Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abul-Rahman naji cikin Kuka yana cewa"Aunty Please kizo Su Yaa Umar da Anty Zainab sun dau key din Dakin Dad๐Ÿ˜ญ" iya Abinda naji kenan wayar ta katse.

Tashin Hankali!, ai bansan lokacin da na hankade Robar gabana ba na Mike ina haki, Da mamaki na Sai naga Hafsah ta 6ingire tana bacci ban tsaya nazari akan Dalilin baccinta lokaci guda ba na gyara mata kwanciya nja mata bargo na dau Robar awara nakai kitchen Nasa shi cikin oven.

Ina dawowa na bude drawer na dau makullin mota na nafice, har nayi nisa da driving na tuna banida isasshen Fuel din da zai kaini Kaduna . kai tsaye motor park dinda ke sabonGari na nufa na parka na dau taxi ya dawo dani .
Ina Shiga cikin Saa babu kowa A falor , key din motar yaa Arry nagani a saman Center Table, da Sauri n dauka nayi waje

Inda driver ya parka motar dazun na nufa, na hau na tada Gateman ya wangale min Gate, ina isa Daidai gate din na dakata tareda zuge glass din Motar na kalle Malam Ali mai gadi nace"Saura in an tambayeka ka koro Masu bayani" ban tsaya jin Abinda yake cewa ba nayi gaba Abina.

Daga Zaria zuwa kd tafiyar 45-50mins ne a motar gida ,1hr a motar haya, Amma Dan tsananin Gudun da nake Sheqawa 20mins na isa Kaduna (kunsan gudun Firari ba na wasa baneh)

Ina isa bai gadi ya Fara kirari "AngoAngo Ango kasha kamshi" duk daukan shi yaya ne fah.

Sai da nayi parking na Zuge Glass din motar, yana tozali da Fuskata, Yan hanjin cikinShi suka kada ji kake kululululu.....๐Ÿ˜†

Na galla Masa wani Mugun hararar da yasashi ja da baya batare da ya shirya ba,


Kai tsaye Part din Su inna Rabi(kishiyar Umma) na nufa , a falo na tarar da Abdul Raku6e gefe guda yana kuka kaman maraya... Allah sarki Dan kani na, Yana gani na ya Rugo da gudu ya rungumeni "Anty pls karki bari Su bude Dakin please Aunty"

Ganin kaman ba cikin hayyacinshi yake ba yasa na zaunar dashi da nufi Fridge na Dauko mishi ruwan Sanyi Dan ya kora ko yaji dan Sanyi a ransa, Amma sai yaqi amsa sai nuna min Part din Dad dina yake.

Riqo hannunshi nayi muka nufi part din, Ga mamaki na Sai ganin Su nayi tsaye a bakin kofa Suna kiciniyan bude kofar.
Ta baya na jawo Wuyar rigar yaa Umar Wanda ke faman zura key a mabudin kofar.
Gaba dayansu Waro ido Sukayi a razane Dan ko a mafarki basuyi zaton ganina a wannan lokacin ba.

Cikin zafin nama na fizge makullin A hannunshi, Aikam kaman raba ruhinsa nayi da gangarjikinsa, haka ya wani zabura yana Zazzare min ido kaman maye sabon kamu(Wayasani ma ko sabon mayen ne?๐Ÿ˜)
Na kalle Abdool Cikin Murya mai Nuna tsananin 6acin rai nace " Twin cikin Su, waya ta6a ka?"
Da hannu ya Nuna Suwaiba da Zainab
Suwaiba wacce itace kanmu daya a cikin Su tace "Eh an dake shi din me zakiyi?,Rama mishi zakiyi ne ko me?" Bata ida Rufe baki ba taji Saukar tafi a kuncinta, nan na shiga lafkarta harsaida na tabbata tayi laushi.
Juyawan da zanyi naga wayam duk sun Ware, Nima bin bayansu nayi Dan na tabbata suna Dakin uwar su
Aikam anan na taddasu Sunyi tsuru-tsuru suna Gayama innar tasu Zuwana.

