Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya Cikin Mood dinshi, haka koda yaje Gaida Ammie Sama Sama suka Gaisa Daga Biyani ya wuce Waje Aiki๐Ÿ‘ฏ๐Ÿฝ.

***

A Gida kuwa Sosai nasha Tsokana wajen Su Hafsah, Haka kuma duk Abinda Sukeyi iyaka na Murmushi , ban Yarda na Bude baki nayi magana ba Kuma ban Motsa daga inda ya direni ba, Gudun kar na Furta wata maganan Suji yanda Muryata ta dishe a Shaqe, Kar kuma na Miqe Suga yanayin Tafiyata A juya Akalar Tsokanar Zuwa Dayan Fannin......

Ko Abincin da suka kawo sama sama na Ta6a dan Bakina babu Taste Gashi mugun Yunwa

Da suka Gajida zuba Suka Wuce Sashen Janaan suna mamakin yanda Bakin Parrot dinsu ya Rufu a Yau Dinnan.

Suna Fita na Shige dakina na Sa makullin tareda Fadawa kan Gado na Lumshe idanu nan danan Barcin Wahala yayi Awon Gaba dani.

Bani na Farka ba sai Qarfe biyun Rana da wani Irin Matsanancin yunwa na tashi da qyar na fada Ban daki nayi wanka Tareda dauro Alwala na Gabatar da Sallar Zuhur.


Sannan na Shirya Cikin Qananan Kaya Riga Pink and white Sleeveless, da Blue Jeans nayi matuqar kyau Sosai ,dukda kallo daya zaka yimn kasan ina jin jiki Juriya ce kawai.

~kar kuyi zaton Nasa qananan kayan ne don na burge wani ko dan wani,A'ah dama Chan na Saba da hakan ne ,banasa manyan kaya sai ya kama~

Wayana na Dauko na latsa numbern Abba,Dan na Gaya mishi Abinda Matarsa da 'dansa suka mn jiya ,Bugu daya ya dauka,Bayan mun Gaisa


Yake tambaya na lafiya yaji muryata wani iri?,

"YaaAary ne ya Shaqe ni jiya kuma ya Wanke ni da Mar....." Na kasa qarasawa Saboda Qamshin turaren sa da naji ya mamaye ko'ina na kafan hanci na.


Waige Waige na farayi ko zan gansa,Amma banga ko kalar Tufafinsa ba, hasali ma sai yanzu na tuna da na Rufe kofar Tun dazu Kafin na ....


Ajiyan Zuciya na Sauke na kuma kara wayan A kunne nace "Hello Abie na kanaji na?, "

ya Amsa da

"Eh inajinki Angel, Bayan Shaqeki Mai yayi"


Gabana Ya Fadin jin Qamshin turaren sa na Sakeji

"Cikin in'ina nace Haba Abie Wa ya Gaya ma ya shaqeni?,Nifa Bance ba!, kawai ka manta da wannan zancen ...... Please ka fada Mishi Ya kawoni Gobe inyi muku Rakiya kaji Abie na" na fada cikin Shagwa6a.


Wani Irin Ajiyan zuciya ya saki Wanda Harni da nake Rubutun sai da naji๐Ÿ˜‹

"Har kin bani Tsoro na dauka Wani Abun ya Mki ne, da na dau mataki akan hakan ".



Qarar Bude kofar da naji yasa na saki wayan ba tareda na shirya ba na fara Zare ido kaman wacce taga Maye.

A hankali ya Tako har inda nake ya Duka ya dau wayan da ya Fadi a Hannuna ya duba screen din Wayan Ganin Sunan Abie yasa ya Waro ido da Cikin sauri yayi hanging Call din yana Duba na yana mn Kallo na Tuhuma ,Fuskar nan A murtuqe babu Alamar wasa.


Tuni na kuma Tsurewa,Bansan Lokacin da bakina ya fara Furta

" Dan Allah kayi Haquri Wlh Wlh ban fada ba"
Na fada Cikin tsananin Tsoro da Firgici .



