Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tattare dashi ,Kuma yayi tunanin Ganin Fiye da hakan a tattare dani.

"Sa mn Hular ,Kisa mn Albarka zan fada Miki komai inshaallah"

Hular dake hannunsa ya kuma miqa mn a karo na Biyu, babu musu na kar6a na Sanya masa Kaman wata sakarya Saida ya Umurceni da na tada Motar


Sannan nayiwa motar key mai Gadi ya bude mana qofa muka bar Gidan Muna Fita Wasu Motocin Suka Mara mana baya.


"Yayan hafsah ,kaman ana bin mu fa"

"Eh na Sani Yarana ne....Nasan Kinyi mamakin kasancewana a matsayin 'dan Sanda Labari ne mai tsawo Amma Bari in taqaita mki........."

Nan ya bani labarin yanda Akayi amma a takaice don bai Gaya mn yanda Akayi ya Samu matsayin nan ba da kuma dalilin Shigarshi ba ya daice sbd miyagun da sukayi yawa Cikin 'Yan Sanda yakeson Kawo Gyara Cikin Al'unma.


Fatan Alkhairi nayi masa tareda Fatan samun nasara ,yaji dadin Haka Sosai har ya kasa 6oye jin dadin sa Ga hakan.


A hanya ya kira Daya daga Cikin Yaran sa Wa'enda suka biyo mu yace ya tsaya Ya Siya Garin kwakin da sugar ,kuli kuli da Ruwa mare Sanyi Amma mai 'dan dama dama Da Cup ....


Aikam yanda yace haka din Sukayi , Suka Cin mana a hanya muka tsaya ya kar6a ,da kansa ya Gyara mn garrin ya bani Sannan ya kar6i driving din yana kallona ta madubi yanda nake Cin Uban kwaki ,Murmushi kawai yake aransa yace ~Allah ya saukeki Lafiya Sulthy~

Muna isa Aviation Girgin Su na sauka ,Dama Tun Daren Jiya jirginsu ya sauka a Kano Sai yau suka hayo Private Jet zuwa zeetown๐Ÿ˜‰..

Abba ne ya fara Saukowa daga Jirgin Sannan kakus Follow by Hajiya Umma.


Ina Zaune Cikin mota na zubama Masu Fitowa daga Jirgin ido ,Sai baza idanu nake Chan idanu na suka hasko mn Umma Dake Saukowa daga matattakalar Jirgi , Tayi wani irin fari ta rame ta rage kuzari kaman wacce tayi Shekara tana Ciwo.


Gabana ya yanke ya fadi ,A tsorace nakai dubana Ga Cikina Wanda ya 'dan Fara Girma sannan na kai dubana Ga Umman

~Shikenan tawa ta qare~ na fada a raina yayinda Hawaye ke zuba a Idanuna.


Duk Abinda nakeyi Yana sane Murmushi kawai yayi a Ransa yace me zaisa ya Yarda ya qara sakaci Akaro na Biyu kuma akan cikin da ya fi so Fiyeda Komai a Rayuwa ?.


Maganar da yaji inayi shi ya katse masa Tunaninsa

"YaaAary bari in koma Inada Lectures 4:00 "

"No bazaki ko ina ba Da sauran Time ai"

Shuru nayi kawai sai na fara hawaye .


"Sorry Sulthy, Nasan Tsoronki 'daya kada Ki rasa Cikin Dake Jikinki kaman yanda Ramlah ta Rasa nata ne koh"

Na gyada Kai Alamar EH

Yayi Murmushi
"Meree Patnee(My wife) .... this ur foolishness must be a vector quantity because it has magnitude and Direction , This is what we call locomotive foolishness........, they say Penny wise pound foolish, but in ur own case its penny Sence pound hopeless...... ,In fact did u see this SOHCAHTOA ,Opposite over hypotenuse equal to sine theta but to ur own case ur head over ur brain raise to power two equal to foolishness raise to power twenty...."


