Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dazun, yagaya mn wani mummunan labari , kinji Wai An Sace Hajiya larai ,shima Malam bala ance har Gida Akazo aka Sace shi... Ni ba ma wannan ya dameni ba ,banida matsala dasu Gabaki dayansu na Rufe Bakinsu babu Mai Iya Ambaton Sunana inma Hukumace ta kamasu don Sanin Sirrin mu ,Amma Tsorona daya Kada Ace Yaron nan ne ke kamasu don naga Tunda Ya shiga Aikin 'yansanda Ake Kama mana Yara , Gashi yanzu sun bar qasar Sunce India suka tafi Amma jikina na bani Cikin qasashen da Muke Binne sirrikan mu ya tafi ,donshi ba kowa yake Gayawa Abubuwa irin wannan ba ,don ko ubansa sai daga baya yake sanin yayi tafiya yaje India , wlh na tsorta Yaron nan ya fara bani tsoro ,Kinga har Gida yaje ya Kama mutumin mu Tsohon ACP HAFEEZ UMAR ,yanzu haka yana nan an yanke masa Hukuncin daurin Raidarai Sakamakon kisan kan da ya Aikata, Wanda ada babu wani dan iskan Dan sandan da ya isa ya tunkare su , komai sukayi Daidai ne a hukumance dukda kuwa Duniya na ganin Abinda suke aikatawa ,A Gaskiya hawwah Ina Tsoron Ranar da Aaryaan zai Zo Gareni Ya kamani ,ya daura mn Handcuff a matsayin Mai Laifi Wacce a sanadinta ya shiga Aikin 'yansanda , Ta6di da duniya ta Dauka anta yadani a Gari 'da ya daure Uwarsa ....hello kulu kina jina?"


Hajiya kulu taja Ajiyan zuciya

"Hakan bazata ta6a Kasancewa ba, ya kamata Kiga dodonki Don shine kadai zai iya Haska mana qasar da ya tafi ,da kuma Abinda ya kaishi qasar inaga shine Kadai mafita ,kindaiga yanda Muka Raba Uwa da 'ya so Raba Uba da 'ya bazaiyi mana wahala ba"


Sai a yanzu InnaRabi tayi dariya.


"He he....Lallai kin kawo Shawara tabbas sanin inda suke shine mafita ,Ni anya Haleemah ita ta haifi Ramlah kuwa ?"


"Me kika gani?"

"Aahh, tho baki ga yanda ta tsane ta bane?, kin ta6a ganin inda Uwa ta tsani 'yarta?, koda kuwa bata Santa ba akwai Connection dake yawo a jikin mutum Wanda ke haddasa Qauna tsakanin Uwa da 'ya ,Wlh idan da bani na Bada Umurnin akayi komai ba ,kuma da Kaman da sukeyi Wlh da nace ba ita ta haifeta ba"


Kulu tayi dariya tace

"Baqin hali ne irin nata ,ta dauka Jinina ce shiyasa Take Gasa mata Aya a hannu ,Dama ance idan zaka Gina ramin mugunta ka ginashi daidaika , idan kuwa ka Gina Wanda yafi qarfinka thofa Kai zaka Afka Ciki turawa Sukace Cut ur cloth according to your Coat......Shashasahr banza harda ita a Koranta a Gidan nan"


InnaRabi tayi dariya Sosai, Hajiya kulu ta Dora da cewa


"Yawwa Umman Faruq, mezai hana a Gamada JY ,kinga Muma sai mu huta Ma'aikan suma Su huta, Ma'aikata 1500 fa Kika zuba suna Tsaron just Single Person For that matter Sai kace bakisan zafin Kudi ba"


InnaRabi ta bushe da dariya kaman bazata daina ba daga Bisani ta fara magana a dake kaman ba ita ta gama sheqa dariyannan ba..