Ba tareda ya tanka mn ba ya fara latse latse a wayan Chan naji Yana Playing Voice Recoding na Call dinda mukayi da Abba sai da ya Gamaji sannan naga ya sauke Ajiyan zuciya tareda Sakin fuska, ya saka Wayan A cikin Aljihu yayi Ficewarsa, da Harara nabi bayansa tareda turo baki kome zaiyi da wayana oho.


Nima a hankali na Tashi na Fito a General Parlor na iske su dukka Shida Ramlah suna kallo.

Da ido ya mn Alama da na Gyara tafiyata ,Sai nayi tamkar ban Fahimce shiba, na Qara langwa6ewa ina Tafiya kaman Agwagwa.

Itama Ramlah kallona tayi ta kuma maida hankalinta Ga Aaryaan Wanda Tunaninsa kaf kega Munayferh

"Doctor ya Akayi wancan ta shigo ba tareda mun Sani ba?"

Kumbura'uba Wato nice Wanchan ,Nida Gidan Mijina Wata ta Ringa mn tambayan Rainin hankali

Kafin nayi magana har ya bata amsa a takaice

"Itace Amaryar"

"How comes?,ya akayi hakan ta kasance?,"


Wuri na Samu na zauna nayi taagumi ina jiran Amsarsa


Tiryan tiryan ya bata labarin yanda Abubuwa suka kasance Harda Auren Titin da mukayi kwanaki, Jikinta yayi Sanyi matuqah batasan haka Abin yake ba ,da batayi pretending bah...


Daga Qarshe ya Qarashe dayi mana Nasiha, Wanda Zan iya cewa Ramlah kadai yayi mawa domin ni tunda ya fara na maida hankalina Gabadaya kan Series dinda Ake nunowa a Television har ya Gama Surutunsa na daiji yace ya Raba kwana Amma banji ko kwana nawa bane....


Ya kalleni yace inada Abin fada ne?, sai a lokacin na Juyo nace A'a Itama Ramlah ya tambaye ta tace A'a


"Yaa nifa Yunwa nakeji"

Na fada ina Yatsine Fuska tareda Dafa Ciki na.


Kallon Ramla yayi yace "ki Dauko mn ledar da na shigo dashi dazu"

Miqewa tayi ta Dauko ta dire a Gabansa, ya miqa mn ledar na Amsa ko Godiya.


Na zame daga kan kujera na zauna saman Rug, na Saki wata qara tareda Fadin Wash Sakamakon Zafin da naji ya Ratsani .


"Meya faru" ya tambaya Cikin kulawa.


"Zafiii" na fada a Shagwa6e kaman zanyi kuka

"Me ke mki zafi?" Inji Ramlah.

Nq bude baki zanyi magana muka hada ido dashi ya sakar mn Harara hakan yasa na ja Bakina nayi Shuru na fara Cin Abin ci na.......

Duk suka Bini da kallo, shi yana kallon yanda kayan Jikina suka Amshe ni suka mn kyau ita kuma tana kallon yanda nake Cin Abincin sai faman Yatsine Fuska nakeyi kaman Ana Takura mn Dole Saina ci.

*****



Tun Magriba na Shige Daki tareda kullewa da makulli Gudun kar Ya Afko kaman yanda ya Shammaceni a jiyan,ina idar da Sallar isha'i na fada Bandaki nayi wanka Dukda har yanzu ban Gama warwarewa ba Sosai kuma Fa ya bani magani Dazun.

Na Jawo daya daga Cikin Akwatin da aka kawo mn na, Wanda Ke Danqareda Nightes da Ready-mades,


Wata 'Yar Qaramar Pink Gown Sharaยฒ na dauka na saka Yakuwa mn das kama Danni aka Qera
~damaAl'ada tace duk Sanyi duk zafi nafison kwana da kaya Mara nauyi~

Na kwanta kan Gado ina kallon sama kaman mai Tunani, barcin ma yaqi zuwa Gashi babu waya Abokin Taya hira.