Kulle kofar nayi da makullin dake jikin kofar, na jefar da makullin ta window...

Salati inna rabi ta saki "Innalillahi munaifa, wannan wane irin Sakarci ne?, kin kulle mu kin jefar da makulli ta taga ta ina zamu fita?

Ban tanka ta ba na Jawo wuyan Rigar Zainab na gwarata da bango nace " Uban waya Baku izinin daukan makullin part din mu?,Me kuka Ajiye anan ?,Eh tambayanki nake me kuka ajiye anan?? Shine Dan Abdool ya hanaku shiga harda dukan Shiko?,Wannan wane irin Rashin imani ne?" hawaye ya gangaro bisa kunci na Dan tausayin yanda naga Qanina cikin kwanakin da basu wuce 3ba duk ya rame ya tsukare kaman bashi ba


Muryar inna naji cikin hayaniya tana cewa "Dan mun dakeshi bamu isa dashi bane?, faruq oya jawomin Dan banza nayi maganin shi yanzunnan


Sakin wuyan Rigar Zainab nayi na hankadeta tayi gefe na kamo hannun Abdool nazo gaban inna na ce " Ba sai an kawo miki shiba! Gashi na kawo mk shi da kaina!, duk Wanda ya isa ya ta6ashi na gani"

Ai ban gama Rufe baki ba naji tassss An tsinka mishi mari ta baya, muryar yaa Umar naji yana cewa "An dakeshi din ko Zaki zama mishi ne?"

Kallon inna nayi sai faman murmushi take yi, tausayinta ya kamani, Da na tuna irin hukuncin da zanyi mata.
Nan da nan na fara jaa da baya hannu na riqe da kai, na wangale baki na saki ihu..........







See you tomorrow๐Ÿ’ƒ


Fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ

18th AAugust



๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._



_
Aunty Hafsah A Garkuwa wannan page din naki ne_ โค๏ธโค๏ธโค๏ธ

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...

*_Chapter 7_*

Dan kwalin Jallabiyar dake kai na na cire nayi wurgi Dashi, Na Yi Kacha-kacha da Gashin kaina, nayi tsalle na dira a wuyan inna Rabi, Na kai mata wani wawan naushi a ciki (Irin na Yan wrestling), Ai ban bata daman ihu ko kuka ba Dan mugunta na Gwarata da bango tayi kasa ji kake TIMM....๐Ÿ˜†,Sai A lokacin ta Samu dabar ihu cikin muryar nan nata kaman An burga tsohon bajaj "Wayyo ummaru , ka zo ka taimaka min xata kassara ni, Zainab ina kike,suwaiba kuna Ganinta zata kashe muku uwa Baku ce komai ba?'' Har ga Allah maganganunta Sun Sani dariya hakan yasa na shiga darawa kaman wata mahaukaciya,And still ina Mazgar ta, Saida na tabbata nayi mata Raunuka kuma tayi laushi sannan na barta najuya ga Zainab wacce take ta faman daga kafa Alama fitsari takeji kuma kiris take jira Ta Antayo ta....

Na Shiga darawa ina tafi kaman wata zararriya "Wato Ku Masu karfin hali Har kun isa Ku ta6a mana kani , har a gabanta zaku iya daga hannu Ku dakeshi, yanzu Akafara ,Yanzu na Gama da uwar Ku ,Saura ke....." Dakatawa nayi jin zuban wani Abu kaman ruwa,Zainab ce ta tsula fitarin da ya tarun mata a Mara Dan tsananin tashin hankali.

Abdool banda dariya babu Abinda yakeyi nima dariyar nakeyi na cigaba da cewa "mai girma Tunbul yace karku taba wanchan mai bargajajjen hancin," na Nuna Zainab da Dan yatsa

Wani irin Ajiyan zuciya ta sauke har saida najiyo shi, Dariya na kara sheqewa dashi nace "An gama Ranka Shi Dade..., ke mai katon hanci Naki hukuncin ba na dukabane idan kinyi biyayya ba zamu taba lafiyar ki ba, Dukawa zakiyi ki lashe Fitsarin nan Tass in ba haka ba Mazgar da uwarki tasha Somanta6i ne akan naki.."

