Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A lokacin nayi sati Biyu bangansa ba ,Ashe wannan abin shine qaddarar Ku na Kasancewar Ku tare ?"


Ta dan tsagaita tana kallon yanda yanayi na ya chanza ta kuma Juyawa ta kalle Hajiya Asiya sai kawai suka kwashe da dariya.


Ta cigaba d cewa

"Munayferh daga yau babu wani mahaluqi da zai Sake kallonki a matsayin Mutum ,Ganinki za'a Rinqayi tamkar Dodo ko Kuma Vampire saboda a Halin yanzu kama kike da dodo ta dayan 6amgaren kuma Sak Vampire ,Ina Fararen idanun nan naki Masu matuqar daukar hankalin Mutane ?, a Halin yanzu Fararen idanun Sun koma Jajir tamkar Wuta yayinda Baqin Cikin idonki ya Koma Blue ,Duk ilahirin Jikinki Gauraye yake da Gashi Babu Inda babu Qarin Abin Farinciki anan shine jikin nan naki mai Daukan hankalin 'dana da yake wani Manne mki yana Shaqar Qamshin Jikinki a yanzu ya koma Busuยฒ ba'a Ganin Komai a tattareda Fatar dake jikinki face Gashi ,Gashin ma irin na dodonin nan Masu Zuwa a horror Movie Yayinda Muryanki take kamada na Tsofaffin nan Wa'enda Haqoransu Gabaki 'daya suka zube''.....


Kallon kaina nayi a Firgice Gani nayi babu wani sauyin da Umma t lissafo a tattareda ni ,Dagowa Nayi hawaye suka Ciccciko a Idanuna.
Na bude baki zanyi magana Sai kuka taci qarfina



Hajiya Asiya Kuwa tsabar yanda abin yayi mata Sugar yasa ta kasa magana sai binmu da kallo take tana wani Shu'umin Murmushi ,Umma kuwa ko ajikinta Ta cigaba da cewa

"Ke kadai Zaki Rinqa Ganin kanki a matsayin Mutum , haka kuma A Halin yanzu Aaryaan yana Abuja yana Aiwatar da wata Aiki idan Kika sake idanun yaransa Suka hadu da na yaransa Rasashi zakiyi na Har Abadah don Mutuwa Zai yi Akwai Gubar da na saka Cikin idanun yaranki Da zarar sun hada ido zai Mace ,Ni ban damuba idan na rasashi Don inada Wasu yaran Wa'enda suka Fiye mn shi a Gareni ,Haka kuma idan Kinaso Mutane Su Rinqa kallonki a matsayin Mutum Su bar Ganinki a matsayin Dodo sai kin bar qasar nan shine kawai magani idan har kina Nigeria Tho fa Kowa Ganinki zai Rinqayi a matsayin Dodo Harda iyayenki da mijinki kuwa ......โ€


Hajiya Asiya tayi shewa Tareda tafawa irin Abin yayi mata Daidai Dinnan


Ta tako Gabana Cikin Tafiyar Ta na Qasaita ta qare mn kallo sai kuma ta fashe da dariyan Mugunta.

" Munayferhn Aaryaan, Mummyn Twince Shalelen Abba Da kakus Yar gaban Goshin Daddy da Ammie Yar Gatan Abdool da Twince , Inye kinganki Kuwa Kinyi kyau Sosai Kyakkyawa 'Yar qwakisa , kin tuna sanda Kika daga qazamin Hannunki kika yarfa mn mari?, Kin dauka kin mari bulus kaman yanda kika saba Ko?, Inaa Ni ba'a ta6ani a tafi lami , kinga wannan Abinda Mukayi miki Soman ta6ine Babba na nan tafe Idan Kika sake kika Qara Wata daya a wannan qasar ba tareda Kin barta ba Ko kuma kika bari idanun Aaryaan suka hadu da na Yaran nan naki Aradu Mutuwa zasuyi daga 'ya'yan har Uban ,Wannan Hukuncin Uwar mijinki ne Ni 'Yar jagorace kawai a wannan Aikin Amma nawa Punishment din na nan Tafe idan baki bar qasar nan ba Cikin kwanaki talatin , sainasa Mutanen Gari sunyi mki Jifar mutuwa Sannan Na Aikata Abin nan Ga Uwarki wacce a sanadinta Haleemah ta ke samun Matsala a Gidan aurenta ,Oya Ware mn da gani......"


