Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wifey ,Me zanyi da Shaidaniyar yarinyar nan?,Matar qaninah ce fah...haba har kin Goge mn hadda....Please Stop Crying karki sa ma kanki wani Ciwon....Uknow Bai dace ace Junayd yana Riqe hannun Matarda zai Aura ba cus za'a iya samun matsala hakan kuma ba Daidai bn,Kuma wlh ba janye hankalina tayi daga Mum ba,Kawai kallon mamaki nake mata yanda take tafka Tsiyarta Cikinku babu Mai tsawatar mata...hakan yasa na tafi da ita don Hukunta ta..................." Haka ya Cigaba da Rarrashinta Cikin Tausasan kalamai da Dadin baki.

Yasha Wahala kafin ya Shawo kanta ta Amince dashi,bason ta yakeyi ba

~(๐Ÿคค)tsakanin mata da miji~.

WasheGari

Aka kawo Akwati Set uku Maqil da Kaya,na Gani na fada,biyu Nawa,Daya na janaan, Dama tuni an kawo na Aunty zee.


Koda Aaryaan Yaga Lefen Cewa yayi na Amaryar Junayd sunyi yawa hakan Ai asarar kudine.

Umma kuwa A fili ta Rinqa Sakin Zance Tana Nuna baqin cikinta Qarara akan Auren, kuma A dole ita danta bazai Auri Fasiqah ba....


InnaRabi Ma danne nata Baqin Cikin tayi Don Kayan da aka hadowa Munayferh ya ninnninka na Diyarta....


~Oho Yan Baqin Ciki saidai Suyitayi na gaba yayi Gaba๐Ÿ’ƒ~

Ni kuwa ban Ma san irin Wainar da Ake Toyawa ba,Inanan Chan a Daka,

Takaicin BaqinCikin DA yaaAary ya Kunsa mn ya hanani saqat, Sai a yanzu na Tabbatar da Tsanar da yake mn ba na wasa bane.

BayaGa tsana Bai dauke ni da wani Muhimmanci ba,Ya za'ayi ace Duk hadewana da Iya daukan kaina na qare a 3k, Banda haka ko Cikinsa da nake dauke dashi ya Ci ace ya Mutumtani,ya kuma darajani ...... Meye 3k danAllah Sai kace Na roqa ko ya bani sadaqa?,Ai wannan Wulaqanci ne da Rashin Daraja Dan Adam

(au dama kin sani๐Ÿค”๐Ÿคจ)


Saida yamma liqis kafin a kawo Lefen sashen mu,Ban Fitoba bare su sa ran Zan duba.


WasheGari Akaje Jere a Gidan Aaryaan na Badarawa ,Dukda Sabon gida ne Saida aka kuma Gyarawa aka Chanza mshi Fasali.


Katon Gidane Sosai mai daukeda Shuke Shuke Masu daukan Hankali ,Tun daga Balcony Zaki Gane kudi ya zauna A wajen yana Dauke da Parts har Biyu,Masu dauke da Dogon Bini Alamar Akwai bene ta ciki,Fasalin Ginin Iri daya ne.

Bangare daya aka kai kayan Janaan dayan kuma aka jera kayan Munayferh a sama ,Sannan na Ramlah a qasa.


Duk Bidirin da Akeyi a Gidansa,Bai Sani ba,Dan Sosai training dinda yakeyi ya dauke hankalinsa, Kuma haryanzu banda Hilal babu Wanda yasan Yanayi.....


Yau Saura Sati daya biki,Gabadaya Fargaba da damuwa sun hanani Saqat,bana fita ko'ina Kullum ina Kulle a daki.


Ko Ammie ta Fahimce Wani Irin sanyi da natsuwan da 'yarta ta kara.


Duk ta dauka Sanadin Auren da za'ayi mata ne,Shiyasa take tasata Gaba kullum da Nasiha,da Rarrashi...


Kaman Kullum ina zaune a daki Hafsah ta Shigo ta Gaya mn Wai na Fito Za'a kai mu Saloon, da tho na Amsa Mata, Sannan na Dauko wayana na lalubo numbern Mijin titi na Tura mishi Short message kaman haka.