Ina nan kwance haka naji kaman ana kiciniyar bude kofa ta baya.


Cikin Rudu da Fargaba na Miqe ina Zazare idanu kaman maye ya smi nama,.

Shigowa yayi hannunsa Riqeda Ledar Magunguna , ya Diresu a qasa shima ya zauna a qasan Ya kalleni "Taso" ya fada a takaice


Ban iya amsa mshi ba illa qara kame jikina da nakeyi, Bai damu ba ya tambayeni ya jikin?, na Amsa da sauqi
Ya kuma tambaya naci Abinci ne?

Nace Eh


Ya Miqe daga Zaunen da yake ya nufi Fridge ya Dauko Ruwan Gora ,ya dau Ledar maganin da ya Shigo dashi ya haye kan Gadon inda nake Chan Tsakiyan Gado,

Ina Ganin ya hayo Gadon na diro daga kan Gadon ina ja da baya tareda Zaro ido saboda Tsananin Tsoratan da nayi.

Murmushi yayi yace "Ki dawo ki zauna babu Abinda zan mki ,Magani kawai zan baki"


"Ba nasha Magani dazun ba!?" Na fada Hawaye na Fita daga Idanuna


"Eh....wannan na darene Oya Come Forward kina 6ata mn lokaci" ya fada Cikin Baasarwa.


Sake ja da baya nayi ina Hawaye "Kabani maganin zansha Dakaina"

Yar Guntun Tsaki yaja Tareda Saukowa daga saman Gadon taku daya yayi ya riqoni , na fada Jikinsa hakan yasa na saki wata 'Yar qaramar qara.


Sake Rungumota yayi Wanda ya haddasa Abubuwa da dama A tattare dashi.

"Dan Allah ka Cikani zan Sha Maganin dakaina" na fada Cikin Hawaye, ina kokarin kwace kaina daga Riqon DA yayi mn.

Sake Riqoni yayi da bakinsa yake hura iska Saitin Wuyana ,hakan yasa naji wani Baqon yanayi ,tuni qafafuna Suka dau Rawa.

"Please dan Allah ka bari..... Inajin wani iri" na fada ina Daga kafafu


''How're you Feeling" ya fada yana Juyowa dani n Fuskanceshi.

Na bude baki zanyi magana ya๐Ÿ‘„+๐Ÿ‘„




Daganan na tarkakata nawainawa na bar musu dakin















Sannan






Nayi





Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ




Fahnaan๐Ÿ˜„










10th oct๐Ÿ’š
[15/10 12:21 am] Fahnaan๐Ÿ’–: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 47_*


2:30am

A hankali ya Riqo hannunta Cikin Rawar murya ya furta


"Please Forgive Me Sulthy,Ba da son Raina na Aikata hakan ba, Sonki ne yasani Aikata hakan,Believe me ,Wlh I love You so much....." Yayi magana Cikin Sanyin kwantar da Murya.


Ita Kuwa Munayferh Bata ma San yana Yi ba ,Dan Tuni ta Sume dan Azaabah.

Hannunsa ya daga Sama yana Mai roqon Allah yace "Yaa Allah na Gode maka da ka bani Munayferh A matsayin mata, Ina Roqon ka ka Shirya mn ita , ni kuma ka Rage mn Zafin Zuciya da Saurin Fushi , ya Allah ka dai daita tsakanina DA Matata kasa ta soni koda Kadan ne daga Cikin Siyayyan da nakeyi mata, yaAllah ka Shirya mn mahaifiyata kasa taso Mataana , Tasa mu zauna lafiya Tareda su Cikin kwanciyan hankali kaman yanda sauran ma'aurata Suke Zaune lafiya a Gidajensu....,ya Allah ka yafe Mana Kurakuran mu Wanda Muka Aikatamuna sane da Wanda Muka Aikata a ke6e.........." Haka ya cigaba da Zuba Adduoi kala kala da masu ma'ana da mar..,Wa'enda yasan yanayi da Wa'enda baisan yanayi ba mah, Gaba daya ya rasa Bakin da Zai gode Wa Allah, Addu'a yayi ba kadan Bah, Daga nan ya miqe ya hada Ruwan Zafi , ya koma daki ya daukota kaman Jaririya, bai direta ko ina ba sai cikin Ruwan zafin, Wani irin Ihu ta Saki Ina "Ammie Ya kasheni ,Ya kasheni ..." Kuka nake Sosai

