Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Na nufi kitchen kasancewar babu Abinda babu a kitchen Din Sai na fara Soya Irish ,Da plantain Gefe Guda kuma ina hada Arabian brown tea Saida na Gama hada komai na soya Qwai na Jerasu dukka a Dinning sannan naje na taso yaran yaran Nayi msu wanka na tasasu Gaba duk sukayi Alwala suka gudanar da sallar Asubah , Suna idarwa nayi msu wanka na shirya su cikin Qananun kaya nima na fada bathroom nayo wankan na shirya sai wani zubar qamshi nakeyi.

A parlor na barsu Bayan na kumna msu Cartoons , Na wuce don na tashi nawa mijin .

Yana kwance yanda na barci , kwanciya nayi kusa dashi nasa hannu ina shafa fuskarsa.


Cikin Barci yaji ana shafa Fusakarsa hakan yasa ya'dan bude Idanu don ganin kowaye , yana ganin nicce ya maida idanun ya rufe Cikin jin Dadin shafar Da nakeyi masa.

Da na lura ya farka izganci ne kawai sai na miqe na saita bakina saitin kunnensa na dage na kwada masa ihun da ya sakashi Miqewa A Rude kafin yasan Abinyi har na Gudu ina sheqa dariya, ina kaiwa bakin Qofa na tsayar da dariyar ina cewa

" kar ka Shigo mn Parlor da Dirty body dinka, Na hada maka Ruwan wanka ka farayin wankan Tukunna"


Bansan Lokacin da ya iso Gareni ba sai gani yayi ya jani ,yana Fadin Saidai Muyi wankan Tare ,babu yanda na iya dole na biye mshi tunda abin na qarfi ne kuma yafini qarfi ๐Ÿ˜ฉ
























Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธgabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ



1st Janโœ๐Ÿป
[1/2, 7:38 AM] Fahnaaanโฃ๏ธ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€

Na
๐Ÿค *Fahnaan*๐Ÿค

ยฉ๐ŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...โœ๐Ÿป*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...



*Chapter 98*



Haka Rayuwa ta cigaba da Kasancewa a tsakaninmu cikin farinciki, So da qauna Da Girmama juna.


Cikin hukuncin UbanGiji yau aka shiga Court don Gurfanarda InnaRabi , bayan Qwararan shaidu da aka gudanar a gaban kotu ,kotu ta yanke mata Hukuncin daurin rai da rai kaman yanda akayiwa sauran, bisaga Laifin kisa da aka tabbatarta aikata ,bisa jajircewan Barrister Junayd Aabaan, qarqashin Jagorancin DCP .A.A COSTEIN .


A lokacin da aka fito da ita duk rashin tausayina Saida na tausaya mata domin kuwa har yanzu Jikinta bai gama Komawa normal ba Ga kuma Acid dinda ya dame mata Fuska .

Ana Shirin tafiya dasu ta juyo ta kallemu ,Hakan yasa na Gane da magana a bakinta Take na qwace Hannuna dake riqeda na Aaryaan na nufeta da gudu lokacin da Police ke Shirin dannata Cikin motarsu.



Hawayen dake malala a idanunta suka kasa tsayawa ,Cikin kuka take Roqon na yafe mata, nan take na Gaya mata na yafe mata Nima na roqi gafara a wajenta take tace ta yafe mn , Kuma ta gaya mn tana mutuwa asirin da tayi mn zai Karye , Lokacknda su Abba da su suwaiba suka qaraso .


Cikeda nadama da danasani take roqon gafarar umma da Ramlah don tanajin tafi cutarsu akaina ,ta raba Umma da diyarta Ifrah har na tsawon Shekaru 20+, haka kuma Ta Quntatawa rayuwan ramlah wacce a Sanadin Haka ne yasa batasan Dadin Uwa ba .


