Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa Komai .

Da taimakon Shawarar Drs da Nurses Nake Shayarda Yaran kuma a lokaci Guda nake Kulada Cikin dake Jikina ,Kasancewar Cikin yazo da laulayi Sosai Sai na bar zuwa makarantar Gabaki 'daya Da cewar zanyi Deffer In Allah ya saukeni lfy sai na koma. ..


Dukda Kuwa Na Bar zuwa makaranta hakan bai hana su Teemah da sauran friends dina Zuwa suna Dubani ba ,kasancewata mai Saurin shiga rai da saurin Sabo da mutane ya yaran nawa Allah ya zuba Msu farinjinine Shiyasa gidan nawa baya Rabuwa da mutane .


Haka kuma kasancewar Mutanen Garinn nasuda katsalandan Da shiga shara ba Shanu Sai tafiyar mu tayi daiยฒ dasu Nake jin dadin zama dasu ta fannin Harshe Kuwa Nan banida Matsala Tunda Inajin Hindi kuma Mutanen Yankin sunfi Jin yaren hindi da larabci akan wani yaren ,kuma duk inaji ina Ganewa.


****


*Nigeria*

Zaune Yake a Katafaren office dinsa wanda yasa Kayan Alatu na More Rayuwa ,komai yaji ,Idan ka Ga Office din Sai ka Rantse Ba a qasar Mu Nigeria yake ba Sbd tsantsar Haduwa da tsari

Knocking dinda Akayi ne yasa ya dago daga Kallon Hasken wayansa da yakeyi ,ya Qurawa Qofar ido Saida Aka sake Buga qofar a karo na biyu Kamann bazaiyi magana ba .


Sai Ya ja numfashi, Murya Chan qasaar Maqoshi yace
"Come in"

Haidaar Ne ya Shigo Da sallamarsa ,Yana sanye Cikin Kakin 'yan sanda , Ya jawo Kujerar dake Fuskantarsa ya zauna Yana Dubanshi.


Shi kuwa Aaryaan Ko dagowa baiyi ba Bare ya dubeshi , Inda sabo Hydar ya saba Da Halin Abokin nashi ,don haka ya Kawdakai Tareda ta6e baki.


"A.A Abba ya Kirani Dazun Yace yana buqatar ganinka Cikin gaggawa"


Bai dago ba ,Kuma Bai daina Kallon wayansa ba, kai kace badashi Akeyi ba , qarar Wayan Aaryaan ne ya Katse masa Abinda yakeyi Cikin wayan ,Ganin sunan Abba ne yasa ya dan ja 'yar qaramar tsaki ya share Kaman bazai daga ba , Saida Aka sake Kira a karo na biyu kafin ya daga yana hararar Hydar .


"Good Morning Dad..."

"How is Ur night son "


Bai Amsa ba illa ma shurun da Yayi yanajin 'dacin Katse Masa Kallon da Abba yayi .


Shima abba shuru yayi yana Jiran Amsar Sa Amma sai Yaqi magana , Aaryaan kuwa Ganin lokacin na tafiya yaaa ya dan Ja numfashi ,Murya Chan qasa yace

"Dad ina Aikine Idan na samu time ,i'll Call u back"


"No Aaryaan ,lets Talk now , Yaushe Rabonka da Gida?, Almost 6mounths Fah ...."


"Ohhhh dad Am i a baby?, I think Ko shekara zanyi ba tareda na leqo kD ba ,Bazaka samu matsala dani ba ... But Anyway Nasan dalilinka Na son inzo Your wedding Abi..... Don't worry Am coming Next Friday Please dad Don't say No Bye!"



Ya qarashe Da Katse wayan , Hydar dake zaune Kusa dashi Ya dafa shi Cikin sanyi da tausayawa Abokin nasu


"A.A bai kamata Kayiwa Abba Magana In such manner ba , Aaryaan Banida Iyaye Kaida Iyayenka kune Kuka Zame mana Gata ,A dalilin Abotan mu na Yarinta , Bai kamata naga......"


Bai qarashe maganar ba yaga Aaryaan ya Miqe ya fita Ya bar masa Office din...