Wannan karon ma dakansa ya Wanketa, hadida Alwala ya Nadota Cikin Towel, Ya Direta kan Gado ya dawo ya Dauko mata kayan Sawa ya Saka mata, Nan take Barcin wahala yayi Awon Gaba da ita.


Miqewa yayi yayi wanka kana ya dauro Alwala ya Shimfida Sallaya Ya tada Sallah ya fara Zuba Nafiloli, Bai bar sallan Ba harsaida Aka Kira sallan Asubah.


Koda ya dawo daga Masallaci ,Yanda ya barta haka ya Isketa sai shahar barci Take Matsowa yayi Gab da ita ya tsura Mata ido


Zuciyar sa na Bugawa, haqiqa yana son Munayferh Sosai Son da yakeji idan Wani ya ta6a masa ita Zai iya daukan matakin da Gabaki daya Duniyasai sun Girgiza da irin matakin da zai dauka, haka kuma yanaji A ransa da Sonta Aka haifeshi dan Tun Randa Aka Haifeta ya Dora idanunsa Akanta Yaji wani Abu ya tsaya Mshi a maqoshi Wanda ya Rasa Gane komeyene?, koda yasha Ruwa Baya Wucewa haka kuma Akoda Yaushe in ya Ganta sai ya tsinci kansa Cikin Matsananciyar Faduwar Gaba, hakan yasa ya tursasawa kansa Tsanarta baya ko son Ganinta ne sai daga Baya ya Fahimci tsantsar Soyayya Ce kawai ba Tsana bace....

Motsin da Yaga na danyi ne yasashi, Saurin maida hankalin sa Kaina ,da kuka na tashi ina a Kiran Sunan Ammie Cikin matsanancin Wahala, Shidai ido ya tsura mn Yana kallona har na Miqe zaune Ina hada idanu dashi na kuma Fashewa da wani irin matsanancin Kuka mai sauti,

A hankali ya dagoni idanun nan Sunyi jaa sun kumburo kaman Wacce Tayi kukanMutuwanUwarta ,A hankali Cikin Sanyin jiki ya Jawoni Jikinsa yana shafa bayana Cikin Sigar Rarrashi ya fara magana "Sulthy kiyi Haquri, inshaAallah bazan sake Forcing dnki ba, Please Forgive me ....Komai na Aikata ba laifina bane, laifin Zuciyata ce, I can't control myheart, My Heart Control me on Every thing I did to you....Trust me bada son Raina na yi Forcing dnki ba, sonkine ya jawo hakan....Please Forgive me Nasan nayi Miki ba Daidai ba" ya dan tsagaita tareda Furxar da Huci ya cigaba

"I'm a bad person, I deserve Any Punishment From you, but Please help me keep My Secret Between Us, Don't tell Anybody About yesterday's Incident Between U and My mum, Please help me keep it as secret...Duk matakin da Zaki dauka Please ki dauka But please Tell nobody About it please.... Dad ya Kirani dazun yace Dole na kawoki kuyi Sallama kafinya tafi and I don't have any Other Option dole na kaiki... krpaya kisee ko na bataen (Don Allah karki Gaya)


ban tanka mshi ba, haka kuma ban daina Kukan da nakeyi ba, A raina kuwa karkaso kaji Abinda nake Qulla masa Dashi da Umman sa., haka kuma Tsanar da nake mshi yanzu ninkuwa yayi.


