Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qare



Ya fara magana Rai6ace Amma cikin natsuwa yace"Mum!, I'll do as You said, bazan Qara koda kallonta ba Bare Shiga dakinta ....." maganar ya tsaya mai a maqoshi ya Girgiza kai Sannan ya juya ya nufi Hanyar Fita,Umma ta bishi da kallo Gabanta na dukan 3-3 Yanda taga yanayinshi har ta Sadaqar Itama bugunta zaiyi saitaga Aikasin haka.



Har ya kai bakin kofa Sannan ya juyo Yace" pls mum idan na Fita Ki Kasheta ne kafin na dawo Shi zai Nuna mn Tsananin Tsanan da kike Nuna mata" yana kaiwa nan yasa kai ya fice, Dan bai fiye Dogon magana ba in yana Cikin Yanayi na fushi.

Yana Fita Umma ta Fashe DA wani irin Kuka Wanda batasan Dalilinsa ba Tana Surutai.


Hafsah dake duqe ta kalleta Sannan ta kauda kai ,Batason Ganin Zubar Hawayen mahaifiyarta,Miqewa tayi itama ta fice ko Sallama batayi Mata ba.

Umma ta share qwalla Sannan ta miqe ta nufi dakin Ramlah.

Ramlah dake daki tana jiyo Zantawansu ta Zube kan Gado tana Hawaye,


Babu zato babu tsanmani Ta ji muryan Umma tana fadin"Tashi munafika AlGunguma DanGin marasa Asali, yanzu hankalin ki ya kwanta kin sa Dan da na Haifa ya wukaqantani ya tozarta ni duk Saboda ke, to wallahi yanda kika bari 'dana ya ci mutunci na Sai na ci naki mutuncin da na iyayenki dama Chan ba mutunci Gareku ba"

Ramlah ta tashi zaune tareda katseta Ganin Ta fara Ta6o Iyayenta baki na Rawa tace "Um..ma k..iyi Haq..uri"


Cikin Tsawa Umma tace"Rufe min baki Manafika, ina miki Gargadi Da babban murya daga yau Idan na sake Ganin kin Kalle 'dana Saina tsiyaye idanunki Dan Bakida Hurumin yin Hakan,idan kuma Kika Sake kuka qara hada hanya dashi koda wasa Saina Yanke kafafunki inyaso daga baya ko mezai faru ya Faru, idan kuma hannun ki ya sake y ta6a koda Tufafinsa ne Sai nasa An yanke hannayenki Gaba daya, Idan kuma Hancinki yayi kuskuren Shaqar koda kamshin Turarensa ne Saina yanke hancin ,idan Idanunki Suka Yi kuskuren sake Kallon koda Kayansa ne Saina Qwaqulesu Gaba daya !, Kinji na Gaya miki,in kunne yaji Ganganjiki ya tsira" umma Ta fada ranta na Suya .

Ramlah ta Daga kai Alaman Gamsuwa hawaye na malala Saman Fuskarta.


Umma tace "oya Tashi kije ki karasa Aikin da na saki.., Mayyah kin Takura Wa Rayuwa ta Kin rushe mn Farin'cikina Kin Haddasa Raini Tsakani na da 'dana Tsakani na daku Allah ya'isa sai Allah ya mana hisabi Ranar Gibe qeeyamerh"

(Chai๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ)


Ramlah ta miqe tana kuka jiki na Rawa ta nufi hanyar Fita, Umma ta Shureta Ta fadi Ruf da ciki ta qara ham6arinta da Kafa,Kukanta ya tsananta ta tashi cikin Qarfin Hali jiri ya jaata Ta kuma Faduwa

*******


Aaryaan kuwa yana Fita Ya kira Driver ya jashi Dan bazai iya tuqi cikin Fushi ba.