"Kulu idan na kashe Mutumin nan faduwa nayi ,babbar faduwa ma ,Na farko Shike biyan dukkan Ma'aikatan nan Salary ,Don ni ban ta6a Fitarda Sisina na Basu Suyi wani Abinda ya ji6inceshi ba , Na Biyu Cikin kudin da muke Tilastashi ya tura mana Every month nakan samu nawa kason ,na Uku Jininshi da muke deba Muna kaiwa Dodo every Saturday Anda Last one Banason ya mutu Mijina ya Auri Matarsa Don Shi namiji ba kunya Gareshi ba ,kaman Jira yake wata qaddara ta raba shi kuma yayi ma Abun wuf ,Ina matuqar Qaunar Mijina kuma ina kishinsa , idan na saki ya Auri Jeedah To wlh kashina ya bushe don Na tabbata Ba qaramin so zai Nuna mata ba, take a look at yanda Yake tsananin Son 'yarta Fiyeda Yanda Yake Qaunar nasa Jinin ,yake kuma Nuna tsananin Kukawarsa akanta Fiyeda Sauran Inaga ya Auri Uwarta inaga @that season sai mun cika Form zamu Rinqa Ganinshi, Ni wannan ba damuna yayi bamah Cus nasani duk Cikin 'ya'yana Babu nasa a Ciki so I have nothing to bother about ,Burina na Mu cigaba da yanda Mukeyi a da , inyaso sai mu Cigaba da Sending Pics Dinsa as usual yanda Muka saba Don kar suyi zaton Ya mutu neh ,Anda lastly ki Kira Saleem ki jaddada masa Yasa ido akan Mutanen nan don ina ji a jikina akwai 'dan leqen Asiri Acikin su , Sannan kuma nayi Sacking Doctor mai Kulada Nurse Dinnan, Cus Kwanaki ya bata Pure treatment Wanda Yasa har saida ta Motsa hannayenta For that matter ohh..."


Haka suka cigaba da tattaunawansu akan Wadannan Abubuwan dake shirin Tunkararsu...


*****


Door bell dinda Aka danna ya farkar dashi daga Daddadar barcin da yakeyi, a hankali ya sauko yana Murza ido.


Ganin Haske yasa ya ware idanu Dakyau ya kai dubansa ga Agogon dake manne a bangon dakin , Qarfe 7:30 ,Kallonsa ya maida Gefensa Yaga wayam babu kowa ,wato Ni Tuni na tashi kenan ko na tasheshi Gashi yanzu yayi missing time din sallar Asubah.


Qarar Ring Din da ya kumaji ne yasa ya Tashi yana yatsine Fuska.

"Waye " ya tambaya a daqile kaman yana Ganin mai Dannan qararrawar.


"Ni ne" muryan saleem da yaji yasa ya ja Yar Guntun tsaki ya dau Remote ya bude Qofar .


Baice komai ba ,yana tsaye sai kallonsa yakeyi , murmushi saleem yayi ya bashi Hannu sukayi musabaha sannan ya Dauko wata CD plate ya miqa wa Aaryaan batareda yace komai ba ,daga Gani shima Saleem yana da Ji Dakansa Ganin Yanda yake abu Cikin Qasaita da shan Qamshi.


Amsa Aaryaan yayi ya juyyuya shi yana ta6e baki ,kafin yayi wata magana har Saleem ya 6ace.


Ta6e baki Aaryaan yayi a Zuciyar sa yace ~Don't worry buddy don ka bamu masauki Kake wani shasshan Qamshi sai kace Wanda ya bamu Kyautar duniya?, A yau Dinnan zamu bar maka Ultimate Cage dinka which serve as our Ultimate aspiration ,banza township Goat kawai ,ni in banda inada tabbacin kana Cikin 9ja Force ni mai zai sa na Hada Aiki dakai?, banza jaki kawai mtsww~

Yaja Tsakin a Fili yana Hararar hanyar da yabi.


Komawa yayi yayi taking shower dinshi sannan yayo Alwala ya Gudanar da sallah Tareda Istigifari na jinkirtawan da yayi...



Ni kuwa ina Zaune bisa sofa Ina kallonsa Banda zagi babu Abinda nake Auna masa a Raina ,


Ina kallonsa har ya Dauko Plate din CDn yayi fixing tareda Connecting dinshi da TV....


Abinda na Gani yasa na Tashi a Razane ,Razanar da nayi yasa ya dubeni A kaikaice yace

"Keh koma sitting Room"

Ban tanka shi ba haka kuma hankalina bai bar TVn ba.


Cire plate din yayi yana Jan tsaki , Da sauri na Miqe na nufi inda yake ina 'dan Dingisawa ,Yabini da kallo don baisan Abinda zan kumayi ba.


CDn hannunsa na Fizge Kafin yayi wani Yunquri har nasa a CD player , bai hanani ba ,Dakansa ma yayi Controlling dinshi.


