Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Shekara daya suka sato daddy ,


Haka shima Isma'il yana Nasa qoqarin Wajen Tabbatar da Ya saka ido kan Cameras Dinda ya Zagaye Gidan Dashi Don zai taimaka matuqa Wajen Gano shirinsu na gaba don bazasu ta6a bari su ganosu ba.

Shi kuwa Hydar tare Suke aiki da Aaryaan Wajen Binciken Gidan da kuma Su Hajiya Larai...


****

Zaune nake Gaban Daddyna Ina Yanke masa Farcen qafansa ,kallo daya zakayi mn ka fahimci Tsantsar Raman Da Nayi ,Wanda Ko ba'a Gaya ba Nasan Damuwa ne da ya addabeni a kwanakin nan ,Nayanda Aaryaan ya Wani shareni yafi bawa Aikin sa muhimmanci akwanakin nan ,Kwata Kwata baya samun Lokacina , a zahiri kuwa Kyaleni Yayi ganin nima ban damu dashi ba kuma yajida Abinda Ya dameshi ,In ya gama ya waiwayoni.

Sai da na Gama Yanke Mshi farcen nasa kafin na dago ina Murmushin Qarfin Hali.


"Daddy na Gama"

Murmushi Yayi ya Shafa kaina

"Beetee dna ta Girma kenan ,Kinga yanda Farcen nawa yayi kyau kuwa ,ko wanzamai Albarka"


Dariya Nayi sosai don Har Ga Allah naji dadin Maganganun nasa.


Shima Murmushin yayi don burinsa ya faranta mn ,Yaga dariyana Wanda yayi wahalar Gani a wannan kwanakin.....



Gyara zamansa yayi ya kirani a kausashe

"Beteee"

"Na'am daddy"

"Ina Aaryaan ne?"


Saida Gabana ya Fadi Jin Sunan da ya ambata ,Amma sai na Wani waske na 6ata Fuska tareda Fadin

"Inaga kaman yana daki"


"Oya tashi kije Ki tayashi Hira"

"Kaaii daddy Korata kakeyi ne?"

"Eh tashi ki tafi banson musu "


Jin yanda yy magana babu Alamar wasa a tattaredashi yasa na tashi ina Turo baki a dole y takurani ,Chan qasar Zuciya ta kuwa dadi naji da Yace na tafi....



Ina Fita kai tsaye Dakin mu na nufa ,Amma babu shi Hakan yasa Nayi tunanin ko yana Part Dinda aka Sauke su hilaal ,Don haka na fada Bathroom Nayi Wanka Na Sauya Zuwa parkistan Riga da Wando Rigar Royal blue mai adon Golden Wandon ka sky blue ,dankwalin Rigar wacce take Sky blue na Yafa a wuyana ,na saka 'Yar qaramar Hula Royal blue mai ratsin Sky blue, na saukar da gashina yabi gefegefen Fuskata.


Dukda banyi kwalliya ba ,Nayi kyau sosai kaman na sace kaina na guduπŸ˜….




Ina fitowa kai tsaye Part Dinda aka saukesu na nufa, a Parlon Na iskesu kowannensu Dauke da system yana Latsawa, kallonsu Nayi 'daya bayan 'daya amma banga Aaryaan ba, na kalle hilaal da ya dago yana Dubana Nace


"YaaHilaal ina yayan Hafsah?"

Gaba daya suka dago Suna Dubana ,Hydar ya harareni yace

"Wanene kuma yayan Hafsah?"


Nima hararar shi Nayi Nace

"Ina Ruwanka?, kai na tambaya?"


Ismail yaja tsaki yace

"Ke yarinyar nan na lurada Ke bakida Hankali ,Mijin naki kike Kira yayan hafsah?"


"Kaine babbar Mara Hankalin Ai , Ina ruwanka dani?, kome nakirashi ina Ruwanka?,na kasa da Kaine? Amebo kawai magulmaci mai kamada 'yan tasha kawai"


A Fusace Hydar ya miqe yana Auna mn Wani irin Mugun kallo Yace

"Ke yarinyar nan mu Zaki gayama tasha ,Mu da aka haifemu a tasha ?"