Sai a yanzu hawaye Masu zafi suka zubo suka Wanke mn Fuska ,Ban damu da na Sharesu ba saboda tashin hankali .


Umma kuwa ganin Kalar Hawayen da zubowa daga Kwarmin Idanuna yasa ta kaudakai a tsarace tareda kallon Hajiya Asiya wacce keta faman Murmushi ta Dage mata Gira daya.

"Ummah Ai da kun kasheni Madadin Kuyi mn haka"


"Fiyeda hakan Na nan Tafe ,Kin manta Na dau Alwashin Bazan ta6a bari Ki ra6i Aaryaan ba kuma kika Karya mn Akwashin da na dauka harda Haifa masa Yara Har Biyu ...... I pitty You Girly Rainon Yara har Biyu ba qaramin Abu bane bare Kuma kiga yanda Qaddararki ta kasance Eyyerh So ki zage damtse If not Zaki rasa su zakiyi Aradu ,Anda last thing karda ki sake Ki nemi maganin Wannan Cutar da muka sa miki Da Al'qur'ani ko dawani Abu islamically Cus Da Alqur'anin Mukayi Abinda Muka Aikata "


Tayi maganar Cikin dariya


Share hawayena Nayi da bayan hannu Jikina Kyarma na kalle Umma wacce Tafi bani mamaki ,na bude baki zanyi magana Sai Kuka yafi qarfina ,Nan take suka fashe da dariya , daqyar na iya tsayar da Kukan da nakeyi Na fuskance ta Dakyau tareda Tattaro Jarumta ta ,Cikin Cijewa da Jarumta na fara magana Kaman bani na Gama Kuka yanzu ba.


"Umma Kince laifina Shine Ina Auren 'Danki kuma ina Yawan Ra6arsa dakuma 'ya'yan da Allah ya Azurtani dasu a sanadinsa ,Ke kuma saboda na Mareki ...... haha tho duk Ku tsaya Kuji kaman yanda Kuke Masu Ramuwa Akan komai bakuda Haquri bare yafiya Ni Ramuwan Gayya nakeyi ,Bana Barin Mugu Umma Kaman yanda kikace Nabar qasar Zan bar qasar Don shine Kadai za6ina A Halin yanzu don bazan Iya Jure Ganin Mutane na Guduna ba Amma ki Sani Kafin na bar qasar nan sai na kuma Aikata Abinda bakiso Saina Tabbata Aaryaan ya Sake mn Ciki kuma Saina Bar masa tabon da bazai iya Jure Rashina a Kusada Shiba ,Umma kina wasa da Rayuwan 'Danki Rayuwarsa Gabaki daya yana hannuna idan na bar qasar dakanki Zaki nemoni Don Aaryaan bazai iya Rayuwa ba idan babu ni Yasha Fada mn idan na Rabu dashi Zai iya rasa Rayuwarsa Kuma na tabbata Hakane , Ko Duk jama'an dake Duniyar nannSun gujeni na tabbata shi bazai ta6a Guduna haka kuma koda Dukkanin ilahirin Duniyar nan Sun kasa ganeni a dalilin Fuskar da kuka sa mn Shi Zuciyar sa zata Ganeni Da zarar ina Guri Zuciyar sa na Sanar dashi , Dazarar ina cikin damuwa Zuciyar sa na Bugawa Da zarar Ina tare dashi Ilahirin jikinsa na Tsumayin Ganina Malama Haleemah mark my word Munayferh ce Rayuwan Danki da mijinki , Nice ke playing a tsakanin Igiyar Aurenki wacce kike tunqaho dashi idan na ga dama yanzu Zan turawa Abba komai Ta Email kuma na bashi Umurnin ya sakeki Kuma Dole sai ya sakeki Amma bazanyi haka ba ,Infact Zan 6oye kaina ne as u said "


