Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kwashe da dariya "kana Tunanin Yarinyar nan zata ta6a bude baki ta Gaya ma tana sonka ne?......Lallai Har yanzu baka gama saninta ba,Ko Ni da na Santa da dalilin ka nafika sanin hakan"



Aaryaan yaja tsaki Cikin takaici ,ya Miqe yana daukan jakan laptop dnsa da Wayoyinshi

"Sakarai kama Samu anzo Neman Shawarar gurinka Shiyasa kake Abinda ka Ga dama, dadin Abin ba kai kadai Gareni ba"


Hilaal ya danne dariyarsa ya Riqe jakar da Yake Shirin sa6awa yace "Please Angon 3, ba Izgilanci bane ,maganar gaskiyace da zaka natsu kayi tunani sosai Zaka Gane hakan... amma Ga wata Shawarar"



Aaryaan ya dubeshi Fuska daure yace

"ina sauraron ka"

"Please zauna mana"


Babu musu ya zauna yana huci kaman wani Zaki Don ba qaramin bata mshi rai Hilaal yayi ba.


Hilaal ya cigaba da cewa


"Kasan mace qaramin kwakwalwa Gareta, Gashi yarinyar Qaramace bata Cika Hankali sosai ba, kawai kasan yanda za'ayi?....ka gaya mata kana sonta Cikin tausasan lafuzza in a Romantic way in so Samu ne ma ka durqusa mata Kasan mace da son Girma, nasan bazaka iya ba saboda ji ji dakanka ....but Please Sauke Pride dnka ka Fuskance Abinda na Gaya maka yanzu Shine importanter....."



Bai ida Rufe baki ba Aaryaan yaja dogon tsaki

"Mtswww..Aikin banja" sannan ya Miqe ya Fice daga Office dn a fusace.

Hilaal yayi dariyan Mugunta

"Omo...You're in love zurfin Ciki da iyayin ka sun hanaka Ganewa....nasan With time sai Munayferh ta jaka a qasa kaman kayan Wanki zaka Gane kurenka ne...." Haka ya Cigaba da Maganganu shi daya yana darawa Kaman wani zautacce....




Ni kuwa kai tsaye Gidan Su talatu Maqotan mu (inda nashiga naga Ana fada na 'kara hura wutan.....A Ranar da Munayferh tasha iceCream๐Ÿ˜….....kun tuna?)



Ina shiga kai tsaye Dakin dake hannun dama na fada Da Sallama na.


'Yan matan dake Zaune a parlon suka Amsa mn Cikin sakin Fuska.


'Yan Mata biyu ne zaune a parlon Suna kallon Film a System, sallamar da nayi yasa su dagowa Suna kallona Baki saki.


Nima kallon su nayi Har na tsargu๐Ÿ˜’.


Cikin Jin haushin kallon da Suke mn Nace "Kallon fa?, Ina talatu?"

Siririyar Cikin su tadanyi dariya tace "Sis Kaman kece Amaryar da na Ga an nuno a Fahnaan TV dazu ko?"


Ban kaiga bata Amsa ba Talatu ta Shigo, tana Ganina ta Saki Fuska Cikin Tsantsar FarinCiki ta tarbeni, Har ta fara ja na da surutu .


Na dubi 'Yan matan nan Nace "Sisters naji kunce An nunoni Cikin Fahnaan TV, Ai ba'ayi Auren ba"


Humayda (daya daga Cikin 'Yan matan) tace

"Jiyan nan wasu yara Maza Suka kawo mana IV, Wai na Bikin da za'ayi a maqota, dadaddare saiga Sanarwa a TV , yau Saura 4days kor....Ai Ke kin Wuce Amarya in da sunan da yafi Amarya ma dashi Zan kiraki"


Gabaki daya mukayi dariya.

Siririyar(Nawal ) tace "Ni ai tunda ta shigo naga haskenta na Kuma shaqi qamshin ta na Gane Amarya ce, kai Amarya ta dabance Wlh..Allah ya Aurar damu Tun kafin mu mutu"

Humaydah ta Amsa d "Ameen" Tana dariya.


Yayinda Talatu ta Rankwasheta tace ''Maras kunya"



Humayda da Nawal qannen Yunus (Mijin Su talatu) ne a Gidan Suke Zaune, suka karatu a KASU .


