Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Asibiti ne?"


"Asibitin Uwar ka?, yace babu komai ka tafi ka bamu Wuri" Umma ta fada Cikin Tsawa Sosai


Tsawan ne ya kuma Hargitsani Na kwace da qarfi Tareda nufan hanyan Waje da Gudu kawai sai na ci karo da Janan na fada Jikinta Tareda Fashewa da Wani Irin kuka


"Jaanu Na kashesu Jaan Bindiga ,Bindiga jini!, jini!!, jini!!!, Wayyo jini Sun kashe Aunty Ramlahh"

Janaann ta Qara Rudewa tuni hawaye Suka fara Zirya saman kuncinta Ta Qara Qanqameni Cikin muryan kuka Tace "neryfee ki nutsu Basu kasheta ba!, Ga Aunty Ramlah chan A bayanki Tana kallon mu"



Qara Shigewa Jikinta Nayi Cikin kuka sosai nake Fadin "Ta mutu Wlh ta mutu Wayyo na kashesu"


Jikin kowa yayi Sanyi Harta Umma Dake tsaye Tana kallon yanda n Razana kmn ba ni nake Acting mai Aljanu ba dazun Hankali Kwance.

~Waya Sani ko Aljannun Gaske Gareta?~

Umma ta fada Cikin Ranta yayinda Ramlah tuni ta fara Share nata Hawayen Aaryaan da Junayd kuwa Kasa ta6uka komai sukayi Jikinsu a mce.

Ganin Yanda Na Wani Qanqame Janaan ne kaman naga Uwata,Kuma banida Niyyar barin jikin nata yasa Aaryaan Takowa Har Gaban Mu yasa Hannu Ya Rabani da ita nan Take na kuma Tsorata na Tareda qwala Wani Uban Qara

Tsawa ya daka mn Cikeda Jin haushin yanda Nayi Ihun yace

"Dalla Rufe mana Baki"


Tsawan da ya daka mn ne yasa na dawo cikin hankalina na Dan natsu amma jikina bai daina Makyarkyata ba ,Ya dubi Junayd Cikin Daurewar Fuska yace kuna iya tafiya Sai Gobe ko.


Su Junayd suka msu Sallama Har zasu Fita Umma tace Ita fa bazata iya Kwana anan ba ,Su jirata Ta kwana achan 6angaren nasu don Itama tace Tsoro fa takeji haka Kuwa akayi chan ta kwana


Kuma ikon Allah bata takura suba Yanda take takurawa Ramlah anan



Yau Aaryaan a Dakin Ramlah Yake Shiyasa Ma Ina samun Barci yaje parlor ya Gyara inda Aka 6ata da jini Sannan ya Dau Bindigoginsu Ya 6oyesu Waje daya,.

Ya dawo dakin ta, ya iske ta hartayi Barci ,Ya fada bandaki yayi Wanka tareda sauya kayansa Zuwa Jallabiya mai Gajeren hannu

Kwanciya yayi tareda Jawota ya Rungumeta Ta baya hakan yasa ta Farka , Zatayi magana Taji ihuna daga daga nawa Dakin ina Fadin "Wayyo na kashesu Yaya jini jini Bindiga Wayyo jini"


Tsaki yaja tareda Qara Rungumeta ,adan Tsorace ta Raba Jikinsa da nata tace

"Dr Please kaje ka dubata"

Hannu ya daga mata Tareda cewa "Qyaleta iskanci ne kawai".


