Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da niyyar barin Wurin.

"Amma tir da Halin mutane irin Ku....Damn u, Allah Tsine Wa mutane kwadayayyu irin Ku, Marasa Son Mutum Dan Allah sai dan Abin hannunsa, Haba na daiji mamaki , koda yaushe idan Motarsa ta parka Sai kunzo Ashe Dibar Tsiyar da Akeyi kenan , To Wlh Cikin ku babu mai Cin kidinnnan "

Na juya Ga Aaryaan da ya kafeni da idanu yana mamakin Yanda nake magana Cikin Qarfin hali kallo daya Zaka mn ka Fahimci Lafiyata ba garau ba, Amma Saboda Fitina irin tawa Sai zuba masifa nakeyi.


"Kai kuma Daga yau sai Yau ,Na sake Ganin ka basu Kudi ko Wani Abu Cikin dukiyar ka bada Sanina ba ,Ban yafe maka ba, Kuma babu mai ta6a kudin nan Cikin su Ga kudin ka"
Na qarashe magana ina kwasar Kudin ,tareda miqa mshi.


Qin Amsa yayi yana Dubana Baki sake Nima dubansa na tsaya yi "Bazaka Amsa bane?" Na fada Cikin dan daga Murya.


"Bana maida hannun kyauta baya" ya fada a takaice tareda barin wurin.


Juyawa nayi na dubi Ekon "Kai Arne!, kai kadai kake shan Taba anan Ara mana lighter"

Cikin Rawar jiki ya Ciro lighern ya miqa mn, qin Ansa nayi na Zubar da kudaden a qasa Nace ya Kunnawa kudaden wuta da kansa har su qone, haka kuwa yayi, Tunda ya kunnawa Kudaden Wuta ma'aikatan Suka kama Gabansu suna Aika mn Saqon Allah ya isa da tsinuwa kala Kala.


~Oho ๐Ÿคท๐Ÿปโ€โ™€๏ธ,Aikin banza Harara a duhu, banji su ba bareda Aunty Fahnaan ,Readers ko kunji?๐Ÿค”~


Ina Shiga kai Tsaye Parlon Abba na isa na iske shi a Garqame , Tunowa nayi da Yau fa A sashen InnaRabi yake.


Anan na iske su zaune Suna Tsara yanda tafiyan nasu zai kasance.


Da Gudu na fada Jikin kakus dake Zaune Gefen Abba na fashe da wani irin kuka mai ban Tausayi.


A take hankulansu ya tashi ,Cikin Tsananin Rudewa suka tambayan Lafiya?, me yafaru?, ya Akayi?, Me ya Sani kuka.


Ganin duk Sun Rikice ne ya sanyani dagowa tareda Share qwallata da bayan hannu (Dama haka nake so)

Na fara Magana Cikin Shessheqa "Ba YaaAary bane ,ya mareni kuma ya shaqeni ba, Saboda Umma ma ta Kirani Jiya ta zageni Shine da Na rama ya Shiga mari na harda shaqeni har saida na suma Kuma Sai yayi mn fya...." Da Sauri kakus ta dakatar dani dacewa


"Shi Aaryaan din ya shaqeki harda Yarfa miki tafi?"


"Eh mana , Ki duba.... Fuskata ....Fa har yanzu Akwai Shatin.... hannu ,Anan " na fada Cikin kuka tareda Nuna msu Gefen Fuskata .


Salati Suka Saki Gaba daya Abba yace "Toh ina Shi Aaryaan din Yake!, Ya tafi Gurin Umma ,....Abba na ina Gaya mka ....kuma baya bani Abinci Rabonda naci Abinci Tun kazar da ya kawo mn Jiya Shima danaji shaqa Amayarwa nayi Wlh ni na Gaji baza'a Kasheni ba Tun lokaci na baiyi ba, Abbana bari na kirasu Shida Uwar tasa Muji dalilin Horanin da Sukeyi?, Meyasa Umma ta tsane ni Meyasa bata sona?, Meyasa Aaryaan ya tsane ni ?, Meyasa baya Sona Dole Sai sunyi bayani!" Na fada ina miqewa


Gaba daya Suka Rakani da kallo har na Fice, dan Basu Fahimci inda Shirmen maganganuna Suka nufa ba.

_____

Aaryaan yana Shiga Kai tsaye dakin Umma ya nufa don Ya fara bata Haqurin Abinda ya faru tsakunsu jiya, Yasan ya 6ata mata Rai , yana shiga Ta Shige bandaki dan tayo wanka.

Wuri ya Samu kan kujera ya zauna yana jiran Fitowarta, yana zaune shuru yaji an Budo kofar, juyowa yayi dan Yaga ko Wacece.




