Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita sosai ,tsananin kaman da mukayi da itane yasa wasu suke kiran mu da Twince lei and Tei kasancewar Ni sunana Fateema nake ,Please ka taimaka ka gaya mn Asalin sunanta ko zan Tabbatar da hasashe na"


Ganin Sai wahalar mn da Daddyna takeyi yasa na kar6e Zancen da cewa

"Sunanta Haleematusssa'adiyyah Bintou Sani Nura mai kada , Asalin bakanuwace ,Ko ba'a fada ba zaki iya Gane ita din bakanuwace ta Halayyanta ,kinga Bakuda Any Relation with her ,Kamace kawai"


Ummie bata San lokacin da ta qaraso ba cikin Tsananin Tashin Hankali Gabaki daya ta susuce

"Wlh itace ,She's my blood ,itace....."


Saleem yayi Saurin kamata yana Fadin

"Calm down Mum ,Yanzu ba lokacin Wannan bane ,Nazo da Baqo , bari na bashi masauki yayi Wanka ya kimtsa ,yaci Abinci In ya gama sai Ku tattauna Please, yanzu Ba lokacin Tattaunawa bane , Tunda ba Guduwa Zaiyi ba ,Suna nan tareda Mu".

Ifrah ta kar6e da

"Ahtoh ,Daga Jin Sunan Mutun kin Wani Rude , Kodai kin Fara Tsufa ne ?, mu fara Biyan Bashi , don in kin tafi Babu Sisin da zan Fitar a biya Basussukan da suka hau kanki.....Ehey"

Gabaki daya Muka saka Dariya, in ka Cire daddy da Aaryaan Wanda Tuni Zuciyar sa ta shiga Bugawa Tunda Ummie ta Gayi Asalin sunanta yasan Tabbas wannan Qanwar mahaifiyarsa ce ,Wacce Umma Ke yawan bashi labarin Sun rabu Tun Suna 'yan qananunsu.


Wayansa dake Jikin Chargi ta dauki Ruri hakan yasa Ya dawo Cikin hayyacinsa ,Sai yanzu ya Tuna dama bai Fita da Waya ba.

Ifrah dake zaune kusada Wayan ta dauko zata miqa mn ya Miqa Hannu Ta miqa mshi , Ganin Numbern Hilaal ne yasa Gabansa faduwa , tunawa da yayi Tareda Ramlah zasu dawo


Batareda ya daga wayan ba ya kalle saleem yace

"Dude I think they're here"

"How did you know" inji saleem

"Line Dinda Nace su kar6a a Tyrash Railway, dashi suka kira"

Ya gaya yana Picking call din Tareda karawa a kunne .

"Wa'alaykumussalam ..... Kun Iso ne?.....Eyyerh kuna inane.....Yawwa Eh ,Ku miqe Sannan Ku biyota left hand naku zakuga wasu long Buildings Tho Building din kusada Masallacin dake nan Zaka Ganshi an mashi Glass work ta Waje Tho nan ne "





AFTER 16 MINS


Muna zaune da Daddyna a parlor bayan yayi wanka ya sauya kaya zuwa wasu sherwani wa'enda muka jido daga india , sai Surutu nake zuba masa ,haka itama Feerah don ita bata San Baqo ba, A Gaban kowa take Zuba Surutunta babu Ruwanta , Yayinda cooku ke jera Abinci kan dinning ,Saleem da Aaryaan kuma Suna Dakin saleem kome Sukeyi oho!.

.



Aaryaan da Saleem suka Fito daga 'daki idanun Aaryaan sun kada sunyi jaazir shima Saleem din da ka kalleshi zaka Gane yana cikin yanayi na damuwa.


A sanyaye suka Nufo inda Muke zaune ,Suka samu wuri suka zauna bisa daya daga Cikin Furnitures dindake Zagaye da Dakin .


