Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bani tsoro wlh"


"Ba dole kiji Tsoro bah!,kin Shanya mu a Rana kin dawo Cikin AC kina shan Sanyi Abinki" janaan ta fada tana Rankwashinta a Tsakar kai.


Hafsah ta dafa kai cikin Yar Shagwa6a tace "waish,Muguwa kawai sai na rama"


Janaan tace"Yarinya saidai ki rame" dai dai lokacin da na shigo Cikin Dakin Riqeda FoodFlask na Abinci, Hafsah ta kalleni bayan Na Ajiye Abincin saman table tace"Wai Nayfee Kin Chanza waya ne babu ko labari? "


Nadan harareta "Gulmammiya, So kike kisan yanda akayi na Samu kuma tokwalelenki, " nafada ina mata Gwalo Gaba daya suka kwashe da dariya,Haka muka cigaba da Hira muna cin abinci har muka Gama sannan muka Dauro Alwala ko wacce ta Gabatar da sallar Azhr,

Cikin dabara Janaan ta jani bedroom Ta miqa mn Wasu Yan kaya da wani humra ~(Wai sune makaman da zasusa ya sake ni)~๐Ÿ˜†

Sai 4:30muka koma school bayan mun Gabatar da sallan Asr, Sai a lokacin naga Sabon lecturern Organic dinmu wani Dan Tsukai Gashi Ramamme (Kunsan dai yanda chemistry lectures suke especially ta fannin yan ORGANIC , duk wani\Wata chemistry lecture dake karanta littafinnan I'm sorry in advance Allah ya shirye. Ku๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ).


Sai Karfe Shida na yamma muka Fito ko wannen mu a gajiye,Sai a lokacin na lura da Ashe Bhaddy da boys Dinsa basu nan Ashe tuni sun yi Gabas .


Saida muka raka Jannan Har campus sannan muka dawo bakin titi, na Kar6i number YaaAary a hannun Hafsah na yi saving da MIJIN TITI.๐Ÿ˜‚


Na danna kira, kira daya ya dauka Babu ko Sallama nace"Mun Fito fa ko mu tafi ne?"


Daga Chan 6angaren cikin wata raunanniyar murya yace" karku Je koina Ganinan zuwa "

Da tho na Ansa na datse wayan.


Hafsah ta kalleni tace "Wai me ke tsakanin Ku keda YaaAary cikin Yan kwanakin nan kun zama Friends alhalin Baku jituwa"



Nayi murmushi nace"Hafsah bazai gane bane,Babu Alherin dake hadani da YaaAary sai sharri,Hafsah na tsane yayanki na tsaneshi !na tsaneshi!! Wallahi bana kaunar sa kaman yanda bana kaunar Ranar mutuwata da za'a bani wuqa ace na Kashe Wanda nafi tsana a duniyar nan tho babu makawa Shi zan fara kashewa..."

Hafsah ta dakatar Dani "Ya isheni haka na Gode"..

Na ta6e baki " Dadin Abu shi ke sa godiya,Nasan Bakiji dadin kalamai na ba ,Amma babu yanda zakiyi dani ,Nasan ji kike kaman ki sukeni ki huta ko?,Tabbas yanda kikeji, nima haka nakeji idan an ta6a Tweeny Abdool, Nakanyi Loosing temper na, but Ur brother Is so wicked Mugune na Qarshe... "

Na tsayda maganar lokacin da Motata ta faka A gaban mu .


Dakanshi ya bude mana mota Fuskar nan babu walwala, Ga kansa daure d Bandage ,idan Shi ke tuqi nafi son zama a baya Amma yau Saboda Tsabar Neman Fitinar da nakeji sai na shige Gaba .


Babu 6ata lokaci yaja mota Muka dau hanyar GRA munyi nisa a tafiya babu Wanda yayi magana na kalleshi cikin Danne dariya nace "Yayan hafsah Wai Ciwo kaji ne, ko kuwa Accident kayi, ka Ganka kuwa?, Kaman Monkey Bakinka har wani kara Tudu yayi sai kuma kayi kyau a haka fa, da haka Halittarka take da Kafi ky..."


Hararar da ya galla mn yasa naja bakina nayi tsit har muka isa Gida ban qara cewa komai ba.