Suwayba ,Zainab da Umar kuwa Kuka sukeyi tamkar Ransu zai fice domin kuwa ba qaramin tabo tabarwa yaran ba wanda har su mutu bazai ta6a gogewa ba inama ace Dukkansu za'a yankewa hukunci su tafi su huta da Ace suna raye Bakin mutane yayi msu kisa tsaye.


Shi kuwa Aaryaan ko kallon inda take baiyi ba bare tasa ran zaizo ya Agaza ko kuma ya tausaya Wani 'dan Jarida ne ya nufo Gunshi da mic dinsa camera man na biye dashi.

*_Dan jarida_* :-"Yalla6ai don Allah zamu iya sanin Sunanka?"


"Aaryaan Aabaan Custein"



*_dan jarida_* :- ''menene alaqarka da wanda aka gurfanar?"


"Tsohuwar matar Mahaifinane"


"A yanzu fa?"

"Ina ruwanka?"

"Kayi haquri yalla6ai, Kasncewarta Tsohuwar matan mahaifinka ce meyasa bakuyi mata Afuwa Kunyi maganin Abun a gida ba?".



"Wa'ennan Mutanen A dalilinsu na Shiga aikin 'yansanda meyasa kake Tunanin zasu sami tausayawa daga garemu bayan barinsu a doron qasa tamkar Ruguza ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ ne ,Kai ba tsohuwar matar Uba ba Ni ko Mahaifinane dakansa na samu yana aikata wani abun da ya sa6awa shari'a saina Gufanar dashi an yanke masa hukuncin da ya dace dashi ,ya kamata ku sani Aikin nan da mukeyi ba don kanmu mkeyi ba don Mu amfana Mu kadai, 'ya'yan mu mukeyi mawa, Domin sune Goben Nigeria idan Muka gur6ata qasar Tamu tun yanzu ta hanyar barin Gur6atattunnmutane a raye haka zasuyita hayyayyafa suna Qaruwa kafin Ka sani Qasar ta zama babu ,Don haka Babu wani maganar Afuwa a aikin dan sanda Aikina nakeyi"



"Nagode malam A.A , ....ehm....Naji kayi magana akan cewa Domin 'yannta'ddan ka shiga aikin dan sanda kana nufin Tunda ka kamasu an zartar msu da hukunci shikenan ka bar Aikin ko yaya lamarin yake?"



"Eh kusan Hakane ,Domin akwai wani aiki damuke shirin Zartaswa gameda KIDNAPPERS da suka addabemu Ina gama Zartar dawannan aikin shikenn zan bar aikin"


"Yalla6ai idan bazaka damu ba zamuso muji wane iin shiri ne kukeyiwa Masu kidnapping dinda ka ambata?"


"Kowa yasan 'yan Kidanapars Basuda wani ma6uyan da ta wuce daji , Tho mun tattaro dukka Dajukan dake cikin garinkaduna dukka zamu saka musu na'uran Da zata Rin nuna mana su dazarar sun sato Mutu kuma abin sha'awa anan shine Mun fara gwada abin a dajin da ya taho daga Kafancan Zuwa zango kuma cikin ikon Allah Mun fara kamasu Zamu gurfanar dasu inshaa............"




Bai qarasa ba yaji an wani jawosh ta baya ,Cikeda masifa nake hararar camera man din kaman idanu na zasu fito


"Kai wane irin jaki ne?, bakasan banbancin Gauro da mai mata bane ?,da zaka wani zo kana Daukan mijin mutun zaka yada a Satellite?"


"Haba hajiya meye haka"

"Mele...!, wlh ko labari naji ka saka wannan Videon rantse wlh sai Nasa an kulle Station dinku banza local Champ....." .


Ina fadin haka najashi Mukayi cikin mota ina haki, Don bala'i harta Yaran da na bari wajen Su umma mantasu nayi ,Dakaina naja motar har muka iso gida.