Qarasowa nayi Cikin tafiyata Wacce ta koma Tamkar na talotalo.

Hararar sa nayi

"Abbie na Kiranka kaida Umma" na fada a takaice


Tasowa yayi ya tako Har inda nake tsaye , ya kusantoni Sosai hakan yasa nadan Jada baya ina fadin "Wai meye haka"

Murmushi yayi yace "Sulthy Please, ki Gyara tafiyarki ko so kike Kowa yasan Abinda Muka Aikata ne?"


Maganar ta fada Kunnen Ummah dake ban daki tana Kokarin Kunna Ruwa Dan Wanke Kumfar Fuskarta, Cikin Rashin Fahimta da Tashin hankalk ta tagaita tana Son jin Amsar da Zan bayar, dan Tabbatar da Zaton ta.

"Mtswww, Bayan Ka gama Amfani dani kenan, Aarry!, Bazan ta6a yafe maka mutunci na da ka dauke mn ba, Allah ya isa ban yafe ba!, Sai Allah yayi mana Hisabi A tsakanin Mu!, Mugu, Azzalumi Inshaallah Sai ka Sami Shegun 'Yan mata 'Yan iska Kalan ka sunyi maka Fyade kaman yanda kayi Min!" Na qarashe magana tareda Zubar da Hawaye .



Umma dake bandaki ta kuma Rudewa ,Fatanta daya Abinda takeji ya zamo mafarki ba dagaske ba!, Taya za'ayi Aaryaan ya Sadu da Munayferh Bayan tayi masa Kashedi !, Cikin Matsanancin Tashin Hankali Ta dan Watsa Ruwa a Fuskar ta Dan Tabbatar da Ba mafarkin takeyi ba, Jikinta har Rawa yake Ta kosa ta fito tagani a zahiri Dan ta dauka Shirin wasan Kwaikwayo mukayi Mata dan Raina mata hankali.


Aaryaan ya kuma matsowa Gab dani ya Riqo hannuna Cikin Narkar da Murya yace


"Sulthy Ada nayi tunanin Zan iya Haqura dake Wlh bazan iya Haqura dake ba Ina Sonki ,Munayferh ina mki son da Ni kaina Bansan Adadinsa ba,kuma inada yaqinin da Sonki Aka haifeni Haka kuma da Sonki nake Rayuwa ,A duk Bugun Zuciyata Sonki ke Qara qaruwa Cikin Raina ,Aapane Mujhe Sikhaaya ki main aapase kaise kapharat karate hoon , Main tumase hamesha pyaar karoonga (Ke kika Koya mn Sonki , Zan Cigaba da Sonki) Daga nan Har qarshen Rayuwata,Kuma Nasan Kema kina Sona"


Dukda Yanda nakeji Sakamakon yanayinda Maganganunsa ya Sani, Bai hanani kwace hannu na ba ,Cikin zafi na fara magana

"Love!...My Ass, ...Nabi So da Jifa!, Allah ya kiyaye Zuciyata da fadawa Soyayya dakai,Aaryaan ! Kai ka koya mn Kin ka Taya za'ayi naso ka?, Zuciyata Gaba daya tana ga Jeebreel Jeeboi,Akansa na San Kalmar nan Ta SO , Shi kadai nake so kuma nake Muradin Kasancewa dashi Har qarshen Rayuwata!, Bakaiba!, Dan Ithka Maiyiwa Mata Fyade!,.....Dama Nasani Dazarar namiji ya Sami Nasarar Sambade Budurcin mace ya Gama da ita Shikenan zai fara Yaudararta da kalamai, ka manta Rana mai kamar ta yau Kwana daya bayan Auren Titi da kanka Ka Furta mn kalmar MUNAYFERH I HATE YOU!, Ka manta Same munayferhn da kake Gayawa kalman So ita Ka Shaqe a Daren Farko sannan ka Falleta da mari daga Bisani kayi mata Fyade,Jiya ma ka qara...."Na qarasa da Kuka tareda barin dakin da sauri...

Da kallo ya Rakani yanaji Zafi Hadida Daci tareda wani Abu da ya Tokare masa maqoshi!.

Saukan mari yaji bisa kuncinsa batareda yayi zato ba!, kafin Yayi wani Yunquri An qara wankeshi da wani irin mari.


Umma ce cikin tashin hankali Fuskar ta dauke da kumfar Sabulu wanda bata Gama wankewa ba ta fito dan jin kalaman dake Fita daga Bakunan mu ,kallo daya zaka mata ka fahimci Tsantsar tashin hankalia a tattareda ita Gaba daya ta fita hayyacinta,


"Aaryaan bazaka Kasheni ba, Dama Sonta Kakeyi?......


TOFAH!

