Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Naja kumatunta nace "Naughty Babies ,Ina iyayen ku suke Suka barku da tsallaka titi Ku kadai?" Nayi magana ina daukan dayan Cus ina bala'in son Yan Biyu.


Yarinyar ta kalle idona da yayi Rudu Rudu ya kumbura saboda Kukan da nasha Ga shatin Yatsun hannu shimfide a Fuskar tace "Anti You a biyrifu, See ur face, Kinyi kuka ne?" Ta fada tana Shafa Kumatu na.


"Munayferh!"


Muryar da bazan Ta6a mantawa da mai'ita ba naji ta kira sunan........



















Manage๐Ÿ–‹๏ธ












Fahnaan










14th sep


Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ
Sunday13sep๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*


ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 32_*




Da kallo nbi saitin Inda najiyo Muryan,Tsakanin mu daita Titi daya ne.

Cikin rawar baki data jiki nake kallon matashiyar matan, dak'yar na iya hada kalmomi mai cike da in'ina โ€œA....M....M....I?โ€.


Su Ameerah na Ganinta Suka kwace daga hannuna Suka 6oye a bayan mota.


Bandamu da yan'Tsirarun motocin da suke Giftawa a kan Titin ba,Na tafi da Gudu Saura qiris mota ta bige ni ,Ban damu ba, burina Bai wuce in Isa Ga Uwa ta ba domin ita kadai nake hangowa.

Ina tsallakowa nayi Tsalle na Rungume cikin TsanTsar Farinciki baki na Rawa nace "Amm...ie ke...ce...?, in..a Da..ddyy"



Ammie ta Share hawaye suke Ziryo mata Cikeda Qaunar 'yarta ta raba ta da jikinta A sanyaye kuma Cikeda natsuwa tace "Munayferh Cikani A kan Titi muke fa"


Ni'ina Ruwana sai Qara Qanqameta ma nayi, "Ammie wai kece ko Sai irin Silly dreams da na sabayi ne?, ina Daddy?" Na fada ina qara Shigewa jikinta.



******
KADUNA

Tun jiya Ake ta Shirye Shiryen Waliman tarbar babban Baqo wato yaaJunaid SBD yau zai dawo, sun Gama NYSC dama shi yakaishi Kudu.,Abdool ma babu yanda kakus batayi dashi ba Akan yaje makaranta Amma Fafur Yaqi da yaga zata matsa mshi Sai kawai yasa Kuka a dole ta Qyaleshi, baije makarantaba,

Su Zainab da suwaiba Kuwa Sunanan Sai wani iyayi Akeyi, yaaUmar kuwa shima Baije Wurin aiki ba yau.


8:20am dot motar Mu tayi Parking a harabar Gidan.


Gabaki daya Ma'aikatan Gidan masu Kai kawo a harabar Gidan Suka Tunkaro Wurin mortar ko wannen su Cikeda Tsantsar FarinCiki, Dan A zaton su Aaryaan ne!, (Kun San dai motar sa CE) .


Nayi murmushin Gefen baki Ina kallonsu ta ciki Aradu nasan Da sun San Nice Da basuyi Gangancin Tunkaro ni ba da tuni Sun ware mahh,


Su Ameerah dake Zaune kusa dani Sai kiciniyar Bude kofar Sukeyi, Amma naqi budewa ,Ammie kuwa tana backSeat tana Kallon ikon Allah.


Saida na tabbata ko wannen Su ya Iso Gabda motar Sannnan na danna Control, Kofofin Gaba suka bude,Ai tun kan Su Gama buduwa su Ameerah Suka fice,


Gabaki daya ma'aikatan Suka bi Yaran da kallo baki sake sannan Suka maida hankali Ga mai Fitowa ,gaba daya Idanu Suka Waro Alamomin Tsoro sun bayyana tareda Su Ganin Wacce Ta fito daga Motar, Ammie dake kallon komai tayi murmushi, Wato munayferh I'll never Change , Tana nan da halinta na Rashin Son 'Yan Aiki Shiyasa Babu Yan Aiki a Part dnsu Duk saida tasan Yanda tayi aka koresu ,gata Ba aikin Komai ta iya ba, Bare ace za'ace zata taimaka๐Ÿ˜•,Ammie Ke Aikinta da kanta.