Muna shiga yayi parking a harabar Gidan ya bude lockdn baya Hafsah ta fita nima na murda murfin kofa najishi a Garqame na juyo na kalleshi nace"Ka bude mn manah"

Baice mn komai ba sai Uban sauke Numfashi yakeyi sannan ya juyo ya kalleni Idanun nan Sunyi jajir da sauri na kawar da kaina Gabana na dukan uku Uku.


Cikin murya chan qasan maqoshi yace "NERYFERH, yaushe kika zama Yar daba?"

Idanu na Waro cikin Kidimewa"Yar daba kuma?" Na fada ina kallonsa, tunawa nayi da Aikin da nasa amn Akansa Sai na fashe da dariya Na shiga kyakyatawa.


Bamm naji an Buge mn baki '' Sai yanzu na tabbata baki da hankali, Kin dauka Yaran da kika Turo sun isa Ku ta6a koda Hannuna su Kwana lfy ne?..."


Na katseshi "Eh manah ,Basu isaba Shiya sa naga An maka Rawani da bandage"

"Daga nesa suka jefeni da Dutse,Cikin Rashin Sa'a suka Sameni a Goshi" ya fada yana Qara matsowa kusa dani,Tsoro da firgici suka kamani na shiga Neman Hanyar da zan tsira ,cikin Sa'a kofar da Hafsah ta fita a bude ta ke Nan take sunkuce jakata nayi baya na fice ta kofar ina kwasar dariya.



********


Tunda Umma taga Ramlah ta fadi ta fice, Amma Abin mamaki sai ta kasa natsuwa ta tsinci kanta da tausayawa Halin da Ramlah ta shiga, Amma ko kadan ta kasa tunkarar dakinta ,Dakanta ta dafa Abincin Rana,Ganin har lkcn bata Fito ba yasa ta je dakin Dan ta duba ta a kwance t sameta ta kudundune cikin Bargo tana Rawar Sanyi, Saidai tana kallon Fuskar ta taji tsanarta ta dawo mata sabuwa ta ta6e baki tayi ficewarta,


Koda na shigo a falo na isketa ,Gaisheta nayi ta Amsa babu yabo babu fallasa Sannan na wuce Dakin Ramlah na Gaida ta har ta watsake tace mn Dan Allah idan da Abinci a Gidan na kawo Mata bata jin dadin jikinta ne kuma bazata iya Fita falo ba,Wani kallon banza na bita dashi Sai kuma ta bani tausayi na gyada kai nace "Aunty baki da lafiya ne?"

.tace "Bana jin dadin Gabobin jiki na ne kawai"

"Eyyah,Allah ya baki lafiya bari inje in tambayo Umma" na fada tareda Ficewa daga dakin.


A falo na iske Umma tana yiwa YaaAary fada Akan tuqin Ganganci Dan na lura cewa yayi accident ne sanadin Raunin kanshi.


"Umma akwai Abinci a Gidan?" Na fada ina duban Umma

"Ki tambayi matar Gidan nan mana" Umma ta bani Amsa.


"Kece matar Gidan Ai ke da kika isa ki Tsara ,ki sa ayi kuma ki hana Ayi ai kin Wuce matsayin matar gidan, Ni kinga Ba Dogon magana na zoyi ba, kawai A nemo Wa aunty Ramlah Abinci bata d lafiya ma,inaga Bata ci komai ba tunda safe"



Wani irin Zabura Aaryaan yayi Wanda yasa dukkan mu Dubanshi a......











Waiting for Ur comments๐Ÿคข



Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ




Fahnaan

12September๐Ÿ–‹๏ธ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 30_*



Wani irin Zabura Aaryaan yayi Wanda yasa dukkan mu duban shi a Razane,


Miqewa yayi cikin Hanzari ya nufi Hanyar dakinta,

"Kar ka kuskura ka shiga dakin nan,Idan ka shiga kuma Sai dai ka nemi wata uwar bani ba" Umma ta fada kakkausar murya dake Nuna tsananin 6acin Rai.


Chak ya tsaya ya kasa qarasawa Amma jin Abinda Munayferh ke cewa yasa ya daga kafarsa Tare da juyowa Gabaki daya.

"Kai YaaAary juyo kalleni" Munayferh ta fada a Gadarance,Shima Juyowa yayi yana kallonta,Umma ma kallonta tayi tana jirar cewan ta.


