Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hararana ,Ni kuwa na leqo tareda Sakar mata wata Uban Gwalo


Ummie ta dubemu duka tace meya faru duk Kuka wani Shigo mana Daki a Guje babu ko sallama?.


Saida na Tsagaita Dariyar da nakeyi tukunna na fara Magana Cikin dariyar da nake qoqarin hadiyewa.


"Ummie Kinsan jiya sunyi fada Da ya ILU (Ismail) ko?, Tho ai nice na hada su , Don na lura dasu Halinsu 'Daya Ita masifaffe Shima masifaffe ,Shine Dazun na dauko wayanta na saka mata numbernshi na tura masa Saqon Soyayya da ban haquri..."


Ifrah ta jifeni da pillow Alamar nayi Shuru Amma sai naqi na cigaba da cewa.


"Koda na Tura mshi sai na Saka sunanta a qasa , na qarashe da I LOVE u my makaho ,Don ya Yarda ita dince ta Rubuta da kanta kunsan Dai makaho take Kuranshi Don yana yawan saka eye Glass, Shima da yike Mayene Ina Turawa kaman Jira yake ya turo mata I LOVE YOUMore ,Nima ina sonki my sandar Rake But Apology Not accepted Sai kin zo kin durqusa har gabana kin Sake Roqon gafara sannan Ki Sake Furta mn Kalmar Nan naki ta qarshe ,Shine fa da na Nuna Mata,na kuma gaya mata Nice Msabbabin fadarsu na jiya ta Biyoni a Gudu wai zata dakeni bayan ni taimaka mata Nayi"


Gaba dayansu Sukasa Dariya ,Harda Ramlah yayinda Ifrah ta Cika tayi FAM ,nan take ta fara hawaye dama shagwa6a66iyace ,Dariyan da mukeyi ne ya tasar da Hamdah dake kwance......


Da sauri Na Isa da Daukota Daga Kan gadonta na Shiga Jijjigata ina fadin

"Sorry Haleematy matar Tweeny ,Mums Dinkine Suka tasheki Da ihunsu ko?, Sorry babyna Very Soon zan Haifa Mki baby Sister Wacce zata rinqa Tayaki hayaniya kema Kinji?"


Ifrah da ta iso Kusada ni ta Leqa Fuskar Babyn Tace

"Ke ai inaga Ba Zaki Haife Cikin nan da Rai ba , Don nasan Dakanki Zaki kasheshi da GujeGujen nan ,Ni ban ta6a Ganin Mai Ciki tana Zuba Uban Gudu Ko nauyin Jikinta bataji ba sai akanki ,wayasani ma ko tuni kin Dade da kashe Cikin Gawa kawai Kike Jide dashi?"

Turo baki nayi na Miqa mata Hamdah da tayi shuru ta fara barci ,Na Sa hannu na na dafa Cikina Da yayi wani qato kaman na wata Bakwai alhalin watanninshi Biyar .


Nace "Wlh bai Mutu ba, Ko dazu Naji motsin shi ,lokacin Kuwa Nasha Wahala ,Aunty Ramlah dama kema haka Kikejin Zafi idan Cikin ya tashi Juyawa ?, Kuma kika Yarda Aka zubar dashi?, Koda yake Ga Takwarar Mara imanin nan ,An haifota daqyar....."


Na qarashe maganar tareda kallonta nayi dariya ,Ita kuma ta Galla mn harara

"Mara Kunya kawai ,Uwar tawace Mara kunya ko?"

"Oho Wannan Ke ta shafa ,I hate Your mum passionately, sorry Ummie I hate Ur sister she's Heartless and Selfish Bata da imani bare tausayi "


Nadanyi Shuru jin duk sunyi shuru sun zuba mn ido ,Na kalle saleem dake Dubana fuskarsa babu yabo babu fallasa Tunani nayi nan fa ba 9ja bane ba irin mutanen da na sabayi msu rashin kunya su qyaleni bane, Na tabbata Ina sakeyin Wata magana Zan iya jin saukar tafi a Bisa kuncina shiyasa nayi waje da Gudu , ina fadin


"Yaa Saleem idan ka gama, yaaAary na Jiranka A balcony, kayi sauri fa Amma Tun dazu ya aikeni'"


Ina Fita kai tsaye Computer lab dn Gidan na nufa inda Aaryaan Ke kwance yana Kallon yanayin Aikin 'Yan sandan da Ya musanya A matsayin Tsagerun dake Tsareda Daddy a da.