Simi Simi Suka Juya zasu Wuce

Na daka musu Tsawa Wanda yasa Su dawowa batareda Sun Shirya ba.

"Hey Bitches ina Zaku?"

Kansu a Sunkuye babu Wanda ya bani Amsa Cus kar amsar ta zamar musu Another problem.

Mukullin Part dnmu Wanda tunda na kar6o a hannun su YaaUmar, Yake Hannu na ban ta6a chanza mashi Wuri ba Idanna Sa kaya sai na Sagala a inner Pocket dina badan Tsoro ba Dan tsaro ๐Ÿ˜‰.

Na Wullashi ga Ekon Wanda ya kafeni da idanu yana mamakin Shatin hannun da ya gani shinfide a fuskata.


Nace "kai da Zoyi kuyi Selecting 3 more peoples kuje Ku gyara Mentor part,In The next 15 minutes , Dustinga kadai zakuyi ...Saura Ku mana Bincike...." Na karashe magana ina Hararar sa.

Sannan na danna Control dake Jikin makullin motar hannuna, kofofin Boot Suka Bude na kalle Uthman Nace "Ehm Othman kanaji.. carry Those bags ka Adana min su a Wajen ka, sauran Su 6ace mn da Gani"

Ekon yayi Gaba Dan Cika Umurnin na,yayinda Uthman ya Kwashe kayan Dake Boot sauran kuma sukayi Gabas,

nazeeru Abokin Uthman ya Nufoshi Dan tayashi kwashe kayan na daka mshi tsawa "Hey Kayi hauka ne?, Na saka ne?"


Tsuru yamin yana kallona bakina rawa yace "Ma'....am Taya shi z..an yi"


Na nuna mishi hanya "Oya Get lost"


Cikin jiki na Rawa ya bar Wajen yana waiwaye, Uthman na gama kwashe kayan nayi side dn UMMA Cikin Tsantsar Murna .

.a falo na Tatar da Abdool da Abokinshi Julaybeeb Suna kallon ball, Abokin na sanye cikin Kayan Makaranta yayinda Abdool Ke sanye Cikin Farar Vest da wando 3quarter Sun baje kayan Ciyeยฒ a gaba Suna ci Suna kallo,

Da alama Abokinsa ne ya biyo masa yaja shi da Shirme๐Ÿ˜.


Basu San na Shigo ba Saida na janye Tray din Fruits dnda Ke Gaban Su,Sannan Suka juyo Suna kallona.


Julaybeeb ya Gaidani na Amsa Cikiยฒ, Yayinda nake kallon Abdool da ya qureni da ido yana kallon Shatin Yatsun dake kwance bisa kunci na.

Na dage Mishi Gira Nace "Kallon fa?"

Ya daga hannu, hannun na rawa ya kai Fuskata ya shafo kumatuna Baki na Rawa yace "Aun... Ty what happen to ur fa..ce"


Nifa har na mance da wani Marin da nasha.

Nayi murmushi lokacin da kakus Ke Saukowa Riqe da waya Tana cewa "Kai duba min Wannan Wayan sai wani ....."


Turus Tayi Ganin munayferh Zaune a Falon, Da Gudu na Miqe tareda Rungume ta,
"Oyoyo kakus !,SURPRISE"
tayi baya kaman zata fadi "Ke ja'ira Cikani kar ki kaada Ni "

Na kama hannunta Nayi hanyan Fita Cikin dariya Nace "Kakus ki Rufe idanunki I have a surprise For you" Ta Rufe idanunta da Tafukan hannunta Abdool ma ya Bimu Dan jin kwafKwaf๐Ÿ˜.



