Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ,Shiyasa ya kasa koda dagowa ya kalleni ne, har na Fice.


Umma kuwa Ganin hama yasa ta Gasgata Zatonta akan Abinda taji A take Zuciyar ta tafara Bugawa ,Jikinta ya dau Rawa Tunowa da tayi Zan iya samun Cikin 'danta ako wani lokaci fa.


โ˜…

Ni kuwa ina Fita ban zarce koina ba Sai Part dn Ammie na , Fadawa jikinta nayi Cikin Matsanancin kuka


Dagoni tayi Cikin mamakin Ganina tace

"Ya dai?, Me kika zoyi anan kuma"


Qara Shigewa jikinta nayi cikin Kuka nake fadin "Ammi Ba'a sona A Gidan Nan,Ammi ayau Abba yayi mn fada,Ammie Don Allah ki Gayawa Abba Ya kashe Aurennan Bazan iya ba, Na gaji Wlh bazan iya ba, zai Kashe ni , Wayyo Ammie dan Allah kiyi magana mana"


Tureni Ammie tayi tana Fadin

"Dallah Dagani Shashashar banza, Dan Abban naku yayi mki Fada shine kike wannan Uban kukan?, koda yake b laifinki bane laifinsa ne , ya dau Son Duniya ya Dora kainki Bayason Ganin 6acin Ranki, gaba daya ya 6ata ki , Gashi Tunba'a kai ko ina ba Har kin fara Gunduranshi ,Wai tsaya ma Me kikazoyi A Gidana?"


Ban bata Amsa ba na Miqe na fara Takawa na nufi Hanyar Dakin Abdool ina fadin


"Ammie nah, haka zakice ko?, YaaAary zai kasheni ,Umma na Zagina, Abba na mn fada ,Ammie bakice komai ba....Ammie kema baki sona ko?, Abdool ina kake , Kai kadai kake Sona, Abdool Zo kaji Abinda Su YaaAary suka mn ,Su Abba sun mn taron dangi Sun zazzageni,Tweeny ina kake " Na Qarshe magana Cikin kuka lokacin da na isa Kofar dakin Abdool din.



Sai yanzu Ammie ta lura da yanayin TafiYata Cikin Kulawa tace

"Duk me hakawo Surutan nan ne?Ina kika ta6a ganin Uwa ta haifi 'yarta Tace bata sonta, kuma Abdool ya tafi makaranta Ko kin manta yau Monday?, Sannan kuma Meyasa naga Tafiyarki ta Sauya?"


Cikin Masifa nace

"Ammie babu Ruwan ki ,ko kin Sani Babu Abinda Zakiyi Akai! ,Ammie bakya Sona kin tsane ni" na fada tareda Fashewa da wani irin matsanancin kuka mai Tsuma zuciya.


Ganin haka Ammie yasa ta Gano matsalar 'Yar ta ta ,Takowa tayi ta Riqo hannuna Tana cewa

"Toh Sarkin kuka wayace mki bana Sonki ,Muje kiyi Wanka Sai kici Abinci kafin Ku tafi Zakifi jin dadin jikinki"


~Kodai Ammie ta Gane Abinda ya farune~ na fada A Zuciya ta

A fili kuwa kwace hannuna Nayi Cikin Turo baki hawaye na Zuba daga Idanuna nace

"Nifa tafiyata qalau, "

"Nasani Muje ki Watsa Ruwa Zaki fi jin dadin Jikinki"

A kunyace nabi bayanta ,ina tafiya a waware tareda Dingisawa ,Idanu fal da kwalla.