Ya fada Cikin dariya ,Wanda hakan ya tuna mn da Daddy na idan nayi wani Shirmen haka yake Mn ,idan yayi maganganun nan sai na Tuntsure da dariya nace

"Peetรก ohh ,(daddy ohh) The best Physician in 9ja Wanda ya iya baqar magana da Physics Kai din Ba baya ba wajen iya Tsara Mutum da mathematics"




Nan ma dariyan nayi tareda rungumeshi

"Ohh yayana The best Copyยฒ in 9ja har Ka tuno mn da daddy na ,Allah sarki Meree Pitรก I miss you Amma ba Sosai ba"



Rungumeshin da nayi ne yake neman dama masa lissafi ,A hankali yasa Hannu ya Rabani da Jikinsa Tareda 6alle Murfin Motar ya fita sannan ya zagayo Ta inda nake Zaune ya Bude mn ,Na fito muka Nufi filin Jirgin inda Su Abba ke tsaye suna Jiran mu.


Dagudu nanufi inda suke tsaye ina tsalle cikin murna.

Qwaqume kakus nayi cikin tsananin murna ina tsalle itama Kakus rungumeni tayi cikin murna.


Shima Aaryaan Zuwa yayi ya Rungume iyayensa Cikin Murna da dawowan nasu.


Gaba dayan Su babu Wanda ya lura da Cikin dake Jikin Munayferh Amma da yake Umma Idanunta AltraScope ne Gani take Har hanji Tana Ganina Babu Abinda Idanunta suka Hasko mata sai Cikin dake Jikina ,Shiyasa ko Gaisuwan da Aaryaan yay mata sama sama ta amsa, bata ma lura da Uniform dinda ke jikinsa ba Abinda masifarta ta hasko mata kawai take Gani๐Ÿ˜†


Sakin kakus nayi na nufi inda Abba yake tsaye da 'dan Gudu na Zan Rungume shi Aaryaan ya balla mn wata Uwar Harara Wanda ya sanyani kama kaina na tsaya ina Dariya.


Daga nan muka Nufi inda Muka parka Motan mu yayinda Aaryaan ya Umurci yaransa da suka rakomu da su Kwashe Kayan Tsarabar da suka zo dashi tunda dama Tareda Kayansu suka Iso

Sai A lokacin da muke Komawa inda muka Parka motar mu Sannan Suka Lura da Abin da Munayferh take tattare dashi ,itama Umma a lokacin ta lura da kayan Da Aaryaan yake Sanye dashi.



Tashin hankali kan tashin hankali ,Tayi Qoqarin Hadiye Tashin hankalin da take tattare Dashine kawai har mu isa Gida ta San Abin yi, tunda A yanzu kam babu Abinda Zata Iyayi ,Bazataso Abinda ya faru a baya ya kuma Faruwa ba ,Dole Tasan Abunyi don ta dau Alwashin bazata Ta6a hada dangi da JEEDDA (Ammie) ba ,barekuma 'Yarta Rasa kunya wacce bata ganin mutuncinta bare darajarta.

Duk Qoqarin ta nason 6oye 6acin ranta kallo daya zakayi mata ka Fahimci Tsantsar tashin hankalin da take ciki ,Cikin Munayferh ba qaramin Girgizata Yayi ba ,Ga kuma danta da Uniform din 'Yan Sanda Wanda Gaba daya Duniya babu Aikin da ta tsana Sama da na 'Yan Sanda, ko a lokacin da 'Yan daban nan suka Afko mana Har Aaryaan yazo ya cecemu Tayi zaton Aron kayan yayi ,Amma Ganin Yanda yake bawa yaransa Umurni Yasa ta tsorata ,yau kam taga Tashin hankali mare misaltuwa ba in banda Allah ya nufa tana da sauran kwana ba da Tunda ta Ganmu Ta kuma ga Mummunar Abinda Muke tattare dashi(A cewarta)da Tun a lokacin Zuciyar ta ta muga ta mace.


Aaryaan Dakansa yake Jan motar yayinda Abba ke zaune kusa dashi.


Nikuwa ina baya na Zauna tsakanin Umma da kakus ,Nayi Zaman Masu Ciki sai wani matse Umma nake Wai a dole ta Takura mn Kakus sai Fada take Wai ta Matsa mn na Sami Isasshen Wuri.

