Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cikin yini Guda Rayuwa ta ta sauya Daga Jin dadi zuwa fargaba Da Rashin Samun Kwanciyar hankali.

***


A dayan 6angaren Kuwa kafin kace me ?, labari ya karade koina Diyar JY ta 6ata 'yan jarida da 'yan Quf Quf Abin nema ya samu nan Aka Cigaba da Zuqu da qari.


Abu kaman wasa Har tsawon Sati Biyu babu Ni babu Alamana Duk iya Qoqarin da Jibril Yake Don Ganin ya taimaka na koma Gida A daina nemana Abin ya faskara Har takarda ta rubuta Amma suka kasa Fahimtar Abinda Yake Nufi.

Gida ya Hargitse Kowa ya koma babu walwala harta Ma'aikatan Gidan da nake Takura mawa sunji babu dadi KO babu Komai Diyar Ogansu ce ta 6ata....


Harta Umma Saida Abin ya tsorata ta Don Tunda Abba ya samu lbrn 6acewana Ya Fara Ciwon Zaune , Baya iya komai sai bin Mutane da idanu hankalinta ya kai maqura a tashi Amma badon Danasani ba ko nadama Sai don Fargabar Rasa nata Mijin ,Duk Bidirin da Ake Ciki Aaryaan babu Wanda ya sanar da Aaryaan Gudun tashin hankalinsa .


Sosai nake samun Kulawa daga Mahaifiyar Jibril da qanwarsa Dukda kuwa Suma Suna Ganin Munin Halittata Amma hakan bai sa sun qyamaceni ba , a Kullum burinsu Shine na kwantar da hankalina , Mahaifiyar Jeeboi wacce Suke kirada Mama Ta lurada Abinda Ke tattaredani yanada Nasaba da Sihiri don haka ta dage Wajen Nemo Mn Addu'oi Tana bani harda Su Haseen don Suma Har yau basu farko daga barcin da Sukeyi ba ,

a Gefe Guda kuwa na Cire duk tunanin Komawa Gida a Raina Har zuwa Ranar da zan Cikawa Umma Da Qawarta Alqawarin da na daukar musu ,Nauyin Alqawarin da Tunanin halinda su ammie Suke Ciki ya hanani saqat Kullum sainasa Jeeboi yaje Gidanmu Ya Nemo mn Rahoton Abindake Faruwa Anan dukda Kuwa daqyar Yake iya Fahimtar Abinda nake Fadi kasancewar Muryan sai a hankali.........

A yau Nayi niyyar Aiwatar da qudurina Ga Hajiya Asiya don haka na rubuta Abubuwan da nake Buqata a takarda na bawa Jeeboi Na Riqe shi da ya siyo mn su , babu Musu yaje ya siyo Batareda ya San me zanyi dasu ba ,don harga Allah Tausayi na Yake ji Har Cikin Ransa ,A natse na hada Komai Na chakudasu Waje daya Maryam qanwarsa wacce bata wuce Shekaru 19 ba Tana zaune Tana kallon Yanda nake sarrafa Chemicals.

"Sister wannan Abinda kike hadawa Na meye kuma"

"Na daukan Fansa ne "


Na bata Amsa bataji me Nace ba Ta kasa kunnenta Sosai saitin Bakina tace me kikace.


Hawayen da Suka tarunmn a idanu na share da bayan Hannu Shikenan Ni a haka Rayuwa ta zata qare Cikin BaqinCiki a haka zan dawwama Kafin A fahimci maganar da nakeyi ma sai an kasa kunne dukda Amsa Kowar da Muryan keyi.


Maryam na Gani na fara hawaye ta shiga Rarrashi na Cikin Tsananin tausayawa.....


***

A yau Aaryaan yake Shirin dawowa Kaduna Saboda Mugayen mafarkin da yakeyi akaina Cikin 'yan kwanakin nan ..


1:00pm.

Motarsa Qirar Firari Ta danno kai Cikin Unguwar , haka kawai ya tsinci kansa cikin matsanancin Faduwan Gaba.