Ai ban gama Rufe baki ba ta duka ta fara Lashewa tana yatsine fuska Hawaye na tsiyaya daga idanun ta...

Na juya ga Zee da Umar Wanda Firr suke jira su zura a guje

Kwalbar champagne din da na gani saman Fridge dinsu na Raruma na Narka qasa, nace su taka kwalbar har sai kafarsu ya fashe, kuma banason ganin jini , idan ko naga jini, Lashewa zasuyi.....

Ina Gama fadar haka na nufi Hanyar toilet Dan na cire makullin dake nan ina dawo Wa na gansu jini na kwarara daga kafar Umar ita kuma zee hannu tasa tana tana Tare jinin Ga kuma suwaiba da ta gama lashe Fitsari innaa kar har tayi baccin wahala, tausayin su ya kamani na kalle Abdool da shima yayi tagumi ya koma kalar tausayi.
Nan da nan na yakice tausayin su Wanda ke Neman dunkusar Dani Na shiga darawa kaman wata mahaukaciya Dariyar da nikeyi ne ya farkar da innaRabi ta tashi firgigit Tana ihu dakatar da nawa dariyar nayi na murde fuska kaman bani na gama Dariya yanzu ba?

Na fara magana cikin muryan mai kamada Wanda ba nawa ba(kai Hausa akwai wuya fa๐Ÿ˜ฉ) ina Nuna Masu key
"Nasan da wannan kuka dogara,Toh kusha kurumin Ku dantsalle yarigada ya dakko mn, in mun fita sai nan da kwanaki uku zamu dawo!, Ku gode ma Allah akwai Fridge mai dauke da kayan marmari da talabijin mai dauke kewa" ina kaiwa nan na dara naja hannun Abdool mukayi waje, na kulle kofar da makulli ta baya. Muna fitowa naga Yan Aiki dan gulma harda mai-Gadi Sunyi cirko-cirko a bakin kofa Kowanne da son jin kwakkwafin sa...

Tsawa na Daka Masu "kunzo kun manne jikin kofar mutane lafiya?,"

Simi-Simi suka juya zasu wuce nace "a cikin ku Duk Wanda ya bude kofar nan ko bana nan, Sai na yanka shi nabawa Su talbudulmusuyanu Sunyi layya da namanshi," suka Gara tsurewa hanjin cikinsu ya kada
Direct part din Umma na nufa, Dakin da yake mallaki na na shiga na yi wanka na dauro Alwala na gabatar da Sallan la'asar , Shima Abdool sallar yayi bayan duk mun idar ya dubeni yace "Anty munayfa ce?"

Harga tambayar tasa ta ban dariya nayi murmushi"to da wacece"

Rungume ni yayi cikin farinciki"Wlh na dauka aljannun gaske gareki ne!,I love You So much Anty naaH"

"I love you too my stubborn Kani, yanzu dai jeka kwaso kayanka Yanzunnan mu wuce Zaria tare"

"I thought anan Zaki kwana?" Ya fada yana dubana

"No ina da wani deal da wani lecturer, kuma inada lecturn safe"

Tashi Abdool yayi ya hado kayansa muka bargidan, kaman yanda nazo 20 min motar ta kaini zaria

********

Tun bayan lokacin da na Warce Awaran Umma ta shiga tunanin kalamai na tana tufka da warwara daga karshe ta Sami bakin zaren, Daidai lokacin da yaa Aryaan ke sakkowa daga matakalar bene "Aaryan Wato Yarinyar nan zamanta a part dinnan bai kamata ba, kamata yayi a Gyara wanchan part din su koma itada Hafsah ko ya ka gani"

Aryyan ya Dan Sosa qeya aransa yana fadin _dama ke kika koma chan da nafi Sakewa da matata_ , A zahiri kam cewa yayi "Hakane Umma Amma harda ke Zaki koma ko?"