A tare Sukayi wa Daddy sannu da Hutawa , Aaryaan ya maida dubansa Gareni kallo 'daya ya mn ya fahimci irin tsantsar Farincikin da nake tattare dashi ,Rabon da ya ganni Cikin Farin Ciki irin haka Kuwa Har ya manta ,FarinCikin da yaga inayi ya 'dan Rage masa damuwansa.


Franka (Cookun dake tayasu Girki) ta Fado Parlon Tana Fadin food is Ready ,Take muka nufi dinning don Mu kore yunwa , muna zama Gateman ya shigo yake sanarda Munyi baqi ,nan take Saleem ya bashi umurnin ya ce musu su shigo dasu shigo.

Gateman ya fice, babu jimawa Hydar ,Hilaal ,Ramlah da Isma'il Suka shigo Tareda su kuma Larai ne da Malam bala Wa'enda Kallo daya zakayi Musu ka fahimci Hankalin su ya Gushe daga Jikinsu ,daga laran Har bala din babu mai iya Fahimtar Abinda Ke wakkana Banda kallon mutane babu Abinda Suke iyayi Don Aaryaan ya umurcesu da Suyi masu Alluran da Zai zasu hakan ya zamo Babu Abinda zasu iya ta6ukawa Sai tafiya ,shima da qyar...


"Bismillah Ku qaraso " Saleem ya Gaya Yana Nuna msu Wurin zama a dinning dinda Muke zaune....


(Daga zuwansu Sai ka Wani nuna msu dinning?โ˜น๏ธ)


Babu Musu Suka qaraso ,Saleem ya miqe ya Ja hannun su Larai da Bala yayi Wani 'daki dasu ya Kulle ,Sannan ya dawo.


Aaryaan kuwa Tun Shigowansu ya kafawa RAMLAH ido ko kyaftawa bayayi ,Hawaye suka tarunmasa a idanu Gabansa na Cigaba da dukan Uku Uku ,Sanye take Cikin Navy blue Hijab ,Tayi haske ta Qara kyau Haka kuma tayi Rama ba kadan ba ,Idanunsa ya kaiga Cikinta Wanda Yake Tamkar babu Ajiyarsa A Ciki Dukda Kuwa yanzu Cikin yana Wata na takwas ne zuwa na Tara , Kasancewar Hijab dindake Jikinta ya 6oyeshi amma dukda Haka ita ba mai Girman Ciki bane a haka ba kowa bane zai iya Fahimtar Tana da Ciki ba.


Hawayen dake Qoqarin sauka daga Fuskarsa ya hadiye ,Sakamakon Girgiza masa kan da Saleem yayi Alamar yana Basa Qwarin qwiwa.

Ifrah ta dago Tana Binsu da kallo'daya bayan 'daya kafin ta saukesu akan Ramlah wacce Idanunta Suke qasa.


"Ke Shegiya Ramlah ,Ashe kina nan?,ya Akayi Kikazo nan? ,kar Kice mn Tare kukazo"
Ta gaya cikin Izgilanci Wanda suka sabayi idan sun hadu da Juna.


Dagawa Ramlah tayi ta hada Ido da Ifrah take Dariya ya kufce mata itama Cikeda mamaki take Fadin ,

"Inye lallai Yarinya kin Girma ,Ni dince Ramlah babu Ko Auntyn nan da Aka saba ko ?, Any way as You can see tare mukazo ,Ke kuma fa?, me kikeyi anan?, Ina my Saleey Da Ummie?"

Dariya Ifrah tayi tace

"Nabi Auntyn da Gudu ba takalmi ,Kin ma rainani dayawa , a Date of birth dinmu fa rana daya aka haife mu Kuma nice na rigaki shaqar iskan Dunya Tunda Saida aka haifeni da Awanni Uku kafin A haifoki ,so kinga the different is clear ,Kuma hala Ke makauniyace bakya Gani?, Ga Ummie Ga Romeo dinki , Ga kuma baqi ,Makauniya kawai"


Ramlah ta dago tabi Kowa da kallo ,Muna hada idanu na galla mata Harara Ganin yanda Aaryaan ya Wani kafeta da Idanu๐Ÿ˜’.