Ganin sai zuba yakeyi naqi Amsa shi yasa ya tadani Ina tafiya daqyarยฒ Digisawa ya taimaka mn na dauro Alwala sannan nazo dan na Gabatar da Sallah ,Bayan nan da kanshi ya Shiga Kitchen ya hado Mn shayi Kakkaura, Amma Fafur naqisha dan na dau Akqawarin Bazan ta6a Cin Abincin Da ya Girka da hannunsa ba, ko kuma Ramlah ta Girka.


Babu yanda ya iya dani haka ya Qyaleni Acewarsa in Munje Gida zan nemi Abin kari, sannan ya Tasani Gaba ya bani Magungunan da ya kawo mn Jiya InaGamasha Barci yayi Awon Gaba dani,


Ban tashi ba sai Karfe Goman safiya kuma babu Laifi naji dadin Jikin Sosai,Infact Harta Muryana da ta dishe ta dan Ware,
Babu kowa a dakin
A daddafe na Fada Nayi wanka na Sauya Shiga zuwa Atamfa Blue and White Mai Ratsin Baqi nayi kyau Sosai Dukda babu kwalliyan da nayiwa Fuskata, burina Bai wuce Na Ganni Kusada Abbie na ba...


Yunwa nakeji Sosai Gashi Girki Wahala take mn, kuma na dau Alqawarin Bazan iya Cin Girkin Kishiya ba Barena Wanda ya Ajiyeta Wato mai Gidan.


Cikin Qarfin hali naja Qafata zuwa inda nake Zaton Kitchen ne, na dan leqa , Akwai komai Aciki saidai Abinda Baza'a Rasa ba.


Fitowa nayi na nufi hanyar fita ina Cije lips Sakamakon Yanda nake jin kaina Cikin Yanayi na wahaltuwa na Kulle kofar Shiga Na Garqameshi da makulli harda sa sakata ba don tsoro ba, dan tsaro.

sannan na koma kitchen, na hada black Tea ,Na soya Qwai ina cikin Soya Irish naji knocking ta kofar falor ,da sauri na juye Irish din batareda ya ida Soyuwa ba ,Na Fito ina Rarraba idanu Jin an Qara Knocking kofar ne yasa na Koma daki tareda rufo kofa ,na fara Cusa Abincin kaman wacce tayi Shekara bata Ci Abinci ba.


Ina idawa na Fada bathroom na sake yin Wanka, sauya Shiga Cikin Wata Tsadaddar Atamfar launin jaa da Baqi ,Nayi kyau Sosai duk da banyi kwalliyah ba,
Na zauna Gaban Madubi ina kallon kaina ,Har yanzu Akwai Shatin Yatsun Marin da nasha Wajen Aary ,Ga kuma yanda Idanuna suka kumburo Alaman Nasha Kuka ba kadan ba,Murmushin Yaqe nayi da na tuna irin Shirgin da Zan hada masa Shi da Umma Sai Sunyi Nadamar Shiga Gonata da Sukayi.


Karar knocking dinda na Sakeji ne ya sa na Miqe ina Jan Tsaki Dan na Tabbatar Aaryaan ne.


Har na kai bakin Kofa sai nadawo Na maida Kwanukan da Nayi Amfani dasu , Na Ajiye kowanne a ma'ajiyinsa Na kuma Dauko Turare na Fesa koina Barin Ma Kitchen saida na Karar da Kwalbar Turare daya Anan Gudun kar ya Shigo yaji Qamshin Girki.


Saida na Tabbatar ko ina ya dau Qamshi sannan na bude kofar ,Shi dinne tsaye Sanye yake da Wata Lallausar Baqar yadi Simple Dinki akayi mshi Haka ma Hular dake Sanye a kansa baqi ,Yayi kyau Sosai Hasken sa ya Qara Fitowa , Fuskar nan Dauke da Murmushi ya qarashe Shigowa yana Fadin

"Sulthy Barci kakiyi ne?, Tun dazu nake Tsaye ina knocking ko Bakiji bane"

Tsaki naja tareda Turo baki na Biyo bayansa ina Fadin "Nidai Ka kaini Nayi Wa su Abbie Sallama"


"Anqi" ya fada a tausase.