Kai tsaye bathroom Ammie ta Shiga ta hada mn Ruwan Zafi Kunshe da Sinadaran Gyaran jiki kalakala, Sannan ta dawo ta iskeni a Dakinta na hada kai da Gyiwa ina Rusar kuka tace Na shiga nayi Wanka, Wankan nayi kuma Sosai naji dadin Jikina

Ina fitowa ta kamo hannuna Cikin Kulawa datsantsar tausayi irin na uwa da 'ya ta Zaunar dani Bisa Lallausar katifanta cikin kulawa tace

"Kiyi Haquri Munayferh ki share Hawayen Ki, ki bar kukan nan kinji Bari na hada mki Abin kari nasan baki karya ba,daga nan Sai ki kwanta Ki huta"


Ta fada tareda miqewa


Dakatar da ita nayi da cewa "A'ah ammie ni A qoshe nake,Nci Abinci, dakaina n Girka mah"

"Kin iya Girki ne?" Ta fada tana dan hararana

"Lallai Ammie kin Rainani dayawa ,Meye Acikin Girki da bazan iyaba?, kawai Wahalan Girkin ke Sani qinyi"

"Toh naji..Kinga Bari na hado miki Abu mai Zafi ya tafida Dishewr da muryanki tayi kinji?" Ta fada tareda nufar hanyar Fita.

Muryata taji ina cewa "Ammie da kin barshi kawai ,A hakan ma Muryan Ta ware Kenan fa Sbd Shayin da nashaDa safen nan, Bakiji Muryar ba a jiya ko Magana Daqyar nake Iyayi "


Ganin 'Yar tta na shirin yin 6arin Zance yasa taja kafarta tabar dakin ranta tana Son Ganin Randa bakin Munayferh zai mutu Ta daina 6aro Zance, ita wuya ko wahala baya hanata fadin Abinda ke Zuciyar ta.

******


Achan dakin Kuwa Abba ya Dora dayi msu Nasiha mai Ratsa zukata daga Bisani ya Sallame su.


Umma da InnaRabi wacce Dama Gulma ne ya zaunar da ita Suka tashi Suka fice.

Yayinda Aaryaan ya Qara qasa dakai Cikin In'ina Da son Bayyana Abinda ke Ransa ya fara magana.


"Ehmm....Dad....Uhmm....Da....ma...."


Ido Abba ya zuba mshi Yaga yanda 'dan nasa ke kame kame Da Alama kuma maganace mai Muhinmanci yaje son Fada mai.

"Aaryaan me kake son Fadi ,Feel Free kamin magana ,Ni mahaifinka ne"

Aaryaan ya fara magana Cikin qwarin Gwiwa

"Abba Don Allah ka Gafarceni Haqiqah ban Kasance 'da na Gari ba, Haqiqah na Kasance mai Boyewa Abbansa Damuwansa A Dililin wani nasa Qudurin....Abba ka Gafarceni ka Fahimceni DonAllah karkayi Mn mummunar Fahimta" Sai yayi Shuru tareda Jan Yar yatsansa Ya kuma Gyara Zaman sa A qasa ,idanunsa Sun Kada Sunyi Jazir.

"Kai bamua son Shashanci fa, idan magana zakayi ka bar mana Wani Corner Corner, ka Fito ka gaya mana kawai, Meye na Dogon Lafazzi?"


Inji Kakus cikin quluwa,Abba kuwa kasa magana yayi ya zuba masa idanu Cikin Nazarin Yanayin nasa.



"Abba dama Ba Transfern Wurin Aiki Akayi mn ba na dawo Kd Da zama... Uhm..ka Gafarceni Abbie Dama...Dama..."


Abba ya kalleshi Shima Cikin Fargaba yace


"Aaryaan ba Aiki Kakeyi A KD ba then me Kakeyi?, Me yasa kabar Aiki a Shika?"


"Abba badaina Aikin nyi ba,Jinginar da Aikin nayi.....Sbd....ehm....Wani....Aikin .....da....nake...Son..yi....Uhmm...dama Aikin DanSanda na Shiga!",


Cikin Rashin Fahimta Abba yake Dubansa itama kakus Kallonsa takeyi Cikeda Mamakin da nazarin inda Zancen NASA ya dosa .



"Eh...Abba Nayi zaton Zaka hanani Kuma UmmA bata son 'yansanda Shiyasa Naqi Sanar daku .....Nan ya kwashe duk Yanda Akayi ya fada msu Da dalilin 6oyewar da yayi.


Abba ya Share 'Dan Guntun kwallan da Ke maqale a idonsa sbd tuno Dan uwansa da yayi yace

"Ada na dauka ni tsayayye ne, Amma a yanzu na gane ba haka bane tunda Dana bazai iya Dubana ya gayamn muradinsa ba ".......