Suna hada Ido da Aaryaan Taji Gabanta yayi Wani irin Faduwa Ganin irin kallon da Yake Auna mata, Da sauri ta kawar da kanta nan take kuwa suka hada ido da saleem da shima ita Yake kallo Cikeda rudu ta kuma Maida Dubana Ga Ummie wacce tuntuni Itama ita take kallo
Murya Cikeda Tsantsar Rudani take Fadin

"Me Ya faru?, Me Ke faruwa ne?, ya Naganku anan ?, please tell me?, me Muka zoyi ne anan?, what's going on? ,Answer me"

Aaryaan yayi Murmushin Qarfin hali Tareda Daukan Cup din Ruwa ya zuba mata tareda Miqa mata .

"Oya sha Ruwa Qanwata ,I'll explain Everything to you later".

Babu Musu ta kar6a ta dan kur6a ,sai a lokacin taji Wani sanyi a zuciyarta.


"Yanzu dai muci Abinci ,Idan mun Gama zamuyi muku bayanin komai" inji Saleem shima cikin Sanyin Murya.


A tsaitsaye suka tsakuri Abincin don Gabaki dayansu sun qosa a gama suji mai ya tarasu...


Bayan Sun Gama kowa ya hallara a babban Parlor.


Daddy ya bude taro da Addu'a tareda Godewa Allah da ya Fito dashi daga Hannun azzaluman bayinsa ,sannan ya Umurci Ummie da ta Gaya mana tarihinta don Maganganunta na dazun Sun tabbatar masa da cewa 'Yar Uwar Ummace But how comes.


"Da farko dai sunana Fateemah Sani Nura mai dala ,Ni haifaffiyar 'Yar Garin Kano ce ,a cikin Garin sharada ,Mahaifina Malam Sani Mutum ne Wanda Allah ya azurtashi da wadatar Arziki yanada Mata Biyu Salame da Jummala , Salame itace Mahaifiyata sai Jummala kuma mahaifiyar Haleemah ,Mun taso Cikin Tsananin Gata da kulawan iyayen namu ,iyayen Mu kansu a hade Yake baka ta6ajin kansu ,Sun zama Tamkar 'yan Uwa ,haka Nida Haleemah Wanda Inba gaya maka akayi ba sai ka rantse 'yan Biyu ne ,Don kuwa Kamar da muke Har ya 6aci ,hakan kuma ko a makaranta Twince Ake kiran mu ko kuma LEI Da TEI.

A lokacin da Muka Isa Shekaru Tara Tara da Haihuwa mahaifin mu ya kaimu makarantar kwana Wanda Ke chan Kaduna ,A cewar sa anan zamu fi samun Ingantacciyar karatu nagartacciya ,haka kuwa akayi ,koda Muka Isa Makarantar Sosai Muka maida hankali Ga karatun mu don Cikawa Iyayen namu burinsu ,Ana haka Aka Gano students dake aikata madigo ,da Male teachers masu Shigowa Suna 6ata Rayuwan 'yan makaranta ,Ciki kuwa harda shugaban Makarantar ,Gudun kar asirinsa ya tonu duniya tayi masa Allah wadaran yasa ya yanke hukuncin qona Makarantar jnyaso sai ya sanar Qonewa yayi.Haka kuwa akayi a lokacin da makarantar ta Fara Qonewa Muka farga , daganan Muka yanki hanya muka Gudu kowa ya kama hanyarsa ,Ba hanya daya mukabi da lei ba, Dama kuma makarantar yana cikin Dajine ,so nasha wahala kafin na Fito Titi ,Ina Fitowa Cikin Rashin sa'a Mota tayi Gaba dani ,a lokacin ba kowa Ke tuqa mota ba, idan Kaga mutum mai mota tho ka tabbata wannan Babban Attajirine .


