Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu lafiya.


"Hey!, Abi u don sold ur tongue for market!... Ahh answer me naa"

Tsaki naja tareda qoqarin Cire Airpod dindake saqakale a kunne na.


Wani irin bugun da naji a Glass din motar yasa na Maidashi A Tsorace.


Da qarfi Nace "Wayyo" na Qara Gudun motar don Ganinmutanen da Nayi Suna Biye dani kafin Nayi yunquri Har an fasa Glass Dinmotar ta dayan 6angaren.


Na Qara sakin Wata Qara, Aaryaan Dinda Ke Jin qaran da nake saki Har Tsakiyan kansa ya fara tambayan Abin dake Faruwa Cikin matsananci tashin Hankali..


Wani irin bugun da naji Akai mn a tsakar kaina ta Wajen motar yasa na saki motar Batareda na shirya ba na koma da baya sumammiya.


Aaryaan dake jin Abinda Ke faruwa yayita kiran Sunana yaji shuru, hakan ba qaramin tada mshi hankali yayi ba.



Motar na kaiwa jikin Wata Gini Ta Tsaya .


Yayinda Uban Mutanen da Suke bina a baya Suka Iso inda nake ,Suka bude kofar suka Fito dani....


Tareda Daukan mn wayana.


Kasancewar layin babu wasu jama'a hakan yasa suka Sami nasarar Daukeni sukayi Gaba dani Batareda kowa ya Sani ba suka bar motata A yashe anan....


Wani irin Abu suka fesa mn hakan yasa na dawo Cikin hayyacina .


Na qarawa Wurin kallo Wata 'Yar qaramar 'dakine Babu komai a Ciki Sai Wata qatuwar Computern dake danqare a Bangon Dakin , Sannan Mutanen dake zaune a A qasa duk sun tanqwashe kafafunsu Duk kansu Sanye Suke da baqaqen kaya.

Wani irin yuquri Nayi naji hannayena sun Riqe ,Ashe daure Suke ta baya .



Wani irin Dariya naji saitin kunnena kafin daga Bisani na farajin maganar mutun yana Fadin

"Heheee Ashe Qaryan Aljannu Gareta ,Eh mana idan Da Gaske ne ta kirasu Su Kwanceta manah" sai ya Qara Fashewa d Wani irin mahaukacin Dariya ,Sauran na tayashi.


Aaryaan dake jinsu yaji kaman Zuciyarsa ta Faso Qirjinsa ta fashe don baqin Ciki

A tsorace ya kira sunana

"Sulthy kina jina?"
"Kinsan inasuka kaiki?"

"Bansani ba " na fada a tsorace.


Gaba dayansu suka kai subansu Gareni Ganin ina magana Ni daya kaman zararra.


Wani Dogo kuma baqi daga cikinsu yayi Dariya sosai Sannan yace
"Kin dauka mu shasha sha ne da zamu Yarda da Aljannun qaryan da kikeyi Wa wasu?, Ai Mu ba shasahashai bane munfi Qarfin Ayi wasa da Hankalin mu".


" baabah Nifa Babe dinnan ta min ne ,kuma Wallahi sai na Huce Akanta don dukan da nasha Ranar nan ba banza ba" inji Wanda ya tsira Daga cikin 'yan daban Ranar nan..


"Hehehei Kaga Mu fara hada ta da Ubanta suyi sallama kaman yanda Babaah yace Sannan Muyi Anfani da ita a Gaban idanunsa yana kallo Kaga daganan sai Shima ya hadiye Zuciya ya mace Kaga mun huta kenan"



Gaba daya Suka kwashe da Dariya Tareda Kunna Sigarinsu Suka Shaqa duk a lokaci Guda.


"Handsome Hadata da ubanta mana ,Mu fara Aiki"
inji Baqin nan da ya fara magana.


Wani farin saurayi ya tashi ya Kunna qaton Computer ya gauraye Duk ilahirin Dakin .


Babu jimawa Fuskar Daddyna ya bayyana a Jikin Computern Da Alama video call suka hada mana


Fuskar nan tasa ya jiqe da jini Amma Dukda hakan Saida na ganeshi..