A bakin Mota naja Nayi Burki Sannnan kalle Abdool dake ware idanu na harareshi "Close ur Eyes johr"

Shima Rufe idanunshi yayi yana dariya,


Ammee dake kallonmu daga cikin mota ta Share qwalla tana murmushi.

Saida na tabbata Sun Kulle idanunsu sannan na danna Remote Kofar backside ya bude Ammie ta Fito Tana Yar'Murmushi..

"Now!,OPEN YOUR EYES"

Har rigeยฒ suke Wurin Bude idanu ,Kusan A tare duk Suka ware idanunsu Akan Ammie.

Cikin Sassarfa Kakus ta tako Har inda Ammie Ke tsaye tana Share kwallar Farin'Ciki ciki na rawa takai Hannu ta Ta6a Fuskarta Cikin In'ina Magana mai nuna tsantsar Mamaki ko daburcewa zance ne oho๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ(Ina hausawan Suke)

Tace"Jee...derh, Ke..ce..." Sai kuma ta Rushe da kuka, Ammie da tuni Dama kukan takeyi ta Rungumeta cikin Tsantsar FarinCiki ta kasa Cewa Uffan....

Abdool kam kasa motsawa yayi Daga inda Yake ,Ai tuni yan'Aiki sun fara kawo Gaisuwa Kafin na ankare Ko'ina Ya cika da Yan kallo.

Ni kuwa Har Ga Allah na tsane ma'aikatan Gidan



Wai waya baya nayi Dan Bansan inda su Ameerah Suka Shiga ba, Tunowa Nayi ai lokacin da na Bude Su direct part dn Inna Rabi Suka yi,Sulalewa nayi na nufi Part din, A falo na tarar da Aunty Zee tana yiwa Suwaiba kitso,


Suna hada ido dani naga sunyi Wani Irin Zabura kaman sunga Fatalwa,infact they Look very Scared and Upset.


Kallonsu nayi Cikeda zargi nace"Aunty zee,Ina Yaranda Suka Shigo nan?"


"Yara kuma?, Anan ?,Uhm,Uhm!,Basu Shigo ba?," Suwaiba ta bani Amsa tana kame-Kame.


Muryan Ameerah naji Cikin Kitchen tana cewa "Taya ni can Faya Butewa"

(Ashe Lokacin da suka Shigo basu Sani ba,suna daki, sunyi Musu kaca-Kaca DA Parlor ,Sai Motsin Su Sukaji Shine fa Suwaiba ta zazzage su ta Fitar dasu,Shine fa suka dawo sai kace sun basu ajiya๐Ÿ˜‚,Zainab boyesu Cikin Kicen A cewarta ko waya kawosu Shi zai kwana A ciki, Dan basu kar6i baqoncin Yara ba ,baza'a zo a takura musu ba)


Da Gudu na nufi hanyar kitchen din , na ganshi a Garqame ,Dawowa nayi na dau Keyn da nagani saman Table ina Hararar su, na bude su


Sunyi Biji biji da kitchen din,Jikinsu sai qarnin Kwai yakeyi,Alamun sun farfasa Iya son ransu.


Naja hannunsu muka fice Ina Hararar su Zee..

Kafin kace me labari ya bazu ko'ina ,An sako matar JY ,Batareda Sanin ko ya Akayi ba labari ya fara Karade ko'ina Gidajen TV,Radio Stations da different Newscasters, Wasu harda qara karya akai Wai dama Chan ba 6atar dasuAkayi ba dama Chan DanSon Yawon qasashen Duniya ne Shiyasa ma yaqi dawowa, Da Maganganu marasa kangado Dai hk.


Su Abba Ae tuni labari ya iso Mishi, Yanzu haka ma ya taso yana hanya shi daya, Dan Fafur InnaRabi taqi binsa batareda ya sanar da kowa zai dawo ba,Dan dama yana Tafe ne da kyakyawan Albishir na Murnar Gama bautar qasan YaaJunayd da YaaAary dn ma bah๐Ÿ˜Ž..

