Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa hannu ya dau wayar,ya karanta saqon,Bai karanta dukka ba,Yana ganin an daura yaja mota ya ๐Ÿš˜,Sai Aafreen Hotel.

Gaba daya bansan yanda Akayi ya kama mana daki ba,HotRomance ya fara Aika mn nima banyi qasa a Gwiwa ba wurin maidar masa da martani,Na fada wata duniya ta daban, Daga ni harshi kowa yafita hankalinsa, dan idonmu yarufe bamusan me Muke aikatawa bama,Barin ma ni da Tun kafin A shigo na Tashi daga Munayferh zuwa BABYDOLL

Hankali na Gaba daya baya jikina,Wani irin Murdawa da marata tayi bansan lokacin da na Riqe na kwala ihu ba,Na fadi qasa sumammiya.



Ihun da nayi ne ya Firgitashi yasashi dawowa cikin hayyacinsa, Sai a lokacin lura da Abinda yake shirin Aikatawa.


Tashi yayi a kaina ya koma Chan Bakin Gado,Ya dafa kansa dake wani irin Sara mshi,Saida Ya saita kansa Tukunna kafin ya juyo ya kalle inda nake Yashe babu Alamar Numfashi a tattare dani,


Ya Dauko Ruwa daga Fridge dindake dakin har zai yayyafa mn, Ko me ya tuna oho,Sai ya fasa Ya dauko Biro da paper Saman Deck yayi Yar Rubutu Sannan ya kira A turo masa messenger.


2mins tsakani Saiga Messenger ta kwankwasa kofar,Bude kofar yayi ya miqa mata Takardar da yayi Rubutu, yace ta Je Chemist ta Siyo mshi magungunan.


Ta kar6a tayi Gaba shikuma ya fada Toilet yayi wanka,Sannan ya hada Ruwan zafi ,A lokacin yaji ana knocking,

Yaje ya bude kofar,Messenger ce Riqeda Leda,ta miqa mshi ya amsa yana Godiya.

Sannan ya dawo inda nake Kwance,Yasa hannu ya dagoni Ga mamakin sa Sai Yaga jini duk ya 6ata farar blanket dindake Shimfide a kan Gadon,


Waro ido yayi,Shi dai yasan Babu Abinda ya mn Amma me ya kawo Wannan jinin kuma?,Tunaninshi ya Tsaya Chak lokacin DA ya tuna kwanan Watan...


Bude Ledar yayi ,Yadauko Wata tablet ya 6are ya sa min A baki,Sannan ya Dauko Ruwan Gora ya Zuba CIKIN Bakin.

Sannan ya Yayyafa min Ruwa ,A hankali na bude Idanuna har na waresu a kan sa,Rumtse idanu nayi Dan a Halin yanzu Babu Abinda zan iyayi ,

"Keh Open Your Eyes"

Babu musu na bude Idanu Amma Na kauda kai Gefe,Dan bazan iya hada ido dashi ba.

Ya cigaba da cewa '' d'agani,Ga Bayi nan kishiga kiyi wanka"ya fada yana Nuna mn bandaki..


Maimakon na Tashi Sai turo baki nayi , na fara kuka har ina Shidewa,

A hankali Kwakwalwata ta fara tariyo mn duk abinda ya faru, dani tamkar a mafarki,Wasu hawayen suka Kara zirya Saman kunci na,Wayyo ni Munayferh yaaAary ya Gama Dani ya Rabani da mutunci na,๐Ÿ˜ญShikenan! Wayyo Allah na Shiga 3na lallashe.....



Jinayi kawai an dagani Chak kaman wata Yar Tsana zuwa bayin an direni Cikin Ruwan zafi,Rumtse Ido nayi Ganin yanda Ruwan ya fara Sauya kala zuwa launin Jaa.

Fita yayi ba tareda ya Cemin Kala ba,Na bi bayansa da Harara.

