Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonta , Ta wani Tsofe ta qauje ta zama Qashi da rai ga yanda Fuskarta ta wani Kwa6e sai ta dada Munanta , inba don Nice na gaya masa haka ba da ya rantse qaryane.


"How Comes?, ya akayi ta dawo hakan ?, taya Akayi ta dawo wajenki Am...confuse...."

Magana Yakeyi yana Riqe hannayena Cikin neman Qarin bayani.

Ganin abin nasa bana qarewa bane ya wani rude ya shiga Trauma yasana Kamo hannayensa , na Fuskanceshi, A hankali nayi locking din la66enmu waje daya

Take jikinsa ya Mutu , Yayi baya Ya jingina da Seeat Nima na Bishi tareda Mannewa a Jikinsa Na zura hannu Cikin Rigar Uniform dindake Jikinsa Na fara shafa Kirjinsa ,Gaba daya na susuta shi na mantar dashi komai mun manta Da wata mai rai a Cikin motar.

Saida na tabbatar ya Fice a hayyacinsa hankalinsa yakai qololuwa a tashi sannnan na cire bakina daga nashi ina kallon fuskarsa daya yi ja ya koma Fuskar tausayi ,Tuni ya manta da maganar wata rabi.

A zuciyata na Furta _Jarababbe_

A fili kuwa cewa nayi ya dawo Inda nake zaune naja Motar ganin Kamar bazzai iya tuqin ba, Amma ga mamakina yace min na zauna kawai zai iya.


Abinda ban saniba , ya shirya Rama Muguntar da nayi masa ne ...
































Nayi gabasπŸšΆπŸ»β€β™€οΈ
[12/31/2020, 6:03 PM] Fahnaaan❣️: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

Na
🀍 *Fahnaan*🀍

Β©πŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…...



*Chapter 96*


A sanyaye Na kwantar dakai Bisa Kafadarsa Na cigaba da Kallon titi ,gabaki 'dayan mu babu wanda Ya sake Furta wata magana .


Saida Muka kama Hanyar Kabala ya Juya Ya nufi hanyar Unguwar sarki ,Da mamaki na dago na dubeshi ,amma ganin yanda ya murtuqe Fuska Yasa babu Shiri na hadiye Tambayata

A Gaban Wani Qaton Gida y Parka Gidan babba ne sosai kuma Tana da fadi Ta waje Haka zan Iya rantsewa ban Ta6a ganin Qaton Gida irin wannan Ba Domin duk yanda Zan misalta mku Girman Gidan Bazai Misaltu ba, Harta Gate Din Gidan qato ne sosai ,Motarsa na Tsayuwa Gate din Ya wangale Muka shiga Daga Ciki, mamaki ya cikani har ya kasa 6oyewa A fuska ta ,Yana Lura da haka amma ya share ,Muna Fitowa daga Motar masu Gadi Suka Gaishe mu.


Daga Kaina Nayi na dubi tsayin Gidan da kuma Tsarin Gidan , Ya burgeni sosai Amma da Alama Gidan ba Na mutum daya bane , Domin kuwa yana Dauke ne Da 6angarori har shida A saman Tsakiyan Dogon Ginin Rubutu ne kaman haka A J I S H H sannan aKAYI rubutu kaman Haka *ΰ€‘ΰ€Ήΰ₯‹ΰ₯‹ΰ₯€* a qasa Ta6e baki nayi tunda ba Gane yaren Nayi ba .

Ji nayi ya kamo hannuna ya Riqe Muka Shige Side dinda yafi kowane Haduwa a ciki ,Tsaruwansa ma Na daban ne harta Girmansa da sauran Dabanne , Da ido nake Rakashi batareda na Furta wata magana Ba .


Ban tashi Tsinkewa Da kyawu da haduwan Gidan ba saida muka shiga Sitting Room , qaton Parlor ne wanda tsantsar Girmanshi yasa Aka Rabashi Biyu Dukkanninsu shaqe da Kayan Furniture na Alfarma Komai na dakin Royal Blue ne da Golden Harta Royal Chairs dindake Jere A dakin Tsarin Gwanin ban sha'awa , Bayyana Mku yanda haduwa da tsarin Gidan yake 6ata lokaci ne Don haka a taqaice Gidan ya Hadu Haka kuma ya tsaru iya tsaruwa.


Saida ya kaini na Zagaya ko'ina na gidan sai faman Santin Gidan nake, Shi kou Lo kulani baiyi ba haka kuma yaqi sakin Fuska .