Na cigaba da cewa"Dan Umma ta ce Zata cireka daga cikin 'ya'yan ta sai me kasan bazata ta6a iyawa ba Amma Amanar 'Yar mutane da ka dauka fa?, Kasan Tanada haqqi akanka ko?, Ka tuna akwai mutuwa akwai hisabi kuma duk babu Wanda ka isa ka tsallake, me zaka gaya Wa Allah In ya tambaye ka kan yanda ka Riqe Amanar Yar baiwar Allahn nan ,Eh?, Misali idan Hafsah ce tayi Aure ba tada lfy kuma Takai war haka bata karya ba tunda safe wane Irin hukunci zaku dauka,Haba ai wannan zalunci ne,Dan Umma tace zata cireka cikin ya'yanta sai me Mu muka qaru dan barin mana Gida zatayi Gaba daya Dan bada kudin ubanta Ko na mijinta aka Gina ba kuma ta takura mana ko ince ta takura maku...Nasan ko Hauka Umma tayi bazata ta6a Cireka cikin 'ya'yan ta ba Tsabar iya Qalya da muzgunta ne kawai, now.... Choose.... Ur Mum or Ur Wife" na fada ina Nuna Umma da hanyar dakin Ramlah da hannaye na Biyu

.


Tsuru yayi mn har yanzu Hausa bata Gama kama baki na ba hakan yasa bana iya Dogon magana Cikin Harshen, Shiyasa Wasu ke Ganin na kaman Mai son Takaita magana ,Alhalin Rashin iya Sarrafa harshen A lokacin da nake magana yakesa na Takaita, idan na Tilasta Wa kaina yin hakan Sai a Samu Kurakurai kaman yanda kukaji Maganar๐Ÿ‘†๐Ÿป๐Ÿคญ.



A sanyaye ya fara takawa yana barin Gurin har ya kai Exit na Parlorn Sai ya juyo Ya kama Hanyan Dakin Ramlah .


Da ido Umma ta bishi har ya shige,Bata iya cewa Uffan ba ,Hannu nasa na tallafo Fuskarta sannan na juyota a Gareni nace "Madam kin fasa Cireshi daga Cikin ya'yan naki ne?"


Harara ta zabga min ta miqe Fuu zata wuce nace " Da ace da son Raina na zama Abinda danki ya maida ni da Kinci ****Nki Saina Gyara miki zama.... Wicked Inlaw....Mtsww"naja Yar qaramar tsaki Cikeda Jin haushinta,Daidai lokacin da su Aary suka Fito Da Alama Asibiti zasu , Suka wuce ni ko Sumin Godiya(๐Ÿค”?)


Da Harara na bi bayansu ina Jan tsaki.


โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…
.

WasheGarin Ranar Aka kawo ma Aaryaan sabon Motanshi Kirar Firari 488 GTB fara ,OMG I admire that car zaiyi matuqar dacewa dani.dama inason Mota kirar FIRRARRI Shiyasa Na sa mishi ido kan motarshi tada, Kowa na tayashi Murna Amma ni Baqin cikin hakan nakeyi, kuma Ban Nuna A zahiri ba ni kadai Nasan Yanda Nakeji Cikin zuciyata, Mota na Kuma ya ba Driver makulli akan shi zai dinga Kai mu makaranta yana dawowa damu, Su Umma kuma Sai wani daddaga kai akeyi Ana Iyayi Adole 'danta ya Sayi The most Expensive and Latest Car in de Era.

Tun daga Ranar da ya Siya Motar na daina Ganinshi,Ashe Sun fara Training nan ne na na POLICE ACADEMY da AsubarFari zai fice sai dayan dare yake dawowa, Su Umma an tasa an tsare Ta Kara nemo wani sabon Salon Takura Wa Ramlah Dan ko Abinci zata Girka sai Umma ta Auna,Kai Harta banza Maggi da Gishiri Umma ke bata iyaka Abinda zatayi amfani dashi, Gaba daya ta Lalace ta rame tayi wani fari Yau ciwo Gobe Lafiya, Aaryaan ne kadai yasan Abinda ke damunta Amma bai fada Wa kowa ba Hatta Ramlahn, ya barma Ranar da zai Fito a sani๐Ÿคฐ๐Ÿป.

Da zarar ya Samu Interval zai kunna system suyi ta Video call, idan kuma ya dawo Suna Gama Sallama da Umma ta shige daki sai sadado ya Shige Na Ramlah.