Karfe 2:00pm YaaJunayd ya iso Nan fa Walima ya zama Biyu, na Murnar dawowan Ammie da kuma taya Copper Murna! Parte After Parte๐Ÿ’ƒ.

Ni kuwa duk Shagalin da Akeyi ban Sani ba, ina nan Rufe a daki Tunanin 6aqin cikin Marin da Nasha A gun hafsah ya Sani Gaba har Zazza6i nayi.

Yan Biyu suma ba'a Ganinsu Da an gansu anan Kafin kiftawan ido Za'a gansu tachan, kowa ya gansu Zaice mashaAllah nima nace hakan๐Ÿ˜˜.


*****


Hafsah kuwa ko a makaranta ta kasa Sukuni Saboda tasan Tabbas bazan ta6a barinsu ita da Umma ba, Batasan Hukuncin da zan dauka akansu ba!.


Janaan ma ta Fahimce hakan daga Gareta, Tayi tambayan duniyar nan Amma Amsar Guda ce, babu komai,

Ta tambaye ta me yasa banzo yau ba, nan ma Amsar itace bata Sani ba!, tayi trying numberna Amma har ya gama Ringing Ban daga bah.


Daga Qarshe Suka Rubuta min Attendance, bayan An tashi driver ya Daukesu Suka wuce Kd....



Sunyi mamakin Ganin Gidan maqil da Mutane, Saida Suka Shiga Suka Tarar da Abin Farin cikin da'ake ciki.

Sun Nemeni Sama da qasa Amma babuni babu labari na,Shiyasa hankalin su ya Dade tashi Especially hafsah DA tasan 6acin Ran da na fita dashi.

Saida Suka tambayi kakus tace "Ai tare ma muka dawo tareda Ammie Amma Tun Lokacin bata sake Gani na ba".

Hankula Fa suka fara tashi...

Sai a yanzu Jannan ta tuna Fa bata Duba Dakin mu na part din mu ba Dan ta gani a bude.

Aikua tana Shiga ta Ganni kudundune Cikin bargo sai makyarkyata nakeyi Da sauri ta Isa wajen Ta yaye bargon ta Daura hannunta saman Fuskata taji Zafi radau...


Zaro ido tayi tace"Neryfee Na shiga uku dama bakijin dadi ne?, bari na kira Hafsah "
Ta fada A rude tana Shirin Fita.

Cikin Qarfin hali na Riqe hannunta ina Girgiza mata kai Alamar kar taje

"Please don't!" Na furta a kausashe Cikin Qarfin hali.

Dawowa tayi Ta zauna saman Gadon tareda Dago kaina ta daura bisa Cinyarta

"Haba ,Neryfee ya zakice kar inje ,Alhalin baki da lafiya!, ko so kike ki kashe kanki!" Ta fada a Raunane kaman zatayi kuka.


"Jaann Nasan Abinda ke damu na!, Ba na Buqatar taimakon Kowa!" Na fada Cikin Disasshiyar murya Mai rauni, nima kaman zanyi kukan.


"Kinsan Abinda ke Damunki kikace?" Ta fada Hawayen tausayi na na Silalowa daga Cikin idanunta Dan Tsabar tausayi na.


"Jaanu" na kirata A hankali, Murya na rawa.


"Naam Nayfee...Tell me", ta Amsa Tana kara Rushewa da kuka.

" Stop crying "

Ta sa Bayan hannu ta share hawayen ta.


Na Rimtse Idanu na cigaba da cewa "Please idan an sadu da mace For the First Time Tana iya Samun Ciki?" Ta fada Cikin Karyewan kalamai.



"Eh mana!, Meyasa kika tambaya?, " Tayi maganan tana Duban cikin lumsassun idanu na....