Baki ta riqe tana fadin "In koma ina, ai kasan ban iya nesa dakai ba,bazan iya barinka kai kadai da wata bare ba!,Ai bazai yiwu ba, yanzu dai kaje ka kira masu gyara su fara Aiki kafin Gobe su koma chan din"

"Umma Tun yanzu?"
"Eh ko bazaka bane" Dakinsa ya nufa, sai da yayi wanka ya sauya kaya sannan kai tsaye ya nufi inda yake parka motarsa yaga wayam, mamaki ya kama Sa yasan tunda Driver ya parka motar , Bai sake Aikan kowa ba Amma Dan ya kauda kokwanto ya kira Driver ya tambayeshi ko ya sake fita da motar ne Amma cewa yayi har makullin motar ma duk ya bashi

Ya kuma tambayan Malam Ali mai Gadi shima cewa yayi babu Wanda ya fita da motar , Wurin Driver ya koma yace ya bashi makullin dayan Motar wacce take ta hafsah ce Sbd bata iya hawa ba yasa Aka jingineshi anan duk yayi kura ....
Shi ya hau ya Shiga Gari yana Neman motar sa a cewan sa ko barayi ne suka Shammace su suka Sace motar, har Mangariba bai ga mai kamar motar ba, hakan yasa ya Koma masallaci Dan Gabatar da sallah

A lokacin da na isa Gida kuwa har A lokacin Hafsah bacci takeyi, Gidan Tsit kaman babu kowa Dakin Umma na shiga Dan Dauko Remote dinTVn Dakin mu da na manta anan jiya...

Ga mamaki na sai ganinta nayi da wata bakuwa duk sun Saki baki Suna Bacci ga Robar Awara da doya a gaban Su nan na gane Ashe Sleeping pills Akasa cikin Awaran Allah ma yaso ni da ban ci ba da yau bazan Samu damar Garewa da Yan iskan mutanennan ba

Na dau Remote nayi Waje ina cewa "Yau su yaa Aary zaa chaskale fa๐Ÿคช"

Ina Shiga daki na tarda har Hafsah ta tashi Sai faman surutu suke zubawa Nace "Kin tashi?"
Tace "Eh , Wa ya kawo Abdul-Rahman?"

Nace"Nice nan, kiyi sallah muje Dakin Aunty Ramla muyi hira Umma tayi barci"

Tana idar da sallah ta ja hannun Abdool mukayi Sashen Su Ramla, A kitchen muka tarar da ita , Abdool na ganinta ya ruga ya rungumeta yana fadin Matar Uncle dama Gidanku daya da Aunty Maesh?

Shafa kanshi tayi tace "Eh yarona waya kawo ka?"


Mamaki ya kamani Baki bude nake kallon su Dan a iya Sani na Abdool bai ta6a ganin Ramla ba, kasa haquri nayi nace "Aunty dama kinsanshi ne?"

Tace "Eh lokacin da nake NYSC dina school dinsu Aka tura ni, kuma koda dad dina ya hadani da yayanki Sun ta6a zuwa tadi Gurina tare "

Na rufe baki cikin dariya nace
"Kai aunty wai tadi ko kunya?






















TOHFAH


WAI CIKIN INNA RABI, SUWAIBA ZAINAB DA UMAR WA YAFI JINJIKI NE?


INA JIRAN RAAYOYINKU AKAN WANNAN CHAPTERN....



DON'T FORGET TO
VOTE
SHARE
AND
COMMENTโค

Wattpad @Fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ






Thanks for Reading

See you tomorrow๐Ÿ’ƒ
Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ



19th AuguthAug


๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
**HAWAN-JINI NA*
~{uwar mijina* ๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._


Afwan Readers,Na na Sauyin Sunan littafin da kuka Gani daga uwar mijina zuwa hawan jini naa๐Ÿ’”, Hakan ya faru ne Sbd wani sa6ani da Aka Samu, so don't be confused Duk dayane๐Ÿ˜๐Ÿ˜....