A hankali na kusa kai dakin Bakina dauke da sallama ,Ya Amsa Still idanunsa kan Desktop Dinda Ke Ta faman Aiki


Qarasowa nayi na kwanta luf a Kirjinsa tareda lumshe idanu Sakamakon Shaqar qamshin Sanyayyar Turarensa da hancina yayi ,Shima Haka Kusan a lokaci Guda muka sauke ajiyan Zuciya ,A lokacin da ya shaqi Daddadar qamshin Humran da yake tamkar Amanne yake da fatana Don Tunda Aunty Sara (Auntyn su janaan) tayi mn wankan turarurruka a lokacin Bikin mu qamshin ya bi jikina ,har yanzu yana manne da fatana ,Sai qamshin ya hade da Humran da na Fesa Dazunnan.


Munyi shuru na wani lokaci kuma dukkannin Mu idanunMu a lumshe ,kallo Daya zakayi mana ka fahimci Gaba 'dayan mu muna Cikin Yanayine na nishadi Wanda Kasancewar mu Cikin Wannan yanayin ya Haddasa mana.


Kaman an tsikareni na Bude idanu a hankali na furta

''Ina Wuni Yayana"

Shima ahankali ya ware idanunshi ya sa hannu ya rungumoni jikinsa Tareda matseni ,Cikin qirjinsa Cikeda Mamaki ya furta

''Ashe Kin iya Gaisuwa Auntyn Abdool"

Dagowa nayi na gyara A jikinshi na Kwanta Flat ,
Saikuma ya matso fuskata dab danasa har muna shaqar numfashin juna, idanunshi cikin nawa, nasa hannayena Naja Kunnensa na manna Goshina da nasa nace

"Daddyn humdah, Yaushe zamuci ragon Sunan Baby?"

Na fada Cikin narkarda Murya, Wanda Saida tsigar Jikinsa ya tashi dama tuni jikinsa Ya fara rawa Sakamakon hawa Jikinsa da nayi.


Bazai iya jure irin Abubuwan da nakeyi masa ba ,shiyasa ya sa Hannu ya dage Fuskata dake Manne da nasa ya maida kafadarsa sannan ya bani Amsa murya Chan qasa kaman Maijin sanyi..



"Abiee....ya Riga ya Yanka ..... Ku...Ku..kum...kuma....anyi taron achan Nigeria"


Daidai Lokacin naji ana qarar door bell da sauri na tashi daga jikinshi Tareda bada umurnin A shigo ,Don Nasan na sa Aaryaan a Cikin yanayin da bazai iya magana Ba.


Saleem ya shigo da sallama ya miqawa Aaryaan Tickets dinmu da Suka shirya mana na komawa India ,ya Qara da cewa.


"A.A mun Gano wacce take behind this Case da taimakon Isma'il da Ramlah ,Amma bazamu gaya maka ba kasancewar Sun fara Farmakin rayuwanka ,Sbd Sun Gane kana cikin qasar nan Sun Kuma tabbatar da ka Qwace daddy daga hannun Mutanen su Amma basu farga da 'yan sandan ka ba ,So muke mu hada msu tarko ,Shi yasa Muka hada Mku Tafiya kaida matarka da Daddy Ku koma India Har sai ta haihu karku sake Ku waiwaye Nigeria Cus zaka iya rasa Matarka dama 'Dan dake Cikinta ........"







๐Ÿฅบ๐Ÿฅบ๐Ÿฅบ๐Ÿฅบ

MEKE SHIRIN FARUWANE?



YA AKAYI SU INNA RABI SUKA SAN AARYAAN YA JU6UTAS DA DADDY?