Muna isowa na fashe da wata matsanancin Kuka maiban tausayi ,Aikam na Gigitashi na kuma Rudashi ,A rude yake kallona ya kasa magana ,don yasan dalilin kukan nawa.


Ganin ina shirin Tara masa jama'a yasa ya jawoni kikinsa da niyyar rarrashi Take na shiga dukan Qirjinsa a shagwa6e ina kuka.

Dafe kansa yayi yanajin yana sara masa "ohh Sulthy ...please stop it meke faruwa ne...?"

"Ba kai bane kaqi Zantawa da innaRabi ka wani Tsaya kana zantawa da wasu damn 'yan jarida?"

Na fada a shagwa6e tareda sake shigewa jikinsa ina Shaqar qamshin jikinsa.

"Maaf .., Ni ko ganinta banasonyi Jinake kaman na shaqeta ta mutu na huta , kinsan Halina shiyasa na nisanta kaina da ita domin kuwa idan har Naje inda taje babu shakka saina Fitar mata da jini kuma babu abinda zai faru since Dukka police dinda aka hadata dasu yaranane..."

Sake narkewa nayi a jikinsa


"Allah sarki innanmu ,Tasha wahaala a wajena Tun farkon littafin nan takeshan AZaba a gurina babu kaman na page 7 , inda na kullesu ita da yaranta a daki na tsawon kwanaki uku ,koda zan Bude su banyi msu dasauqi ba saida Aljannuna na qarya suka chaskalasu๐Ÿ˜† ,Allah ka yafe mn Kasa Tuban da tayi Tubabbiyace, na tausaya mata kadan Don taimakon da ta ta6ayi mn a Karachi"


Murmushi yayi yana shafa suman kaina

"Tace ta maidake mafadaciya , But believe me tun usuli ke Mayyar fadace kawai qari akayi mki akan wanda kike dashi "


"Qarya ne ,Ni mu'minatun ce babu ruwana da fada"

"Aiko muslimatun ce Anjima zaki tantance abinda nake nufi ,Idan An karya asirin" .


"Abege Forget this trash, Tunda yaran basua Nan let's just do this... New Life..."


Ta qarashe da ......(They owe me no explanation)๐Ÿ˜…..



****


"Hello....Ramlahteey...kina jina?,....hope kinzo mn da Devices din .....ohhh, okay mu hadu a Gidan Umma ......yes i'll be there Right now, Thank you Ramlahteey...."

Bai qarasa ba yaji an wani fizge wayan ,juyowa yayi don yaga waye mai qarfinn halinbda ya isa ya qwace masa waya .


Kafin yayi wani yunquri har Na kara a kunne ina haki

"Ramlah or wettin U be...? , i don't need to warn you ki fita a sabgata ,Na rantse baki isa ki kashe Aurenki kice zakizo ki ra6e da nawa mijin ba, Gara ma tun wuri Ki sake Riqe aurenki kafin ki zama bazawarar titi , idan a baya na zauna dake a matsayin Kishiyar qaddara yanzu bazan Laminci hakan ba, Domin baki saniba ajalinki ke tunkaroki domin kina kashe Aurenki zan sa akasheki in yaso nima a kasheni daga yau karki sake Kiran Wannan Layin ki manta kin ta6ayin miji mai suna Aaryaan ki manta kin ta6a sanin Wata mace wai munayferh ki gogemu a rayuwanki...please"

Na fada ina nuna kaina da yatsa hawaye na taruwa a idanuna na durqeshe ina shessheqa.


A sanyaye ya Sunkuyo ,Ya zare wayan dake manne a Kunnena ya manna a nasa kunnen sa

"Kiyi haquri Ramlahteey kinsan Halin qanwan naki ,I'll be there Right now"

Yana Gama fadar haka ya datse wayan , Ya maida dubansa gareni Gani yayi na dafe saitin zuciyata ina fidda wano irin Numfashi a wahalce ,Cikeda tausayawa yasa hannu ya dagoni yana mn sannnu.