Zanje Gyaran Gashi๐Ÿ’ฌ


Aiko Kaman jira yake ya Maida mn Da martani a takaice shima kaman yanda na Tura mshi.


Ban Amince ba๐Ÿ’ฌ

Ina Gama karantawa Na shige Bedroom na Kulle kofa na Fada Gado ina kuka mai Tsuma Rai,Wanda Da Ana sabawa da kuka da tuni mun zama 'Yan Uwa.


Shikuwa Aaryaan ba komai yasa ya hanata zuwa ba,sbd yasan don Junayd za'ayi.


Ramlah kuwa an dan Sami 'yancin kai yanzu ba da ita Umma keyi ba,Burinta bai wuce tasan Yanda Zata hana Yiwuwar Auren Junayd da Munayferh.


****
Ramlah ce zaune da Qawayenta Rucky da yaseerah.


Yaseerah ta dubeta Tace "Wai Ramlah,Ina wannan fitinanniyar Uwar mijin naki ne?....Ban ganta ba tunda Muka shigo"

Rucky ta Dan dara tace "Hegiya ba da haqoranta a wage kaman Garma....har na tuna Ranar da tayi mana korar kare,Dan cincin Din amaryarnan da Muka zo ci tayi mana Buqulu akanshi."

Ramlah Takai mata Duka Cikin wasa "'Yar Air ,Uwarmijinnawa ce mai Haqora a wage?"


Yaseerah tace "tama fi hakan, ni Gani nayi kaman baki damuwa da wulaqancin da takeyi mki?"

Ramlah ta ta6e baki cikin Halin ko'in kula tace "Toh damuwan me zanyi,Ni wlh jinta nake kaman Uwata wacce ta haifeni ni kaina Mamakin Hakan nakeyi...yanda nake Binta sau da qafa ko Mamy Albarka dan ko kafin nayi Aure ba komai Take Sani nayi ba,Kuma duk Abinda tamin indai Banji dadi ba nakan iya Fuskantarta na Gaya mata......"










GEHN๐Ÿ˜Ž



Ah no Fit talk for this matter.




Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ




25th Septe[30/09 1:08 pm] Fahnaan๐Ÿ’–: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 40_*


Sai Gani nayi ya durqusa a Gabana, ya hada hannayen Sa biyu Bakinsa na Rawa, kaman mai son yi magana Amma ya kasa cewa komai..



Kallon mamaki na tsaya ina yi Mishi,I can't believe yau YaaAary ne durqushe a gabana Cikin qasQantar dakai


A hankali naga Fuskansa ya fara Sauya yanayi daga Fuskar Tausayi Ya fara Hadewa kaman Hadari


Tsoro ya qara kamani, Anya babu wata a qasa kua?, Kodai hanyar Hukunta Ni Yake nema cikin sauqi, Don dazunnan na Gama zaginshi ta text message, yaqi mn Reply, Tunowa nayi da Baqaqen magananun da na yarfa Mishi dazu yasa na juya da niyyar in Gudu
.


Shikuwa dukqusawan da yayi sai yaji zuciyarsa na La'antarsa ~Meyasa zai zubar da Girman Sa Ajinsa ,Da izzar sa A Gaban yarinyar nan? ,Akan Abinda Zai iya tilastata tayi Kuma dole tayi~ ,Shiyasa ya kasa magana yana tunanin yanda Zai tilasta mn in Gayawa Abba Ina son Sa, Tunowa yayi da Abinda nafi tsoro,


A lokacin yaga ina Yunqurin Guduwa, Miqewa yayi Cikin zafin nama ya Damqi hannuna, na dawo da baya Na fada 'kirjinsa.


Hafsah da Fadeelah dake la6e suka Rufe baki Cikin mamaki Suka zaro ido.


Hafsah Taja Hannun Fadeelah tace "Please Mu bar nan, Wanda muka Gani ma ya'isa"


Fadeelah tace "Aradu babu inda zani sainaga iya Gudun Ruwansu"

Hafsah bata saurareta ba Taja hannunta Sukayi gaba.