Daganan ban sake sanin inda nake ba,sai a Gadon Asibiti, na samu karyewan qashi ,Kuma Bana iya magana, saidai Idon da nake bin kowa dashi ,nasamu tsantsar Kulawa daga Mutanen Wanda dama su suka kade ni ,wasa wasa Saida Na kai Shekara 'daya Bana Iya Magana ,Gara ma qarar ana Samun improvement ,A lokacin ne Suka yanke shawarar Tafiya dani qasar Waje don nema mn magani ,ko zan iya samu Nayi magana asan inda iyayena suke ,Cikin ikon Allah ana Fita dani qasar akayi Aikin Kuma an dace alhamdulillah ,nan suka nemi sanin Sunan garin mu da Sunan Mahaifinmu su kaini inda na Fito ,Koda na Gaya msu basuyi wahalar samun Wajen ba ,Amma sai aka Ce mn Sun kai watanni Hudu da barin layin ,Sunyi Neman duriyan nan babu Su babu Alamar Su, daganan sai suka Cigaba da Riqeni Suna bani Kulawa ta musamman Wanda ko iyayena ne iyakar Abinda zasuyi mn kenan,Mutanen da Suka Riqe Ni kuwa sune .


Alhaji Muneer da matarsa Hajiya Harirah ,mahaifin Alhaji Muneer Babban 'Dan kasuwa ne ,yanada Yara Biyu Da Muneer da Yazeed Shi yazeed mahaifinsa ya gado da son kasuwanci Shiyasa mahaifinsa ya dorashi Akai har ya Girma ya bunqasa Yake saro kayyayyaki daga qasashen Waje , Ana haka Wata Rana Yayi tafiyarsa na Zuwa saro kayayyaki kaman dai yanda ya saba ,qaddara ta Afka msu Sukayi Gobara Har hakan yayi sanadiyyar rasa ran mahaifansu ,Ya rage sai Muneer kadai ,A lokacin ya Bar Gidan amma ya tafi qasashe dadama Don Neman Dan Uwansa Yazeed Allah bai nufa da rabon su sake haduwa ba.