"Raaajaaa , You're.... cheating on ...me....."

sai na sarke da tari na rink'a amayar jini guda-guda bak'k'ik'irin dashi, take ya rude ya firgice yana neman zaucewa , Gaba daya ya rasa gane irin wannan kishin dake damun munayferh akan Abinda bata tabbatar dashi ba tana neman Hallaka kanta ,kai ya shiga Juya mn Cikeda tausayawa hawaye nabin fuskarsa ya kasa magana.

Cikin aman na kamo hannunsa daya tari ya kuma sarqemin na qanqameshi Cikin azaba numfashina na fuzga.

Cikin qanqanin Lokaci Jikina numfashina ya dauke Jikina ya sake ,Ganin kaman bana Numfashi ya qara kidimashi ya shiga Jijjiga ni yana Kiran sunana amma inaa Babu Amsa....












Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ



2nd jan
[1/2, 11:31 PM] Fahnaaanโฃ๏ธ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€

Na
๐Ÿค *Fahnaan*๐Ÿค

ยฉ๐ŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...โœ๐Ÿป*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...



*Chapter 99*


Suman da nayi yayi bala'in gigitashi, a firgice cikin tashin hankali da Tsananin Rudewa ya dauketa sai asibiti, take Drs suka Fara aikinsu.


Cikin qanqanin lokaci Asibiti ya cika da 'yan uwa da Abokanan arziki wasa wasa saida nakai tsawon Kwanaki uku bana cikin hayyaci na A rana na uku ne aka samu akayi mn aiki a zuciya wanda ake sa ran idan anyi sa'a zan iya rabuwa da ciwon Gabaki Daya.


Anyi aikin Cikin cikin hukuncin ubangiji kuma naji sauqi har an sallamoni.

Wani sabon Abun mamakin da Aaryaan ya tashi dashi a ranar , Dakaina na bashi haquri akan abinda nayi ranar da naji suna waya da Ramlah Mamaki ya cikashi har ya kasa 6oyuwa a fuskarsa don yasan Munayferh bata ta6a laifi ta bada haquri saidai tayi laifi a bata haquri nan take ya yafe komai ya wuce dama company dinda ramlah ke aiki ne suka ba Contract din hada Devices dinda zasu riqa Leqo msu asiri a dajuzzukan dake fadin garin kaduna wanda hakan Zai taimaka wurin kama 'yan ta'ddan dake garkuwa da yaran mu suna 6oyesu a daji don Neman kudin Fansa.


A ranarsu Hafsah da sauran Suka dawo Gidan , Kuma a ranar naji labarom da yafi faranta mn rai wai hafsah na dauke da cikin Watanni Uku.

Allah kenan Mai kyauta da qari , Komai na rayuwan nan zuwa take ta wuce, Idan munyi haquri mun jure wahalhalun dake cikin ta cikin qanqanin lokaci Komai zai zama kamar ba'ayi ba ,labarin cikin Hafsat ya Haddasa Farin Ciki cikin dukka ahali guda biyu both Family dinmu da nasu Hillal kasancewar Shine babbar 'Da a family din Kuma ana saran Shine zai haifan musu babban jika.


Cikin Hukuncin ubangiji Hada Devices dinda companyn su ramlah Sukayi yasa An fara ,Samun nasara wurin Kama 'yan ta'addan kuma hakan Ba qaramin Daukaka ya kawowa companyn ba ,Kasancewar Ramlah itace ta jagoranci hada Cameras din Sai Govenati ta karramata tareda bata kyauta ta musamman a matsayin Mace ta farko da ta fara gada ireiren wainannan abubuwa a Qasar nan tamu (๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ) ,haka kyma sun karramata hadida bata Kyaututtuka da dama, Ciki harda Visa Zuwa Finland don Aiwatar da wani work shop dinda yi na qarawa Computer Engineeres ilimi akan yanda ake hada watoyin hannu, wanda zai gudana nan da sati uku, da farko saleem qin amincewa yayi amma da aka gaya mshi Na sati daya ne Kuma mace bazata tafi ita daya ba saida Muharraminta ba shiyasa ya nutsu ya Amince Suka tafi tare ..


