Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Acika yaji sosaiShi nake Jinci ...Kaji please Don Allah"


"Toh naji, ina Auntyn naki?"


"Ta shiga kitchen, Nagode sosai Sosai Allah yayiwa Rayuwarka Albarka yasa kafi hakan
.....yauwa yaya yanzu nan Hafsah ta dawo yanzu haka ma muna tare ne"



Ganin ina Son 6ata masa Mood da Salon maganarda nakeyi yasa ya janye wayan daga kunnen sa tareda Katse kiran jiki a sanyaye.


Nikuwa Ganin ya katse Kiran yasa naja tsaki a fili tareda Furta


"Hakinka kenan a hakan zaka qare Mutum sai Shegen baqin hali kaman Wani Arne?"


"Neryfee Fada mana meye Sirrin mana Wanan Cin Awarar Anya na Allah da Annabi ne?" Hafsah ta fada tana kanne mn ido daya,Don ta lura Bana son irin tsokanar nan.


Harara na wurga mata Nace
" 'Yar iska kyaji dashi"


Daidai wannan Lokacin Ramlah ta shigo Riqeda tray din Abinci...


Saida taci ta ture Sannan Muka Shiga Kitchen a tare dani da hafsah Don Cewa Nayi Janaan tamn WankeΒ² na Yafe sauran Kar a wahalar mana da ciki......

Muna kitchen anjiyo muryar Umma Tana qwalawa Ramlah kira

"Ramlatu Ke Ramlatuwa bakyajina ne?"


Chan kuma naji Muryan Ramlah Cikeda ladabi Tana Cewa

"Kiyi Haquri Umma na Dan kewaya ne ,Gani"



"Don Uwarki zonan Shegiya Tsinanniya 'Yar Marasa Asali"



Da sauri na tsame hannuna Cikin Abinda nakeyi Na nufar hanyan Fita duk Suka Bini da kallo


"Ina zakije?"

"Ina zuwa yanzun zan dawo" ina Fadin hakan na sa Kai na fice.

A Dakin Umma na tarar tarar Da Ramlah tsaye hannunta daya Bisa kuncin ta yayinda Idanunta Suka kada Suka Rine Zuwa Launin jaaaaa



Da sauri na qarasa ina duban Umma dake ta faman huci Nace


"Lafiya? Umma meye haka kardai Marinta kikayi "


"Ina Ruwanki da ita ?, Me kk zo yi Anan Fice Mn da Gani Tun kafin na Kyafta ido na sake waresu akanki ,Shashasha kawai"


"Gaki babbar Shashasahan !, Inba Rashin Hankali da Rashin kamun kai irin na Surukan Zamani ba ,Mutum Nada Gidan mijinta ta baro chan ta Tare Gidan Surukai Don kawai Tana so ta Wulaqanta su...please Riban me Zaki samu idan Kin wulaqanta mu? ,kin San Allah da Nayi niyyar korar ki a Gidan nan da tuni na Koraki kuma Babu mai hanani yin hakan ,So nake Nayi mki kora da hali Nq wulaqantaki ta inDa kanki Zaki Bar mana Gida Batareda Mun Furta ki Fita ba .... amma na lura duk Abinda Nakeyi ba damunki yakeyi ba Tho Tsaya kiji Idan kika sake Kiran ta mare Asali ko kika Goranta mata Akan Wani Abu a Gidan nan wlh sai na hadaki da Abba don Na tabbata Baisan Kina nan ba Ballagazar Uwar miji kawai Mara kamun kai Mtsswww"



Na guya Na kalle Ramlah da tayi tsuru hannunta Dafe a kunci Nace

"Ke kuma Aunty sai kace ba Wayayyiya ba ki Tsaya Tana marinki Akan Me? , Wai Don ta haifi Mijinki? ,ki tuna fa mijinki ta Haifa ba keba Kina Wani qanqatar dakanki A gabanta Sai kisa ta Raina ni ta dauka Gaba daya Haka muke To meye Ribar Biyayyar ma tunda ko anyi A banza ,na Girmama mutum Sannan yazo ya wulaqanta Ni Ai inaaa Ai Ba'ayi wannan halittar ba kowaye kuwa harta Wanda ya ajiye Ni a Gidan bare Wata Banza chan Wai Uwarsa "


"Ya Isa Munayferh" Ramlah ta fada cikin Tsawa tareda Daga mn Hannu.