Koda yayi horn mai Gadi ya bude masa qofa MaiGadi ya Bude masa Qofa Tundaga yanayin mai Gadin ya fahimci Akwai Matsala don haka yana shiga kai tsaye Part dinmu ya nufa .


Turus yayi a Bakin qofa Ganin Kakus Mimmiqe a Kan 3seater Doctor na dubata Ga Daddy da Abba dake Zaune Sunyi Jugum Jugum sun Wani Rame sai kace wa'enda Sukayi Shekara Suna Ciwo .



"Abbie...." Ya kira Sunan Abba A raunane .


A razane duk suka dago Suka kalleshi ,Binsu yayi da kallo 'daya bayan 'daya kafin yace

"Daddy ina Sulthy?...."


Ya qarashe maganar Cikin fuzgar Numfashi, Ganin sun kafeshi da idanu babu Amsa yasa haura Dakina da Gudu yana qwala mn kira ,Babu inda bai duba ba amma Babuni babu Alamana.

Dawowa yayi ya kafesu da jajayen idanuwansa Wa'enda suka rikide Suka koma tamkar Gauta.....


"Abba ina Munayferh take ?, Daddy ina Sulthy taje ?, ina Yarana?, ina ta tafi Batareda ta nemi izini na ba? ,Abba ko Wani Abu ya faru da ita ne?, Meyasa kuke 6oye mn ne? Ku gaya mn me ya faru da ita"



Gaba dayansu Ido suka Zuba masa Cikin Tsananin Tashin hankali 6acewar Munayferh ta dawo msu Sabo Cikin Rudani Hawaye suka fara bin kan dakalin Fuskar Ammie , Abba Kuwa bashida Qarfin yin komai ido kawai ya zubawa 'Dan nasa yana kallo kaman ya Sami television ,Daddyne mai Qarfin hali Wanda ya iya Gaya Abinda ya faru bayan yaja hankalinsa da Rarrashi da Nasiha.


Tunda Daddy ya fara magana Aaryaan ya zuba masa idanu yana jin ransa na quna Yanaji idan daba Daddy ya gaya masa wannan maganar ba da ya tattaka Duk Wanda zai tunkareshi da maganar.


A hankali ya koma da baya ya zauna bisa Cushion ya jingine kansa ya kalle sama Duk Suka bishi da idanu don Jin ta Bakinsa Amma Baiyi magana ba Al'amarin ya kuma rudasu , yakai Kusan hour daya a hakan bai motsa ba hakan yasa Daddy ya tsargu yana dagoshi ya kifa a qasa Hakan yasa Duk suka sake Gigicewa

Umma da taga Shigowarsa ta window tabiyo bayansa Ta Dora Hannu aka ta fasa ihu ,daddy kuwa sai Qwala masa kira yakeyi yana Girgiza shi ,Ganin baya motsi.


Cikin qanqanin Lokaci Aka Isa dashi Asibiti ,Likitoci suka fara Aikinsu , Abba ya koma Gefe yana Sharar qwalla Tausayin 'Dan nasa ya mamaye masa Zuciya ya Sani Duk inda Munayferh take tana cikin mawuyacin yanayi Kuma Tana Buqatar taimakonsu , yafi tausayawa Rayuwan Munayferh Fiyeda na 'dan nasa.


Umma kuwa Kuka takeyi tana qarawa Sosai badan Danasani ba ko kuma nadama sai Don halinda 'danta yake ciki....



Aaryaan yana farfadowa ya zubawa mutanen Cikin Dakin idanu, tabbas ba mafarki yakeyi ba Munayferhnsa Da Yaransa duk sun 6ata ...



"Da.....dd....y meyasa Ku..ka boye mn ......"