Fuskar Daddy na ya bayyana a Fuskar Television din Cikin yanayi na tsananin wahaltuwa yake fadin.


"Aaryaan ,Saleem ya Gaya mn kana qasar nan , Please karkayi Yunqurin tunkarar Wajen nan kai daya , Mutanen suna da Matuqar hadarin Gaske ,kai daya bazaka iya da Masu tsaro har dubu da Wasu 'Yan kai ba ,Gashi kowannensu Yana dauke da makamai ..... Anda Maganar da Ya gaya maka Akan Matar ka Gaskiyace , Qanwarka kake Aure ,saleem yana dauke da Muhimman Hujjojin da zasu Bayyana maka hakan ,daga Qarshe ina Roqon Alfarmar ka ,ka kar6o Ajiyan da na bawa beetee na tabbata Shima Yanada Muhimmanci Kuma zai taimaka maka Wurin Gano Wa'enda suka Aikata wannan Aika Aikan...."














Waiting for ur comments

Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ


13th novโœ๐Ÿฝ




Bintou๐Ÿ–ค
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~


๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€

NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ† *AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป

_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_ _{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}


._ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...

*_Chapter 65_*


*Zarian Girly group wannan page din naku neh๐Ÿ˜˜*







Abinda Aaryaan ya iyaji kenan hannu na rawa ya dau Remote ya dakatar da Play din.

jijiyoyin jikinsa sunyi rada rada, wani irin kuna yake ji a ransa, hancinsa tayi jajazur ta kara tsini, haka idanuwansa sun kada sosai sunyi ja ,Lokaci guda Gaban sa ya fara Dukan tara tara ,da qarfi ya shiga Fadin..

"Nooooooooooo Never ,She's not my sister, Noooo! Never !, never!!."

Gaba daya ya Susuce ya fita daga Hayyacinsa ,Jin shessheqar kukana yasa ya maida Dubansa Gareni.

nikuwa ban ma Fahimci inda Maganganun daddy Suka nufa ba ,Duk daukana Ni dince sustern nasa Cus Kunsan Nidin Cousin Dinsa ce ko, Dalilin da ya Sani kuka kuwa shine Yanda naga Daddy na Maganar kamar wani Sauna Yana Lumshe idanu kaman Bugaggen Mashayi ,Gashi ya qanjame ya Rame kamai Mai cutar AIDs ,kuka nakeyi ina qarawa , Burina a Halin yanzu bai wuce ya Fito ba.


Tsawan da ya Daka mn yasa na dago a 'dan Tsorace ina kallonsa , gabaki daya ya koma Tamkar ZAKI idanun nan sun Koma tamkar Wuta don tsananin 6acin Rai ~Ran maza ya 6aci~


Ya Nuna ni da 'Yar yatsa

"Keh ,Idan na sake jin Nishin kukan ki anan Saina karkaryaki ,Na 6alla qasusuwanki na Watsa kwararo ,idiot Shameless lunatic thoughtless wretch ,Useless and ingrate Wife kawai Abege Get Loss From here"

Ya qarashe Masifar da Rushewa da kuka Wanda hakan yayi matuqar Gigitani ,Ban ta6ajin Yayi zagi irin haka ba Ga kukan da yakeyi kaman Ransa zai fita ,Ni sai Abin ya zama mn strange ma ,The Whole Aary in Tear Me ke Shirin Faruwa kenan, tabbas Akwai Gagarumin Matsala , Abinda Tunani ba yanda bane.


Ringing Din wayansa ya katse mn Tunani na ,Baiko kalle Fuskar wayan ba bare yasan mai kira ,kawai dauka yayi Cikin zafin rai ya fara masifa.

"Get the Hell out of my phone trash"

โ€ขThopa Wani yace ka dauka?๐Ÿ™„โ€ข


Yana gama fadin haka yayi jifa da wayan Nan take ta tarwatse ,Cikin zafin nama ya miqe ya nufi bathroom yayi wanka a gurguje Zuciyar sa na Tafarfasa kaman zata qone ,har yanzu bai Amice da maganar daddy da saleem ba Kuma ba yanzu ya shirya kar6ar Ajiyan dake hannuna ba ,Cus ya daukeshi ne a matsayin Waste of Time kawai....