Ya juya ya kalle su Hilaal DA Gaba dayansu Shi Suke kallo yace

"Ku duba Ku Ga mutum jarumi kamam A.A , amma yarinyar nan ta siye manashi Ta mai dashi kaman Bawanta ,ya sauya Komai nasa zuwa sunanta sai kace ita kadai ce mace a duniyar nan, ya rasa wacce Fada Soyayya da ita sai Mara kunyan nan Wacce bata San darajarsa ba, yana Mijinta amma da yayan Hafsah take kiransa ,Kumafa da yana nan Amsawa Zaiyi ,Amma tirrr da soyayya irin nashi"



Isma'il ya kar6e da cewa


"Wlh da zai bamu hadin Kai ko ,da mun shimfida mata Wani shegen Rashin mutunci ,Mun gyara mata zama tasan Na Gaba da it...."


Maganar sa ya maqalene Sakamakon shigowar da Aaryaan yayi yana Fadin.


"Lafiya duk kuka bar Aikinku kuka kama Surutu bayan... Ehmmm"


Ya kasa qarasawa Lokacin da idanunsa Sukayi arba dani.

Kallonsu yayi hakan yasa Duk suka fice a Dakin
.



Sunq Fita ya maida dubansa Gareni yana Murmushinsa mai qawata Fuskarsa.


"Sulthy Shigar nan yayi mn kyau"


Kama quguna Nayi tareda yin Wani Far da idanu Na kada harshena Nace


" Tho Shigar ce tayi kyau ko kuma nice nakeda kyau din "


Dariya yayi Wanda ya Bayyana fararen Haqoransa yace


"Ke din kece mai kyau din Amma kash Bukeken Cikin nan ya Kwafsa mki"


Turo baki Nayi Tareda kai mshi duka a kirji Cikin shagwa6a Nace

"Eh naji nadai Fika kyau"


Riqe hannun yayi yana Dariya

"Yarinya Qaryanki ,Kema Kinsan baki iya Comparing kanki dani see me see handsome Fancy boy Wanda 'yan mata Ke Suma idan sun ganni"


Cusa kaina Nayi a qirjinsa na tureshi ya Fadi ta baya kan Rug Yana dariya ,Still hannuna Na Riqe a Nasa
A shagwa6a kaman zanyi kuka nake fadin
"Wlh bakada kyau kai mummunane Ko Baby Haleemah da ta kwaso kamannin Umma tafika kyau"


Murmushi yayi kawai don naso na Sosa mshi tabon da Yake Qoqarin Batarwa A Zuciyar sa ,sakin hannuna yayi ya shigayi mn Chakulkuli ina Dariya kaman zan shide.


Ganin bashida niyyar dainawa yasa na sauka a kansa na koma Gefe ina maida Numfashi...




Tasowa yayi ya zauna kusada Ni yana Fuskanta ta a hankali Ya Furta.


"Ina Qaunarki Sulthy na, I know you Also love me, Ko? ,Talk To me kina sona ko?, Never throw away chance to say β€˜I love you’ to the people you care about because we are not promised tomorrow , When I dream, I dream of you. Maybe one day, dreams will come true. Because, I really love you and Inaji a jikina one day You'll Look into my eyes and Say I LOVE YOU A.A"



Hararar sa Nayi na Tsuke Fuska Kaman bani na gama Qyalqyale Dariya yanzu ba na ce

"Kaiba wani kyakkyawa bane sosai ba fa, ka Sani?, Kuma baka da Abinda Zai rude zuciyata Har Naji na fara sonka ,Taya akayi na Amince na Aureka at the first place ma?, Kawai na taimaka maka ne Fa ba Wani abuba Ganin yanda Yake Neman zaucewa Har kake Qoqarin Halaka kanka akaina ,Amma ai Nayi haqurin zama dakai sosai idan ba haquri Taya za'ayi na zauna fa mutum mai dukan mutane? Na tsaneka Aaryaan Bana sonka, kuma bazan ta6a sonka ba""












πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†

Nayi gabasπŸšΆπŸΌβ€β™€οΈ






19 nov✍🏽
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
**HAWAN-JINI NA*
~{uwar mijina* πŸ’”}~
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
NA
*🀍Fahnaan🀍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

Β©πŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_Aβ€’ Wβ€’ Aβ€’_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._



Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…...