Maganar tasa ta daina Fita sai kuka ,kuka yakeyi tamkar qaramin Yaro ,Gaba dayansu suka Zuba masa idanu Jikinsu a Sanyaye Masu Share hawaye nayi Haka Umma ji take kaman ta rufeshi da Duka akan Yarinyar da ta tsana yake kuka har yake Yunqurin hallaka kansa


"" Abba Da gaske an rasa Matata da 'ya'yana kenan?, awane hali suke a Halin yanzu ?, Shikenan Munayferh ta tafi kenan ta barni Cikin Kadaici? ,Meyasa Baku sanar dani Tun wuri ba?, Da kun gaya mn da dakaina zanje kuma zan nemota Daddy bazan Ta6a saurarawa Wanda ya Rabani da 'ya'yana da Matata ba ,Umma Abba daddy Ku yafe mn dakaina Zanje na nemota "


Ya qarashe maganar tareda Miqewa ya nufi hanyar fita Daddy yayi Saurin shan Gabansa yana Basa Haquri tareda tausarsa ,Amma bai tsaya ya saurareshi ba ya Ratsa Ya bi Gefensa Ya wuce jirina dibansa.


Umma ta bi bayansa da kallo tana hawaye tana ganin yanda Aaryaan ya Fita a hayyacisa a Wuni Guda ,bata yi zaton qaunarda Yakeyi mata ya kai har hakan ba ,duk yanda sukaso Su hana Aaryaan Fita a Asibitin Abin ya fasakara Saida ya Fice Don rikidewa yayi ya zama tamkar mahaukaci.....





Nayi gabas๐Ÿง๐Ÿฝ๐Ÿšถ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ
[12/27/2020, 10:01 AM] Hawwa Babah: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
**HAWAN-JINI NA*
~{uwar mijina* ๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._



ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...


*_Chapter 78*_


Aaryaan yana Fita Motar Junayd Na danno kai Cikin Asibitin, Ganin yanda Yake tafiya da sauriยฒ kaman zararrene yasa ya fahimci da Matsala don haka ya Parka Ya Fito tareda Janaan Riqeda Aabir (danta) Cikin tashin hankali .


Cikin sauri Junayd ya taroshi yana Tambayan Lafiya ,Amma bai tanka shi ba Illama Qara Saurin tafiyarsa da yayi.


Junayd yasha Gabansa Cikin tashin hankali Yana Qara tambayan sa ina zashi Shida bashida lfy.


Chak Aaryaan ya Tsaya yana Auna masa Wani irin Kallo , kallonsa Yake From head to toe Ganin Carkey a hannunsa ysa ya murmusa kadan tareda Leqa Bayansa yaga Har su Daddy sun Fito.


Da qarfi ya Fizge Key din hannun Junayd, kafin yayi Wata Yunquri Har ya Shige motar yaja Tareda barin Gurin ya barda msu qura ......

Cikin tashin hankali Suka Kira driver Ya zo da mota Suka bi bayansa Amma basu Gansa ba ,Kuma babu Alamar sa ko sama ko qasa.


Yana Fita kai tsaye Prison ya nufa inda Mamy da Alhaji Isa Suke tsare.

Cikin Fushi ya dubi Corporal Dindake Tsareda Su A Fusace Yace

"Har yanzu basu Fadi inda take ba?"


Yanda yayi maganar Cikin tsawa ne yasa Corporal din Sara masa tareda Qamewa yace

"Yes Sir ,babu yanda bamuyi dasu ba Amma they Deny telling us Sir ,Dem just dey Behave Like Jinx Oga "

Tsaki Aaryaan ya Buga Cikin Fusata ya Ce

"Ka jona Mn battery"

"Consider it Done Sir " Ya gaya Tareda Sara mai ya Fice ,yayinda Aaryaan ya qarasa Ciki.

Wuyan Hajiya Kulu (Mamy) ya shaqo ya kaimata Wata Uwar mari Wanda Tsabar Azaba Saida Ri6a66un Haqoranta Uku suka zubo dukda haka bai saurara mata ba yasa qafa ya shureta ta Fadi Timmm Wata Uwar Qara ta saki Qarar da saki ba qaramin Bashi haushi tayi ba Cikin jin haushinta Ya Taka qafar tata ya murza Da qasa Daidai nan Corporal ya Shigo da Battery ,ya jona yana Yiwa Kulu dariyan Mugunta a fakaice.