Hankali na ya kuma tashi sosai


Da iya qarfina na Furta

"Pitaaa"(daddy)


Shima cikin Wahaltuwa ya Furta

"Beteee"(daughter)










Tofah



Nayi gabas๐Ÿš˜


2nd nov
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: *HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}.


_ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 61_*








Aaryaan dake jin komai ya kuma shiga Cikin Rudani Tabbas Muryan Uncle dinshi yaji kuma yasan Shine kadai nake Kira Peetaa


A rude Shima ya maimaita Kalmar Peetaa?

Kafin na bashi Amsa Har Wani daga Cikin Mutanen nan Ya rigani Magana


"Hahaha Malam junaydu kake kor! ,Taurinkanka na burgemu Sosai fa ,Baka damu iyalanka Su rasaka ba ka Gummace ka Dawwama ahaka da ka Fada mana Gaskiyar inda ka Ajiye mana Ajiyar mu! , Eh tho idan baka Gaya mana Cikin lalama ba ,zaka Gayamana In Kaga Abinda Muka yi da 'diyarka daga Bisani Mu kasheta A Gabanka "


Ya qarashe maganar Yana Qara Tuntsurewa da Wata Irin wawan Dariya Wanda Ya sanya Gabaki dayansu suka dauka Wani daga Cikinsu ya Iso inda nake zaune Hannaye da Qafafu duk a daure

"Wow Wannan da Alama Akwai 'yan Moro a Jikinta ,Kaga komai sharr kuwa? ,naso ace budurwa ce Aradu da yau babu Wanda ya kaini sa'ar morar mace a duniya ,Amma nasan Cikin dake Jikinta ma zai Qara mata Sweat ne Hehe ..... Gofree! ,Daga mn ita ka kaimn Dakin Chan idan na gama Sai Kuma Kushiga Ku kwashi Rabon Ku"


Ya qarashe tareda Kecewa da Wata malalacin Dariya , Wanda Aka kirada Gofree Yazo zaijata.


Daddyn Munayferh dake kallonsu tacikin Computer ya rimtse idanu da qarfi Tareda ware murya Da qarfi yace

"Ku dakata"

Gofree dake Shirin Daukan Munayferh ya dakata yana Dariya ,Yayinda ita kuwa Munayferh Fuskarta babu Alamar tsoro illa binsu da idanun da takeyi Tana Tunanin Abinda Zatayi msu.

"Eh Malam Nasan Wannan shine Weak point dinka ,bazaka so muyiwa 'yarka fyade a gabanka kana Gani ba Hehe Malam kaifa muke jira ka gaya mana Inda Saqon Yake mu tafi dashi"


"Munayferh...... Vah dibba Jo mainne tumhen diyatha!"

(Wannan Box Dinda na baki Ki 6oye mn)

Kafe Computern nayida Kallon Cikin Alamar tunani daga Bisani Nace

"Haan Pitaajee"

"Yah hoohen den" (ki basishi)


Wata irin Dariya na kece dashi Sosai mai ban tsoro Kaman Wata mahaukaciya ,idan kaji yanayin dariyan sai ka rantse Wata Jaruma keta Sheqa dariyar Amma deep down karkaso a tona yanda Gabana Ke dukan Uku Uku , Dalilin dariyan kuwa Maganar da naji Aaryaan yayine a Waya.


"Hello ice small kana jina....na turo maka Wata 'Yar number ka Duba mn distance dinmu da ita in the next two mins......karkayi Cutting call din.........OK yana Conern shahada na Kofar doka kenan?, ni ina Kongo ne Kaga bamu da nisa ma OK thanks"




Hakan da naji ne yayi daidai da maganar Daddyn da naji yana Fadin in basu Akwati sai Abin ya bani Dariya.

"Peeta jee ,wlh main nahim karoonga" (Daddy wlh bazan basu ba)

A tsawace Kuma Cikin Tsare Gida yace

"Yah hoohen den" (ki basu )

Su dai Mutanen tsuru sukayi Suna kallon mu don basu fahimci me muke Fadi ba, Cus basu fahimci yaren ba ,kuma basu Ankare da Airpod dindake kunne na ba.