~Shin Me innaRabi take nufi ne?~

~Kenan tanada Alaqa da 6atar Abban Munayferh?~


~Me Abba zaice dangane da wannan lamarin?~

Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ



Waiting For your Comments....



Wattpad@fahnaan



17th oct๐Ÿ˜Œ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
HAWAN JININA

~(Uwar-Mijina)~

๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
By
~FAHNAAN~

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...



*Chapter 50*


"No dad Please ka Fahimceni ...Amm...."


Ya Kasa Karasawa ne Sakamakon muryan kakus dinda yaji Cikin Rauni tana Cewa


"Ba Rashin Fahimta bne Aaryaan ,mun Fahimceka Sosai ,Sbd Raya Aikin lada kk son yi!, Aikin da Ma'aikatan Hukuma suka kasayi, Allah yayi maka Albarka ya sa Albarka Cikin lamuran ka Yayiwa Rayuwanka Albarka ,Allah yasa Ka Fara a sa'a , ya Raya Zuri'ar ka , Ya Haskaka maka hanyan Aikin Cikin Aminci" wani irin Matsanancin Kuka ya kufce mata ,Cikin Tsananin Tashin hankali SBD Tuna danta da tayi


Abba ya kafesu da idanu Ya Kasa Fadin komai, yana Al'ajabin qarfin Hali irin na Aaryaan ,Yaja dogon Numfashi hadida jingina da kujerar da yake zaune ,Cikin Sauke numfashi yace


"Aaryaan Har yanzu baka bani Amsar tambayata ba, Meyasa Zaka 6oye mn Maradinka?, Kana tunanin Idan ka Gaya mn zan iya hanaka ne?, ko kana Tunanin Zanqi Goya maka bayane?, Uhm? Meyasa Aaryaan!".

Cikin qara duqar da kai Murya A raunane yace

" ka Gafarceni Abba, UMMA nake tsoro, kasan Bata son 'Yan sanda Tunda Aka Kashe mata Jaririn 'Dan da ta Haifa a Gabanta ,Muka kai qara 'Yan sanda Sukayi Fatali da Zancen mu Daga Qarshe Suka Juya zancen Akan ta wai ita ta kashe 'yarta da Hannunta, tun Daga Ranar ta fara Tsanar 'Yan Sanda ,Bata kuma qaunar koda hanyace ta hada su , Kasanta idan ta tsane Abu ,Shiyasa na yanke shawarar 6oyewa Gudun kar in Fama mku Raunin da ya Dade Yana Kunshe a Ranku, inyaso Daga baya Sai taji...."

Cikin Fahimta Abba yayi masa Fatan Alkhayri hadida Yi msu nasiha mai Ratsa zuciya, Daga Bisani ya Umurce shi da ya kirani na Rakasu Airport,


Koda yazo Part dinmu Ya Gaida Ammie tareda tambayanta INA nake CE mai tayi nayi barci kawai.


Ya juya ya gayawa Abba nayi barci, Saqo Abba ya Bar mai Idan na tashi ya bani ,Daga nan Suka Dunguma Airport 12 :00pm dot jirginsu ya Daga Zuwa DENMARK, Dan Duba lafiyar Kakus....


Ni kuwa tunda ta faษ—a duniyar bacci bani na farka ba, sai gaf da'ana ฦ™iraye ฦ™irayen sallan zuhur Kuma ba laifi naji dadin Jikin sosai..ย 

Kaitsaye banษ—aki na wuce naje tayi wanka haษ—e da ษ—auro alwala tazo ta kabbara sallan Zuhur.

Kayanna marar nauyi nasanya haษ—e na fito Parlour , zaune na iske Ammie tana faman ฦ™oฦ™arin Cire wa su Ameerah Kayan makaranta.


Cikin sauri na qarasa Wurinta

"Ammie na Bari na tayaki"


Da kallo kawai tabini ,Cikin mamaki da Al'ajabin wai yau nice nake fadin ta kawo Na tayata.

"No barshi kawai " ta fada lokacinda Take Cirewa Ameer Stocks.