Hakan yasa Nayi Shuru Tareda mata Duban Mamaki


Ta Cigaba da cewa

"Ki natsu kisan Dawa kikeyi ya kamata Ki San irin kalaman da Zasu Riqa Fita daga bakinki ,ki riqa Tauna zance kafin Ki Furta ..."



Nima tsawan na daka mata.


"Ya Isa Ramlah ! ,Cewa zakiyi bai dace Na shiga fadar da bata Shafeni ba okay na Gane No Qualms kingama tafiyata"


Ina Fadin haka na galla Musu Harara ita da Umma da tayi Suman tsaye Cikeda Hushi da 6acin Rai.

"Kiyi haquri Umm...."


"Dakata Acting dinnan y bada light Sosai Amma fa ko kadan Baki Burgeni ba Dan haka Ki fice mn da Gani Sakarya Yar Marasa Asali kawai.....Zaki fice mn Dagani ko saina Chanza mki Kamanni Tukunna ?"

Da sauri Ramlah ta Fita Har Tana waiwaye Ranta na quna Ji take kaf Fadin Dunya babu Wanda ya kaita Rashin Dacen Uwar Miji, Tunowa tayi da Saleeem Tsohon saurayinta ta tabbata dashi ta Aura da Tafi kowa Sa'ar Uwar miji don Uwarsa Tun kafin Ayi Auren ma kaffa kaffa take da ita, Bata so ko Kusa ya Ra6eta Gaba daya Ahalin su Saleem haka Suke Dukda basuda wadatar Hannu Amma Akwai na zuci ,Karo na farko kenan da tayi nadamar Auren Aaryaan, a rayuwanta Dama chan ba Auren Soyayya sukayi ba Auren manufa Aka hada Ta wani 6angaren kuma Auren Hadi nan danan Rabuwa da Masoyinta ya dawo mata Sabo , Tana Shiga daki ta fada kan Gado tareda Fashewa da Wani irin kuka Tunowa da tayi Wacece ita.




WAIWAYE ADON TAFIYA.


Mahaifan Ramlah Malam Isah da Hajiya Kulu haifaffun Garin Kebbi ne, Sunyi Soyayya Sosai daga Bisani Iyayen Kulu Sukayi yunqurin RabaSu a dalilin Wani Dan masu Hannu da shuni da ya danno kaiπŸ˜†.


Nan fa Isah ya Rude ya rasa yanda Zaiyi Ganin ana Shirin Rabashi da Rabin Ransa , Nan fa Wani Wawan Abokinsa ya bashi banzar Shawara Wai Ya Afka mata idan iyayenta Sunga 'yarsu da Ciki zasu sallama Mata.



Koda ya tunkareta da maganar batayi masa Musu ba duba da yanda take sonshi kaman Ranta....



Bayan Wasu 'yan Watanni Aka Gane Kulu na dauke da Cikin Isah dama bisa al'adar Mutanen Yankin idan mace da Namiji suka aikata Abin kunya To Wlh Jeheshi Sukayi Har ya mutu .


Ganin An Ganosu ne yasa Su barin qarnin Cikin dare Batareda An San da Fitarsu ba, Sun sha wahala Sosai daga bisani Suka sauka a garin Jos inda Malam Isah yakama Aikin Gadi a Wani Gida Ana hakane ya dirka Wa 'Yar Gidan Ciki nan ma akayi msu korar kare Don A Gidan suka basu Masauki.



