Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa yayi Cikin wasa tace

"Kaine ya kamata ka tashi ka bar mn nawa 6arayin "

Ta fada tana Miqewa , a Daidai Lokacin aka Kira sallar isha.

Da kallo ya bita ,Yana Mamakin Wai yaushe ya fara sakar mana fuska ne muka Rainashi haka?, Gaskiya ya kamata yayiwa Tufkar hanci, bazai yiwu ya Zuba mana ido muna kallonsa Muna ya6a masa maganGanu yana kallon mu ba dole ya dau.mataki....

Sannan ya tashi ya tafi masallaci
Koda ya dawo bai yi Yunqurin Tunkarar ko daya daga Cikin Matarsa ba, yayi Nasa dakin Rai a jagule .

*****

Umma kuwa Yau Ajiya Aseeya ta Aiko jameelu ya kawo mata DA Alluran !, Dan haka take Shirin Zuwa Barnawa Gobe Goben nan! ,Ta tarkata kayayyakinta da Abubuwan Buqatanta haka kuma Wannan karon Shiri takeyi Sosai na yanda zata Wulaqanta Munayferh (Rasa kunya )a cewarta da kuma Ramlah (Mare Asali)

*****

Yau na waye Garine Cikin tsananin Murna, zanje naga Ammie na ,Tun bayan Asubah ina Gama Sallah ban tsaya jiran Janan ba na shiga Kitchen na hada shayi da Qwai dama Mafi Akasri shine Abinci na Na safiya ,

Qarfe 7:30 na fito Cikin Shiri na Cikin Shiga ta Alfarma ,Cikin Wata wata hadaddiyar Code lase Golden Takami da Porse ma Golden Sannan na yafa Milk dn Gyale, Fuskar nan dauke Da Heavy makeup Wanda na zauna na Chanchada Wa Kaina Nayi kyau Sosai Sai maqiyi.

A dinning na iskesu Suna karyawa ,Qarasawa nayi Cikin sakin Fuska nace "Aunty ina kwana!"

Ta Amsa minda "lafiya....How is ur night!, ina Zuwa haka da sanyin Sassafen nan?"

Shikuwa Kallona yake A kaikaice ,Sosai kwalliyan da nayi ya tafi da imaninsa Shiyasa ya kasa dauke Idanunsa Akaina.

Cikin yatsine Fuska tareda Ta6e baki nace "Kai kuma kallonfa?, Zuwa nayi Kabani Keyn motar na tafi Gidanmu"

"Gidan ubanwa zakije da sassafen nan, Da wannan Uban makeup din?"

"Gidan Ubank...." Na kasa qarasa Wa Sakamakon Wani Uban kallon banzan da ya Watso mn hadida Harara,  Cikin dan Gigicewa chanza maganar da cewa

"Uhm......Gidan....Ubana"

"Toh bazaki ba" ya fada yana kai lomar Abinci bakinsa.

"Haba Doctor!, Why naa.... Bai dace kace hakan ba"

Ko Amsata Baiyi ba ya cigaba da Cin Abincin da yakeyi.

Ni kuwa Tuni hawaye Sun Gama Wanke mn fuska har ina shidewa Saboda tsananin kuka,Cikin kuka nake Roqonsa da yayi Haquri ya barni naje naga dangi ,Amma kaman Baisan inayi ba.

"Aunty DanAllah ki sa Baki ki bashi Haquri Nasan Zai Haqura kinji!" Na fada Cikin Kwantar da murya Idanu na Fidda Kwallah.

Murmushi tayi ta kamo hannunsa
"Please Hun!, Ka barta Taje kaji Please ba dan Halinmu ba" Ta qarasa Magana Cikin Sigar Rarrashi.

Dagowa yayi ya kai Dubansa Gareni wacce har Hawayen sun Gama Wanke Fuskar nan, Sosai na Basa mamaki Ayau dan Ban Cika Yawan kuka ba idan an hanani Abinda nake muradi Saidai na qara da Rashin Kunya,Hakan yasa ya Fahimci Akwai Abinda Yasa nake son Zuwa Gidan.

"OK zauna kici Abinci"

Ya fada yana Nuna mn Kujerar Kusa dashi.

Kin zama nayi nace.