Qarasawa nayi Na ja hannun Ameerah ina fadin
"Qattin Banza, da Girmanku Sai an Cire muku Uniform ,Ku ko kunya bakuji Kuna Wahalar mana da Ammien mu"


Turo baki Ameerah tayi tace "To ai ni na iya Ami ne Bai iya ba"

Ameer yayi carab yace
"Kayya ne Ni na iya ,Amiyya she mata iya ba ,ko jiya ni Ma ciye Nawa Da kaina Ko ammmi?" Ya fada Yana duban Ammie da ta Soma Cire mishi Buttons na Rigarshi.


Murmushi Ammie tayi tace "Ba Gara Su Akanki ba ,Ke yaushe Kakus ta daina Mki wanka Kina 15yrs Ma ba'a daina mki ba, dukda ta Tsufa Kike wahalar mana da ita ,da Anyi magana kice Ke komai Wahala yake mki, Gashi yanzu Aure Akayi mki Zanga Mai kular mki da mijin Nan Gaba kuma in kin haihu inGa mai kula dasu Gabaki Daya"


Nima Murmishin Cikin dariya qasa'qasa nace

"Ammie Tona mn Asiri zakiyi?, So Kike yaran nan Su Raina ni ne?" Na fada Daidai lokacin da Na Gama Cirewa Ameerah Kayan Makarantar.


Na Dan Jingina da kujera Cikin Sauke Numfashi nace

"Ammie Shi YaaAary yana da Mata Meye aikin ta?, Ni kuma Wa ya Gaya mki zan haihu?, Ni bazan haihu ba!"

Na qarashe maganar Cikin son kawar da zancen.


"Fatan da kikeyiwa kanki kenan?..."


"Ammie donAllah abar maganar ,Yunwa nkeji "

"aikin kenan! Ga Abinci Chan a dinning " ammie ta fada Cikin Ta6e baki.


Murmushi nayi hade Da Jan Hannun 'Yan Biyu

"Muje Muci Abincin Ammien Mu, Nayi missing Girkin ki fa Sosai, Allah ya bar mana Ke Ammie Zan Riqa aiko da kwano Kullum Ana kar6o mn Daddadar Girkin ki ,kinji Ammie na"

Na fada Cikin dariya.


"Karki fara!" Inji Ammie


Saida yamma liqis Aaryaan Yazo Daukana Nan ma da qyar ya samu nabishi, Dan Sosai nayi ta kuka kaman Wacce akace JEKI A KASHE Ki

Saida ya kaini nayiwa UmmA Sallama Sannan muka fito duk bada son Raina ba

****


Suwaiba na dawowa ta fesawa Uwarta Abinda ya faru da dukan da tasha Wajen Munayferh da Aaryaan, hankalin InnaRabi in yayi dubu to ya tashi ,kamar wata mahaukaciya haka ta Fito Tana Balbamin bala'i.


Har zataje ta Fesawa Umma Rashin M din da ta saba Suwaiba ta Riqo hannunta tana Girgiza mata kai


"Inna Basai Mun tada hankali akan Wannan 'Yar matsalar ba, Ki duba na dauko mki Hoton Gidan kaman Yanda kikace, Amma Part din Munayferh a kulle yake ,Ban Ga yanda Aka Tsara mata nata ba, bakiga part dinsu YaaJunayd ba wlh ya ninka nasu AuntyZee sau dubu a kyau, na tabbata Na Munayferh yafi nata Tsaruwa da kyau"

Ta karashe magana tareda nuna mata hotunan da Suka dauka A gidan.

InnaRabi dai Kasa cewa komai tayi Gaba Daya Cikin ta ya dau Rawa ,Idanunta Suka Firfito Tsoro baqinCiki da 6acin Rai Suka Ziyarceta ,Suwaiba kuwa bata ma kura da yanayinta ba ta Cigaba da nuna mata hotunan ,Daidai lokacin da idanunta Suka haska mata hoton Ramlah.


Kar6ar wayan Tayi ,Murmushin samun nasara ya ziyarceta Ganin Ramlah nada Ciki har Ciyar ya fara Fitowa, Tana Duba hotonA zuciyarta Tace ~Akafta Rabi ta fara nasara~ ~Haleemah Ke ya kamata Ki fara Ganin Wannan Albishir~


Miqewa tayi ta nufi hanyar Fita ,Suwaiba tace "Inna Ina Zaki?, Wayana!"