_*Chapter 68*_




.
Aaryaan yayi Wata qasaitaccen Murmushi Mai Qara qawata Fuskarsa ,Ya Jawoni Jikinsa tareda Manna mn Kiss a Goshi.

"Calm down ,Baby I know very soon Zaki soni , inaji a Jikina "


Lumshe idanuna Nayi ,Tareda Sauke ajiyan Zuciya Cikin Jin dadin Kalamansa na dazu Nace

"Yayan hafsah Inajin yunwa "

"Me Zaki Ci?"

"Dafaffen Irish"

Zaro ido yayi kaman Zaiyi magana,Amma da ya tuna laluran da nake fama dashi sai yayi shuru ,sannan ya daga Ni daga Jikinsa ya miqe ya nufi hanyar kitchen ,nima na biyo bayansa.

Chak ya tsaya ya waiwayo Yana Dubana ,Kafin ya samu damaryin Wata magana Har na kar6e da cewa

"Ka tafi Zan dafa dakaina"

"Ke bakyajin Nauyin Jikinki ne?, Nifa kar ki wahalar mn da baby Jeki zan hada Miki kinji"

6ata Fuska Nayi kaman zanyi kuka Nace

"Nifa Har mantawa nake da Wai inada Wani Ciki ,Inba dadaddare ba banajin komai a tattaredani saidai kuma Nauyin Amma Tunda ba Wani nauyi bane ai hikenan"

Murmushi yayi kawai tareda Girgiza kai Wato har mantawa nake da wai inada ciki ya qaya a ransa tareda qarasa cikin kitchen din Batareda yace komai ba ,Nima na bi bayansa .


A tare muka hada Abincin ,Amma Tun Wajen wankin Irish din naji na Gaji ,na samu wuri ina hutawa Yayinda shi kuma ya qarashe Girkin Yana dan Satan Kallona Yanda Nake Wani Yatsine Fuska kaman wacce Nayi Shekara ina Aiki bahutu.


Qarasowa yayi yana Cire Apron Dinda Ke Sanye Jikinsa Ya dubeni yace

"Sulthy are You okay?"


Girgiza kainayi Alamar A'a da sauri ya Qaraso ya zauna kusadani yana Dubana Ina Ke miki Ciwo?, Cikin ne?, Saida Nace Karki Zo nan ki barni na hada dakaina amma kika qi ,Gashi kin tsokalo wa kanki Ciwo .


Dariya Nayi Ganin yanda ya Wani rude

"Babu komai fa ,yunwa ce kawai "

Shima dariyan yayi yace

"Kinsan banason Wani Abu ya Tabamin Lafiyan Babyna ko ,Oya Jeki Sitting Room Gani nan zuwa "

Saida ya taimaka mn sannan na samu na miqe na nufi Sitting room, shi kuma ya Dauko Abincin da ya hada mn ,Da kansa ya rinqa bani Har naci na qoshi ,ina Gamaci Na Amayar Ban bar ko kadan a Cikina ba dole ya nemo mn Kayan marmari Wanda Zan samu yariqe mn Ciki Kafin Ya siyo mn magani.


Su hilaal na Fita kai tsaye Dakin da Ake tsare su Larai suka nufa .


Kowannen su zaune Gabaki daya kamanninsu ya sauya


Hilaal ya dubi Larai da tasha tabon sallah a Goshi Sakamakon Fadowan da tayi Garin Neman hanyan Guduwa


"Ke Larai ,Kin fiye taurinkai fa ,Ki tuna kinada 'ya'ya Da Miji kuma Suna Buqatar ki , banaso na maida su marayu ne shiyasa Nake tsaronku nan,Amma this will be the last time idan na tambayeki kika Sake yi mn qarya saina Fasa kanki da Bindiga" ya Fada yana Pointing Bindigar a Goshinta.