"Na qoshi"

Daure Fuska yayi Tamkar baisan Meye dariya ba ,Yace "Me kukaci?...Common zauna kici Abinci my friend"

Kicinkicin nayi da Fuska Cikin turo baki nace "Nacema Na qoshi,Dole ne?"

"Idan Bakici ba,Babu inda Zaki!" Ya fada yana Maida hankalin sa ga Abincin da yake Ci.

"To sai me?, da dai na ci Abincin nan Gara kar naje"

Na fada ina Share hawayena Tareda Juyawa zanyi Ciki

Itakuwa Ramlah Zuba mana idanu tayi tana kallo kaman ta Sami Television, Draman mu da YaaAary yana 'dan Burgeta ,dukda kallo daya zakayi ma kowannen mu ka Fahimci Tsantsar soyayyar dake Cikin Idanun kowanne a Cikin mu hakan baisa Mun Nuna ba illa Tsanar da Muke nunawa A fili.

Ganinfa da Gaske Komawan zanyi batareda naci Komai ba, yasa ina Juyawa ya jawoni na fada jikinsa ,Hakan yasa Ramlah dawowa daga duniyar Tunanin da ta shiga.

Wata 'Yar siririyar qara na Saki, Tuni jikina ya soma Rawa na fara Kiciniyar Kwacewa.

Da qyar ya samu ya zaunar dani bisa Cinyarsa ,A Lokacin har nay laushi.

Da sauri Ramlah ta kawar dakai daga duban mu ta maida hankalinta Ga Abinci da takeci

Shi kuwa daGangar Yayi hakan ,Dan so yake ya Rama Rashin M dinda mukayi masa jiya.

Debo Abincin yayi ya kai bakina Yana Fadin "Oya Bude Bakin"

Qara Tamke bakin Nayi, ina Fidda Numfashi tareda Wulla Qafa Cikin qoqarin Da son Qwace kaina, Amma Ba qaramin Riqo yayi mn ba.

"Gara Ma ki bude bakin in ba haka ba ,Zanyi following next Step Wanda zai Tilastaki Ci"

Ban tankashiba na Sake Yunqurin kwace Riqon da yayi mn nake.

"Haba Hun tunda tace bataci ka Barta ,Taje inda ta Saba...."

Harara ya watsa mata ,Wanda ya sanyata Jan bakinta tayi tsitttt.

Hannunsa daya yasa ya Riqeni GAM, Sannan ya Sanya dayan hannun ya debo Abinci yakai bakinsa Ya tauna, Saida ya tababbata Ya Gama Grinding dn Abincin Cikin bakinsa.

A lokacin kuma na Bude baki Cikin tsananin Wahaltuwa na fara magana

"Dan Allah Yayan Hafsah ,Ka Cikani Zanci ,Zanci..Wlh zanci dakaina..."

Ban ida Rufe Bakiba naji saukar nasa Cikin nawa ,Saida ya Tabbata Narkakken Abincin bakin nasa ya Gama Shigewa bakina, kuma na hadiye Sannan ya  Cire Bakinsa Yana Cire bakinsa na Qwala wata Uwar Qara Da iya karfina ,Ganin Yanda na Kwala Karan ne Cikin Firgici yasa yayi Azamar Rufe bakin da nasa.


Tsoro Mamaki, da Al'ajibi Sukayiwa Ramlah Dirar Mikiya Ganin Mijinta na kissing Wata A Gabanta Bata ta6a zaton zai iya Aikata Hakan ba!, Miqewa tayi jikina Rawa   har tana hardewa

Nima Kusan Hakan ta kasance Gareni don Ni Sam Banyi Tsammanin azaiyi mn hakan ba,Ai da Tuni na hadiye ihuna ,Tuni Jikina Ya dau Rawa kaman mazari Hawayena Suka Ninku Akan nada.