Ganin munata yare mun kasa basu Abinda suka Bida yasa Suka kamani , daddy sai cewa Yake na basu .

Ni kuwa nantake fa ido ya fara Raina fata Amma Dukda haka ban bari Tsoro na ya Fito fili ba, Addu'oi kalakala babu Irin Wanda banayi Cikin Raina.

Da Qarfin tsiya Gofree ya Tureni Nayi baya na Fadi ,Wata irin Gigitaccen Qara na saki Sakamakon buguwanda Nayi akaina ,Da sauri Daddy ya sunkuyar da Kai hawayen baqinCiki suka Kwaranyo masa ,ya rasa Gane taurin kai irin na Munayferh take danasanin Bata Ajiyan ya shigeshi a karo na farko



A lokacin nan kuwa Tsoron Gaske ya fara bayyana a Bisa dakalin Fuska ta yayinda Hawayen tausayin kaina Suka zubo mn.

"Bhaae va mere balaatkaar karana chaahate hain" (Yaya zasu mn fyade)

Na fada Cikin matsanancin kuka.



"Koee kah raha ki band karo krypya apana aatm kee raksha Ke lie ek kaarravaee kareen" (No stop saying that, Please make an Action to Protect yourself)

Inji aaryaan lokacin da Yake bin sautin da yakeji yana tashi Cikin Wayan Alama dai ya shigo unguwar ,ma6oyansu kawai Yake nema.



Hakan da naji ya kuma bani qwarin qwiwa take na nemi tsoron da nakeji na rasa , Nasa qafa na Ture mutumin dake tsaye Gabana yana kiciniyar Cire Rigarsa Yayinda Sauran Suka zuba mn idanu Cikin tsoro don Sunga dai ina magana Ni daya basu San Dawa nakeyi ba, sun dauka Aljanan ne Suka motsa ,daddy kuwa tunda ya sunkuyar dakansa bai sake dagowa ba.

Wani irin yunquri Nayi Cikin son Kwance Daurin da sukayi mn a Hannu na ta baya, Sannan na kece da Dariya Cikin dakiya na fara magana


"Anti 'Yar kuturwa tashe Ku Kwanshe Ni in kawo Mku Akwatin Yana shan"

Na fada Tareda kecewa da Wata Bahaguwan Dariya.


Basu fahimceni ba, Wani daga cikinsu yace

"Ka dakata Gofeen ,inaga kaman ba'ita bace Aljanunta ne suka tashi, Gashi Har naji ta Ambaci Sunan Akwati Abinda muke nema Kaga maybe Sune Suka Kutso suka gaya mata Inda ya ajiye"

Gofee yaja tsaki

"Mtsww Nabi Aljanun da Gudu,kyaleta Raina mana hankali Zatayi, Ni ko Ifritanta ne suka tashi yau saina Moreta Sannan na barta" ya fada tareda Sa Hannu ya Cire mata 'Dan kwalin kanta Sannan yasa Hannu zai ta6a rigar dake Jikinta ,nasa Haqora na kai masa Cizo ,dasauri ya sakeni tareda sake tureni na Fadi ta baya Cikin Zafin Cizon da Nayi masa Sannan ya Mara mn baya ya hau kanta yana Sauke Numfashi kaman Wani Tsohon Maye.

Wani irin One Blow aka kaiwa Kofar Wanda yayi sanadiyan Tarwatsewanta a lokaci daya ya Fadi qasa kasancewar Qofar ba Wani Aukine da ita ba.


Cikin Zafin nama ya ficiki Wuyar Rigar Gofee ya janyeshi Daga kaina Ya Ciro Wata 'Yar kibiya daga Aljihun Rigarsa ya Chaka masa ita Cikin qwayan idonsa daya , Take Idon ya tsiyaye ya kwarma Wani irin razananniyar Qara tareda Fadi qasa yana Kururuwa a kawo masa agaji ,

Yayinda ya subkuya ya Kwance min daurin da sukayi mn A Hannu da qafa

nan take sauran suka fara Neman hanyan Tsira ,Fahimtar hakan da yayi ne yasa ya janyeni ya 6oyeni a bayansa Sannan ya Rufe Fuskarsa da mask Dinda yazo dashi Sannan ya Fito da Wata 'Yar kwalba ya Fesa anan take Mutanen nan suka fara Fadi qasa Suna Suma , gaba dayansu Saida suka suma .