Ina nan indanake banda kuka ,Banda Ajiyan Zuciyata babu Abinda nakeji.


Tsaki yaja Na Ciro kayansa Ya shiga sawa yana satar kallona ta mudubi ,yanda na wani kifa kai ina Kuka mai Tsuma heart....


Daga nesa ya tsaya yana kallona ina kuka nan take Zuciyar sa ta tsinke , Ya kamata ya kwantar mn da hankali kafin ya tafi, ya kamata ya Sani dariya koda sau daya ne.


A hankali ya tako har inda nake zaune saman sofa ya zauna kusa dani Jin an zauna Kusada ni yasa na dago Jajayen Idanuna ina kallonsa batareda nayi magana ba kuma Hawayen Basu daina Fita daga Idanuna ba.


Dariya ya shigayi yana tafa Hannaye ,Kaman Bashi ya Gama hawaye yanzu ba ,Ni kuwa Chak hawaye na suka tsaya suka daina Zuba na zuba mshi idanu kawai,Saida yayi mai isarsa kafin ya tsagaita ya nunani da 'Yar yatsa.

"Ashe ke matsoraciya ce ,you Always Prove you're strong so what Make u cry About this Silly Play?, Tell me naah ni na shirya komai?, It's Just a Game And You Fail it ,so Am gonna Go with my Gift dama na Saka Gift ,Kyauta mai tsoka Shoky babe You done loose"


Kallon mamaki da Ka raina mn hankali na bishi dashi kafin nace

"Which Type Game be that?, ya za'ayi naga Fuskar daddyna Yana Magana In need of help kuma kazo kana wani Maganar Game ,To hell with you Anda Game"


Dariya ya kumayi Cikin yanayi na 6oye damuwar nasa yace

"Love...kinsan ni I'll never lie to you , so ki yarda ,dama suna tareda Saleem nine na Bashi Umurnin yayi hakan don na Gwadaki Gashi naci ,Raman da Kikaga Yayi ma ba Real bane Editing ne , lemme tell you a Good news mah , Daddy is Gonna be back Tomorrow inshaallah, I promise You"

Ya qarashe maganar Da wani Smirking Wanda Akace yafi kuka Ciwo.


Sosai na Gamsu da bayanin sa ,Jin Gobe za'a ku6utar da daddyna yasa na Rungumeshi Cikin tsananin Murna , na qanqameshi Sosai kaman Zan Koma jikinsa ,Daqyar ya Samu ya Rabani da Jikinsa


Na kalleshi ido fal da hawaye

"Yayana Ina son daddyna Please keep Your Promise, banason na Rasa shi" kuka ya sake Kufce mn .


Bazai iya Jure kukana ba ,Shiyasa ya qara Jawoni Ya mannani jikinsa ,saida nayi kukan mai isata sannan ya Rabani da Jikin nasa....


Kallona yayi ,a ransa kuwa yace Ya zama Dole Daddy ya Fito Ayau Dinnan ko Gobe , ya gaji da Rainin hankalin Saleem dole ya cika mn burina ,ba Masu tsaro dubu ba , sunkai ko million saiya Gama dasu Dole daddy ya Fito Dole ne.


Wata irin iska ya furzar daga bakinsa , ya sunkuya gabana yayi kneeling bisa Qwiwowinsa , yasa hannu ya dage Rigana daga qasa ,Banyi Yunqurin hanashi ba , illa ma kallon da na bishi dashi.

Hannunsa yasa ya Shafe Cikin Wanda Ya taso Kaman ba na wata 4 to 5 ba

Ya fara magana a raunane.

"Dear son Or daugher ,Am Going But Am gonna be back , you cant be Orphan No , Am still Your dad Ni ubanka ne kaji...Zan dawo gareka Bazan mutu ba ,Baby kayiwa daddyn ka da Grandpanka Addu'a Kaji..."


Sai ya dago ya kalleni ,ya ko ci sa'a nima shi nake kallo ,inayi msa wani irin kallon zararre ko sabon shigan Haukan nann don Gaba daya Ya fice hayyacinsa ,Ban ma iya Gane Inda zancen sa suka nufa ba ,Bare kuma Readers Masu karatu,ya Cigaba da Cewa

"Sulthy promise me , promise me you'll love my child, you'll take care of him, you'll be a best mother for him. Give him a good future, I trust You sulthy nasan zaki kula dashi koda bayan raina ne ,Bare zan dawo ma Bazan Maida 'dana maraya ba ,I'll come back and Play with You son"

Yana Kaiwa nan ya Mannawa Cikin kiss ,Tamkar Mahaukaci haka nake kallon sa ,Hawaye Masu zafi na kwaranyowa daga Fuskata .