*Aikin banza baimasan kinyi ba๐Ÿคง๐Ÿ˜„*.


Yana Zaune a dakin Dafe da kansa yana mamakin A ina na samo icecream me dauke da sinadarin Sa sha'awa?,Kodai wannan danIskan saurayin DA ya ganmu tare Yabani?.

Kusan 30mins Shuru ban fito ba sai yayi Tunanin ya dubani ko lfy.

Yanda ya bar ni haka ya Sameni.


Banida niyyar notsawa bare nayi wankan,yasanni da Raki da son jiki,Banqi nayi ta zama a cikin Ruwan nan ba har saina Gaji Dan kaina.

Ba tareda 6ata lokacin ba ya Sauya Ruwan da nake zaune a ciki Wanda tuni ya Koma Sak jini .


Sannan Ya Shigo Cikin Bathtub ,Ganin yana Shirin Yi mn wankan yasa na Bude baki a hankali nace

"Please Ka Fita,Zanyi da kaina"

Bai kulani ba,Saida yayi mn wankan ,Ai kam yasha Cizo da yakushi Amma Bai sarara ba saida Ya Gama,sannan ya Dauke ni kaman yanda ya kawoni ya Maida ni cikin Room din,,Amma fa naji dadin jikina Sosai,


Ya saka kayanshi sannan ya Fita babu jimawa ya dawo Riqeda kayan Sawana na Baqar Jallabiya doguwar Riga Ya Wurgo mn,sannan ya miqamin wata yar leda yayi Ficewarsa.


Ledar na Fara budewa ,Pads na Gani a ciki da sabbin Pnties....


Saida na Gama kimtsawa kafin ya Shigo kallo daya nayi mshi na kawar da kai gefe

Ya jawo kujera ya zauna Saitina yana Fuskanta ta,Fuskar nan babu Alamar wasa yace"Munayferh ina Kika samo Icecream dinda kk Sha dazun?"


Duk da nayi matuqar tsorata da yanayinsa ,Amma Saina kawar da kai ina turi baki nace"Yo ina Ruwanka da Iceceam dinda nasha?,Kai ka bani ne?"

baice komaiba,Amma Nasan maganganuna sun Sosa ransa ainun,

kaman bazai tanka mn ba chan kaman an tsikareni ya wani zabura yakamani ya hada da bangon dakin,Ya matse ni a kirjinsa sosai da Qyar nake iya Fitar da numfashi ,

Gani nake kaman kasheni yake Shirin yi,Idanuna sun Firfito waje, ya wani ci uban Magani fusakarsa amatuk'ar murtuke, yace โ€œIdan kika Sake mn Gardama Saina kasheki Na birneki anan Kuma babu mai Kamani akan hakan"

Yanda yayi magana babu Alaman wasa na tabbata a raina Tabbas zai iya Aikata Hakan,Baki na Rawa cikin murya mai Nuna tsananin Tsoro da fargaba nace"Yaa Dan Allah ka Cikani wlh zan fada ma"

Kara matse ni yayi da bangon yace"Fada mn waya baki ?"


Baki na Rawa nace"Ba bani akayi ba"

"To a ina kika samo shi"

"A motar yaa Umar na Dauko"

Wani irin Bugu zuciyarsa yayi,Ya ja da baya tareda sakina yace "What!, You mean Umar ne yasa pills cikin icecream...?"


Yana Sakina nayi qasa Ragwab ina maida numfashin wahala a raina sai Jero masa Allah ya isa nakeyi.


Ganin da yayi Hankalina Gabadaya baya wajen shi yasa ya dagoni ya zaunar dani a kan kujera yace"Munayferh waye wannan mutumin da na ganku tare?"

Baki na rawa nace"Sau...ra...yi na ..ne"

Harara ya watsa min "Ke ko kunya bakiji ba ki rasa Wanda zakiyi soyayya dashi sai Yaron nan...Mtsww" yaja Dogon tsaki yana kawar dakai Gefe.