Wani irin kankameta nayi Cikin Rawar jiki, Murya a dishe nake kuka "Jaanu Am Pregnant, Wlh ciki Gareni๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ"


















Chai how comes๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ





Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ




Fahnaan


๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 33_*

*Alqalami dashi nake Rubutu*

*Sunan Ku in baiwa Wasu Suyi karatu*

*Farkona da Qarshe na Soyayya ce Nasan kun fini Sani*


*Tarkona da nayi dani ku yakkama domin Ku zama maganiii*๐ŸŽถ


*Babu Sani babu Sabo duk Gun ke shirin bata ranku zai Ganii*โค๏ธ


*Takardata da Littafana bani inriqe Ku kuma Ku biyoni baya*๐Ÿ’ƒ

*Hausa novel Group*

*Littafan Hausa Novel group fans*


*Silar Halacci fans Groups*

*Fahnaan novel*

*Zazzzau Writters Fans groups* Etc
*gaskiya naga soyayya a zahiri da badini jinjina gareku masoyana nasan soyayyar ~Hawan-Jinina~ ce ta shafeni ina matuqar godiya gareku Allah yabar qauna ta har Abadah*

~~~

"Munayferh kinsan Abinda Kike cewa Kua?,Inaga baki cikin hayyacinki, Bari in Kira Driver ya Kaimu Asibiti, Tunda YaaAary baya nan...please take it easy...bari naje I will be back right Away...."

Da Kallo na bita har ta fice,daya bayan daya.

Da taimakon Janan na miqe na saka Hijab ,Muka Ratsa Cunkoson Jama'a,Babu Wanda ya lura da mu.


Ta kofar baya muka bi inda Driver ke jiran mu.


A.M SPECIALIST HOSPITAL.


Da taimakon Jaanu da Nurse aka kamani suka kaini daki, izuwa yanzu jikina yayi rau kamar garwashi, Gani da Raki, ban iya Ciwo ba!, ko Ciwon kai nakeyi Sai Anji ni bare Zazza6i fa.


Kwantar dani sukayi Dr ya Dan Bubani ya daura mn drip hadeda Allurar bacci.

Jannan na gefe Tana kallo Cikin mutuwar Jiki, Saida Na Samu nayi barci sannan ta Sauke Ajiyan zuciya ta dubi doctor tace "Doctor ya naga Kun sa Mata Drip Kwantar da'ita Zakuyi"


Doctor Dake shirin Fita , batareda ya juyo ba yace "What are you Expecting?" Ya fada Lokacin da ya Fita daga Room din.


OhhhDamn!, Wannan wane irin Golon Doctor ne?,

Da Gudu tabi bayansa, Har zai shige Office Dinsa yaji an kirashi.


Juyowa yayi yana dubanta har ta iso Gabanshi Cikin Qufula da qosawa tace "Baka fada mn Abinda ke damunta ba, ka daura mata drip, kayi mata kayi waje!, what next!, Haka Aikin Ku yakeneh ko yah?"


Doctor Ya dafa Goshin Sa cikin Damuwa yace "Muje na Rubuta miki magungunan da za'a siyo mata" ya fada yana Shigewa office Dinsa.

Binsa tayi taja, ya zauna A mazauninsa Sannan ya jawo wata Yar takarda yafara Rubutu.


Kuru janaan tayi mshi Gabanta na Faduwa Kardai ace dagaske Cikine Gareta๐Ÿฅบ.

Ya dau Some seconds yana Rubutu kafin ya dago ya dubeta tareda Miqa mata takardar ,

"Have dis.....Malaria Ne ke damunta, A matsayin Ku na educated People bai kamata ace Kuna kwana Cikin Sauro ba ,You need To take responsibility...."


"Mtchwww" janaan taja tsaki.

Ta cigaba da cewa