****


Yau dakaina Naje na dauko yaran Daga makaranta , Da shigana Sai na Iske babu su A inda Na saba , Malamarsu da na iske anan na tambaya ta gaya mn suna Staff office batareda na tambayi me sukayi ba.


Da isana Staff Room na iskesu Sunyi Jugum jugum dukkansu Su (hasnah ,Haseen Sadeeq ,Humdah ,Aaban , Munayferh, Yazeed) ,HM nata zazzalesu Gefe guda kuma wasu yarane suma sanye da Uniform suna Kuka.


Ina shiga Sadeeq da Hasnah suka Rugo suka Rungimeji suna Kuka, Shi kuwa Haseen Ko kotsawa daga inda yake baiyi ba Sai faman huci yakeyi ,Sauran suma suka zugo tareda Rungumeni .

Cikeda takaici na dubi HM din ina tambayanta Me ya faru? ,mai sukayi mata take zagan mun su haka budar bakinta cewa tayi wai hasnah ce tasa Sadeeq ya hau bishiya ya tsinko msu mango da yake an Hana yara hawan Bishiya shine da wannan Yarinyar (wacce na iske tana haki) ta gansu tace zata sanar da Head teacher dinsu duk Suka tarun mata sukayi mata Duka.


"Yanzu don 'dan wannan Abunn kike zagar mn diya?, kinsan Zafin Haihuwa kuwa na tabbata baki san Zafin haihuwa ba shiyasa kike zagin mn yara Akan wani damn bloody Creepy mango Wanda qila ma Bai gama Nuna ba, Don't worry a yau dinnan Zamu Ciresu Duka a makarantar don na lura ba Ganinsu kikesonyi ba ..."


"Sorry ma'am Ehmm...i don't wish to hurt u ....."


"To hell With U and Ur Stinky office common , Give the way make i pass"


Na qarasa tareda Jan hannayensu Mukayi waje, cikeda jin haushin Reactions dinta akan Yarana.


Ina fita a Office din Kiran aaryaan Ya shigo wayana .
Murmushi Nayi hadida dauka na kara a kunne na tareda sakin Wani Irin Qasaitaccen murmushi

"Amincin Allah ya tabbata a gareka Mijina Abin Alfaharina ,Da fatan kana Cikin farinciki da kwanciyan hankali.....Hmmm Na daukosu yanzun haka ma Ina hanyar Gidane ,.....Ohhh fine.....Companyn da na qona maka zaka ce......Tho ganinan Zuwa Ranka shi dade.... Hhhh au irin sarautar da ka bani kenan ..... A'ah Zanfi dacewa idan ka bani sarautarka Kai karan kanka da duk wani abun da Ya danganceka...eh harda ita aini natace Itama tawace....okay sainazo Choppa Kiss Muah๐Ÿ’‹....bye"

Na qarashe da sauke wayan Ina Murmushi, hasnah dake Kusadani tana Kallo a dayan wayana ta dago ta dubeni.


"Ummie, da daddy Kika gama waya i guess?"


"No da mummy na gamawaya ba Daddy ba ,Gulmatu....ke komai sai kin sani"


Gabaki daya sukayi dariya munayferh dake Kusa da ita tayi mata gwalo daga nan sai dambe ,Ban sake tankasu ba Har sukayi suka gaji haka suma mazan Sabgansu sukeyi inda sabo Na saba da wannan Halin nasu.