Nan Fira ya 6arke a tsakanin mu kai ka ce mun dade da haduwa ne, dama na dade banyi Surutu ba Shiyasa na Zaqe na zuba Abina.


Ita kuwa Kishiyar talatu Wato Hadiza Wai tayi Tafiya sai nan da kwana Uku zata dawo.


Saida yamma liqis kafin na koma Gida, Su Humaydah Suka mn Rakiya, mukayi Exchanging Contacts, sukace inshaAllahu zasuzo Gobe.


Koda na koma Gida Har Baqin nesa Sun fara Zuwa sun yada zango a part dinmu Shiyasa na Koma Part din Su Umma nan baqi sun Dan fara Zuwa.

A Dakin Hafsah na yada zango, Suna Zaune itada Cousin dina ('Yar qanwar Ammie) wato Fadeelah , Hafsah na nuna mata lefe na Wanda ta dauka a wayanta,Fadeelah ce ta fara Gani na tana Gani na tace "Gata nan".


" Me Ake kallo ba'a son Na Gani?" Na fada ina Fizge wayar a hannun hafsah Wacce Ke kokarin Boyewa.


Waro ido nayi Ina kallon yanda Akwatnan suka hade kaman Saman Alale.


"Wow ina kika Ga wannan Pic din?" Na fada Cikin Santin yaba kyawun Akwatunan.


Me zasuyi inba dariya ba?, Nan Suka shiga darawa Suna tsokana na .




****


Aaryaan tunda yaga dare ya farayi Hankalinsa ya Tashi baya son Rabuwan Auren nan, ko babu komai saboda ko a Addini Ba'a son Rabuwan Aure batareda wani dalili mai Qarfi ba.


Daga Qarshe y yanke Shawarar Bin Shawarar Hilaal kawai Don yaga shine mafita.


Ina tsakiyar su Fadeelah na Riqeda wayana, tana kallon Photos, Suna tsokanata itada Hafsah.


Wayana dake hannun Fadeelah Ya dau Ruri...


Waro ido Fadeelah tayi Tana qarewa Screen din Wayan kallo.

"Wake Kira na?"

"Mijin TITI" ta bani Amsa cikin Dariya.


Da sauri na Miqe na kar6i Wayan ina harararta, sai na Tsinci kaina Cikin Rashin son daga Wayan A Gaban su.


"Babe...Kamar fa Angon ne Ke kira Shiyasa bata son dagawa A Gaban nu, kin Ga mu Fita kawai" inji Hafsah.


"Ina nan Babu inda zani,ina nan sai naji tadin masoya" Fadeelah ta fada cikin tsokana.


Tsaki naja na hararesu sannan na daga,as usual, Gabana na Faduwa

"Gani a Garden ..Please ki Fito ina son Ganinki" ya fada a tausashe.


Mamaki ya kamani Cikin murya mai nuna Tsantsar mamaki na Nace "Please?....."



"yh" ya bani Amsa a takaice.

"Garden da daddaren nan?"


"Toh ko dai na shigo ne?"


"Tab....Allah kyauta....Tunda Gani Rasa kunya kazar birni ba....Kaga Banida lokacin ka yanzu, Bye" diff na datse Wayan.

"Munahika...Dan kin Ganmu shine bazaki Tadin ba ko ya?" Inji Fadeelah


"Kunfi karfin Ku hanani Zuwa ,Kawai dn baikai matsayin da zan bishi bn!"

Nan muka fara Jayayya cikin Tsokana.


Muka hakan naga An turo kofa an shigo Babu ko sallama ko yayi nidai banji ba.


YaaAary ne Sanye Cikin Farar Riga Mai Ratsin baqi da Baqar Wando Gashin kansa Sai sheqi Yake, Aaryaan kyakyawa ne sosai da ka Ganshi kaga Sai jinin Sindh.


A 'Dan Razane na 'dago ina kallonshi ,Su Hafsah suka Gaidashi ya Amsa CikiCiki.


Ni kuwa a Raina Auna masa zagi nakeyi Taya zai Fado Dakin Mata babu ko sallama ,Allah ya so da suturar Arziqi a jikin mu da yaga Bati๐Ÿคญ.


