Aaryaan ya taje burinsu kar Wani abun ya sake shi, kirar salllahn da Akayi ne yasa su Abba tashi Don Gabatar da sallah.


Yayinda Umma da Furayrah suka Shige Kitchen Don hada Dinner .


Ramlah kuwa Yau Fashin sallah takeyi Don haka take zaune a Parlo Tana yiwa Humdah wasa da Teddies dinta.


Saleem ne ya shigo da sallamar sa , Ramlah najin Sallamarsa ta miqe Cikeda Farinciki Ta fada Jikinsa tanayi masa Oyoyo Yayinda shi kuwa ya dagata Chak yana Juyi da ita a tsakar Parlon Gaba daya sun manta inda Suke Cike suke da Farinciki Da begen Ganin Juna Wanda ya mamaye msu Kewar da sukayiwa Juna nsu.

Umma kuwa jin hayaniya yasa ta Fito , Turus tayi jiki na Rawa Ganin Abinda Ke faruwa , daidai nan Motar su Daddy ya danno kai Cikin Gidan ..


A tsorace ta ra6a Gefen su tayi Waje don Harga Allah yanzu shakkar Ramlah takeyi Tana kuma tsoron karta Kulasu Tayi mata Abinda yafi na rannan Yanzu ko gaidata Ramlah batayi Ko biyayyan da takeyi mata a da yanzu batayi , idan sun hadu da Harara take rakata Wanda hakan ba qaramin tsorata Umma yakeyi ba hakan kuma ya haddasa Shakkar Ramlah Yayi tasiri a Zuciyar Umma.


Tana Fita ta tarar dasu zasu Fito Daga Motar Cikin huci Da tashin hankali take Fadin

"Alhaji Kazo ka Gani Za'a hawa qona mana Gida"

Yanda yaga tashin Hankali shimfide a Fuskarta yasa Ya 'Dan tsorata yayi Ciki da Gudu ta Mara masa baya , a zatonsa fa Gobarar Gaske Ce..


"Sa'a diyyah ina Ke qonewa?"

YA tambaya yana Yarfe hannu.


Umma ta nuna msu Saleem da Ramlah wa'enda Tun Shigowar su Umma suka farga Kansu a qasa , Sai a yanzu ya fahimci Abinda Ke faruwa.

Tsaki yaja

"Mtswww.....kefa kin fiye Sa ido?,ina Ruwanki dasu?"

"Auww Alhaji haka ? Ma zaka ce bayan Qiri qiri Kana Gani fasiqanci Ake Yi a Gidan nan Da igiyoyin Auren 'Dan mu kace ina Ruwana?"

Umma ta gaya Cikin Gigicewa



"Kome kikaga sunayi babu Ruwanki ,inace Kin saketa ne?, Dakanki Kika saketa saki Uku ,kin dauka ban Sani bane?"

"Eh na saketa Saki Uku ,koda Matsalane ?, na saketa din kuma Ba 'anan ya kamata ta zauna ba zuwa Zatayi ta nemo Iyayenta shegu Wa'enda sukayi Cikinta suka haifeta a kororo ,idan ta nemusu sai Su zauna tare inyaso sai Su zauna tare amma ba anan ba ,Don haka a yau ba sai Gobe ba dole sai kin bar Gidannan don ba Gidan Uban ki bane , tashi Ki kwashe tarkacenki ki bar mana Gida kar a Shafa mana Fentin Zina...."


"Babu inda zataje Saboda nan Gidan Ubanta ne, tafiki iko da gidan ,Kuma 'yata ba Mazinaciya bace ,Diyata ba fasiqah bace , Diyata ba 'Yar shege bace Amma qila 'Yar Shegiya Ce ban Sani ba Tunda Uwarta da bakinta take Fadin hakan .... Ramlah Da kika tsana ba kowa bace Face Diyarmu Ni dake Kuma Matar saleem a halin yanzu Wanda Aaryaan ya saketa bayan ya Gano Gaskiyar dake Tsakanin Wannan Qulalliyar.............."










πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
**HAWAN-JINI NA*
~{uwar mijina* πŸ’”}~
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
NA
*🀍Fahnaan🀍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

Β©πŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_Aβ€’ Wβ€’ Aβ€’_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._



Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…...


*_Chapter 79_*

Ido Umma ta zaro Cikin tsantsar Firgici Da Gigicewa ,Take Gabanta ya shiha dukan Tara tara ba qaramin Tsorata tayi da Jin Furcin Abba ba.


Cikin tsananin tashin hankali da Maganganun Nasa Suka haddasa mata take Fadin

"Aljaji Ahir dinka Wlh bata sa6uwa Ramlah ba diyata bace Shegiya ce , uwar Riqon ta Kuli da kanta Ta tabbatar mn da hakan , bayaga hakan ma Jinin Nufawace , wallahi na rantse bazata qara Daqiqah daya a Gidannan ba , sai ta fice ta bar mana Gida Tunda har ka fara kiranta Diyarka Gobe in ka Samu dama Matarka zata kirata kenan ,Ke tashi ki kwashe Kayanki kibar mana Gida kuma ki hada tarkacen Kayanki da Shegiyar Diyarki Don Ban yarda Yarinyar Jinin Aaryaan bace ,kuma idan kin tafi karda Ki sakeki sake Koda tunanin mu ne bare kiyi tunanin Kin ta6a Rayuwa damu ,Oya Jeki Kya mazahπŸ₯΄....Jeki ....jeki....kina 6ata mn lokaci fah."


Ta qarashe magana Da ture Ramlah wacce ta tsareta da idanu Tana kallo ko kyaftawa batayi illa ma murmushin da takeyi ,Wanda ke sake Qufula Umma...

Abba ya dube Saleem da Ramlah yace su fita Babu musu suka fita Ya juyo ya kalle Umma daketa faman Huci ya ta6e baki

"Ko ki yarda ko karki yarda Ramlah diyar muce Nidake ,itace wacce Kika Haifa Shekaru ashirin Da Uku da suka Gabata Wanda aka sassare ba 'Danki bane Dan Kulu ne ,A Qoqarin Gano wannan Qullalliyar ne suka Sace Akheey (Daddy)......"


Nan take Ya sanar da ita duk yanda akayi har suka Chanza Yaran da kuma manufar InnaRabi Akan hakan ya qarashe maganar da cewa Nurse dinda Suka dawo tare daga LIOS itace ta Sauya yaran da hannunta kuma ta hada Hujjojin Wanda hakan yasa Suka Rabata da danginta yanzu bata da Kowa Gaba da baya Kuma ya Yanke Hukuncin Zai Aureta tunda ya Riga ya sake InnaRabi...



Tun kafin Abba ya qarashe maganar Hawaye Suke Tsere a Dankalin Fuskar Umma Gabaki daya ta Firgice Jikin ta ya dau rawa babu inda baya Karkarwa A jikinta ,wani irin kuka takeyi mai cike da nadamar abinda ta aikata, ji take ina ma tabud'e ido taga duk a cikin mafarkine komai yafaru saidai inaa *k'addara ta riga fata* ,da wani ido zata kalle Ramlah a matsayin Uwa a Gareta bayan Wulaqanci da Cin Mutuncin da tayi mata a baya ta ina zata fara?, ta ina zata Fara kallonta a matsayin 'Yar da ta Haifa?, Tashin Hankali ne ya Rabun mata Biyu Ga Tashin Hankalinnda take Ciki na Rashin Aaryaan, ga Kuma wannan.

Juya kanta tayi tareda kama damtsen hannun Abba Da qarfi Cikin kuka take fadin .


"Ka taimaka mn ,Don Allah ka karyata Abinda Kunnuwa na Sukaji daga Gareka ,Wlh bazan iya kallon Ramlah a matsayin 'diya ba ,har yanzu a matsayin Matar 'dana Nake Ganinta ,Alhaji ka taimaka Karkasa Wannan Abin kunyan ya tabbata a Gareni ......"