Hydar yabishi da kallo kawai Tareda Jingina Kai....

*Karaci*

"Munayferh please Karki Shaqa mn Wannan Abin In baso kike na Mutu ba Please Ki tausaya Mn Don Allah"


"Ke dama Kinsan Allah?, a lokacin da kike Aiwatar da naki Muguntar wa ya sani?"


"Don Allah munayferh na Roqeki Da Girman Allah ,idan kina qaunar iyayenki ki taimaka Min ,bakisan Wahalar da nakesha ba idan Na Shaqa Abinnan Ji nake tamkar zan Mutu wlh"


"Kinci darajar Iyayena "

Na gaya tareda Saka Kwalbar Cikin jakata, na gyara xama ina fuskantar ta

"Wai don Allah Mene ne Asalin Labarin ne?, me iyaye Na suoayi mki da zafi ne Haka da Kika za6i horasu na tsawon Shekaru 2-3?"


Hawayen dake manne a Idanunta ta Share sannan ta Sharce Majina da Gefen zaninta ta kalleni da Rinannun Idanunta Da suka rine Suka Koma tamkar Garwashi ,Murya na rawa Ta fara bayani


"Ni 'yar Kungiyar Asiri ce Masu kisa don Amfani da wani sassar Jikin mutum Wurin Samun Kudi ko dukiya ,Tun kafin na Auri Aabaan Nake Harkar Shiyasa Na kasa barinshi ,Bansan Mahaifinki ba Saida na Auri Aabaan Don haka A lokacin da na Qyalla Idanuna A kansa na Kamuda mAtsanancin Qaunarsa sbd yana Da Kudi ga kyau Haka Structure din jikinsa Mai burgewa...."


Cikinn Fusata Na Take qafarta Da qarfin Tsiya Zatayi ihu na Bige bakin.


"Ki gyara Kalamanki" .
Murmushin Qarfin hali ta qurqiro sannan Ta cigaba

"Haka Na cigaba Da dakon Soyayyarsa , bazan 6oye Mki ba Munayferh, nice na Hana Mahaifinki Aure da wuri ta hanyar Qullaceยฒ na Haka Kuma koda Ya Auri mahaifiyarki akasi aka samu wurinn aikin ,Ban ta6a Nuna Masa Abinda ke Zuciyata ba bare na bayyana ,ni daya nake Haukana ,Ban tashi tsinkewa da Lamarin ba Saida Kika zo duniya ,A lokacin Ne kuma na Tunanin na rasashi Ne gaba daya ,Amma baqin Kishi ya Hanani Amincewa da haka ,Koda Kika fara Girma na Lurada Yanda Kowa Ke Qaunarki Sai Abin ya qara 6ata Mn rai , naso ace Ni na Haifi Gudan Jinin Junayd ake Jida Ita ba'a son quda ya Ra6eta Bare Kukanta .... Baqar Zuciya Irin tawa da Rashin Yarda Da qaddara tasa Na Je akayi Mn aiki akanki ,Bazanyi Mki qarya ba Ni nasa aka mauda ke WAR MONGER mayyar fada ,masifaffiya Mara barin Bashi kome Akayi mki ki rama Komin Girman Mutum kuwa ,nayi hakan Ne musamman domin kowa ya tsaneki Kuma na kasa Cinma Wlh da nasan zan kasance cikinn wannan Halin da Banyi tunanin Aiwatar da hakan Ba, dalilin da yasa nasa aka 6oye mn Mahaifanki kuwa shine Akwai Wani Aikin da Mukayi har mukayi Yarjejeniya da Wata nurse Ta Bijire mana har take Qoqarin tona Mana asiri ....."


"Wane Aiki kenan!?"

Na tari numfashinta. .