Ana haka Cikin Biye biyensu Suka sauka a Cikin Garin Kaduna A Kabala Custein Inda Alhaji Junayd ya taimakesu Koda ya nemi jin asalinsu Cewa sukayi Ai basu da Asali Gaba daga ahalinsu Sun mace Su kadai suka Rage a family kuma 'yan Garin Sun msu korar kare Sbd laqa Musu Satan da Akayi da yike shi Alhaji Junayd din Akwai tausayi nan danan ya tausaya msu ya basu masauki a Gidan su ,inda yake Zaune Yayansa da matan harda 'ya'yansa hudu a Gida Daya Aaryaan Umar Junayd da zee sa agida daya Yayinda A lokacin Uwar Gidan Yayan nasa Tana dauke da wani Cikin ,Shi kuma Junayd Har lokacin Baiyi Aure ba.

Amma Abinda Junayd ya lura dashi Kulu da Rabi Sun hada kansu Waje daya Yayinda Uwargidan ta Tsane Kulu kullum sai an jisu tare Don Goranta mata da takeyi Amma Da yike itama Kulun ba kanwar Lasa bace nan Zata saki baki tayi ta zaginta Tana maida martani.


Ana haka Haihuwa yazo msu lokaci daya A lokacin babu kowa a Gidan sai 'yan Aiki da inna Rabi yayinda Yara sun tafi makaranta Mazajen kuma sun tafi Wurin Aiki.



InnaRabi ce ta taimaka Msu ta kira Wani Dan uwanta ya kaisu Asibiti Dan Cewa tayi bata Yarda da Drivern Gidan ba Wai ya iya Driven ganganci .........
















IN FASA QWAN A NEXT KO SAI NA KAI QARSHEN LITTAFIN?





update din yau harda na jiya fa

😌😌😌






Nayi gabasπŸšΆπŸΌβ€β™€οΈ




27th octπŸ˜‡
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
NA
*🀍Fahnaan🀍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

Β©πŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻_Aβ€’ Wβ€’ Aβ€’_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…...


*_Chapter 55_*




Koda Suka Nufi Asibitin nan da nan Aka shiga basu taimakon Gaggawa..



Cikin Ikon Allah Kulu ta Sull6o 'danta Namiji yayinda ,Haleemah kam tuni ta fice a hayyacinta, Ta galabaita Iya Galabaita Cikin ikon Allah Itama Allah ya nufa Ta haifi 'yarta mace..


A lokacin Likita tazo ta sanarwa InnaRabi daketa Zirya a Farfajiyan Asibitin ~Dan da Kulu ta Haifa Ya koma~


Murmushin da naga InnaRabi tayi shine ya bani mamaki nan Taja Nurse Dinda ta kar6i Haihuwan Gefe Suka tattauna Suka qulla yarjejejeniya A rubuce Zatayi ma Haleemah Alluran barci Sannan Ayi Exchangn yaran da suka Haifa Daga nan tabar Mata komai a hannunta Tayi Al'qawarin zata biyata maqudan Kudade ,Kudaden da Suka Rikida kwanyar Nurse din Har ta kasa yi Msu Gardama Akan nasu buqatan Ta Amince da sharadin Sai An Rubuta komai A rubuce a matsayin Yarjejeniya Haka kuwa akayi ta Yarda zata bata kudade A chanza yaran kafin Haleemah ta Farka Haka kuwa akayi ta sanarwa Kulu Yanda sukayi da Nurse ta Qara da Cewa.

"Kulu Nasan Zaki Amince da buqata ta!, Wannan shine kadai damar da kike dashi na Rama Wulaqancin da Take mki da Goranta mki da takeyi na Rashin Asali ,Na tabbata bazata iya jurar Ganin wannan Ranar ba ,Tasha Wahala Sosai Wajen Haihuwa Ba komai yasata Wahalan ba sai Maganin da na zuba mata cikin Ruwan da ta nema dazun ,Eh nasanta da son yaranta Especially Wanda tasha Wahala Wurin Haihuwan Sa , na Kira mutane na Suna hanya yanzu haka ma Sun Kusa isowa haka kuma na sayi Duk masu Gadin Asibitin nan Eh Dama ai mutane na ne mun saba hakan dasu Idan Mutanen nawa suka Iso Nurse zata farkar da Haleemah Sai su Sassare Gawan Yaron da kika Haifa a Gabanta Kinga daganan ma Zata iya hadiye Zuciya ta Mutu kin Gane Ai kawai Kiyi biyayyah Ki bada Gawan 'danki Shine kawai Zaki Sami ingantaccen Rayuwa"