Kai tsaye Asibitin Shika Suka nufa,Ya ba Driver kudin Taxi yace ya wuce Gida sannan Ya shige Asibitin, Bayan ya Gama Abinda zaiyi yana zaune a Office dinshi Yana Tunanin Halayya irin na Umma ya Rasa mai yasa bata son Ramlah,Ya rasa meye laifinta Dan Iyayenta basu da Asali basu da Dangin kowa, Dagasu Sai su ne, yayi zurfi cikin Tunani Baisan lokacin da Hilaal ya Shigo ba ,Yana magana baijishi ba Saida ya Dan ta6a shi sannan yayi Firgigit ya dawo Cikin Hayyacinsa.



Hilaal ya zauna kan Desk ya Ajiye Yan takardun dake hannunsa Sannan cikin zolaya yace"Angon 3k har ka Fara Tunanin kwailar Amaryar taka ne Tun ba'a kai ko'ina ba?"


Aaryaan bayaso Hilaal ya Fahimci Yana cikin damuwa shiyasa ya Danne 6acen ransa yayi yar dariya yace"Kaifa banza ne wlh ,Me Yarinyar ke dashi da har zata Sani Tunanita?, Ai bata kai matsayin nan ba, Mai Sani Tunani Ai sai Ramlah "

Hilaal yayi dariya yace "Abinda kukasha Cikin Icecream Shi Take dashi kuma ya isa ya Saka tunanin ta,With Time zakayi bayani ai, tunda ba da 3k aka daura Amren ba" ta fada yana qara tubtsurewa da dariya.

Aaryaan ya Jefeshi da Hularshi da ya Aza kan desk, yace"Zan kama ka ai,Zaka mn Bayanin ko da Nawa aka daura"

"Allah bada 3k aka daura ba,Baka Kalle Videon bane?"

"Ina na Samu time"


Hilaal yayi dariya yace" akan 200k aka Daura".


Zaro ido yayi Cikin mamaki "Two hundred me?" Ya furta cikin mamaki da Al'ajabi.

"Thousands" Hilaal ya qarasa mai Yana danne dariyar sa.


Aaryaan yace "Allah bazan Biya 200k akan Sadakin yarinyar nan ba!, Sai in kai zaka biya Dan ni bazan biya sadakin 6era akan sadaki 200k ba,She's just 17 fah,Ni Allah na tuba in banda taimako Ina ni ina Yarinyar nan da ko hankali bata Cika ba?,Amma Wlh Hilaal Raina ni, Halan baka San zafin nema bane"


(A Zuciyar shi kam ya karyata kanshi Dan Munayferh tafi Qarfin a Hadata da qwaila ko 6era a wuni Guda ta Tafi da Tunanin sa, yayi zaton yanda Yar Fikika a Shekaru Haka take a Ehmm....Shiyasa ya Rufe ido ya Yanka dubu Uku a matsayin Sadakinta)


Sai yanzu ya tuna ya baroni a Gida babu kowa,Kuma Yaga Hafsah tayi Shirin makaranta ya tabbata idan Suka hadu da janaan Saita tambayeta ina Munayferh.


Zumbur ya miqe Kaman Wanda Aka tsikara yana tattara Wayoyinsa yace" Rakani inje in Dubata,na barota ita kadai a Gida"




******


Sai 12:00pm na Tashi da matsanancin Yunwa, Zazza6in da na kwanta dashi har ya ware.

Miqewa nayi ina hamma na nufi Bayi nayi wanka Sannan na Shiga daki Dan daukan kayan Da zan Sauya, dakinsa kadai ne a bude Shiyasa babu kayan mata a dakin Sai nashi.


Dube Dube na farayi a dakin kaman wacce ta bashi Ajiya, Saida nayi kaca kaca da dakin Sannan na Dauko wata Farar jallabiya cikin kayansa na saka na fito kitchen Dan Girka Abinda ZansaWa baki na.


Amma Abin Takaici duk kayan Abincin Sun lallace Saboda mun Dan Dade bamuzo Gidan ba.