Larai fa ta Kidime Ta rude iya Rudewa bata San Dalilin da yasa ta kasa gaya msu Sunan wacce ta Aikosu ba ,Alhalin Ga Sunan a bakinta furtawan Keyi mata wahala.


Kaman Isma'il ya lurada hakan , shiyasa ya dauko Ruwa daga cikin Fridge dindake Parlon ya Kwance marufinshi Ya nemi Wuri ya zauna yana Tofa addu'oi a Ciki.ya jima ynayi kafin daga Bisani ya Miqe ya taka Har I da take ya miqa mata Fuska babu Alamar wasa yace

"Oya Shanyeshi Yanzunnan"

Jiki na 6ari ta kar6a ta fara sha, bata kaiga Gama sha ba ta fara Wani Uban attishawa Wanda ya sanya ta wurgar da Kofin Ruwan ta shigayi Tun tanayi a zaune Har ta Koma yi a Kwance ,Gaba 'daya suka zuba Mata ido Don basu fahimci Komai ba.


Ta dau tsawon Lokaci Tana tarin ,haka Babu Wanda ya Fasa KallonTa Cikeda tambayoyi a ransu , ta dau tsawon 15min tanayi babu qaqqautawa daga Bisani ta Fadi qasa kaman matacciya in banda ajiyan Zuciya da take Fitarwa Babu Wanda Zaiyi Zaton Tana da rai Sbd yanda Jikinta ya Wani sake.


Hydar ya dubi Isma'il da Alamar tambaya yace

"Meye wannan da Kayi ?, me ka bata tasha?"


Isma'il yayi Dariya sosai yace

"Don ubanka poison na bata "

Hilaal ya zaro ido

"Is she Dead?"

"Don't Worry She'll wake Up and explain to us..."
Isma'il ya Fada Yana dubanta.

Hilaal da hydar ma ita Suke kallo ,Sai a yanzu Hilaal ya fahimci Tana Numfashi don haka nan take ya Fahimci Abinda Ke Faruwa......



**********

*9ja*

Umma ce Zaune a Parlon Hajiya Asiya Wanda Aka qawata da Furnitures na Alfarma da kayyakin more Rayuwa kallo daya zakayiwa Dakin ka fahimci Naira tayi kuka a Wurin nan.

Gaban Umma kuwa shaqe Yake da kayan Marmari kalakala.


Hajiya Asiya ta dubi Umma tace
"A Hajiya sa'adiyyah ,Na tayaki Jaje Kuma ina tayaki baqinCikin hada Zuri'a da banufiya Kuma Shegiya Haihuwan Titi ,tawagar la'anannun Allah ta'alah ,Kuma abun qarin BaqinCiki anan Shine Sunankin da Akasawa Qaddararriyan Babyn da Suka Haifa Cikin tq6ewa da la'anta kai amma Abin yayi muni dayawaa ,Yanzu Don Allah ya akayi kika bari tayi Ciki Har na tsawon Watanni Baki Sani ba ,bayan Wanda Muka zubar?, Anya Cikin ya zube Kuwa?"


Umma takai Fresh Apple bakinta ta gutsura ,Sannan ta maida dubanta Ga Hajiya Asiya wacce Taketa Zaqewa Tana Tada jijiyan Wuya irin Abin yayi mata Ciwo sosai dinnan.....