"Akan Chanza 'ya'yan Haleemah da Kulu da nayi ne Nurse Salma Itace ta jagoranci Komai har yarjejeniya Mukayi ,kasancewar Nan ne muke Kwaso Jarirai alokacin Bansan da CCTV camera anan ba ,Sai Nurse salmah ta hada hujjojinta da Clips din da na hanata Kudinta Sai Ta mn barazanar Zata hadani da Hukuma ,Haushin A wannan lokacin naso Na Kasheta Amma Dokar Aikin mu bai bamu damar kashe mace ba , Shiyasa nake bin Duk samarinta nake kashewa kasancewarta Budurwa wacce bata ta6a aure ba ,da an sa Rana sai na Kashe mijin nayi anfani dashi ,a lokacin da ta farga Tazo har gida Tacin mn mutunci kuma tamn barazanar zata kai hujjoji wajen En sanda , da naga Alamar da Gaske Ta shirya tozartani ne sai nA aika a kar6o mn Folder dinda ke Kunshe Da Komai ,cikin rashin Sa'a ta 6oye a wani waje Mahaifinki ya dauke batareda Mun sani ba , Haushin Rashin samun Folder din dasukayi ne yasa Suka sassareta Suka kawo mn ita ,Gudun Kar a nemeta a rasa a afara bincike a Gano nice Na saceta ne Yasa na 6oyeta a Lios inda nake Gudanar da Kasuwancina , gefe Guda kuwa na fara binciken inda ta 6oye Folder din Har duba saida nayi garin hakane na Gano Mahaifinki ne ya Dauia shiyasa na Fara bibiyanshi ,Amma bann gano komai ba Koda yayi tafiya zuwa LIOS na sa An Qwamuso mun sune Harga Allah ba da niyyar nna Su dade a waje ne ba Sai don Na Samu Abinda Nake so Wajen Mahaifinki Kuma Na Hukunta Mahaifiyarki akan Aure Mn masoyin da tayi , Na kafe da Folder dindake Hannunsa ...."



Miqewa nayi Cikin takaici don Maganganunta Ba qaramin tunzurani sukeyi ba , na nufi qofa zan fita na Jiyo muryanta tana Fadin


"Munayferh, don Allah Ki ki kawo Mn Abinci Yunwa nakeji"


Juyowa nayi a Fusace Nayo kanta kamar zan Rufeta cikin huci na ce

"Yunwar ta Kasheki ,perohistoric uncivilized shaidaniya Fasiqah Kawai"

Na qarashe da Hambarinta....

































Ni kuwa nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ


24th Decemberโœ๐Ÿป๐Ÿ˜Œ
[12/27/2020, 10:02 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€

Na
๐Ÿค *Fahnaan*๐Ÿค

ยฉ๐ŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...โœ๐Ÿป*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...



*Chapter 86*


*Saleemah junayd*

*hajee*

*ShafZy*..

*Billi Faruq*

~_Wannan page Din naku ne_~๐Ÿคž๐Ÿฝ๐ŸคŸ๐Ÿฝ


*****


Shuru Tai cikin haษ—iye wani takaici daya zame mata ฦ™ululu a maqoshi....

Ina Fita babu jimawa na dawo da plate din Abinci a hannu na tura Gabanta ,Tareda Zabga mata wata Uwar harara .

Take ta fara Yagar Abincin tamkar zaki ya samu nama ...


Haka Rayuwan mu ta cigaba da kasancewa ,Na rage fesa mata Gas dinda nakeyi Gudun wataran Za'a samu matsala , dukda haka Ina Tsoron Wataran Kar ta maqureni tayi mn dukan Tsiya ko tayi Mn wani illa Domin A halin yanzu banida wani qarfin da Zan iya Kare kaina daga Wani hari ko cutarwa ,Kullum Cikin Ciwo nake harta su haseen basua Wani Samun Kulawan da ta dace daga gareni ,Gashi su Radheekah Sun bar Unguwar .


Amma abn mamaki koda na bar InnaRabi Ba tareda Wani Tsar ba , bata tsere ba hasalima Tana 'dan taimaka mn wayen kulada Su hasnah Tun kan na tashi zata tashi tayi msu wanka Sannann ta sauya Msu kaya , kasancewar ban bata Izinin Shiga mn kitchen ba shiyasa bata Girki amma Ko Shara da wankeยฒ ita ke yi .