Sai da ya zaga dani Lungu da saqo na Gidan kafin ya dawo dani Parlor ,Ya zauna Bisa Kujera tareda Sauke Ajiyan numfashi.

Nima zama nayi Na Duba Ma'ajin Remote na Dauko na kunna TV kasancewar Inverter a kunne Yake.


Sai a Lokacin ya dago ya dubeni ,Kaman zaiyi magana Sai kuma ya fasa.


"Raja whose house is this?"

Shuru yayi bai amsani ba hakan ya taimaka wurin qona mn rai, Tsaki naja Tareda miqewa Ina turo baki

"Ni da kasan Bazakayi Mn magana ba Meye na kawo ni nan? ,Ni ka tashi ka kaini Gida ma na fasa zuwa yawon , kaji?"

Na qarashe a raunane kaman zayi kuka tareda da Riqe hannayenshi.


Wani irin Kallo ya watsa Mn wanda Saida 'yan hanjin Cikina sukayi Tsuwwa ,Gabana ya shiga Faduwa Da sauri na dafe zuciyata da naji ta fara mn bqrazana.


"Tell me ,Taya akayi InnaRabi ta dawo wajenki ,Meyasa Image dinta ya chanja?, Explain......!"


Sakin hannunsa Nayi tareda Jada baya Ina Watsa Masa wata Ubar Harara batareda na furta wata magana ba Nayi hanyar fita ,saida nakai wurin qofar sannan Na dakata ina duban qofar domin Ni bansan Taya zanyi ta bude ba ,Babu shiri na dawo wajensa Yana zaune Sai kallona yake ta Qasan Ido.

"Rajaa Please Open The door , idan mun dade Ammie zata zargi wani abu"…


"We're spending the night here"

Ya fada kaman na Tursasashi

"What....!"

"Yep"

"Maf....maf karana ....krypya (Please Sorry) zan Gaya maka Komai ,don Allah ka bude Mn qofa"

Na qarashe hawaye na Malala a idanuna.

"You better swallow that tears cus it won't help"

Ya fada in a husky voice ,

'Hadiye kukan nayi Na dawo kusa dashi na zauna Ina shessheqa.


"Am listening"

"Please Ka kaini Gida , Zan Fada maka Later"

Kallona Yayi a Tsanake , sai yanzu ya Tuna abinda nayi mata A mota, hannunsa ya dora Bisa Kafaduna Ya qura mn Ido ,Saida Ya tabbata Saqon ya Yake son Isarwa ya Isa har inda yake Buqata , sannan Ya Kwantar dani bisa Dogon Kujeran da yake zaune ,jiki a sanyaye Na Miqe Zaune Ina Kallonsa a raunane Gabaki daya Jikina ya mutu ,Cikin Rashin samun madafa Na Fara Kuka ina Tambayansa me yake shirinyi?, bai tankani ba Sai harshen sa ya da yasa yana Lashe Hawayen dake Kwaranya a Idanunta Cikin wani irin salo take Wasan ya fara sauya Salo ,Cikeda Mugunta yake Juyata ,Baiyi mamakin hadin kan da ta bashi ba , domin kuwa Tun farko saida ya isarda saqo kuma ya tabbata Tasirinsa ne ya bada hadin kai wajen zafafa Abinda yakeyi , Saida ya tabbata Hankalinta ya Gushe ,ya kai Qololuwa a Tashi sannan Ya qyaleta ya Koma gefe yana Sauke numfashi ,yakai Almost 23min kafin ya saita Kansa Kasancewar ya dade Bai tsinci kansa a irin wannan Yanayi ba .


Ita Kuwa sabon yanayin da tsinci kanta a Ciki ne yasa Ta kasa koda qwaqqwaran Motsi , bakajin komai Sai Ajiyan zuciyar da take saukewa Akai akai .

Cikeda Mugunta ya iso gareta yana Qare mata kallo, taso ta bashi tausayi Kasancewar ta baquwa a wannan Fannin amma Son samun Bayanai daga gareta ya Hanashi tausaya mata.

Juyowa yayi yana Qare mata kallo , Sosai Ta fita hayyacinta Sai faman Saukan numfashi takeyi idanunta a lumshe.


Cikeda natsuwa ya dagota , ware idanunta ta dorasu a kansa , Tana Ganinshi ta saki Kuka Mai ban tausayi , Har cikin ransa yana Jin zafin Kukan da takeyi Amma ya qosa yaji Daga gareta.