Murmushi tayi tace zan Dawo mki dashi yanzu yanzunnan.

Tana Fadin haka ta Fice kai tsaye Part din Umma ta nufa Ta fesa mata Ramlah fa Ciki ne da ita harda nuna mata Hoton .


Cikeda Firgici Umma take kallon Hoton Gaba Daya jikinta Babu inda baya Rawa ,idanunta Suka Firfito ,Tuni Jiri ya nemi kaita qasa Ta koma da baya ta zauna Bisa kujera tareda dafe Kirjinta da qarfi ta Furta

"HazbunallahuWani'imalWakeel"


Ganin yanda Umma ta Wani Rude ta Fita hayyacinta ne yasa InnaRabi dariya tareda Ficewa Daga Dakin.

Hankalin Umma ya kai kololuwa a tashi ,Gaba Daya Kanta yayi mata nauyi!, Ga firgicin Abinda Aaryaan yayida Munayferh Ga kuma Cikin da Ramlah kedashi.


"No way!" Ta fada da qarfi Cikin Wani irin murya mai Cikeda tashin hankli, Hannu na Rawa ta dau waya ta Latsa number Qawarta Hajiya Asiya bugu Daya ta Daga.

Bata Amsa Ko Gaisuwan da Hajiya Asiya takeyi mata ba,ta Dora da Fesa mata Damuwanta.


Hajiya Asiya tayi dariya tace
"Toh Ai ni Tuni Na gaya mki mafita kece kikaqi ba ,wai Gaki mai tsoron Allah"


Umma ta katseta da cewa "Ke dalla Rufa mana baki Har Abadah bazan ta6a daukar banzar Shawarar nn nakiba, duk shaidanci na baikaiga Shirka ba, nidai Urgent Mafita nake nema Daga Gareki, yanda zanyi na 6arar da shegen Cikin Da Yarinyar nan kedashi , Sannan Ita Shegiyar yarinyar Chan Kuma ya zanyi da ita ,Asiya ina matuqar tsoron hada Dangi dasu Banason Tarihi ya maimaita kansa Please ina Mafita?"



Hajiya Asiya tayi Dariya irin nasu na Tsagerun Mata tace
"Indai Wannan ne ya kwana Gidan sauqi ,Ni yanzu haka ina Taraba ,zan Aiko mki da wata Allura zakiyiwa Mai dauke da Cikin ,ina gaya mki ko Cikin dutse Gareta Sai ya zube Kuma tayita Bleeding Har na tsawon Watanni Ta yanda 'Dan naki bazai sake tunanin Kusantar ta ba, Dan Sai ya Riqajin Qyamarta Daga qarshe fara tsanarta ,ita kuma Rasa kunyar nan Nata hadin Sai na dawo....Zan Ba Jameelu Alluran ya taho mki dashi Nan da kwanaki bakwai Kinji Ammma fa Sai kin mn Akqawarin Cika mn Account dina"


"Wai har naji dadi wlh idan kudine baki da matsala, Ni burina bai wuce naga An salwantar da Cikin nan ba"


Daganan Suka cigaba da tattauna Yanda Zasu Salwantar da Cikin Tareda kunsa mn Baqin Ciki....

***

Tun daga Ranar Aaryaan Bai sake Yunkurin Kusantar Munayferh ba ,Iyaka in dare yayi ya tabbata nayi barci Ya Shigo Yayi pecking Goshina Sannan yayi mn Addu'ar Bacci ya Furta *"Ina sonki Matata"* a saitin Kunne na Sannan ya ja mn bargo hafida Kashe Fitilan dakin Dan ni bana iya kwana Cikin duhu.


Haka kuma Ban ta6a Yarda naci Girkin Ramlah ba , Daga Qarshe ma Fitowa nayi na Gaya mata tafa daina Hada Girkinta da Nawa , Kullum Ina Part din Janaan Ina Zaune zatayi Girki ko tayata banayi in ta Gamababu ko kunya na zauna na Cika Tumbina da Girkinta.