Surutai takeyi tana kuka kaman Zararriya, Abba kam Ganin zata iya Karya masa zuciya yasa yaja tsaki tareda Fizge Riqon da Tayiwa hannunsa Ya miqe zai Fita ta Riqo Rigarsa Cikin Tashin hankali Idanunta har wani .

"Please Ka taimaka ka dawo ka karyata Furucinka Akan Ramlah ,Wallahi ba Jinina Bace ,Ban ta6ajin Sonta a raina ba koda na second Daya ne ......."


Juyowa Abba yayi a fusace ya katse ta


"Haleemah watch Ur tongue ,She's Still your daughter no matter how Kome zakice Wannan qaddarar bazata ta6a Goguwa ba a Rubuce yake Ramlah diyarkice , Cikin mu babu mai iya Sauya hakan ,kuma Ishara Allah ya fara Nuna mki Tun a duniya Gashi Tun ba'akai ko'ina ba kin fara Girbar Abinda kika shuka kin Takura mata kin tsaneta Kin hanata Rawan Gaban hantsi Duk a cewar ki batada Asali ne ,kinyi hakan don Ki Quntatawa Wasu Alhalin Kanki kike Cuta ,Duk Wanda yayi jifa da toka Fuskar sa yake Komawa ,Kin Kasa kin tsare 'Danki bazaiyi Rayuwan Aure tareda matansa ,Kinkuma Kafa Msu qahon Zuqa A cewarki wannan Shine Mafita a gareki Ban San Ribar ki akan hakan ba koda yake ga riba ta farko Kin Cutar da Diyarki da kanki Saura Na biyun,Haleemah Wlh ke nake Zargi akan 6atan Munayferh idan Hasashena Ya tabbata ki tabbata Zamana dake yazo Qarshe kenan kuma sainasa An Kulle ki Wlh"


Yana qarashe Maganar yayi waje Yana Share Kwalla

Umma ta sha Gabansa da sauri ta rink'a juya kai Jikina b'ari kar-kar kamar mai farfad'iya wani irin zufa da Gumi daga tsakiyar kanta har kan d'an babbar yatsar k'afarta hatta cikin gashinta sai diga Take cikin tashin hankali.


Tsaki Abba yaja tareda bangajeta ya ra6a Gefenta Ya wuce Cikin takaici.


****

Leqa plate din yayi ya jawoshi Gabansa sannan ya saci kallona Ko kallon Inda yake banyi ba sai faman Latsa wayansa nakeyi ina Turawa Umma hotunan da muka dauka tareda shi bayan na Cireta a Unblock List ina Gama turawa na Goge Message din.

Fizge wayan yayi a hannuna yana Harara na Da Gefen Ido ,Nima Hararar na mayar masa tareda Dora kaina Bisa kafadarsa .

"Sulthy....nayi Missing Delicious Meal dinki Sosai ,kaman kin San Rabona da Abinci Tun Last Two weeks Idan kinga nasa Abu Cikin Cikin nan nawa tho Ruwa ne ko Coffee...Ban San dame zan Biyaki ba May Allah Bless ur hand Sulthy Allah ya Biyaki da Aljannah Firdaus , ya baki Lafiya yasa Zaman mu ta dore har Abadah"



Da Ameen na Amsa Cikin Jin dadin Addu'ar nasa na dau Spoon na Dibi Buryanin da na hada masa na kai bakinsa ina Murmushi

"Yayana Ya kamata ka koyi Rayuwa batareda ni ba, Don Dole wajibine Wata Rana Mu Rabu ko kaso Ko kaqi..."


Da qarfi ya ture Spoon dinda nake Shirin kaiwa bakinsa Yana Auna mn wata Irin Muguwar kallo Wanda saida ya hargitsa Yan hanjin Cikina .

Cikin dakiya na gyada masa kai

"Eh... Dole Mu Rabu Gabaki dayan mu Masu Raine Ko wani Abun bai Rabamu ba Dole mutuwa ta raba ...."

Kallonda ya watsa mn ne yasa na hadiye sauran Maganar na kasa qarasawa.