Ji kuwa duk abinda takeyi ba Burgeni takeyibba haka kuma bazata ta6a Burgeni ba InshaAllah , bare na sassauta mata Hukuncin da na tanadar mata bayan na Haihu๐Ÿ˜Œ.


A kullum idanna dube kaina Na tunada Rayuwata A baya sai nayi tunanin duk duniya babu wanda ya kaini Rashin Gata , Sai a yanzu na Qara tsanar halina Don shine Musabbabin Kasancewana Cikin Wannan halinn da na kasance mai biyayya ga Uwarmijina da duk makusantana Da hakan bata Kasance dani ba , idan ina Irin wa'ennan Tunaneยฒ Sai naji zuciyata nayi mn wani irin zafi tamkar ana Chakka Mn aallura Anan Amma nafi danganta jakan da qunar zuciya da Akeji idan ana cikin qunci. .....


Cikin wa'ennan Watanni Rayuwa ta juya mn baya , na zamo Abar tausayi , Dukda kuwa banida matsalar kudi ,Sutura , Ci da sha Amma Ina Cikin Jinamin kadaici da kewar Iyayena Da Mijina Na rasa Abindake Hanani Tunanin Hanyar da zanbi na kusanta kaina Dasu ,Ga Cikin dake Hanani saqat Saina Jera Kwanki Biyu Cikina Baiga Ruwa ba Don ba komai naKE Iya ci ba , idan Kika Ganni a halin yanzu dole Ki tausaya Mn .


Lallai dole ne idan Kina tareda Iyayenki Da 'yan Uwa Ko Mijinki Ki Godewa Allah koda Baku ajituwa ne , Don na tabbata Akwai taimakon da zasu iyayi mki idan Kina halin kadaici , Bazaka/ki ta6a sanin darajar 'yan uwa ba Sai Kinn rasa su๐Ÿ’”๐Ÿ˜ฅ,

'Yan Uwa da makusanta rahama ne a Garemu ,Allah ka bamu ikonn Kyaukyatawa Iyayenmu da Makusantan Mu Dama Wa'enda suka Shafemu Ka qara Kusanta mu dasu Ameen ๐Ÿ˜Œ



A chan Nigeria Kuwa .


Yanayin da Umma ta tarar da Hajiya Asiya Yayi matuqar Gigitata ,Koda ba'a gaya mataba Tasan Wannan Aikin munayferh ne don bata Manta Kalmar ta na qarshe akanta ba , Hajiya Asiya ta koma tamkar Dodon Gaske Gashi bata Iya daga Koda 'yar yatsan tane Idanunta kadai suke Aiki .


Da tunanin Nata Hukuncin da bata san taya zata zo mata ba Ta koma Gida (kano ) ,chan ma koda Suka Nemo sanin Dalilin dawowanta bata 6oye msu komai ba ta sanar dasu harta Yanayin da ta iske Qawarta ta Saida Ta sanar dasu Aikam mahaifinta dajin Abinda ta aikata have ba'a Gidansa ba , Taje Ta Nemo msu Diyarsu ...

Qarin Abin baqinCiki a wajen Umma Shine bata San Yanda akayba..aka hada Tsuggun ba ,Itadai tasan ta bada kudi kuma ta gaya Abinda ya kanata ayi ,Kuma da wiki ya kammala bata Nemi jin qarin bayani ba .

Ta rasa ta inda zata Fara nema Na , haka Kuma batasan Hanyar da zata Bi Don ganin ta samu Masaniya Akan inda nake ba .

Sauqinta 'Daya Tanada Gidan Da Aaryaan Ya Gina Mata a Malali , nan ta Tare Ta killace kanta Don harta Kunyar Fita takeji Gudun kar a Ringa Nunata , Domin kuwa har duniya Ta Fara Sani ko'ina Ka shiga Abindake Trending kenan
*UWAR MIJI TA BATARDA MATAR 'DANTA AKAN KISHI* ๐Ÿ˜ฒ(bani na Gaya ba Fahnaan ce ta Rubuta๐Ÿ˜…).