"Munayferh"

Ya kirani a kausashe .

Da sauri na ware fararen idanuna wa'enda suka Rikide Suka Koma tamkar garwashi ,Jin sunan da ya Ambata sai ya Kuma dimautani , Bai damu ba ya cigaba

"Banason Taurin kai Just tell me "

Kuka na fashe dashi , wato bai damu da yanayin da ya barni ba shi Burinsa bau wuce ya samu bayanai ba, Cikin kuka na fada Qirjinsa jikinarawa da na Budi baki zanyi magana sai naji Numfashina fuzga.


Cikin sanyi ya 6ambareni daga jikinsa Yana Auna mn wani irin kallo ,Chan qasan zuciyarsa Kuwa tausayina ne Fam a cikinta.


"Tunda bakida niyyar gaya Mn Lemme Go , See you tomorrow ,Babu Abinda babu a Gidan nan So chill...."

"Ple..ase ka ...da wo zan gaya maka"


Murmushin mugunta yayi sannan ya dawo ya zauna Yana Qare mn kallo , Cikin kuka na zayyana Masa Komai tun daga Ranar da na dauketa da Abinda nake shaqa mata , Da kuma taimakon da tayi mn Da Muguntar da tayi ta aikatawa ciki harda Maidani Wa r mongern da tayi , Haka kuma Harta Abinda na Aikatawa Umma Saida na Gaya Mashi …


Ya tausaya Mn sosai Kuma ya sha Alwashin hukunta InnaRabi bisa ga laifin da ta Aikata ,

Batareda Yayi mata Komai ba Cikin ya Dawo da ita Cikin hayyacin ta sannan Sukayi wanka suka baro Gidan ,daga nan kai tsaye Station muka nufa Ya Maka InnaRabi a Cell .

Daga nan Muka nufi Gidan janaan don dauko yaran , Amma da isar mu muka iske Haseen a Bakin Gate yayi shuru Fuskar nan a Kumbure alamar halin ya motsa .

Da sauri na qarasa Ina tambayansa Lafiya ,Bai ce mn komai ba Sai faman Sauke Numfashin da yakeyi , Aaryaan ne yaja hannunsa Muka Nufi ciki , da isar mu sai muka iske Hasnah rungume da sadeeq wanda yayi barci Fuskarsa da Alamar busasshen hawaye alamar yasha Kuka.

A rude na isa garesu ina Tambayan Lafiya?, meyasa nagansu a haka ,Kuma meya 6ayawa Haseen rai har Ya zauna Wajen gate shi daya.

Janaan ce tayi mn bayani wai Hasnah da Aabaan (danta) ne sukeyi msa Gorin Sun girmeshi da Awanni uku shine yayi zuciya yabar wajen.

Murmushi nayi nace

"Wa'ennan Fa me ya Sasu kuka?"

"Rashin Dawowanku da wuri Kunje kaman Bazaku dawo ba"

Dariya nayi ,Dai dai lokacin da junayd ya shigo Daganan Muka cigaba da hira , Cikin Hikima Aaryaan yaja Junayd waje yayi masa bayanin Abinda na Gaya mshi dazun Dangane da InnaRabi, kasancewar a hannunshi case din Yake dama Daga nan Suka tattauna Akai suka samo mafita batareda na sani ba.


Saida yamma liqis 5:41pm muka baro Gidan ,Muka iso namu Gidan .


Ya lura tunda muka baro Gidan Ban yarda mun hada ido dashi ba ,ya dauka Fushi nayi sbd haka yana Parka motarsa ya Budewa Yaran Don su fita har sun Fita Suka dawo na dubesu ina tambayan lafiya suka dawo ,cewa sukayi babu kowa a Gidan .

Na dauka shirmene irin nasu shiyasa na Bude msu Kofar suka Shige muka zauna Shuru sadeeq ne ya katse mana Shurun .


"You guys, did you all notice we're all wearing Blue and black?"


"Woww one Cute family" cewar hasnah


Dariya nayi sosai ,Nace

"We're the cutest family in the world"

Aaryaan yayi murmushi, ganin na dan saki raina Ya juyo ya kalleni yace


"Am very Sorry Sulthy"


Nimq kallonsa nayi

"For what?"