Daidai tsohon Companyn Da daddy ya bawa Aaryaan a shekarun baya (har yayi mn laifi na qonaaaa) daidai nan na tsayar da motata na fito cikeda mamakin sauyin da na gani a wurin an wani gyara shi sosai anyi Expanding dinshi ya koma qaton Ma'aikata Wanda akalla girmansa zaikai Girman Asibitin Shika dake Cikin garin zaria Haqiqah duk wanda yasa asibitin ABU shika dake Cikin garin zaria yasan Irin fadi da girman da yake dashi.

Haka kuma da ka ga tsarin Ginin da kanka Zaka Tabbatar da cewa ba Maginan Ciki sukayi Ginin ba kuma duk wanda ya Tsara Ginin gwararrene kuma wanda yasan Aikinsa .


Gabaki daya na shagala da kallon yanda tsaro da Haduwan Ginin yayi ba ni kadai ba harta yaran suman tsaye sukayi suna kallon zallar haduwa .

Ji nayi an ta6oni ta baya wanda hakan yadan so ya tsoratani ,Juyowa a dan Rude ganinshi ne yasa na fada jikinsa tareda Sakin murmurshi hadida sauke ajiyan zuciya, Daidai saitin kunnena Ya rada mn

"Your Children are watching"


Daidai lokacin da sadeeq , Hasnah da Munayfer suka rugo wajensa a Guje tareda qanqameshi suna Dariya.

"Uncle Daddy Kaina ka kira ummy yanzu ko?"

Kallona yayi lokacin da nake watsawa hasnan wata muguwar harara .

Aaryaan yayi yar gajeruwar dariya ya Dagata sama Tana Dariya.

"My Haseenah Kin Cika Surutu like parrot"

"No daddy You always Say Like Ummy Why Parrot today?"

Ranqwashinta nayi ta baya Hadida zungurinta a goshi ina dariya, Naja hannun Humdah da sadeeq mukayi ciki sauran suka mara mana baya .


Nan fa Bakina ya kasa Rufuwa Ganin tsari da kyawun wajen wanda Ciki yafi Wajen kyauw da tsaruwa Sosai Nesa ba kusa ba ,Inba dakaina na kawo Kaina Wurin ba da sai narantse Ginin ba a qasar mu yake ba, Kyan wajen ya gigitani sosai sai yaba Wajen nakeyi yaran na tayani shikam uban gayyan sai murmushi yakeyi yana jin dadin Ganinmu dukka cikin farinCiki.

Munyi tafiya mai nisa duk a cikin companyn Muna zagaya wurare Batareda nasan Ko companyn menene ba, Kyawun wajen ya hanajin Jin nisan tafiyan da mukeyi.


Mamaki ne ya kamani Ganin Motocin Gidan mu a Parking lot B ,Tunda mun baro P-lot A a farko.


Dukda mamaki da tarin tambayoyin dake Cikina ban yarda na Tambayeshi wani Abu ba dangane da wurin Don na lura ko na tambayeshi ba amsa zan samu daga gareshi ba.



Sai wani Binsa mukeyi kaman Raqumi da akala, muna Wuce Buildings da dama Gabda zamu shiga ainihin inda yake son mu shiga Mitocin su Janaan suka danno kai dukkansu Su Biyar Din Junayd da janaan , Hilaal da hafsah wacce a halin yanzu Cikinta ya fara nauyi ,Sannan Isma'il da ifrah , Hydar da humaydah wa'enda suma a halin yanzu Sun Hau kan Layi๐Ÿคฐ๐ŸผSannan Ramlah da saleem,


Tsayawa mukayi muka jirasu har Suka Fito Yaran na Ganin iyayensu Kowanne ya ruga ya rungume .


Humdah dake manne dani ta dubeni ta dubi aaryaan ta sake Duban Saleem da ramlah tace

"Mummy ....Ummy....Uncle Daddy....Big daddy.... I think i'm the Luckiest angel in the world, Two dadies two mummies ,Three Brothers, One Lil sis ohh yeahhhhhhh"


Ta qarashe da buga tsalle ta rungumeni kana Ta sakeni ta kuma rugawa ta Rungume Ramlah da Saleem Cikeda farinCiki muka shige Ciki.