Hafsah Taja Hannun Fadeelah suka Ratsa Gefen Sa Suka Wuce ,Nima na Miqe zan Bisu ya damqi hannuna ya maidani baya, Har Saida na saki Yar Qara...


"Please Cikani, zaka karyani ne?" Na fada a 'Dan shagwa6e .


Sakin Hannu na yayi Ya kurawa hannun Ido Tabbas Zanen lallen dake kwance a fatar Hannu na ya mn kyau sosai ya kumayi matuqar dacewa da kalar hannun nawa,Shiyasa ya kasa dauke kallonsa daga hannun.

Nima shi nake kallo yanda ya shagala Wajen kallon hannun nawa.

Sake Ratsawa Gefensa nayi zan Wuce Naji ya qara Riqo Hannu na ,Ba tareda nayi zato ko tsammani ba naga ya daga hannuna ya kai Saitin bkinsa ya sumbace shi.

"kinyi kyau" ya furta a Hankali yana sakin Hannu na.


Wani irin Yaarr naji Wani Abu ya Ratsa tun daga tsakiyan kaina ya tsirgo har tafukan kafafuna ...Tuni qafafuna Suka fara Rawa.

Na nemi Guri na zauna ina Sauke Ajiyan zuciya.


Matsowa yayi Kusa dani Ya zauna ya kamo hannuna , hakan yasa na Fuskanceshi Cikin tsoro.



Ya Lumshe ido yana Tunanin girman Kalmar da zai Gaya mn,Da kuma yanda zan Daukeshi.


"I.....Love..... You.....Munayferh" ya furta a tsorace kaman Munafiqee.

Kwace Hannu na nayi na Miqe tsaye a Fusace

"You Love Who?....Me?....Never!" Na fada a rude ina kara ja da baya..


Ya kuma tasowa zai Riqe hannuna Cikin tsakanin tashin Hankali Wannan shine last Chance dnshi idan Baiyi hakan ba babu makawa a darennan Aurensu zai Yanke.


Matsawa baya nayi ina Girgiza kai ,Cikin kidimewa Anya wannan Aaryaan dinda na Sani ne kuwa?, Aaryaan dinda na Sani bazai ta6a takowa Har inda nake ya Furta mn Yana so na ba.

"Please dear, ki saurareni mana....Am saying This 4rm the bottom of my hrt....Aap Meri zandagi mera pyar (you're the love of my life).


"Ni kuma na Tsaneka, I hate you I hate you!, Aaryaan, na Tsane kaMai nafrat karta (Na tsaneka) ....." Na qarasa da Fashewa da Matsanancin Kuka.

A sanyaye ya tako Gabana yasa Hannu zai share mn hawayen na kawar da kai Ina haki.


Ga mamakina sai Gani nayi ya durqushe Gabana........






Baabaa yaji ta matah ๐Ÿคญ๐Ÿ˜น









Team Munayferh Cheers๐Ÿป๐Ÿป๐Ÿป


Team Aaryaan How market๐Ÿ˜น







Waiting For ur Comments






Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ



27th September
[30/09 1:08 pm] Fahnaan๐Ÿ’–: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 38_*


Yaseerah Taja Yar Gajeruwar tsaki tace
"Aikin Banza, mutum naqinki ke kuma Kina wani ji da ita"


Rucky ta ta6e baki

"Gane mn hanya fa"


Ramlah ta Hararesu "Wa ya Gaya mku Bata so na?,Ita fa ba dan bata sona Take mn hakaba,Akwai dalilinta nayin hakan..... Kunsan Allah, ko Sau daya ban ta6a Ganin tsanata a idanunta ba,Kawai horo ce..."ta qarashe maganar da ta6e baki.

"Horo laifi kika yi mata?" Inji yaseerah.

"Uban laifi nayi mata,Wai ina Ruwanku ne!" Ramlah ta fada Cikin 'Dan fusata.

Rucky tayi dariya
"Yalinya Bazaki ta6a Gane tsanar da take miki ba sai ta Aikaki chan duniyar, ta kuma aika Ahalinki Kaman yanda ta fada da bakinta......Nasan ko ba'a fada ba itace ta zuga 'danta ya qara Aure ko Dan ta Cusa miki baqin Ciki.."