Follow me on wattpad @Fahnaan

Follow this links for my WhatsApp Groups
https://chat.whatsapp.com/D0SYu5RSmLUFREhHLaeucU (Maesherh novel)

https://chat.whatsapp.com/EPVrcHSiQNC6h8CuVGukhW (Fahnaan novel)




Salma jabeer, Amina, ZeeShaf,
Jidda Dillaliya, da A w a members this page dey for u๐Ÿ˜

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 8_*

"Au na manta fa, Ashe da qanwar hubby nake zancen" Ta fada tana Rufe Fuska da tafukan hannayen ta

Gabaki dayan mu mukai dariya, haka muka cigaba da hira cikin raha har lokacin fa Yaa Aary ya dawo.

Yayi mamakin Ganin motarsa Parke Gefe guda inda driver ya parka dazun, kuma babu Alaman An ta6a shi, Ya nufi wurin Maigadi yana tambayanshi waya dawo da motar Aikam nan ya shiga Rantsuwa "Wlh Tunda ka fita babu Wanda na kara bude Wa gate,Na rantse, ka yarda dani ranka shi Dade, Kila Aljannu sun Ara ne , kai Amma lamarinnan da ban mamaki yake"

Baice komai ba ya shiga ciki kanshi ya daure yana tambayn kanshi ~Wai Aljannu na tuqa mota ne?~(toh Gareku Readers)๐Ÿ˜‚

Tun a falo yake jin hayaniya ta side dinsu Mamaki ya kamashi ya San Dai Ramla ba zata ta6a kawo baqi cikin Gidannan da daddare ba!,Shi ya ma manta basu kadai bane a gidan.

Abakin kofa ya tsaya yayi folding Arms dinsa bisa kirjinsa yana kallon mu sai faman Washe Haqora mukeyi cikin nishadi ,zai iya rantsewa tunda yake bai ta6a ganin dariyana cikin nishadi ba , ya saba Ganin dariyana cikin mugunta๐Ÿคช

Abdool ne ya fara Ankarewa dashi, Yaga ya kurawa wuri daya ido tracing inda yake kallo yayi "Laah Aunty ,ji yanda Yaa Aaryan ke kallonki kaman bai ta6a ganinki ba" ya fada yana dariya

A Dan Razane duk muka dago muna kallonshi, Dan bamuyi zaton dawowanshi a wannan lokacin ba.

Shikam waskewa yayi yana kauda kai gefe tare da ta6e baki, A ransa kuwa mamaki yake waye kawo Abdool Gidannan?, A iya Saninsa babu mai kawo shi gidan nan Duba da yanda Yan gidan basu kaunar Yan Dakin mu, toh tabbas munayferh ce ta dakko shi, kenan nice na dau motarsa kenan?,

Ji yayi An Ratsa ta gefen sa An wuce, Hafsah da Abdool ne suka Ratsashi Suka wuce, nima ina Gabda isowa Wurin kofar naji an Fizgo hannu na.
Zaro ido nayi cikin tsoro, Ganin Fuskar shi A murtuke ya lokaci Guda ya Rikide mun ya koma Asalin Aaryan dinda nasani a da

Ya karasa Shigowa Dakin yasa kafa ya Rufe kofar,Da dayan hannun ya Ciro makulli daga Aljihun wandonShi ya kulle kofar.

Ido na zaro "Wayyo ni yau Na shiga uku, Me nayi maka?,Aunty Ramlah kin ganshi ko?"

Ramlah kam Raku6ewa tayi, itama tsoro ya kamata Dan bata ta6a ganinshi cikin fushi irin na yau ba.

Tsawa ya Daka min "keep Ur dirty mouthShut Johr, First, ina makullin motana?"

Ido na zaro cikin in ina nace"Yaa wlh banga makullin motar ka ba, Wai tukunna ma wani motar kake nuf...." Ai ban Gama Rufe baki ba naji An dauke ni da wani malalacin Mari,Wanda yayi Sanadiyyan daukewan Gani na na Tsawon Wasu Yan seconds..