Ya wani damqi hannuna da Qarfin Tsiya har saida na tsorata , idanunsa suka rine Suka koma tamkar Gauta a lokaci Guda har wani karkarwa yakeyi ,Take gabana ya fara Dukan Tara tara .

Bakinsa ya Bude da niyyar yayi magana Amma sai maganar ta gagareshi ,Baki na rawa nace

"Don.....All..ah....ka...yi Haquri"

Ina Qarashe Maganar naji SaukanπŸ‘„ cikin πŸ‘„ take Kidan ya fara Sauya salo Cikin qanqanin Lokaci ya fara Fita Hayyacinsa Yake Neman zaucewa ,Don tunda yake bai ta6a Kissing dinta ta maida masa da martani ba sai yau Gaba daya Ji take kaman ba 'a duniyan nan yake ba , Saida yayi mai isarsa Sannan ya janje bakinsa a kasalance jiki a Mace Lokaci guda har Yanayinsa ya Chanja.


Nima a kasalance na kwanta a kirjinsa Tareda Jan Numfashi.

Lumshe idanu yayi tareda Shafa kaina ,

"Sulthy bazaki mutuba Tare zamu Mutu ,Zan Ragu dake zan Mutu dake Harta kabarin Mu daya za'ayi mana please karki sake fadin Haka..."


Tausayin Sa ya kamani da na tuna Abinda nake Shirin yi ,dukda nima Zan Cutu Sosai Amma Raina Fansane Akan Raba Abinda Umma tayi mn.

Jin nayi shuru yasa ya dagoni Ya kalleni Ganin Idanuna A lumshe yasa ga daga ni Chak yayi Master bedroom dani Duk a cewar sa Barci nakeyi, yana Direta akan Gadon tasa hannu ta jawoshi ya dawo da baya Ya fada kanta.

Daganan na tattara Tarkacena Nayi ArewaπŸšΆπŸΌβ€β™€οΈ


After 2hrs🀨

Mummunar Fuskar Dodon nan na gani Ta fito daga ban daki tana Goge Buzubuzun Gashinta da Wata 'Yar qaramar Towel.

Matsowa tayi Wajen Gado Inda wani mutumi ke Kwance yana Kallon Celin Sai faman Murmushi yakeyi Zama tayi kusa dashi tareda 'dan Rankwa6awa ta hura masa iska a kunne ,Cikin Muryan Dodonni tace

"Raaajaaa Goan Bath"

Lumshe idanu yayi ya sake waresu akanta a raunane yace

"Please Sulthy Ki bari qara Ko Daya ne"

Hannunta ta dunqule ta kai masa Duka a qirji Cikin Turo baki nace

"Maye kawai .... Kai ko Gajiya bakayi ?"

Miqewa yayi ya nufi Hanyar Bathroom cikin dariya yace

"Ni Ai banqi na kwana Inayi ba ,Cus You too sweat Kullum jinki nake kamar Budurwa ,Babu Abinda zan Iya Saka mki dashi saidai nace Allah ya Biya mki buqatunki na Alkhayri ya Tsundumaki Cikin Aljannah Firdaus"

Ya qarasa maganar tareda manna mn Kiss a Goshi sannan ya shige Birth room,


Da kallo Na bishi hawayen Tausayin sa Suka zubo mn ...



Yana fitowa Yaga Bana dakin Sai yayi tunanin qila ina Parlor ne Shiyasa baidamu ba ya cigaba da Shirin shi.....















Manage Please🀌

Nayi gabasπŸšΆπŸΌβ€β™€οΈ

3dec✍🏽










Z\GIRLY fan group Ku fara Shirin yima Umma dannan Kirji faπŸ˜‚







Nayi gabasπŸšΆπŸΌβ€β™€οΈ



2nd December
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

Na
🀍 *Fahnaan*🀍

Β©πŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…...



*Chapter 79*


A daidai Qofar Gidan hajiya Asiya yayi parking ,Ina Fitowa ya qara Gaba kasancewar haka muka shirya dashi .