Fizge Fizge na farayi ina kokarin qwatar kaina amma na kasa,Tun ina Yunqurin qwace kaina Har na koma nayi luf a kirjinsa.

Tuni Hular dake kaina yayi gabas, Sai a yanzu yaga Kitson da Aka mn, Wani irin 'daci Wanda baisan na Meye ba, Ya turnuqeshi , shi Koma mai zai faru Saidai ya faru bazai ta6a sakin Munayferh ba, idan kuma Aka nemi a tilastashi zai dauketa ne ya Gudu da ita kawai Kowa ma ya huta.

A sanyaye ya Raba jikina da nashi, Ina Ganin ya Cikani na qwala ihu da iya qarfi na, Wanda ya Jawo Hankalin UMMA, Abba, Fadeelah, Da Hafsah dake zaune a General Parlor.


Abba ya dubesu Yace "kaman ihun Munayferh nake ji?"

"Eh, bari naje Na dubata, Suna tarene da Yaa Aaryaan, Fadeelah zoki Rakani" Hafsah ta fada tareda Miqewa.


"Dawo ki zauna, babu Ruwanki dasu" inji Abba.


Dawowa Sukayi Suka zauna, Fadeelah tace "Abba Amma fa Su kadai muka bari a Room dn"


Miqewa UMMA tayi tana cewa "kamarya Su Biyu aka bari a daki ? babu ko dadinji, Kunga bari na dubosu"


Gabaki daya suka bita da kallo, Har ta fara takawa sai ta Tuna Abinda ta Gani Ranar nan(Ranar da aka bi Shawarar janaan๐Ÿ˜…)


Chak taja ta tsaya ta kasa qarawa Wa Abba yace "kin fasa Zuwa ne?"

Qaran Sautin Ihuna da ta kumaji ya qara bata Qwarin Qyiwan tunkarar hanyar a cewarta ~Wannan qarar bata lafiya bane~.

Shi kuwa ganin tana Shirin Tara masa jama'a yasa ya Damqi dukkan hannayenta biyu ya Hada ya Riqesu a hannu 'daya tana Tittirjewa Amma ba Qaramin Riqo yayi mata ba .


Dayan hannun kuma Ya Tallafo Fuskarta Ya kalle Cikin qwayan idanunta Yana Girgiza mata kai Alamar tayi shuru tareda zare mata idoanu , Wai saboda taji tsoron Shi tayi Shurun, Amma kaman Cewa yayi ta qara Volume dn ihun nata tana Yunqurin kwace Riqon da yayi mata.


Cikin Rudewar da ihun nata ya haddasa masa baisan lokacin da ya saki hannayenta ba, ya tallafo kugunta, ya hade bakinsu Waje 'daya,ya sake Mannata jikinshi.


Tuni Jikinta ya Fara Rawa , Dukda ba yau ya fara kissing dnta ba ,sai Taji na yau yy daban ,Tsoron da takeji a baya ya'dan Ragu, hakan ya dirar mata da Mutuwan Jiki.


Shima 6angaren nasa Kusan haka ne, Amma da wani Salo Na Mugunta Yake mata, A Dole sai ya Sa Tsorata ta ta yanda zaiyi Amfani da tsoron wajen tursasata Ta Gayawa Abba tana sonshi.

Umma na Zuwa ta iske Qofar dakin a bude, hakan yasa ta kutsa kai Ciki batareda Tayi ko sallama ba๐Ÿ˜.

Abinda ta Gani yasa ta Saki salati da qarfi.

Wanda yasa shi Saurin Janye bakinshi, batareda ya Shirya Ba, ya duqar dakai tareda Sosa qeya ,Da yk shike facing kofar, Munayferh kuma ta juyawa kofar baya.


Itama a 'Dan tsorace ta juya ta kalle Umma Wacce tayi mutuwan tsaye , ta 6alla mata harara harda Murguda baki,Tunowa tayi da yanda Umma Ke zaqalqalewa akan Sai an Raba Auren su.

( ~Shaidaniyar mata~)

Ta furta a zuciyarta


Sannan ta juya ta kalle Aaryaan Wanda kansa Ke Sunkuye kaman Munafiqee , ta Dora hannayenta Bisa qirjinsa tana masa tafiyan Tsutsa Cikin wani irin salonda ita kanta bata San tanayi ba.