Tun Randa nasa Su bhaddy su Zane YaaAary Na daina Ganin Giftawan su a makaranta, Kuma ban damu da sanin hakan ba,


Yau wata daya kenan da Auren su YaaAary, kuma sati Biyu Auren Mu, kullum Cikin Tunani nake yanda Zan fada mshi ya Sakeni Tunda ba sanin lokacin dawowanshi nakeyi ba,na zama Wata Shuru-Shuru ,Sai Muyi Zaman Awa Guda da mutum har ya tashi ko kallon Inda take bazanyi ba bare na yi magana, Harta su Hafsah sun fahimce hakan Kosu ba wani maganar kirki mukeyi ba, Abinnan na damun janaan Dan Ita kadai tasan matsala ta ,


Yau muna makaranta Gaba daya muna da 2hrs interval kafin mu Shiga next lecture,cikin dabara taja ni student common Room batareda sanin Hafsah ba.


"Munayferh Wai me yasa Kika juya mana baya ne this days, kin Fiso Ki zauna ke kadai kina Tunani ,I hope all is well"


Kallonta nayi na kawar da kai Gefe Batareda nayi magana ba ,Kusan 3mins ina kallon Gefe batare da na bata Amsa ba, Har ta cire Rai da samun Amsa na Sai taji nace "Ba komai Please Go, leave me alone" na fada cikin Sanyi Murya na narawa kaman Zanyi kuka.


"No qualms,Am taking my leave Right now, But kisani as I am Going sai na fadawa YaaJunayd duk yanda Ake ciki Nasan Damuwanki baya wuce akan Auren dake kanki...." Ta fada a raunane sannan ta miqe tareda daukar Jakarta.


"Jaanu" Na fada Lokacin da Kuka ya kufce mn.


Dawowa tayi ta zauna, kusa dani Tareda Rungumonicikin Sigar Rarrashi ta fara magana "Behold bae ,Ki natsu ki mn bayani Please me ke damunki" ta fada hawaye na taruwa a idanunta.


"Jaan ,ina so YaaAary ya Sakeni kuma na daina Ganinshi ban San yanda Zanyi ba, Babu Yanda zanyi na Gaya mishi ya Sakeni...... I'm doomed!," na karasa ina kara Rushewa da matsanancin kuka.


Jannan ta dagoni ta kalleni, na bata tausayi matuqa da YaaAary mutumin banza ne da ta bani Shawarar Rabuwa dashi Cikin Sauki, Amma tana hango Alheri cikin Auren namu Gaskiya bazata iya Sa hannu ta Rusa wannan hadin ba.


"Look Nayfee, Ai tuni na baki Shawara kece dai kika qi bi,ai da tuni ya manta ya ta6a Aurenki"


Na share kwalla nace "Nifa in wanchan,Shawarar da kika bani ne Gaskiya ki Riqe Abinki I can't"


"Aikam Zaki dawwama da igiyoyin Auren sa, kawo kunnenki kiji,"

na matso kunnena Saitin bakinta ta rada mn wata Gulmah na Waro ido Gadi da tuntsurewa da Dariya mai hade da kuka.


Tace"Just Remove that pride and Do as I said, Yau a Gidana Hafsah zata kwana, i'll pretend as if I'm sick, Sai nace tazo ta tayani kwana , Sai ki jira har 1:00am in yadawo komai ta fanjamafanjam"


Nayi dariyar Qarfin hali nace "Janaan I can't Zai raina ni ne kawai"

''Mtsww, Ur pride won't take you any where jare , just do as I said my Friend "

Na gyada kai alamun Gamsuwa, Sai yanzu naji Sanyi a raina Tabbas Riqe Abu a zuciya cutane mai lahani Wanda Fitar dashi shine magani.




Kaman yanda Jannu ta tsara haka akayi ,Hafsah na Gidanta da Cesar zata kwana ta dawo Gobe da safe,


Sai safa da marwa nakeyi a Tsakar daki ni daya kamar mayya Nakai duba ga Agogon dakin 12:45pm Bayi na shiga nayi wanka Sannan na zo Gaban mirror na fara Yan ShafeShafe na body Spray.