Fitowa nayi na nufi Garden Dan Tsinkan Fruit,Daidai lokacin Motar yaaAary ya parka a harabar Gidan.....Zaro ido nayi na koma ciki a Guje, Ashe ya Ganni, yace Wa Hilaal ya jirashi a waje wai kar ya kalle mai mata๐Ÿ˜.


Ina Shiga na Zube kan 3seater na kulle idona Dan ya dauka barci nake.

Saukan Dundun da naji a baya na yasa na Miqe a Razane Ina Zumburo baki tareda Sosa bayana Saboda Dukan ya shige ni Sosai.


Saida ya kalleni Tun daga Sama har qasa sannan yace "Kayan Wa kika sa?"



Baya baya na farayi da Sauri dasauri Yana bina ahankali, ina shiga Daki na daga murya Sannan nace"Ka tambayi kayan mana" ina Gama fadin Haka na Rifo kofar da sauri ina ....







Waiting For Your Comments๐Ÿ–‹๏ธ



Don't Forget To share fa๐Ÿ˜ƒ




Fatima Nike ba Farha ba๐Ÿ˜‰



Fahnaan na nufin FATIMA da NaNa(Bestie๐Ÿ˜‰๐Ÿ’–)




Kun gane ko!๐Ÿ˜Œ




Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

9thSeptember๐Ÿ–‹๏ธ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 28_*

Na Rufo kofar ina dariya Sannan na fara Dube-Duben makulli

Jinayi ya Banko kofar ya Shigo,Fuskar nan dauke da murmushin mugunta, Wanda ya saba yimn.


Chak na tsayarda dariyan da nakeyi,Tsoro ya kamani,Jikina ya fara Rawa baki na Rawa nace"Ki...pya, Chama"(So....rry Pl...ease)


"Sorry for what?,Nifa zuwa nayi na tambayi kayan" ya fada yana dago Fuskata dake Sunkuye,Alamar na kalleshi,Ni kuwa Tun jiya da Abin ya faru na kasa kallon Cikin Qwayar idonsa ,Saboda ko na kwatanta hakan Sai naji Gabana na fadi.


Gabana ya qara faduwa cikin Rashin Sanin Madafa na fara Hawaye, Sakin Fuskata yayi Sannan yace" kukan Fa?"

"Main bhookha hoon"(Yunwa nake ji). na fada ina matse ido



Da yatsa ya mn nuni DA Kitchen sannan yace"jao aur khaana banao"(kije kiyi Girki)


"Ai duk kayan Abincin Sun lallace"

Maganar ta bashi dariya, kayan da kwataยฒ basu wuce Sati Uku da Siyowa ba yace"Kodai Girkin ne baki iya ba?, taya za'ayi foodstuffs dinda basu wuce 3wks ba su lallace"

Na kwa6e fuska nace"Wallahi Dagaske nake Duk sun lallace harda Qasa-qasa a kansu ma"

Dariya ya sakeyi kafin yace "Kin yarda muje a duba idan Basu lallace ba ,Zaki bi duk Abinda na Umurce ki kiyi koda Ranki baya so,Amma idan Sun lallace da Gaske Na yarda ki juyani Kaman bawanki"


Tsoro ya kamani ,Tunawa nayi da Yanda naga Kayan Abincin ~(Yasin sun lallace~) Raina ya qara bani Tabbacin hakan.


Gyada kai nayi Alamar "Eh" a raina ina Kitsa yanda zan juya yaaAary idan hakan ya kasance Gaskiya ne,Saina maidashi Abin tausayi๐Ÿ˜†.

Ya tasani Gaba muka nufi kitchen, Kayan suna nan yanda suke babu Wanda ya lallace a cikinsu,Sunyi kura ne kawai.