"Please hun !, This is Serious ta tsorata ne Sosai, Bai kamata a barta a daki ita daya ba ,Please kaje" ta qarashe magana Cikin kwantar da murya

Tsaki ya kuma ja a Fusace yace "Tunda a tsorace take Naje na Goyata kenan ko kuma ta dawo nan ta kwana tunda bata iya kwana ita daya"

Ta fahimci ya Hasala ne hakan yasa tace

"Eh Kaje ka kwana da ita, Ni na Yafe maka kwana anan"


Ta fada daidai lokacin da Sukaji qarar Bude qofar daki Tareda Takun qafan mutum Alamar ana Guduwa Ai babu Shiri ya miqe da Gudu Har yana tuntu6e


A saman matattakalar bene ya iskeni Garin Gudu na Fadi qasa ,Qarasowa yayi a gigice Ganin ya Iso inda nake Na miqe a Tsorace Nayi sama ina Fadin

"Wlh bani na kashe su ba Wayyo kalle jini!, Jini ,jini, jini Yaa kazo Sun kashe Aunty Ramlah"


Shima da Gudun ya Bini Don ya fahimci Sosai na razana kuma me yuwa Abinda nagani ne ya firgitani Har yasa na kasa natsuwa Kuma tabbas idan na Cigaba da Razana haka Abin zai iya shafan qwaqwalwata.


Hakan yasa ya Bini da Qyar ya hadani da qirjinsa Yana bubbuga bayana sai da yaji na fara Sauke ajiyan zuciya Sannan Ya Rabani da Jikinsa ya Kaini Dakina yayi mn Allurar Barci dama baya Rabuwa da Alluran Barci Saboda idan yanaso yayi sammakon zuwa Wajen aiki Kuma Barcin yaqi zuwa....




Yana Ganin na samu isasshen Barci ya koma Dakin Ramlah wacce Tuni barcin ya Saceta.


***


Wasa Wasa Saida na dau kwana Biyu ina Razana da Zarar na tuna yanda na harba bindigan nan ya kuma samesu Duk a qasa sai na Fasa Qara na fara kiran Ga jininan Jini jini...



Kuma fa duk d hakan ban bari Umma ta Sami nasarar wulaqanta Ramlah ba, Ako Wani motsinta akan idona Yake ,janaan kuwa yanzu kullum tana namu part din Dazarar taga Ramlah na Aiki sai ta tayata harta Girki tare Sukeyi bayan ta Gama nata Don ita Aiki baya mata wuya hakan yasa na Dan fara cin Abincin Cikin Gidan, idan ta Gama ta koma nata 6angaren.



Yau Zan kar6i Girki Tun jiya Aaryaan ya shigo ya gaya mn na shirya Kar6ar Girki tareda Duk Wani Hidima na Gidan yanda nake Ganin Ramlah tanayi Naso nayi masa Musu harda Cewa nifa ban iya Girki ba,amma sai ya zare mn idanu Tareda Cewa Idan ban iya ba Nayi Jagwalgwalo Ahakan Zan kware ai da koyo Ake iyawa ,naso Nayi Gardama Amma babu yanda na iya Don cewa yayi idan na sake Nayi masa gardama ko Taurin kai sai yayi Abin Da Nake Tsoro ....



Hakan yasa na kama kaina ,Tun da na Tashi bayan na Gudanar da sallah na watsa Ruwa na Shiga kitchen


Na hada Break kala kala Tareda Orange Juice dnsa Wanda Yake sha kafin ya karya .


Ai tuni Gida ya Gaure da qamshi ,Murmushin Mugunta Nayi Tareda hada nawa Break dn Saida naci Nayi nak Sannan na sauko na jera masu nasu saman Dinning.


Naje na qwankwasa Dakin Umma Nace ta Fito Sannan na koma Dakin Ramlah na kwankwasa ta Fito Shikuwa ya Fita bai dawo ba.


Ba'a jima ba Ya shigo ,Jin Qamshin Abinci na tashi yasa Yunwan da ya kwana dashi ya motsa Ya lumshe idanu Tareda nufar Dinning Area inda kowa muke jiran sa


Gaishesa ya amsa tareda Gaida Umma itama ta Amsa mai ya kai dubansa Gareni "Ke baki iya Gaisuwa bane?"


Turo baki Nayi tareda hararar Gefensa kafin nayi Magana Har Umma ta kar6e da cewa

"Gaisuwa ai sai 'yan mutunci Wannan kam ai bata Gaji mutunci ba"


Dagowa Nayi na harareta Tareda murguda mata baki, Inba Don Aaryaan na nan ba babu Abinda Zai hanani Ramawa.