Cikin Mamaki da Al'ajabin Yarinyar yasa Hannu Zai Cire nata hannun.


Babu Zato ko tsammani ta fada jikinsa ta qanqameshi Cikin Kissa da Salo Wanda batasan tayi ba ta fara mgn

"Haba Baby, Why're u so traumatized?,....What're u scared Of?....Let's Continue Enjoying our selves....."


A zahiri Maganar takeyi Cikin natsuwa, Amma karkaso ka tona yanda Zuciyar ta Ke Bugawa Dan tsananin Tsoro, da zaka Qureta da kalloma zakiga jikinta har Wani rawa yakeyi..

Tadaiji Umma na wasu maganganu Amma bazata ta6a cewa ga Abinda take fadi ba, kafin Taji Gehm.... Anyi banging kofar.


Da sauri ta Cire hannunta dake kirjinsa Taja da baya Ganin ya Turmuqe Fuska ya wani hada Rai, ya koma Sak Aaryaan dnshi .


Tsoro ya kamata Ganin yanda idanun nan Suka Sauya kala Zuwa ja,


Bakina Rawa ta furta

"Don ....Allah Kayi.... haquri"


Baiyi zaton zata bashi haquri ba ,Hakan yasa Ya qara hade Rai.


"Who the Hell is ur baby? kin Rainani Ko!" Ya fada Cikin murya mai nuna Alamun fusata.

Bata bashi Amsa ba, hakan yasa ya Cigaba da cewa.


"Don kinji na Furta miki ina sonki Shiyasa kika Samu Qwarin Qyiwan kirana Baby ahbi?......irin ga Perfect lover dinnan.. Da Kinsan yanda na tsaneki ne Bazaki ta6a kirana da baby ba, Mummuna Kawai" ya qarashe maganar yana Jan kunnenta.


Ta saki wata'yar siririyar Qara ta qara Furta "Don Allah Kayi haquri" a karo na biyu, Cikin Tsoro.


"Abu 'daya Zaki mn na Yafe mki,....idan kuma Kikayi taurin kai, We'll enjoy Our selves As u said "


Zaro ido tayi Cikin Firgici, jikinta ya soma kyarma, kafarta Har Wani Rawa ya farayi.


"Ina son Yanda kika ga nayi miki dazun, Nace ina sonki ki Gaya duk Abinda na Fada miki a Gaban Abba Sannan ki Qara da ~You Cannot live without me~ daga qarshe sai ki Roqeni akan kar na sakeki"


Wani Irin kallo na watsa mai na Juyar dakai Gefe

"Bazan iya ba Gaskiya"


"Then let's Enjoy" ya fada yana takowa inda nake.


Waro idanu nayi Cikin tsoro naja da baya


"Please Stop!, Na Amince zan gada"


Yayi dariyan Mugunta yana Shafa Gemunsa.

"Better"


"Amma kasan hakan Zalinci ne ko?, kuma Allah ya hana zalunci" Na fada kaman zanyi kuka.


"Oohh Da Gaske a wane Aya ko hadisi"


"Akwai Cikin Al'qur'ani da Hadisai dayawa...Cikin Suratu Ibrahim Ayata Arbain da Biyu Allah (SWT) yana cewa ูˆู„ุง ุชุฎุณุจู† ุงู„ู„ู‡ ุบูู„ุง ุนู…ุง ูŠุนู…ู„ ุงู„ุธู„ู…ูˆู† ุฅู†ู…ุง ูŠุคุฎุฑู‡ู… ู„ูŠูˆู… ุชุดุฎุต ููŠู‡ ุงู„ุงุจุตุฑ(Kada kuyi zaton Allah mai shagala ne ga Abinda Azzalumai suke Aikatawa, Yana jinkirta musu ne zuwa ga wani Guri Wanda idanu Suke Fita Turu - Turu Cikin sa) Wlh YaaAary ina jiye maka Ranarda Allah zai kamaka Akan zaluncin da Kakeyi".