Kulu ta tsare InnaRabi da idanu Ita duk Rashin Imaninta yau taga wacce taci Uwar nata Nan danan Tsoron InnaRabi ya shigeta


"Haba Inna Ya zakice haka? ,Dan da na Haifa Za'a sassare?, Wannan ai Ni Za'a ,Ni wlh na Yafe a Burne mn Dana haka Abarta Tajida Abinda Ke damunta"


"Ke Dalla chan Shashasha Ina kaiki kina komowa baya?, Ke Har kin Isa kija da magana ta?, To kijini da kyau Wannan Abin ba kaina zanyiwa ba Ke nake nemawa ingantaccen Rayuwa, Eh mana Kinga idan kin Amince Kin samu Abu Biyu kenan a lokaci Guda ko ma Nace Uku in Zaki Amince , Nasan kuna Neman naku masaukin na kanku Ko ba haka ba tho idan kin Amince Ni dakaina Zan Baku Kyautan qaton Gidan Da nasa Aka Gina mn Kwanaki Sannan na baki jari na Sa mijina ya Ba Isah Aiki a babbar Ma'aikatarsa Kinga sauyin Rayuwa kenan , Secondly Wannan Yaron da Zaki bayar fa Gawa ne babu Amfanin da Zaiyi mki ko Ambar mkishi so idan Muka Yarda da sauyin nan Zaki Sami daman huce Fushin ki akan yarinyar In Allah ya Rayata Ta dandani Zafin Gori itama Kinsan ta Wani hanya?"


Kulu da tunda taji an Ambaci Kudi Jikinta yayi sanyi ta Girgizakai Cikin Girmamawa InnaRabi ta lura da haka don haka ta murmusa Dan Tana Ganin Alamun nasara Cikin Takun nata Kenan Don Ta lura da Kulu mayyar kudi ce


Ta Cigaba da cewa "Zamu San yanda Za'ayi Mu Hada Auren Babban 'danta Aaryaan da Jaririyar (In ta Girma) ta inda da kanta Zata Wulaqanta Abinda ta Haifa Batareda ta Sani Ba, kinga idan Sun haihu Suka haifi 'da namiji Sai mu sa ta kashe shi Mu kuma kashe Aaban din Kinga Sai 'dan da suka haifa ya Qwamushi Gadon Duka Kinga daganan Munyi mata Duka Biyu kenan Kedai Kiyi biyayya zakiga yanda Zan mayar dake".


Kulu Taja Gauron Numfashi a da dai Tana tunanin qila bazata Amince da Buqatar InnaRabi ba Amma yanzu da taji qudurinta da Maqudan kudaden da Za'a bata infa bata manta ba harda Gida da jari Za'a basu Sannan idan haqansu Ta cimma Ruwa su qwamushe Dukiyan mai Gidan Chaske Ai tuni ta Amince Har ta bada Goyon bayanta 100%


Nan dai suka hada Abinda zasu hada Akayi Abinda za'ayi Koda Haleemah ta Farka tayi baqin Cikin Abinda ya faru Ganin yanda akayi Fatse Fatse da jariri a gabanta Dole Abba yabar Harkokinsa ya Dawo Gida Aka sanar Wa 'yan sanda Amma Abin mamaki cewa sukayi Babu Wani hujjan da Zai nuna da Gaske Sassare 'Dan nan Akayi mai Yiwuwa ma ita ta kashe Abinta da kanta tunda Anyi bincike a iya binciken Su kuma babu Wani Wanda ya Shigo Asibitin A lokacin da Ta Haihu harta CCTVn dake maqale a Asibitin ma sun Cire Clip dn Ranar da Abin ya faru Sbd haka tun case din na tsakanin Corporals aka Ruguzashi Ba'a bari Manya Sun Sani ba ,Tabbas Sun Sami nasarar Qunsawa Haleemah baqin Ciki Don saida tafi watanni Tana jinyar Abinda ya faru Ya kasa Gogewa daga zuciyarta Har yau...