Bamm naji an buge mn baki da sauri na dafa Bakin ina Fadin" Kayi haquri"

Baice komai ba Ya dubi Ramlah wacce keta faman Murmushi yace
"Ramlahty Yau Wani Irin Spices kikayi anfani dashi ne Wajen Girkin nan naji yana qamshi ne haka?"


Ta nuna Ni da 'Yar yatsa tace "Ga Wacce tayi Girki nan tambayeta"


Aaryaan yadan xaro ido yana Kallona "haba, Kice Dama Chan kin iya Iskanci ne kawai da iya shege"


Murmushin Mugunta Nayi kawai ba tareda Nace komai ba yayinda Umma Ke ta faman Jifan mu da Wani wawan Harara.



Dakaina Nayi serving kowa Batareda na zuba nawaba.

"Sulthy Baki zuba naki ba"


"Eh kudai Ku fara Ci"


Umma ta hararemu Wato Sulthy wannan Wani irin Sabon kafce ne?



Ramlah ce ta fara Kai soyayyen Irish dindake ta faman zuba qamshi Bakinta ,Jin Wani irin yaaji da Gishiri mai hawa kai Da suka Ziyarceta ne duk a lokaci Guda yasa ta Dan Zabura tareda Furzarwa


Umma ta dubeta Cikeda tsana tace

"Ke lafiya?"

Ramlah ta juyarda kai Tareda cewa

"Ba komai fa"

Daidai lokacinda Umma takai shayin da na hada mata bakinta ,Ai da sauri ta Furzar itama Sakamakon wani irin Tsami ,Daci da baurin da suka Ziyarceta Duk a lokaci Guda .



Aaryaan ya dubeta Lokacin da Yake Kur6ar Orange juice Dinsa, Shima Fa da sauri ya Furzar a razane don jin Tsami da Yajin da suka Ziyarcesa kaman zai datse masa harshe.



A tare Suka kai dubansu Gareni da tuni Na fara Dariya Cikin Mugunta ina Fadin

"Ya kukaji Girkin ne?, Eh?, Yayi dadi ko?"


"Ke Don Uwarki Waya saki Girki?"

Sake tuntsurewa da Dariya na Nace


"Ba dai Dan Uwata ba, Kuma koma meye laifin kine ai Tunda A wajenki na Girma Nayi Wayo baki damu da na iya Girki ba bare Wani Abinda ya danganci hakan ! ,Kai kuma"



Na fada ina Duban Aaryaan da ya kafenj da ido Fuskar nan a daure tamau ,Da sauri na kawar dakai sakamakon wani irin Kwarjini da yayi mn

Amma dukda hakan bai hanani Turo baki ba na cigaba da Fadin

"Ka Wani daure Fuska kana Harara na ba kai kace Nayi Girkin ko jagwalgwalone"

Ramlah tayi murmushi Tareda Fadin "Bari na hada mana Wani kar Kayi latti"



"Dawo ki zauna ita din meye Anfaninta!, Ke kuma dawo nan ki zauna" ya fada tareda Nuna mn Gefen sa Kusa dashi.


Gabana ya Fadi Don bansan irin Muguntan da ya shirya mn ba sbd kallon Mugunta Yake mn..

Ganin ina 6ata masa lokaci yasa ya daka mn tsaka


"kya aap bahare hain?" (Bakya jina ne?)

"mai aap ke liye ky kar sakt hu?" (Yo zan yi maka?) Na fada Cikin Turo baki


Umma da Ramlah dai Ido Suka zubamana Don ba Fahimtar yaren Hindi Suke yi ba bare Su fahimci me muke cewa.


Ganin ya fara Fusata yasa na tako duk ilahirin Jikina Rawa na nufi inda Yake zaune na zauna kusan da shi Tareda kame kaina.