"Shine aka Gaya maka a Cikin Sauro muke kwana bah!, banson Shiga Shara ba Shanu fa ....just do Ur work Abege!,..." Ta Qarashe magana tana murguda mashi Dan qaramin bakinta.


Ganin ya kafeta da kallo yasa ya dage masa Gira "Yah dae?, banda maleria babu Abinda ke damunta?"


Kaman Wanda aka Zarewa laka doctor ya girgiza kai Alaman "ahah"


Daukar Papern Gabansa tayi,Tayi ficewarta..

Zaune take Bisa kujerar dake Facing Gadon da nake Kwance, Tunani kala kala takeyi,


Ta kura mn Ido Fuskar nan tayi fayau ga wani Rama danayi har na fara Bushewa, Ga Qashin wuyan da ya fara Fitowa...Akwanakin baya Tasan yanda nake Son zaman waje Ni kadai kuma da daddare... May be a nan Na kwaso Maleria.

maganganuna na dazu suka fado mata ~jaanu I'M pregnant wlh Ciki Gareni~


Da Sauri ta miqe ta nufi Office din doctor yana nan inda ta barshi....

"Doctor please.... Ehmm..."


Sai kuma ta Kasa qarasawa Ganin yanda ya kafeta da idanu Alaman tuhuma,

"What Again" Doctor ya fada Yana qara kafeta da Idanu..

Jaanu ta Sunkuyar da kai,Sai yanzu taji ba dadin yanda ya ya6a mishi maganganu dazun, Murya chan qasan maqoshi tace.


"Please dama Gwajin Ciki za'ayi mata"
.

Bai tanka mata ba ya Nuna mata Hanyar waje


"Get Lost"

Dagowa tayi tana Kallonshi,

"Ban Gane ba!"

"Zaki gane 6ace mn da Gani"
Simi ยฒ kaman wacce Kwai ya fashe mawa a Ciki ta wuce tana Kunkuni

Har ta kai bakin kofa taji yace"Kishiga wanchan Office din ki tambayi Sis khadeejah , Aikin ta ne "

Saida ta juyo ta Harareshi, Sannan ta Yi banging Kofar ta fice Cikin Fushi....


Ya bita da kallo kawai tareda Girgiza kai.

Janaan na fita ta Shiga office din Sister Khadeejah ta fada mata Buqatan ta Amma bata so a Sani.

InaBacci tazo ta Dibi jini na tayi Test sannan tayi Yan dube-duben ta.

Bayan Wasu Yan mintoci Sai ga ta , tace babu wani Ciki,Infact the patent in Question is Virgin.

Zaro ido Janan tayi

"Yanzu da Allah da Gaske kike ba'a ta6a saninta ba?"


Sister ta Girgiza kai Alaman Eh.



"Ehm ,please sister, A Dan taimaka mana Manaah!"


"Taimako kuma?" Sister ta tambaya da Alaman tambaya A tattare da ita.

"Uhm!..., please Fake Result zaa Rubuta mana akan test Dinnan da Akayi"

"Ban fahimce ki ba?" Sister Khadeejah ta fada innocently.


Janaan tayi Dan Gyaran murya tunawa da Dan raininwayon Doctorn Dazu "nothing kije kawai"

__________

"Doctor Pregnancy Result zaka Rubuta mana !, please be fast Sauri nake"


"Nace Bazan Rubuta ba ko Sani Dole zakiyi?"


A qudule janaan ta yagi Takardar Gabanshi ta dau Biro Tayi Rubutu da hannun Hagu,sai Rubutun yayi kama Sak da na doctots๐Ÿ˜† Sannan ta Juyo gareshi..


"Oya Sign and Stamp on it!,"

Shuru yayi Yana kallonta yana jinjina Karfin hali irin nata,


Janaan Ganin yana 6ata mata lokaci yasa ta damqi hannunsa ta dau Stamp dinda ke saman desk ta buga a inda ya kamata..

"Oya ur signature here" ta fada tana Nuna mishi Inda zaiyi signing.


"Dr Sufyan Mai zan gani haka?"
Muryan Aaryaan sukaji a bayansu.

Gaba daya Waigowa sukayi cikin Kidimewa janaan ta dauke Takardar da ta manna stamp.