Bayan wasu mintuna ,bayan ya tabbatarda Maganin ya Dan fara Gushewa Sannan ya juyoni daga bayansa ,ya zuba mn ido kaina babu 'Dan kwali , harta Rigar da nasa Ya dage Kusan Rabin jikina duk a Waje Suke


Take Wani irin kishi ya Turnuqeshi , yanzu haka na Bari Wani wawan Qaton gardi ya Ganni?.


Baisan lokacin da ya daga Hannu ya wankeni dawata irin Razananniyar mari ba,


Hannu nasa na tallo6o kuncina Take hawaye suka Shiga Zirya a bisa dakalin Fuska ta


"Yayan Hafsah me nayi maka da zaka mare Ni" na fada ina hawaye.


"Ubanki kikayi mn, Shashashar kawai"


Ya fada yana Gyara mn zman Riga na, Ni kuwa na sa kuka.



Daddy kuwa da Tunda Aaryaan ya shigo ya kafeshi da ido yana Mamakin yanda ya Qara Girma ya zama Cikakken mutum MaiI cikakken haiba da kamalah ,Sai a yanzu ya Fahimci Dawa nake magana dazun .


"Aaryaan....." Daddy ya kirasa a hankali Cikin Rawan murya.

Da sauri Aaryaan ya juyo tareda Tsurawa computern ido Ganin daddy yasa ya Ruga da Saurinsa kaman zai Rungume TVn sai kuma yaja ya Tsaya .


"Daddy.....! Ina ka....Ke?, "

Girgizakai Daddy yayi Cikeda damuwa yace

"Bansan inda nake ba Aaryaan"


"Daddy Ammie ta Kasa gaya mana inda aka kaiku Kaima haka meyasa kuke mna hakan ne?,meyasa Baku damu da yanayin da muke shiga Sbd kuba?, Kaga yanda Fuskar ka ta jiqe da jini kuwa?, Mutanen nan sunada hadarin Gaske ina tsoron rasaka Daddy ,Gashi kai kuma baka damu ba.....suwaye waennan da suke neman Naqasa Rayuwan mune?, Meyasa Suke mana hakan?, Menene Abinda ka tsare msu Har Suke farautar Rayuwanku ne?, meyasa? Meyasa " ya qarasa magana hawaye na gangarowa saman kuncinsa.


Salim dake zaune a Gefen Daddy yana jinsu yakai duba Ga Uban jami'an tsoron dake tsareda Su a Dakin yace


"Kudan bamu wuri mu Gana da 'Dan Rainin Hankalin nan "


Babu Musu Suka fice daga Dakin Salim yaja system dindake Gaban daddy ,Fuskar sa ya bayyana a garemu.


Kallo daya Nayi masa na fahimci shine Uncle Hoodyn dasu Ameerah Suke yawaita bani labarinsa don Gashi ko yanzu haka ma yana Sanye ne da Hoody Fara qyal ya kuma Rufe Fuskar sa da baqar glass hakan yasa na kasa Ganin Gabaki daya Fuskarsa.


A hankali ya fara magana


"Muna qasar Lous ,Cikin Babbar Fadar Taryash Estate na Biyu kusada Wata Qaton masallaci idan kazo baka Gane Wurin ba ka kira wa'ennan numbobin.......nan take ya bashi Numbern Wayansa".

Aaryaan yabishi da kallo

"Tho kai waye? ,Meyasa kake Shirin taimakon mu?"


"Agent Saleem" ya bashi Amsa Cikin sigar Ra'da ,Sannan ya janye laptop din yana Fuskantar daddy.


Ina Ganin Fuskarsa na Qara Fashewa da kuka

"Daddynaa......" Abinda na iya fada Kenan Sai kuka.