Saida Yayi Mai isarsa Sannan ya yaleni yana Maida Numfashi

Ina Ganin ya CikaniNayi Yunqurin Miqewa Amma Sai Kuma Jawoni jikinsa Cikin kunni na ya mn Rada

"Babu inda Zaki fa in baki Ci Abincin nan ba"

Kuka Na saki Wanda Dama Shi nakeyi

"Wayyo yaya Wlh na qoshi, Naci Abinci!, Don Allah kayi Haquri !" Na qarashe da Rushewa da Wani irin Kuka mai Sauti

Sosai yake jin Kukan da nakeyi har Cikin Ransa Amma Duk da Haka ya Sake Tamke Fuska

"Yo Ai hikenan Tunda Kin fi son Na baki da bakina"

Da sauri na Girgiza kai Tareda Daukar Chokali zan debo Abincin Ya kar6a Da kansa yayi ta dirka mn ,Harsaida Yaga Na Fara Yunkurin Maidowa Sannan ya Qyaleni , Tareda Saukeni Daga saman Kafar Nasa, Ya azani bisa Kujerar Kusa dashi.
"Kukan fa?" Ya tambaya Yana Yatsine Fuska yayinda yake Tarkata kayan da muka Gama Amfani Dashi.

Hararar sa kawai nayi, Sai a yanzu na lura da Babu Ramlah a Gurin .

Maganarsace Ta katse m. Tunani

"Jeki Sauya Shiga, Sannan ki Goge makeup din Nan ,Ki saka Flat shoe Da Hijab, Bangles Dinnan Ma bana son Ganinsu A hannun ki!, Haba Sulthy Kiji Tsoron Allah mana ,Yanzu da Aurenki Kike wannan Shigan Dan sbd kawai Zakije Gida?, Bayan dakinki kinsan Akwai Maza dayawa A gidan namu"
Ya qarasa tareda miqewa ya nufi hanyar kitchen

Tsaki naja Hadida Harararsa "Kaaaji Dashi, Wannan kuma Matsalar kace Mugu Azzalumi 'Dan Iska kawai......."

Na fada tareda haurawa Sama da Gudu.

Shikuwa Tunda nayi Tsaki ya Tsaya Chak yana kallona Har na ida zuba na Gudu!, Bai iya cewa komai ba!, A Duniya ya tsane Tsaki ya kuma Tsane mai yinsa ,Lallai yarinyar nan ta Rainashi dayawa Ya kamata ya fara daukan mataki!, ya kamata ya koma mata Aaryaan din da Mara daukan Wargi ,Mara Murmushi bare Uwarta dariya!, ya zama Dole ya Nuna mata Kuskurenta.

Ina shiga nayi wanka Na shirya kaman yanda yace Cikin Dogon Rigar Atamfa Sky blue da Dark blue tana da Ratsin Black and.milk  Atamfar ta Qar6eni Sosai kuma tayi matuqar  dacewa da Launin Fata ta, wurin Wanka na dirge Makeup dinda nayi ina Kuka tareda kwararo masa Allah ya isa ,Koda na kimtsa Ban kuma Wani kwalliyan ba, kuma Ban Sanya Bangles ba,Takalmi ma Flat nasa Kuma ban sanya Gyale ba, Hijab na saka.

Da zan fito ne na Tuna banyi sharar Dakina na Don haka na Cire Hijab na Ajiye Gefe ,Nayi Shara wanda Tun kafin na Gama Har na Galabaita ,Saida na  koma gefe  na shiga Fidda Numfashi Daqyar Na Samu Na Dawo Normal.

~(Ni kuwa Inba Qaddarar Aureba, Mai zai Sani Shara Dakaina !, Kuma ba don Bana Son qazanta ba !, da Na barshi Hakan)~

Wayana dake Saman Mirror ta dauki Ruri ,Hannu nasa Cikin sauke Numfashi na daga Batareda na Duba sunan Mai kiran Ba Murya Chan Qasan Maqoshi nake Fadin.

"Ya Akayi ne"

Muryan sa naji Cikin masifa yana Fadin

"In kinga dama ki Fito ke nake jira ,Idan kuma Bakiga dama ba Ki gaya mn I have A lot To do!"

Cikin Inina nace "Ga...ni...na..nnn...Zuwa"

Kit ya datse wayan, Harara nabi wayan dashi sannan Na Dauko Hijab dina na sagala Na zura takalma na Fito Na iske shi A Parlorn qasa ,Ramlah na Tayashi sanya Agogon Hannunsa!, Fuskar ko wannen su kunshe da Murmushi.