Kalamaina ba qaramin Razana Umma sukayi ba idanu ta firfito waje Don tasanni sarai bana daukar Alqawari batareda na Cika ba Shiyasa nakeda Wuyan daukan Alqawari ,Tsoronta daya kar na nemo Aaryaan na Fada mshi komai Ya biye mn Har na Samu ciki kaman yanda na fada.


Na maida Dubana ga Asiya Wacce keta faman taunan Chewing Gum tana Harara na nace


"Kinsa An Sa mn Fake face ,batareda Kinyi Tunanin Abinda zai Biyo baya ba , kema Kaman yanda kika bani Umurnin Zan bar Qasar as u said kuma bazan ta6a bari ya hada ido dasu Hasna ba Cus banaso na rasasu ,Amma ki Sani Ni fake Dodoce Kuma da na bar qasar zan dawo normal ke kuma na dau mki Alqawarin Saina Maidake Dodon Gaske...... sai na Nuna miki ni Chemist che wacce tasan Abinda takeyi tasan Amfanin Elements"


"Ke dallah Rufama mutane baki ,Da wannan Kwa6a66en Jikin naki Zaki Sauya mn kamanni? This's so crazy kinada Qarfin Halifa "


"Heyyy Excuse Abege Point of Correctio....."

Gau naji an daukeni da wata irin waawan mari wacce tasa saida naga saurari a Idanuna kafin na dawo Cikin hayyacina Har ta daga hannu ta sake wankeni da wata Wanda ya Sanya Idanuna makancewa Da Wasu 'Yan seconds.


"Ewwa Qara mata " cewar Umma a muguntance๐Ÿ™„..


Hajiya Asiya ta nunani da 'Yar yatsa Cikin masifa take fadin

"Mara kunya wato duk Abinda Mukayi mki bai isheki ba Tsabar Tsaurin ido ina magana Kinayi don Tsabar tsaurin ido da Rashin kunya, Kika sake magana anan Saina Nakasaki wlh na maidake Vampire din ta gaske Shashashar banza kawai"



Kambalastin na fada tareda Dafe Kuncina hawaye suka sulalo a bisa Dankalin Fuskata , Aikam tana Dasa Aya na daga hannu na rama Marin da tayi mn ,ban bata damar Sosa wurin ba na qara mata na qara daga hannu zan wanketa da wani Umma ta Riqe hannuna tareda Wankeni da wata Marin.

Aikam ban yarda ta sauke Hannun ba Cikin Fusata na daga hannuna Na shiga Wanke Fuskar tata da maruka Masu Kyau Cikin Fitar hayyaci Ni kaina bansan adadin marukan da na yarfeta da Su ba don Fita nayi gaba daya daga Cikin Hayyacina tamkar zararriya haka na koma ,Umma kuwa Ganin ina Shirin kasheta da mari yasa ta fara Yunqurin Kare kanta nan take fada ya kaure tsakani na da ita .


Hajiya Asiya kuwa Ganin ina shirin kashe Umma da ranta yasa ta Tayi Cikin Gida da Gudu ta kirasu Wai dodo ta kama Umma zata kasheta , nan take Gabaki daya ahalin Gidan suka Fito Aikam suna Ganin halittar wacceke Laftar Umma sukaja da baya Cikin tsananin Tsorata da Firgicewa aka rasa mai kwatar Umma a hannuna saida nayi mata lilis sannan na barta na koma Gefe ina Maida Numfashi.