Kabbara yayi daura da cewa "MashaAllah ,Alhamdulillah Su Baby Anji Aya a radio...." Alarm dn Agogon Hannunsa ya katse shi batareda ya qarasa Maganar ba yaja hannunta Sukayi Hanyar Fita yana Cewa "Lokaci yayi Muje ki Gayawa Abba "


Gaba daya Aaryaan ya manta Ba'ayiwa Munayferh dole, idan kuma an tursasata Za'aga Shirme.


A General parlor ya tsaya ,Umma d Abba kadai ne a parlorn,

Ya Gaidasu duka ni kuwa Abba kawai na Gayas.


Umma kuwa Qurenu da kallo tayi ji take kaman ta kamani da Duka, Ganin yanda na Fito, kaina babu ko dankwali.

Ta ta6e baki Hadi da Jan tsaki , Abba ya dube Ta yace lfy? ,bata Amsa mshi ba.

Abba yace "Me kajeyi a dakinSu ,Ba na Hanaka Zuwa inda take ba?"


"Kayi Haquri Abba naje kar6o Abu ne"


Umma ta mere baki tace "Kar6o wani Abu indeed"

Abba ya kalle Aaryaan yace "Ina Alqawarin Mu"

Aaryaan ya gyara zama ya Fiddo Takardar Da janaan ta Rubuta as Result dn Ciki ya miqa mishi, ya kar6a yana'yan dube-dube Kafin ya dago ya qare mana kallo gaba daya yace.


"Wannan ai Gwajin daga Asibitin ka ya Fito , Anya ba kai kasa Aka Rubuta ba, don Cinma naka Manufan?"


"Aah Abba bani Nan Akayi Lokacin da Aka Yi Gwajin Ba mah"


"Okay ina Takardar ta?"

"Abba ta ce tana so na Kuma bata son A raba Auren"


Tsaki Umma taja ta miqe ta bar Wajen duk mka bita da kallo, abba ya maida kallonsa Gareni Yace


"Angel, Yayi miki Wata Magane ko".

Nace "Eh yace in Gaya maka yace yana Sona Kuma Nice Love Of his life ,Ya kuma Cewa na qara da Ehmm...." Na daga kai Alamar Tunani.

"Yawa Cewa yayi Sannan ki qarada YOU CANNOT LIVE WITHOUT ME"

Kallona yake yana Huci , yau da babu Abba anan DA ya 6a66alla qasussuwa na.


Abba yace "Ohh dama Abinda ka gaya mata kenan?, Toh yayi kyau tace bata sonka kuma bazan Mata dole ba....na Qara maka Two days Ana Gobe biki kafin Ranar Biki kasan Yanda zakayi naji Zance mai dadi Daga Gareka"


"Abba Kana Nufin dole in saketa ne?"


"Ah dunno, So nake naji Good news From you people ,Ehmmm....Kar ka manta Gobe da safe Nace Ku tattara kwarmatsanku dakai da First Wife dnka Ku bar mn Gida, nasa An gyara Gidanka na Barnawa Nan zaku koma.....,Zaku iya tafiya"


A Ranar Kusan a Zaune na kwana, yanda naga Safe haka naga rana Tunani nakeyi Yanda Aaryaan ya Kalleni ya Furta mn Wa'ennan kalmomin ya kuma Daurewa ya Zuba mn Rashin Mutunci.



Shima Kusan zan iya cewa Cikin qunci ya kwana don ji yake Kaman Abba ya takura shi dayawa, Shi da Matarsa a Rinqa tursasashi dole sai ya Taketa wannan ai Rashin Adalci ne.



****


WasheGari Tun da safe muka fara kar6ar baqoncin Manyan qawayen mu Wa'enda mukayi secondary sch tare da Wa'enda Mukayi Yarinta tare harda 'Yan ABU (course mates) dn mu ,Gida ya Cika da Jama'a , Nikuwa da kallo nake binsu Bansan Wanda ya gayyato su ba ,Kuma bansan Abinda Sukazo yiba, ban kuma Tambaye su ba dukda kuwa Mun taru Muna hira har Wasu na tsokana na Da Mrs Aaryaan, ban Fahimce suba, Na dauka Janaan ce ta Gaya msu Inada Aure Saboda Sa6anin da muka Samu dasu.