"Beteee ki daina Kukan nan ,Share hawayenki kinji.......inshaallahu Zan dawo bada dadewa ba kinji ,ki share hawayen ki"

Ya fada a raunane Yana Qoqarin hadiye nasa Hawayen.



"Daddyna Meyasa Kayi Saurin karaya a dazun ?, Meya Tsorataka ne?, har kace na basu Akwatin da kabani Amanarsa na tsawon Shekaru? ,Daddy Har ka bani kunya wlh ,bansan ka da tsoro ba Kai na Gado Amma Sai gashi Ayau ka nuna mn tsoron ka akan Mutanen da basu wuce na 6a66allasu da Hannayena kaman yanda Ake 6alla Rake ba"

Na fada cikin Fusata Hawaye na Ambalia A Idanuna


"Betee bazaki Gane ba ,Har yanzu Ke Yarinya ce ,mu bar wannan maganar...... Kinyi Aure ne?"


Ya qarashe maganar Cikeda Qarfin hali yana Qago murmushi ,Wanda Akace yafi kuka Ciwo.



Saida na saci Kallon Aaryaan da ya zuba mn idanu Har yanzu yana Huci ,Sannan na ta6e baki na maida Kallona Ga Television din ,Hawaye suka zubo mn.

"A'ah Banida Aure ,Me ka Gani?"

Daddy yayi Dariya for the First time .

"Aaryaan"

"Na'am daddy''


" Nagode sosai Da taimakon da Kayi mana ,Allah yayiwa Rayuwanka Albarka ,Yasa ka Cika da Duniya lafiya ,Allah ya saka maka Da Mafificin Alkhay......"


"A'ah daddy Please ka daina ai kaina nayimawa"

Aaryaan ya dakatar dashi Cikin dakiya

"Naji dadi Sosai ,Amma wanene Mijin Beteee "


Shima Saida ya sace Kallona Sannan ya harareni ,Cikin sunkuyar dakai Yace

"Daddy nine"


"Mashaaallah Allah ,Amma Nayi FarinCikin hakan sosai ma kuwa, Allah yayiwa Rayuwanku Albark....."

"Sir junayd, time yayi Gasu nan Tafe " saleem ya fada yana qoqarin Katse Video call din.



"Uncle hoody ,one minute Please" na fada ina Fizge Wayan Dake aljihun Rigar Aaryaan.


Na Kunna Camera tareda Share 'yan qwallan dake bin fuskata ,Daddy ma ya gyara Fuka tareda qago murmushi Nayi mana selfie ta cikin Computern,Dukda kuwa Hasken System din yadanyi Fau amma hakan Bai hana Fuskarsa fitowa ba.

Ina dauka System din na daukewa.


Kar6ar Wayansa yayi Ya kira Wata layi Yayi magana Yace Su Shigo ,Nan danan Saiga tsirarun 'yan sanda.


Suka kwashi Mutanen nan sukayi Gaba suka bar Wanda Aaryaan ya sokeshi a ido Wanda Tuni ya Suma Sbd Azaba.



Suna Fita na fashe da Wata irin matsanancin kuka ,Yayinda shi kuwa ido ya zuba mn yana Ayyana Rashin hankali irin nawa ,Gani yayi shi ya kamata yayi kukannan ,Shi da Ake Shirin yinma Matarsa Fyade kuma ta Tsaya bayan Abubuwan da ya gaya mata tayi , Shida Aka zubawa mahaifiyarsa Maganin zubar da Ciki cikin Abinsha , Shida Wani sabon Al'amari Ke shirin faruwa Cikin Rayuwarsa.


Tsawan da ya daka mn ne yasa na hadiye kukana batareda na shirya ba.


"Keh! Kukan me Kukeyi ne?"


Dukda kuwa tsawan da ya daka mn ya shigeni sosai Amma hakan baisa na Amsa mshi ba, Shikuwa idan da Abinda ya tsana a duniyar nan bai wuce yayiwa Mutum magana yanajinshi Yayi banza dashi ba sbd haka Zuciyarsa ta kuma tafarfasa haushina da yakeji ya Kuma ninka na da

Ya Nufo Ni kaman Zai makeni.