Su Abba kam basu ma San Munayi ba ,Tuni sukayi nisa Wurin hiransu na 'da da uba...

Kafin mu isa Garin Kaduna har Umma tayi laushi Don Tsabar masifar Munayferh cus daga bayama da taga kaman matsetan da takeyi Bai wani dameta ba ta shiga muntsulinta , Da na muntsuketa sai na saki qara na ce ta yaqusheni Nanfa Kakus Ta hayayyaqota tayita masifa.


Abba kuwa yasan Halin 'Yar tasa Shiyasa ya Qi saka baki Cikin fadan Aaryaan kuwa Takaicin yanda Kakus ke biye mn ana Cin mutuncin Uwarsa yake Gashi Abba yaqi tankawa.


Muna Isa nayi wata wawuyar Hamma taredayin miqa

"Kakus yunwa nake ji"

"Tho me Zaki ci?"

"Danwaken flour"

"Tho halima kinji Abinda 'yarni take jin ci, kina Shiga kishige Kitchen ki hada mata"


"Yawwa kakus ,harda Yaji mai Citta Sabon Daka , ta hada mn da kunun Aya a Cika dabino"

"Kut" inji Aaryaan dake Gaban mota yana Jinmu.


"Ja'iri Me kakenufi da qut" inji kakus Cikin hayayyaqowa

Bai amsa mata ba yace

"Keh, Kinsan Allah babu Uban mai hada maki Wannan Shirmen ,inso kike sai Ki shiga kitchen Ki hada da kanki ,Bawai kizo ki takura mn uwa ba"


"Ja'irin yaroh to Sannu mai uwa ,Uwar taka kake marawa baya Kake cewa bazata Shiga Kitchen ba ,Ni uwar tawa ta Sha Wahala kenan Ga jigilar Cikin da ka dura mata ga kuma na shiga kitchen da wanne zataji?"


Wani irin Kunya ne ya kama Aaryaan Amma sai yace''Oho nidai Uwata bazata Shiga kitchen akan wata ba, Ga Masu Aiki nan kala kala sai ta za6i Wanda take so ma ,taje Su Girka mata manah ,Idan kuma Girkin Masu Aikin ne bazata ci ba, kuma bazata Shiga kitchen ba ta dafa Abinda ranta keso ba, saidai ke ki shiga ki Hada mata Abinda take buqata"


Abba ne ya dan talla6e masa qeya tareda Murda Kunnensa cikin wasa yake fadin

"Wato Uwarka bazatayi Aikin Wahala ba ,nawa tayi ko?"

"Ouch Abba kunnena ,da Zafi fa"

Haka Suka Cigaba da hira cikin Raha har muka isa Gida.


Muna Shiga Na hango Yaa Umar ya fito daga Part dinsu ,kome ya mata oho da sauri ya nufi cikin Gida ,Sai Ganinsu nayi sun fito kaf ahalinsu harda Aunty zee itama da nata tsarabar cikin.


Cikin Farinciki suka tarbenu ina lura da Wani irin kallon da InnaRabi ke Aunawa Aaryaan kaman a tsorace take dashi oho koma menene chan ta matse mata.


Muna shiga na tunasar da kakus akan danwaken da nake muradi da kunun Aya nan take ta Tadawa Umma dole ta miqe dukda bata sauke Gajiyan da ta Dawo dashi ba ta nufi kitchen Don hada mn Abinda nake muradi.....โœ๐Ÿฝ


Ina Ganin ta shige na koma Part din Ammie na gaya mata su Umma fa sun dawo ,Da Farincikinta ta nufi Part din tayi msu Sannu da zuwa yayinda ni kuwa na zauna tareda 'yan qanne na muna zuba shirme.


Abdool ne y shigo Riqeda wata takarda

"Yawwa Aunty dama yanzu nake Shirin zuwa Zaria,....jamb Form na kar6o nake son ki cika mn "


Harararsa nayi "kai meyasa bazaka cika Dakan ka ba"


"Pls Aunty..."
"Aunto tafi ka bani wuri" na katseshi tareda Harararsa.