Gefe Guda kuwa InnaRabi ta Cika Akqawarin da tayiwa Kulu ta Bata kyautar qaton Gidan da take Ginawa cikin Garin Kaduna haka kuma ta bata jari tareda Maqala Isah A sabon babbar ma'aikatar Mijinta ,Hankalin Kulu ya kwanta sun bar msu Gida sun huta babu mai takura su, Ranar Suna Ba'ayi Wani taro ba duba DA yanayin Garin da yanda Ake Ciki Nan Yarinya taci Sunan Ramlah ,A Ranar suka Ke6e da wasu Malamai aka daura Aurensu da Isah, Kunsan Ba Aure sukayi ba ko! ,Kuma ai Koda suka zo kd Cewa sukayi sunada Aure .



Kafin shekara ta zagayo Harka ta Bunqasa Arxiki ya zauna a Gidan Isah kwanciyar hankali kuwa Ba'a cewa komai ,Ransu Fesss Jinsu Suke sai yanzu suka fara Rayuwa.



Koda Ramlah ta taso ,Ta tasone Cikin Tsana da tsangwama Na Iyayenta ,


Koda ta isa Shekaru biyar a duniya basu Sakata a makaranta ba Duk kudinsu Sunqi su Sata Sbd basu Son Ta taso Cikin Wayewa irin na 'yan Gayu Saida Alhaji Aabaan yasa baki Tukunna suka Sata nan ma na Gwamnati ,Don basu Yarda Su 6arnar da kudinsu akanta ba.


A lokacin da ta Cika shekaru15 da Haihuwa Lokacin Arziqi ya Zauna ,komai nasu ya kuma ha66aka Abin sai San barka ,Dukda kuwa jahilaine Rabi tasan yanda Tayi tasanya su a jerin masu Alhazan Da Ake jida su a qasan nan lallai Abin sai San barka Dan hakama Suke Girmama Rabin Fiyeda Ubayen Gidan nasu wato Junayd da Aabaan.



Lokacin ne kuma suka Samo masu yi masu hidima Maza da mata Cikin su kuwa harda Saleem Wanda ya kasan ce a matsayin Drivern su Yake kaisu duk inda Suke son Zuwa hakan yasa yasan Wasu Abu dangane dasu , Shaquwa Ta Shiga tsakanin Su da Ramlah Wanda Har Shaquwan nasu Yake bama kowa mamaki Duba da yanda Ramlah take Bata son yawan Magana Da Son Hayaniya Idan ka gansu tareda Saleem sai ka Rantse Ba ita bace Shuru Shurn nan Ba



Saleem ya kasance maraya ne bashida uba haka kuma bashida Wasu 'yan uwa Sbd haka Yake tareda mahaifiyarsa wacce take Daukan Nauyinsa da na qaramar qanwarsa IFRAH sun kasance basuda komai Face Wadatar zuci Wanda ya zame msu Garkuwa akan lamuran su Hajiya Fati (Mahaifiyar Saleem) tayi Kowane Aiki Dan Ganin ta sama Wa 'ya'yanta Ingantaccen Rayuwa Yanzu haka Saleem AGENT ne a Ma'aikatan Binciken Sirri na Tarayya yanzu haka ma Aikin ya kawoshi Gidan yake msu Aiki a matsayin Driver.


Sun dau Tsawon Shekaru Suna tare daga Bisani ya bayyana mata Shifa Sonta Yake kuma zai aureta idan Za'a bashi ita Babu 6ata lokaci ta Yarda ta kuma Amince Batareda ta Duba Matsayin shi a Gidan su ba ,Hakan yasa Yake Qara sonta don ya lura ita din ba mai son Abin Dunya bace.