Banyi mamaki ba da na iske Gidan babu masu gadi ba Don nayi zaton fiyeda hakan .

Haka Koda na shiga Ciki ban iske ma'aikatan dakeyi Mata hidima ba ,A bedroom dinta na isketa Ta zauna bisa Mirror tana kallon kanta cikin Mamaki DA damuwan yanda Gashi ya Fito Mata a ko'ina na jikinta kuma A kullum sai qara Girma sukeyi kaman Ana Sa musu taki


Ta mudubin gabanta ta ga mummunar halittatar nan tawa ,ai a Dan Razane ta juyo tana qare mn kallo cikin tsananin firgici tsoro tashin hankali da mamaki .


A dan rude ta Nuna ni DA yatsa Cikin Tsoro tace

"Keh....you....!....Mai kika zoyi anan?"

Kallonta nayi daga sama har qasa na ga yanda ta wani gigice DA ganina tun bata san dalilin zuwan nawa ba.

Kallonta na sakeyi naga yanda Fuskar nan ta gama Rufewa da gashi ba'a ganin ko qwayar idanunta Ga yatsun hannayenta DA suka qara tsayi sukayi tsini kaman na dodonni in fact idan ka ganta zaka dauka Asalin dodon ce saida nayi Dariya sosai sannan daga bisani na tsagaita don kaina ammma na kasa Hadiye dariyar Don harga allah Halittarta a halin yanzu yafi a kirashi DA abin dariya Don babu KO kyaun gani. .

Cikin dariya nake fadin

"Creeper you look So beautiful.....Ji yanda na sa kikayi kyau so amma Professional Makeover"

Na fada tareda Qara tuntsurewa DA dariya.


Cikin Gigicewa DA firgici hajiya Asiya take kallona Cikin mamakin DA bai Gama barinta ba ta nunani DA 'Yar yatsa baki na rawa ta Nuna ni DA 'Yar yatsa

"You mean You did this To me....?"


"Are You Asking?....Any way if you did....Yes.....I did"

Na gaya Tareda Juya Idanu cikin salona Mugunta.


A tsorace kuma Cikin Gificewan DA bai Gama barinta ba ta tako inda nake , na Dan ja dabaya

"How Comes taya hakan ta faru?...."

Ta qarashe Cikin rauni kaman zatayi kuka.


Yanda tayi maganar ba qaramin Bani dariya yayi ba don haka na Shiga darawa Cikin mugunta Na kuma Shashantar daita, ita kuwa bata iya Cewa komai illa Idanun DA ta xuba mn Cikin Qufula haushi da kuma Gigicewa a 6angare Guda.


"Nice na maidake hakan ...Dama na dau Alqawarin bazan ta6a barinki ba dake da Haleemahn DA ma duk mai sa hannu Akan wanann Abun ....na San zakiyi mamakin yanda akayi har na maidake hakan tho saurara kiji ingredients din πŸ‘‡πŸ»
*Aquavirun* *Mintop* *Hyena Hair* *Elephant Teeth* , DA na Samarda wa'ennan Abubuwan Masu fitarda Gashi Sai na ChakudaSu Waje Guda na Shigo Gidanki A lokacin da kika Fita Yawonki wanda kika Saba Batareda wani ya Ganni ba na sauya mayukan Shafawanki ,Turarukanki ,DA Sabulan Wanki Batareda Kinsani ba Su kike amfani dasu All dis while ......"

Na gyara tsayuwana Tareda Qirqiro murmushin mugunta .

Na cigaba

"And More Are Coming...Yanzu KO kin tafi Asibiti babu likitan DA zai baki maganin wannan Cutar don Ni kadai nasan Abinda na hada kuma nakeda maganinshi Abu daya Zakiyi mn Na gaya baki maganiin Fitar Gashin nan ,Amma idan Kin yarda ..... Please Explain to me Me Kukayiwa 'ya'yana Suka Qi tashi tun Ranar DA Abin ya faru? ,And Explain to me meyasa Kukace na Bar qasar and why All these happening to me?...."" .