Orange Juice Dinda yaji Yaji da Tsamiya ya Debo a Kofi yakai bakina qin bude bakin nayi Don Ni kadai Nasan irin hadin da Nayi mshi


Hannu yasa ya Jawoni Jikinsa ,na saki Qara Ganin Umma na Aika masa Wani Uban Harara yasa ya kasa Aiwatar da Abinda yayi niyya kawai sai ya muntsuleni a baya na haka yasa na Bude baki tareda Fasa Wani ihu ina Fadin "Wash"


Kafin na Rufe bakin naji saukan Cup dn a Bakina, Hannu daya yasa ya Riqe kaina GAM Saboda kar na Juya ya zube dayan kuma ya Na kan Cup din hannunsa A dole Babu Shiri na Shiga sha Ina hawaye Kafin na ida Sha kuwa ji nake kaman An Cire mn Bakin nawa ne an Musanya shi da Wani Saboda tsananin Zafi Ga Ciwon Cikin da ya Dirar mn a lokaci daya.



Yana dire Cup din ya jawo Cup din tean dake Gaban Umma Ai kuwa ina Ganin haka na kwace da iya qarfina na haye sama da Gudu dan na tabbata Aaryaan bashida Imani yanzu Zai mn Dure Nikuwa idan Hakan ta kasan ce Mutuwa ne kawai bazanyi ba Don Ni kadai Nasan irin Mummunan hadin da nayiwa Tea din



Ina shiga Daki na fashe da Wani irin Kuka mai ban tausayi Har ina Shidewa, jin An bude kofar ne yasa na dago Jajayen idanuna na zuba mshi shima Ni Yake kallo



"Tashi ki Shiga kitchen ki hada mana Wani Break din!, In kin Ga dama ki Jagwalgwala Ke zakici kayanki!" Yayi maganar Cikin Wata kakkausar Murya.



Da Sauri na Miqe zan shiga Kitchen Din, Aikuwa da sauri Nayi Hanyar Bathroom Saboda Aman da yazo mn, Girgiza kansa yayi kawai tareda Ficewa daga dakin Don yasan Za'a Rina ,Kai tsaye Wani Chemist ya nufa ya siyo mn magunguna Don kar Sinadaran da na cika Cikin Abincin ya illata Ni.



Yana Shigowa ,Wani Irin Qamshi ya ziyarci hancinsa hakan yasa Ya lumshe Idanu tareda nufar dinning inda Kowa Ke jiran sa, Ya miqa mn Magunguna yace nasha in na Gama cin Abinci


Nace ai Ni tuni na qoshi, Baice komai ba illa jawo plate din Abincin da yayi ,Ganin Umma da Ramlah na cin Abincin Cikin kwanciyar hankali Umma harda Lumshe idanu


Shima Hannu yasa ya faraci Wani irin Dadine y ratsashi Tundaga Tsakiyar kansa ya kada kunninsa hakan yasa Ya lumshe idanu Cikin santi yace "Sulthy ,Dama kin iya Girki haka kika wahalar min da kanki a banza?"


"Kai Aaryaan!"
Umma ta daka mshi tsawa


Sunkuyar da kansa yayi ya Cigaba da cin Abincin sa yana Satar Kallona yanda nake ta faman kumbure kumbure.



Yana Gamawa ya Fice Kai tsaye inda ya Kulle 'yan ta'addan nan ya nufa ya same Abokinsa Jauz (Ismail) Dama shi Ke Gadinsu Saboda A Aunguwan Su Gidan Yake Saida ya tabbata komai daidai kuma An basu Abinci Sannan ya fara tambayan su Waya Aikosu ,Kaman kullum dai Amsar su Itace Bazasu Fada ba duk wuya duk Rantsi Hakan yasa ya Dan Gana masu Azaba Amma duk da haka Taurin kansu Yafi Duk yanda Suke tunani haka ya barsu ya wuce Wurin Aiki Tare da Fadin Jauz yaje ya huta ya kira Hilaal yace ya taho in yana Free Dan Su kadai ne Amintattun Abokan sa .....