"Wato bazaki fito dashi ba kou?"

Nan danan Hawaye Suka Wanke min fuska "Ni wallahi ban ma San kalar Makullin motar ka ba, kuma Allah ya isa Marina da kayi, Mugu Azzalumi mai siffar mahaukata, kuma Allah sai yayi mana hisabi Ranar gobe qiyamah ...."

Maganganu na Sunyi matuqar tunzurashi , Ya ture ni na fadi kasa ya shiga Ball dani Still Bakina bai mutu ba Ina Ta Aika mishi tsinuwa da Allah ya isa Ganin ina Neman wahalar yasa yazare belt dn wandonshi ya Shiga Mazgarta

Ramlah kam banda kuka babu Abinda take, gani take kaman idan tazo Rabon Fadan hadawa daita zaiyi,

Ihu na ya Gauraye Gidan Gaba daya Harta Umma dake bacci Sai da ta Dan mirgina Ba Dan pills din mai karfi bane da Ta farka๐Ÿคญ, Su hafsah kam Sun jima da Hallartar kofar, Sai kuka Sukeyi Dan ji suke kaman kasheni kawai zaiyi Ayau dinnan.


Ramlah tayi karfin Halin tunkarar inda muke da niyyar Rabon fada itama ta Sami Rabon mari๐Ÿ˜†(Allah shi Qara, Wa ya gayyato ki)

Sai da baki na ya mutu murus sai numfashi nake fitarwa daqyarยฒ, sannan ya kyale ni, Ya bude kofa ya wurgani waje kaman kayan wanki, ko kallonSu Hafsah baiyi ba ya Garkamo kofa

Ya taka Inda Ramla ke Tsugunne ya dago fuskarta da ya jiqe Shar kab da hawaye, ya shiga Share mata "Sorry Ramlahteey ,Nine ko?," ya Rungume ta " in ina Fushi banaso Ana Tunkaroni,cus I can't control my Self, Yarinyar nan ta raina ni da yawa, Haka jiya take fadawa Hilal Wai ni nake da mental disorder..., please Forgive me wify"

Tsakanin mata da miji..nan danan ta yafe masa Tare da bashi Shawara akan Yanda zai dinga kiyaye Shiga Fushi irin wannan.......Nan fa Abu ya fara chanza salo๐Ÿคช , Suna tsaka da wktqxzdfg NEPA Suka dauke wuta .

A Daidai lokacin kuma Umma ta Tashi tana fadin Subuhanallahi , Ganin duhu Gashi batajin motsin kowa nan fa Su Umma aka Shiga karanto Adduoi (Duk a zatonta mutuwa tayi Kabarinta ke da duhu"
Tadan Tsagaita da Addo'inta jin nishi na tashi a Dakin dake kusa da nata( Dakin Ramlah),

Na Shiga uku๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

Ai batasan lokacin da ta diro ba tana laluben wayanta , cikin Saa kuwa aka kunna converter haske ya gauraye dakin

Ta fito tana gyara daurin zaninta da ya fara Kwancewa, ta nufi Dakin Gadanยฒ, Babu ko Sallama bare knocking ta tura kofar.

Abinda ta gani yasa ya dafa kai ta saki ihu

A tsorace duk suka dawo hayyacinsu Ramlah taja bargo ta Rufa jikinta babu inda baya Rawa,

Shikam bedsheet dinda Ya zamo kasa ya Ya raruma ya daura yy kaman hijab .

"Haba mum, ya Zaki Shigo mana daki babu ko Sallama" yayi magana cikin Fitar hayyaci Dan shi gaba daya ya manta da Wa yike magana.