Ledar Kayan da Janaan ta bani Lokacin da Mukaje Cin danwake a Gidanta ,na bude Wasu Tsinannun Sleeping dress ne d Humrah ~(Yo ina jaanu t Samu Waennan tsinannun kayan๐Ÿค”)~ Wannan ba Abin tambaya bane Yanzu,


kwance kayan nayi na saka ,sannan na Dauko Kwalbar Humran, Humran akwai sanyin Qamshi mai Sanyaya Rai,cikin Rashin Sa'a ina bude murfin Humran ya Zube min a hannu,dafa kai nayi "ohhShitt" Gashi ya zuba sosai Kusan Rabi ya zuban min ,Rufe Kwalbar nayi,Sannan na Dauko Kimono Sky Blue mai Ratsin Milk na saka,dama kayan RoyalBlue ne mai adon golden sai yayi mata kyau matuqa.


Agogon dake Manne da bangon dakin na kalla karfe daya da minti Goma, dama Tun ina Bayi naji tsayuwar motarsa ,by now yaci ace ya gama Cin Abinci Dan Nasan Umma bazata ta6a Bari yayi bacci ba tareda ya Ci Abinci ba.


Warware Ribbon dinda na tufke Gashi ta tayi,ya baje har Gadon bayanta Sannan ta fito Gabanta na dukan Uku uku,


A falo ta tarar da Umma tana Rufe windows,(an gama Gadi ba๐Ÿ˜†)


Kallo daya nayi mata na watsar, na cigaba da takawa da kallo ta Bini tana mamakin Ganina da Erin kayan nan Gashi sai kamshi nake zubawa, har zan Haura kan stairs tace "Hey, ina zuwa haka?, Ajiyar me kika bada a Saman?"


Tsayawa nayi ina Tunanin Amsarda zan bata sai kawai nace" Banida lokacin ki Amma idan kina Buqatar Amsa ki biyo ni" na fada ba tare da na juyo ba, na cigaba da tafiya , ta Bini da kallo har na shige dakin.




A Bedroom Dinsa na tarar dashi kwance a Kan doguwar Kujera, ya daura System Dinsa kan cikinsa da Alama idanunsa a lumshe da Alama barci ma yakeyi...


Hannu na Rawa na janye System din na Ijiyeshi gefe,


Ji tayi ya finciko hannunta ta fado jikinsa yana Shinshina hannun dai-dai inda Humran nan ya zuba ,Tsoro da firgici Suka kamani Jikina ya hau makyarkyata.


Daidai lokacin da na hango shigowar Umma t Mirrorn bayanshi,


Ai tana Ganinta ta sa Hannu ta Rungume shi kyam Still idanun ta basu bar Kallon Mirrorn dake Saitin Umma ba.


Wata irin Qara Umma ta saki Wanda yasa Aaryaan yunkura Kaman zai tureta,

Munayferh na ganin ya tsorata Batayi wata wata ba ta๐Ÿ‘„+๐Ÿ‘„ (๐Ÿค).


Daga nan fa Ya mance a Duniyar da yake.

Gaba daya Umma ta tsure Gani take kaman a mafarki Wai Da gaske Take Ganin Abin ko a mafarki, ta kasa Matsawa daga inda take ji tayi kaman an jona mata Electric Shock sai makyarkyata takeyi .





Gogan naku da haqamah daga Wasan kwaikwayo sai ya zarce da kwance igiyan Kimono.



Umma na Ganin haka,ai bata San lokacin da taja kafarta ta bar dakin ba.


Ina Ganin ta fita na Tattaro dukkan Qarfina na tur..................























Su Umma anga Edi


Ke kuma Munayferh Fyade Zaki mshi ne?๐Ÿค


Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ



Waiting For Ur Comments if not zan tsayda typing ba sai next year in Allah ya kaimu๐Ÿคค




Wattpad @Fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 31_*

Munayferh na Ganin Umma ta fita ,ta tattaro dukkan Qarfinta ta Tureshi, Amma ina.... ko Gezau bai yi ba, Sai qara Qaimin da yakeyi, Gana daya Ya susuce, koda yke hakan baya Rasa Nasaba da Kamshin Humran dake tashi a jikinta.