***


Haka Rayuwa ta Cigaba da Kasancewa Gaba daya na takurawa Umma kaman nasani ko kadan Ban bari ta Sami damaryima Ramlah Alluran nan ba da zarar naga Sun ke6e sai na hallara a Wajen ,hatta Fada da Gorin Rashin asalin da take yiwa Ramlah yanzu ta Rage Sosai Don Tana Farawa Zan qarasa mata da cewa ai itama bata da dangin saidai ta nuna mata Asali Dazarar ta Cemn Kule zan ce Chas


Umma bata Kunyan Raba Abin kunya tsakanin mu hakan yasa nima Bana jin kunyan Zageta Tass iya son Raina kuma bata Isa Aaryaan ya dawo ta fada mshi ba ,Don Tana Gaya zan fashe dakuka Tunda Nasan Shine weak point dinsa Baya son Ganin kukana nan kuwa Yake Rudewa...

Kuma Tunda Umma ta dawo bai ta6a kwana a Dakina ba, Don Gudun kar ya kuma ta6o mata baqincikin da yasa Har ta suma ba kwanaki.



Yau Wata daya kenan da sati Biyu da Auren mu haka kuma Saura Kwanaki Uku mu koma Makaranta, Yau da zazza6i Janaan ta tashi Tun Tana daurewa Har Abin yaso yafi qarfinta Hakan yasa Junayd daukanta zuwa asibiti koda Suka Isa Asibitin Gwajin Farko likita ya tabbatar msu da Cikine Fa gareta nan danan ya shiga Murna Kaman zai Zuba Ruwa a qasa yasha



Koda Suka koma Gida babu kunya yayi ta Yadawa yana Gayawa Umma Aishi ya Kusa zama baba ,Irin Tsananin Murnar da Umma ta nuna ne ya bani mamaki ,Wato Jinin Aaryaan ne ta tsana kenan Tunda A fili ma nunawa take ta tsane Cikin Ramlah



Hannun Janaan naja Muka Shige daki na kalleta Tareda Tuntsurewa da Dariya.




















CHAI๐Ÿ˜˜


WLH COMMENTS DINKU NA JIYA YAYI MUGUN MUGUN BANI DARIYA TEAM MUNAYFERH WANNAN PAGE DIN NAKUNE


KUMA INA GODIYA DA RAAYOYINKU


ALLAH YA BAR QAUNA TA HAR ABADAH๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜







bintou๐Ÿ“Œ
Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ



25th Oct๐Ÿ’‹
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†L'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...



*_Chapter 54_*




" jaanu Ke din fa babu dama ,Daga Shiga Sai Ciki?"

Duka ta kaimun Cikin wasa na Kauce ina Dariya.

" 'Yar iska wayasani Ko Anko mukayi?, Don Wannan Hasken Da qiban da kika Qara ba Abanza ba"



Wani farr Nayi da idanu tareda kallon kaina Nima sai yanzu na lura da Irin qiban da na Dan Qara amma sai na waske Cikin Dariya nake Fadin

"Nikuma Ai iskancin Nawa bai kaiga hakan ba!, Daga Shiga na kwaso Ciki?, Ta6 Allah Shi kyauta Kwai Tsananin tsabar Yanda Yayan nawa ya iya kiwane da bai iyaba ai da Arame Zaki Ganni"



Itama dariyan tayi Cikin Dariya take Fadin

" 'Yar iska ai Dama daga Iya kiwon Ake farawa.... ,Da Anyi magana Ace ba'ason Yayan namu amma da bakinki kike Fadin ya iya kiwo in tayi wari zamuji!"


"Ehh!...Ai gaskiya na Fadi ya iya kiwo ,Kuma Bana son sa ko Qarya kikeso Nayi ne?....Kinga bari na kira Masoyiya na Fesa mata!"

Na fada Cikin Dariya ina Ciro wayana.


"Wa Zaki kira?" Ta fada cikin zare ido


Miqewa Nayi na nufi hanyan Waje ina dialling Numbern Nace

"Hafseey mana" ina Fadin haka Nayi Waje da Gudu
Itama Da Gudu ta Bini Tana qoqarin Kwace wayan .