Ya kakka6e Kurar da hannunshi Sannan kalleni yana Murmushin mugunta yace"Finally I'm the winner "


Narai-Narai nayi da idanu Hawaye na shirin Zuba nace"Nifa ban dau Maka al'qawari ba"


"Tun baki San Kudiri na ba Zaki fara min kuka,Aap kya Ummeed kar Rahe hain? ~what are you expecting?~ ,Ni yau Girkin Amarya nake son ci" ya fada yana Shafa mn Dattin Kurar hannunsa bisa Fuskata.


Sunkayar da kai nayi Hawayen da nake dannewa suka zubo Saman kunci na ,Tabbas da na San manufar sa kenan Da banyi Saurin Amincewa ba, jiki a sanyaye murya a sarqaqe nace "Bazan iya Girki ba,hannu na ya Gurde dazun"Murmushi kawai yayi ya fice zuwa Store ya debo dankalin turawa da Kwai ya Zube a gaba na Sannan yace na idan hannun nawa ya Dawo Daidai na Gyara Kitchen dn Na hada masa break yana tare da baqo ,ya fice Abinsa,


Yana Fira na bi bayan sa da Harara na kwashe potatoes na Wanke, na fara Tunanin Next abinyi.



Wuqa na Dauko na fere dankalin,Wanda gaba daya Rabin nayi asarar su ne,Sannan na dauraye FryingPan na zuba mangyada Na Dauko lighter zan kunna Gas,Toh anan fa akeyin ta Dan nida Hafsah Tsoron Gas mukeyi,Fitowa nayi na nufi falo Naga bayanan



Sannan na nufi hanyar waje,A jikin motarsa nagansu Shida Hilaal Suna hira,Hilal ne ya fara Ankarewa dani ya ta6o Aaryan cikin dariya yace" Angon Ga amaryar fa"

Aaryaan ya dago ya dubeni Ya wani murtuqe fuska.


Hilaal ya cigaba da cewa"Ege Abokin, Manya kenan Cikin sati Biyu ka Auro Mata Biyu,Ai ba ko wani Namiji bane zai iya taka sa'a irin Wanda ka taka ba,Auren mata Biyu a sati Biyu kachal, Lallai kai waska ne nima a samo mn irin qwailan nan nayi sama da ita mana"

Aaryaan ya watsa mashi Harara Sannan ya nufo inda nake tsaye na kasa karasowa ya fizgo hannuna yayi ciki dani,Ya watsar dani Saman cushion yana Huci ya nufi daki inda nayi Chaka-chaka ,Da qyar ya samo hijabi na ya kawo mn nasa ina Zaro ido jiki na har wani kyarma saboda Tsoro bansan me nayi masa ba lokaci Guda ya wani chanza ya koma Ainihin YaaAary Dinsa.

Ban gama Saka hijabin ba ya funciko hannuna Mukayi waje ya bude mota Wurgani gabanMota, sannan ya shiga ya tada engine.


Hilaal dake tsaye inda ya barshi dazun yace"Man tafiya zakayi ka barni?"


Aaryaan ya dakatar da motar ya shiga Yaja muka bar Lowcost.


A mota kua Gaba daya muka koma kurame Babu mai magana dagani har Aaryaan da Hilaal dn.Ayau nayi niyyar daukan fansar Dukan da Yamin A satin Farkon Auren su shiyasa na shiga tunanin ta inda zan fara,Shi kuma Hilaal Tunani yakeyi akan dalilin da yasa Aaryaan 'daurewa kaman ba yanzu suka gama raha tare ba.


Muna isa Tudun wada Hilaal ya sauka Aaryaan ya Ciro Form ya miqa mashi sannan yace zanzo Anjima Dan yin thumb print, Hilaal ya gyada kai ya wuce, Aaryaan kuma ya ja motar.


Sai yanzu ya Rage Gudun tuqin da yakeyi ya kuma sakin Fuskar nan,Wata Ajiyan zuciya na Saki batare da na kalleshi ba nace"Yayan hafsah ,Wai Dama haka Namiji ke Auren mace yana horar ta da yunwa?"