Sannan yasa hannu cikin Aljihu ya Ciro Rafar Yan biyar biyar har Guda uku ya miqa mn yace"Ga sadakin ki nan!"

Kallon sa nayi cikin Rashin fahimta ina Neman qarin bayani,ai kua kaman ya San tunanin da nakeyi yace"Dazu kinsha icecream mai kunshe da Sinadari mai sa sha'awa shine na taimaka miki na aureki Dan karki mutu"


Mamaki ya kamani Bakina har rawa yakeyi nace"Wallahi Qarya ne babu Auren da Aka daura,Dan Rainin wayo Yan biyar-Biyar ne sadaki na?"


Bai tankani ba ya Ciro wayanshi ya bude Text message dinda Hilaal yaturo masa ya miqa mn wayan


Amsa nayi jiki na rawa Ina karantawa ciki na ya wani irin murda min,Ban San lokacin da na yi jifa da wayan ba na dafa cikina Nace "Wash"...


















NIMA WASH NAYI GABAS๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

TEAM AARYAAN KU BIYONI MU TAFI๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ


TEAM MUNAYFERH KU TSAYA KU TAYATA KUKA๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜„๐Ÿคฃ


TEAM RAMLAH KU FARA TAYATA KISHI fa๐Ÿ˜ญ๐Ÿคฃ





Aradu na arce๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ



Wattpad @Fahnaan

3rd Sep?๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 23_*

"Wash Cikina"

Na fada hawaye bisa kunci na

Ko Kallona baiyi ba Ya ta6e baki tareda daukar wayanshi Yace "In kin Gama kukan ki biyoni" ya dau kudadenshi ya maida Cikin Aljihu yayi hanyar fita,Na biyo bayanshi Ina Tafe kaman wacce Kwai ya fashe ma a ciki!,Ya sallemesu muka bar hotel dn


A mota kuwa Jingina nayi da seat din Motar ina kuka mai ban tausayi, Sai yanzu Memoryn kaina Ya fara Tariyo mn Abinda ya faru Tun bayan Fara shan Icecream dinda nayi,Harda wayan da Sukayi da Hilaal,Kuma na tabbata yaAary bazai ta6a mn karya akan Hakan ba.


Shikenan Tawa ta Qare na zama Matar yaaAary a dalilin Icecream na Rasa daraja ta๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ,Na shiga uku Rayuwa ta tazo Qarshe Innalillahi wainna ilayhirrajiun Kuka nakeyi da iya karfina har ina shidewa, Amma ko sau daya bai juyo ya kalleni ba Bare nasamu Darajar Rarrashi.


Muna isa PZ ya yada zango a chicken Republic yy mn ordern Abinci,Muna hanyar GRA Hafsah ta kirashi Saida ya Sace kallona kafin ya daga yana murmushi.

Yace "Ya akayi Auta?"

Hafsah tacd"Yaa ka ganta ne?"

Yace"Yanzu haka ma muna tare"

Hafsah Ta sauke Numfashi sannan ta ce"Alhamdulillah To ka Ce ta karaso School Saura 15mins Mu shiga Ajin CHE122 kuma ance Yau Test Zaiyi"

Yace"Tho Gatanan Zuwa"

Tace"To ka hadani da ita mana"

Yace"Call her line" sannan ya katse wayan.


Kaitsaye ya Juya Akalar motar Zuwa ABU Zaria a Chemistry Department ya Farka mota Harna yunkura zan bude kofar motar,Sai najishi a Garqame na juyo na kalleshi ba tareda nace komai ba

yace"Wipe Ur Tears"

Babu musu na Goge hawayena Amma kaman ina Bude kafar Fitar hawayen ne Suka Dingi fita kaman An bude famfo.