Kai tsaye Dakin Ramlah Nayi Tana tsaye Gaman Closer Tana jera 'yan kayan ta da mai guga ya kawo mata ,A bayanta na 6oye tareda Qanqame ta ina Dariya.


"Wa ya biyo mn Ke kika Wani shigo da Uban Gudu haka"


Banyi magana ba Sai Uban Sauke ajiyan numfashin da nakeyi Daidai lokacin hafsah tayi Picking wayan ,Ban jira Cewarta ba Na shiga fesa mata

"Masoyiya Albishirinki !, Mun Kusa zama mummies!"


Daga dayan 6angaren Hafsah tace "Hello !Hello!!, Nyfee Bana jinki fa ,Na dawo Gani nan a kawo Zan qaraso barnawa yanzunnan"


Tsaki naja Cikin jin haushinta Nace

"Banza Cewa Nayi....."

Ban qarasa ba Sakamakon Fizge wayan da Janaan tayi a hannuna Tana hararana.


Nima dariyan Nayi na saki Ramlah na koma Gefe na zauna Kan gado ina maida Numfashi kaman wacce tayi fada da Qato.



Saida na dan Sami nutsuwa Sannan na dubi Ramlah da ta Gama Jera Kayayyakin da ta jido Nace


"Aunty wai Kinji Janan ce DA Ciki, Mun Kusa zama iyaye"


Ramlah Tayi Dariya tareda Duban Janaan da ta cika tayi Fam Dan Ganin Irin dariyan da nakeyi Cikin izgilanci.


Cikin Hadiye nata dariyan tace "Toh sai me Don Tana da Ciki? ,Waya Sani ko kema Cikin Ganeki ne?"



Janaan ta fashe da Dariya tareda qarasowa Tana Fadin

"Aunty Gane mn hanya fa, Wannan Hasken da qiban ai da walaki "


Harara na daka mata tareda Fadin

"Uwar Cikin nake dashi ba Cikin ba....Ni in an fada mku inada Ciki Zaku Yarda?"


"A'ah bazamu Yarda ba tunda ba Aure kikayi ba "


Turo baki Nayi ina Fadin "harda Ke Aunty?... Ni ina zan samu Ciki? 'Yan iska kawai"


Dariya Suka yi Gaba ki daya suka hadunmin Suna Tsokanata Wai inada Ciki Ni kuma ina Kokarin kare kaina Don sun lura in ba haka Suka mn ba Zan addabe su ne da Tsokana kawai Gara su juye akaina ...



Da Gudu Hafsah ta shigo Gidan Tana

" Neryfee Aunty Ramlah Ina Kuke Gani nazoh"


Turus tayi Ganin Umma da tayi Zaune a parlor tareda Qawarta Suna Kwasar Hira dama bata San Tana Gidan ba Don ko Sau daya banyi Yunqurin Fada mataba , Haka itama Janaan.


Umma kuwa jin Muryan Autar tata ne ya dawo da ita Daga duniyar hirar da suka Shiga Ta dago Tana kallonta.


"A'ah Auta Saukan Yaushe?, Shine ko ki kira ki gaya mn Zaki dawo?"



Jiki a mace ta qarasa tareda Durqusawa Har qasa ta gaida ta tareda Qawarta ta Suka Amsa mata Cikin Sakin Fuska

"Auta Saukan Yaushe?" Inji Umma


Maimakon ta bata Amsa sai ta Jefo mata Wata tambayar

"Umma me kikeyi anan kuma?" Ta fada Tana binsu da idanu Itada Qawar



Itadai qawar bata ce komai ba, Kallon hafsah takeyi ~Tabbas idan ta nemawa danta Auren Yarinyar nan Zai more, Amma Tana sane da yanda Umma Ke jida autar ta tah ,bazata so ta aurar da ita Ga Wani daga Cikin zuri'ar su ba Saboda Tashin wadataccen Tarbiyyan da Suke tattare dashi~


Umma tayi murmushin qasaita Cikin Isa tace

"Nida Gidan 'ya 'ya na ?"