Hajiya Kulu kuwa Ganin ana Shirin Saka mata Shocking yasa miqe ta zauna Cikin wahala Da Azaba , ta Tofar da Jinin da ya Cika mata baki a wahalce, Aaryaan ya watsa mata Wata muguwar kallo.

"Ni Bana dukan mata Amma Munin Aikin da kika Aikata yasa na daga hannuna Akan mace ,Wlh yanda nakeji Cikin Raina a halin yanzu banqi na kashe ki ba ko zan huta da Radadin da zuciyata Ke Ciki , yanzu duk ba wannan ya kawoni ba Zaki Gaya mn inda Rabi take kosaina Kashe ki"


Cikin wahala da Rauni , jiki na 6ari Kulu ta fara Rantsuwar Bata San inda take ba ,Ganin Tana Shirin 6ata masa lokaci yasa ya Jona mata Shock idanunsa Sun Rufe babu tausayi bare Rahama ,Gani Yake Kaman Tana da Hannu Wajen Sace Munayferh tunda Tana 6oye masa ma6oyar Muguwa RABI don A zatonsa InnaRabi ce ta sa aka Sace Munayferh๐Ÿ˜”.
. .




Tun tana Iya ihu har bakinta ya mutu Saida ya Ga Idanunta Sun fara kafewa Alamar mutuwa ko Suma sannan ya Cire Wayan Daga Cikin wuta , Cikin Mugunta ya Debo Ruwan sanyi ya watsa mata nan danan ta tashi Tana Rarraba idanu.

Aikam Suna hada ido da Aaryaan ta Firgice ta fara Rantsuwar zata fada ,Ganin ta rude Sai faman rantse Rantse takeyi Gashi bata Fadi Abinda Yake bidaba yasa ya Qara Jona Battery din Ai Tana Ganin haka ta fara magana Kamar haka.


"Wlh Wlh bansan Asalin inda take a halin yanzu ba , Amma amma..... Nasan bazata ....Wuce tsakanin Garki Ba ko Gidan DoDonta na Conern Shahada ba "



Huci Aaryaan ya Furzar kafin yace ta bashi Full Address din ,nan take ta bashi ya juya zai fice Har yakai Bakin qofa ya kuma dawowa ya Duqa daidai ita tareda Zare mata manyan idanunsa Wa'enda suka Sauya launi Don Tsabar 6acin Rai

"Idan Ta Cutar mn da Sulthy na saina qonaku Na babbaka Gawawwakinku Wlh kinji na gaya mki"


Yana Gama Fadin haka ya fice Fuuuuuuuuuuu.

******


"Munayferh!..... Munayferh!!.....,Munayferh!!! ,ina kike bakya jina ne?,....Okay tho Neyferh dodonniya"


Duk kiran da Yake mn inajinshi Nayi nisa Wurin kallon kaina a mudubi ina Mamakin yanda mutane Suke Ganina a matsayin dodo yayinda Ni kuwa nake Ganin kaina a matsayin Munayferh ,Saida naji ya Ce Dodon niya sannan na Fito Cikin gunguni ina hararar bango yana Ganina ya washe baki

"Ai Nasan Zaki zo Dole , Albishirinki"

"Goro!"

"Tho dodo ba Gowo Ake Cewa ba Goro zaka ce"

Ya gaya Cikin sigar Zolaya.


๐ŸฅฒMurmushi kawai Nayi Wanda akace yafi kuka Ciwo , Shi kuwa ya Cigaba da Cewa.


"Na nemo mki Visa da Passport kaman yanda kikace Kuma naci sa'a Anyi mki Transfer din Ammafa Na kashe Kudi dayawa ,Ga Papers din"


Ya fada yana Miqa mn Papers Din hannunsa.