WAI MEYE ALAQAR QANWAR RAMLAH DA SUWAYBA? DAMA SUN SAN JUNA NE?





WACECE RAMLAH?, DAWA TAKE KAMA ??, MEYASA YATSUNSU YAYI DAYA DA NASU MUNAYFERH?



WAI ME UMMA KE SHIRIN AIKATAWA NE?






MEYASA TA TSANE MUNAYFERH KUMA TAKE QIN RAMLAH?


INA LABARIN ABBAN MUNAYFERH DA SALEEM?



DUK AMSAR NA CIKIN WANNAN LITTAFAN,




ALL I NEED IS UR COMMENTS KAWAI๐Ÿ’ž๐Ÿ˜˜












Yanzu wasan zai faraโœ๐Ÿผ

Mafari kenan๐Ÿ˜ƒ


My First Hausa Novel Wanda na Rubuta shi har nakai Kusan rabi๐Ÿ˜‹

Dear Readers ina Godiya a Gareku Mara Adadi bisa Goyon bayanku, Kune Jagorata kuke bani qwarin qwiwan Rubuta mku wannan labarin

A dalilin wannan Littafan na hadu da mutane da dama Daga wurare da dama Wuraren DA Bandaban Wuraren da ta6a zuwa ba Saidai na Ganshi A tV๐Ÿ˜‹kaman Su BoRno (Boko Haram Family land)๐Ÿ˜ƒ


Allah ya bar qaunah ta har Abadah๐Ÿ˜˜












Bintouโœ๐Ÿผ
(Fahnaan)






15th Oct




Nayi Gabas๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
HAWAN JININA

~(Uwar mijina)~

๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
by

~Fahnaan~

(Bintou)

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...



*Chapter 48&49*



*Fateee Faruq (Name Shake๐Ÿ˜˜)*

*Yar mutan kanawa Bayin zazzagawa Wannan Shafin Nakine ,Kiyi yanda kikaso dashi, in kin Ga dama Ki siyar Ki Siyo Gurasa da Kudin.. nasan Ke Mayyar Gurasace๐Ÿ˜œ*



_______

Hankalin Umma ya kuma tashi ,Cikin Tashin hankalin ta Cigaba Da cewa

"Toh Wlh baka isa ka kasheni ba, Baka isa ka Sani Min hawanjini ba, Aaryaan Wai yaushe ka Sauya ne?, Fada mn me kayi Wa Yarinyar nan?, Kai nake Sauraro fada mn"

Ta fada Cikin tashin hankali Da Fitar hayyaci,Jikin ta har rawa yakeyi, Zuciyarta na Tafasa Jikinta na karkarwa Idanunta Sun kada Sunyi jazir sbd 6acin Rai, Ji take kaman ta Shaqe Munayferhn ta mutu Ayau Tsanar da takeyi mata A da ya kuma ninkana Daa.


Shuru yayi mata kansa Duke ,Hannunsa dafe da Kunci Saboda marin da tayi masa,Cikin Fargaba, Rudu da 6acin Rai Gabadaya ya ma Rasa Amsar da zai bata.

Umma kuwa Shurun da yayi ba Qaramin 6ata mata Rai yayi ba, nan danan ta qara hasala 6acin Ranta ya ninku Taku daya tayi mshi ta Damqi Wuyar Rigarsa, Cikin Murya mai nuna tsantsar 6acin Rai da Rudu take magana Idanunta Gaba daya Sun Firfito bakinta har Rawa yake

"Aaryaan Kamin Bayani Me kayi mata!, Answer me!" Ta qarasa magana Cikin Daka masa Tsawa murya na karkarwa.


Sai A yanzu ya dago Tareda Cire hannunsa daga Kan kuncinsa , ya Riqo hannayenta dake Chakume da Wuyar Rigarsa ,Cikin Sanyi yace


"Mum Calm down Crpya.."

"Don't Tell me to Calm down " ta fada Cikin Tsawa Idanu jazir kaman mai shirin yin kuka tareda Cire hannayen nata daga Wuyar Rigar nasa.

Cikin Sanyi ya fara magana

"Umma na..Bai kamata Ki riqa Tada Hankalin ki Akan Abinda Bai taka kara ya karya ba, kisawa Zuciyar ki Natsuwa da Sallama ,Mum duk duniya banida kamarki Haka Kuma kece Jigona Mezaisa na Gujewa Umurnin ki?"

Ganin tayi shuru tana Sauke numfashi yasa ya taka yaje Ya Dauko Ruwan Sanyi Cikin Freezer ya Fincike Marufin Goran Ya Azamata Saman Bakinta


Cikin Haushi da Takaici tasa hannu ta kwa6e Gorar ya fadi Ruwan Dake Cikin Gora ya Zube.