"Kwaji dashi"

Yaseerah tace "Mugun ma!....Kinsan kuwa wacece Amaryar?"

Rucky tace "Aa,Bani nasha".

Yaseerah ta Fito da Wayan tana Dan Latsawa.


Kunna Wayan tayi Sannan ta haska ma Rucky

"Kin Tuna ta....?"


Gaban Ramlah ya fadi,ta matso kusa dasu tana son Ganin hoton, Dan Tasan tabbas Basu San jaanaan ba...

Rucky ta buga Salati innalilahi "Kice Fitinanniyar Qanwarnan tasa..."

Fit Ramlah ta Fizge wayar.
"Mtssw,Har kin bani Tsoro....Matar Da qanenta zai Aura ce fa''


" Mtssw...kin cika shirme wlh,Yanzu ko kishiyar taki baki Sani ba kenan"


Ramlah ta harareta "Nasanta mana Kawar yarinyar ce Matar"

"Wlh ba ita bace,wannan ce"


"Nace miki ba ita bace,Qawarta ce"

"Itace"

"Ba ita bace". haka sukayi ta jayayya Suna musu sai kace yara.


Rucky kuwa tana Ganin Sun fara ta dauko Wayan ta tafara msu Coverage tana dariya, inda Sabo ta saba da Halin Qawayen nata.

Da taga Abin nasu Ba Qarau bane sai ta tsayar da Coverage dn ta fara qoqarin Saita su,As their lawyer.

"Ke Seerah, Meye naki na jayayya da Ita, tunda tace Ba'ita bace Sai ki qyale ta"


Yaseerah tace "baza'a barta ba,Wannan itace Amaryar"

"Ahw kaina kk Komo?"


"Ehnn naah...Help us Settle this matter,ni Inada Evidence Wa'enda zasu Nuna tabbas Wannan ce Matar"


"Ke kuma fa" inji Rucky tana duban Ramlah da ta kusa Surrender.


"Mahaifinsa ne ya hada ,kuma Aaryaan ne ya Gayamn da bakinsa.... I'm sure Bazai mn Qarya ba"

Yaseerah tayi shewa "Ahayye....Your own love na blind ooh, waya Gaya miki ana Yarda da Namiji a wannan marran?,Har zai Gaya miki Ga Matar dazai Aura kuma ki Yarda..., Wlh dukda Ban Sani ba,Nasan Akwai Soyayya mai karfi a tsakanin su, da ba Don kar na Nuna miki wani Abu Hawan Ruwanki ya tashi ba da na nuna miki Hujjata".

A halin Yanzu Ramlah ta fara karaya,Amma zataso taga Hujjan da Seeyrah Ke Boyewa.


"Feel free ki nuna mn Hujjar na Gani"


"I won't" yaseerah ta fada Cikin murya mai kaman Na rada Da tsokana.

"Please Yaseerah, wai Meye haka?, Tunda tace Bata Yarda ba Feel Free and show her ur evidence manah"

Yaseerah ta kalle Ramlah Wacce ta qureta da idanu tace "Lemme have my Phone"

Miqa mata Wayan tayi,Ta fara Latsawa, ta nemo wasu Hotuna.

"Rucky take a look at this Please me kika Karanta Cikin kallon Kallon Kallonnan...Ba haka ba mah inada ire-Iren wa'ennan hotunan dayawa Nayi screenshot dinsu a Instagram, Mr-Blaq beauty (hilaal) shine yayi Post din jiya with the Caption 06Couples,kuma naga Talla A tV da safennan....in fact Dan na tabbatar da hakan Yasa Nace Rucky ta rakon ..."


"Mu Gani" Ramlah ta fada tana Kar6ar Wayan

Hotonmu ta Gani ina Rungume da hannunshi ina kallonsa ina dariya,Shima Dariyan Yakeyi Idanunsa Cikin nawa,dkkan Sanye muke Cikin kaya Sky Blue mai Ratsin Royal Blue,Ba qaramin kyau mukayi ba.