Umma ta riqe haba "Sallama?,inyi sallamafa kace?,Har sai nayi Sallama kafin na shigo Dakin da na?" Sai ta shiga matsar kwalla "Ai Nasan bayin kanka bane Dan da na bahaka yake da ba" yana Direwa tafi ce tana Sharar hawaye

"Umma please help, Aunty is bleeding" muryan Abdool taji cikin kuka yana fadin haka,har taso ta Share shi ,Sai ta nufi Dakin ,Ganin munayferh kwance kafar Hafsah jini na fita ta baki ta Hanci yasata zaro ido, ta koma da baya, Ganin Aaryan tayi yana sakkowa daga Matakala "Arry zoka taimaki Yar mutane kar ta mutu ace a Gidan ka ta mutu" bai San inda zancen nata ya nufa ba, sai Binta yake Abaya Ganin munayferh cikin jini yasa ya tuna da Aikin da yayi mata.

A kan Table Yaga makullin motarsa ya dauka Aka fito dani rangaยฒ Shida Hafsah da Abdool , anbar Umma da tsron gida..

A Asibiti kam Gado Suka bani Tare da bani taimakon gaggawa, na karin jini,Dan nayi Asarar jini Sosai





WasheGari

Ringing din wayana yasa na bude idanu na ahankali ina kallon inda Nike babu kowa A dakin , Sai Asannan ne na tuna Abubuwan da ya faru dani a daren jiya,cije lips dina nayi Daidai lokacin da wayata ta qara ringing,

Hannu Nasa na jawoshi, a bedSide dina Muryan janaan naji tana cewa "Nayferh,Akwai matsala fah, Yanzu muka fito lecture din KS ,wlh babu Sunanki A class list,Daman Attendance zan rubuta muku "
Bance komai ba sai Sniffing dinda nayi tace"Are okay "
Nace not Really, but Wait for me, I will be on my way Right now" ina gama fadin haka na katse wayan ,nasan zatayi mamakin yanda ta ji muryana wani iri but ya na iya?"

Sakkowa da qyar nayi na shiga bayin Dakin na dauro Alwala, hijabin hafsah na hango saman Drawer na dauka na sa ina yatsine fuska ,Dan yanda nakejin jikina kaman bani ba.

Ina idarwa idanuna suka Haska min makullin motan yaa Aary saman Desk, Ai da sauri na dauka ina rintse idanu tareda ciza lips, Bayi na shiga na kunna tap in case in sun Shigo su dauka ina toilet ne๐Ÿคช


A harabar Asibitin naga motar yaa Arry a Parke, na saki murmushin mugunta cikin Karfin hali...........



Driving nakeyi kaman Anmin dole ina yatsine fuska, sai fama ciwon hannu na nakeyi Na fashe na kuka mai cin rai babu mai Rarrashina๐Ÿ˜ข


Ina isa ABU Zaria na parka a bakin Gate na kira Janaan nace ta fito gate, bata wani Jima ba sai gata, nace ta shiga ta ja motar ta kaini office din HOD.


Baki janaan ta bude tana mamakin yanda na koma tsakanin jiya da yau "keko Nayfer kinyi Accident Shine ko ki Gaya mana?"

Harararta nayi "Abege jaa mana mota,"

Shuru tayi batare da ta kara cewa komai ba taja mota muka shiga School,

Daidai office din HOD ta parka ta Shiga bata Dade ba sai GaninSu nayi sun fito a tare

Subuhanallahi munayferh me ya sameki?,kinyi Accident ne? HOD ya tambayeni cikin Rawar murya


Kuka na fashe dashi "Ba KS daud bane, jiya bayan mungama lectures Ya kirani office dinshi" ina kaiwanan nayi Shuru kuka yafi karfi na.....






AMMA WAGGA YARINYA AKWAI TAURINKAI DA SHU'UMANCI


Kumin comments ko na tafi Yajin Aiki







Wattpad @Fahnaan

21thAug

๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

*kai kai kai gaskiya na fuskanci mutane ma sunfi son Munayferh Akaina , zan fa koma 'yar adawarta dan na fuskanci hmmmm bari dai kawai nayi shuru,Comments Dinku Na saani Farinciki I โค๏ธ u All*


~Sarah, Zainab Ali,Mum Ameerah, Hafsah Tukur and Da duk Fahnaan Novel member Wannan page din naku ne๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜~

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky

Please Login or Register in order to submit comment