(A raina nace Har An dinke kenan!, Koda yake mata da Miji sai Allah)

Qarasowa Nayi Fuska Tamke kamar wacce Aka Aikowa saqon Mutuwa ina duban Agogon hannuna,Cikin Yatsine Fuska Nace"Lokaci Na Qurewa, Nifa zan tafi, Dama Chan bada kai na tsara Zuwa ba!"

Juyowa yayi Ya wani hade Fuskar nan kaman bashi yake Murmushi yanzu ba!,

Hakan yasa Naja bakina nayi Gum ,Dan Banshirya kabar Hukuncin sa a karona Biyu ba.

Saida Ta gama sanya mashi ta kalleni Fuskar nan ta ta dauke da Murmushi

"To sai An dawo Qanwata ,A Gaida Su Umma da Ammie da My Naughty Twince! , Karfa ki Gaida mn Abdool...."


Nayi Saurin Tare Numfashin ta da cewa "Inace Kinada Kafa ko ,Idan kinje Ki Gaida Su Dakanki Ni ba 'Yar Aikenki bane"

Na fada Ina Ficewa dan Ganin yanda Fuskar Aaryaan take Tamke kaman Dussa Yanzu ya kamani kashina ya Bushe.


Gabaki daya Suka Bini da kallo har ba 6acewa Ganinsu..
Aaryaan ya Juyo Da kallonsa Ga Ramlah Wacce Tayi mutuwar Tsaye ya kamo hannayenta,Cikin Sanyi ya fara Magana

"Ramlaty Nasan Kina da Haquri , Ki qara akan Nada Please karki bari Al'amarin Yarinyar nan ya dameki ,Mu bita a Sannu Yarinta Ke damun ta, inshaallah Tana kaiwa 20yrs zata Rabu dashi Mu tayata da Addu'a kawai, Kumaa Please ki qara Haquri akan Ummah Don iyayen Yanzu sai An riqa Haquri dasu Ana lalla6asu In muna so Mu gama da duniya Lafiya, Umma ta Kirani jiya Ta Gaya mn zata dawo Gidan nan yau! ,Har sai Abbie Ya dawo"


Da sauri Ramlah ta dago ta kalleshi Don Tabbatar da Abinda Yake Fadi, Sai kuma tayi shuru Hadida qagan Murmushin qarfin hali.

Ya cigaba da cewa
"Nasanki Da haquri da juriya ,Please kaman yanda na saba gaya mki Umma haka take Koni bata bari Abu kadan zanyi ta zageni Tasa ta Kuma Daurawa da Gorin Ni ko kunya banaji Bada Kudin Mahafina nayi karatu ba , Kinga haquri ya zama mana dole In baso muke Mu shiga Fushin UbanGiji ba "

"Ayya Dr ,Din Allah ka daina Wannan Maganar mana,Nifa a matsayin Uwa take A wajena,Wlh koda Sau daya ban ta6a kullatarta Da wani Abu ba Kaima Shaida ne ,Mezaisa na kullace ta ma Ai ta isada nine Shiyasa ,Kuma idan ban Kyautatawa Mahaifiyarka ba Wa Zan kyautata Mawa!, Dama zaman Aure ya Gaji hakan ,Yana zuwan maka da siffofi kalakala, Saida haqurin Ake Cin moriyarsa ....Kaga Qanwata na Jiran ka a Waje Kaje kar Ku makara Naga tama Fika Qosawa"


Murmushi yayi Jiki a sanyaye ya Jawota Jikinsa ya Rungume, tareda Manna Mata kiss a Goshi "Thanks Ramlateey " ya fada A sanyaye Don Ya ma rasa Me zai gaya mata Taji dadi yanda ya ji dadin Zantukan Nata

Kawai sai ya daura da "Me zan Siyo mku ne keda Babyna?"

Zare Jikinta Tayi daga Nasa Cikin juriya tace

"Icecream"
"Kadai?"
"Eh !, Allah ya kiyaye Ku ya dawo mn daku lfy"

Da Amin ya Amsa tayi masa Rakiya Har inda nake jirarsa A Wajen Mota.