"Keh ,bada Ke nakeyi ba?, Uban me Akayi mki kike kuka?, sokuwa kawai ba abinda kika iya sai koke-koke banza kawai duk kin cika min kunne. ,Abege 6ace mn da Gani"


Juyawa Nayi tareda nufar hanyar Fita ,Waro idanu yayi Ganin fitan Zanyi akan .


"Ke ina Zaki?"

"6ace maka Dagani zanyi" na fada Cikin kuka.


Tsaki yaja ya dauko Mn Dan kwali na ya daura mn, Sannan ya Cire Rigar Coat Dinda Ke Sanye a Jikinsa Ya daura ya bani nasa.



Sannan Ya sunkuya ya dauki Mutumin nan ya sunkuceshi ya aza bisa kafadarsa ,yaja Hannu na mukayi Waje


Inda Muka tararda 'yan sanda Suna Tsare da Wurin.

Ya bude mota ya shimfida Gofree a baya sannan ya zagayo ya bude mn na shiga Gaba yaja Muka bar Wurin๐Ÿš˜.



Kai tsaye AA specialist hospital ya kaishi aka shigayi masa Treatment na Gaggawa ,daga Bisani Muka fice ya bar Asibitin Tareda jami'an tsaro masu tsoron Gofree.



Daga nan kuwa Gida Muka nufa ,Muna shiga yace na Shige Ciki na kwaso kayana Yana jirana.



Nayi mamaki Amma Ganin yanda ya Wani hade Rai yasa na shiga Taitayina ,Nutsuwa ta shigeni Babu Musu na Aikata Abinda ya Umurceni Nayi.


Koda na Shige Ciki ,Su hafsah basua nan , Sunje School ,shiyasa ma basu saniba ma Har na gama kwashe kayana Nayi Gaba Basu Sani ba ,.


Wayan janaan na Ajiye mata Gefe sannan na dau nawa da Nagani saqale a charge nafito na same shi Cikin mota inda Yake zaune yana Jirana..

Kai tsaye KD Muka nufa, bamu Tsaya ko inaba sai Gidan mu.


Ramlah na Kitchen Tana Qoqarin hadawa Umma Abincin da zata Kai Mata Asibiti.

Yana Shiga kitchen din ya isketa Tana wanke kayan miya.

Bayan tayi masa sannu da zuwa yace tabar Girkin ya kawo wacce zata Qarasa ,Babu yanda ta iya dama a gajiye take haka Ta bar Girkin Ta koma daki ta fara Shirin Zuwa Asibitin.


Ni kuwa ina Shiga Part dina na Fada toilet Nayi Wanka sannan nayi Alwala na Gudanar da sallolin da suka hau kaina Ako Wani sujjada inayiwa Daddyna Fatan Allah ya fiddashi daga Hannun Azzalumannnan ,a karo na farko kenan da naji inason Fitowan Daddyna , ada kuwa ko zancensa banaso naji Sbd ina Ganin kaman baya sona Yana takura mn, baya Hanani rawar Gaban hantsi duk sbd Yana hanani Abubuwa Marasa kyau ,kuma nake Ganin yana dawowa takuran da Yake yi mn zata dawo Ina tsaka da jin dadin qaunar da Abbie da kakus Suke mn,


Ina idarwa saigashi ya shigo Fuskar nan a murtuqe ,Wata Uban tsawa ya daka mn Wanda yasa na Dan Zabura.


"Ke !"

Zuru Nayi masa ina kallonsa.

"Tashi kije Ki Girkawa Umma Abincin da zamu kai mata Asibiti..... Kuma ki shirya tare zamu tafi"


''Kama raina mn wayau Ni zan..." Kafin na qarasa naji Wata Uwar bugu a Bakina.


Wanda ya sanya Ni dafa Bakin nawa ina qunquni qasa qasa.

"Zakije ne ko sai na tattaka ki anan"

Jin yanda yayi maganar ne yasa naja qafata na nufi kitchen, babu jimawa na hado Abinci mai sauqin Ciyuwa Ga mare lafiya..