Ramlah kam Ranta ya Gama 6ace, wani irin daci da kishi Suka dirar mata a wuya,Meyasa Aaryaan zaiyi mata Qarya?,Meyasa zaiyi anfani da Son da take Nuna mshi ya cutar da ita, ko Dan yaga Auren hadi Sukayi ba Na Soyayya ba!,Ji take kaman ta fashe Don kishi,A Hankali hawaye Suka fara Diga kan Fuskarta,idan Munayferh ta Auri Aaryaan nata ta ta ta Qare,Don harga Allah tana mugun tsoron Munayferh.

Dafata da akayi yasa ta dawo cikin hayyacinta, ita tama manta da Mutane a Gun.

Jiki a sanyaye Suka shiga Rarrashinta.

Ruqqayyah tace "please ki kwantar da hankalinki, ko ya dawo karki nuna msa damuwanki ,Share zancen zakiyi kaman bakisan Da wani Abu ba,Idan yayine Don ya Kuntata miki Allah ya fishi...."



******

"Keh,Banson shashanci ,Tashi kishirya Ku tafi inda zaku"

"Ammie, dan Allah ki qyaleni Nace bazani ba, dole ne" Na fada Cikin Turo baki tareda Miqe na koma daki na Kulle kofa.


Ina shiga wayana ya soma Ringing.

Jawo Wayan nayi na duba mai kira.

ABBIE ne ya kira.

Dagawa nayi Na kara a kunne Tareda mirginawa saman Gado.

"Abbiey naa"

"Naam princess"

"Ya Aiki"

"Alhmdllh,Princess Hafsah ta Kirani ta Gaya mn kince bazaki Gyaran Gashi ba"

"Eh,YaaAary ne ya hanani"

"Zancen banza kenan,ki Shirya yanzu Junayd ya kaiki"

"Abbah....to ka....yi mshi Bayani" na fada Cikin Murya mai nuna Alamar tsoro.

"OK bari na kirashi na hada Conference Call"


Kafin na Sake magana Har ya datse wayan.

Ya kirani bayan ya hada Call dn da na Aaryaan.


Abba yace "Aaryaan, Meyasa ka Munayferh Zuwa Gyaran Gashi?"

"Dad babu Amfanin haka ne kawai" Ya fada Cikin murya mai nuni da Tsantsar rashinGaskiyan Sa.

Abba yace " Amfanin shi da Rashin Amfaninshi Duk ba Abinda Ya shafeka bane,Tunda babu Ruwanka da ita.....Princess Oya ki Shirya Zan Turo Junayd yanzu nan"

Wani Irin Ihun Murna nayi.

"Wowww thank you so much Abbie na!,Ahloveyou muah" na sumbaci Wayan .


KamBala'i dama Conference call Abba ya hada masa da yarinyar nan,Amma ba qaramin Goge masa hadda yayi ba,yanzu duk fadan da Abba yayi masa A kunnen ta?....


Dif ya datse Wayan ya lalubo number na yayi dialing, kaman Jira nake na daga.

"How far" na fada Ina hararar Wayan.

"Idan kika kuskura Kika tafi tareda Junayd sai Ranki ya 6ace"

"To Kai baka Ji maganar Ubanka ba,shine kake Tunanin Ni zanji naka?" Na fada Cikin turo baki.

Shuru yayi na 'Yan wasu seconds, kana yace

"To ki Shirya Gani nan Zuwa,Zan kaiki"


"YaaJunayd dinfa?" Na fada ina Zaro ido.


"I don't Fucking Care ki Fito yanzunnan ina Balcony" yana Gama Fadin haka ya datse Wayan.

Bude labulen Window nayi na leqa naga Tabbas yana nan zaune a farar kujera Riqeda waya.

Ina Shirin Rufe kofar naga Shigowar Janaan, Sai na tsinci kaina da Kasa Rufe windown, Na kura mata ido.

Har ta wuceshi naga ta dawo,Da Alama shi ya kirata, Sun danyi magana Kafin ya Ciro wata Yar takarda ya miqa mata,ta Amsa Sannan ta qarasa shigowa.



Rufe windown nayi Ina Auna msu zagi a Raina, haushinshi da na Janaan ya kuma ninkuwa A Raina.