Murmushi Hafsah tayi ta miqe tareda fadin

"Kinzo Dan ki takura Su dai" Tana Gama Fadin haka Tayi Ciki Da 'Dan Gudunta Tana Dariya.


Qawar Umma ta dubi Umma da bi bayan Hafsah da kallo Tana Murmushi

"Hajiya " ta kirata Cikkn kakkausar Murya.


Umma ta Amsa Tana Kur6ar Lemun da ta zubo a cup.

"Gaskiya 'Yar nan taki ta hade Fah ,Ni da Za'a bamu ina Kamu Don Ba Dan Kar kice Nayi Saurin baki ba da Nace nayiwa FeeYzie Mata Ai zasu Dace sosai Eh yahne ko ya kika Ganine"


Wani irin qwarewa Umma tayi Sakamakon jin Zancen Qawar tata ,Nan danan ta shiga Tari Tareda Sauke Cup din da Take Shirin kaiwa baki ,Saida Tarin ya lafa mata kafin ta dago Rinannun idanunta ta dubi Cikin idanun Qawar Ta fara magana


"Fee....Me?, Wannan Dan Iskan yaron?, ai ina badai da 'yata bah!, 'dar iska sai 'Yar iska Don haka akaishi cahn ko Za'a Sami second hand wacce zata iya Kwasar sa!, Ke bari ki bude kunnen ki Kijini dakyau 'yata An bada ta Ga Abokin Aaryaan (Hilaal) Don Tuni Suke Soyayyar su a 6oye Kwanannan Suka Fito Har manya Sun Shiga Maganar yanzu ma Jiran dawowar alhaji mukeyi Asanya Rana Ayi biki ,Ehe So ki Kwashi danki kije chan a nemo masa 'Yar tasha irinsa Ni 'yata mai tarbiyyace sai Dan Tarbiyyah inbanda Lalacewa irin na zamani ma Uwace zata haifi da A rada mshi Suna mai kyau mai dadi Faisal Ya Wani Chanzashi Zuwa Wani Wai Fezie su feeizie manya to 'yata tafi qarfinsa akaishi Chan Tallar bata qar6u anan ba Ehe" Ta qarashe magana Tareda sake Kur6ar lemun tareda Lumshe ido.

Nan Fa Hajiya Falmata (Qawar) ta shiga kumfar baki Ita a dole wannan Cin mutunci ne ,Nan Umma ta hayyayyakota Suka Shiga Raba Abin kunya (Da Girman Su๐Ÿคค)


*****


Kaitsaye Dakin Ramlah ta nufa kaman tasan Muna nan Tsalle daya Tayi ta fado kanmu Cikin Tsananin Murna Da Daukin Ganin Junan mu, Saida hayaniyan ta Dan lafa ne Suka Gaisa da Ramlah wacce tayi Shuru Tana kallon yanda kowannen mu ya Cika da murnar Dawowan hafsah.


"'Yan Mutan Maiduguri, Irin wannan bazata Haka? ,Saukan Yaushe ko dama kina hanya ne? " Inji Janaan Tana qare mata kallo


"Kinsan Maid babu service Shiyasa naqi kira Naso na kira Lkcn da na Iso kd Amma Sai naga kiran banzan nan Gaba daya ma fa banajin Mai take cewa sai Wani Magana takeyi Kaman mai Rada sai kace Tana magana da YaaAary" ta fada Tana Nuna Ni da 'Yar yatsa tareda Ta6e baki.


Duka na kai mata Cikin Wasa Ina Dariya Nace


"Kece banzar Ai .....Gulma na Feso maki Tunda zafi Zafin ta Amma yanzu na tabbata Har ya Huce Don ko na fada bazaiyi Armashi ba tunda juyewa zakuyi akaina Marasa Imani kawai"


Na fada ina hararar Ramlah da Janaan Dasuke ta Faman Sheqe Dariya Don Su Kadai suka fahimci mainake nufi.