4:00pm dai dai , kaman hadin Baki , naga duk sun Sauya shiga zuwa Maroon Skooba Anyi msu ado da zanen milk , Dressing Codes dinsu iri daya haka kuma kallo daya zakayiwa kayan ka Fahimci Dinkin company ne. Ni kuma Su Fadeelah Suka tasani Gaba na Shirya cikin Gown milk da ratsin Maaroon a jikinshi Nana makeover tazo tamin kwalliyah, nayi Kyau Sosai ba qarya sai maqiyi.


Da dan tazara tsakanin Gidan mu da Gidan Su janaan Saida aka Sani a mota sannan muka tafi, Wai Ashe duk wannan Shirmen Bridal Shower za'ayi๐Ÿ˜†.


Itama tana Sanye Cikin shiga Irin nawa Amma Nafita kyau Sosai, Sai harara nake watsa mata,itama tana Maiyar mn da martani.

A harabar Gidan aka Gudanar da Taron Anci ansha An kuma Raqwashe Anyi wulaqanci da Naira har Ina Mamakin inda suka Samo kudin da Aka kashe dan ba qaramin kisa akayiwa kudiba.


Na Samu kyaututtuka da dama Daga Qawayen, kowacce saida ta Bani Kyau ta mai tsoka,


anan Nasan Gaskiyan Lamarin Wato Aaryaan zan aura, ita kuma janaan Junayd, Na Tabbatar da hakan ne a Dalilin IV dinda na Gani, kuma Yanda naji anata kirana Mrs Aaryaan Shiyasana Gasgata hakan.


Hankali na ya tashi matuqa, Amma ban Nuna ba Saida na bari aka Fara watsewa, Lokacin janaan ta shiga Daki dan Chanza kaya kawai na bita.......

















KIKa BITA ME ZAKI MATA?๐Ÿ˜





28sept๐Ÿ–‹๏ธ
[30/09 1:08 pm] Fahnaan๐Ÿ’–: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 39_*

"Ban Gane kar ace ka saketa ba?, Me hakan Ke nufi...Auren Wa Ake Tsoron Tsinkawa?....Eh?...kun mn shuru!"


Abba yayi Murmushin su ta manya yace "Wata magana 'danki yazo mn da ita Wai......." Nan ya kwashe komai ya Gaya mata.


Tun Kafin Abba ya dasa aya ta Fara Bala'i , wannan Ba Abu mai yiwuwa bane Auren titi sai kace a Shirin Film, itafa Bata Yarda ba kuma bata jin zata ta6a Yarda da Wannan Labarin.


Saida Abba ya tsawatar mata Kafin ta natsu Sannan ya nuna Mata Videon daurin Auren ,nima sai yanzu naga Videon, Amma Abin mamaki A videon Naga An daura Aure kan Sadaki Dubu Dari Biyu, Amma Ni dubu Uku ya bani, Me Yake nufi da haka???. ( ~ya rainani ne kawai~) inji zuciya ta.



UMMA kuwa Sauya Topic dn masifan nata tayi "Toh Alhaji tunda Abinda ya faru ya Riga ya Faru Kasa ya sake ta kawai Ni Banga Anfani Auren ba tunda Baya sonta itama Ba sonsa takeyi ba"


Abba ya kalleta na wasu 'yan lokuta kaman Mai nazari "Toh banqi taki Ba ,Amma Su Suka Gaya miki basu son Juna?"


"Abba Don Allah kace ya sakeni Bana sonshi
" na fada A raunane.


"Princess Meyasa bakison 'dana?" Ya tambaya yana kallona.


Saida na 'dago na dubi Aaryaan ,Shima Ni yke kallo, ya cika yayi Faam ,Na Galla mshi harara harda Murguda baki,


Sannan na kalle Abba Na gyara zama na fara Magana cikin natsuwa.