Daganan ya tattare duriyan mahaifinsu ya fara Sana'a don dogaro dakai ,ana haka Cikin ikon Allah ya hadu da matarsa Mai kirki Hajiya harirah , Wacce suka dau Shekaru masu dumbin yawa babu Haihuwan mace ba ,'ya'yansu Maza Biyu Taheer da maheer, daga bisani Allah ya hadasu dani a matsayin 'yarsu , Sun bani Gata da Kulawa sun Sani a makaranta ,na Cigaba da karatuna, Taheer shi ya fara Aure ya Auri Wata'yar Kaduna Shekara daya da Aurensu matarsa ta haifi 'da Namiji wato SALEEM ,inaGama secondary school suka hada mu Aure da maheer kasancewar Mun dade muna Soyayyar mu a 6oye shiyasa Muka Amince da hakan a lokacin Saleem na 'Dan Shekaru Tara da Haihuwa , Nima kafin Shekara daya Allah ya azurtani da diyata Ifrah , ifrah na da Shekara daya da Haihuwa Maheer da Taheer Sukayi tafiya zuwa Abuja don halartar daurin Auren Amininsu Dake aiki achan ,tafiyar da basu sake dawowaba kenan Sakamakon mummunar hadarin da sukaci karo dashi Allah ya kar6i Rayuwansu ,Haka Rayuwa ta Cigaba da tafiya Na Cigaba da zama qarqashin Alhaji Muneer da matarsa , ita kuwa mahaifiyar Saleem Ta koma Gaban iyayenta , Ta bar mana Riqon saleem , dama ko a da chan baya Saleem yafi sanina a matsayin Mahaifiyarsa shiyasa bansha wahalar riqonsa ba ,Na hadasu da Ifrah ,Saleem Nada Shekaru Goma a duniya Allah yayiwa Alhaji Muneer rasuwa ,Bayan Wata daya matarsa ta bishi , munyi baqinCikin Wannan Rashin da mukayi don Ni Saida na dau Watanni ina jinyar zuciyarta akan wannan Gagarumin Rashin da Nayi ,Bayan mutuwan sa da wasu watanni muka samu labarin mahaifiyar Saleem wacce dama tayi aurenta a chan Qauye ,itama ta rasu Nayi baqinCiki Mara misaltuwa ,da wa'ennan Rashin da mukayi Daganan na Cigaba da Riqon Saleem da diyata Ifrah, nice Ke sama mana Abinda zamuci musha harda Biyan kudin makarantar su ,Har lokacin da Saleem ya kawo karfi ya zama agent a Babbar Ma'aikatar Gudanar da Bincike na qasar mu wato 9jeria ,daga nan ya dauki Nauyin mu dani da qanwarsa Cikin Binciken sugudanarwa Akwai na Wani Qungiya na tsafi wa'enda Ake hasashen sune Suke daukewa Mutane 'ya 'yansu suna amfani dasu don biyan nasu Buqatar, don haka aka rarrabasu Zuwa Gidaje dadama don Gudanar da Binciken amma zasu Tsaya ne a maysayina masu aiki ,Haka kuwa akayi aka tura Saleem Wata Gida inda Anan ne Allah ya hadashi da Ramlah ,Mace mai haquri ,da sanin ya kamata , Anan Soyayya mai zafi ta qullu tsakanin Su , Har Yake kawo mn ita mu Gaisa tunda shine Drivern su , amma Abinda Saleem ya lura dashi ko kadan iyayen nata basu qaunar Ramlah hakan yasashi Kokwanto Anya kuwa sune mahaifanta kuwa ,don Tsananin wahalar da Ramlah kesha a hannunsu , Akwai Ranar da Saleem yazo mn da ita Naga hannayenta a tsatsage Kaman razor aka samu aka yayyanka hannun nata ,na tambayeta Ya akayi hakan ta kasance tace mn Mamy ce ta Yanka hannun nata don ta tambayi Abinci yau kwananta Biyu babu Abinda ta saka a baki yunwa takeji,Alokacin Hankalina ya tashi sosai Har Nayi yunqurin tunkararta don na Gaya mata Kuskuren ta Amma Saleem ya hanani ,a haka rayuwansu ya Cigaba da kasancewa Har Ta Gama jami'a a lokacin Suka tunkari Mariqinta wato Malam Isa da maganar Auren Saleem da Ramlah, Amma sai ya nuna masa da Akwai Wani Aikin da yakeson yayi masa a Chan qasar LIOS idan ya gama zai aura masa Ramlah ,Koda Saleem ya tunkareni da maganar na Basa qwarin qwiwan 100% Hakan yasa ya zo wannan Qasar Yake tsaron Mutumin dake 6oye a Wajensu ,dayaga babu Ranar dawowansa Nigeria yasa aka dauko mu ya Siya mana wannan Gidan Da muke zaune a halin yanzu Sannan ya nemawa Ifrah Transfer ta dawo nan take Cigaba da karatunta dama achan Tana 300l ne yanzu haka ma Saura watanni Hudu Su gama ,amma shi Saleem ya dau Alqawarin sai mutumin nan ya ku6uta daga hannunsu zamu koma Qasar mu ,koda Ifrah ta gama nata Karatun ,Amma Yazo mn da Wata magana Lastweek , Lokacin da baqon nan yazo Wai ya Gano Ramlah tayi Aure kuma ba kowa ta Aura ba sai Yayanta Wanda Suke Uwa daya Uba daya"


Ummie ta share hawayen ta ,Ta Cigaba.

"Ramlah kinsha wahala a Rayuwa, kingamu da jarabawa iri iri ,A Lokacin ne Saleem ya tabbatar da zarginsa Wato Ba Mamy bace Mahaifiyarta "

Sai ta kuma yin shuru ,Gabaki daya Dakin ma ya dau shuru banda Kokekoken mu nida Ramlah da Ifrah babu Abinda kakeji yana tashi .