Shikuwa Ganin yanda Hawaye ke zuba a Fuskata Kaman an Kunna Famfo yasa yayi 'Yar dariya Cikin Sigar zolaya Yakecewa

"Baby Kuka nayi mki kyau fa ,Kaman kar ki daina ,Kinga nayi miki two zero ,Fear Fear kawai Ashe duk kurin banza ne".


Ya gaya yana Kanne mn ido daya ,qaramar dariya nayi ,Still na kasayin Magana.

Agogon sa ya dauka yayi Hanyar waje yana fadin , "Make sure kin Ci Abinci ,kin kuma Sha Maganin ki , karki wahalar mn da son"


Daganan ya Fice Abinsa , Ummie kadai ya tarar a qasa don haka sama sama suka Gaisa ,ya Fice yana Mishi Fatan Samun nasara don saleem ya sanar da ita Wasu Abubuwan.


A balcony ya tarar da Saleem yana zaune bisa Farar kujera ,Gabansa Farar Table ce saman sa kuwa System ce yana Latsawa hankali kwance.


Qarawa Aaryaan yayi ya kalleshi Fuska a Tsuke Cikin Kakkausar murya yace

"Ka bani Address din Gidan ,I'll handle Everything Myself"

Saleem ya Dauko wata 'Yar qaramar jaka wacce ke Kusada Shi ya Miqawa Aaryaan batareda ya dago daga kallon system dinda yakeyi ba ya miqa masa ya Kar6a tareda Binshi da kallo Cikin Neman Qarin bayani, kaman Saleem ya Sani kuwa ya Murmusa

"Check in ,Face Copy mask ne na Sabon Dr dinda Aka Chanjawa Nurse dindake Kulle a Gidan ,Nasaka An Sace mn Mutumin So Idan ka Sanya mask Dinnan Zaka Zama Shi sak a fuska , Ka duba Bag din zakaga wata 'Yar takarda Rules din Gidan ne A ciki tareda Names din Manyan ma'aikata Masu Aiki a Gidan ,As you can see sunana ne a Farko , so I'm their leader, nine shugaban su....Address na Cikin Envelope Dinnan , Be Carefull Guy Read the instruction First zan Biyoka Anjima ,here is My car key ,it can help u All the best "

Ya fada yana miqawa Aaryaan Mukullin Mota ,

Hannu Aaryaan yasa ya kar6i key din Hawaye suka taru a Idanunshi,

"Who're You saleem ?"


Saleem yayi 'Yar takaitaccen Murmushi yace

"That's not important now ,Just Go ,Zan biyoka okay?"


Gyada Kai Aaryaan yayi kaman Wani Yaro , ya dau Jakan Da saleem ya bashi Ya Nufi Parking Space......



****

Su Hilaal sun Isa Pakistan lfy ,Kuma Cikin sa'a anyiwa Ramlah Aiki ta Kuma Dr mahrooz Ya Rubuta mata ingantattun Magunguna don Shi ya saba Crossing ta irin wannan Cutar so he's perfect akan Aikinsa ,A Ranar Jirgin su Ya daga Zuwa LIOS ,dama Akwai Direct Flight daga nan.



*****


Zaune nake a inda ya barni kaman an dasani Babu Abinda na iya ta6ukawa Tunda Ya fita nake Auna maganganunsa Mai kamada Na bankwana ina Jujjuyasu a raina.


Wayarsa da ya tarwatsar agefena ya shiga Ruri ,kallon Wayan nayi kaman bazan Dauka ba ,sai kuma wata zuciyar Raya mn da na Daga ,kallon Screen din wayan nayi Sunan da na Gani Rubuce a Screen din wayan ya haddasa ma Gaba na faduwa.


LOML (Love Of My life) na gani Rubuce a screen din wayan ,kafin na daga har ta katse ,


Take Cikina ya bada wani irin sound ji kake Qulululu Gabana kuwa tuni ya fara dukan tara tara ,Hannu na rawa na zana Pattern Dinsa sannan na shiga Duba Recent call din Kafin na danna kirar har an kuma kira ,hawaye suka samu damar Zubowa daga Kunci na ,ina dagawa cikin masifa na fara magana

" don Uban....."