Tambayoyin DA nayi Mata sun so su bata dariya Dukda Halin DA Take Ciki saida ta murmusa Had saida Jajayen haqoranta suka Bayyana Kana ta Gyara tsayuwa cikin isa ta Fara bayani kaman haka

"Kice qarin bayani Kike nema ,Wannan ba Komai bane face Aikin Bokana DUNA πŸ˜‘, kuma uwarmijinki ce ta Dau Nauyin komai dukda kuwa bata San aikin Boka bane , tafison ki wulaqanta ki tozarta Sannnan Ki bar Mutanen dakeTareda ke dakanki , yanzu haka babu Makawa Dole sai kin Bar qasar KO kin qi KO kinso haka kuma ko kin tafi bazaki Sake Waiwayen gida ba ,hakan na daga Cikin aikin DA Nasa aikayi Mn ,kuma Abinda nayiwa 'ya'yanki sirri ne kuna barin qasar Zasu Tashi idan Kuma Kika Jinkirta barin qasar Mutuwq zasuyi ...... Anda last Thing Kin dauka Sauya mn Kamannin DA kikayi Zai dameni ne?....No.....never hakan bazata Ta6a damuna ba , kuma baki Isa ki rabani DA kowa nawa ki kwana Lafiya ba..."


"Kinyi zaton Barinki zanyi har ki samu Nasarar sake Aikata wani Abun a gareni ne?.....Hajiya Asiya Kike Right?....Zuciyarki ta sa6a tunani"

Na fada Cikin zafi tareda Juyawa kaman Zan fita amma sai na tsaya A bakin qofa na sauke Jakan dake Rataye a kafadata Na dauko Face mask na Daura sannan na Dauko Wata 'yar kwalba na juyo Ina Qare Mata Kallo , ita dinma No take Kallo , Nayi murmushin Mugunta

"Hajiya Asiya ya kamata Ki miqe Ki taka Kiyi Tafiyar Qarshe Don in the next Two minutes Zan matarda Duk ilahirin Jijiyoyin jikinki bazaki iya komai ba kuma bazaki ita Furta komai ba saidai ayi mki ,In the next 40mins Kuwa idan aka rasa Mai taimakonki ya kaiki Asibiti a haka zaki Qare har Ki Mutu.....This is just the Beginning Ma'am Akwai Abubuwan DA ba tanada Musamman saboda Ku ,ke kinada boka Ni ina jida Ilimi ....next Time Don't Try To mess up With Chemistry Student "

Na qatashe DA Bude kwalbar na jefar a Qasar dakin Sannan na Fito DA sauri Na Ja Mata Qofa.



Ina Fitowa na farajin Qamshin Turarensa Wanda hakan Ke nufin Tabbas Lallai yana Unguwar ,take Gabana ya yanke ya fadi Kar dai ace ya biyoni ne Aikam DA na shiga Uku.

Cikeda Tsoro nake bin 6arauniyar Hanyar dake UNGUWAR Wanda zatayi saurin Sadani da Titi ,Amma Cikin Rashin Sa'a ina Shan corner mukaci karo dashi , Take Ilahirin Jikina ya Fara makyarkyata.

"Sulthy Meyasa kika Fito ?, bakya Tsoron Mutanen ban su sake Ganinki Suyi mki Abind Sukayi mki....."



"Dakata malam !, meye haka? ,Ka sanni ne? ,Me na tsare maka da zakazo Ka tareni kanayi mn Maganganu marasa Kan Gado?, Who d hell Are you? ,abege Give dha Way"


Na Gaya Cikin Tsawa tareda qoqarin Ratsa shi.

Wani Irin damqa ya Kaiwa hannuna Cikin Fusatar da Maganganuna suka Haddasa Masa ,Dukda na Tsorata Kuma naji Zafin damqan da yayiwa Hannuna Amma ban karaya ba So nake Na Gama Aikata Abubuwan dake Gabana A yau dinnan Sannan zanzo Muyi sallama Don Harga Allah bana Son rasa 'ya'yana .