"For all that happens some Past hours"

Ya fada a raunane ,Hannu na aza kan Lips dinaa


"Shhhhh....please ka daina bani haquri , Ka tantanci ka mn komai Ciki harda abinda ya wuce hakn Ma ,komai nawa naka ne , Idan kana Bani haquri sai naji kaman Ban chantanci Na zamo abokiyar Rayuwanka ba,ni ya kamata na baka haquri Son Boye maka da nayi fatan zaka gafarceni.....dan Bude mn qofar"


Na qarashe Da son Share maganar .


Murmushi yayi Yana jin sanyi na ratsashi da zai iya da ya furta mn maganar da zata sanyaya Zuciyata kaman yanda Na sanyaya masa nasa ,Amma idon yaran yasa ya aika saqon ta ido kawai.


Bude qofar ya fito tareda Zagayowa ya Bude Mn nima harda dan Russunawa , yana Budewa na zura qafa da niyyar fita wasu Baqaqen Motoci hudu suka danno kai cikin harabar Gidan , Hakan yasa na Kasa Fitowa na Bi motocin da idanu har suka parka Shima kasa Rufe Motar yayi ya qurawa motocin Ido.


Motar farko aka fara budewa Abdool ne da Abba da Aunty salma suka fito a motar sannan mota ta biyu Ameer Da Ameerah Da kakus,Mota ta uku driver ya fara Fitowa sannan Ya zaga ya bude Msu Ammie ce ta fara Fitowa tana Amsa waya sannan Daddy ya fito ta dayan 6angaren Shima amsa wayan Yakeyi ,Motar qarshe Kuwa Umma ce da qawarta Hajiya Asiya Wanda a halin yanzu siffarsu ta Koma Abar tausayi barin ma umma da Manyan Boils Suka firfito mata fatarta ta dame In ba donnice na aikata hakan ba ba ganesu zanyi ba.


Take gabana ya shiga Dukan Uku uku, jikina ya fara kyarma Tsoro da fargaban abinda na Aikata da abinda ke shirin faruwa suka dirar mn.





















Nayi gabasπŸšΆπŸ»β€β™€οΈ
[1/1, 5:08 PM] Fahnaaan❣️: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

Na
🀍 *Fahnaan*🀍

Β©πŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…...



*Chapter 97*



Gaba daya Jikina A sanyaye yake ,Tunani , Tsoro da Fargaba Duk suka Cika zuciyata , Sai zare idanu nake kamar kulya a lungu jiki na mazari.

Shima Su yake kallo baki sake Ya kasa Sakin Qofar Motar ni kuma na kasa Fita .


Sanin Halin Ammie idan na bari ta gama wayan Da takeyi har ta Ganmu Kashina ya bushe , Shiyasa na Fice kaman Wata Munafuqah na Ra6a Gefensa Da niyyar zamewa kafin ta farga Dani.

"Dawo Munayferh"


Muryan Ammie naji Cikin kausashi,ban Amsa mata ba yi nayi kamar banji ba Haka na cigaba da tafiyata batareda na waiwayo ba.

"Munayferh are you deaf!"

Muryan Abbie naji Cikin daka tsawa ,Abinda ban ta6aji ba daga gareshi tsawon shekarun da na dauka taredashi, Bani kadai na tsorata da wannan sabon Al'amari ba Harta Aaryaan ,Ammie ,Abbie ,kakus da Umma dake wajen Domin kuwa tuni sauran suka Nufi cagin su..


Jiki na 6ari na Dawo har ina Hade hanya ,Na iso har gabansu Tareda Sunkuyar dakai.


"Ina Kukaje?"
Daddy ya tambayeni yana Dubana.


"Ehmmm.....daddy Munje Duba InnaRabi ne"


Aaryaan ya bashi Amsa.


"InnaRabi kuma?"

Duk suka hada baki cikeda mamaki da razana.

Shi kuwq Aaryaan ya fadi hakan ne Gudun Kar su zargi wani abu a Tsakani.


"Ina Rabin take?"

Cewar daddy

"Tana Station ..... Take ya fada Msu abinda ya faru da kuma Labarin da na bashi harda hukuncin da ya yanke a Kanta ya qara da cewa

Yanzu haka so nake ta samu lawyern da zai tsaya mata A yanke mata hukuncin da ta dace da ita Kasancewar tuni mun shigar da qararar Tun tuni kawai Tadota za'ayi.