Dr Sufyan yanuna ta cikin Alama ta Rashin Gaskiya yace "Sir Ehm..."

"Ehmm..?...What happened" Aaryaan ya fada cikin Kufula yana Kallon Jannan da ta firfito da idanu Sbd Tsananin Tsoro,da paper Riqe a hannunta.

"Lemme have DAT paper" ya fada yana Miqa mata hannu Alamar ta bashi.


Tsoro ya kuma shigarta lokaci Guda,bazata iya mshi musu ba, tana mamakin yanda Munayferh take iya kallon Cikin Kwayan idanunshi tayi masa Musu ko ince Rashin kunya.


Jiki narawa ta miqa mishi papern ta Fice.



Tana zaune a Kan Kujera Wanda ke Fuskantar Gadon da Aka Kwantar dani ,Tunani kalakala takeyi Idan YaaAary yasan da kwamachalan da Ta hada Ta kade har Ganyenta....yo ya Akayi yazo Asibitin?, ko dayake kaman akwai Sanayya tsakaninsa da Doctor Dan Rainin Hankali ~Dr Sufyaan~ .

Kusan 30mins tana Zaune ta kura mn ido ,bata San taYa Akayi suka Shigo ba ,Sai ji tayi Yace Yusrah (nurse ) ta bashi Allura, ya kalle Janan ya Galla mata Harara Wanda ya sanya Yan hanjin Cikinta kadawa.


Da sauri ta miqe tareda ja da baya ,Ya zauna kan kujerar da ta tashi , nurse ta miqa mshi Ruwan Allura da Syringe.

Juyowa yayi ya kallesu "Ku fita" ya furta a hankali kaman maijin Barci..

Fita Sukayi suka bar dakin ,yayinda yayimata Alluran da nurse ta bashi ,Nan take na faramotsa Yan yatsu na ,Sannan Bakina ya fara motsawa Cikin Layin Bacci na fara magana "Wayyo jaanu, Wlh inada Ciki Na shiga Uku na...๐Ÿ˜ญ"





Me janaan take nufi ne wai๐Ÿ˜’๐Ÿ˜.


Kun tuna Sufyaan ko?, Wanda Aka daura Auren Munayferh bayan nashiiii.....








Nana ke kika tilastani Typing yau With ur big head naki anan Tun na haihuwa๐Ÿ˜..

Wannan Page din naki ne my witch Allah ya Shirya mn Keh.













16th sep





Au






Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 34_*

.


Shuru ta kumayi kaman Anyi Ruwa an Dauke,


Saida taja Some Seconds Sannan ta Bude idanunta..


Dishi Dishi na fara Ganinshi ,Saida na kulle idanun Sannan na bude daya A hankali na kalle hannu na Wanda naji yana mn zafi-zafi ,Sai naAnkare Ashe Alluran Qarjn ruwa ce a jikina.


Zumbur na tashi a tsorace ina kallon YaaAary Wanda ke zaune a Gefena Riqeda Syringe Wanda ya Gama min Alluran Yanzu...



"Yaa Me ya kawo ni Asibiti" na tambayeshi ina kalle'kalle kaman Sabon kamu..



A hankalina fara Tuna Abinda ya faru,Rumtse ido nayi cikin tsananin fargaba da Tashin Hankali, Allah yasa Ba da gaske Ciki ne dani ba,Dan taga Alamomin masu ciki qarara daga Gareta.


InaCikin tunanin Ne naji YaaAary yace "Sannu ko" in a calm voice.

Kara Rushewa da kuka nayi "Yaa Wai da Gaske Cikine dani?" Na fada Ina shessheqar kuka.


Kukan da nakeyi ba Qaramin Tada hankalinsa yayi ba,Gashi Baisan manufar Janaan na Rubuta Result dn ciki ba, bare ya Samu Amsar da zai bani....



Miqewa kawai yayi ya bar dakin Ya barni Ina Gurzar Kuka.


A bakin Kofa ya Sami Janan tana Safa da marwa ,Anan ya tambayeta manufarta na Sawa a Rubuta mata RESULT din Fake Pregnancy....?