"Tho Big Aunty matar Big Brother Mummyn Big Unborn a taimaka mn, Nasan idan na cika form Dinnan dakaina Shirme kawai zan Rubuta ,Amma idan ke Kika Za6a mn am sure shine zai zama Best Choice a Gareni ...ki taimaka Kinji Aunty naaa"

Dariya nayi na Kar6i Form din na Cika mshi.

Ina Rubutu yana tayani da surutu.


Ina Gamawa Naji sallamar Umma a Qofar Dakin "A shigo" na bada Umurnin ta shigo.


Shigowa tayi Hannunta Ruqeda Flask din Abinci , Furairah na biye da ita da jug din kunun Aya.


Abdool ya miqe da sauri ya kar6a a hannunta yana mata Sannu.


Zata Fita nace ta dawo, babu musu ta dawo ta tsaya, ta dauka flask din Abincin zan bata ta tafi dashi sai taji nace ta tafi da kunun Ayan da Furairah ta shigo dashi bazansha Kunun Ayan da 'Yar Aiki ta ta6a jug din ba ,saidai ta hada mn wani , sannan Kuma 'dan waken da ta kawo mn bazancishiba shima saita dandana Idan naga tayi Minti Talatin babu Abinda ya sameta tho zanci ,Kar ya kasance nima ta zuba mn Maganin Zubar da ciki a ciki.

Haka kuwa Akayi saida nasa ta hada mn wani Kunun Ayan Kuma ta dana dan waken na tabbata babu Komai a ciki sannan nafaraci ina Santi , Gaskiya babu qarya Umma ta iya Girki Ba wasa ba , Shiyasa ma nake bala'in son Girkinta.


Abdool dai yana nan zaune yana Al'ajabin yanda Umma tayi Sanyi take bina sau da qafa Kaman ba Umma bala'i ba ,Tare muka Qarasa Cin Danwaken dasu Ameerah Sai Santi suke yi suna Yaba Girki.

Ina kammalawa na fita nayi part din Umma


Daidai Lokacin da Umma ta dafe qirji da qarfi

"Yau na shiga uku na lalace yau ga 'dan Sanda a Gidana, Wai me yake damun Kwakwalwarka ne Aaryaan? ,Tho kajini dakyau, idan nice Uwarka na kuma Sha wahala akanka baka ka zama 'Dan Sanda ba, ba a wannan Gidan ba, yanda na tsane 'Yan Sanda Wlh Baka isa ba"

Inna Rabi ma Tace

"Ai shine fa?, ya za'ayi ace Mutun yana likita Amma Akan wani dalilinsa na banza Wanda bai taka kara ya karya ba yake Neman Komawa Wani Aikin mabarata?"


"Yau naga ikon Allah Me dan Sanda yayi muku Kuke tsanarsu haka?"

Aaryaan Dakansa ke qasa ya dago ya dube Umman tasa yace

"Umma 'dansanda dai na Riga na zama Umma kisa mn Albarka kawai"


Umma ta dago ta dubeshi a Fusace

"Albarkar ma Idan akwaita a cikin Aikin ka Allah ya Cire makashi gaba daya ka dawo likitan ka yamafi dacewa dakai, Shegen Yaro ka tafi Indai Albarka na ne bazaka ta6a Samu ba...."


"Ke Haleemah idan bazaki fadi Alkheyri ba tho kiyi shuru Banson nasake jin kinyi wata daga gareki , Aaryaan kaje Allah yayi maka Albarka yasa ka Fi haka ka gama da duniya lafiya"


Ina Gamajin zancensu na sulale nabar Wajen Ina mamakin yanda Umma take taqi 'Yan Sanda.


Ina Tafe ina tunani Saura qiris nayi karo da wani Yaron da Aunty zee tayi Aike.


"Kai lafiya?, baka Gani ne?,"


"Kiyi Haquri"

"Anqi Haqurin ....mugani meye wannan a hannun ka?"