Aaryaan ya miqe zai bar Wajen ,duk muka bishi da idanu Har yakai Bakin qofa sai ya kuma Dawowa ya Ciro Wata 'Yar takarda a Ajihunsa Ya miqawa Ramlah ,Daga nan ya Fice.


Jiki da Hannu na Rawa Ramlah ta Bude takardar ,bata iya karanta dogon bayanin da yayi a takardar ba Kawai Ganin Qarshen layin rubutun Tayi wato


KIYI HAQURI QANWATA NA SAKEKI SAKI UKU

Shikenan ya tabbata ba ,Mamy ta haifeta ba, Umma ce ta haifeta?, how comes ,ya Akayi hakan ta kasance?, wani irin qaddarace Ke bibiye da ita?.

Wata irin Qara ta saki daganan ta Fadi qasa ,sumammiya......






Daga nan Bata sake sanin Inda take ba Sai bude ido tayi ta sameta Kwance Bisa Gadon da ko ba'a fada mata ba na Asibiti ne, Hannunta Riqeda Na Saleem kansa duqe a qasa ko ba'a gaya masaba tasan banda hawaye babu Abinda da yakeyi tunda tanajin digar hawayensa a hannunta da Yake Riqedashi.


A hankali ta bude baki ta Furta


"Saaleey"


Daidai Lokacin Babyn dake shimfide a gadon jariran dake kusada Shi ta fara Kuka.....






Nyeeeh.....


Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ

Kar Ku biyoni



17th nov๐Ÿ˜Œโœ๐Ÿฝ
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...



*_Chapter 67_*



A hankali ta kai duban ta Ga Babyn daketa Tsala Kuka ,Ta kuma maida dubanta Ga Saleem da ya kafeta Da ya kafeta da idanu kafin ta bude Baki a hankali Cikin muryan Mara Lafiya tace

"Saleey ,Nan ina ne?"

"Asibitine " ya bata amsa tareda Kauda kansa Gefe

Wani tambayar ta kuma jefo masa

"Me ya kawoni Asibiti ?"

"Calm down Bby ,duk yanzu ba Lokacin wannan Bane, Kin Gane?, relax bari na kira Doctor ,One minute kinji?" Saleem ya fada Tareda miqewa ,Amma kafin ya kaiga qarasa miqewan Har Babyn ta kuma Sanya kuka Wanda yasa Ramlah kamo Gefen Rigarsa

"Wacece Ta haihu Aka bar Babynta Anan ?, ko nan haka Sukeyi ?"

Murmushin Gefen Baki Saleem yayi kafin ya qwace Riqon da tayi masa ya dawo ya zauna , sannan ya Sa Hannu ya zaunar da ita , ya fuskance ta ido Cikin ido ya fara magana Cikin natsuwa

"'Yarki ce , wacce Biological Mum dinki bataso zuwanta duniya ba, yau 3days kenan da zuwanta Duniyar nan tamu mai Cikeda Abubuwa mabanbanta Masu Birkita tunanin 'Dan Adam ,So welcome Your Daughter"

Ya fada yana sake Nuna mata jaririyar .

Nan take ta tunada Abubuwan da suka faru Tun daga Farko Har zuwa inda ta karanta Kalaman sakin da Aaryaan ya rubuto mata ,Take hawaye Suka zubo a Idanunta, a hankali ta dago ta kalli saleem Wanda shima ita Yake Kallo Murya na rawa tace..

"Saleey da Gaske Aaryaan ya sakeni?, da Gaske Ni 'Yar Umma ce?, Ummace Mahaifiyata ba Mamy ba?, Ya akayi hakan ta Faru ? ,Meyasa Zaiyi Saurin yanke hukunci Batareda ya Tabbatar ba ,Shikenan Ni haka Rayuwata zata Qare babu Uwa babu Uba kuma babu miji?, Gaba daya Duriyan Da Mutanen Cikinta sun Tsane Ni Meyasa? ,Why is this Happening to me?, Why always me ? ...."