Tun Suna Soyayyar su a 6oye Har Ta Fito fili nan fa Ake yinta ,Hajiya kulu Ganin yana Shirin 6ata mata Aiki yasa ta Tuntu6e shi Da Maganar Tana so ta hadashi da Manyanta Su nema mshi Aiki a Abroad, Abinda yasa tace masa haka kuwa shine ,Shi Saleem yana mata Wani irin kwarjinin da ko kallon Kwanyar idonsa bata Jureyi bare ta Fada Mshi ya Rabu da 'yarta kai tsaye.



Shima Bai Wani ja da maganar ta ba Ya Amince ,Don Ya lura ta nan zai kuma Samun Muhimman bayanai akan Aikinsa Koda ya jewa mahaifiyarsa da maganar fatan Alheri kawai tayi masa tareda masa fatan Nasara.


A lokacin kuwa Har Ramlah ta Kammala karatunta Na Degree Har ta Fara NYSC dinta kasancewa karatunta yayi sauri Sakamakon Promotions dnda take samu a makaranta Hakan ba qaramin 6ata Ran Isah da kulu yakeyi ba,Babu yanda Suka iya Don burinsu bai Wuce ta Wulaqanta ba Amma da Yake Uban Gayya mai gayya ya Tsaya akan sai tayi karatu babu yanda Suka iya


Bayan Hade hade da qulle qullen da sukayi sunyi nasarar Kai Saleem zuwa qasar LIOS da cewar Zai Riqa koyawa Wasu yara karatun islamiyyah.


Ranar da Zasu Rabu Ramlah tayi Kukan Rabuwa dashi ba kadan ba Dan Har cikin Ranta takeji Ta rasashi kenan ,Shima Gareshi hakan ta kasance .



Bayan komai ya lafa ne ,Hajiya Kulu ta Shawarci Mijinta Alhaji Isah akan maganar Auren Ramlah da Aaryaan y farayiwa Abba magana (πŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ€¦πŸ»β€β™€οΈπŸ™πŸ»β€β™€οΈπŸ™ŽπŸ»β€β™€οΈπŸ™‡πŸΌβ€β™€οΈ)

~Waiyazu billah hajiqa jahilci Baiyi ba~



Koda yayiwa Abba magana bai Wani ja dashiba don Har Cikin Ransa Yake qaunar yarinyar ,Kuma Yana qaunar hada Zuri'a da ita dubada yanda take kamila kuma natsattsiya Gata da ilimi both na bokon da na Arabi.



Koda ya tuntu6i Aaryaan da maganar Cewa yayi idan Yarinyar ta kwanta mshi a rai Shima ta kwanta mshi, Ya Amince


Abba yayi murna Sosai da Amincewarshi Amma Koda ya gayawa Umma Cewa tayi bata sa6uwa hada 'Yar Marasa Asali da 'danta nan ta shiga 6arin zance itafa bazata Yarda ba *.*.*.*.*


Daga qalshe akafi qalfinta aka daura Auren Aaryaan da Ramlah A Ranar da Za'akay Ramlah Mamy (Hajiya kulu) tajata Gefe tayi mata bayani Akan Dalilin hada Aurensu ~A lokacin an sace Mahaifan Munayferh~

Tace Ba komai yasa suka hada Aurensu da Aaryaan ba illa So Suke ta dauko masu Wani 'Yar Akwati Wanda Yake danqare da Diamonds, Abinda yasa Suka za6eta A MATSAYIN mai daukowa kuwa shine sbd ba kowa Suke barin Su Shiga Part dinba ,So idan Sunga ita Amarya ce kuma Suruka Zasu iya barinta ta shiga ,idan Ta kawo Akwatin zasu siyarda Diamonds din Su Sami ingantaccen Rayuwa su fi haka dauka ka..

Ramlah ta kasance mai haquri da biyyya Gun iyayen Riqon nata Duk da kuwa Su din masu kasan ce nagari a Wajen ta ba Kullum burinsu bai wuce Su azabar da itaba tareda bata wahala Amma duk da haka bata Gaza ba Wajen Yi msu biyayya iya Gwargwado .