Su Munayferh Ido ya fara Raina Fata, Tuni hawaye Suka Gama wanke mata Fuska ,A ranta kuwa sai antayawa Janaan Allah ya isa takeyi,

Tunawa tayi da yanda Ta tsira ranar 20th december, Batayi wani jinkiri ba ta dage ta kai mishi Cizo a Gefen Wuyan shi ,


Wani irin kara ya saki tareda Sakinta a Razane ya dawo hayyacinsa ,saboda yanda Zafin cizon ya ratsa shi.


Munayferh na Ganin ta Tsira ta dau Kayan ta bata ko tsaya Sawa ba ta arta na kare,


A Falonsa ta tsaya ta Gyara zaman Riganta,har zata wuce sai idonta ya hasko mata Key dn sabon motar sa,

Karasawa nayi na dauka,Sannan nayi waje da Gudu.


Ranar Umma kwana tayi tana kuka Ji take ina ma ace abinda ta Gani yau mafarki ne ba Gaskiya ba,She was scared Tayiwa Aaryaan kyakkyawan Shaida Amma meyasa zai watsa mata Qasa a ido?, Meyasa zai nemi yarda Ta tsana take shirin hada Aurensu Sbd A Ganinta Zai Hora ta,Meyasa ,Meyasa, meyasa!, Meyasa Aaryaan zai nemi matan Waje dan ta hanashi Ta Aure?
~(Ni zaki tambaya?๐Ÿค)~


Shi kuwa Aaryaan mamaki yakeyi akan Yanda Yarinyar nan ta Afko mshi, yasan wannan ba tunaninta bane, dole akwai Wacce ta bata Shawarar yin hakan!, to waye kuma meyasa? ~(Ka tambayeta mana๐Ÿ˜’)~


Daga Qarshe ya sadado kaman yanda ya saba ,Yayiwa Ramlah dadin baki Ya sauke akanta.


Munayferh kuwa Kusan kwana tayi tana Auna Wa Jannan Allah ya isa, A Daren ta kirata ,Amma har ya Gama Ringing bata daga ba, Ganin hakan ba shine mafita ba yasa ta shiga hada kayayyakinta da cewaar Gobe zata Bar Gidan Gaba daya Ta koma Kd inyaso sai ta Ringa Zuwa Sch daga nan tana komawa.

**โ˜…**


WasheGari
.

Tun Asuba Hafsah ta Kirani Wai gata a hanya Ta6e baki nayi batareda na bata Amsa ba na datse wayan, a raina Kuwa cewa nayi Kila kafin tazo nayi Gabas.

Sai da na Gama Jera kaya na cikin Mota ina kan Daukan last Trolley Na fito cikin Sanda naji Umma tace "Ina Zaki kaishi Dan (Kazan) ki "


Juyowa nayi na kalleta na basar, idanun nan Sunyi Rudu-Rudu Sun kumbura alamun tasha Kuka ta qoshi,

Takowa nayi har inda take Tsaye na kalleta face To face Fuskata a daure tamau,Hakan yasa Umma Tadan Tsorata har na Gani cikin kwayar idon ta, ni kuma Haka nake so

"Hey,Old Woman bazaki daina Shiga harkata ba ko?, Wlh sainayi Mugun sa6a miki, Wanda kika Gani jiya Kadanne, kukan da kikayi Jiya bai Isheki ba kenan, .. Sa ido kawai"

Naja tsaki na juya zan wuce Naji ta Fizgo ni ta juyoni Ta falla mn mari.

Dafa kunci nayi na kalleta Cikin tsananin mamaki, nima banyi wataยฒ ba na daga Hannu zan Rama Naji an Riqe mn hannu an kuma wankeni da Wasu tagwayen Maruka a ko wane side na kunci na ,

YaaAary Ne Sai wani Huci yakeyi,dukda zafin Marin ya ratsani matuqa, Amma ban sajuda ba ,na kuma daga Dayan hannun a dole fa sai na Rama.


Na kumajin an Riqe hannun tareda Wankeni da Wani bahagon mari again ,Wanda ya haddasawa Idanuna Ganin Triple stars.


"How dare you,How dare you Raise Ur foolish hand on my mum, Who the hell did You think you are?,Kinyi kadan ki Wulaqanta min Uwa, Dan kinga ana barinki ba tsoronki akeji ba , kinyi kadan Wlh Idiot,Bloody nuisance" Hafsah ta fada Cikin Rawar murya Baki na rawaHawaye na zuba saman Fuskar ta.