Bayi na fada nayi Wanka, A gaggauce na Shirya, cikin wani Maroon Arabian gown na nade kaina da gyallen rigar sannan na rataye side bag dina black.

Mashaallah Dukda banyi Wani kwalliya ba, nasan nayi kyau sosai Sai maqiyi.

A falo na Iske Janaan Har ta shigo Tana zaune qasan Rug tana yankewa Ameerah farce, Suna Dan Ta6a hira da Ammie...



Tana Ganina tace "Yewwa Neryfee,Dama....."


Bata Qarasa ba, Sakamakon Hararar da Na 6alla mata, Hadi da Jan doguwar tsaki.

"Ina Zuwa kuma"
Ammie ta tambaya tana Kallona.

"Saloon" na bata Amsa a takaice.

Ameerah na jin haka ta Miqe da Gudu ta nufi dakinsu.


Janaan tayi Dariyar izgilanci tace
"Ammie, YaaAary ne zai kaita fa... Yace na Ganshi a Waje yace na Gaya mata sau....."


A zafafe na dakatar da ita ta hanyar Rankwashinta

"Munafika kawai haka Zaki qare banja kawai" na karasa ina hararar ta.


Ta Riqe kai zatayi magana Ameerah ta shigo Riqeda takalmanta tana Fadin "Anti na tilya"

Cikeda masifa nace "Dalla Koma ki zauna babu inda Zaki.. da lebenki anan kaman na tilya"

zama tayi a qasa ta fara mirgiman 'Yan bori tana kuka..



Kamota janaan tayi tana cewa "Dan Allah Aunty A taimaka aje da ita, karta mana masifar da ta saba....taso muje a wanke Fuskar Bari na kawo Miki wasu kayan"


Suna Shiga daki nayi tafiyata.


Jingine na Ganshi A jikin motarsa Yana latsa waya, yana Ganina ya shige motar yana kokarin tadawa, Saiga Ameerah ta Fito da Gudu Cikin readymade Sky blue Mai ratsin Fari tana Fadin

"Anti ki jiya Ni"


Dafe kaina nayi Cikin Jin haushin Ta, na kamo hannunta na bude Backseat zanshiga Yace na dawo Gaba.


Saida na harareshi Kafin na Shige Gaban ina Turobaki ,na daura Ameerah kan kafata yaja mota muka bar Gidan.

Na dubi Ameerah cikin Kufula Nace "Kinsan Allah Amiya zan farayi miki Bulala, tunda bakyaji"


Bata fahimce Ni ba sosai Don haka tace "Allah Anti?..Zaki koya mn yanda Akeyi?"

"Zaki Gane kurenki"

Ta fashe da dariya tana duban hanya ta madubin motar

"Laah Aunty ,Uncle ku kalle Shanuwa"

Aaryaan yayi Dan Murmushi Hankalinsa akan hanya,Nima murmushin nayi na gyada kai Shirmen banza Na fada a Raina.

Ita kuwa hankalinta ya koma kan Shanayen da ta Gani Suna Gefen hanya ,Tsallenta takeyi tana Waya

"Shanuwa mai janbaki, tayi 6ayi bata Kashe fa, yashe Allah yaisha Ga geyo Ga dawa....."

Na dubeta na kama dariya,komai ta Gani A hanya sai Tayi magana akansa Idan kuwa bata Sani ba sai ta tambaya ya Sunan wanchan Abin,Haka na Cigaba da Biye mata muna shirme Shi kuwa bai tanka mana ba sai uban murmushi yakeyi Akai Akai,Yanaji nishadi na Ratsashi.


Har muka Isa Shagon Akayi mn itama Ameerah nacewa tayi sai anyi mata Akayi mata na yara daidai da Qwaidus dinta๐Ÿ˜„....


A hanyarmu na dawowa ya kira Ramlah.

Tana dagawa yace "Akwai Abinci a Gidan?"