A take ta Amince da Qudurinsu Amma a Badini Bata Amince da hakan ba ,Kawai Ta Amince ne don Tanaji Idan tayi Auren ne kawai zata huta Da Wahalan da takesha A Gidan su Sai Gashi tazo ta tarar da Uwar Wahalan ma.......


*******


Aaryaan ne y shigo Riqeda hannun Ameerah Ameer na Goye a bayansa Suna ta Kwasar Dariya.


Ganin Ramlah tayi Tagumi yasa ya Sauke Ameer tareda Fadin Kuje Wajen Aunty Munayferh ina zuwa , a guje Suka yi Waje shikuma Ya qaraso wajenta.

Da Alama bata ma San ya shigo ba, Hannu yasa ya Cire Mata hannun da tayi tagumi dashi,


Firgigit ta Dan Razana da Ganinshi daga Bisani tadan waske da Fadin


"Sannu da zuwa! , yanzu ka shigo"


Bai amsaba Illa kallon da ya bita dashi ,

"Ramlateey Tunanin me kikeyi?"


Ya tambayeta Cikin kulawa "Nothing, Kawai ...." Sai kuma tayi shuru


Ya fahimci inda Zancen ya nufa don haka ya matso ya fara Rarrashin Abinsa tareda Ban baki Akan tayi haquri Wata rana zataci Ribar haqurin.....



A Gefe Guda kuwa Tare mukayi Girki da Hafsah don qiri qiri na hana janan ta tayni Muna Gamawa Yaajunayd ya dawo hakan yasa ta Fice ta barmu mu Biyu


Muna Gamawa Muka jera komai Kan Dinning Saiga Su Ameer sun Iso da Gudu kaman wa'enda aka koro,Suna Fadin

"Aunty mun dawo"

Sai kuma sukayi Shuru Ganin Hafsah tsaye Gefe na da Gudu suka qarasa wajenta Suna Dariya tareda Fadin


"Anti In dawo ye?"
Ameer yace "Ba haka hake shewa ba ,Shewa Ake In dawo yafiya?" Gaba daya mukayi Dariya


Nace "Amiya Waya kawo Ku?"

Tace "uncle"
Hakan yasa na fahimci Yana Gidan Dan Haka naqi Zuwa kiransu ,Saida Muka Gama Cin Abincin na dauko wayana

Na tura Dan na tura mshi text amma Abin mamaki ,Na rasa Numbern shi Sama da qasa Nidai Nasan ban Goge Numbern ba Tho Ya Akayi Numbobin Suka Gudu?, , Wani tunani ne ya zo mn don haka na Shiga Resent Calls don Shine y kirani last.


Ina Shiga Kuwa mamaki ya kamani Ganin Sunan da Nayi instead naga

MIJIN TITI kaman yanda Nayi saving sai Ganin mithaee Aary (Swt Aary) Nayi.



Kallon hafsah Nayi cikin tuhuma Nace "Uban Waya baki izinin ta6a mn Waya?"


Zaro ido tayi tace "Yaushe kika Farayi mn iyaka da wayanki?"


Ganin Nayi shuru sai kallonta nake ina Huci yasa tayi Raising hannayenta don bata San Dalilin Kunburin da taga inayi ba

"Nifa ban ta6a miki Waya ba, inaga jaanu ce"



Sai yanzu Nayi Murmushi na maida hankali na Ga wayana na fara tura mshi saqo kaman haka

πŸ’¬Malam idan kuka gama Abinda Kukeyi Sai Ku Fito Food is Ready....

Idan zaka Fito ka Fitomn da Car key dna ,Zamu Fita Nida Su hafsah mu Dan zagayaya gari daganan Muyi siyayyan School Sai na maida Su Ameerah Gida.