Saida na tabbata na dawo Cikin hayyacina kafin na dago na kalle Su Ammie Wa'enda Suka zuba mn idanu A hankali na Miqe tareda nufarsu Amma Abin mamaki Gabaki dayan su Sukayi baya Yayinda Yaran sukayi Ciki da Gudu.


Murya na rawa kuma cikin Kuka na Furta


"Ammie"

Su Kuwa jin muryar wannan BAquwar halittar ya kuma firgitasu Ya razana Suka Kuma Tsorata Da sauri Ammie ta Qanqame Daddy Cikin Tsananin Rikicewa don Ganin ita kadai nake Kallo .


Abba Cikin Jarumta ya ce

"Don allah Dodo ka/kiyi Haquri Kibar wajennnan Don Girman Allah kaji Idan Laifi Tayi maka kayi Haquri Munada Qananan Yara Anan karka firgita mana su kaji"



Idanuna Suka Cicciko da qwalla Bakina Rawa nace


"Abbi...e na nice ....."


abba kuwa Jin irin Mummunar Muryan da Yayine yasa ya daga mn hannu Cikin Fusata tareda cewa

"Wallahi idan ka qi barin nan Saina Sa6a maka kuma na hada ka da Hukuma Don nan Gaban Gidana ne"

Cikin Qoqarin maida hawayena na nufosu tareda fadin

"Ammie kema a dodon Kike Ganina? ,Dagasske Muryata Ta koma tamkar na dodonni? ,Abba yaaUmar, Ammie ,Abbie, Twiny Yaasaleem Aunty Ramlah Meyasa Kuke Guduna da gaske Shikenan Na zama dodoniya?, Don Allah Ku tsaya Ku saurareni"


Haba ina ko fahimtar Maganganuna Ma basua yi ,Gabaki Dayansu Suka Shige ciki Cikin tsananin Tsorata da rudewa ba ganin sabon halitta"....


Durqushewa nayi kuka ya qwace mn na shiga fashe da kuka da iya qarfina jikina ne ya bani ana kallona Don haka na Dago don na duba waye , Ammie ce har yanzu qanqameda Daddy har ta fara hawaye Kasancewar ta mai rauni da Shegen Tsoron Tsiya.


A hankali Daddy ya furta

"Baiwar Allah or bawan Allah don Allah ka taimaka mana ka taimakawa Kanka ka bar nan wajen Badon komai ba Don gujema Abinda ka iya afkuwa ,Mutanen Layin nan sunada Hadari , idan Suka farga dakai da jifa zasu Raka ka kuma basuqi su kasheka ba ,Kaji please ka tafi na lura kai ba mai cutarwa bane Tunda baka Cutar damuba"

Wani irin matsanancin kuka na fashe dashi tareda miqewa maimakon na tafi kaman yanda ya umurceni sai na Nufo Gate din Gadan Gadan ,Da sauri Ammie taja da baya tana share hawayenta ,Daddyma Jada bayan yayi Yana mn kashedida karna shigo Cikin Gidan .

Bansaurareshi ba na kutsa Kai Cikin Gidan Aikam ina saka Qafa Cikin Gidan Masu Gadi sukayo kaina sukayi waje dani Da Qarfin Tsiya๐Ÿ’”๐Ÿ˜ญ.


Mutanen da Ko daga nesa Suka Ganni sai sun Russuna sun gaidani Suna mn biyayya tareda karramani tamkar Uwarsu amma a Halin yanzu suke Jana a qasa Suna Fitar dani daga Gidan Ubana a qasqance...