Muryan Umma da naji ya Sa na hadiye maganar ,Tareda sauke 'Yar siririyar Ajiyan zuciya ,nasa bayan hannu na goge Hawayen da suka gangaro mn.


"Son!"

"Bayanan ina kwana Umma" na fada ina Hararar gefe Kaman an Sani dole.

"Lafiya ,Uban wa ya baki izinin ta6a wayan 'dana ,har Zaki daga mn waya ,wato wuyanki...."



"Dakata Inlaw ,...Zaki fara ko?, tho am not in the mood today ,So Get the hell out of my Phone , if not .....you know the rest"


Umma ta kuma hayayyakoni da fadin

"Rufe mn baki shashashar banza wato ni kike gayawa Baki a mood ,kin maidani Abokiyar wasanki kenan ko Game mate dinki abi?"


Tsaki naja

"Inlaw hang the call" na fada a qufule.

Qin hanging tayi sai ma hayayyaka da ta kumayi.

Murmushi nayi mai sauti kafin nace

"Umma Nasan All this zafin ran da kike nunawa bai wuce , don nayi wuf da 'Danki ba ahbi , tho bari in gaya mki old woman kin jawa kanki ,Saina 6ata mki Yaro I'll spoil ur child ,Sai zan Mayar dashi tamkar Raqumi da akala a wajena ta yanda in kikayi masa magana ni kuma na bashi Umurni tho lallai Umurni na zai bi , Umma ni ba kamar Aunty Ramlah bace ,Ba Irina ake zagi a kwana lafiya ba ,daga yau karki sake kiran wannan Layin You're already blocked, so now hang the call , or you need more "


Ai kam na gama Rufe baki ta datse wayan.

Murmushi nayi ,nabi wayan da kallo a fili na furta Shameless Inlaw , saida na makata a blacklist kafin na bar masa wayan ina Jera tsaki.

***

Wasa wasa saida Aaryaan ya dau Tsawon kwanaki Uku bai Dawo ba, Gabaki daya na damu Na rame kallo daya zaka Fahimci Tsantsar damuwan dake tattaredani.

Ga Zazza6in da nakeyi time to time ,Ummie da Ifrah ne Masu kwantar mn da hankali , don shima saleem din bai dawo ba tun ranar ,Sosai mutanen suka shiga Raina Kuma ina jinsu Har cikin Jini na ,Gaba daya ma na dawo part dinsu da zama ,A kullum in na kalle Ifrah sai gabana ya 6ace Don Kamannin 'Yan Gidan mu da ta kwaso ,Ga yatsun hannayen mu da na Qafa duk iri daya.




Su Aaryaan kuwa Suna zuwa ya duba yanayin jikin nurse din , Nan take ya Fahimci Guba ake dura mata , nan take Yaji Tausayin Nurse din kuma yayi Alqawarin taimakon ta bi'iznillah , A Ranar kuwa saida ya Tabbata ya San Every movement na Ma'aikata kuma Masu tsaron Mutanen , Nan take ya Ari wayan Saleem ya kira 'Yan sandan da suka biyo shi a Sace yace Su kasance Cikin Shiri , nan yana fita ya siyo Hot pizzas Wanda zai Isa Dukkansu , Yabawa Saleem yace Ya gaya msu daga sama ne , daganan Zasu 6ingire da barci Sai su San yanda suka Sauya Ma'aikatan da 'Yan sandan da yazo tareda su ,haka kuwa sukayi a Ranar bayan sun 6ingire a wajen Suka Sace Daddy suka sanya wani a madadinsa sannan suka kwashi Ma'aikatan nan Suka Musanyasu da Wasu dukda kuwa basu kai yawan 'Yan daban nan ba......




***

Kaman dai kullum Zaune Muke a Sitting Room dinsu Wanda yasha furniture na Alfarma Muna kallon Wani Korean Series, Mai suna Doctors ,Ifrah sai surutu take tana Min bayanin film din don ita tuni ta kalla ,ni kuwa daga Uhm sai Uhm....


Ina zaune na qurawa TV din idanu naji Door Ring, da sauri Ifrah ta miqe tana fadin

"Ina zuwa " batareda ta tambaye ko waye ba.