Amsa anyi Cikin Murna Tareda Godiya ,Kallona yayi Ta qasar ido Kaman Mai nazari kamin daga Bisani yace

"Neryferh ,Na Samu nasarar Shiga Cikin Gidan Matar nan ,Wlh tallahi tafiki Muni a halin yanzu Inba don Kince karna Dauki Hoton ba ,wlh da na dauko mki ita kin ganta Amma don't worry Gobe zamuje ki ganta ai"

Nan ma Murmushin Nayi kawai Cikin sanyi Gabana na Tsananta faduwa ,Shikam bai ma lurada yanayina ba Cigaba yayi da cewa.

"Kuma Koda zan dawo na hadu da Mahaukacin nan naki ,Wlh baki Ganshi ba tamkar mahaukacin Gaske , Har na bishi na Ga Gidan da ya Shiga "

A mamakance na dago idanuna Na kalleshi

"Da Gaske? ,,da gaske Shi ka Gani kuwa ,Anya shine?Yaushe ya dawo? "

"Wallahi shine na rantse miki, kuma ko yanzu Kikace na kaiki Zaria Ki gansa zan kaiki don ki tabbatar da Abinda na gaya mki .....โ€

wani irin murmushin jin dad'i nayi wanda har a fuskar nan za, a ga tsantsar farin cikin sa, Shikam ajiyan zuciya ya rink'a sauk'ewa tamkar wanda aka cirewa abu mai nauyi Saboda Ganina Cikin FarinCikin da yayi wand Tunda Ya kawoni Gidansu Bai ta6a Ganin Nayi Irinshibba.

Maganar da Nayi ne ya dawo dashi daga Duniyar Tunanin da ya Lula

" yaaJeebril ,Please Har yanzu Jikina na Qamshin Turarena? "

Shuru yayi Tareda Matsowa Gab da Ni ,Ya shaqa kamin yace

"Eh yanayi Amma ba sosai ba"


"Tho don Allah dauko mota ka kaini Zaria yanzu Mu Siya Turaren A shagon JA'AFAR Sannan ka kaini inda ka Ganshi Please .....Shi kadai zai iya Gane Ni wlh "


Gyada Kai yayi a raunane Cikeda Tausayi na Sannan ya Aikata yanda Nace , awajen Mama Muka bar su hasna wa'enda Har Yanzu Barci sukeyi๐Ÿฅฒ๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜“๐Ÿ˜ฅ๐Ÿ˜ฐ๐Ÿ˜ช๐Ÿ˜ญ...

Jin yayi shuru yasa na Riqo hannunsa ,Abinda ban ta6a yi masa ba Cikin Hawaye na Ke Fadin

"Jeeb don Allah ka kaini Zaria ina son Ganin Aary , ban San A wane Hali Yake Ciki ba ,Don Allah Wlh idan ban gansa ba Zuciya ta zata iya bugawa kowa ya rasani"

Girgiza kansa yayi

"Yanda kikace haka ZA'AYI neryferh , idan kin shirya nima a shirye nake "


Hawayen dake Maqale a Gefen Idanuna na share taredayi masa Godiya Cikin Mummunar Muryan nan tawa..

A Ranar muka dau hanyar Zaria bayan mun barwa Mama su Haseen.


3:51Pm. Muka Isa Zaria Lokacin anata kiraye kirayen Sallar Asr ,Bayan mun Siya turare a Sabon Gari ya kaini Gidan da yaga Ya shiga ,Abin mamaki Gidan Aaryaan ne Na Zaria Inda muke zama In muna sch..


Mamaki ya kamani ,Mai Aaryaan ya zoyi a zaria?, bayan ya daina aiki a Zaria?.

Jeeboi ne ya Fito dakansa ya kwanqwasa , tareda tambayar mai Gadi Ko mai Gidan na nan Amma yace Baya nan ya tafi Sectaria Na Fada , nan take muka rankaya nan dai dai Lokacin da ya Fito daga Motarsa ya shiga Ciki ,Dole muka jirashi har tsawon Awanni Biyu kafin ya Fito Lokacin Har mun Samu Guri mun Gudanar da sallahn Asr.