Tayi murmushin qasaita

"Asiya kenan, Na gaya miki Ni da hannuna Nayi mata Alluran Cikin ,Kuma koda zai zube Dakaina na Kaita Asibiti ,Kuma Wlh koda ta dawo Bana sata a ido kullum Tana Daka Kulle TANA Aikin Kuka ,Kinga kuma Ni ba damuwa Nayi da lamarinta ba bare na Dubata .... But a Ranar da na Farga na Sani Ranar ne na je dakinta Na iske ta Cikin yanayi na Rashin Lafiya inda nan ma Ni na Kaita Asibiti aka dubata ,a Nan na Gane Cikin bai qarashe Zubewa ba ,Abinda yasa ban dauki matakin Qara zubar da Cikinba A lokacin Sbd Irin Cututtukan da Dr ya ambata Wai Tana Tattare dasu Wanda Duk Nasan ta sanadi na ne, Tsoron kar Allah ya kamani da Alhakinta yasa na barta ,Amma dukda haka na quduri aniyyar zubar da Cikin in ta samu sauqi ,Tho bata ida samun sauqi ba Rabi ta sameni da maganar da ta Girgiza kwanyata ,Kuma idanna tuna Har Gobe nakeji a Raina kaman nayiwa Aaryaan Allah ya Isa yabi duniya ,Wlh bazan ta6a yafewa Alhaji da ya hada Auren 'dana da Shegiya ba, haka kuma shima Aaryaan din bazan ta6a Yafe mshi Ba Amincewa da Auren yarinyar nn da yayi ba ,Kuma qarin Abin takaici anan Shine Tun randa Aka aura masa ita nake iya qoqarina don Ganin Bai kusanceta ba Amma Abin ya Faskara ,Can You imagine Har Kazar Anarcinta Nice nan na sambadeshi Duk Don Karya kusanceta na hada dangi da Marasa Asali?, Tun bansan ita shegiyace ba kenan ,Amma don yaron nan yana Neman tozarta Ni ,yanason 6ata mn Suna a Idon duniya ya nuna mn Shi jarababbene Irin Ubansa ,haka ban isa dashi ba ya zaga ta bayan Fage ya Afka mata ,Ita kuma duk Sharuddan da na gindaya mata harda barazanar da nayita yi mata na Mijinta na dauke da Cutar daji na jini kuma bazai Iya ta6a Haihuwa ba saidai ta rasa Mutuncinta a banza daga Qarshe ya mutu ya barta da Abin kunya ,Kai Ni babu Irin Barazanar da banyi mata ba akan karda ta kasance 'Dana Amma tayi kunnen Uwar Shegu Ta bi Dadin bakinsa Har ta Kwaso mana Cikin Sa yanzu dai babu yanda zan iya ,Shegiya ta shiga Zuri'ata ,Ga Fitsararriyar 'dayan matar tasa Da ta riga ta Rabani dashi Wlh tun ranar da Ya tafi ban sakejin Muryanshi ba, bai damu da ya kirani ba ranar da kewarsa ta isheni na kirashi ma matarsace ta dauka ta zazzageni , tacin mn mutunci, Tun daga Ranar ban sake jin Duriyarsa ba ko na kira a kashe kullum a kashe ....."


Ta qarashe magana Tareda share qwallan da ya tarun mata a idanu da farar handkerchief.


Hajiya Asiya tayi Dariya sosai irin nasu na 'yan tasha tace

"Hehhhhey Lallai Haleemah ,kin Sosa mn inda Yake mn qaiqayi ,kin iso point dinda nake son mu kawo , don har yanzu na kasa Manta Marin data Zuba mn Ranar ,Can you just imagine Yarinyar nan Raise her hand And Give me a slap in Ur present amma kika kasa cewa komai,.....Wlh tallahi Tun da nake ko Uwata wacce ta haifeni bata ta6a marina ba Har ta bar Gidan duniyannan Sai Gashi yanzu Yarinyar da Takai tsarar Jikata ta mareni ,Na rantse Haleemah wlh ,Wlh ,Wallahi tallahi, yarinyar nan na gabda fara dukan ki don bazance mari ba ,tunda Bansani ba Maybe ta ta6a kwatantawa Gara ma Tun wuri ki dau mataki akanta ,Damani ba qyaketa nayiba She'll surely pay with Her life "


Umma ta gyara zama Jin furucin Hajiya Asiya ,Tasan qawarta tantiriyace Kuma shaidaniya na qarshe ita kanta tsoron shu'umancinta takeyi don Kowa ya Santa harta babu Mai ta6ata yaga dakyau yanzunnan zata Hadaka da 'yan Tsubbu shiyasa koda Munayferh ta mareta ta Zuba ido Tana Jiran ganin Hukuncin da Asiyan zata zartas akanta.