Abba Kuwa Tuni ya Auri Nurse Salmah Kuma ta tare Cikin kwanciyar hankali, Su Ammie Kuwa Hatta Umrah sunje Don Roqon Allah ya bayyana Msu diyarsu haka kuma basu Gaza ba wajen Sadaqa da Yawaita Ibada Kasancewar Daddy mai jama'a ne Mutane dadama Masu Unguwanni Masallatai da sauran wurare Suma suna Sanarwa Kuma Ana Tayasu Da Addu'a Basu ta6a gazawa Ba Don sun San Allah shine Sami'ul Aleem Yanajin Roqon bayinsa kuma yana sane .


Aaryaan kuwa Ko sau daya Bai waiwayi Umma ba ,(Mutuminda bashida Lokacin kansa mah๐Ÿ’”) ,Aikinsa Kadai yasa a gaba kuma yana samun nasara ,Sai Qarin Girma Yake samu A koda yaushe . ...

Yau yana Free Don haka yayi Niyyar leqawa Gida .

Qarfe 10:00am ya baro Abuja Ya kuma Isa Garin Kaduna Da qarfe 2:06pm .

Part dinsu Ya Fara Shiga Babu kowa hakan yasa ya juya ya Nufi part dinmu .
Kakus ce zaune bisa Cushion Kallo Daya zakayi Mata ka fahimci tsantsar ramar da tayi ,kuma tana tareda Damuwa , gefe Guda kuwa Amarya Salmah De Tsugunne A qasa tana Yankewa Kakus farcen qafa .


Da sallama Ya shigo duk suka Amsa Masa kusan A tare Cikeda mamakin Ganinshi a daidai wannannLokacin ,Qarasowa yayi ya zauna kusada Kakus , yanaa harararta


"Kallon fa? , ko Kin Fara Maita ne ban sani ba?"

"Aah Lallai Mutumin Baki ya Bude Kodai Anqa Juliet dinnka ne?"

Kwantar da kansa yayi bisa Cinyarta Kaman qaramin yaro , ya dubi Salmah Cikeda Girmamawa yace

"Ina kwana Aunty Salame"

Dariya tayi sosai

"Aah lallai Da gaske ne baki ya Bude , harda samin Suna wai salame"

"Yo ai dama duk salma Asalinsu Salamatu ne ko salame , qaryar wayewa ne kawai da Iyayi Irin na 'ya'yan zamani"

inji kakus Cikin zolaya

"Salame da Salamatun sune Sunan Amma ba wani ssalma ba Sai kace Miya lami?"

Inji Aaryaan Cikin tsokana


Gabaki Daya Sukayi Dariya harda Ammie dake Saukowa Daga Kan stairs ,

Ta qaraso tana 'yar Dariya

"Yau Shagwa6ance ta motsa ,Daga dawowa Zaka 6alla mana 'yar tsohuwa ?"

"Kai Ammmie na lura bakiyi murnar Ganina ba ,But don't worry Yanzunnan Zan koma ki Cinye Tsohuwarki Tunda ni Akeyiwa Rowar qafarta...."


Kakus Ta mere baki tace

"Qyale 'yar baqinCiki ,uwarta Ce za'a 6alla baniba"

gabaki dayansu sukayi Dariya Amma banda Ammie da take jin kanta wani iri

Tayi Murmushi kawai don ta Lura Yau Abin ya Lafa Masa ne , da tsokana ya dawo Koma ta rasa dalilin hakan , Wayanta dake Kusadashi ne ta dau Ruri ,Hannu yasa Ya dauka Ya qara Gyara Kwanciyarsa ACiyar Kakus yayinda ita kuwa take Dan shafe Suman kansa a hankali.

"Ammie Ana Kiranki Amma Private number ne!"

"Qyalesu Sun Saba idan Kayi banza dasu Dakansu zasu daina Kira" inji Ammie

"No Ammie Bai kamata ba ya kamata Ki Daga Kiji ko Waye , kika sani Ko Alkhayri ne ?"

INJI salmah


"A'a karki Daga Idan Alkhairi ne Ai bazai 6oye Number ba , ni ban Goyi bayan ki dau wayan ba gaskiya " cewar kakus.