Turo baki Nayi kaman Zanyi kuka nake fadin "Pleasee"

"Ouuh ....Kin Samu Sauqi kenan Kor... Harda Turo mn baki Ahbi" ya fada Tareda Kanne mn ido 'daya yana kokarin kamo hannuna.


Ja da baya nayi ina Cewa "Please Forget All these ...Don Allah ka kaini na ga Babana da kakata"

Na fada kaman Zanyi Kuka,Ya dubeni yana 'Yar dariya ya bude baki zaiyi Magana wayansa dake Gefe ya dau Ruri ,Ya lalubo wayan Da sauri Ya kara A kunne Ganin Abba ne ke kira.


"Good Morning Dad"

"Morning Son, Ku kadaifa Muke Jira"

Saida ya dubeni Kafin Ya Bashi Amsa

"Ehm...Dad She's Sick ,Bazata Samu daman Zuwa ba Ku tafi kawai in yaso Sai Ku...."


"Abie Nah....Lafiya ta qalau I'm Fyn and not Sick, don Allah kace Ya Kawoni Please Abie na... "

Na fada Cikin daga dasasshiyar Muryata dan yajini dakyau Kuma ya sa Aaryaan ya Kawo ni Gida.

Abba yayi 'Yar dariya Cikin takaicu yace "Son Bansanka da Qarya Yaushe ka fara Qarya ?, Meyasa Zakayi Yunqurin Hanata Zuwa bayan Na Baka Umurnin kazo mn da ita?, Meyasa zakayi Yunkurin Hanata Abinda take Muradi Akan naka Son Ran?....."


"Dad kayi Haquri, Ba qarya nayi ba ,Serious batada Lafiya ..."


Abba ya katseshi da cewa "Qarya zatayi maka?, Eh?, Nace qarya zatayi maka ne?, Wlh ka Guji 6acin Raina kazo mn da ita na baka nan Da 10mins ,Saura kayi mata Fada ,nasanka da 6aqin hali zaka iya Hucewa akanta ,ka sani Ko kallon Banza kayi mata saita Gaya mn kuma Zan dau Mummunan Mataki Akanka " Kitt ya datse Wayan Yana Huci.


Aaryaan ya Dubeni yaja 'Yar qaramar tsaki tareda Shan Mur
"Jeki sako Hijab ki iskeni ina qasa" ya fada tareda barin Dakin

Da Harara na bisa ina Jan Tsaki Sannan na Shige na Dauko baqar Gyale na yafa.


Fitowa nayi , babu kowa a Parlorn Sai Tvn dauketa Faman Aiki, Daukan Remote nayi na kashe kallon Sannan na Nufi dakin dake kallon Saitin TVn.

Na fada dakin Babu ko Sallama ,Aaryaan na Gani Rungume da Ramlah yana Shafa bayanta tana maida numfashi Jikinsa a sanya Dukkan su Suna Zaune a tsakiyan Gado ,

Wani Uban Tsaki naja tareda Banko Masu kofar da sauri na Fice cikin Jin haushin su, ina Fita wani irin kuka ya kufce mn Wanda bansan na meye ba,

Motsin mutum da nayi Abaya na yasa Nayi Saurin Share Fuskata DA bayan Hannuna ,Na juyo ina kallonsa shima kallona yakeyi Cikin Tuhuma kaman mai son Gano wani Abu, Gane Hakan da nayi shiyasa na kauda kai Gefe tareda Jan Yar guntun Tsaki


"Tsakin Fa" injishi.

"Please muje " ba bashi Amsa Cikeda Jin haushinsa.