Ya maida Kansa ya jingina da seat yana kallon sama ya dau 2mins kafin ya ce"Idan Kin Tsayar DA Hawayen Sai ki fada mn,A Lokacin Zaki Fita"

Chak Hawayen Fuskata Suka tsaya Dan Zaman da Nayi a motar ji nake kamar a Kurkuku nake

Ya dan lumshe idanu kafin Yace "Dauko hijab ki saka" ,Da sauri na Janyo jakata na dau hijab na saka.


Ya bude min Kofar har zan Fita naji yace"aaie yahaan"(Zonan)


Na dawo na zauna Idanuna Fal da Hawaye yace""Mai wada karta hu chupa ke rekhunga" (Ki mn Alqawari wannan zai zama Sirri a tsakanin mu )



Na kalleshi a hankali cikin in'ina nace"Gum....su..da?"(Sirri kuma)


Yace"Eh aurennan ya zama Sirri! A tsakani na dake karki bari ko su Hafsah su sani"

Na maida kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna nace"Mai wada karta hu"(Nayi Alqawari),Na fada Hawaye na Kara zubowa Saman Fuskata.


Ya furzar da wata iska mai zafi ,Sannan in his cool voice yace "Rona band kro"(Stop Crying).

Jiki a sanyaye nasa Gefen hijabina na Goge kwallar da suka zubo mn.


Da kanshi ya bude mn sannan ya miqa mn ledar Abincin da ya sayo a Chicken Republic.

Ina Fita ya Rankwafo ya leqo yace" Idan kuka tashi Karki Je ko ina Kice Hafsah ta kira ni zanzo daukan ki dakaina"

Kaina na Gyada a Raina nace ~Kana Ruwa๐Ÿ˜’~


Ya tada mota ya bar Harabar Makarantar ,Ina tsaye nabi bayan motar da kallo ina kitsa Abubuwa da dama a raina,Saida na Bar Ganin kurar motarsa Sannan na Chanza hanya na nufi hanyar Fita daga Makarantar.


Kai tsaye Gidan Jaanaan na Nufa na Amshi makulli A hannun neighborn ta,Ina shiga na Fada Gado Taredaa fashewa da Wani irin kuka mai ban tausayi,Ni da Babu hukunci akan Wanda ya kashe kanshi ne yau da na Kashe kaina na huta ,Addu'a kawai takeyi Allah ya kar6i Ranta ๐Ÿ™„Da zama da yaaAary ta gunmace ta mace ko zata huta..



Shikuwa yana Barin Makarantar ya kama hanyar Kaduna .

KabalaCosten

Yana Shiga Gida ya hango Umar zaune a wata farar kujera nan Balcony Riqeda Waya yana latsawa, Kaman Wani Mahaukaci haka ya Parka Motar Dan Jin Zuciyarsa yake kaman zata Fashe Dan Baqin ciki.

Ya nufi inda Umar ke zaune hankali Kwance yana Sipping Wing Tail๐Ÿน .


Yayi mishi wani Irin fincika Ya daga Shi sama sannan ya hada shi da bango ya dingi Dukanshi babuji babu gani,Dukanshi yake ta koina, Gaba daya ya makance ko ina ya Samu Duka yake kai mshi,Saida yayi Liliss ya tabbata ya daku Sannan ya Qyaleshi.


A lokacin kuwa ma'aikatan Gidan Sun Taru Suna kallo Babu mai hanashi Dan Sunsan Halinshi, idan yana Mazga yanzu sai Abu ya Shafe su..


Aaryaan ya jawo wuyan Umar ya zaunar dashi yana Huci yace"kai wato banda Shayeยฒ,Har ka fara Neman mata kor?" Ya fada yana Kara Gara kanshi da bango.


Cikin wahaltuwa Umar ya fara magana"Wlh ya..ya ba..na ne..man mata....Na rantse da All..ah Ban ta..6a sanin 'ya ma....ce ba"

Aaryaan yace"Are you insane!, Ni zaka Raina Wa hankali kenan?,A ina kasamo Abinda kasa cikin Icecream! ".