Maganar ta bashi Darya shiyasa na ya dara, a ko DA yaushe nakan 6ata masa rai Amma wauta ta ke sa shi Nishadi.

Shima ba tareda ya kalleni baYace"Ina kika ta6a Ganin An Auri mace bata iya Girki ba?"

Nace"ni ai na iya"

"Toh me yasa Baki dafa kinci ba"

"Ai amare basua Girki,Kuma ai hannuna ya gurde sai yanzu ya dawo dai-dai"


Ya kalleni yayi Yar murmushi ~(wato amare Masu Girki lallai Yarinyar nan)~

Bai sake cewa komai ba Har muka isa wani Katon Store ya tsaya anan ya Siya min kayan Sawa harda hijabai Dan ya kura bani da Wasu hijabai,anan na Sauya kayan Pakistan Maroon Ne da Pink hijab nayi matuqar kyau shi kansa Aaryaan Sai wani Satan Kallona yake yi, Har muka isa ABU anan School Cafeteria yayi mana ordern Abinci Saida naci nayi nak,Sannan ya Rakoni hargaban Theatre da kin Ganmu a lokacin Zaki dauka masoya ne dukda ba wani Magana mukeyi ba.


Har zan haura Saman lecture theatre naji Kirani ,Na juyo na kalleshi yace"A Riqe darajar Aure a tsayda hankali Guri daya ayi karatu,Banda shirme ,Allah ya bada sa'a"


Kallonsa nayi cikin mamakin kalamansa Wai da gaske Shi din ne ko dai wani mai kamar sa ne!,Ni tunda nake bai ta6a mn magana cikin taushin Murya irin haka ba harda Addu'a Waiiii.


Murmushi nayi Wanda ya qara Fito da Asalin kyawu na nace"daganan ina zaka wuce?"

Yace"Babban dodo(secteria) zani sai 5:30 na yamma zan dawo amma me yasa kika tambaya?"

Nace"Laifi ne idan Mata ta tambaye mijinta inda zaI je"

Yayi murmushi tareda kawar da zancen da Cewa "idan an tashi ki Kirani da wayan Hafsah, Zanzo na dauke Ku"


Na Ta6e baki"ka Sani ni ban aran Abin wani,Haka kuma ban anfani da Abinda ba nawa ba "

Ya Ciro wata Waya daga Aljihun Gaban Riganshi ya cireSim din ya saka wata layi ya miqa min ba tare da ya ce komai ba,Da murna na amsa babu ko Godiya๐Ÿ˜.


Yana Wucewa nabi bayansa da Harara lallai YaaAary ka raina ni ka dauka na Manta dukan da kamin ne?,Ka manta bana barin bashi kor ,ka tanadi Abubuwan Gashin jiki Dan A yau sai nasa an Zane min kai har Sai ka koma Abin tausayi.


INA shiga Aji Gaba daya Yan Aji suka Bini da kallo,Har saida na Tsargu na kasa karasawa inda Su hafsah suke na zauna a front seat ,Matar dake zaune kusa dani ta kalleni tace "Kece Munayferh junayd ko?"

Na gyada kai Alamar Eh nace"Lafiya naga duk kuna kallona Sai kace naci bashinku?"

Tace "Ai Dole abiki da kallo Kece fa kikasa aka Korar mana mugun malamin ORGANIC Wato KS daud,Kuma daga lokacin kika yi kaura da Makarantar, Ai irinku mukeso Masu Hana Shuwagabanni Alfasha Ai kinyi kyan kai "

Zaro ido nayi Wai dama korarshi akayi?,To taya kuka San nice dalilin korar sa"

Zata bani amsa lecturer ya shigo daganan muka maida hankali karatu ya kankama,Bayan mun Gama lectures ne Muka Samu ganawa dasu Jaanaan Amma na lura da kallon da Janaan take Auna min kaman na tuhuma,


Library mukaje Dan mu danyi karatu kafin Time din next lecture yayi Muna zaune muna karatu muna Dan Ta6a hira akai akai hafsah tace"Wai Dan Allah Nayfee a'ina kika samo kayan nan Da Alama Sabo ne Sunyi miki kyau fa"


Nayi murmushi nace"yayanki ne ya Siya min dazu"

Ta zaro ido "a ina kuka hadu?"