Muna shiga ciki ya kira janaan Ya rada mata wata maganar da ni kaina banji ba kallonsu Kawai nakeyi ina ta6e baki don na lura Gulmar tasu ce basuso naji , Take ta kwashe yaran (Ban san Inda tayi dasu ba) ,Suka shige Ciki Nima yaja hannuna Muka shige wani 'yar qaramar daki a entrance door dinshi An manna Plastic band mai rubutun *Dressing Room* _Me zamuyi a Dresaing Room kuma?_

Kafin na qarashe Tunanin da nakeyi har ya jani ya shige dani Ciki.


*_Duk yanda nakaida Iya gulma yau Alqalami na ya hanani Daukan Rahoto๐Ÿ˜ซ_*


*~ยฐโ€ขAfter 20minsโ€ขยฐ~*


Kusan A tare muka Fito kusan a tare Gaba dayan mu mun sauya shiga.

Sanye yake cikin baqaqen suit , sai White shirt dake ciki da Blue neck tie irin dan qaraminnan, sai blue handkerchief daya dan leqo ta aljihun gaba ,Kansa babu hula amma Suman kansa ya kwanta Luf sai sheqi yakeyi wanda yake nuna ba qaramin gyara yakeskesha ba , Hannunshi na haggu na sanyeda baqar agogo rolex sai baqaqen canvass a kaffafunshi , fuskarsa Manne da Sun Glass wanda Ya dace da irin Kayan.


Nima sanye nake Cikin wata material gown Sky blue da akayima ado da Royal blue . Sosai rigar ta amshe qirar jikina tamkar a jikina aka dinka.


Saida muka fito sannan Ya tsaya yana dubana kaman mai shirin tuna wani abu Nima shi nake Kallo ,Chan ya dan nisa a sanyaye ya Fitoda Wayansa daga Cikin aljihunsa ya danna wata number tareda karawa a kunne ba'a 6ata lokaci wurin dauka.


"Hello Philips.... kanajina .....Yeah Ka Gayawa khadija ta siyo Mn hijab dinkakke 4yeards Royal blue dinkin mai hannu....please I need it in the next 20 mins....meet me In Dressing Room5...kk bye"


Yana gama wayan Ya datse wayan Ya sake Kiran wata number shima ba'a 6ata lokaci ba wajen dauka.


"Wa'alaykissalam.....where are you?.... Ahto bismillah shigo mana..." Cikin 'dan qanqanin Lokaci saiga wata 'yar Budurwa Doguwa Hannunta riqeda Makeup kit , Nan take yayi mata jagora zuwa ciki nikam nawa ido don ban fahimci mai ake Shirin yi ba.

Yana zaune har Yarinyar ta gamayi mn Makeup ta fice ,Saida ta fita ya maida duban sa Gareni batareda yayi magana Ba Yaja wata doguwar tsaki.


"Baby lafiya Why the hisss?"


Sake jan Tsaki yayi

"Wlh danasan Haka zakiyi kyau idan akayi mki makeup dinnnan Da ban Gayyatota ba , Please Muje Na wanke maki zakifi Kyau A haka babu Makeup"

Yayi maganar a raunane Kaman mai shirin yin kuka ,Ta6e baki nayi hadi da Miqewa daga kusadashi na sauya wajen zama ina harararsa.

"Sannu sara Mai baqar Buttocks, Wlh babu abinda zan wanke saida a fasa fucking damn Abinda kake 6oye mn or whatever, Amma baza'a goge mn makeup dinda nasha Zaman 20mins akanshi ba"

"Ko kinso Ko kinqi sai An Goge makeup dinnan"

Ya qarashe da damqe hannuna Yayi hanyar toilet dani .


Da qarfi na ja hannuna da niyyar kar6ewa amma Riqon da yayi mn bana wasa bane.