Umar cikin karfin Hali yace "DanAllah kayi Haquri Ba Dan ita na Ajiye ba,Trust me please"


Aaryaan yy jefa dashi yayi Gefe sannan ya juya, Chak ya tsaya Ganin Umma Riqeda Kugu ta cika tayi Fam Sai huci takeyi,


Kallon kallo sukayi Wa juna Sannan a sanyaye ya janye idanunsa Cikin nata ya ra6a Zai wuce ta kira sunanta "AARYAAN!"

Bai kulata ba Dan yasan babu Abinda kulata zai Jawo masa sai tijara.



Da sauriยฒ ya nufi inda ya parka motarsa ya Shiga yaja Ya wuce yana Tunanin Tsiyar da zasu kwasa da Umma Idan sun sake haduwa.


Umma kuwa yana fita ta fada daki ta tarkato tarkacenta ta kwalawa Driver kira ,tace ya kaita Zaria.




***********


Saida yamma Liqis kafin janaan ta dawo tunda taje kar6ar makulli Neighbourn ta tace nazo amsan key mamaki ya cikata,dama tana mamakin mai ya hanani zuwa School bayan Hafsah ta Tabbatar yaaAary yace ganinan Tafe.


Kwance ta Sameni Saman Gadonta ina barci, Fuskata tayi Kacaยฒ da hawaye.........


Chan Gefena kuma Ledar Abinci ne yashe a qasa,


Bata tashe ni ba ta shige Toilet tayi wanka Ta daura Girkin dare sannan ty Alwala ta Gabatar da sallar Magrib.

Sannan ta dawo inda nake kwance ta Bubbuga bayana na bude idanu na waresu akanta,


Tace"Neyferh Ki tashi ki koma Gida dare yayi"

Cikin muryan mayen barci nace"Anan zan kwana"

Tace" wai Lafiya naganki Wani iri See Ur face ,yayi kacakaca da hawaye, Meke damunki ne!?"

Naja Dogon Numfashi Sannan na tashi zaune hawaye suka kara Gangarowa Saman Fuskata cikin kuka nace"kawai yau Banason kwana ko Ina ne sai nan, Please ki kira Hafsah ki fada mata ina nan!"


Tayi murmushi tace "you've changed,yanzu kin zama Cry Cry baby" ta fada tana Fidda wayanta

Nayi Yar Smirking nace "I will never Change dear, my Tears don't fall on nothing"






TOFAH GA UMMA HANYAN ZARIA


WACE KWASAR TSIYAR Z'AYI IDAN TAZO?



GAKUMA MUNAYFERH A GIDAN FAHNAAN.



WAISHIN ME ZAI FARU IDAN AARYAAN YA GANE MUNAYFERH BATA GIDA?



TEAM UMAR YA JIKI?




Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

Wattpad @Fahnaan

๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 24_*

Lokacin da Umma ta isa Gidan Aaryaan babu kowa a Gidan Sai Ramlah itama tana kitchen tana Girka Wa OGA AARYAAN Abincin dare.

Umma Tun A falo take kwala kira "Aaryaan! Aaryaan!!, Wai ina Ka Shiga ne?, Bakaji nane?,Eh? Kafito, Tunda ka Guji uwarka Gani nazo ,Kar ma ka fito Gidanka ne kuma na zo ,Bani komawa Ko ina Sai Alhaji ya dawo tunda Abin ya kaiga haka har Da zai Guji Uwarsa oh ni Sa'adiyyah banyi sa'ar Haihuwa ba wlh"

Ramlah dake kitchen taji hayaniyan Umma Gabanta ya yanke ya fadi Shikenan Qarshen Farin-Cikinta yazo,Jiki asanyaye ta fito Falo inda takejin Surutan Umma.