Ina gama Girkin na Sauko inda na taddasu A parlon qasa Duk Sunyi shirinsu na zuwa Asibitin.


Nima babu 6ata lokaci na shiga Nayi Wanka na Fito ,ko babu komai inason Inga yanda Umma ta koma ,Tumbinta ne ya zube ko kuwa?,Dukda babu Abinda ya gaya mn kan Ciwon nata ,Amma ai Ni Nasan Aikaaikan da nyi kafin na barosu.


chan qasan zuciyata kuwa Tausayin Daddyna ne ya Cika mn zuciya shiyasa Na kasance bani da Wata walwala.


Babu 6ata lokaci ya dauke mu duk Muka dunguma zuwa Asibiti.


Junayd ne zaune Gefen ta sai faman zuba surutu Suke ,Suna kwasan Dariya sai kace Abokan Juna.

Da sallama Muka Shigo ,Suka Amsa sallamar


Umma na ganin mu ta hade Rai kaman ba ita ta gama kwasan dariya ba



Aaryaan ya kauda Kai Gefe Ransa na suya ,ya Rasa Gane Irin Uwarda Allah ya bashi ,Ada shine na Gaban Goshinta ,batason ganin koda Damuwane a tattaredashi ,Amma a yanzu duk qaunarda take nuna masa ta juyeshi izuwa Kan junayd ,Ya rasa Qaunar Uwa a sanadiyyan Amincewa da Auren Ramlah da yayi.


Jiki a Sanye ya qarasa ya durqusa Har qasa ya Gaisheta ,ta Amsa Ciki Ciki kaman An tursasata.


Ramlah ma Gaisheta tayi Nan ma Amsawa tayi babu Yabo babu Fallaasa ,Nima na gaidata Amma Batako Amsa ba Idanunta na kanta Tana Mamakin Irin kayan da Ramlah Ke sawa a tsakankanin nan ,kayan dake sanye a jikinta mah Kayane masu tasada Wanda Aqalla zasu haura Dubu Dari bakwai zuwa sama ,Ga kuma Uban Agogon Gold Dinda Ke Sanye a hannunta Wanda aqalla Yakai Dubu Dari Ada kuwa bazaka ta6a Ganin Ramlah ta sanya kaya mai tsada ba Kullum tana lullu6ene Cikin Robar Atamfa wacce akafi sanida ~Matso kusa~ Takalmanta kuwa basua wuce na Roba suma, dukda Kuwa Irin tarin Azikinda dukiyan da Alhaji Issah ya Tara.


"Ke zonan " Umma ta fada a 'Dan Rude tana Kallon ramlah


Babu musu Ramlah ta qarasa wajenta Kanta a qasa.

"Ke wato An samu bulus ,za'a wanki banza a barshi da lahaula....da kudin uban wa ya kika siyar wa'ennnan tsadaddun Kayan?"

Ramlah batace komai ba Illla qara sunkuyar dakanta da tayi, Don ta lura yau 'Yan Rigiman Umma ne Suka motsa ,yo inba haka ba Ta saba ganinta da tsadaddunkaya wa'enda Suka taka Wannan a tsada mah ,sai yau tasan tana sanya kaya mai tsada? .


Nikam tsayawa nayi ina kallon ikon Allah Yayinda Aaryaan da Junayd suma mamakin sukeyi dukda kuwa ba sabon Abu bane a garesu tunda Umma ta saba wulaqanta Ramlahn a Gabansu.


A sukwane Junayd ya sulale ya bar dakin ,Don yasan Maganar da zata fito next Daga bakinta ba mai dadi bane..


"Keh , wai bada Ke nakeyi ba?... ,Nace Da kudin Ubanwa aka siya Wa'ennan Kayan? ,Don nasan Shegen ubanki Isah da Annamimiyar Uwarki Kulu Bazasu ta6a fitarda zunzurutun kudi su siya mki Wannan Kayan ba ,Sbd ysabar Maqo da Rashin Son 'da irin na mazasa Asali....Don haka kina komawa Gida inaso ki kwaso mn duk ilahirin kayanki Mai tsada ki tattarasu duka kisa Driver ya kai mn Gidana ,harda Golds da Sauran Abubbuwan Adon da 'Dana ya siya mki mai tsada ,Duk inason a kawo mn su, ni kuwa zan aika a siya mki matso kusa Wanda kk saba sawa nakai a dinka mki nasan shine yafi dacewa dake kina jina?"