SHIN SU ZASU SAMI NASARAR AUWATAR DA QUDURINSU KUWA?





YA MAGANAR JEOBAI ?, KUN MANTA SHI KO?




INA MAGANAR KS DAUD SHIMA KUN MANTASHI AHBI?๐Ÿ˜‰







To sunanan kuma zasu dawo inshaaah.



Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ


20th novโœ๐Ÿฝ
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
**HAWAN-JINI NA*
~{uwar mijina* ๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._




ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


_*Chapter 69&70*_






Aaryaan ya kawar dakai Gefe Cikin Tsananin 6acin rai ,lokaci Guda Saleem yazo ya tarwatsa Mshi Farincikin da Yake Ciki A ganinshi wannan Rainin hankali ne kawai ,ya dauke shi Rago ne bazai iya kama Masu laifin da yake Burin Kamawa da hannunshi Ko ta halin qaqah! Ba, ko tunanin su Wata 'Yar qaramar barazana Kamar wannan Zata iya Hanashi kama masu Laifin ne?, Inba Dan yasan Halayensu Gaba daya ba ,Da yace hada baki Sukayi Suna son Ganin bayansa da Na case din ma Gabaki daya.


Dunqule hannunshi yayi Ya daki Qasa ,Saida Floor din ya Girgiza nima na Dan Razana a Fusace yace

"Who the Hell is that Idiot ?, Wanene wannan Criminal din ?, And Why Are you chasing me out of this Case?, Wai Tsaya mah! Meyasa ka biyoni nan ? Ba a Balcony Nace ka Jira Ni ba?"


Ya nuna Saleem da 'Yar yatsa "Saleem na fara Zarginka ,Kuma idan na tabbatar da Abinda Nake zargi a kanka saina 6a66allaka ,Saina harbeka da Bindiga Ka Mutu A banzah! ,So Get the helll out Of my sight"

Ya qarashe Cikin karaji tareda nuna mishi hanyan Waje ,Qin Fita Saleem yayi idanunsa kyam akan Na Aaryaan daketa faman Huci yana Jinjina Zuciya irin na Aaryaan ,Ya kuma jinjinawa Ramlah da ta iya Rayuwa da shi na Tsawon wasu watanni Batareda ya halakata ba ,Muryan Aaryaan da Ya sakeji a karo na Biyu shi ya dawo dashi daga Dogon Tunanin da ya zurma .

"I said Get ur Fucking self Out of my sight"

Shima Saleem a tsawace yace

"Am Going No where !,A.A ,babu inda zanje Sainaga Ka fara Shirin Barin qasar nan ,Idan kai baka damu da Rayuwanka ba Ka damuda Na bayin Allahn dake tareda kai manah ,I know Everything about these people Sunada Hadari ,Neman Ku Ake EveryWhere anan Country din anda They wanto take Out yr life ................"


Nan ya Cigaba dayi masa bayanin Yanda Suke farmakinsu Ko yanzu haka ta Private Jet zasubi Ya Sauke mu A Wani qasar mu hau Wani Zuwa chan don basu son sugane Sunayensu A jerin wa'enda Suka bar qasar ta kowane National Airlines na LIOUS.


Jikin saleem yayi sanyi Sosai qaunar Abokanan nasa ya shiga Ranshi ,A sanyaye ya dago ya dubi Saleem dake kallonsa Shima yace

"Tho inasu Hilaal ?, Meyasa Mu kadai zamu tafi?, Meyasa zaka 6oye mn Wanda yayi sanadiyyar Mayar mn da qanne Marayu na tsawon Shekaru Uku, Ya quntatawa Danginsa , ya barsu da Jimami ?, ya sanya BaqinCiki Cikin Rayuwan qanwata?, ya haddasa Auren na da qanwata? ,Yaso so Jinin Uncle dina ya Kusa qarewa a dalilin Neman Biyan nasu Buqatar?, Who is that?, Meyasa Bazaku Gaya mn Ba Naje na Kamashi na mashi Hukunci daidai dashi?"