"Maganine Aunty zee ta Aikeni na siyo mata" ya fada yana Nuna mn maganin.


Kar6a nayi ina jujjuya maganin tareda ta6e baki

"Maganin meye?"


"Maganin Zubar da ciki ne ,Amma tace kar in gayawa kowa"


Farinciki ya lullu6eni dama ina tunanin ta inda zan Samu maganin Zubar da ciki in Ramawa Aunty Ramlah Abinda Umma tayi mata, sai Gashi Ta fadi a Daidai.


"Kai Amma Anyi manafuqi Ire Irenku Ne mutanen nan na qasan wuta Wa'enda bazasuji koda Qamshin Aljanna ba bare su Shigeta ,....yanzu dama Cewa tayi karka Gayawa kowa Ka gaya mn ?, Tho ka nemi wani kudin ka Siya mata wani ..Bace mn da Gani"

Da sauri ya juya ya bar wajen yayinda na nufi part dinmu nayi wanka na Sauya kayana Zuwa Dogon Riga Brown mai ratsin Milk, Cikin kayan da na bari a gidan.

Sannan na dauro Alwala na Gudanar da sallar La'asar Don na farajin ana kiraye kirayen Sallah..

Ina Gamawa Na fito na Samesu A parlour suna Tattaunawa.

Na faki Idanunsu na shige dakin Umma ,Sai nayi sa'a Ta hada wata hadaddiyar Coffee mai Zafi kuwa ta zuba a Cup ta rufe da Paper hannu nasa na cire marfin sannan na Debo maganin da na shigo dashi Na 6are Sannan na saka Cikin Coffeen saida na tabbata ya narke sannan na 6oye Raguwan Maganin Cikin rigata na Fito ina Waige .



Aikam sai mukaci karo da ita a Hanya nayi Murmushi tareda fadin
"Dama nazo nayi mki Godiya ne ,Dan wake yayi dadi Gaskiya babu makusa"


Ta Harareni tareda Fadin
"Zanyi maganinki ne Shegiyar Yarinya kawai mai kamada Aljanai"

"Eh nadai fiki kyau ,Jibekifa Hanci kaman whistle ga kuma Bakin nan Kaman Ganda Ke Gaba daya Siffarki fa babu fasali Anya kuwa kina duban madubi kuwa?"

Na fada don Na Cusa mata baqinciki,kuma na Samu nasara don Kuwa ta kai iya wuya.

Roban Sugan da ta Riqo ta wulqa mn na chafke tareda Artawa a Guje ,itama ta bini, ni ko tunanin Cikin ma Banayi don Harga Allah nakan manta da cewa da Wata Ciki a jikina .

Haka mukayi ta wasan Tsere a dakinta Tana bina da niyyar kar6ar Robar Sugar ni kuwa ina gudun Ceton rai.

Saida nayi laushi na Saki Robar Nayi General parlour inda su kakus suke zaune suna tattaunawa .


"Yayan Hafsah zoka koma dani Inada lecture 4:00 Gashi yanzu 3:50 "

"Kinyi sallah ne?"
Abba ya tambaya yana dubana

"Eh mana, Tun tuni mah"

"Okay Aaryaan ka tashi ka kaita Allah ya tsare hanya"

Miqewa yayi yana msu sai Anjima ,saida yaje Dakin Umma yayi mata Sallama sannan muka kama Hanyan Zaria,

Muna hanya Ramlah ta kirashi Suka Sha hira Abinsu Ina jinsu


Mutane dayawa na ganin Aaryaan a matsayin miskili Wanda Bai damu da magana ba ,Amma idan kukaga yana waya da Ramlah ko kuma yana tareda ni sai Kayita mamaki kana cewa Anya Aaryaan ne kuwa....


A lokacin da muka isa Zarian kai tsaye Makaranta ya kaini har sun fara lecture din mah.


Lokacin da muka koma Gida kuwa nasha Tsokana da Tsiya kalakala wajen su Hafsah Wai daga Ganin miji har na bishi dukda na gaya msu su Abba fa mukaje daukowa basu ragamn ba, daqyar na qwaci kaina a hannunsu nan ma sbd na hanasu tsarabar da ya zo mn dashi n shine fa suka shiga taitayinsu suka fara Roqona.....