Ramlah ce ta Fito daga Daki tana Cewa "Sai Anjima Doctor, Qanwata A Gaida mun Su Allah ya tsare ya dawo daku lafiya"

Kallonta nayi Gabana na faduwa ,As Usual Yanda na Sabaji idan Na dubi Fuskar ta ta, Dan Wlh kama take mn DA wata, wacce nafi tsana A Duniya, sanyinta da Yanayin dabi'unta kuma Sak da na Mutanen dake tareda ni Mosoyana ,Kara kai dubana nayi Ga Yatsun Hannunta Shima Sak da namu


~Wai ya haka ne?, Meke Faruwa ne?, Ya kamata inji Asalin Kowacece Ramlah!, Duk yanda Akayi tanada Alaqa damu~


Aaryaan kuwa Cikin Farinciki ya Amsa mata da "Ameen Nima Allah ya kiyaye min ke da kiyayewansa Take Care of My Unborn Muah"

Ya qarasa magana tareda Wulga Mata Distance Kiss, itama ta Wulga Mshi tana dariya .

Inaga Ramlah da Aaryaan sun Manta dani a Dakin Fa๐Ÿค”, Tsaki naja tareda Ficewa daga Dakin ,Kai tsaye Parking Space na nufa Ina jiran Fitowarshi, Chan naga Maigadi ya Wangale Gate Motar Gidan mu ta shigo, suka Parka Daidai kusa dani ,Ban Bar kallon Motar ba har Suka Fito.


Suwaiba Ce tareda Qawarta da Muneerah (Autan su Ramlah), ban bar kallonsu ba har suka Iso Gareni.


"A'ah Amarya ina zuwa kuma haka ?, Kodai an Kar6o Red Card ne?,Eh?"
Inji Suwaiba.


Banyi niyyar tankata ba,Amma jin ta Ambaci RedCard na Fahimce ta juyowa nayi Tareda Fuskantar ta nace

" Abanza Wai Akuya ta kori kare, Ni nafi Qarfin Red card Dan Tana Jiqewa,Eh Ko a yau na Mace Nasan Na ta6a Aure Ban mutu A gauruwa ba, kuma naji yanda Akeji... Ke kisamu ki shiga daga Ciki kafin kizo kina Wage mana Rafkeken Bakin nan naki kina Maganan RedCard ....Nabi RedCard din da Jifa....Bi'iznillah Rabice Za'a bawa Red Card Shegiya Da Dogon wuyanki Anan kaman igiyan Lipton"


"KanBura'Uba?, Suwaiba!, Kika Yarda Take Zaginki harda Kiran Sunan Inna kaitsaye?" Inji Busasshiyar qawarta da Sukazo tareda.


Tsaki naja tareda Juyar dakai Gefe, banyi Aune ba naji An jawoni na Fadi kasa Kafin nayi wani Yunquri har suwaiba ta hau kaina ta fara kai mn Naushi tana Fadin "Dan Ubanki Uwar tawa za'a baiwa Takardar Saki dan Rainin hankali Harda kiran sunanta kai tsaye?, Toh wallahi Saina Cicci Ubanki inga mai kwatarki Anan" ta fada tana kai mn naushi a Ciki, Ni kuwa Ihu na saka dan Azaba ina Fadin "Idan kin Isa ki dagani Kiga yanda zanyi mki Dukan wulaqanci Wlh Saina Kusan kasheki"

Ita kuwa qawar Suwaiba sai zugata take tana ta qara mn ,Muneera kuwa dama tuni ta shige Ciki, Tun kafin Mu fara Chachar baki.


~Su Suwaiba da Hegen Fitinar Tsiya har Gidan Mijin Mutun zasu iske shi Suce zasu Zane su kwana lfy?~

Dukana takeyi babuji babu Gani, Ta koina ina ihu haka kuma ban Fasa Tsinarta ina ta Tashi a kaina in Nuna mata koni Wacece
"Dan Uwarki, dama ina kume dake!, Wlh yau mai Rabani dake sai Allah!, Yau Sai na Sa6a miki kamanni,dama Masu Goya miki baya Yau zasu ware ,Inga Uban da zai Goya miki baya!"


Fincikan da taji Anyi mata ta baya yasa ta Zabura tana fadin" Haba Lawisa Barni in Gama Laftar 'Yar shefiya..."