Haka kuma Tun Randa Ya bani wayata da ya qwace Amma Abin takaici ya Gogen duk Strange Contacts dnda Ke Wayana daga na mazan har matan,Numbern wa'enda ya Sani Kawai Ya bari ,Ranar nayi kukan baqinciki Dan Ba qaramin Bata mn Rai yayi ba.

Yauma kamar Kullum ina Zaune a kitchen din Janaan ina latse latse a Wayana Yayinda a Gefe Guda ita kuma take Hada Abincin Rana.


"Neryfee Taimaka mn ki dau Abincin nan Kikai mana dinning" inji Janaan tana Cire Afron dindake Jikinta tareda nufar inda zata Wanke hannayenta.



Tsaki naja Cikin kufula nace "Ke nifa Zaki takurani ne kawai ,karkiga Dan ina Zuwa ina cin Girkin ki Ki fara Raina mn hankali ,ki Bini a sannu matar yaya nake Talk to me With Respect"

Janaan taja 'Yar Guntun tsaki tace "Kinsan Allah nayfee idan Baki dau Abincin nan kin jera kan Dinning ba Saidai ki kwana da Yunwa"


"Baki isaba Aradu Sai na hada kida Daddy"

Daidai lokacin Da muka jiwo Muryan Yaajunayd yana sallama.



Janaan ta kwashe Abincin tana Zuba mn harara tayi Gaba ,Ni kuwa Ta6e baki nayi tareda Gyara zama ina Latsa Wayana.


Saida na 6ata Almost 20mins ,Dan na tabbata a lkcn tayi wanka Ta Gama Kimtsawa ,Sannan na Miqe na nufo dinning dn.


Zaune na iske su kan dinning dn ita da Yaajunayd , qarasawa nayi na zauna ,ina fadin


"Sannu da Dawowa daddyna ,Au lawyern mu"


"Daddy dn dai ,Daughter baki Gaida Mum dn naki ba" inji Janaan Cikin dariya.


Duka nakai mata a kafada nace

"Yalinya nafi karfin Ki haifeni ,Matar yaya nake ki koyi Girmama na Gaba dake"


"Ouch!, Hayatee daughter zata 6allani wayyo hannu na" ta fada A shagwa6e Cikin Narkar da Murya tareda kwantar dakanta Bisa kafadarsa.


Dariya yaaJunayd Yayi yace
"Daughter Mum din naki Zaki nakasa ko?, Wlh Kika Kuma dukan mn mata sai munyi Shari'a dake, Sannu Jannu kinji ,Kyale daughter zamuyi maganinta...Muguwa kawai"

Ita kuwa Janaan sake Narkewa tayi tace "Muguwa Da hannu kaman Guduma!"

Cikin kokarin matso kwalla na a hannu ina Gurge ido n turo baki

"Shikenan daddy ka daina Sona Kafison matarka Akaina , Abba da kakus ma sun daina sona Ammie Ke kadai mai Qaunata Ita kadai Ke Rarrashi na A yanzu.... Shikenan ba komai Kuci Abincin Ku na fasa Ci mah"


Janaan kuwa Cikin son Kunsa mn baqin Ciki tace

"Ki tafi Dan Allah ,Kinga Abincin zai qara mana Auki...ina kema kinada miji kije Chan ya Rarrasheki"


Junayd ya kalleni yaga yanda na Cika nayi FAM ,Harga Allah na bashi dariya sosai ,Amma sai ya Toshe dariyar tasa

"Jaanu meye haka?, Sorry daughter na, Kyale Jaanu Bulala take nema, Bari na Diba mki Abincin dakaina Kinji Sulthyn YAYA"

Ya qarasa magana Cikin Kwantar da Murya tareda daukan plate da Spoon yana Kokarin zuba mn Abincin.


Da sauri Janaan ta kar6i Plate din da Spoon "Haba hayatee ,Bari na hutashe ka karta Wahalar mn dakai"


Murmushi yayi tareda miqa mata , Ka Zuba mn tana harara na ,Dama Tuni su Sun fara ci.