.....



WasheGari ma Tun da sassafe Aaryaan yazo , ya dubani Don ya lura ina Buqatar mai kula dani Sosai ma, idan ya barni Ni kadai zan Rinqa horon kaina da yunwa ne kawai.



Saida ya Samu naci Abinci sannan hankalinsa ya kwanta ya tafi.



*****


Hilaal ne Gaban Hajiya Larai ,Ya tangwashe qafafunsa tareda sunkuyar da kansa.


"Hajiya Ki yarda dani ki gwadani da yardar Allah Zan nemo maki Su duk inda suke a fadin duniyar nan, Nidai Burina Na samu Aiki Ranki shi Dade"


Hajiya larai tayi murmushin isa, ta fara magana Cikin shauki tareda Shafa Kan kafadun Hilaal dake zaune a qasanta

"Taso ka zauna anan "

Ta fada tareda nuna masa kusa daita, babu musu yazo ya zauna, Amma a tsorace Don Yanda Take wani shafashi fa Idan ba'ayi hankali ba ,Zai iya kwafsawa yayi mata Zuban Wulaqanci donshi ba dan iska bane๐Ÿ˜ซ

Ta cigaba

"Kaifa danyen Saurayi ne ,baka gama dafuwa ba ,gakada Jini a jika,ina matuqar son Mutane irinka Amma ba ta wannan Fannin ba ta dayan 6angaren"


Aaryaan dake kallon komai cikin Computern sa yayi dariya sbd yanda Yaga Hilaal yana Wani Yatsine Fuska Sakamakon sabon Al'amarin da ya fara Gani.


Yayiwa Hydar Text Alamar Aiwatar da nasa Show din kafin Hajiya Tayiwa Hilaal Fyade๐Ÿ˜…

"Ehm....Hajiya....do..."


Maganar ta ta katse ne Sakamakon shigowan wani 'Dan Saurayi yana Sanye da baqaqen suit ya dan Russuna a Gabanta

"Ranki shi Dade kinyi baqo"


"Kace ya shigo " ta bashi amsa.

Hydaar ya shigo Cikin Shigar Crazy shirt da crazy Jeans hannun sa Riqeda Wasu takardu.

"Eh Hajiyo ,Allah yasa nazo da sa'a ,Eh mana Nifa na gama Shiri na Ke kadai nake jira Kawai Eh kingane ai " ya fada tareda dage mata Gira daya Yana 'Yar dariya.


"Waye wannan kuma?"
Ya fada yana Nuna Hilaal kaman bai San sa ba.


"Yazo Neman Aiki ne"

Hydar ya gyara Na'urar daukan Hoton dake Jikinsa Ya fuskanci Hajiya larai Sosai yace

"Hajiya abar Wannan shashashan Anan Eh Yanzunnann zamu Gama Mu dawo Na gama Gyara mana ko ina a Gidan na ,yanzu ma a matse nake am totally over Fed with maganin Mazaaa......."













TOFAH

WANNAN WANE IRIN TARKO SU AARYAAN SUKA DANA WA Hajiya?๐Ÿ˜˜



KUNA GANIN WACE TSIYAR ZA'A KWASA IDAN UMMA TASHA Coffeen nan...๐Ÿ˜‰




GASKIYA ZAN BAR TYPING TUNDA NA DAINA GANIN SHARHIN KU ,MAFI YAWANCINKU KUN BAR SHARHI SAIDAI KUYI COMMENT DA STICKER KO THANKS, BAZAKU BAYYANA ZA'AYINKU AKAN PAGE DIN BA ,CIKIN KU 'DAIDAIKU KE BAYYANA RA'AYOYINSU


KUMA COMMENTS DINKU SHIKE BANI QWARIN QWIWA.

Afwan pls ,a last update na sa cewa an bawa Aaryaan matsayin inspector Har Nace qaramin mataimakin CP, tho ba inspector nake nufi ba ,ACP nake nufi.