Saleem yayi murmushi Yace

"MAN calm down ,Abokanka Suna lafiya Kuma babu Abinda zai samesu Inshaaallah Don Babu Wanda suka Sani Cikinsu , kuma bamu san sunan Wacce Muke zargi ba ,Haka kuma hoton ta ,Infact bamusan Komai dangane da ita ba ,so Relax mahn Kaine Zaka kamata da hannunka Ka Zartar da hukunci dakanka , Dole zaka Bima Wa'enda Aka zalumta Hanqqinsu Dole Kaine Zaka kamata da hannunka, Babban yayanmu .....SIR!"


Ya qarashe Magana tareda 'Yar Sara masa yana 'yar dariya Sakamakon Wani Uban Hararan daAaryaan ya watsa masa.

"Ohkay Thanks you can Go" kawai yace a taqaice...


Saleem Ya Dan Sosa qeya yace

"Ehmm...sir Dama Baka bamu BoX dinnan ba na hannun madam"

Aaryaan ya juya ya dubeni da na Wani kafesu Da idanu yace Ina kika Ajiye ajiyan Daddy.


"Yana Cikin Kayana"

"Ohkay ,Bari na dauko !, kar na wahalar dake "

Ya gaya yana Miqewa ,Ya dubi Saleem dake tsaye ya fitoda Waya ya fara Turawa su Hilaal Saqon cewa ya Samo kansa daqyar Ammah ,A tare suka Fita ya dauko Ya Miqa masa Batareda ya Duba meye a Ciki ba.....


_____

Washe Gari


Tun a parlor yakejin Kukan Humdah Da kuma Muryan Ummie tanayiwa Ramlah fada , Da sauri ya qarasa Amma da Shigar shi yaji dalilin da Yasa Yarinyar Kuka ta dalilin fadar da Ummie keta famanyi.

A Fusace Ya Qarasa shiga Dakin ya dauki yarinyar dake Shimfide A Gefen Ummie ya juya zai Fita Ummi ta Kira shi

"Ina zaka Kaita kuma"

Juyowa yayi ya kallesu Gaba daya yace

"Na kar6i 'yata ,Tare zamu bar qasar''

" haba Aaryaan meyasa ...."


Dakatar da ita yayi da cewa

"Ummie ,Meyasa Ramlah bazata Yarda da Qaddara ba ?, Meyasa take horon HUMDA akan Abinda Ya shafe mu Gabaki daya?, Meyasa Zaki Zuba mata ido Har na tsawon Saki 'daya Bata shayar da Yarinya Ba kuma ki Tsaya Kina Wani Rarrashinta Akan me?, Ita yarinyar me ta Sani? Bata San komai ba! Bata da lqifi Mune nan masu laifi ! ,Don Tun farko Saida Umma tace kar mu ra6e juna Harta Qamshin Turaren Juna ta Hanamu ji ,Daga qarshe mukayi kunnen qashi muka sa6awa Umurnin ta akan namu Buqatar ,Ayau Ga illar sa6awa iyaye mun Gani tunda Gashi Harda Rabo tsakanin yaya da qanwa ! Tho muda mukayi laifi mun Yarda da qaddara Meyasa zamu hukunta baiwar Allahn da bataji ba bata Gani ba?, Humda me ta Sani da Zaki horeta da Wannan Hukuncin?, Ke kuma Ummie kika zuba mata idanu Duk sbd bakya son Ganin 6acin Ranta!, so....na lura yarinyar ce bakua son Gani Cikin Zuri'ar Ku shiyasa Kuke Neman Halaka mn ita ,So don't worry The war has Come to an End....Na kar6e 'yata Har Abadah , Ki kwantar da Hankalin ki Ramlah ki manta kin Ta6a Haihuwa dani I think this I'll solve Ur Problem idan kin daina Ganinta Bazaki Rinqa Tuna Abin Kunyan da Ta ta6a Giftawa Cikin qaddararki bah.. ,Ke kuma Ummie Ki zauna da Ita tafi miki HUMDAH Sau Dubu Million, Tunda ta zama 'Yar Gold Bazaki iya Tursasata Ta Shayarda 'yata ba ,Na tabbata da Munayferh ce dukda bata sona bazata Ta6a Bari jinina yayi kuka Ba, Sai Gashi 'Yar Uwata Wacce ta haifi jinina ta Gummace Ganin Kukan Gudan Jininta akan ta bata Haqqinta .....Ummi mun tafi ,ki Taya mu da Addu'a na tafi da qayar da take daamunku....."