"Abba 'danka Mugu ne kuma Baisan darajar 'Dan Adam ba, Abba Wai sbd Rashin Imani irin na YaaAary ya Aureni batareda Amincewana ba Maimakon ya Lalla6ani Har na haqura na zauna dashi ,.....Auren ma bude mshi sabon shafin Muzguna mn yayi, Ya Wani hanani saqat!, Sadakin 3k ya bani mah, sbd Tsantsar Rashin Sanin darajar mutum!, ....Ai ko busasshen Fara zan Siya mai mutunci Zan Siya Na 5k a Banza Mah....."

Abba ya dakatardani Cikin danne dariyarsa yace "Dubu Uku ya bakine a matsayin Sadaki?"

"Ba Gashi Gabanka ba?, Qalya zan masa ne?"


Aaryaan yace "Dad ban Riga na bata sadakinta ba,Kawai kyautace Dubu Ukun da na bata!"


UMMA ta bude baki zatayi magana Abba ya dakatar da ita da cewa "tunda baka Riga ka biya sadakinta ba ,ta kwana Gidan Sauqi Maza ka Rubuta mn takardar ta"


UMMA ta murmusa Cikin jindadi tace"Kawai ba"


Aaryaan yadan Sosa qeya cikin JinKunya yace "Uhmm...Ehm....tana dauke da Juna Biyuna Fa"


"Raina mana Hankali zakayi?, Ji Yarinya shar babu Alamar wahala ko Laulayi a tattareda ita kace tanada Ciki.... Ciki fa kace Kana Cikin hayyacinka kuwa?" UMMA ta fada Cikin fusata .



Abba yace "kika Sani ko Cikin ne da ita?"


Aaryaan yace "Dagaske tana dauke da Juna Biyu Har na watanni Biyu, .....kuma inada Result na test dnda Akayi mata"


UMMA ta kura Mn ido cikin Tsakanin TashinHankali TanaSon Gane Gaskiyan Lamarin, Ni Kuwa Sunkuyar dakai nayi Saima naji Kunya ta kamani.


Abba yace "tho ina Result din Yake"

"Yana Dakina "

"Kaaii Alhaji wlh yarinyar nan bata dauke da Cikin Kowa Dubeta Fa" inji Umma Cikin Kokwanto.


"Ke ina Ruwanki dasu?...Tunda kinga taqi magana To babu shakka Da Akwai Cikin ne" ya fada yana Sake dubana.

Ni kuwa 'kara duqar dakai Nayi, Ina Boye Fuska da Gefen mayafina Cikin Matsanancin kunya.


Umma tace "Munafika,meya Kuma na Rufe Fuska bayan An Gama zuba...."

Bata Qarasaba Abba ya daka mata tsawa Cikin Fushi.

" ya Isa Haleemah, idan Bazakiyi Shuru ki saurari bayanina ba Zaki iya Fita, Dama ban Gayyaceki ba.....kai kuma Aaryaan Ina jiran Result dn Cikin,da Takardar Sakinta Gobe Iwar haka , Na baka Awanni Ashirin da Hudu, banason wani Wai-Wai ka tashi ka bani Guri"



Ai kaman Ni yace na Tashi, da sauri na Miqe Qafafuna Na Rawa na bar Dakin .


Ina komawa Na fada kan Gado na fashe da matsanancin Kuka, Wanda bansan dalilin Kukan ba.


Saida na ci kuka na nagode Wa Allah , sannan nayi Shuru dakaina .

Bacci ma Gagarana yayi, na koma tunane tunane ,Chan na jawo wayana na Kunna data na hau WhatsApp Saqonni Suka Fara shigowa kasancewar ya kwatakwata ban Hau online ba.


Abin Mamaki sai Ganin Messages nayi daga Mutane daban daban Suna tayani Murna hadi da Godiya,harda new numbers na Mutanen da tuni na manta dasu.


Cikeda mamaki na tambayi wata Qawarmu ta yarinta Wacce ta Turo mn da Message kaman haka


๐Ÿ’ฌHM in Addy.....Allah ya kaimu Yabada zaman lafiya.....kuma muna Godiya, Allah Qara budi da 'daukaka


Ni kuma na tura mata ๐Ÿ’ฌThanks.... but Ya Akayi kk Sani.