Kuka nakeyi da iya qarfina hawaye na Zuba a Idanuna yayinda Su suke Ganin Hawayen Kaman wata baqar Abu Abin gwanin Ban qyama


Kuka nake da iya qarfina ina kiran sunayen Su Ammie Amma Kaman tunzurasu nakeyi because muryana yana bala'in Irritating dinsu shiyasa Koda suka Daukeni babu inda suka Direni sai a tsakiyar titi, a cewarsu idan Mota tazo wucewa tabita kaina ,nima a halin yanzu abinda nafi Buqata kenan amma da na tuna da alqawarin da na dauka Sai nayi wuf na miqe Ina Dirzar kuka mai Tsuma hrt a lokacin kam har 'Yan anguwa sun Hadu ana kallon sabon halitta yayinda wasu ke Jifana da duwatsu , A daddafe na Daddafa na nufi inda na parka motata sai a lokacin na tuna da Wai inada Wasu 'Yara Leqasu nayi Allah da ikonsa barci sukei hankali kwance.


Jeeboy da tun da na fito daga mall Dinnan yake biyedani ya la6e a wani Guri yasauraron tattaunawan mu da Umma da kuma irin Wulaqancin da akayi mn a gidan Ubana..










Nayi Gabas๐Ÿ’”๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ





30th novโœ๐Ÿฝ
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
**HAWAN-JINI NA*
~{uwar mijina* ๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._



ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 77_*




Su daddy na komawa ciki Ammie ta fasheda Wani Matsanancin Kuka mai Tsuma rai kukan take tana qarawa Ita kanta bazatace ga musabbabin kukan nata ba.

Cikin Sanyi daddy ya zauna Kusada ita tareda Kamo hannayenta da take Qoqarin Share hawayenta dasu ,A hankali Cikin sanyi yace

"Jeedderh Kukan nan Kuma na menene ?โ€

Fadawa Jikinsa tayi Cikin Kuka take fadin

"Ina tausayawa Wannan Halittar da Alama yana Neman Taimakon mune, Kuma Baiyi kamada Abu mai cutarwaba ,na tabbata da mai cutarwace Bazai barmu muna kallonsa ba tareda Ya Cutarsda mu ba , Don Allah Daddy Ji yanda Mutanen nan Suke Jifan shi sai kace Wanda yayi msu sata ,Ka duba yanda Masu Gadin Gidan nan suke Janshi a qasa a wulaqance , Bamusan Damuwan shiba Bamusan dalilinsa na Zuwa nan ba, Bamu saurare Abinda yake Fada mana ba dukda Kuwa ba Wani fitowa Muryan sa keyi ba ,Amma ya kamata Mu duba Lamarin nan bai dace Mu barshi Cikin wannan Yanayin ba Wlh"

Murmushi mai sauti Daddy yayi tareda Sake Qanqameta Cikin jikinsa a hankali ya Furta

"Ammien Twince , Inaga har yanzu Quruciya ke damunki Shiyasa Kika Gaza gane tsakanin Na Gari da Mugu ,Kin manta Mugu bashida Kamanni Ki tuna da Abinda ya faru Lastweek da wannan ya isheki ishara ,Kinga Share Wannan Maganan Banason Sakejin Wata magana Da ta danganci Wannan Dodon anan wajen"


Dagowa Ammie tayi ta dubeshi Amma ganin yanda ya murtuqe fuska yasa ta sunkuyar dakai a sanyaye

"Kayi Haquri Daddy Inshaallah Bazaka sakejin Nayi wata magana da ta danganci wannan ba ,Kaji "

"Tho " ya fada tareda gyara zamanshi ya dauki remote zai Sauya tasha Har yanzu bai saki fuskar ba.


"Daddy Please Smile naa ,Duk wannan shan Mur din na menene?, ai nace Tuba ko so kake Na Durqusa na ta6a qafafunka ne?

A hankali daddy ya maida dubansa Gareta Murmushi manne a Fuskarsa

" ba komai Jeedateey Hawwa Kulu ta, my CryCry cubbie"

Dariya Ammie tayi tareda kwantar da kanta q kafadarsa

Cikin dariyar tace

"Ka Cika Tsokana Wlh...A kullum idan na kalleka sai ka dawo kaman wani 'dan saurayi"

Shima dariyar yayi Tareda Shafa kanta yace

"Ai dole kice haka ,Tunda Kinga ke da qurciyarki kin Gama Tsofeni Zakiyi mn Wayo kice Kina Ganina Kaman wani Yaro Dallah chan"

"A'ah wlh ba wani nan wani irin Quruciya Gareni Am just 35 fah......"