Nima Abincin na faraci Ba tareda na kuma wata magana ba
Soyayyar Janaan da junayd na Burgeni ,Nima Da So samu ne Na samu Wanda zai riqa kula dani yana lalla6ani kaman yanda Junayd yake yiwa janaan.

Lomar Abinci nakai bakina Ina cewa '' Besty Kinsan Wani Abu"


Murmushi tayi Cikin kula tace " Aa sai kin Fada Daughter ".

" Bintou Emran banaso"


"Naji Bintou Hayatee"

Harararta nayi nace

"Wlh Jaanu Ina Tausaya mki Ranar da YaaJunayd zai Juya mki baya, Alokacin kin fara Tsufa kin haifi yara Hudu ko biyar Alokacin babu Wani Jaanu ko Hayatee in kin samu ne ya kiraki Ummu wance , Iba hakaba Janaanuwa zai Riqa kiranki ,Shifa namiji ba Dan Goyo bane ,A lokacin da yake Neman Aure Juyawa yake ya Zama tamkar Akuya , A lokacin da ya sameta Kuma ya zama tamkar doki...Abinda Nake nufi anan Shine A lokacin da YaaJunayd yake Neman Auren ki Zakiga idan yazo hirama har Wani Sussun dakai yake kaman Akuya ,Kinsan ita Akuya bata Tafiya idanunta a sama dole sai ka sameta Idanun nan qasa tana Tafiya A hankula"

Na qarasa magana ina nuna msu yanda Akuya Ke Sunnarda kai in tana Tafiya, Junayd ya kafeni da idanu .


Na harareshi tareda daurawa da cewa


"Ka kalleni da kyau Gaskiya nake Fadi...janaan kina Jiko?...dazarar kuma ya mallaketa ta zama nasa zai zama tamkar Doki Kannan A Dage Idanun nan Asama yana kallon kowa a Dole shi Oga ne Sai Abinda ya yanke...Dazarar kuma ta fara Haihuwa Daya Zuwa Biyu ,Uku ko hudu Abinda zai fara Lalacewa Tunda y gama Samun Abinda yake nema a wajenta Saikiji yana cewa Wance Kinsan zaman haquri kawai nakeyi dake babu Abinda Kike ta6uka mn, Banga Anfanin zmanki A Wannan Gidan ba, Kaji hege ya manta lokacin da yake Jaanu I can't live Without You kece Annurin zuciyata, idan bake ba sai Rijiya yanzu Dan Ta rage sugar Sai ta zama kece Shuwakar zuciyata?, YaaJunayd kaji tsoron Allah ka riqe mn besty Amanah , Akanta Zan iya komai...idan har ka sake ka Rage koda kadan ne Daga Cikin Qaunar da kake nuna Mata saina Hada Chemicals na watsa maka Fuskar nan taka ta koma Abin tsoro ,Kaji na Gaya maka Ke Kuma ki Riqe Daddy na da Amana Kika sake kikayi Abinda zai 6ata masa Rai sai naki zan Ya 6aci sai nasa ya qara mki Kishiya"



"A'ah nyfee Ai duk Abin Bai kaiga Haka ba,as the matter of fact yaune Rana ta farko da naji magana Mai Amfani Daga Gareki kuma Wlh da Gaskiyarki haka suke basuda tabbas, Har kinsa daddy ya fara bani tsoro.....







BARI NAYI GABAS


WAI Y MAGANAR UMMA NE?, ZATA SAMI NASARAR ZUBAR DA CIKIN RAMLAH KUWA KO YAYA?...



SHIN ME INNARABI KE NUFI NE?, MEYE MA'ANAR MAGANARTA NA TA FARA NASARA!!!













NAYI GABAS๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ



Bintouโœ๐Ÿป
(Fahnaan)


18th oct

๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
HAWAN JININA

~(Uwar-Mijina)~
ย  ย  ย ย 
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  by FAHNAAN~
ย  ย  ย  ย 
ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
ย  _Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
ย 
ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...

ย  *Chapter 51*

Saida yamma Lis kafin Na koma namu part din bayan Janaan ta hadani da Abincin darena .