Gabaki dayansu Shuru sukayi suna Sake nazarin Kalamansa Ji suke tamkar a Mafarki ,Zasuso suga InnaRabi suga yanda Munayferh ta sauya mata Kamannin , hakaKuma suna mamakin Hali irin na Rabi da har zata so qanin mijinta ta kuma maida Diyarsa Mafadaciya Akan wane dalili?, sun rasa gane Ribarta nayin haka Ai dama masu iya magana sunce Duk Muguntar mugu idan Bai Cuci kansa ba bai cika mugu ba.



Ganin sunyi shuru jikinsu a sanyaye yasa Ya danyi gyaran Murya yace


"Kuyi haquri ,Munayferh ta aikata hakan ne a Bisa Kuskure bayinta bane , Abba daddy ina Roqonku don Allah kar ku bari Wannan Abin yasa muku tausayinta a Cikin rayukanku yasa Ku hanani Aiwatar da nawa aikin....please Ku gafarceni idan na furta ba daidai ba"


Ya qarashe maganar da hade hannayensa waje Daya.


Daddy yayi qasaitaccen Murmush yace

"Ka kwantar da hankalinka Aaryaan ,Wannan Maganar ba ta tsaye bane zaifi kyau Idan Mun sami zama ,Don yanzu Haka ma daga asibiti muke munje duba Mahaifiyarka Sai Muka tarar da qawarta dukkanninsu Suna cikin hali na matsanancin Jinya A iya gwajin Likitocin sunce basuga komai ba ..... Shine Mahaifiyarka ta gaya mana duk Abinda ta aikata ta kuma bayyana mana cewa munayferh ce kadai zata iya dawo da su yanda suke domin itace ta maidasu hakan "

Dafe qirji nayi da qarfi na furta

"Ni?....Ni kuma?....ni wlh bani bace bata daiji dakyau ba " ..

"Dalla Rufema Mutane baki ,Kafin Mu iso nan wurin saida Mukayi ratifying komai , which means idan kikayi denying kina Nufin qarya muke"

Cewar ammie

"No ya kamata Mubita a hankali Don kar tasake Rikide mana , Yanzu dai mu shiga daga Ciki"


Gabaki dayan Mu haka muka rankaya Zuwa Parlon Abba Sun sha Wahala kafin su shawo kaina Na gaya msu gaskiya nice na aikata hakan babu kunya jaddada musu bazan Maidasu yanda suke ba sai sun sha wuya Garama qawar umman ta dandani Taskona na har tsawon shekaru biyar Gashin Kuma har yanzu Tsirowa Suke Tun tana askewa har abin yaci qarfinta yanzu ko dodon da ta maidani yafita kyawu a Ido.


Umma Kuwa wasu manya manyan Quraje ne suka Fito mata wa'enda Girmansa Ya Wuce misali , sun Fito mata a ko'ina Na jikinta Masu Qarfin tsiya , babu damar fasawa domin sbd qarfinshi idan ba kyakkyawan sani Kayi mata ba sai ka rantse ba ita bace.


Da qyar Abba ya shawo kaina Da rarrashi na Amince zan Maidasu yanda suke , take sukasa na rubuta msu abinda ake buqata , nan take akaje Siyowa ,Sannan Aka maida haj iya Asiya Gidanta ,Umma kuma tausayinta Yasa Abba ya dawo da ita. ....kuma ya dada Qarfafawa Aaryaan qwiwa akan hukunta InnaRabi daidaida Laifinta ,Ana siyo Abubuwan da na Rubutawa umma aka farayi mata Amfani dasu akamar yanda nayi msu bayani.

Bayan Komai ya lafa Kowa ya koma Makwancinsa Ammie tace bata yarda na Shigar mata daki ba ,Nabi mijina Kar na Aikata msu abin kunya a Gida bayan munada namu Gidan.

Dukda naji dadin hkan amma yanda ta shammacemu ya dansa naji babu dadi Atleast ya kamata ta zaunar dani tayi mn Nasihar da ta saba , Ko kuma shawarwari , Domin a Halin yanzu su nafi buqata Na lura Ta hau dokin Fushi ne ,Amma Nasan Very soon zata sauko Shiyasa ma nayita roqonta amma fir taqi amincewa Da na cika mata kunne ma Kulle qofar tayi gabaki daya ta barni a waje.