Bata qarasa ba taji Saukan Wasu Tagwayen Mari tako wani Kuncen ta Wanda yayi Silar daukewar Ganinta na Wasu 'Yan seconds, Dukan ta ya shigayi babu qaqqautawa yana Huci kaman An aikoshi ,


Lawwisa qawar suwaiba na Ganin haka ta duqa ta kwashe takalman ta ,taArta a Guje bata ko Waiwaye ta barGidan, Yayin da Drivern da ya kawosu ya dafa kai Baiso Aaryaan yazo ba, yafiso Suwaiba ta koya mn Hankali, Dama yana Kunshe da Haushi na...


Ni kuwa ina Ganin Na tsira na Shigi Rarraba idanu Ganin Aaryan na Sheqa Mata mari yasa na sauke jakata dake saqale a kafadata na Zare Handle dinta na Shiga laftar ta dashi ,Shima Aaryaan Ganin na fara Laftarta yasa ya Tsagaita ya koma Gefe ya Jingina da Motarsa yana kallona, bai kuma hanani ba ,Harsaida nayi mata lis dukan Mahaukata Naga Tayi laushi ta fara Fidda Numfashi daqyar ยฒ, Sannan na qyaleta na juya muka hada ido ya sakar mn Murmushi, na gyara Handle din jakata Na saqala Ya Bude Mn kofa na Shige Gaba yaja Muka bar Gidan ,Muka bar Suwaiba a yashe .



Driving yakeyi Hankali kwance Yayinda Na hada kai da Gyiwa ina Rusar kuka Mara sauti, Ba komai nakeyiwa kuka ba,illa Haushin kaina da nakeji Wai Yau ni Wata banza Suwaiba na naka da qasa harda hawa Ruwan cikina ta min Duka, Ga zafin Abin Jiya bai Gama barina ba,Ga kuma zafin Duka ,duk suka hadu Suka sanya mn Tsamin Jiki A lokaci Guda.


Har muka kai Gidan Babu mai magana Cikin mu ,duk daukan sa barci nayi, Ganin yanda nayi kuma bayajin sautin komai Daga Gareni....




Muna isa ya Parka A parking Space Na Gidan inda ya saba Parka nasa Motar idan yana Gida.


Kaman Kullum Ma'aikatan na Ganin Tsayuwar motarsa Suka fara Tasowa Suka tsaya wajen Motar suna Jiran Fitowarsa,

Cikin Izza da taqama hadida Ji da kansa ya Fito Yana 'dan yaqe .


"Ango! Ango!!, Ango Kaga ango wajen amaryar sa Munayferh tauraruwar Mata, Mace 'daya tamkar Ga dubu diyar maiGida, , ango kasha qamshi, kana kuma kan shan qamshi kuma zaka sha qamshi,A'ah Wannan Qamshi haka?, Ango kasha mai Fah" inji Nazeer yana Dunqule hannayensa waje daya Alamar Girmamawa.


Aaryaan yayi Murmushi Wanda ya qara Fidda Asalin kyawunsa, ya Shafa Gemunsa "nazeer baka da dama fa" ya fada yana Fidda Wasu 'Yan Kudade daga Aljihunsa


"Gashi Ku raba ba yawa, Wannan kuma Tukuicin ka ne Sarkin tsokana"


Duk Abinda Sukeyi ina Gani ta madubin Motar, kudaden da ya fito dasu Masu yawa ne Sosai ~Ashe dama sbd kwadayi suke bin motarsa Da zarar sunga ya shigo?, Yasin sai nayi maganin Su Daga yau bazasu kuma ba~ na fada a Raina.


Fitowa nayi daga motar Cikin Qarfin hali , na tako har inda suke tsaye, Daidai Lokacin da Ekon yasa hannu zai kar6i kudaden YanA masa Godiya.


Wani Uban Tsawa na Daka masa Wanda ya sanya Wasu Jan kafarsu

Please Login or Register in order to submit comment