Umma tayi murmushi Wanda iyakanta Fuska tace

"Asiya wane Hukunci kike tunanin zakiyi mata a matsayin Daukan Fansa?"

Hajiya Asiya tayi Dariya sosai Tace

"Sa'adiyyah kenan ,inace Kin manta Wacece Nine ?, kin manta Ba'a ta6a Cin bashina akwana lafiya ,Hmmm....Koda Yake yaqin nan Ba nawa bane Ke y kamata ki gaya Irin Hukuncinda yayi daidai da ita"

Umma ta katseta da cewa

"Ai laifi kala kala tayi so dole hukuncinta ya zamo kashi kashi"


Hajiya Asiya ta gyara zama tareda Daukan banana Cikin Fruits Dinda Ke Tray din dake kan Centre table a Gaban Umma

Ta gyara zama Tareda 6are ayabar, Saida ta Sanyashi a baki ta gutsura Ta Dubi Umma tace

"Nagode da kika bani wannan Opportunity din, Ni idan da so samu ne Wlh mu zuba mata Abinda zai sauya mata Fata ko kuma kamannin ta Gabaki 'daya , ta yanda Babu Wanda zai iya ganeta ma bare a kusanto ta ,Kinsan yanda Fatarta Keda Daukar hankali ga taushi kaman Auduga ,Ga uwa uba kyau Na diri da Fuska ,Kai gaskiya yarinyar hadaddiya ce tun Fil'azal ,Inada Yaqinin kyawunta ta samu ta yaudari Aaryaan har ta Sace Zuciyar sa Har take Qoqarin rabashi dake Completely....so Akwai Wani Abinda zan zuba mata Fuskarta Ta Jagule da manyan Quraje Wanda zai sauya Mata kamanni".


Umma ta jigina da Kujaren da take zaune sosai ta lumshe idanu ta jima Idanunta a lumshe kaman bazatayi magana ba sai ta waresu akan Asiya ta ce

"Hajiya Asiya,wannan hukuncin naki Yayi Sauqi dayawa inda so samune Ta wulaqanta Fiyeda haka"



"Kyawunta shine ya jawo komai, a 6ata kyawunta ,Wannan hadadden Jiki da dirin da take taqama dashi Zansa a 6atashi ,Ta lauye a cikin jin kunya , A watsa Mata acid komai nata ya lalace Kowa ma ya huta"


Umma ta Girgiza kai tareda kama Lip dinta na qasa ta Ciza da qarfi tace

"Fiyeda haka"

Hajiya Asiya Taja tsaki cikin qufula tace

"Tho sai cewa kike Fiyeda haka, meye ya wuce duk hakan?"


Murmushi Umma ta saki Tace Akwai Abinda ya wuce haka.

"So nake na Rabata da Duk masoyanta ,Don Gaba daya Gidan nan banda tawagar Rabi da masu aiki babu Wanda baya sonta Saboda Kwarjinin da Allah yayi mata ,So nake na Rabata dasu Su daina ganin ta ,ta daina Ganinsu Gaba 'daya ta haka zan samu na zauna lafiya da mijina , sannan kuma Nasan yanda kakus take Tsananin son yarinyar nan ,kinga da An wayi Gari babu ita zata hadiye Zuciya ta Mutu ,Ni kuma na sami damar Cin Mutuncin Shegiyar Uwarta jeeddah dama Tsohuwar nan Ke hanani Rawar Gaban hatsi ,Kinga da ta sheqa shikenan dama Alhaji ba Wani zaman qasar nan Yake yi ba ,koya kika Gani.