Muna Shirin Shiga Saiga Junayd ya shigo Gidan Hannunsa Riqeda Leda ,ya qaraso Har inda muke ya gaida Aaryaan, Ya Amsa mshi CikiCiki yana hararar Sa


"To yaya hararar Fah, Kaidai ka Shiga Uku Wlh Abu kadan Sai ka wani hade Fuska Da Hararar mutum....Ke kuma daughter Duk Kunburin nan Na Meye ne !, Allah yasa ba Zane Mn Ke yayi ba,Aikam idan Zaneki yayi sai na Rama miki"

Ya dubi Ramlah Dake Gefe tana 'Yar Murmushi
"Ke Kuma mai kama da Auta ,Ya dai kallon Fah Baki iya Gaisuwa bane?, Koda Yake Ance Masu Ciki in Suna Laulayi basu Gaisuwa Don Kar 'Dan Ya Zama 'Dan Gaisuwa da yaga Mutum A hanya Ya Gaisar ,Ba tareda ya San shi ba!" ya fada Cikin tsokana yana 'Yar dariya.

Aaryaan ya ja Kunnen Sa ya Dan Murda yana Fadin

"Junayd ,Wai yaushe zaka Girma ne ,Kaifa yanzu Ba yaro bane"


Matse ido y shiga yi yana cewa "Kai yaya Nifa Tuni na Girma Tunda Gashi inada Mata"

Ni kuwa tunda Yake magana Idanuna suke kafe a kan ledar da ya shigo dashi

"Laah Daddy ,Meye A hannunka"

"Kwadayayyah IceCream Ce Zaki sha ne?" Ya fada cikin sigar Tsokana Don yasan Tunda Nasha Icecream Dinnan 🙄, Na daina Shan ice cream bana ma zama kusa da maisha Don kar naji shaawar Nasha din.


Ta6e baki nayi Nace "Gaka babban Kwadayayye Maye mai shan Icecream da sanyin Safiya "


Dariya yayi ya dubemu duka yace "yaya ina Zaku haka?"

"Gidan Uban Mu" na bashi Amsa.

"Harda Ke mai Ciki?", ya fada yana Nuna Ramlah Tareda dariyansa na tsokana.

" Eh mana ,Tunda Gani irinka ba!"

"Da kinji dadi Wlh... yaayaa ladhky (daughter) Safe Trip muma sai Munzo" ya fada yana mana Waving da hannayensa


Aaryaan ya shiga Mota ya tayar ,Nima na Bude Front Seat ina Msu Waving, yaja muka bar Harabar Gidan.


Motar ya dau Shuru bakaji Sautin Komai sai na Qira'ar ABDULLAHI ABBA dake tashi Cikin motar.


Nikuwa Gajiya nayi da sauraro na fiddo wayata nayi Connecting da Airpod dina Na saka waqan SONU KE TITU KI SWEETY NA ZACK KNIGHT DA JASMINE WALIYA.

Na kwantar dakaina bisa Seat dn motar Tareda lumshe idanu Cikin jin dadin waqar ,Ban jima ba Barci yayi Awon Gaba dani.


Shikuwa Ganin shurun yayi yawa yasa ya fara Mn magana Cikin Rarrashi.

"Sulthy Ya kamata kisani yanzu Ke ba Yarinya bace ,ya kamata Ki shiga Taitayinki kisan Abundake damunki Kisani kefa yanzu Kinshiga Layin matan Aure... Kina jina ko!"


Shurun da yaga nayi ne yasa ya juya ya dubeni, Ganin na bingire sai shar6ar barci nakeyi yasa ya Ta6e baki yana Addu'an Allah ya Sa yaga Ranarda Munayferh zata shiryu ta daina Miyagun Halayyanta, Ranar kuwa da yafi kowa Farin Cikin Ganin wannan Ranar.


Haka Muka kasan ce Har muka Isa Kabala Costen ,Kai tsaye part din Umma muka nufa na Gaisheta Ga mamakina Naga ta Amsa mn Cikin sakin Fuska, Abinda ban ta6a Gani ba.

Daga bisani na Wuce part din inna Rabi,ita ma Muka gaidata Itama Cikin sakin Fuska ta Amsa!, Mamaki ya Cikani Anya kuwa babu wata a qasa?, Oho Koma Meye ne ya qare akansu ni munayferh nafi qarfinsu.