Ta fadada Fuskarta da Murmushi Tanacewa "Sannu da zuwa Umma ya hanya?, Ai Aaryaan din ya Fita Tun DA safe bai Riga ya dawo ba"

Umma ta katse ta"Na tambayeki ne?, iyeh!, Watoh duniya ta miki dadi Har wani Fresh kikayi Ga wani Kiba da kika karayi, lallai an Sami hutun Sati Biyu an murmure An barni sai Qashin wuya da Tayani muni nake Tarawa, to na dawo nima Kibar nakeso nayi Na murmure na more dana Ehe!,..... Ji yanda Fatarki ta Sauya kala ta koma Jaazir kaman Baturiya, ke anya ba Ciki Gareki ba kuwa"


Ramlah ta sunkuyar dakai Cikin Jin nauyin tambayan umman tace"Ni!, Nida Wanda Nike Aure ke dauke da Blood cancer ai babuni Babu Haihuwa har abada Sai in ta Allah ta kasance na Auri wani, ko kin manta ne Umma?"

Harga Allah Ramlah bata fadi maganar nan da wata manufa ba Magana tayi tsakanin ta da Allah Amma da yike Umman Al-Masifatu ce Sai ta hayayyakota "Munahika Dama Burinki bai wuce ki ga bayan dana ba kin daura mai Cutar Blood cancer bai isheki ba har Fata kike ya mutu ki Auri wani Ki barni da Asara kenan koh,To ahirr dinki Wallahi sai dukka Ahalin Ku sun mutu kafin dana ya mutu, Munafikan Allah, ni in banda kaddara inani ina hada Dangi da marasa Asali, Wa'enda aba'a San daga wace duniyar Suka zo ba?!, Mugaye dangin mayuh?"


Ramlah Ta danne 6acin Ranta Ta duqa zata dau mata jakarta ta dakatar da ita Tace" Dakata dakata dakata, karki kuskura ki Ta6a min jaka,Me kika Ajiye jikin Jakar?,ko na saki ne?"Umma Tadan tsagaita Tana bubbude kofofin Hanci kaman maishaqar wani Abu kafin daga bisa ni tace "Wai warin me nakeji kaman Abu na Konewa?"

Sai a Yanzu Ramlah ta tunada ta aza Sanwa kan wuta, da Gudu ta koma kitchen din, Umma ta biyo bayanta dan Ganin Kokof๐Ÿ˜‚ ,

Gaba daya Abinda ta Daura ya kone kurmus Sai Kauri ke tashi, Umma ta Riqe baki tace "Me zan Gani ?,Abincin ne ya qone haka?, Lallai Yarinya Kin Samu Sake dayawa ,toh wlh Sai kin Biya Abincin da kika Qona ,ko kuma ki kwashe ki Adana Shi Zaki ci har na tsawan kwanaki Uku, yo ai Wannan ko ni zai mn Kwana Biyar In Gaya miki, Gara Aaryaan din ya dawo Muyi sabon zama Dan Aradu bazata Sa6u ba!" Yanda take zuba kekia ce itace mai nemowa..


Ramlah tace"Haba Umma akan 'Dan Abincin nan kike daga Murya haka?, Ai idan wani ya jiki zaiyi zaton ya wuce haka ne,Alhalin Abincin daga nawane Sai nashi dana Hafsah "


Umma tace "Wai da Aka auro ki Garan me aka kawo Gidan nan?,Inace Cewa akayi a barshi, daganan ya isa ace kin Gane Ba Matsiyaci kika aura ba munada Zuciyar nema kuma Bazamu bari wata bare tazo ta wulaqanta mana Dukiya bah,Duk wannan Uban Abincin da kika dafa kice naku uku ne...Toh Abun yazo qalshe,Daga yau idan ina Gidan nan ni zan dinga Auna Iya Abincin da Zaki Dafa Dan naga Albazarancin ki yayi yawa kinji ni kor"

Ramlah ta Gyada Kai Alamar Gamsuwa Umma ta juya ta fice tana Sababi


Daga Zuwan Umma har ta Fara Shimfida tabarmar Tsiya.๐Ÿ˜†






Aaryaan kuwa yana barin Gidan ya dau waya dan ya duba TYm Yaga miss calls Daga Asibiti ya tabbata ana nemabshi ne Shiyasa ya Garzaya Shika direct, Dama akwai Aikin da ya baro a chan.