Motarsa na gani Parke a harabar Gidan Yasa Gabana Faduwa ,Da 'Dan Gudu nayi Ciki Ina Waiwaye ,

A parlor na iske Ramlah Riqeda Remote tana kallon Wani Korean series

Kallona tayi Cikin Alamar tambaya tace
"Ke wai lafiyarki kuwa ,Kin Wani shigo da Gudu babu ko sallama?"

Ban Amsa mata ba sai qara zaro idon da nakeyi Cikin qasa da Murya kaman Mai rada. Nace

"Ya dawo ko?"

Ramlah ta Dan Gimtse dariyarta Cikin sigar tsokana tace

"Eh mana, Yana dawowa Ke ya Fara Tambaya"

'Dan zaro ido nayi ,Daga bisani na Turo baki "Aunty nifa Amso Abu najeyi, Kuma ai ban Dade ba"

Dariyar da Ramlah Ke 6oyewa ne ya fito fili "Ke nifa wasa nake mki, Koda ya tambayeki Ni cewa nayi Kina chan daki kina barci ,Yanzu yana Nasa dakin Yaje wanka ne"

Murmushi nayi Cikin jin dadi nace
"Yawwa Aunty naa,Na gode sosai Shukriya....Amma fa Bai dace Ace da Girmanki kina Qarya akaina ba!"

Na fada tareda Haurawa sama da 'Dan Flask dna.

Da kallo ta Bini Kawai tareda Dan Girgiza kai,

Ni kuwa ina Shiga Bandaki na fada nayi wanka ,na dauro Alwala nazo na Gudanar da sallan Magrib ,Sannan na jawo Flask din Abinci na fara Dirka wa Ciki na ,Saida naci nayi Nak Sannan na dawo Parlon qasa, inda na Tarar dasu Yana Zaune a qasa yana latse latse a laptop Ga kuma wasu Files a kusa dashi , Ramlah ma na zaune kusa dashi ,Kallo Daya ,zakayi mshi kasan Kansa fa ya dau Chargi.

Nima Samun wuri nayi Gefen Ramlah na raku6e "Sannu Aunty "
Na fada ina Zama Daidai kusa da ita.

Da yawwa ta Amsa mn Idanunta na kan Laptop dn,

Shikuwa Ganin Sabon Iskancin da na 6illo dashi Yasa ya Rufe Laptop din yana kallo na Fuskan nan A murtuqe kaman Dussa.

"Lafiya?, Baki iya Gaisuwa bane?, Wai tukunna ma waya Gayyato ki nan!" Ya Watson mn tambayoyin Duk a lokaci Guda.

Kawar da kai nayi ina Dan Hararar Gefe tareda Ta6e baki na Miqe ina fadin

"Wannan kuma kai ta shafa, Mutum sai mugun hali kaman Tawagar Qaruna?,ย ย  Abinda ya dameka kar ya shafi sauran dangi ,dama nazo ne dan na tunasar dakai !, kamar yanda Namu Aladar yake Gobe Zanje Gida!, Kuma basai ka kaini ba, Kasa a turo mn motata kawai nayi......"

Ban qarashe ida maganar nake Shirin Furtawa ba na Arta A guje, Sakamakon yanda ya Yunqura kaman zai kamani

Ramlah dai dariya take, ya dubeta Cikeda Takaici ya Furzar da wani huci mai xafi tareda hararar ta.

"Dariyar fa?,"

Ya fada yana qara harararta Cikin Hasale.

Itama Cikin tsokana tace

"Koma me tayi maka kai ka jido,,,Kafa San halinta ,Ba'ayi mata ta qyale ,Meye naka na kulata? , Kamata yayi ka qyaleta Lokacin da tazauna iyaka kayi mata Magana Akan Rashin Gaishekan da tayi Shima Cikin lallami Don naga tafi ganewa hakan..."

Tsawar da ya daka mata Yasa taja bakinta ta Tsuke ba tareda ta ida Bazar zancen ba.

"Tashi ki bar mn nan..." Ya fada a takaice yana nuna mata hanya.

Dariya tayi tana kwashe masa files dinda Ke yashe a qasa ,ta kuma Daukan Laptop dinsa ta saka Cikin jakanshi, ta miqa mai

Qin Amsa yayi yana kallon ta ,Hararar

Please Login or Register in order to submit comment