Nan take ta sanar Dashi Dalilin nata, yayi mamakin Sanin wato Ashe tasan da Auren, maybe ita ta Bata Gurguwan Shawarar Abinda tayi mshi jiya, Kuma yaji dadin hakan ๐Ÿคช , Ko ba komai Cikin nan da za'ace tana dashi Zai sa Ta rage Tambayan Takardarta, dan Bazata So Ace Cikin Hege Gareta bah,Da wannan ma Zai iya juyata yanda Ransa keso, Dukda yaji dadin shirin da Janaan tyi Amma sai bai nunamata ba ya Rufe ido ya Wanke ta da Masifa!, Wai tanada Gulman tsiya Inbanda gulma wayace ta tasa kunne akan Abinda yake Fadi har Taji Masu Sirrin Yanda Akayi Aurensu, Daga Qarshe ya Gargadeta Akan Kar ta Gayawa kowa wannan ya kasance Sirri ne a tsakanin su..


Jikin Janaan yayi Sanyi har ta fara nadamar result dinda ta Rubuta,Har ta juya zata Shige Dakin da Aka kwantar dani Sai taji yace "Idan ta Tambaye ki da Gaske Tanada Ciki Ki Amsa mata da EH, "


Ba tareda ta juyo ba ta gyada mshi kai ,Kafa na rawa tayi shivewarta.


Saida qarin Ruwan ya qare sannan ya maida mu gida Da kanshi, Lokacin har Abba ya dawo kuma ba Laifi naji sauqi Sosai, sai dai Abinda baza'a rasa ba, Dan Har waliman da Aka hada Saida na halarta,

Tun Ranar da Ammie ta dawo Na tare A gidan mu Permanently, Daga Kd nake zuwa School, da motar YaaAary,Kuma Mun shirya tsakanin mu da Hafsah a Zahiri, Tunda banida mai mn wanki sai ita, Amma a badini nikadai Nasan Irin tausayin da take bani idan na tuna da Marukan da ta yarfa mn,

Tun Ranar da YaaAary dawo damu daga Asibiti na daina Ganinshi, Hakan ba qaramin tada hankali nayayi ba, Dan inaso na Tabbatar da Zato na akan Cikin da dauka ina da shi,


Tunda Abba ya dawo, naga Ammie tana Wani kaffa kaffa dani, tareda bani Wasu tarkace Wanda bansan Anfaninsu ba, Kar6a kawai nake ina Antaya Wa batareda Nasan Anfaninsu ba .



Gashi Cikin Week Dinda ya wuce muka fara Exams Sai Nan da Two Weeks zamu gama.

Umma kuwa Tun Randa Abba ya dawo itama ta tarkato Kwarmatsanta harda Ramlah Suka Taho kd,Takura da Nuna isa kuwa sai Abinda ya qaru ,Koda Taga Motar Aaryaan A wajena Batayi mamaki ba,Dan yanzu tasan ko Abinda yafi hakan Aaryaan zai iya bani tunda Har zai iya nema na,


Aaryaan kuwa tunda Abinnan y faru , ko gaisuwa sama Sama sukeyi Da umma ko sau daya bai bata damar tambayansa Alaqarsa da Munayferh ba, ya lura Ta damu da tasn hakan

Kuma fa a Anan KD suke training , Ammafa babu Wanda ya Sani, cewa ma yayi An masa transfern wurin Aiki ne.


Yau Saturday Babu School


Ammie ta Aikeni Gidan Wai na Amso mata tsumin da Take Tsuma mana nida jaanu ,Dama ni Dan Naga Janaan na sakin Ranta Tana Sha yasa Nike Dan Sha....



Bayan na kar6i saqon Jannan ta jani dakinta,Muka dingi hira...

"Yawwa Jannu, ina kika Samo wannan turaren da kika bani Last week" na tambaya ina Dubanta.

Saida tayi dariyar mugunta sannan tace

"Tsarabar Da Aunty Saratu ta siyo mana daga Sudan ne"


"Ta6, Wannan turaren!, Ai ni na manta inda na jefa, nawa!,...Amma turaren matan Aure ne ko?"


"Eh ai Shiyasa na baki ki

Please Login or Register in order to submit comment