Yana Gama Fadin haka ya fice ,Yanajin Ummie na kiranshi amma yaqi Juyowa ,Yasan Zafin Raba tsakanin Uwa da 'ya Tunda Yagani akansa yanda Umma taqi damuwa da lamarinsa ,Amma Yana Gani Kamar Ramlah bata qaunar Humdah ne Wanda Kuma ya rasa Gane dalilin hakan ,Kuma yayi Akqawarin kome zai faru saidai ya faru Amma babu mai hanashi barin qasar da Ita ,Saidai Rauyuka su 6aci...........

Yana Fita ya kira Haidar a Waya yace ya siyo masa Kayan jarirai ya kuma tura masa Sunayen Ingantattun madarar da Ya kamata a bawa Jariri ,Babu jimawa ya Siyo daga nan muka ci gaba da Shiryeshiryen Tafiya .



Babu magiyan da Ummie da daddu basuyi masa ba Amma yaqi Tankasu ,yana Sa6e da ita a kafada har Muka bar qasar....

Ramlah kuwa Tasha Kuka Har ta Godewa Allah ,Bata San tanason 'yarta ba Saida Aaryaan ya Rabata daita.


Nikuwa Wani Mugun dadi nakeji mun samu baby ,Dama Ni kaina inajin haushin yanda kullum Ake Wani durawa Yarinya Madara ko Zuma bayan Ga Uwarta Lafiyayya ,Ko irin kallon banzan da Ramlah takeyi Wa yarinyar yana damuna sosai ,Amma Nayi tunanin Maybe Saboda azabar da tasha Wajen Ummane Yasa tsanar Umman ya shafeta kasancewar Kamanninsu 'daya haka kuma Sunan su daya.




Alhamdulillah Mun Iso India Lafiya ,muna Isa Aaryaan ya Turawa Abbie text message Don Saleem ya gargadeshi da Karya sake kiransa sai ya Isa India don sanadin call dinda yayi da Abbien ne aka samu damar Duba Digit din Qasar da Yake Aka San inda Suke...



ARanar Abba ya kiramukayi Video call Gabaki dayansu Suna zaune Cikin qaton Parlon Abba , Umma na Zaune a Gefen shi na hagu Yayinda InnaRabi take zaune a Gefen dama ,Ammie na zaune kusada InnaRabi, yayinda junayd Ke zaune Kusada Umma janaan a Gefen sa ,Sai kuma umar dake tsaye a bayan Abbie Ya Wani zama Babban mutum ,Sai kuma Abdool ,Suwaiba ,Twince dake zaune bisa Rug ,Fuskokinsu dauke da murmushi.


Haka muma Fuskokin mu dauke Yake da Murmushin, ina Zaune na Wani kwantar da kaina Bisa Kafadarsa Hannuna Riqeda Humdah.


Fira Mukeyi sosai Cikin raha da nishadin Ganin Juna ,Gaskiya Nayi kewar Ammie sosai ,na kuma lura da Wani irin Raman da tayi , Nasan duk kewar Mijinta yasa ta zama hakan ,don har yanzu bata san muna tareba ko a yanzu Da muke VC mun 6oyeshi ne bamuso a sani๐Ÿ˜ ,kuma na dau Aniyar sadata dashi koda sau dayane kafin mu dawo Nigeria, ta Dan kwantar da hankalinta , Haka kuma Nayi Mamakin Ganin su Janaan a Gidan Amma da Nayi Tunanin Maybe Abbie ne ya kirasu Sai na shanye mamakina.