"Ayyerh nayfee kisan ko kowa zai juye Shi akanki Ni bazan mki haka ba ko Dan Fesa mn kinji!"


"Tunda Gani Faisalco Ba....yauwa kin siyo mana Tsaraba dai ko?"


"Eh Amma Goruba ce Ke kuma bakida Haqorin Cin Goruba "


Ramlah tace "DanAllah dagaske Kin Taho da Goruba?, Har kinsa Inajinci"


Janaan tace "nima wlh"


Nima Dariya Nayi Nace

"Hafseey please me kika fahimta cikin Wannan Ankon da sukayi"


Kallona tayi cikin Rashin Fahimta tace

"Anko...? Bikin Wa za'ayi?"

Gaba dayansu suka kwashe da Dariya Ganin Gulma na cina Amma na kasa Fadi.


"Shashashar Banza Ba nan na nufa ba, Amma tunda na lura baki Gane maths mubi ta Physics hope Zaki iya haddace Formulan!......Toh banza Gulmar ce itace Munkusa zama mummies"



"Ke Dagaske?....Kice YaaAary ya zuba Aiki Anan!"



Hannu Ramlah tabawa Janaan suka tafa sbd yanda Sukaga Itama hafsan ta juya Zancen Cikin Rashin fahimta..


Qara Tunzura Nayi na Dan bugi kafadanta tareda hararar Su janaan Nace


"Sokuwa baniba ,Janaan ce mai cikin.... Aini inba A Ruwa Ake shan Ciki ba bani ba Ciki yanzu Don bansan inda Zan Samu ba"

A tare suka zaro idanu tareda Kama ha6a kaman zasuyi magana sai Sukayi Shuru


Hafsah ta Tsuntsure da Dariya ,Gaba daya Muka bita da kallo Tace


"Kuce nan bada dadewa ba zamu zo cin Ragunan Suna Aunty Ramlah na saukewa Sai Nyfee daga ita sai janaan ,A'ah Abin yayi fa Kuce Nima nayi Zuciya Nayi Auren Kodan nasamu na...."


Maganar ta Maqale ne Sakamakon uwar hararar da na 6alla mata Naja tsaki ina cewa


"Ni Waya gaya mki ina da Ciki daga dawowanki Har Zaki fara ko?"



"Eh Ance kinada Ciki din Sai ki Hau kanmu ki daddaka " inji janaan


Dariya Ramlah tayi Tareda miqewa ta nufi kitchen Don nemawa Hafsah Abin ta6awa Don ta lura Bamu da Niyyar Nema mata.

Tana Fita wayana dake Hannun janaan ta dau Ruri ,Tsaki naja tareda Fadin

"Wake kira na ne?"


Kallon Screen din wayan Tayi Ganin an Rubuta MIJIN TITI yasa ta Fashe da Dariya Tareda cewa


"'Yar Air Wato Mijin Titin nan bazai bar Rayuwanki bako?, Tunda anyi cancelling Auren Titi An daura na Gaske A Sauya Sunan mana"


Nima dariyan Nayi Nace "Ban wayan "


Miqa mn tayi Nayi picking tareda karawa a kunne


"Howfar " na fada ina hararar Wani Wajen..



~How far~ ya maimaita a ransa wato Yarinyar nan ta Rainashi Da Har zai Kira ta taqi sallama Instead ma saita Wani Ce mshi how far sai kace Tsararta.

"Ke baki iya Sallama bane Sai Wani How far Ni tsarar wasanki ne?,"


"To Assalamu Alaikum shikenan?"



"Wa alaykumussalam Na Aiko Adamu (Mai Gugan sa) da Saqo ki Gyara Kiyi komai kafin na dawo"


"Meye saqon ?" Na fada Cikin son jin Mai ya Aiko shi dashi .


"Naman Ragone kawai da kayan miya"


Turo baki Nayi kaman Zanyi kuka Cikin Shagwa6a tareda Narkar da Murya Nace


"Please yayana idan Zaka dawo ka Siya mn Awara mai qwai

Please Login or Register in order to submit comment