Ta turo mn๐Ÿ’ฌ Janaan da Hafsat Sun Aiko mana IV kuma sun kar6i measurement dnmu Wai ba sai mun Siya Anko ba,A company za'a dinka mana... Angonki ya bada kudin.

~Chai Wato yaaJunayd da Sabon Salon da yazo kenan?๐Ÿค”~

(Waya Gaya miki Junayd ne)๐Ÿ™„


Shi kuwa Aaryaan Bacci Gagaransa yayi, Ya rasa mai yasa ya kasa sakinta kuma ya tabbata ba sonta yakeyi ba, bare Yayi Tunanin Don kar wani ya Aureta yaqi sakinta....Dole ne yaje Zaria Don Neman Shawarar Hilaal... baya jin Gobe zai iya Zuwa Aiki, Zaria kawai zaije ya Nemi Shawarar Hilaal,..




WasheGari Tun da safe wata Sabuwar Number ta kirani Wai in zamo Cikin shiri Itace Wacce aka Kira zata mn kitso zasu zo tareda Mai Henna ,da tho na Amsa mata Don Ban fahimci inda Zancen nata ya dosa ba.


Karfe sha Biyun Rana sai Gasu sun zo, lalle aka fara mn sannan zuba mn qananun kitso zubin Lemonade, hafsah sai santin kitson takeyi ,ana Gama mn akayi Mata itama Amma ba Same style ba.


Ana kan na hafsah na sulale na bar Gidan Don bazai yiwu ace duk hadewan da nayi babu Wanda ya Gani ba, ina Fita na Ciro wayana na Turawa Mijin titi saqo kaman haka.


๐Ÿ’ฌZan shiga maqota.


๐Ÿ’ฌBan Amince ba" ya turo mn a takaice.


Saida na dara sosai Kafin na tura Mishi

๐Ÿ’ฌKai ka huta ,komai hanawa kakeyi, nidai na Fita Tun tuni....Don Allah idan ka dawo kar ka barni da rai Mugu Mummuna Mijin 3k (Mยณ)kawai๐Ÿ˜’.


(Daga Mijin titi Zuwa Mijin 3k๐Ÿ’”๐Ÿ˜ฎ)

Yana gama karantawa ya Girgiza Kai tareda Cije lips dinsa da qarfi cikin zafi. ~Mai hali dai baya ta6a barin halinsa~ ya fada a zahiri.


Hilaal dake kusa dashi yace "Me yafaru kuma?"

"That's none of ur business" ya bashi Amsa a fusace.


"OK ooh" hilaal ya fada yana dage kafada Alaman He don't care.

Aaryaan yace "Ehm... Hilaal nayi maka magana dazun bakace komai ba"


"Toh me zance?,Bakaga post dna na Instagram bane?"


"Na Gani mana Ba Wanda Kayi photoShop dn Photos namu bane?...so what next?, Meye Gamin Photos da zancen Mu?"

"What!....you mean!...." Sai yayi shuru ya dafa Goshi, Tunowa yayi a kwanakin baya Aaryaan ya gaya mshi Abba zai hadashi da janaan ,amma Yayi mamakin yanda Hotunansu ya gama karade ko'ina ,Ko wane TV and Radio stations Gayyan Bikin Akeyi, Meyasa Bai Sani ba tho, Abinda ya kasa Ganewa kenan.


"Yaushe Rabonka da kallon Television?" Inji hilaal


"Gaskiya na dade kasan baya Gabana, kuma An datse Connections na Gidan mu"


"Ohh no Wonder...... Yanzu dai Shawarar da zan baka itace kaje ka Gayawa Yarinyar kana sonta Shine kawai mafita"


"Amma Kai banza ne, Ni nace ma ina sonta?, ko so kake ta Raina Ni ?" Ya fada a Dan Fusace.


"To tunda baka sonta Sai ka sake ta mana"

"GaskiyaBazan iya ba,.... just tell me yanda zanyi Har na Samu Ta Gayawa Abba Tana so na, hakan kadai zaisa Ya daina maganar Saki"


Hilaal ya

Please Login or Register in order to submit comment