Muna Cikin Hira hafsah ta Shigo ,Itama ta samu wuri Kusada Ammie Ta zauna ,Nan fa mukafara Magana Da ido tsakanin Mu Uku Wanda Mu kadai Muka San Ma'anar Yaren namu ,Ina lurada Yanda Umma Ke zuba mana Wani Uban Harara Akai Akai Amma ban damuba ,Shiyasa ma Nake Wani Shigewa Jikinsa Ko kunyar Ammie da Abba banaji๐Ÿ™ƒ basai na kalle su ba ma?๐Ÿ™„......


Munsha Hira sosai kaman kar mu daina nan Abbie Ke sanar mana da Ansa Ranar Bikin Hafsah da Hilaal nanda watanni Hudu masu zuwa Wanda dama Aaryaan ya Riga ya Sani Tunda Hilaal ya sanar dashi.


Wayyo zokuga Murna a wajena kamar wacce akayiwa Albishir da Gidan Aljannah, a Ranar kuwa bayan mun Gama wayan, saida na sake kiran Hafsah Nayi mata tsiya sosai Tun Tana bani amsa Har nafi qarfita daga qarshe ta Gaji ta Kashe wayan......



Sosai Humdah take samun Kulawa ta wajena da Wajen Uban nata ,Haka kuma Ni kaina nake samun Kulawa Ta wajensa Sosai ,Baya barin Nayi Aikin komai ,shikeyi mn komai iyaka Nayi Wanka na nemi na sakawa a Cikina , Kullum sai mun Fita mun Zaga wuraren shaqatawa da dama mubar daddy a Gida Shikadai ๐Ÿ˜™ ,Haka idan muka shiga Cikin Mutanen Qasar muna Juya harshe sai ka rantse Muma asalin 'yan Indian ne ,Hakan yasa muka 'Dan saba da Maqotan Mu Wa'enda muke zaune a Kusada Mu ,da Yake Suma sabbin Ma'aurata ne Kuma Mayun Fita yawon Shaqatawa Tho duk in mun Fita sai mun hadu dasu Har Suka farayi mana Magana Daganan muka fara zuminci.....




Akwana a tashi babu wuya Wurin Allah ,Cikina ya shiga watar HAIHUWA, Nayi Wani qiba na kumburo Qafafun nan Kuwa suma a Kumbure Suke Ko tashi wahala Yake min ,Haka kuma Dakansa yakeyi mn Komai harta Wanka da Wanki, dama chan shi Yake Girki da wasu Abubuwan ,Rainon Humdah ya koma Ga Daddy .


Sosai Suke bani tausayi Ganin yanda Suke wahala don Faranta mn.


Yauma kaman kullum zaune nake akan kujera Shi kuma yana duqe a qasa yana matsa mn. Qafafuna da Suka kumburo , Tun. Da sake nakejin Ciwon baya da Nauyin Jiki harta Cikin yau Wani irin nauyi ya Qara Shiyasa na kasa koda tashi daga Inda nake sai faman Yatsine Fuska nakeyi tareda Cije lips dina Akai Akai.



A hankali ya dago ya dubeni yaga yanda na Wani 6ata Fuska yace


"Sulthy lafiya?"


Girgiza kai Nayi kawai Batareda Nace masa komai ba ,shima bai sake cewa komai ba ya maida hankalinsa Ga Tausar da yakeyi mn.


"Sulthy idan Allah ya saukeki lafiya ,Aka Sami 'da Namiji zaici Sunan Abbie, idan kuma mace Ce zataci Sunan Ammie, kinji"


Shuru Nayi ,Ban tanka ba ,Hakan yasa ya fahimci Tabbas Akwai Problem da sauri ya Sake qafar ya dago zuwa inda nake yana tambayan Lafiya?, me Ke faruwa Kodai cikin ne ,Amma sai na nuna masa komai lafiya.


"Ban Yarda ba, ko yunwa kikeji?"

Girgiza kai Nayi daidai Lokacin da Cikina yayi Wani irin Murdawa na qwala Wani irin Uban Qara mai razanarwa.....