"Wlh baka isa Ka share mn Makeup ba na rantse ko ka Goge mn saina kira wata anyi mn wani ,Mugu kawai"


Sakin hannuna yayi yana qare mn Kallo ,Cikin qanqanin Lokaci har idanunsa Sun Sauya kala.


"Sulthy nine mugu?"


Ya fada uana nuna kansa
"Eh kamafi mugu"

"Sulthy ni"

"Eh kaifa"

A qarashe da murguda masa baki.

Daidai nan akayi knocking daga qofa, Ya barni don Yaje ya bde qofar yana juyawa na mara masa baya, bude qofar dazaiyi na mamayeshi ya fice da gudu ina kyalqalan Dariya.


Saqon da ya kar6a a hannun Messenger ya Jefa mn Yana hararana nima harararsa nayi na dauka na ciroshi daga cikin ledar .

Dogon Hijabi ne wanda duk tsawona saida yakai mn qasa ,Har na juyo zanyi magana sai naga fuskar nasa a Hade hiyasa na Hadiye abina .


Take na saka hijabin wanda ya fito mn da asalin kyawuna na zura hannun hijabin ina 6ata fuska.

Murmushi yayi a karo na farko ya Riqo hannuna a kunnena ya rada mn

"Komai naki dabanne meere cheeku ko wane irin kaya kika sa Sai yayi mki kyau ya kuma dace da yanayin Jikinki ,inaga Ko tsunma kika sa zaiyi mki kyau saboda je din ta dabance"

Ya qarashe da 'yar gajeruwar dariya.

Turo baki nayi hadida jefa mshi Ledar hijab din cikin shagwa6a nace

"Just tell me the truth don't bribe me with Ur sweat words"


Dariya yayi sosai har saida fararen haqoransa suka bayyana ya riqo hannuna Muka Fara tafiya, mun danyi tafiya mai dan nisa kadan Kafin mu isa wani qaton Hall, Wanda tun daga wajensa Naje ganin yanayin tsari da adon da wurin yasha, a zuciyata sai mamakin Dalilin da yasa mukazo wajen nan Nakeyi kuma Unexpectedly.


Koda muka shiga Hall din Babu wasu mutane da yawa a cikinta daga Su Janaan dasu Saleem sai yaran da daddy Abba ammie Ummie umma aunty salma kakus da qannena Babu baqi sai Dr safwan da matarsa sannan Kuma Jarumin Littafin Maqaryaci (littafin da zai Biyo bayan wannan) wato Mahfouz Chilli๐ŸŒถ๏ธ duk fadin wajen Kuwa , Yara sai Qiriniyan su sukeyi suma har an chanza msu kayan makarantar dake jikinsu.

Shigowan mu yasa wajen Ya dau shewa da hayaniya ,Taku mukeyi with passion Cikin wani irin salo mai cikeda Natsuwa, hannayenmu manne da na juna haka kawai sai na Tsinci kaina da Kunyan su Umma Hadida fargabar Abinda ya tarasu anan.

Kai tsaye wajen Kujerun da aka tanadar mana Na alfarma muka nufa, muka zauna Kaina a Sunkuye.


Cikin qanqanin Lokaci ,Mahfouz ya fito yayi addu'a tareda bayyana dalilin da ya taramu anan wato Kammala Ginin Asibiti At the same time kuma ma'aikatar Hulda da Chemicals wato Laboratory Wanda Aaryaan ya mallakawa matarsa *Munayferh* halak malak.


Daidai lokacin Na dago a Rude na dubeshi na samu bani yake kallo bamah , hankalinsa na wajen mai gabatarwa.


Hannu nasa na 'dan muntsuleshi wanda hakan yasa ya juyo gareni batareda ya shiryaba.

"Kai Kaji abinda Kunnena suka jiye mn kuwa?"


Murmushi

Please Login or Register in order to submit comment