Ramlah ta Gyada kai Alamar Gamsuwa, dukda kuwa sosai taji zafin Abinda Umman tayi mata Amma ko kadan bata nuna mata ba.


Shikuwa Aaryaan zama yayi Bisa Kujera tareda Sauke numfashi Cikin nutsuwa yace


"Nikam indai nine na Fiyarda kudi aka siyesu tau Babu inda zata kaisu , ....Umma me zakiyi dasu bayan kinada Wa'enda sukafisu tsada mah?, kefa dakanki kikace bata sanya Tufa mai tsada a gidansu Shine akace haramun ne tasasu A gidan mijinta? ,Umma idan Kayan kikeso ai basai kin Ci mata mutunci ba tukun magana zakiyi mn in sayo mki irinsu koma Fiyeda irinnata don bazan ta6a hadata dake ba"


Umma ta qwala mshi Bedpillown dake kusada ita Cikin hayagaga take fadin

"Kai Aaryaan ka nutsu kasan dawa kake magana ,Nice uwarka , wacce tasha Wahalar daukan Cikinta Sannan nasha Wahalar naquda Daga qalshe nasha Wahalar haihuwanka , SBD haka Abinda Nace shi za'ayi"


"Taah!" Na fada Cikin takaici.

Gabaki dayansu juyowa sukayi suna dubana.


Na hararesu.

"Umma na gaji da tsayuwa babu wurin zama ne?" Na fada ina 'Dan yatsine fuska...

"Fitsararriya nan ma futsarar kike son yi mana ko me?....idan bazaki iya zama a qasa ba ki barshi ki cigaba da tsayuwa...Aaryaan meyasa ka taho da yarinyar nan bayan kasan bana Son Ganinta?, Makarantar fa?"

Aaryaan ya 'Dan Sosa kai

"Umma dama na kawota ne ,ta Ga yanayin jikin naki Sannan tayi mki sallama Gobe zamu bar qasar"


Maganar ta tsaya Dif sakamakon Wani irin zabura da Umma tayi

"Zaku bar qasar Zuwa ina?"


"Tafiyan gaggawa ne ya kamani ,Kuma ya kama dole saina tafi da ita ,Don Akwai mutanen dake farautar Rayuwanta yanzun haka ma Daqyar Na iya qwatota ,da banzo b da yanzu an Gama da ita"


"Kai dalla zufe mn baki....Wai Kai Shashashan Inane? ,dan ana farautar Rayuwarta Sai me?, nace sai me?, I think she can Pretend to save her self!, ka manta yanda ta qwaci kanta Rannnan da Suka zo mata har Gida? ,ka manta A Ranar Cewa tayi su tafi dani? Me zakayi da wacce bata qaunar Uwarka?, Me zakayi da wacce take burin Ganin 6acin Ran Uwarka,Me akeyi da irin wa'ennan matan !....,ni? ,Ni Aaryaan idan ka tafi da ita ba da yawuna ba ,kuma bazan ta6a yafe maka ba har duniya ta nade Gara ka tafi ka barta ko an sami nasara akanta Bazai damemu bah......Ehey"



Nikuwa Kallon Umma na tsayayi ina maimaita kalmar Fitsararriyan da ta kirani a raina Don na Tambayi wurin zama ,kuma duk maganganunta Shiga kunnena suke Ina mamakin irin tafiyan da zamuyi mubar qasar batareda na Sani bah...



Kallon ko'ina nayi a dakin babu inda zan zauna Gashi bana son zama qasan Rug ,Bare kan Gadon Umma Wanda yake shine kadai Wurin Zaman da ya rage a dakin kasancewar an fidda kujerun dake Asibitin za'a Sanya wasu..

Kalaman Umma Suka sake

Please Login or Register in order to submit comment