Hajiya Asiya tayi dariyan Mugunta tace

"Lallai sa'adiyyah kinfini Rashin Imani ,Ni qaramar Qwaqwalwake Gareni ,shiyasa nake tunanin 6ata mata Sura zaiyi Wani tasiri ,Bayan Nasan True love baya ta6a gushewa Idan na Zuba mata acid din zai iya Cigaba da sonta Har Soyayyar da yakeyi mata yafi na da mah ,Amma yanzu na Yarda da A 6atar da ita din naga zaifi amma ,Bazamu iya 6atar fa ita ba sai Munbi ta hanya daya Inba haka ba dole sai ta dawo".

Umma ta dau Ruwan dake Gaban ta ta tsiyaya a Cup ta kwara baki Saida ta shanye sannan ta dire cup din tayi Gyatsa tace.


"Na Gaji da Wulaqacin da yarinyar nan takeyi mn Akan 'Dan da na Haifa ,Nasha wahalar haihuwansa ,Asiya yarinyar nan ta wuce duk yanda kike tunani tafi qarfina , Can you imagine yarinyar that call her self my Inlaw Looks into my Eyes ta gaya mn Kullum sai Aaryaan ya shigeta Kuma ta shayar Da shi ,And the worse part of it shine Yana nan tayi maganar kuma ya kasayin komai ,Wlh da bani na riqe yarinyar nan ba har ta Girma na kuma San Halinta Ciki da bai ,da nace Asiri tayiwa 'Dana Don nasan Aaryaan dinda na Haifa jarumi ne ,Mai Nuna 6acin ransa akan duk Wanda Zai 6atawa uwarsa koshi waye kuwa ,haka kuma ta mayar mn da miji bawanta duk Abinda takeso shi yakeyi koni da nake matarsa ban isada shi ba kamar yanda ita ya Isa dashi ..... Haba Wannan ai yafi Hukuncin da na zartar da Zuciyata tanada wani additional Hukuncin da zan qara akan Wanda na Zayyano ne wlh da na Fada ,Amma with time....anda One more thing ina Neman taimakonki Kisan yanda zakiyi Please ki nema mn yanda Cikinta zai zube a sauqaqe ,Batareda an gane zubarwa Akayi ba, I'll pay you huge Ko Nawa Kikeso Zan biyaki idan kinyi mn Wannan Aikin"



Haka Suka cigaba da tattaunawa akan yanda Zasu 6atar da Munayferh Daga bisani Hajiya Asiya ta nema musu Mafita wai zata tuntu6i masana Magani da Alqur'ani suyi mata aiki da ayar Allah ,ta hakan ne kawai Zasu iya 6atar da ita kuma sune kadai Zasu iya zubarda Cikin Munayferh da zarar sun dawo....ta Gayawa Umma hakane Don tasan halin Umma batason shirka Gashi tadau Alqawarin Wulaqanta Munayferh ,kuma Harda kwadayin maqudan kudaden da Umma tayi mata alqawarin bata Idan har aikin Ya Tabbata..


*******


LOIS

Satin Ramlah a asibiti aka sallamota Kullum saitayi Kukan Abin kunyan da ya kasance a matsayin qaddarar ta ,haka kuma har yanzu bata Gama Yarda da Ummace Asalin Mahaifiyarta ba, Gani take kaman hada baki Aaryaan yayi da Saleem Don Saleem ya sami damar Aureta dukda kuwa tana sonshi...


Yauma kwance take a qafar Ummie Banda hawaye babu Abinda Ke Zuba a idanunta ,Ummie kuwa sai rarrashinta takeyi tana bata baki.

"Ramlah" Ummie ta kirata

Ramlah ta dago jajayen Idanunta ba tareda ta Amsa ba .