Shi kuwa aaryaan wani irin dadine ya ziyarceshi ji yake kaman Ya bawa aammie kyautar duniyar nan , FarinCikinsa ya kasa 6oyuwa sai faman Murmushi yakeyi yana wasa haqora duk ban kura dashi ba koda mukaje Don muyiwa Su abba Sallama Turqunewa nayi nace nifa a nan zan Kwana da take aunty salma ta koroni wai bazanzo na takura msu ba.


Babu yanda na iya haka nan nabishi muka tafi a Yaran sai Murna sukeyi zasu koma sabon Gida.

Banda hayaniyansu Babu abinda kakeji Ni kiwa shuru nayi ina saqe saqe Cikin raina har muka iso Gidan Da mukazo dazun Wannan Karon mai gadi ne ya bude mana Qofar kasancewar Remote din baya Kusa.


Muna Shiga yaran suka Shiga santin Wurin Amma ni babu Uhmm bare Uhmmmm Sai kallo, Shima ganin nayi shuru yasashi Yin shuru .

Cikin qanqanin Lokaci ya nuna mana Ko'ina Na gidan lurada yanda nake wani cin magani yasa Yacewa yaran Sujesuyi wasa a dakinsu da murna suka tafi in kuwa na samu waje na zauna bisa daya daga cikin Royal chairs dindake Shaqe a palon.

Cikin sanyi ya kamo hannayena Ya qura mn ido , yanajin sonta na Shiga kowane kafa na jikinsa.


Ni kuwa gefe na kawar dakaina tareda Qoqarin qwace Riqon da yayi mn.


"Please sulthy why all these bakida Lfy ne?, banajin dadin ganinnki a haka"

Nima a sanyayen nace

''Babu komai fa ,i just lost my apatite..."

"On what?"

Shuru nayi masa hakan yasa yA GANE maganarce bana sonyi , Shima ya miqe ya Nufi inda yaransa suke Suka cigaba da Shirmensu Ina kallo.


Da kansa ya shiga kitchen ya hada mana Dinner , Ya hada mana Abinci mara nauyi , Yaran na tayasa Wanke plates don sunyi qura .


Cikin qanqanin lokaci sukayi kacha kacha da Kitchen din ,Ni kuwa na samu yanda nakeso Wuri na samu na mimmiqe qafafu Tareda kunna Kallo Dama chan Dole kesani Aiki Cuz idan banyi ba babu mai Tayani .


Suna Gamawa suka jera a dinning Lokacin ana Kiran sallar Esha'i don haka ya kwashi mazan suka Nufi Masallaci .


Ina ganin Ya fita naje na Gyara Kitchen din na Kwashe tarkacen Da suka 6ata da kuma plates dinda suka fasa a qasa na Share kitchen din Nayi mopping dinshi Na saka Turare .


Na fito nayi wanka na saka wasu Arnayen Kaya tareda Feshe jikina Da humra da turare masu Sanyin qamshi ,ita ma hasnah na Shiryata cikin Pink pajamas.


Sannan Muka dawo parlor muka zauna Muna kallon Cartoons basu wani dade ba Suka dawo, Duk muka rankaya don bawa Cikin mu haqqinsa.


Tunda Ya dawo nake lurada yanda yake wani satan kallona ,tamkar yau ya fara Ganina ina lura dashi Amma sai nayi kaman Ban Gani ba na cigaba Da biyewa Shashanin sn har muka Gama Na raka yaran Dakinsu nayi msu Addu'ar barci sannan Na koma daki inda na barshi.


Yana nan zaune kan Gado ya dafe kansa ,Qamshin turaren da ya shaqa ne ya tabbatar masa da na iso wurin ,A raunane ya Dago ya dubeni da Rinannun Idanunsa wa'enda suka fara sauya launi.

Murmushi nayi mai sauti tareda Kwantar da kaina Bisa qirjinsa Ina sauke ajiya zuciya.


"Meree raajaa(My King) ka iya Girki fa sosai , kunne na kaman zasu Tsinke don dadi , Kaga yanzu na huta Tunda inada kai sai ka zame mana Cooku a gidan ko ba haka ba Daddyn Humdah" .

Murmushinsa Mai qayatarwa ya bayyana a fuskarsa, ya kamo hannuna da hannunsa daya kana yasa dayan hannun ya gyara mn Gashina da suka barbazun Mun a Fuska.


"Sulthy kin san Allah ni har matawa nake wai inada wata diya wai Humdah"


"What!....."

"Yeah ....cus Mummynta ta haramta mn ita"

Dagowa nayi daga kwancen da nayi akirjinsa nace

"Raajaa, Please in roqi wata alfarma a gareka?"