Aaryaan na fitowa Ya shaqi Qamshin dake bin iska ,Haka kawai yaji a Jikinsa Sulthynsa ta Gifta ta wannan Guri Don Haka a razane Yake kallon Ko ina ko zai Ganta Amma babu mai kamarta ,Tamkar Zararre haka ya koma sai Kalle kalle yakeyi Yana dube dube ko zai Ganta Amma babu kowa a Unguwan.


Kallon Jeeboi Nayi a hankali Na Furta

"Yaa Jibril ,Wallahi ya Gane ina Nan , na gaya maka idan ina Guri Dole sai ya Gane ,Idan na wuce ta Hanya Yabi dole sai ya Gane ..... shi kadai zai iya ganeni a halin da Ake Ciki ,Ya Jibril ya zanyi in Isa Gareshi , ina sonsa banason Ya shiga wani hali saboda ni ,Ka taimaka Mn kar na rasa shi a wannan lokacin ,ina son sa Fiyeda yanda Nake Son Rayuwa ta ,bazan iya Rayuwa da Soyayyar sa ba Saboda bansan Lokacin Da ya shigeni ba........" Na fada Cikin matsanancin kuka Numfashi na nafuzga.


Cikin sanyi ya bude mn qofa Batareda yayi magana ba don Shima gab Yake da fara Kukan , inda Aaryaan Yake tsaye yana shaqar Qamshin Turare ya nuna mn Sanan a hankali yace

"Ki tafi Gareshi fatan Nasara "




Aaryaan kuwa Jin Qamshin na Kusantoshi bugun zuciyarsa na ninkuwa yasashi durqushewa a Wurin Tareda Kame kansa kaman mai Ciwon Sanyi , a hankali hawaye Suka fara bin Fuskar sa .


Inuwar mutum da ya Gani da Kuma Qamshin Jikin Sulthynshi Da yaji A Gabansa yasashi ware idanunsa ya zubasu a kan halittar dake tsaye a kansa .


A tsorace ya miqe yana Ambaton Sunan Allah tareda Add'ar Neman Tsari daga wannan Halittar , Yau duk Jarumtarsa Saida ya Rude da Ganin Wannan Mummunan halitta Shi koda wasa bai Ta6a Cin karo da Mummunar halitta irin Wannnan ba , A tsorace ya ja da baya Yayinda na bishi da kallon mamaki bakina ya Gaza rufuwa ,Wanda Hakan ba qaramin Muni ya qarawa Fuskar ba dama chan ya aka qare bare An bude baki.

cikin sauri yana waiwaye ya fara tafiya Ina Biyeda shi ina Fadin


"YaaAary nice fa .... Nice Fa Sulthynka...."

Amma inaa bama Gane Maganar tawa yakeyi ba , Ni tunda nake ban ta6a Ganin Abinda ya tsorata Aaryaan kuma ya kasa Challenge nasa ba sai yau ,Abin sai ya Zame mn Sabon Abu ,Tsoro, takaici da baqinCiki hadida Qunar Zuciya duk Suka hadunmin a Guri Guda , Hawaye masu zafi suka zubo mn Nayiwa Umma Allah ya Isa yafi Cikin kwanddo .


Ina kallonsa Har ya Shige motarsa yaja ya tafi ,yayi nisa sosai Har ya fara qurewa Ganina ban daina kallonsa ba ,Ga mamaki na sai Gashi ya juyo ya dawo Har inda nake tsaye.

Da sauri na qarasa Jikin motarsa ina murmushi.


Shima Murmushin yayi ya Gyada mn kai tareda dauko bundle din 10-10 naira ya Aza Cikin tafin Hannuna , yayi murmushi hawaye Manne a idanunsa ,A Zuciyar sa Cewa Yake dama wannan Mummunar halittar Konace Dodon itace da Qamshin Sulthynsa wacce Yake muradin Gani Fiyeda komai a halin yanzu ...