Tana isa bakin Qofar , da Gudu ta Juyo tana fadin


"Lil sis ,Come oh Mr handsome is back"


Jin haka yasa bai miqe da sauri ina fadin da gaske?.


Ai ban qarashe magana ba naga Sun shigo , Shida Mutumin da ko da wasa banyi tsammanin Sake Ganinsa nan kusa ba.....



















Ohhh๐Ÿ˜ค







Manage This




Bintou๐Ÿ˜Œ

Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ





15th Novโœ๐Ÿฝ
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 66_*





Tsuru Nayi da ina kallonsa idanuna kyar akansa ,Anya shine ko Gizo idanuna Suke mn ,Kaman yasan Mamakin da nakeyi ,hakan yasa ya murmusa yace

"Beteee Am back"

Ai da Wani Uban Gudu na Isa Gareshi na Rungumeshi Qyam ,Cikeda Murna farinciki da Daukin mahaifin nawa Wanda na rabu dashi Shekaru Uku da suka gabata.

Take hawayen Farinciki suka zubo mn ,Shima idanunsa Sukayi jazur ,bazai iya misalta Farincikin dake tattaredashi a wannan rana ba ,Baiyi Zaton Zai sake Sani a ido ba, Don Shi Gabaki daya Ya qaddara a hannunsu zai mutu sai Gashi Allah cikin hikimarsa ya Fito dashi ,Gaskiya babu Abinda zai Iya sakawa Aaryaan sai Addu'a.


Ifrah ,aaryaan da saleem dinda shigowarsa kenan Kuwa Ido suka Zuba mana Suna kallo.

Mun dade a haka Ganin Bamuda Shirin Barin Juna yasa Aaryaan yayi 'Yar Gyaran murya tareda cewa


"Aboki Ya Isa haka a sakar mn mata"


Dama KO adachan Tamkar Abokai Suke.


Sakin daddy Nayi Ina Dariya

"Peetaa ,What a pleasant surprise , Daddy ban ta6a Tunanin sake Ganinka ba "

Na fada cikin dariya Idanu fal da hawaye.

Na kalli Ifrah dake Tsaye kusadani Tana Raba Idanu, Nace

"Feerah my dad is finally Back"


Ummie dake saukowa daga Staircase Ta Kallemu tace

"Baqi mukayi ne?"

Ifrah tayi Dariya tace

"Daddyn qanwata is Finally back ,Soon zamu koma 9ja"


Da mamaki daddy Ke bin Ummie da kallo Ya kalleta ya kuma kallon Aaryaan da ya Riqe Hannu na yana Shirin qarasawa Parlon


"Aboki Haleemah ta biyoku ne dama?"


Da mamaki Ummie ta maida kallon ta Ga Daddy Wanda Ke dubanta Dubana mamaki da Al'ajabi ,kafin tayi magana Har ya rigata da cewa

"No Daddy , Mum din Saleem ne"

Ummie da tayi Suman tsaye ta Waro ido Cikeda Tsananin mamaki tace

"Wace Haleemahn kuke Nufi?"

Daddy yayi murmushi lokacin lokacin da saleem Ke nuna mshi Seat Alamar ya zauna , Ummie ma ta Dawo Kusada Saleem ta zauna ,Duk Muka zauna muna jiran Amsar da Daddy zai bada.


Daddy yace "Haleemah mahaifiyar Aaryaan nake nufi ,Tabbas idan Ba Ke bace Kuna matuqar kama sosai"

Ya qarashe maganar yana duban Ummie da Aaryaan da duk suka kafeshi da idanu ,Tabbas Suna kama sosai Idan ba da don nasan Mun baro Umma a 9ja ba da A lokacin da Na ganta sai na Rantse Ummace.


Muryan Ummie Nayi ta fara magana A 'Dan Rude

"Don Allah baqo ,Ya asalin Sunanta ,Ehm....ina nufin ya sunan Mahaifinta? Ko baka sani bane"


Daddy yayi Murmushi Jin yanda Mutumiyar nan ta wani rude tana tambayansa

"Mum saleem ,bake bace ,Kamace kawai"


Ummie tace

"Inada 'yar Uwa mai sunan nan wlh ,kuma muna matuqar kama da

Please Login or Register in order to submit comment