Kuka mai qarfi ya qwace mata ,Saleem ya jawota ya Rungume ta tsam a Jikinsa , Saida yaji ta fara Maida Ajiyan Numfashi Kafin ya Rabata da Jikinsa ya kalleta ,Tana dagowa suka hada Ido nan Yake Wasu hawayen suka 6ul6ulo.


Girgiza mata kai ya shigayi

''Oh no, Hearty Why does Tears?"

Ya fada inacool voice yana Sharemata hawayen da tafin hannunsa Amma kaman Dada tunzurata Yakeyi sai dada zuba Hawayen sukeyi kaman An bude famfo.

"Hearty baki Rasa Komai ba ,Baki Rasa Uwa ba ,kuma baki Rasa miji ba, Tunda Kinada Nida Ummie , Tun Randa Yayanki ya sakeki Aka Aura Mn Ke ,Tunda dama Bakida Iddansa ,Tunda yana Sakinki kika Suma Har aka zo dake Asibiti a Asibitin kika haihu , Tun daga Lokacin Baki sake Farfadowa ba ,Likitoci ne Suke iyaka qoqarin su don Tabbatar da Kin samu lafiya Har ki tashi ,kuma fa tun ranar da Muka kawoki basu bari mu shigo ko sau daya Mu ganki ,harta ni mijinki ,Even Ur Brother Da matarsa harda tawagarsa da Ummie kullum sai sunzo amma suna Hana mu shiga ,Sai dazu Suke gaya mana Wai Zaki iya farkawa at any Time ,shiyasa Na shigo ,Babynki Kuma tunda Kika haifeta Ake dirka mata Fresh Milk ,Ni nama fison Haka don Wlh bazan Yarda Ki shayar da 'Yar Wani Alhalin Da Aurena Akanki ba,Ki zama mai tawakkali akan duk Abinda Ya faru dake ,Kowane bawa da Jarabawan da Allah ya qaddara Zai sameshi ,Kuma hakan SHIKE tabbatar da Qarfin Imanin Mu ,Komai Kika Gani a Rayuwan Nan Mai Gushewa ne ,Babu Abinda zai dawwama a doron qasa Even wa'enda suka Hada wannan AikaAikan ,Nasan ba Don komai suka hadaba Sai don su quntata mana ko kuma Cimma nasu manufar , manufar Da bazai Wuce samunta da Amfaninta duk Su qare cikin qanqanin Lokaci ba ,Mu da sukayi Don Muzguna Mana sai daga Qarshe Allah Ya daukaka Mu Sbd haquri da juriyan da mukayi don Cin jarabawansa , Duyinan nan ba komai bace Kuma batada Daraja a Wurin Ubangiji ,Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa , ~Da duniya tanada Qima kaman kunnen jaki Wajen Ubangiji ,tho da such a infidel bamazai sha Ruwa Ba~ , Kwata Kwata duniyan Nawa take?, Wannan duniyar wacce zata qare ?, instead muyi amfani dashi don Neman yardansa ,Sai muke aikata fasadi don muzgunawa Wani , Kiyi haquri Babyna Inaji a Jikina qarshen Wahalarki tazo Tunda kin aureni bazan ta6a bari Wani Abu ya sake Cutar mn dake ba ,Ko meye Ko quda In mai cutarwane bazan ta6a Bari ya kusanto inda KKE ba bare ya samu Damar Cutar min dake , Allah yayi Gaskiya da yace Inna Ma'al Usri yusrah ,Lokacin Hutawanki yazo tunda Na sameki Muradin Raina ,Baza ki sake wulaqanta ba ,Anda last thing inaso Kiyi yaqin nan dakanki Muba mara 'da kunya ,Duk Wanda ya hada Auren ki da Aaryaan Don Cinma nasa Manufar Prove them wrong, A Zuciyar ki Karki ta6a kallon Aaryaan a matsayin Yayanki , ki daukeshi ne a matsayin Tsohon Mijin ki Wanda Qaddara Ta rabaku hakan kadai zai Sanya iya Nutsuwa Cikin Ranki ,Harta Fams dinsa Ki daukesu a matsayin ex In-laws harta mahaifiyarki "


a Dan Razane ta dago ta dubeshi.