Banji mai tace ba na daiji yayi dariya yace "Wato Namu Babyn da kwadayin Dankali yazo"

Ya danyi shuru Kafin yace "Ehmana wai Dama baki Sani ba?,....Boye miki nayi Saura seven Months na zama daddy"


Gabana ya Fadi na juyo na kalleshi Cikin tuhuma ,tunowa nayi da Ashe yanada Wata Matar na maida kallona Gefen titi ina Ta6e baki , ~shi dai ya shiga Uku duk macen da ta Ra6eshi Sai tayi ciki~โ˜น๏ธ.
***
Dadaddare Bayan Abba ya dawo ya kirashi yayi mshi Wankin bargo Wai Meyasa Zai kaini Bayan bashi ya Aika ba,daga qarshe yace koma meke tsakanina dashi daga yau ya yanke, kar ya sake Ganin ya takura mn.

Hankalin Aaryaan yayi matuqar tashi dajin Hukuncin da Abba ya zartar akansa,yana Gudun kar Wannan hukuncin ya zamo silar tarwatsewan iguyoyin Aurnsa dake kaina,Shiyasa ya Fito ya Gaya mshi Gaskiya..


"Abba Mata tace fa"

Abba ya dago ya kalleshi da Mamaki fal a fuskarsa "Matar ka?,Kayi hauka ne?".

Abba Banyi hauka ba,Mata tace.....nan ya Gaya mshi yanda Akayi Amma bai fada Mishi A iceCream aka zuba dispensing Pill din ba,ya daice Sun biya Wani Guri ne aka basu Wani Abu mai hade da pill,harda nuna mshi Video yanda Aka daura Auren Inda maqotansa nadaa Wato Abbu (Mahaifin Dr sufyan) da yayaBukar (Babban Dan Abbu) Suka Wakilce Auren.


Jikin Abba yayi sanyi ,Tabbas yasan dansa nason Munayferh kuma taimakonta yayi,Amma dukda hakan Saiya ce zai kirani yaji daga bakina idan ina sonsa Zai Bar Auren idan kuma Bana sonsa babu dole.


Aaryaan yace "Aah Abba,please Basai tace tana sona ba"

Abba ya muskuta Yace "Toh kai Sonta kakeyi ne da zaka ce haka?"

"Aah .....Ehmm....Amma...." Sai ya kasa karasawa ya Sunkuyar da kai.


"Amma me?"


"Tana dauke da Cikina na wata Biyu" ya fada yana Sosa kai.........


Abba ya Kureshi da idanu ya ma kasa Magana,Don Ganin Abin Yake kaman a shirin Film, Wai sunyi Aure babu Wanda ya Sani kuma Suna zaune Gida daya Basu fadawa kowa ba, harda Tsarabar Ciki๐Ÿ˜†..


Abba ya Zaro waya ya kirani Wai inzo yana nemana, Har na dau waya zan tura mai Don Neman izinin Fita,Sai na tuna Ashe darene.


A Falonsa na Iskeshi ,Zaune kan kujera Aaryaan na Zaune a qasa Kansa a Sunkuye,


Haka kawai na Tsinci kaida Cikin faduwar Gaba,ina Shigowa bada dadewa ba UMMA ta shigo Riqeda Tray mai daukeda Coffee ta Ajiye Gaban Abba sannan ta Sami wuri ta zauna tana sonjin Kokwaf๐Ÿ˜† ....


Abba ya dubeni na wasu 'Yan seconds yace "Princess.... Dama Akwai wata Alaqa ne Tsakanin ki da Aaryaan?"


Daammm naji Gabana ya Fadi.

UMMA ma Kallona take tana Jiran Amsar da zan bayar.


Na dago na Dubi Aaryaan naga Shima Ni Yake kallo, da ido nayi masa Alama da ~in Gaya?~


Ya Gyada mn kai alamar Eh

Na kalle Abba Na kuma Sunkuyar dakai Cikin jin kunya ,sai na kasa Fadin komai.



"Ke nake sauraro"

"Ehm..ehmm....Uhmm" na fada Cikin Duburcewa.

...

Daga mn Hannu yayi

"Ya Isa"

Ya dubi Aaryaan da kansa Ke qasa Gabansa na Faduwa yace

"Meyasa Tun tuni baka Sanar dani ba?" Abba ya fada Cikin Fushi.

"Ehmmm....ina fargaban kar...Ehmm...kar kace na Saketa ne Tunda ....uhmm"

Wani irin Zufa ya fara kyakkyafo Wa UMMA tadan Zabura Cikin matsanancin Firgici ta soma magana....




