A part din Ammie na Na Uni Muna Hira Shi kuwa bayan Gaisuwa ya fice ,Ina Gidan Har su Ameerah, Ameer Da Abdool Suka dawo Nan Muka Dasa Hirar daga inda Muka tsaya Cikin So da qaunar Junan mu.


Da la'asar na Tasa Ameer da Ameerah Suka Rakani Gidan Su humaydah, Daga nan na nufi Gidan su Janaan

Saida yamma Lis kafin ya dawo ,Ya daukeni,Saida muka Shiga 6angaren Umma kafin mu tafi Nan ma na kuma jin mamakin yanda ta sake tana A gaida mutan Gida

A hanyar mu na komawa ya tsaya ya Siyawa Ramlah Icecream Nima ya Siya mn ,Amma Sai Nace Ya hada Mata Ni Bana Sha, Ya dauka Iskancin da na sabayi ne na cewa bazanci Abinda ya Fito daga hannjnshi da Ramlah bane

Shiyasa ya Rufeni da fada yana Mita daga bisani ya Rufe fadar da cewa kar ya Sake Ganin na ci Abinci A wani Wuri inba Wanda Aka dafa a Gida ba!


Ni kuwa tunda ya fara Fada na maida hankalina Ga Hanya ina Duban Waje!, Har ya gama mitansa ban tanka masa ba, Kuma ban Ce masa qala ba, ..........




Washegari Bayan Nayi Wanka na koma Barci Don Sosai nake jin Barci, Barcin jiya bai isheni ba,sosai Na kwaso Gajiya.


Sai Goma da Rabi na Farka na Fito Parlorn Qasa ina hamma.


Turus na tsaya Ganin Umma zaune ta wani Hakimce kan Kujera Ga kuma Qawarta Hajiya Asiya dake zaune kusa da ita,Ban Gama tunani ba naga Maigadi yana Shigowa da Akwatunan Umma.


Saiga Ramlah ma ta Fito daga Kitchen hannunta Riqe da Mug mai Kunshe da Coffee


Da kallo na bita har ta Isa Ga Umma ta miqa Mata Mug din harda 'Dan sunkuyawa.

Ta juya ta kalle Maigadin dake Riqe da Tilin Jakar Umma tace

"Bari na qarasa dashi Ciki ko"

" Ke dallah chan qyaleshi bani son munafurci Fa"
Umma ta fada tana kai Kofin Cofeen Cikin bakinta, Da sauri ta Cire Kofin daga bakin ta tana yatsine Fuska ta daga Zata Watsa Wa Ramlah da ta sunkuyar da kanta,Ni kuwa Ganin yana Shirin Zuba mata Coffee mai zafi yasa nayi Supa na Tureta Ta fadi qasa Coffee din Ya zubar mn....


Zafinshi ya Ratsani ,na saki wani irin Qara da iya qarfina Don Sosai Naji Zafin Har kwanyar kaina.


Gaba daya Su Umma basu San na Fito ba,Shiyasa basu ankare dani ba, Gaba dayansu Miqewa Sukayi a kudime ,Daga ita Har Qawar tatan.


"Ke kuwa banda Iskanci Meye na Shigowa Tsakani" inji Hajiya Asiya Cikin daga murya.


Miqewa nayi Cikin qarfin hali ina Cije lips,Don ban yarda na zubda hawaya Saboda Abinda ya faru ba Dukda Zafin da nakeji yana Ratsa Ko'ina na jikina, na Gummace na Hadiye Zafin na koya msu wayau, Dukda kuwa kallo daya Zaka mn ka fahimci tsananin azaba da radadin da nakeji yana Ratsa ko ina na jikina.


Na tsaya Gaban Umma Da tayi zuruzuru Tana Tsoron jin Abinda zai Fita daga Bakina,Don bata qaunar na Gayawa Abba Abinda tayi mn


Na fara magana Cikin dakewa ".....













ME MUNAYFERH ZATA CE?