Na kalle janaan kafin nayi magana ta chafke"Ba na Gaya miki yazo ya dauke ta da safe sun wuce ba ?,Ki bar maganar nan ma pls,Kije campus ki duba kitchen Saman Cabinet zakiga FoodFlask cikin Basket ki Dauko mana "

Hafsah tace"Meye kika Girka mana? "

"Dan wake" jaanaan ta bata amsa kai tsaye.

Hafsah ta miqe ta Dan dakatsalle yes nayi Gabas ๐Ÿคจ,,Sannan ta fice


Ni kuwa na bita da ido har ta 6acewa gani na,Janan ta juyo Gareni ta fuskance ni Sosai ta kira Sunana "neryfee!"


Yanda ta kira sunana yasa Gabana ya tsananta Faduwa dama Tun dazu da na lura DA irin kallonda take mn na tsargu Sosai.



Ta cigaba da cewa" yaushe kukayi Aure da yaaAary?, Kuma meyasa Baku Son a Sani ?, ko da yike na lura Auren Sirri kukayi Amma fa boyewan da kukeyi Yanada Hadari sosai ....."


Na katseta da Cewa "Jaanu ya akayi kika San wannan Sirrin ?"

Tace"Jiya Naji yana miki Gargadi cikin maganganunsa yayi subul da baka ya fada kuma ya fa'da kunna na,Wai ya akayi hakan ta faru ne?,kuma me yasa kuke 6oyewa?,nifa na shiga duhu I'm totally Confused"


Hawaye Suka fara bin Fuskata Shikenan tunda jaanu taji Sirrin babu buqatar na 6oye Mata komai a kan lamarin,


Cikin kuka na kwashe Mata duk yanda akayi har Mukayi Auren kan titi a dalilin Icecream,Na daura da cewa "Wallahi jaanu ba Wai Auren kadai nake Qi ba yanda Zaman mu da Umma zai kasance ne, ke kanki shaida ce akan bana son Auren Namiji mai uwa a duniya,kuma Gashi Banda Uwa Yanada Mata,Gashi ya tsane ni,Ni inda so Samu ne nafi so yanda nake Virgin in Auri mutum Virgin Wanda bai ta6a sanin mace ba koda yana da Aure" na fada ina kara Rushewa da Kuka Sosai.


Jaanaan ta Jawoni jikinta tana bubbuga bayana Cikin muryan tausasawa tace"Kiyi Haquri ,Yanzu ya kike so ayi"

Dagowa nayi na raba Jikin mu cikin Shesaheqan kuka nace"So nake na Samu ya sake ni kawai na huta"

Janaan tace "idan saki kike so wannan ai me sauqi ne kawo kunnen ki kiji"


Ta Rada min a kunne,Zaro ido nayi bayan na Gama jin Abinda ta fadi mn nace "Kai wlh bazan iya ba,taya za'ayi ya sakeni ta wannan hanyan?,Ai sai ya dauka Neman sa nakeyi"

Janaan tayi dariya "Toh banzah,Ai Hakan ne kadai zai sa ya sake ki,kinga Idan Yaga kina masa haka tunda kince ya tsane ki Ko baiyi niyya ba saiya sake ki,Especially idan kina dan kwatantawa a Gaban Umma, bazata so ganin danta yana Aikata Alfasha ba,Kinga daga lokacin da ta fara Ganin Ku a tare zata fara Raba ki dashi ke kuma kina Cusa kanki A gareshi,Idan Umma ta dameshi da masifa Da kanshi zai fito ya fa'da Aure kukayi kinga daganan zata Matsa mai Dole sai ya sake ki,Kinsan kuma baya wasa da Umurnin Umma Shikenan fa....."