Hawayen dake saqale a idanunsa Suka Zubo , jiki na kyarma Taja motar yabar Gurin.

Ni kuwa Kudaden da ya damqa Mn nabi da kallo Cikin mamaki Nabi iskar Motar da kallo , jikina Duk ya dau kyarma Na Matse Kudaden Cikin hannuna Da qarfi na Furta "NO" ,na sake bin Kudin da kallo a akaro na Biyu na dagashi Sama Ina kallo tamkar yau na fara Ganin Kudin Gaba daya Jikina babu inda baya Rawa ,na kai Kudaden Saitin hanci na Daddadan Turarensa Mai sa natsuwa ya daki Qofar hancina ,Amma kash Instead ya sa mn natsuwa kaman yanda ya saba Sai ya Dada Quntata mn Raina , da qarfi na Sake Furta "NO" a akro na Biyu tareda Durqushewa Qasa na fashe da Wata matsanancin kuka , shi kenan Haka Ni Rayuwa ta zata qare kowa baya ganeni ,Koina Tsorona Akeji na zama Abin Gudu Abin tsoro a Sanadin Uwar mijina .


Tunowa Nayi da Alwashin da na dauka akan Umma ,Sake Rushewa nayi da kuka Lokacin da na tuna kallon Tsoron da Aaryaan yabini dashi dazu Wanda hakan Ke nufin Alwashin da na dauka Dazu zai bi iska Kenan ?.


Jeeboi ya share hawayen sa ya Nufo inda nake Daqyar ya samu na Bishi amma fafur na qi Amincewa mu koma Kd a yau ,Cewa Nayi ya saukeni a Gidan Aaryaan kuma ya bani ATM dina Wanda shi kadai na Fito dashi Ranar da nabar Gida Don ko siyayyan da Nayi a Ranar Dashi nayi....


____

Kwance Yake bisa Qayataccen Gadon sa na Akfarma sai faman juyi yakeyi ,ZAZZA6INDE ya nemi ya kwantar dashi dama Bai Gama warkewa ba ya Fito kuma ya wahalar da kansa da yawa ,tausayin wannan Halittar keta faman Gallabar Zuciyar sa 6angare Guda kuma Yanajin Bugun Zuciyar sa na tsananta Alamun ko ina Munayferh take Tana Kusada shi.

Sallamar mai gadinsa da yaji yana kwada sallama ne yasa ya miqe yana Tsaki Ya zura jallabiyarsa ya tafi ya bude qofar.


Saida Mai Gadi ya dan Russuna Sannan yace Yayi baqi Wani mutum da Wata mace wacce ta Rufe ko'ina na Jikinta da kaya Ko Idanunta ba'a Gani.


Bai ganesu ba Amma yace Mai Gadi ya Shigo dasu....


Maigadi ya Russuna Tareda Fita daga Dakin



Da sallama Jeeboi ya shigo Tareda Ni wacce na Rufe Jikina da baqaqen kaya da Niqab mai Rufe qwayar idanu..

A razane Aaryaan ya miqe ya nuna jeeboi da Hannu

"You Again ?, me kazoyi anan? ,Uban me ya kawoka Nan?"


Sunkuyar dakai Jeeboi yayi , ya bude baki zai yi magana As usual idan ya bude baki zai tonawa Umma asiri sai Harshensa ta murda.


Ganin bai ma lura dani ba yasa na Dubi Jeeboi Daketa faman sunkuyar dakai Nace ya tafi ,aikam jiki a sanyaye ya fice yayinda Aaryaan kuma ya maida Dubansa Gareni yana Nazarin irin muryan da yaji Nayi magana dashi

"Ke kuma fa?"

Zare Baqar hand socks dindake Lullu6e da hannuna na Cire , Wanda ya sashi zaro idanu ya bude baki zai yi magana idanunsa suka harbo masa Golden Ring Dinda ya bani A Ranar 18th birthday dina Ranar Auren mu.