"AssalamuAlaykum"

Muryan Umma da Hajiya Asiya Sukaji suna Sallama , da sauri Ammie ta daga Kanta dake kafadar Daddy ta maida kallonta garesu Tana mamakin dalilin shigowarsu A Daidai wannan lokacin ,

Zata iya rantsewa da Girman Allah bata ta6a ganin Umma ta shigo Part dinsu ba sai yau .



Umma kuwa Tsayawa tayi a bakin qofa ta kasa Qarasowa Tana Kallon yanda Daddy ke bawa Ammie Kulawa ,ita ko lokacin Quruciyan Ta bata Samu kwatankwacin haka ba ,illa ma Kishiyar da ya qaro mata Tun kan Suyi Shekara da Aurensu....


Da qyar Umma ta kawarda Tunanin da takeyi ta qaraso Sai a yanzu naga Yarinyar dake biye da ita๐Ÿฅบ.


Qarasowa Sukayi suka zauna tareda Gaisawa

Daddy ya dubi Umma yace

"Haleemah Me ya Hadaki da Dodon dazun ne ?"

Cikeda Jin dadin yanda daddy ya Kira diyar tasa da Dodo Umma ta dago Amma Fuskar ta daukeda Damuwa

"Wlh Babu Abinda Mukayi mashi ,inaga Shima Turoshi akayi don Aga bayan mu ,ya kamata Mu dau mataki akanshi kar a samu matsala ,Ya kamata a sanya jami'ai su gaggauta kamashi ko a Fitar dashi daga Wannan yankin Don Zaman sa anan yanada Matuqar hadari"


A tare Ammie da daddy suka ta6e baki ,Don ganin Yanda Umma ke wani zaqewa tana Bada rahoto babu Ko alamar tausayawa a gareta.


Allah shi kyauta abba yace

Yayinda Ammie ta maida dubanta ga Yarinyar dake taredasu

"Wannan kumafa?, daga ina?"


Washe baki hajiya asiya tayi sannan ta fara Raftako masu bayani

"Hhehehh Ai yarinyar wajenace Na kawota ne don ta taya munayferh rainon Yaranta kunga ai Rainon Yara har biyu da wahala...."


Dakatar da ita Ammie tayi da cewa

"Ita ta Gaya mku tana buqatar mai taimako ?"

Hajiya asiya ta girgiza kai ,umma tace

"Amma..."


"Amma me?, Kinsan Munayferh sarai batason 'yan Aiki shiyasa babu ma'aikata a wannan sashen,Idan Ma munada Buqatar mai raino ba Sai kin taimaka mana ba Da tuni Mun Daukosu Ammma kunga Mungode Please.... ba tareda Dogon surutu ba Ku tashi ku tafida ita Mun gode "

Ta fada tana Miqewa ta bar wajen Daddy ma ya miqe yabi bayanta don bashida Abin fada.

Umma da Hajiya Asiya kuwa kallon juna Sukayi taredayub wata munafiqar dariya wanda su kadai sukasan ma'anar Abinsu .


Kai tsaye Dakina Ammie ta nufa tana Kiran sunana don ta Ga na dade a Daki ban fito ba.

Shurun da taji yasa ta fara Duba dakin kakus don dama nafi zama a chan nan ma wayam ,Take hankalinta ya fara tashi ,Ta sake Komawa dakina Cikin tsananin Rudani take Kirana Amma babu Amsa fitowa tayi a Rude tana qwala mn kira don bataga Fitana ba.