Wani irin Yunquri nayi zan kwace hannaye na dake Riqe da Na Aaryaan da Hafsahn Amma inaa ba Riqon wasa suka mn ba Cikin Rashin Sanin Madafa na fara Hawaye, Wai yau ni Hafsah ta daga hannu ta Mara Ta kuma Zagina ,Ba'a ta6a ci mn mutunci irin na yau ba.


"Hafsah,You Slapped Me!!" Na fada Muryata na cracking.


Aaryaan da tuni yanayinsa ya fara Chanzawa Dan Riqe hannun da yayi ba qaramin Tada hankalin sa yayi ba shiyasa ya kasa cewa komai,


Jiki a sanyaye ya Cikani yayi hanyar fita, Umma tabishi da kallon mamaki,nan danan Ta fara Dirty Thinking..


Qarar Saukar Marin da taji yasa ta dawo da bubanta Garemu ,Nice na daga hannu zan Mari hafsah ta kauce Sannan ta Falla mn wani๐Ÿ˜ญ

(Chai five Slaps๐Ÿ˜ซ),Hafsah ta bani mamaki, Am confused, I'm Scared out Of my Bones


"Hafsah ni
....ki....... Ni ....zakici wa mutunci?," saida nayi Shuru na Dan tattaro Natsuwa na sannan nacigaba
" Kinyi kadan ki wulaqantani Hafsah,Dan na Mari Uwarki ...So what ...I don't fucking Care, ke da ta Haifa ke ta shafa.... Wlh daga ke har Uwar taki Sai kunyi nadamar Abinda kukayi To hell with you and Ur Fucking Mum"

Na fada Sounding very Harsh,Sannan na kwace Riqon da hafsah ta min ,cikin zafin nama naja Trolley nayi waje.

Mutuwa tsaye sukayi, da kallo suka Bini har na Kurewa ganinsu.



Ramlah da hayaniya ya fito da ita ta saki murmushi tana Mamakin yanda nake iya tunkarar waenda Suka Girmeni Ina musu RashinK ba tareda na ga Girman nasu ba..


****

Yau satin Su Ammie Biyu a 9ja ,Suna Gidan tsaronsu na Zaria Ana tsare su ,Sai yau aka Fitar dasu ko wannen su an rufe msu ido da waniScarf , so that baza su Gane hanyar da ake bi dasu ba,Tun kan su dawo saleem yabata Mini connector na CCTV Wanda zata Maqala a Part din Inna Rabi Dan itace first Suspect dinsu.

6:30am dot aka diresu a PZ ta hanyar Railway, Tareda kwance Masu Scarf dinda Suka rufe msu Fuska dashi, sannan suka jefo musu kayansu A wulaqance.



Ammie taja Hannun Ameer da Ameerah ta Riqe da hannu daya sannan ta Rige Jakar kayanta da hannu daya ta fara Tafiya cikin Rashin sanin inda ta dosa.

Suna Fitowa TITi Ameerah ta Kwace hannunta ta kwasa a Guje, Ameer na Ganinta Shima ya kwace hannunsa ya bita a Guje, Ammie Ta kwala ihu tana kiran sunansu Amma inaaaa Wayaga Akuyan kulle๐Ÿ˜‚



****


Tuqi nake ina tunanin Wai Yau ni hafsah tayi Raising Stupid Hand dnta Akai, Sai faman Huci nake ji nayi kaman na koma na karkaryata Amma with time zan dawo, har Na hango hukuncin da zan dauka akansu itada Umma YaaAaryn ma bai mari banza ba,Kuka nake kaman Raina zai fita,


Ganin in na cigaba da driving cikin Kunci za'a iya samun matsala yasa na Samu Gefen hanya nayi Parking Na daura kaina Bisa Stirring Na fara Gurzar kuka na.



Kaman ance in dago Sai Ganin Wasu Yara nayi Suna Gudu akan titi babu Ruwansu da Motocin dake Giftawa,Yaran Sun bani sha'awa Sosai kuma sun burge ni.



Sai na tsinci kaina da Goge hawayena tareda bude Murfin kofar na fito, a lokacin da Suka tsallako.


Yarinyar da Fara tsallakowa Ta bi mota na da kallo for some minutes sannan Ta kalleni tace "Laah Amiy co kaga Flat car like Uncle Hoody mouth"


Murmushi nayi na daga Yarinyar sama

Please Login or Register in order to submit comment