Sake ware idanun sa yayi akan hannun dake dauke da Dogayen Yatsu Masu Dauke da Dogayen Qumbuna.

Matsowa yayi gabdani Yanaji duk Wata Tsoro ta kau a idanunsa ,
abin mamaki sai Gani nayi ya daga Hannu Ya kamo hannuna Jiki na Rawa Kamar wanda aka tsikara yayi saurin Sakin Hannun cikin tsoro da firgici.......

gaba d'aya jikinsa rawa yake kar-kar da ya bude baki Zaiyi magana Sai yaji Numfashinsa na Neman daukewa , na kasa Gane Wannan Reaction din nasa ya Gane Ni ne koya?....


Cikin fuzgar Numfashi yace

"You Bitch .....,Ina kika kai mn mata ta?, where did u find her Ring ,Her perfume, her soft Skin?, and the Shock I Feel When I touch her ..... who the hell Are you? where'er my Children? ,Am Gonna...... Kill you...trash...."

Luuuu yayi qasa Zai Fadi Sakamakon jirin da ya daukeshi , Da sauri na taroshi ya Fado jikina Tareda Qanqameshi Sosai Cikin qirjina.....

Cikin kuka nake Fadin

"YaaAary Nice , nice Wlh nice"


Dukda ba Fahimtar Abinda dake Fadi yakeyi ba Amma Zuciyar sa ,Gangar Jikinsa na bashi Wannan Munayferh ce ,Saboda irin Azababben Qamshin ta dake Dukansa Ga kuma Taushin Fatansa da Abinda yakeji idan ya ta6a koda hannuna ne ,Amma kansa A Kulle Yake Taya za'ayi Mutumin da Gabaki daya Jikinta babu inda Ake Gani Ko'ina lilullu6e da Gashi harta Baki da hanci babu inda aka bari Amma Da ya ta6ata sai yaji Wani irin taushi.


Cikin In'ina daqyar ya iya hado Kalmar

"S...u....l.....t.....h....y"


"Na'am Raajaa"

Sai a yanzu ya iya Fahimtar Abinda Nace kuma ya tabbata nice wannan Halittar ,Sake Qanqame Ni yayi kaman Za'A qwace mn shi daga hannunsa Kuka yakeyi sosai tamkar qaramin yaro Haka nima haka.


Cikin kuka Yake Fadin

"Sulthy... Me ya sameki haka?, ya akayi kika Koma tamkar Dodon Jeji?, Me ya faru dake ? Please Sulthy na Kiyi haquri Akan Abinda Nayi mki dazu Ban Gane ki bane shiyasa...... Kinji ki fada mn me ya faru dake? Suwa Suka saceki Har suka maidake haka?, na rantse bazan ta6a qyale Duk mai Hannu A cikin wannan Abin ba Koshi waye "


Hannu nasa na Na sake Qanqameshi Sosai kaman Zan Shige Cikin Jikinsa na fara bashi labarin Abinda ya faru da kuma wulaqancin da akayi mn ๐Ÿ˜” ,Harda dukan da nasha Wurin masu Aiki amma ce msu Nayi ban Fita da yaransa ba ,Don kar ya dameni da tambayan su tunda Ni ban shirya rasa shi ba...


Tunda na fara magana Yake kuka kaman Dan qaramin yaro yana Tausayawa halinda na shiga , a yau dabadon Umma mahaifiyarsa bace Da Allah kadai yasan hukuncin da zai dauka a kanta yana Ganin Duk duniya shine mara sa'a da baiyi sa'ar Uwa ba amma dukda haka Bazai yiwu taci bulus ba , Zai bar Ni da ita Duk hukuncin da naga ya dace da ita Nayi mata ita Tajawa kanta Don yasan Ko ban fada masa ba Dole sai na rama Abinda tayi Mn yasan wannan wajib ne.


Cikin Disasshiyar murya mai nunida yasha Kuka sosai Yake Fadin

"Allah yayi

Please Login or Register in order to submit comment