KAI JANAAN KIJI TSORON ALLAH WANNAN BA SHAWARA BACE๐Ÿ˜†



Nayi gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ




Waiting For Your Comments


Wattpad @Fahnaan


11th sep๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 29_*

Na Fito da idanu tareda dafe kirji"Please Jaan Rufa mn asiri Wlh bazan iya ba,Ko a yanzu kunyar sa nakeji Bana iya kallon cikin idonsa ,Hakan kuma ba qaramin cikas ya jawo mn ba sai cutana yakeyi yana amfani da wannan daman wajen Cusa mn baqin ciki, please ki sake Tunani ni mafita nake nema ba wurin zama ba"

Jannan taja tsaki"Mtsww,Ke dama ba'a Abin Arziqi dake ,Tashi ki bani wuri " ta fada tana juya mn baya.


Jikina yayi Sanyi matuqa,Gashi NA farajin Qamshin Gaskiya cikin maganGanunta,Dafata nayi ta baya cikin muryan kuka nace "listen to me,Ba cewa nayi bazan iya ba,Kina ganin hakan shine mafita?,taya za'ayi ya Sakeni ta wannan fannin"


Janan ta juyo fuska dauke da kayataccen murmushi Wanda ita kadai ta San ma'anar Abinta tace " Neyfee, nima shaida ce akan yanda yaaAary ya tsane Ki, Ba cewa nayi ki bashi kanki ba,aah...Tada hankalin shi zakiyi Sai kinga ya fara Zaucewa sai ki Zame, ki yawaita shiga dakinsa idan hankalin Umma na Gareshi, kin Gane?, kar ki kwatanta hakan a Gaban Ramlah kinsan Sokuwace tanada Haquri yanzu Zuciyarta zata buga ta sheqa barzau, ki barta ta jida da baqincikin Umma" ta qarashe magana tareda kannemin ido daya.



"Lallai Janaan,Baki ta6a yin body contract da Namiji bane shiyasa kika ce nayi hakan, dama a da ne zan'iya Amma Gaskiya ni kunyar sa nakeji Sosai''


" Mtsww banza tsaya binta kunya bakisan Kudurinsa na hanaki Gayawa kowa ba, daga Kashe Ya Gama dake ya watsar,babu Wanda yasan da Aure A Tsakani ki shiga uku ki lallashe ,kina wana wani kunya sai kace ba Aure kukayi ba Ai cire kunyar nan zakiyi ki Ajiye ta Gefe Sannan Yi yanda nace kiyi daga baya kia Rufe kanki a daki kiyi taji kunyan ki ke kadai".


Nace"Haka ne fa, taya hakan zata kasance?, kinsan Hafsah bata Sani ba, kuma baaso tasani"


"Wannan ai mai sauqi ne,duk randa kin shirya Ki mn magana zan San yanda zanyi na dauke Hafsah ta kwana a Campus kinga sai kuci karenki babu babbaka"




Hararar ta nayi nace "Nifa har yanzu Gama yarda da wannan Shawarar ba, taya za'ayi na dauke hankalin sa da wannan kin sanshi da miskilancin Tsiya , wlh in yaaAary ne nan take zai 6a66allani babu Ruwanshi"


Janaan tayi dariya tana duba Agogon dake daure a tsintsiyan hannunta tace"naga Hafsah bata dawo ba Muje na baki Weapons na daukan hankalin namiji ko wayeshi ba miskili ba sai ya kwanto" ta fada tareda miqewa tana tattara littafin Gaban mu.



Muka Fito daga libraryn, A hanya take bani karin haske akan yanda zanyi yaaAary ya Sakeni cikin sauqi๐Ÿฅด.