Ina jirankaπŸ˜’

Ina Gama Turawa babu jimawa Sai Gasu Sun Fito ,Hannun su Riqeda na Juna sai Kwasar Dariya Suke Alamar sunajin dadin yanayin


Da sauri na kawar dakaina daga dubansu Sakamakon Wani Abu da naga Ya tokaremun maqoshi ,Hannu nasa na Jawo Ruwan dake Gefe na kafa a Bakina Kodan Abin ya tafi Amma ko motsawa Baiyi daga maqoshin ba.


Muryan sa naji yana Fadin

"Ina mum take" a Raina Nace tunda ka bamu ajiyanta ba.


Hafsah ce ta bashi Amsa da cewar "Ai sun Fita itada qawarta"


Murmushi kawai yayi ya jawo kujerar dake Kusa dani ya zauna yana 'Dan leqa fuskata.


"Ammatas Wai Yaushe Zaku Koyi iya Gaida mutane ne?"

Hafsah ta gaidashi ya Amsa tareda cewa ya Hanya? ta Amsa da lafiya.


Ni kuwa banda Turo baki babu Abinda Nayi Cikin takicin zama dayayi kusadani Ni .


Murmushi yayi Dan ya lura yau 'yan tsiyan na Kusa yana Cewa kule zance chass


Dakansa yayi serving dinsu Suna cin Abinci Suna 'Dan ta6a Hira Ni kuwa ko kulasu banyi ba Na dai qosa ya gama Nayi masa maganar Mota ta don tunda aka kawoni ban ta6a Fita dakaina ba So yau na dau Aniyar Fita kota halin qaqa ,Dan haka na Ciro wayana ina danne danne Har suka kammala


Na dube shi Nace "ka bani makullin Mota ta zamu Fita"


Wani Uban Harara ya watsa mn Sannan ya miqe tareda Fadin hafsah ta Tashi ya kaisu Gida


Zaro ido Nayi Nace "Wani irin Gida? , Nace maka Fita zamu yi"

"Fita zakiyi da izinin Wa?"


"Da izininka " na bashi amsa kai tsaye

Hafsah da Ramlah Suka 'Dan murmusa Yayinda a qasan Zuciyarsu Suke Mamakin yanda Munayferh Ke iya kallon Idon Kowanne Mutum ta Ya6a mshi magana sonRanta.


"Idan kinason Fita ki Shirya ki mana Rakiya "


Ya fada tareda Barin wajen .


Turo baki Nayi tareda hararar su hafsah daketa faman Dariya na Shige Ciki na Watsa Ruwa Tareda Sauyawa Cikin Wata Royal Blue Arabian Gown an mata ado da Light blue, Sannan na yafa mayafin Rigar Wacce take light blue Nayi kyau sosai kaman ka saceni ka Gudu duk da kuwa banyi kwalliya ba na dau jakata na Rayata na sa Takalma Nana Fito Inda na iske Hafsah da Ramlah a falon qasa Suna Hira Gefe daya kuwa Su Ameerah ne keta Faman guje Gujen su a parlourn

"Masoyiya tashi mu tafi" na fada ina hararar hafsah da taketa faman Zuba surutu.


Miqewa tayi Tareda kiran su Ameer Sannan tayiwa Ramlah sallama Sannan Muka Fito


A motar sa Muka iskeshi ,Na bude gaba Na Shigarda su Ameer Ciki

Nikuma na koma baya na zauna kusada Hafsah.


Yayiwa motar key yaja Muka bar Gidan,Mun Danyi nisa tafiya Bakajin Komai sai muryan hayaniyan su Ameer

Sai a yanzu na tuna da awarar da Nace ya siyo mn dazu


"Yaa ina Awaran da nace ka siyo mn dazu"


Murmushi yayi ya kalle Ameerah dake zaune kusada Shi yace "Amiya Dauko mn Ledar chan"


Ta dauko ledar ta miqa masa Tana cewa "Uncle Akai nayyi"


Murmushi yayi yasa Hannu 'daya ya kar6a tareda Miqa mn tabaya


Na kar6a ina Godiya Nan Da nan na Faraci

Please Login or Register in order to submit comment