****
9jeria๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ

Tun Jiya janaan ta tashi da naquda Wanda Tun jiyan Suke Asibiti, Har yanzu ta kasa Haihuwa dakanta sai wahala da takesha Sosai Gashi Junayd yaqi Amincewa yasa Hannu Ayi mata aiki a Ciro 'Dan Gani Yake kaman Idan yasa Hannu akayi mata aiki rasata Zaiyi .


Hankalin kowa ya tashi , Umma sai safa da marwa takeyi a ward din Da ka ganta zaka fahimci tsantsar Tashin Hankalin da take Ciki yayinda Abba Ke tareda Junayd yana Bashi haquri akan ya Amince yasa Hannu Ayi mata Aikin ko Allah zaisa A dace ,Shikam Gabaki daya ya ma Rude ne Hankalin sa Gaba daya ya bar Jikinsa Shiyasa Ko Fahimtar maganganun Abba bayayi.....


Qarfe 10:10am Wanda yayi daidai da Qarfe 12:26 na qasar India , nurse ta Fito daga Dakinda Janaan take a hanzarce duk Suka Iso Gareta Suna tambayan Lafiyan Wacce suka kawo.



Nurse tayi murmushi tace alhamdulillah, Yanzunnan ta sauka Ta haifi 'da Namiji And dukkanninsu Suna Cikin qoshin lafiya ,koda suka tambaya zasu iya shiga Cewa tayi a'ah sai an Gama shirya su Tukunna ...


***

India

Tunda Nayi wannan qarar ya fahimci naqudace dama ya lura da yanayina Tun da safe,Don haka dakansa Ya shiga bani taimakon Gaggawa irin nasu na doctors, Qarfe 12:26am Wanda yayi daidai da Qarfe 10:10 am agogon Nigeria na sumbulo 'yata mace Mai Tsananin kamada ni๐Ÿ˜˜.



Dakansa Ya shiryani da Babyn Sannan ya Fice don Siya mana Abubuwan da zamu Buqata ,Amma me?, yana Fita Wani naqudar ya kuma tasowa Another taste of passion, Sai a yanzu na Gane Ashe Naqudar da Nayi a farko Somanta6i ne wannan shine asalin Naqudar don Sosai ya bambanta da Wanda nayi da farko ,Kasancewar Wannan na samu taimakon Gaggawa Tun da na fara ,Sa6anin wannan da yazo Unexpected ,Cikin Lokaci Qanqani na Jiqe da zufa Na Galabaita dayawa Ga yarinyar Sai Ihu take tsalawa .



Ihun Jaririya ya janyo Hankalin Daddy dake kallon news a Daki, da sauri ya Iso Dakin dani ya fara arba ,sai nishi nake Fitarwa sama sama Kamar Zan Mutu ,Gabaki daya qarfina ya qare .


Ganinshi yasa na Bude baki a hankali zanyi magana Amma inaa banida Qarfin Hakan ,gaba daya na gama Ruda daddy kuma ya rasa Abinda zaiyi ,ya rasa wanda zai fara taimako tsakanin ni da babyn dake tsala kuka chan gefe ,Cikin ikon Allah Saiga Aaryaan ya shigo kaman an Jehoshi.


Yana Ganin haka Hankalin sa ya tashi baisan Lokacin da ya watsar da Abubuwan da ya siyo ba ,ya sunkuceni yayi Waje Daqyar ya samu taxi ,Sannan Daddy ya biyomu da sabon BabyGirl da Humdah Harda kayan Haihuwa.


Muna Isa Asibiti aka samn oxygen Don na samu damar shaqar Numfashi ,tareda Shigar dani Dakin Haihuwa nan take likitoci suka fara aikinsu.


Yayinda Aaryaan da daddy Suke Ta TO and FRO a harabar Wurin ,kallo 'daya zakayi msu ka fahimci tsantsar Damuwan dake tattare dasu.