Daddy dake Part dinshi ya Fito yana tambayan Lafiya nan ta sanar dashi bataga Munayferh da yaranta ba ,hakan yasa Suka Shiga nemanta a tare ,Amma me?, babu Munayferh babu Alamar ta Hayaniyansu ne ya tada Kakus dake Barci ,itama jin yanayin da Ake Ciki ya rudata Nan take suka nufi part din Umma ko Tana tareda janaan Amma nan ma babu ko mai kamada ita , Wajen Maigadi Suka nufa Wanda ya tabbatar msu da cewar ya Ganni na Fita da mota amma baisan inda Naje ba ,

Sun kira wayana Amma ba'a Dauka kasancewar a Gida nabar wayan , Dukda kuwa sunsan Ina yawan Fita batareda na sanarda kowa ba Amma wannan yafi daga Masu hankali ,

Kasancewar Tunda mukadawo ban ta6a yunqurin Fita daga Gidan ba ,Kullum ina Kulle a daka.... nan take aka Zuba jami'ai aka shiga nemana Babu qaqqautawa.........


***

Jeebril Kuwa Tunda yaji Abinda muka tattauna da Umma Hankalinsa ya tashi ,kuma ya dau aniyyar Tonawa Umma asiri sannan yasan yanda yayi ya maidani Gidan mu ,Amma koda ya shiga Gidan Ya tarar Har an Fara nemana Da ya tuntu6i Abba da maganar ya Bude baki Zaiyi magana sai harshensa ta Lanqwashe Ya kasa Furta komai haka ya koma Gida Batareda ya fada msu Abinda yaji ba .


Ni Kuwa ina barin Unguwar kai tsaye Wani Wuri na nufa inda babu kowa na parka Motata Nasha kuka na Har na qoshi Lokacin sallah nayi na dau Ruwan dake Cikin motar Nayi Alwala tareda Gudanar da sallah Sannan na Cigaba da Kuka ina tuna hawayen da na Gani a idanun Ammie yau da irin Wulaqancin da Daddy yasa akayi mn Batareda Na Sani ba ,dole na koma Gidan ,Kuma dole Su fahimceni Dole Su sauko su daina Ganina a matsayin DoDo.......


Idanuna maida kansu Haseen Har yanzu barcin Sukeyi ,Gabana ne ya Fadi kardai ace kashe mn su akayi ,Saina na tatta6asu naji suna Numfashi sannan na Sauke ajiyan Zuciya.

Cikin sanyi na dauko Hasna na Fara bata Abincin ta don Rabonsu da Abinci Tun da safe ,kuma ko kadan Bana Wasa da Abincinsu Akai Akai ,Abin mamaki kuma shine Cikin Barci Tasha Sosai Shima haka Dukkansu basu bude idanuba , mamaki na shigayi wannan wane irin Barci ne haka ? .......


Saida na tabbata Duk sun qoshi sannan Na kwantar dasu A baya na Juya akalar Motar na koma kabala, Yanzu ma kaman dazun ne Motar taqi Shiga Layin Saida na parka a Wani Guri Sannan na Fito na nufi Unguwar Gadan Gadan.


Amma Abin mamakin da na fara Cin karo dashi shine ya fi Rikitani ,Ganin yanda Ake nemana ana nunawa Mutane Hotona ko sunga wucewata ,6angare daya Kuwa ana Gani na Ake Artawa ,wannan Karon ban Damu ba da jarumta na na tunkari Gidan ban damuda Mutanen dake Kallona ba ,ina Isa Bakin Gate din Masu Gadin dake nan Suka Shiga korani tareda Zabga mn Dorinarsu Irin na Masu Gadi Suma daga Gani zaka Fahimci a tsorace Suke Kawai so Suke Su hanani shiga Gudun Afkuwar Wata 6arnar .


Dukda Zafin dukan da Sukeyi mn na ratsani yana Shiga Har Cikin jikina Amma ban karaya ba Saida Nasan yanda Nayi na ture Wani na Kutsa kai ciki aikam ina shiga Duk suka Taru suka Turoni Waje da Iya qarfinsu Suna Mamakin yanda Jikin mutum yake rufeda Gashi da wasu Abubuwa launin jikin ma babu dadin Gani Amma da an ta6a fatar sai suji Wani irin taushi kaman katifa.