Chaii๐Ÿคจ


Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ




26th๐Ÿ–‹๏ธ๐Ÿ–‹๏ธ
[30/09 1:08 pm] Fahnaan๐Ÿ’–: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 42_*



*dole in faranta muku masoyan Hawanjinina*

*jinjina agareku da godiya me tarin yawaโฃ๏ธ*





***

"Noooo!, Never!, Bazai yiwu ba, Bazai ta6a yiwua ba, Aaryaan da Shaidaniya ?, inaa Wlh bazai yiwu ba, ina Neman hanyar da zan Tarwatsa Unknown Auren da Suka daura, na saki baki ina jiran ya sakota sai inji An kuma dauresu?, Bazai Yiwu ba Alhaji, kasanni da akan Abinda na tsana....idan kanaso 'yarnan tayi tsawon Rai To ka gaggauta nema mata Takardarta a yanke akaqar da aka kulla tun Wuri...If not wallahi Ko zanyi Yawo tsirara ne sai naga Bayan 'Yar iskan Yarinyar nan da ita da Uwarta .....Sune Silar Rugujewar Farin Cikina, Tun da aka Auro Uwarta na rabu da farin cikina a Gidan aurena, Uwarka ta Fara takura mn Dama chan ba sona takeyi ba......"


Sai tayi Shuru Alamar Ana magana ta dayan Bangaren,


"Nabi sa Albarkan da Gudu....idan har sai na sa Albarka tukunna zasu Sami Albarka Cikin zamansu Allah ya Tsinewa Albarkan Dake Cikin Auren.....Alhaji Gaba daya ka manta Wacece ni shiyasa Kake Min fin qarfi A......."

Ding Taji an datse wayan.



Wani irin Kukan Takaici ya kufce mata, Hajiya Asiya (Aminiyarta) Dake zaune kusa da ita tayi Saurin Toshe mata baki tana Girgiza mata kai.



"Please stop ,Kin manta da mutane a Falor ne?, Ai zasu iya jinki Suyi mki fassaran da ba shi ba, Kiyi Shuru kawai Ki bar mn komai a hannuna"

Da qarfi ta Cire hannun Ta Wanda ya toshe mata baki tace

"Mai Tsoron A mutu shi Shege ne,Gara A jini dakyau asan irin tsanarda nayi mata...Na rantse ko zanyi yawo Tsirara ne Sai naga bayan Wannan Qaddararren Auren, Saina 'dandana msu kadan daga cikin Ukuba da Sharrina"

(Auzubillahi)


***

Can 6angaren angwaye kuwa Abin ba sauqi sai Allah ya sanya alhairi ake zuwa yi musu, Shi kuwa Aaryaan Fuskar nan kaman gonar Auduga Jiyake kaman Wqnnan shine Aurensa na Fari, haka junayd sai Barin naira akewa Maroqa kaman basu San zafin nema ba.

Maroqa kuwa kasuwarsu ce tabude, nan suka baje Akalansu suna wasa angwaye.

****


Sosai ake shagali yau mah Gidan su janaan akayi taron 'Yan matan Amare.


Yauma Ankon Qawayen iri daya ne, Styles da dinkin iro 'daya ne, kuma Sosai akayiwa Naira kisan Gilla.


Kasa Haquri nayi na tambaye janaan Wai ina suka Sami Uban kudin nan ne?, sai tace Wai YaaAary ne ya bata Cheque Ranar Wai ayi Shiryeยฒ dashi, A ranar da Yakaini saloon****

Saida Akayi da Gaske kafin Aaryaan ya Amince za'a dinner don bai Masan da zancen ba, Su Junayd ne da Abokansane Suka shirya komai batareda yasani ba.

****


Sosai Amare sukasha Fada Wajen dangi , Janaan tasha kuka kaman ranta zai fita,dan Sosai Fadan ke Ratsa Kowane kafa na Jikinta yayinda Su Aunty Munayferh take kallon Cikin kwayan idanunsu tana Kirgan kalamansu.



8:00pm aka fara shirin tafiya dinner NANA makeover ta tsaya ta tsantsara musu makeup sosai na Bugawa a Novel....

Aaryaan da Junayd

Please Login or Register in order to submit comment