INA MATUQAR GODIYA GA MASOYAN WANNAN LITTAFIN BANIDA ABINDA ZAN SAKA MAKU DASHI SAI ADDUA KAMAN YANDA KUKE MN AKODA YAUSHE...INA YINKU SOSAI IRIN TOTALLY DINNAN








AMMA FA 'YAN LA6E SUNFI YAWA A CIKIN KU, INA GANIN TEXTS DINKU DA QORAFE KORAFE AKAN RAGE YAWAN POST DINDA NAKEYI WATO BANA posting AKAI AKAI.





TOH GASKIYA DAI BA KOMAI YASA NA DAINA POST DN Akai AKAI BA SAI DON YANDA NAGA KUMA KUN RAGE COMMENTS AKAI AKAI.





SO INSHAALLAHU IDAN NAGA YAWAN COMMENTS DINKU AKAN WANNAN SHAFIN ZANYI DAWO TWO OR THREE PAGES A RANA DAYA SO THAT ZAMU GAMA NAN DA SATI BIYU (KAFIN MU KOMA SCH KENAN)


IDAN KUMA KUKA QI....TO ARADU BARIN TYPING DUN NAKAYI HAR SAI MUN KOMA SCH MUN GAMA EXAMS.....







SAI NAJI DAGA GAREKU






NAYI GABAS🚶🏼‍♀️[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀
**HAWAN-JINI NA*
~{uwar mijina* 💔}~
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
😍

بسم الله الرحمن الرحيم...

*_Chapter 53_*


Aaryaan ya riqeta gam tare da hadata da jikinsa ya rungume ta tsam ya shiga yi mata addu'o'i Tareda Karatun Al'qur'ani a kunne .



Ina jinsa Nayi luf tare da qara gyara kwanciya na a kirjinsa dukanMu sai muka tsinci kanmu cikin yanayi me wuyar fassarawa Nikam sai sauke ajiyar zuciya nakeyi tare da qara shakar daddadan kamshi turaren dake jikinshi har take Naji wani bacci na shirin kwasheni .


Ita kuwa Umma Ganin Aaryaan ya wani rufe ido bakinsa saitin kunnena gashi kuma Ina ta wani lafewa a jikinshi ,bata san lokacin datayi kanmu ba tana zuwa tajanye ni daga jikinsa, inajin an jani ta saki wani Irin qara a tsorace nayi saurin qara langabewa tareda Qara qanqameshi Saboda Tsoron da ya shigeni ,Don Na dauka 'yan ta'addan nan ne!


shi kuwa bude idonsa yayi a hankali ai kuwa ya saukesu cikin na Umma data kafeshi da ido ckin tuhuma tana huci waigawa yayi ya kalli inda Ramlah ta sheme kafin ya maida dubansa ga 'yan daban nan ,Nan take Tunaninsa ya dawo Jikinshi

Da sauri ya daukeni Chak ya azani Bisa Three Sitter Sai Wani qanqameshi nakeyi Alamar Tsoro ko firgici ,Tun da Yake bai ta6a Ganin Tsorona irin Haka ba shiyasa ma ya kasa Rabani da Jikinsa Wani Tsawan da Umma ta daka masa ne yasa na Wani zabura A razane ina Fadin "Wayyo"



Da qyar yq samu ya kwantar dani ya nufo inda Ramlah take Zube a qasa ShameShame


Bude qofar da Akayi ne yasa yayi azamar Daukan bindigan da ya Gani a qasa tareda Nuna hanyar dashi


Junayd ne ya shigo ,Ganin Yayan nashi ya Nunashi da bindiga ne yasa yayi Raising hannayensa Alamar Surrender,


Cikin Sanyi Aaryaan ya Ajiye bindigar ,Ya maida dubansa Ga Ramlah tareda Dagota yace "Cha²dauko mn Ruwa a Fridge"


Da sauri junayd ya dauko masa Ruwan ya yayyafawa Ramlah, Aikam a zabure ta Wani ja dogon Numfashi Tareda Sauke ajiyan Zuciya,


Gaba dayan su sai sannu Suke mata yayinda ita kuwa take bin kowa da idanu Tana son Tuno Abinda ya faru.



Junayd ya dubi yayan nasa yace "yaa Meya faru ne?, jaanu ce ta kirani Wai Taji qaran Harbi Anan Ga kuma mutanen da nake gani Cikin Jini meya faru ne?"