Shikuwa Aaryaan Murmushi yayi tareda Girgiza Kai

"Nidai Zan daga inji wane Dan iskan Ne yake damun In law Dina?"

Ya qarashe da picking call din .


Muryana mai tarin nutsuwa da amo ta daki dodon kunnensa , yayinda hakan Yayi daidai da Lokacin da Zucuyarsa tai wata irin bugawa tamkar zata faษ—o ฦ™asa, idanunsa suka Fito.

"Hello Ammie"

Kaman An tsikareshi Ya miqe zumbur Gabansa na Cigaba da faduwa

"Sulthy..."

Gabaki Dayansu Suka zuba masa idanu Jin sunan da ya Ambata .



Maganarsa ta shiga kunnuwan na babu zato, saurin buษ—e idanuna nayi da mamakin Ashe Zan Sake Jin muryanshi.

Murya Na rawa Na Furta

"Raa ....ja..."

Sai kawai na fashe da kuka .............


























Idan Ana Kuka Yin Gabas nake ๐Ÿ˜ซ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ


25th Decโœ๐Ÿป
[12/27/2020, 1:29 PM] Fahnaaanโฃ๏ธ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
_*Hawan-Jinina*_
_(Uwar mijina)_
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€

Na
๐Ÿค *Fahnaan*๐Ÿค

ยฉ๐ŸŽ†
*Al'umma Writers Asso...โœ๐Ÿป*

_{Al'umma writers,Kungiya daya Tamkar Da dubu FarinCikin mu mu fadakar da Al'umma domin su Farfado su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya namu Ikon fadakar da Al'umma}._


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...



*Chapter 87*



Gaba daya ya tsure ya rude ya kidime ya Gigice , Ya kasa Gasgata Muryan da Yake Ji Cikin Kunnensa Haka Kuma Sautin Kukan da nakeyi Yana shiga Har CIKIN kwanyar kansa .


Ji yayi an kar6e Wayan dake Manne a Kunnensa , A 'Dan razane Ya juyo ya Kalleta ,Ammie ce itama Cikin gigicewa Ta Kara wayan a kunne ,sautin Kukann da nakeyi ya sami nasarar Shiga Kunnenta .

Saida Ta hadiye Wani Yawu Mai 'daci Tayi qoqarin saita kanta kafin ta furta

"Munayferh...."


Cikinn kuka na Amsa Mata

"Ammie....."

Na Qarashe Maganar Lokacin da wani Irin Tari ya sarqe Min , TAKE An shiga Tari babu Qaqqautawa , Yi nake Ina qarawa , Bakajin Komai Sai sautin Farin da nakeyi Ckin wahaltuwa.


Gabaki dayansu Suka Rude Suka Shiga Kiran Sunana ,Amma na kasa Daina tarin bare na Amsa Su .


A zahiri kuwa Tarin Nakeyi sosai Wani Irin Jini baqin qirin Na fita , haka Kuma duk tarin da zanyi Sai Zuciyata ta Amsa da wani Irin suka kaman Ana Choka mn Allura.

Hankalin su yayi Mugun tashi ,Sun kasa datse wayan Sai Sambatu sukeyi Suna Ambaton sunana ,Ammie kuwa Tuni ta Fara hawaye jin tarin yaqi tsayawa Shi kanshi Aaryaan din Daurewa kawai yakeyi Ji yake kaman yayi tsuntsu ya sameni a Duk inda nake .


Tarin nakeyi Sosai babu qaqqautawa Tun inayi a zaune har Nan fadi qasa , hannu na sa Na riqe saitin Zuciyata dake Neman Tarwatsewa Don tsananin Azaba sakamakon Wani Irin Zafin Azamar da naji ta dira Mn Lokaci Daya , Nayi wani Irin Tari mai hadeda Wani Irin baqin Gudaยฒn Jini ..


Daga nan Ban sake Sanin Inda Nake ba , Sai farkawa nayi Naganni a Gadon Asibiti .