Sai 6:30pm kafin ya Samu kansa, A lokacin Hafsah ta kirashi tace Jaanaan ta kirata tace a Gidanta Munayferh zata kwana..



Baice komai ba Amma yana mamakin Hali irin na Munayferh wato idan An kwa6o ta tanan zata koma tachan๐Ÿคง๐Ÿคง



______________


Abinda yasa na Za6i kwana Gidan jaanaan Saboda nasanta,Bata damu da Sanin damuwan mutum ba idan ba Mutum yayi niyyar fada mata da kanta\ kanshi ba!, bakamar Hafsah ba Da idan tagan ni Cikin damuwa sai Tabi diddigi tasan Dalilin damuwan In ba haka ba itama ta Shiga damuwan kenan Shiyasa na fi Son kwana Gidan jaanaan idan ina cikin Damuwa, Cus ni mutun ce mai zurfin Ciki ba kowa ke sanin Ciki na ba duk yanda muke tareda Kai kuwa, Sai in nayi niyyar Gaya kawai.




Cikin Damuwa janaan tace"Nayfee please Stand up mana!"



Cikin Qufula Nace'' Dan Allah ki qyaleni Wai dole ne?"

Tace"For the last time, idan baki tashi ba Saina kira YaaAary na gaya mishi ya aiko a zo dauke Ki kawai,"


Ban tanka ta ba , kawai saiji nayi tana waya da mutum๐Ÿฅบ, ai ban San lokacin da na doro kan Gadon ba na zuba mata ido ina jiran jin ta bakinta, banji me ya gaya mata ba.
Na daiji tace"Bataci komai ba Amma kaman zazza6i ke Shirin kwantarda ita,Tunda kana kusa kawai ka taho mata da magani" sannan ta datse wayan.


Na bita da Harara ta ta6e baki sannan ta miqe ta yi Alwala ta Gabatar da sallahn isha'i.


Ina zaune Har ta idar da sallan.a lokacin wayanta ya hau ruri tasa hannu ta dauka banji me ya gaya mata ba ta dai miqa mn wayan, hannu na rawa na Kar6a Na kara a kunne...



Muryan shi naji Cikin Yar dariya yace"ina jiranki ki fito ko na shigo in dauko ki da kaina"

Babu Shiri na cire wayan A kunne na ina Zare ido.


Jaanaan dake kallona ta danne dariyanta Tace".....Gara ma ki tashi Dan bazan Bari ya shigo mn cikin Gida ba"


Na harareta ina turo baki kaman zanyi kuka na dau wayata Sannan hijab na fito

na iskeshi jingine da mota Yana waya Saida ya gama wayan kafin ya Kalleni yace na Shiga mota, Bai kaiga bashi amsa ba wayan dake hannuna ta dau ruri Jeeboi ne .


Da sauri da dauka ina murmushi Mai Kara qawata Fuskata,Sannan nasaka Wayan a handsFree, Shi dai ido ya zuba mn Ganin Irin murmushin da nayi kafin na daga waya.