"Munayferh Junayd"
Naji ankira ni ta baya,Waigawa nayi ina kallonsa, wani course mate din mu ne Wato badaruh an fi sannin sa da bhaddy,Yaron irin yarannan ne yan ithkan makaranta kuma Masu ji da kansu Irinsu ne bazaku ta6a ganinsa shi kadaiba saida Gang din sa Wato tawagar sa Masu taka masa baya.


Ya tako har inda muke tsaye yana wani munafukin murmushi Cikin muryansa mai kamada na Yan daba yakalle janaan yace" Hy"

Tayi yar takaitaccen murmushi ba tareda ta amsa mshi ba,Bai damu ba ya juyo Gareni yace "Hawfar, Tun randa kika sa aka Kora mana banzan chan kika ware Kikayi wuyan gani Hope lafiya dai ko?, Duk ba ma wannan ba" ya kallemu up and down ya cigaba da cewa "Naga kaman Sauri kukeyi zan iya samun Koda numbern wayan ki ne?, Dan ina so na kiraki na karayi miki Godiya na musamman akan Gagarumin Aikin DA kikayi lallai kin chanchanci yabo,Dan haka duk mai son takura miki a Makarantar nan ki neme ni zan tsaya miki nida boys dna Koshi waye wannan tukuici ne a Gareki"


Na gyara tsayuwa Jaanaan ta dubeni tana jiran jin ta baki na.


Na fiddo wayan da YaaAary ya bani dazun na kunna Sai naga hotonsa kan Wallpaper din wayan ya hade cikin kananan kaya farar Riga logo less Da black jeans kansa daure da Farar band mai Rubutun AAcosten, Fuskar nan dauke da murmushi, nima take wata murmushi ya su6uce mn na nunawa Bhadee nace "kasan wannan?,"


Yace"Eh mana!, Saurayinki Wanda ya kawoki dazu".

Nace"Ba Saurayi na bane,Drivern Gidan mu ne"

Ya katseni"Koma wayeshi ai wannan bata Shafe ni ba, Number wayanki nake buqata"


Nace"NI MATAR AURE CE, kuma mijina bayaso maza na kirana a waya, Amma ka bani naka numbern wata taimakon Gaggawa Zakuyi mn"

Bhadeh ya Ciro complementary card Dinsa ya miqa min na amsa na cigaba da cewa "Mutumin nan shi ke takura mn ya hanani saqat, So nake Ku Zane mn shi kaida boys dnka ya daku Sosai Amma kar Ku ji mshi ciwo DanAllah,"



Bahdee yace"Angama Ranki Shi Dade ai kinfi karfinhaka ko Kashe shi kikace Muyi a shirye muke danUbansa yauzai gane kurensa,Aina zamu same shi? "


"A Fada Babbandodo,wurin Secteriat Yana nan har 5:30 na yamma idn kun gama I'll pay you huge"


Janan ta Bini da kallon mamaki baki sake Wai Yarinyar nan tana fama da matsalar jinnu ne ko me?, Mijinta zatasa Yan daba su Kama?!.

Hannunta d naja yasa ta dawo cikin hayyacinta nace"Muje"


Muka yi gaba janaantace
"Kai neryfee Amma baki da imani wlh,Mijin naki zakisa a Daka?,Me yayi mki?"


Nayi dariya Sosai "Kin manta dukan DA yayi mn a satin Auren su kenan har yanzu ina jinya ,na tabbata Yafi Qarfin su Amma Ance Sarkin yawa yafi Sarkin karfi Su lafta minshi kawai".


Janaan tayi kwafa tace"Allah ya shirye ki"
Na amsa da Ameen


A Gidan muka tarar da hafsah an jawo wuta ta kunna TV tana kallo hankali kwance ta shanya mu.

Bata ma San mun shigo ba hankalinta yayi nisa, zuwa nayi na kashe TVn ta juyo a firgice tana kallon mu na watsa mata Harara sannan na nufi hanyar kitchen

"Kai !dama biyoni kuka yi? har kun

Please Login or Register in order to submit comment