Haka kuma 3star bane ACP rank ne....

Thanks๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜



2ND NOVโœ๐Ÿฝ
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 60_*



















Hilaal ya Miqe a Fusace tareda Dagawa Haydar Hannu Cikin zafi

"Dakata Malam ,Inace anan Ka sameni , so I don't Fucking care akan naka Uzurin Dalla Malam bamu Waje ,in mun gama saika shigo Kayi naka uzurin...."


Larai ta katseshi da cewa


"No...No...No...No....no, ai abun bai kaiga hakan ba ,Stacky"


Ta qwalawaWani kira.


Nan danan Wani Dan saurayi ya shigo Shima Sanye Yake Cikin baqar Suit

Ta nuna hilaal daketa faman huci tace

"Ka Bashi Katin SirBala ,Kai kuma ka tuntu6eshi akan maganar Damuka fara, Zai baka Aiki Cikin sauqi Amma sai ka bi Sharudan dazai Gindaya maka!"


Mutumin da ya shigo ya Dan Russuna Sannan ya fice.

Babu jimawa Ya dawo dauke da Wata 'Yar card ya miqawa Hillal ,hilaal ya kar6a yayi Waje


Yayinda Hydar ya kalle Hajiya Larai yace

"Hajiya mutafi ko"
Da tho ta Amsa Sannan Ta Shige Ciki babu jimawa ta Fito Sanye da wasu Arnayen kaya sai Qamshi Ke tashi a Jikinta.


Hydar ya kauda kansa tareda yin Auzubillahi Cikin Ransa.


A tare suka Fito tareda Shiga Cikin mota driver yaja Sukayi Waje, wasu motocin suka biyo bayansu.

Hydar ya zaro ido
"Hajiya ya naga harda Excorts ,bayan Saboda su Zamu bar Gidan"


"Eh a Waje zasu Tsaya ,Bana iya Fita Batareda Excorts ba Shiyasa"


*Danqari* Hydar ya fada a ransa

Yayinda Aaryaan dake kallonsu ta cikin Computer sa ya jingina kai tareda Turawa Isma'il saqo.



Wani irin Burkin da Driver yaja ne yasa duk suka jakata Suna kallonsa

"Lafiya" Hajiya Ta tambaya a 'Dan Rude.


"Hajiya Wani Dan iska ne yasha Gaban mu, Gashi ya qi tafiya"


Hydar yaja tsaki tareda Bude murfin qofar ya fita yana Huci ,itama Hajiya ta Mara masa baya yayinda Excorts Dinda Suka Nufo tare ma sukayo Wajen Suna tambayan lafiya.


Isma'il ya fara magana Cikin Gauron hausarsa ,Wanda hakan yana daga Cikin shirinsu .


"Ke den Ubenki baki Gani ne?, She Oya wereni ?, Abi Olori Burukun shewo Omoyi ne?,๐Ÿ™„ (wait ohh bafa zaginku Nayi ba ,Da Hajiya Larai nakeyi๐Ÿ˜…) Idon ki ya siyayene Bekiga Motana Tefiyane ba zeki Yi over taking..."


"Kai Dalla Rufe mana Baki ,Kana Wani Zubo yare sai kace Wani Sabin Kamu ,Wallahi kaci sa'a Yau Am not in the mood da naci Kutumar ..."


"Dakinci kutumar me?, Ni kike zagi?" Nan fada ya kawre tsakanin Hydar da Isma'il yayinda Excorts Suka fara rabon fada.


Junayd ya sadado ya baza Teargas ,nan Wuri ya kuma hargitsewa dama su Hydar da shirinsu sukazo Shiyasa Suka Rufe Fuskan su da mask dindake Aljihunsu ,Anan suka Sami nasarar Sace Hajiya Larai.


******


"What!.....Yaushe?, innalillahi wa'inna ilayhirraji'un ....yanzu kuna wane Asibitin ne?, .....Maganin zubar da Ciki?.....How comes? ....Allah ya bata lafiya ...... Zataji Ganinan zuwa mah....okay bye"



Yana Sauke wayan ya Dunqule hannunshi ya kaiwa Bango Wata wawan Naushi ,Yana Huci.