Ya gyada mata kai

"Yes!, adaa Lokacin da Kike Inlaw nata ta wulaqanta ki harda Koranki a Gidan Ubanki ,the Funny thing ma shine harda Furta miki Kalmar saki ta sakeki saki Uku ,Abinda bata Sani ba, da tayi haquri da ta jira Ko bata Furta ba zai sakeki "


Ramlah tayi Saurin Tarar Numfashinsa Cikin Murya mai nunida Jikinta a sanyaye Yake kuma Bata Jin dadin Jikinta tace

"Taya akayi kasan Da dukan wannan Abun?".


Murmushi yayi akaro na farko yace

" CCTVn da na bawa Ammien Twince , Nace ta maqalashi a Part din Amaryan Abie ,Cus itace First Suspect din mu ,tanan nake samun Informations Dangane da Abinda ya shafi Case dinnan ,Karna Cikaki da Surutu Bari na nemo mki Abinda Zaki sa abaki Sannan na kira likita da Ummie suzo su zauna dake Kafin Na dawo kinji...."


Kai ta gyada mshi Alamar tho ,Sannan tabishi da ido ,Tama rasa Farinciki Zatayi ko baqinCiki Farincikin Auren ta da Saleem ko baqinCikin bayyanuwar Wannan Abinda Yafi komai muni Cikin Tarihin Rayuwanta, Amma kalaman Saleem sun 'Dan sanyaya mata Zuciya Amma Abin tambaya Anan suwaye Suka hada wannan Abin?, menene Manufarsu Na hadata da Yayanta a matsayin ma'aurata? Yanzu Shikenan Ta Aurawa Kanta 'ya Mai Kaka 'daya......"

Da fatanda saleem yayi ne yasa ta dawo Cikin hayyacinta.

Murmushi tayi shima ya maida mata martanin Murmushin ,ya juya ya dau Babyn dake ta tsala Kuka yana Jijjigata.


"Hearty Na manta ban fada Miki Sunan Babyn naku ba, HALEEMAH sunanta Sunan Ex Inlaw dinki ,Have Ur baby ,Ki kalleta dake take kama Kinga Har Dogon hanci da Pink Lips Ke ta biyo ,Amma Manyan idanu da Hasken Fatanta Irin na A.A ne"

Ya fada yana Nuna mata Fuskar Babyn .......



******

Tunda Ranar Da al'amarin ya faru ,Kullum ina maqale da Daddyna ,Yayinda Shi kuma Aaryaan Yake Faficikan Neman Asalin Haddasanan Wannan Birkitaccen Al'amarin Kullum yana Tareda 'yan sandan nan Wa'enda ya Zuba a Gidan da daddy ya Fito Suna Aiwatar da nasu Binciken, haka kuma bai sanar da kowa ba ,face Abba Wanda ya kasance Shike Bashi qwarin Gwiwa akan wannan Case din ,Kuma shine ya bada shawarar a sakawa Baby Sunan Ramlah ,Haka kuma Su hilaal Suna matuqar taimaka masa ta fannin Nurse dinnan Kuma alhamdulillah ana samun Improvement sosai don Nurse Dinda suka tarar Tsare a Gidan Bata iya motsa ko wane Sassa na Jikinta ,Harta Numfashi Saida taimakon Oxygen take Samun Fitarwa harta Abinci da Ruwa Duk da Taimakon Drs Ake iya bata ,Amma yanzu alhamdulillah Tana Iya Bude Idanunta Har Abata Abinci Abata Abinci ta baki kuma ta kar6a .


Hilaal Shike jagorantar Kulada Nurse din ,Abu na farko da ya lura da Citar dake Damun nurse din shine ,Ba Wani gagarumar Rashin Lafiya Ke damunta ba ,Illa Alluran da Ake dura mata na kashe Gabobin jiki na tsawon Shekaru Har kusan Hudu don Saida aka Kawota

Please Login or Register in order to submit comment