Umma ta katseshi da Fadin

"Wlh wasu 'yan daba ne Suka far mana Suna son Tafiya da Munayferh bamu San Waya Aikosu ba mah"

Gaba daya Suka Kai duban su Ga Umma Aaryaan yace "Munayferh kuma?, Me tayi msu?"


Junayd yace "Yaya Wannan lokacin bana tamabaya bane ,don bamu da mai Amsa mana Ya kamata musan yanda zamuyi da Mutanen nan Ne Kayi masu Treatment Sannan mu nemi Wani Ke6ataccen Guri mu 6oyesu Idan sun Farka Sai mu Tambayesu Waya aikosu Don Ina Zargin Mutanen da Suka Sace Uncle sune Suka Kuma dawowa Don Daukan Gudan jininsa "


Aaryaan ya juya kai tareda miqewa

"Yeah Zai iya kasancewa ,Don An Sha kai mata Farmaki Nike Kareta Amma bata Sani ba"


Ya dubi Ramlah da Umma da sukayi Zuru zuru Suna kallonsu ,Cikin Rashin fahimta Umma Ke Kallonsu yayinda Ramlah ta fahimci inda zancen nasu ya nufa, badon kar ta Tona ba Ayi asarar Rayuka da ta Gayi Sunan Wanda ya Aikosu da inda Suka 6oye Abban Munayferh.



Aaryaan yace Umma da Ramlah su Shige Ciki yayinda Su kuma Suka kwashi Mutanen nan Suka Kaisu Mota Saida Junayd ya Fita ya tabbatar babu masu kallonsu Sannan ya dawo ya bashi tabbacin Hanyan yana safe



Babu 6ata lokaci Cikin Daren suka Kai Mutanen Gidan Junayd Wanda Ke nan Unguwan Rimi ,Allah ya basu sa'a basu hadu da Night Securities ba shiyasa Har Suka kai babu Wanda ya Gansu.


Nan Aaryaan ya fara basu taimakon Gaggawa A matsayinsa na Likita,Tareda dirka musu Alluran barci yayinda Hilaal Yake Saita Security Din kofofin Gidan zuwa Thumb sai da Gwajin yatsa Kofar zata iya buduwa


Suna Gamawa Suka Fito Junayd ya ja mota suka bar Unguwan

Junayd ya dubi Aaryaan da idanunsa Ke Lumshe Cikeda Gajiya yace


"Yaa dama kai Police ne?"


Tambayan yazoma Aaryaan a bazata hakan yasa yayi Saurin Ware idanunsa ,Sai a yanzu ya tuna da kayan dake Jikinsa A hankali ya maida Kansa ya jingina Da seat din motar Cikin murya mai kaman na mai Rada yace

"Yeah ,But secret police"


Yanayin yanda ya basa Amsan ne yasa ya fAhimci yau fa yayan nasa. Baya Jin magana ne hakan yasa shima yaja Bakinsa yayi Yi shuru Har Suka Isa Gida.



Nikuwa yana kwantar dani na Shiga Barci a wahalce hakan yasa bansan Lokacin da suka Fita ba


A firgice na Farka ina Fadin "Wayyo yaya Jini Jini Sun kasheta Wayyo na kashesu Jini jini Jini"


Da sauri Aaryaan ya Qaraso sakamakon Jin Kukan da yayi Tun Shigowanshi ,A firgice na tashi tareda qanqameshi Cikin kuka sosai Tareda nuna mshi Jinin da nake Gani a qasa Still Bakina bai daina Furta "Wayyo na kashesu Yaayaa jini jini Wayyo jini"

,Umma da Ramlah ma suka Fito a Razane Yayinda , Janaan ma jin shuru yasa Ta Bi bayan nata Mijin Don Jin ko lfy!, Sai Sukayi Karo dashi yana Shirin Shigowa

A tare suka Shigo Suna tambayan lafiya?, Chak Janan taja ta Tsaya Ganin Jini A qasa Ga kuma Munayferh na kuka Qanqame da Aaryaan Tana Fadin ta kashesu.



"Yaa Lafiya?" Inji Junayd Cikin tausayawa.


"Babu komai ,Ya kamata Ku tafi dare yayi Saida safe ko"


"Kodai muje

Please Login or Register in order to submit comment