Lokacin da aka Ambaci Umma tasha Maganin zubarda Ciki Cikin Abinsha , Munayferh ce ta fado masa A rai Tabbas babu Wanda Zai iya Aikata 'danyen Aikin nan Inba ita ba,Shifa akayiwa Laifi Amma tafishi Daukan zafi akan lamarin ,Meyasa Munayferh ta Raina masa Uwa ne?, Meyasa bata Shakkar aikata Abinda Ranta keso Koda kuwa Cutarwane Ga wani ?, bazan barta ba!, I must teach her a lesson of her life ,Dole saina dauki mataki"


Ya fada yana qara kaiwa bango Naushi Da qarfi, daidai lokacin da Hilaalya shigo.


"A.A mun kamata fa, Mun hadata Da yaran nan ,Amma A ke6ataccen daki don Wlh Matarnan Tanada Hadari Sosai mayyace zata iya cin mutum 'danye"


Ganin sai zuba Yake yaqi tanka mashi, Sai famanhuci yakeyi yasa yadan matso Gareshi yana Fadin


"AA lafiya?"


Tsaki Aaryaan yaja tareda Daukan Key din motarsa tareda Wayoyinsa yayi hanyar Waje Batareda yayi magana ba.


Binshi Hilaal yayi don Gudun Abinda zai iya kaiwa ya komo, don yasan Abokinsa idan yana cikin Fushi baya iya driving Gashi Da Alama Fita Zaiyi Cikin wannan yanayin

Amma sai ya dakatar dashi cikin tsawa.

"Kai yadai?, Kana bina naci bashinka ne?"

Hilaal ya daga hannaye tareda Girgizakai

"A'ah Amma babu inda zakaje Cikin Fushi"


"Ahbi?.....Ohkay" ya fada yana qarasa Wa Ya shiga motarsa yayi mar key yaja ya Tafi.


Hilaal na qwala masa kira Amma bai tankasa ba.


Kai tsaye Gidan da muke zaune ya nufa Batareda Yayi sallama ba yasa qafa ya Turo qofan Da Qarfin sa.



Janaan da Hafsah dake zaune a palour suka dago Suna Dubansa a razane.


"Ina take" ta tambaya Cikin muryansa mai tsoratarwa.


"Ta Fita" Hafsah ta bashi Amsa

"Ina taje?"

"Taje Siyo Gurgurune"

"A ina"

"Wlh bansani ba"

Ya cije lips dinsa da qarfi tareda Furzar da Wani huci.

"Ta tafida Wayanta ne?"
"A'ah ta barshi a nan ,Amma ta tafida na jaanu".

"Okay" ya fada tareda juyawa ya Fice abinsa


Janaan ta Dafe qirji da qarfi tace

"Na shiga Uku ,Nyfee ka Qara tono wani fadar ,Kome tayi masa Oho!"


Hafsah ta ta6e baki tareda fadin Koma menene Sunfi Kusa, Haka nasu Salon Soyayyar Yake yau fada Gobe shiri"


Gabaki daya sukasa Dariya tareda Tafawa.


*****

Driving nake hankali Kwance Yayinda Airpod Ke saqale a kunne na inajin Waqa.



Wayan Janaan Dinda Nayi Connecting da Airpod dina Ya dauki Ruri


Nasa Hannu na dauka tareda Dubawa

Inlaw Nagani a Rubuce a screen dinwayan hakan yasa na fahimci shine me kiran ,Dan ta6e baki Nayi kafin na dauka a Raina ina tambayan Kaina meye dalilin kiran Numbern nan dayayi.


"Ke ina kike?" Ya tambaya Cikin Muryan sa mai ban tsoro.


"Ina inda ka Aikeni" na fada ina Hararar wayan.


"If I Ask you for the second time and u Give me same Answer, am gonna Deal with You... Volitant"


Shuru Nayi Batareda na Ansashi ba ,inajin yanda yake Fitar da huci daga Gani

Please Login or Register in order to submit comment