"Menene wannan Alfarman ,Fada mn Komenene Nayi mki alqawarin Yi mki shi"


"Don Allah inaso Humdah ta dawo wajen mu da zama Banajin Dadin Ganin Jininka a wani Gidan a matsayin Agolah ,Hakan na Qona mn rai matuqa"


Qureni yayi da idanu yana sake nazarin Kalamai na ,CikinnSanyi ya Saki hannuna hadida sake Gyara mn gashin da ya baje A fuskata.


"Thanks sulthy nima na ta6a tunanin yin hakan ,Na ta6ayiwa Abba maganar Amma yace na bar mata ita har ta sami nata diyar , Amma yanzu Alhamdulillah tunda ta haifi nata, na gode da kika sake tunasar dani ,Tunda next week zasu Dawo Gidan sai na bari sai sun dawo din"

"Nan Gidan zasu dawo?"


"Eh manah ,Bakiga Different buildings bane?, da Rubutu a sama?, Rubutun sama Farkon Sunayen Mutanen dake gidan ne (AJISHH), A-Aaryaan ,J-Junayd , I -isma'il ,S- Saleem, H-Hilaal ,H-Hydar ,Ruburtun qasan Kuma yana nufin Ma'anar ajishh a yaren hindi wato *Royal*....."


"Wow Hadinkan ku da zumuncinku yasa nake qara sonku, Allah ya qara hada mana kawunanku"

Da Ameen ya Amsa .

Na sake Kwantar dakaina Bisa Qirjinsa Inayi masa yawo da 'yar yatsa Ta a qirjinsa wanda hakan ya fara tsumashi Cikin wani irin yanayi mai wuyan Misaltawa ,Ganin saqon da na fara tura masa ya fara isa har inda nake buqata yasa na fara magana Cikin wata irin Murya mai sanyi wanda ni kaina bansan inada ita ba.

"Raajaa, kasan Yanda zuciya ta ke bugawa Inda kayi nesa dani Kuwa?,....Rashinka a kusada ni shine ya haddasa Mn Ciwon zuciya ,Sonka ya mamayeni ta inda banzata ba , Sonka ya Zame mn Rayuwa Wanda bazan iya Numfashi bataredashi ba ,Saboda bansan Lokacin da ta shigeni ba😭 , .Aap Meri zandagi mera pyar (you're the love of my life) ,Tum mere zandagi (kaine rayuwata) , zuciyata jaririyace Wacce bata san komai ba akan so ko nace tamkar qwai take, da zarar wani abu ya ta6eta Fashewa zaatayi ,na baka amanar Zuciyata mijinah dan Kaine kadai ka tanchachi Ka zamo Mamallakinta na halak malak , zuciyata bazata iya jure Rauni akanka Ba da soyayyarka nake rayuwa da soyayyarka zan Mutu, Don Allah ka Riqeni amanah "



Na qarashe da sharar hawaye, Tausayina Hadida Sanyi da dadin Maganganuna sukasa ya Rungumeni Cikeda Jin dadi ya shiga rarrashina hadida bani baki tareda jaddadamin Da Nice kadai a Rayuwansa Kuma ya yarda ya Amince tunda nace shi zai riqeni amana kaman yanda na Buqata fiyeda yanda Na roqa haka dai ya Cigaba da rarrashi .

Sosai maganuna Suka saki cikin matsanancin farinciki Tareda jefe Zuciyarsa Cikin wani irin shauqi , Bai ta6a tunanin akwai Ranar da kunnuwansa zasu Jiyo masa maganganu masu Dadi da sanyi Daga Munayferh ba ,Cikeda shauqi ya sake qanqameta Cikin jikinsa Yana jin saukan ajiyar Zuciyata.

. A wannan Daren munayferh ta Nunawa jarumin mijinta tsananin kewarsa datayi ,Haka shima Sun Farantawa Juna rai fiyeda Da Tunanin mai Karatu ,Domin ko zan misalta mku Farincikin Da suka Tsinci kansa A ciki 6ata chargi ne ,Ko wacce ta misalta wannan FarinCikin cikin Zuciyarta.


Koda Asuba Aaryaan na idar da sallah ya koma gado ,don Gajiyar da ya kwaso jiyah.


Ni kuwa ina Ganin ya samu Barci na zare kaina

Please Login or Register in order to submit comment