Ganin wannaba shine solution ba yasa A hankali daddy yaja Aaryaan suka fice haraban asibitin, kaman zomo da bindi haka Aaryaan ke binsa kafa'dun Aaryaan daddy ya dafa yace

" Friend don't panic, Drs suna iya bakin 'ko'karinsu, da sannu Allah zai raba matarka da abunda ke cikinta lafiya, so I want to you to be very strong, save your strength remain a man, Allah na jin ro'kon bayinsa koda yaushe dan baya gyanga'di bare barci,Addu'ar ka kawai take Buqata a Halin yanzu ba damuwa ba please be strong"


Kalaman daddy sun qarfafa wa Aaryaan Sosai,

gya'da kansa yayi kafin yace" haka ne Aboky, insha Allah zanyi yanda kace, but daddy inshaallahu Yanda ta haifo Maka second Wife ,Haka nima zata qarowa Ammie na Second husband Lafiya Cikin qoshin lafiya "


Daddy yayi Murmushi ya gya'da kansa yace


"Saidai Third wife don kuwa babu second husband sai kace a jahiliyya"


Aaryaan yayi yaqe

Daidai Lokacin da Doctor fito ya nufosu.... A tare suka nufesa suma.



Aaryaan jiki da baki na rawa yace

" How is she, how is my wife Dr, tell me pls how is she doing?,tell me what happen to her?...... "Dr ya dafa kafa'dun Aaryaan

yace" Dude, you need to calm down everything is gonna be alright,still akwai time Lokacin haihuwanta baiyi Ba, har yanzu"


"Can I see her pls, I really want to see her, Please Don't say No!"

aaryaan ya fadi kaman me shirin yin kuka

"Offcorse why not!?"

Doctor ya fadi yana Dubansu Duka, har rige Rige sukeyi wajen shiga ,nurse Biyu ne kawai a Tareda ita .


Ina Ganinsu wani irin qarfi ya ziyarceni na daga hannu na Cire Robar oxygen dinda ke maqale a bakina .

Na fara magana Cikin Fidda Numfashi sama sama.


"Ya...yaa...Aarry.....da....ddy.......Ku ....kir..a ....mn Ammie.... Da Umma.....in ...ne...mi ......Gafar...ar su....."


Ina kaiwanan na wani ja Numfashi da qarfi hakan yasashi matsowa da Gudu ,Ganin Haka yasa Daddy ya Fahimci Aaryaan Dakansa yakeson Kar6ar haihuwan shiyasa ya fice yayi waje ,yayinda Sauran nurses din suka qaraso wajen ,Amma babu Abinda suka iya taimakawa dashi ,don Shi kadai ya kar6i haihuwar suna tsaye ......


Qarfe 2:40am na sullu6o dana Namiji mai tsananin kamada Aaryaan Kaman An Ysaga kara





Cikin qanqanin lokaci aka gyara mai jego da jarirai Daka Gansu kaman Ka sacesu Ka gudu๐Ÿ˜˜.



Abba shine Mutum na farko da Aaryaan ya kira ya sanar dashi Munayferh ta haifi 'Yan Biyu ,mace da namiji nan Ma Abba yake sanar dashi Janaan ma ta sauka, ta Sami namiji...


Sosai Yayi Murna da samun wannan qaruwar ,daganan Yabawa Daddy wayan suka Gaisa da Abbie dama suna gaisawa akai akai idan Aaryaan ya kirashi.





Cikin qanqanin lokaci Labarin haihuwan 'Yan biyun Munayferh kuwa ya karade koina lunguna da saquna na dangi sai San barka akeyi yayinda ,Umma taji labarin Tamkar Labarin mutuwa ,Hankalinta ya tashi Sosai har ta kasa 6oyewa Ta Shiga Part din Ammie tayi mata Ci mata mutunci Kasancewar ,Kasancewar kakus tana Part din InnaRabi a Lokacin, shiyasa ta Sami damar Zaginta iya son ransu , Su Ameer da Abdool naji suna ji suna Gani Amma babu yanda suka iya haka suka zuba mata ido ta qare

Please Login or Register in order to submit comment