Teemah Da ta kawo Mn ziyara ne ta ganni Ckin wannan halin ta taimaka Mn Da taimakon InnaRabi ta kawoni Asibiti .

Likitoci sunyi Binceke Sun Gano Ina daukeda Ciwon Zuciya Kuma da Alama na 'Dan jima dashi bai bayyana kansa bane kawai sai yanzu ,
Sunyi Admitting Dinmu a asibitin Saida nakai Tsawon sati 'Daya Ina Jinya kafin Daga nan su Sallamoni da Shawarwari Da Qaidojin da zanbi wajen Rage Damuwa da Duk Abinda ka Iya tayar da Ciwon Zuciya.


Duk kwanakin da Nayi A asibiti qawata Teemah da InnaRabi suke Kuladani , kasacewar na yaye su haseen sai ya kasance banida Matsala dasu .....


Duk Qaidojin da likitoci suka Gindaya mn babu laifi nabi Kuma Ina Amfanida Magungunana Yanda ya dace , Don Likita ya tabbatar mn Ciwon Zuciya na Kisa Kuma harga Allah Ina tsoron in mutu a waya Qasar ban sake Ganawa da iyayena ba .

Saidai Duk yanda naso na Cire damu da tunani a raina na kasa Tunanin Dangina ya hanani saqat Shiyasa Ciwon ke yawan tashi .


Ga ciki Ga Wahalar Ciwo , sai Abin ya hade min Yake barazanar Dauke mn 'yar Numfashi na.

A yanzu Ckina ya Cika Watanni Tara , A lokacin kuwa yarana Ke shirin cika Shekara 'Daya da haihuwa.


Dukda halin da nake ciki n wuya , Da azabar Ciki Na quduri Aniyar Hada Msu Birthday party Don Na faranta msu ,Cikin rashin sa'a Ana saura sati 'Daya su Teemarh sukayi Hutu Don haka suka Koma Gida Nigeria, banji dadin hakan Ba kasancewarta Babbar qawata kuma wacce mukafi shaquwa da ita ,Amma da na tuna inada Wasu qawayen Da muke GoodTime dasu Sai naji dadi a Raina .


Musamman Nasa Aka Buga mn IV na Rarrabawa Neighbors Dina Da Coursemates Dina wa'enda suke Zaune a qasar Kuma na Aika a Siyo mn duk Abinda Ake Buqata wurin shagalin Bikin BIRTHDAY , Da kaina Na Lalla6a nayi baking birthday cake din ,Qaton Qaske Kuwa har Guda Biyu Daya na Hasna Dayan Kuma Na haseen Ko wannensu yana Dauke Da sunayensu .


Ana Gobe Bikin Birthday din Ckin dare na Tashi naquda ,Kasancewar dare ya tsala sosai Kowa yayi barci harta Su Haseen da InnaRabi.


Babu Wanda yasan halin da nake Ciki tun Ina Daurewa har Abin ya faskara , Ckin qanqanin Lokaci zufa ya Gama jiqa mn tufafina , Tun Ina Nishin wahala Har na Na koma ihu da sumbatu Daga Qarshe na Fara salati Amma Abin mamaki duk Abinda nakeyi babu Mai jina Ni bare a kawo Mn dauki๐Ÿ˜ข .

Wasa Farin girki Ashe Duk wannan Soman tA6I NE ,Ban Fara Asalin Naqudar ba shiyasa Nakeda Baki da qarfin Ihu .

Cikin qanqanin Lokaci na Fita Hayyacina Na , Don Tsananin Azaba Ko Numfashi daqyar nake iya Fitarwa Sai Nishi , Gabaki Daya qarfina Ya Gama qarewa Na jiqe Da Ruwan Naquda da Jini.

Na Gama sadaqarwa Mutuwa Zanyi , Jiran Lokaci kawai nakeyi .


Wani Irinn murdawan da Marana tayi A lokaci Guda ai bansan yanda akayi na samo qarfin da Na iya Jan Wani Uban Numfashi Ba , Wanda yayi daidai da Sumbulowar Santalelen jinjiri .