Daqyar suka samu na bar Unguwan bayan sun hadani da 'yan sanda Ba qaramin wulaqanci nasha a Wajen Mutanen nan ba ,Har cewa Suke Idan na sake dawowa Layin kasheni zasuyi Don sun fara zargina da 6atar Diyar JY don da zuwana Aka nemeta aka rasa .....


Da qyar na samu na bar Unguwar Jiki a tsame saboda Dukan da nasha Wajen Masu Gadi da 'yan sanda Kuka sosai nakeyi kaman Raina zai bar Jikina Saida Nayi tafiya mai nisa kafin na Isa inda na Parka motata , Sa'ata daya babu mutane anan ....


A daddafe na Rankaya na bude Qofar motar ,Gabana ne ya Fadi Ganin mutum Cikin motar a mazaunin driver ya kife kansa bisa stirring.



Cikin Muryan Dodonnin da Ake Jin muryan nawa na Furta.


"Kai...." Tareda bubbuga Kofar motar.

Dago jajayen idanunsa yayi Wanda suka rikide Suka sauya launi Zuwa launin jaaaa Ga hawayen dake bin Fuskarsa.


Cikeda Tsoro na Waro idanu Cikin Mummunar muryan nan Cikin Cushewar Numfashi Nace

"Jibril Ya akayi ka Shigo Cikin Mota ta?"

Share hawayen sa yayi Yaja Numfashi tareda Girgiza Kai Ya bude baki Zaiyi magana sai Kuka ya Kufce masa ,Nima nan take wani irin Kukan Ya qwace mn .


Cikin Jarumta ya share nasa hawayen kai ya rink'a juyawa jikin cushewar numfashi da zufa dake tsatstsafo mishi,
hannun na rawa ya Riqo hannuna Ya Shigar daini Cikin motar ya zaunar dani Kusada Driver Seat Shima yayi Mamakin Jin Taushin Da fatata tayi bayan A zahiri Fatar Rough take kuma mamaye da Gashi Duk yanda kakai da iya Gane Jinsi bazaka iya ganeni macece Ni ba ko Namiji Harta kayan dake Jikina tamkar Gashi yake ,

hawaye ke zuba a idanuna tamkar an bud'e pompo idanuna da Suke Ja da blue Suka sake Munanta kamar zasu fad'o k'asa ina kuka harda sheshshek'a, bai hanani ba
ido ya kuma tsura mn yana kallon yanda Baqaqen hawaye Ke Fita daga Cikin idanun nawa.


Ganin banida niyyar daina Kukan yasa yaja motar a kasalance ya bar Unguwar dani ,ban Tambayeshi inda zai kaini ba haka kuma bai Gaya mn Asalin inda zai kaini ba , nima ban damu ba Don A halin yanzu na barwa Allah Komai yayi yanda yakeso Dani, na Amince Wannan yana daga Cikin qundin qaddaratane....


A Bakin Wata qatuwar Gida ya parka ya bude back seat ya dauko su wa'enda da Har yanzu barci Sukeyi ya saqalasu a Kafada Sannan ya zagayo ya Bude mn .


Muka shiga Ciki ,Nayi Mamakin Ganin yanda Mutanen Gidan basu kyamaceni ba baresu Korani kaman yanda sauran Mutanen Sukeyi .


Mahaifiyarsa ce kawai da Qanwarsa ke zaune a Gidan kuma da Alama ya sanar dasu Abindake Faruwa don Yanda naga Suna mn sannu da Addu'an Allah ya Fitar dani daga Sharrin Masu Sharri ,Sosai hankali na ya kwanta dasu amma ban ski jiki dasu ba Saboda Tunani da Mamakin Abinda ya farudani

Please Login or Register in order to submit comment