Ummi ta cigaba da cewa

"Inaso ki dauki duk Abinda ya faru a matsayin qaddaranki, ki Sani kowane bawa yanada nashi jarabawan a rayuwa ,Ke musulmace wacce ta Yarda da qaddara mai kyau da mare kyau ,Ki Yarda dani wlh nasan har Abada idan kika kasance Mai Juriya Allah bazai ta6a Barinki a haka ba ,Ina ji a jikina kukanki ya qare ne a duniya Shiyasa Allah ya bayyana Miki komai batareda Anja da nisa ba, kuma kada ki tuhumi HAMDA (Baby haleemah) a kan Abinda Bata da Laifi akai ,Naga tunda kika aka nuna mki ita Kike Wani shasshareta Na lura ko Nono baki ta6a bata ba sai dai a bata Madarara Kanti Please Ramlah Meyasa Zaki kasance Cikin mutane masu Qin Godewa Allah akan Tarin Falalar da Allah yayi msu ne?, ki kasance Mai Tawakkali ,Allah Yasason masu Yawaita tawakkali da Yarda da qaddaransa "


Jikin Ramlah yayi matuqar sanyi da maganganun Ummmie ,Amma tanajin Babu Yanda za'ayi ta iya kallon Hamdah da irin Wannan baqin Fentin ,Haba ai Wannan Abin Kunyan yayi yawa ,Yayi yawanda zata iya Hada ido da 'yarta wacce ta kasance Cousin din kanta mai kaka Biyu a maimakon Hudu ,Tanajin da akwai hanyar da zata iya tursasawa Fahnaan ta kashe Yarinyar nan da tabi kowa ma ya huta...


A hankali ta share hawayenta Cikin shessheqa ta fara Magana Hawaye ba Ambaliya Daga Cikin Idanunta .


"Umminaah Wlh ni ba Yarda, na Yarda da Abinda ya sameni qaddarace a wajena Amma Mamy ta gaya mn mahaifiyata banufiyace , ni shegiyace Gashi ni ko sau Daya Ban ta6ajin 6oyayyiyar Qaunar dake zagaye da Jikin uwa da'ya ba a wajen Umma, na fijin hakan Akanki Ummie ,Zan fi amicewa ne idan An qaryata maganan nan da ake fadi wai ni diyar ummace Wanda hakan Banajin zai iya Faruwa ba Har duniya ta nade ,Ummie Please ki qaryata Abinda nakeji Kice kece Mahaifiyata zanfi Samun natsuwa dajin hakan Akan ace mn Ummace mahaifiyata ,Matarda taso halakani Akan ina Auren 'danta?"


Sallamar Saleem Ce ta dakatar da ita Daga Dogon jawabin da ta fara ,ta maida Dubanta Gareshi ,Fuskarsa Dauke yake da murmushi ya Gaida Ummie Ta Amsa Cikin 'Yar yaqe.


Ya kalle Ramlah da kanta ke kan Cinyar Ummie ta wani kafeshi da idanu ko kyaftawa ba tayi yace

"My shagwa6atu ,yau kuma Ummien nawa akeyiwa shagwa6a? "

Harararshi Ramlah tayi tareda sake qanqame Ummie

Ummie tace
"Mara kunya ,....run dazu nake Jiran dawowanka sai yanzu ka ga daman Dawowa?"

Saleem ya 'Dan Sosa kai Yace

"Ehm...Ummie Wlh nasha wahala kafin na samo msu ticket ,Saida naci layin Mutane Kafin na samu"

Gammm.....Aka wani banko qofar ,da gudu na shigo ina sheqa dariya Har ina Shidewa ,Da sauri kuma a tsorace Ramlah ta dago Daga kan qafar Ummie , aikam kaman Jira nake Ta tashi na Haye kan Ummie Tareda qanqameta Ina Cigaba da dariyar.

Ifrah ma ta Shigo da Gudu tana Turo baki ,Ganin na haye Jikin Ummie na kanainayeta yasa ta dumfaro inda muke GadanGadan ,Ganin haka yasa na koma Bayan Ramlah ina Cewa

"Wayyo Aunty Ramlah ,kin ganta Ko"

Tsawa Saleem ya dakawa Ifrah wacce ta Dumfaromu tana Huci ,Hakan yasa ta tsaya Chak tana

Please Login or Register in order to submit comment