Muryarsace ta Dawo dani Cikin hayyacina

"Are you kidding?"

YA fada Cikin mamaki yana Dubana Na galla masa Wani Uban harara

"What Are you expecting ,I don't Know You Bani hanya Are you deaf!"


Na fada a tsawace ,Wannan Karon ba Muryan Dodo yaji ba kamn yanda na Fara maganr ,Asalin muryana Yaji tangaran . ...


Tsaki yaja batareda Ya tankawa 6a6atun da nakeyi masaba, sannan ya Fara Jana Ina Tirjewa bai saurareni ba har saida ya kaini Inda ya Parka Motarsa Ya Turani Ciki ya Rufe Marufin Kofar sannan Ya zagayo Ya shiga Driver Seat ya zauna Ya kai dubansa Fareni yaga yanda nake wani Huci sake faman hura sakakken Hancinnan nawa nakeyi Take idanunsa Suka hasko masa lokacin da nake Asalin Siffar munayferh Na Idan ina Fushi yayi Comparing Dinshi da wannan fuskar , take ya kawar dakai Zuciyarsa na Raya masa wannan Aikinn shiri ne.

Cikin Rarrashi ya Fara Magana

"Haba Sulthy what did you think You have Done?? Me Kike Tunanin Kinyi?"


A fusace na kalleshi Da jajayen Idanun Dake manne a mummunar fuskar nan nace

"Am doing the Right thing ,Am on the Right way ,Am wanna Leave you and Your Family live You with Your mum since She hates Seeing me With You ,Ban San me nayi wa Umma ba ta tsane ni bata son taga na ra6eka , bata son Ganin ka tareda Wata macen, Aaryaan Umma son ka takeyi kuma ta fini kishinka , zai fi kyau na bar Rayuwanka Ka Auri Uwarka inaga Hakan Zaifi muku Kwanciyar hankali dakai da ita ,AARYAAN Ina so ka manta ka ta6a rayuwa da wata mai suna munayferh ,Delete my image From Your Face , Delete my Love From Your heart Replace it with Ur mum , I can't bare it any more....."


Ma qarashe maganar cikin Rauni tareda Bude Marufin motar na Fice shi kuwa kasa ta6uka komai yayi Haushi Da Baqincikin Maganganun da na Furta a Kan Mahaifiyarsa Suka dirsar masa Yanaji Duk duniya babu wacce zata la'anci Uwarsa a Gabansa ya Qyaleta Koda me tayi matsayin Uwa daban ne a duniyar nan duk 6acewar Uwarsa Tafi masa komai.


A fusace ya Bude motar ya Fito har na Fara tafiya don barin Unguwar .


"Hey You "


Ya qwala mn Kira ,kaman bazan Juyo ba jin yanda yayi kiran Nawa Amma sai zuciyata ta kasa biyewa hakan ,Take na Cire tsoro na Iso har inda yake tsaye .

Kallona yyi a Wulaqance Sanannn ya Fara Magana Cikin zafi kaman An tilasta masa


"Who d he did you think You're to insult My mum and Think You are Going for Free ,Kece a qasa dani don haka dole Kibi Uwata No matter how bad she is Cus She Gave birth to me she Take Care of me when you didn't Exist and she'll Continue till the Rest of her life ,you have To no gut to Insult her in my Presence ,Don kin samu ina sonki Thou lemme tell You son da nakeyi mki Bai Kai Koda qwayar zarra daga Cikin Wanda nakeyi Mata ba ,Stupid .... Insane jaka Kawai Wacce bata san darajar Uwa ba ... Shiga Mota kafin na sake Sauya Mki kamanni "


Cikeda tsoro Da firgike nake kallonsa Inason qaryata Kunnuwana Da abinda suke Jiyo mn daga bakinsa Amma Abin ya faskara Shi dinne fah.


Kafin na Qare Tunani Naji ya damqi hannuna yana Qoqarin sakani a Mota , Haqora na Dora Kan damtsen hannunsa dake riqe da nawa na gantsara

Please Login or Register in order to submit comment