Aikam Fitalowarsa Kaman An Cire mn wani Abu , Nayi baya Ina maida Numfashi Ckin tsananin Azaaba , Niko a haihuwar Fari bansha Wahala Irin Haka ba.


Hannu nasa na Laluba 'yar razon Da na Ajiye Kusadani (incase), na Yanke Cibi.

Sannnan Na Lalla6a na Tashi zaune Ckin Tsananin azaba na dau yaron daketa Faman tsala Ihu ,Na qura mshi idanu baba Iya Ganin Fuskarsa sosai Saboda jinin dake Lullu6e da Fuskar tasa .


Tunowa Nayi da Ranar da Haifi Su Hasnah ,Bangansu Cikin jiniba , Ina haifarsu Kafin na dawo hayyacina aka Gama Kimtsa su


Wasu Zafafan Hawaye Ne suka zubo Minn, na manna Jaririn a Qirjina Na rungume , ban damu da ihun da yaje Tsalawa ba Na koma Na jinGina da bango Ina Maida Numfashi Tareda Tunanin Yanayin da na Kasance Ckin 20mins dinda Suka Gabata , Hannu na Daga Dama nayiwa Akkah Godiya da wannan ni'imar da yayi Mn ,Na kuma roqesa Da ya Bani ikon Basu Tarbiyyah ta turba Ta Gaskiya ....


Na dau Kusan 20mins Ina Addu'a kamin Daga Bisani na Shimfida yaron na 'dan Rarrafa na Nufi BirthRoom Na hada Ruwan wanka nayi Wanka Na Gasa Jikina da ruwa mai zafi sosai , Sannan Na Fito Cikin Dauriya Na Dau Yaron da Har yanzu Kuka yakeyi shima nayi masa Wanka dukda Ba sosai aya fita ba Amma jinin jikinsa Sun fita. ...


Sai a Lokacin na Samu yayi Shuru har barci ya daukeshi.


, Cikin Kayan sanyin da Na siyo na jarirai na saka Masa 'daya Na kuma fesheshi da Turare don qarnin Jininda yakeyi.

A wannan Daren Kasa Barci, Na daren Ina Godewa Allah da wannan Falalar da yayi Mn Wanda Ba kowace Irin Mace take dashi ba ,Ba kowace Mace take iya Haihuwa dakanta ta tsaftace Su Suka a lokaci Guda batareda Taimakon wani ba , Ni kaina Da Ina Tareda Dangina Na tabbata bazan Iya hakann ba Rashinn mataimaki ne yasa Na lalla6a nayi kakan, Don Idan Banyiba Babu Maiyi mn Kuma za'a iya samun Matsala .... .


Cikin ikon Allah Gari na wayewa Ko Farkawa banyiba Muka kar6i Baqoncin JEEBOI da mahaifiyarshi wa'enda sukazo Ganin Likitansu Dake Imad Babar .


Sunyi matuqar Mamakin Ganina da yaro Don Basu San Ina dauke da Ciki ba ,Su Haseen Kuwa Tun tashinsu Suke Tsalleยฒnsu Hankali Kwance Yayinda InnaRabi ke Rufe a dakin Da Na Rufeta.


Da taimakonsu Muka tafi Asibiti Aka duba Yaron tareda Sake Gyarashi ,Nima suka bani Taimako Wanda ya Kamata ,kaaancewar na sha Wahalar daren jiya Kuma ban samu isasshen Barci ba , Sai na Shiga Rama Barcin qarfe 10:00am na Farka Kaman Bani na haihu ba ,Nayi shar Sai Washe baki nakeyi ,Qarfe shabiyu Aka sallamoni.


Na koma Gida , a lokacin har Event Planer Na birthday din su Haseen Sun iso , dukda haihuwar da nayi Baisa na FASA ba Saida Akayi .

Anyi shagali sosai , Kowanne yazo sai yayi Mamakin Haihuwan Da nayi Haka Kuma duk Wanda ya Tambayeni wanene Jeeboi sai nace shine Uban yaran .

Nan dai Akaci Akasha Aka watse , Washe

Please Login or Register in order to submit comment