Daga chan 6angaren Jeeboi yace"Haba Babe, me ya kawo gaba babu fada?, Tun dazu nake ta faman kiranki Amma Bakiyi picking ba Why naa"


Nayi Dan murmushi Nace"Sorry Sweat Heart bana kusa ne"

Yace"Okay Dama Tun dazun da na mutumin nan ya ritsa mu hankali na ya kasa kwanciya, please me ke tsakanin Ku dashi?, naga Akwai sanayya A tsakanin Ku ne"

Nace" laah babu wata sanayya A tsakanin mu fa, Yayan wata Qawata ne Yanada mental Disorder shiyasa Yayi maka haka dazun ,but Am sorry on his behalf "

Jeeboi yace"Babe mutumin fa baiyi kamada Mahaukatan nan ba, Naga kaman Shima sonki yakeyi kuma Kishinki yasa shi yin hakan ko dai Kuna soyayya ne ban Sani ba!,Tell me pls, you know..."

Na katseshi da cewa"Haba Swthrt Am not cheating on you,even if I were to cheat it can be with yaaAary that mad mad With mental disord......."


Ban Karasa ba naji saukan mari saman Fuskata Wanda yayi sanadiyyan daukewan ganina na Wasu Yan seconds.













*Hakika babu babban jin Dadi sama da Allah ya hadaka da masoya,inama ace wannan soyayyar da kuke nunamin ta kasance har Abada ina kaunarku masoya na danaWannan littafin Allah ya bar Qaunar nan har Abada*



wattpad @Fahnaan



Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

6th September







๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 25_*


*Sarah (kdGirl) dake da maryam Sule wannan page din naku neh๐Ÿ’–*



Ya karadauke ni da Wasu Tagwayen maruka duk a lokaci Guda.

Kara na Saki Wayan dake hannuna ya su6uce ya fadi.


Janaan dake Daki ta jiwo karar da na saki da gudu tayo hanyan waje Dan Ganin kor lafiya?, Amma Maganar da taji yanayi yasa ta tsaya Chak.


Hannu aza kan lips dinshi Alaman nayi mshi shuru,Zumburo baki nayi hawaye nabin Fuskata.

Yace "Da Auren nawa a kanki kike kiran wani Qato Chan A gabana ?, are you Insane? Kina Hauka n....."

Dakatar dashi dayi cikin kuka nake fadin"Ni ka daina kirana matarka, Gara tun Wuri ka Rubuta mn takarda ta ,Hankali kwance in nemi wani miji nayi aurena,Kuma idan kaqi sakina Saina fadawa Abie Halin da ake ciki"


Aaryaan da Zuciyarsa tayi masa zafi waishi nake Gayawa zan nemi Miji inyi Aure bayan Taimako na Yayi Ya Aureni,Yaso ya mammakeni Gabaki daya Jikinshi Allah tsine ma inda baya Rawa,Idanun nan Sunyi jaa zir ,Sai haki yakeyi kaman Zakin kullen da ya samu Sake.


Ganin yanda yanayinsa ya Sauya yasa Ya hankali na ya tashi, Amma ko kadan ban Nuna a fuska ba,Na duqa zan dau wayata dake yashe a qasa naji an Fincikoni Ya Hadani da Jikin Mota,Tuni na tsure jikina ya dau Rawa Gumi ya fara Tsassafo mn sbd tsoro.

A hankali anma Cikin Murya mai Nuna tsantsan bacin Rai yace" I Hate You Munayferh, And I will never Divorce you,Aurena dake na Har Abada ne,So idan Zaki fadawa Abba kishirya Gaya mishi Dalilin Auren namu sbd Kwadayi ne....,Kuma daga yau ban yarda ki fito koda Kofar Gida ba tareda Kin nemi Izini na ba, Anya kinsan matsayin da darajar Aure a musulunci kuwa?...."


Babu Zata babu tsammani yaji nace "Ban Sani ba ka Sanar Dani!"

Yace"OK zan Nuna miki"


Murmushin mugunta yayi ,Ya kamo hannuna Ya Shigar Dani cikin mota ina Tirjewa Yaja motar muma bar Campus din.


Janaan da ta Gama jin Abin da muka Gama tattaunawa taja Gauron Numfashi Ta Shige ciki Cikeda

Please Login or Register in order to submit comment