Duqawa yayi zai dauka ya Jiyo tatana Magana Cikin tashin hankalin da bai bar Jikinta ba, Ji take tamkar ta Rufe sa da Duka.

"Son .....ka Raina mn hankali dayawa , ka dauka banji Abinda kuke tattaunawa bane kai da ita Yarinyar?, idan bakayi mata Komai ba, mai zaisa ta Kalleka tace kayi mata Fyade kuma ka kasayin komai?, kuma me zaisa kace mata ta Gyara tafiyarta In babu Abinda ya shiga Tsakaninku?, Amsa mn!, Nace ka Amsa mn!" Ta qarasa Tareda wanke Fuskansa da wata Lafiyayyar mari.

Dagowa yayi Cikin Gigicewa yana Kallonta ,Tun daya taso ya Girma ya mallaki hankalinsa, Umma bata ta6a ko Dungurinsa Ba, Amma yau Sai Gashi ya Sha Mari har Kashi Biyu akan Mace!, A hankali Hawaye Suka Wanke masa Fuska.


Ita kuwa Cikin Kuluwa ta kuma Riqo wuyar Rigarsa tana Baya dashi har ta qumashi da Bango ta Budi baki zata yi magana Hawaye Suka Zubo mata Cikin karyewar Kalamai take fadin

"Aaryaan ka kasheni, Meyasa nake Numfashi bayan ka Gama dani!?, Aaryaan dan Allah ka kasheni na huta da Ganin wannan Ranar , Aary...aan Riga da nayi Ra..nts...uwar Ba..zan Hada Zu...ri'a da Haw...wah bah, Me zai...sa ka Kar....yani? "

Sai ta Sakeshi ta fara Baya baya Cikin Tashin Hankali idanun ta na Fidda kwalla Zuciyar ta na Harbawa da qarfi da Qarfi , Jikinta babu inda baya Rawa, Riqe kanta Tayi Ta kumayin Baya

Shi kuwa Aaryaan Binta yayi da kallo shima Cikin tashin hankali Jikinsa har wani Kar'kar yakeyi, Hawayen dake Zuwa a Fuskar Ummanshi yafi tada masa da hankali.


Bai Ankara ba Yaga tayi baya ta fadi Qasa A Sume .


~Tashin Hankali!~


Da Gudu ya isa Wajen ta yana Bubbugata Cikin dimuwa da Tsananin tashin hankali ya fara Jijjigata ya

"Ummah...Umma....Mum .....Mummmmm!" Ya kirata da qarfi jin bata Ko motsi da Sauri ya dau Goran Ruwan da ya Dauko mata, Wanda ta 6arar har ya ,Zube ya Yayyafa mata.


A hankali ta bude idanunta ,Ta waresu Akansa ,Dishi Dishi ta fara Ganinsa hakan yasa ta qara lumshe Su ta kuma waresu Akansa ,Nan take ta tuno da Abin da ya faru


A zabure ta miqe Zaune tana Zaro ido Kirjinsa na Bugawa Cikin tsananin Dimaucewa da Zafin Zuciya ta ke magana


"Aaryaan, Ka....ka....ka" sai ta Kasa Karasa zancen ta Rushe da wani irin Kuka mai ban tausayi.


A hankali yasa Hannu ya jawota Jikinsa Cikin Sigar Rarrashi ,Shima Muryarsa A sarqaqe Kaman mai Shirin yi kuka yace

"Umma na Please ki daina kukan nan, kina tada hankali na dayawa,Indai wannan Abin ne ya saki Kuka Na daina , Umma wlh bazan Sake ba!, Na Tuba Ki mn Gafara ki mn Rai Na Rantse daga Yau bazan Qara ba''

ya qarashe magana da Fashewe da wani Irin Kuka ,Jikinsa Kuwa har Wani Irin Rawa yakeyi Jijiyoyin Jikinsa Sun tashi sunyi Rudu Rudu, Fatar sa kuwa Gaba daya Har ya Sauya Launi Zuwa jaa.


Itama Hannu tasa ta Zagaye bayansa,Cikin Tashin hankalin da ya ninka na da, Rabon da taga Hawayen Aaryaan Tun Yana 'dan shekara 13 ,Haka kuma ta tabbatar da Abinda yake Fadi ,Cikin qaqaro Murmushi Tace

"Aaryaan donAlllah kar ka Qara, idan Ka sake Zuciyata zata Buga na mutu!, Na tabbata Itace tayi maka Fyade Amma da Hankalin ka Bazaka Ta6a Bijirewa Umurni na ba!"


Umma fa ta haukace,haka ta Cigaba da surutai Cikin Fitan hayyaci, ido ya zuba mata kawai Batareda yace komai ba, yana mamakin dalilin Tsanar da Umma keyi Wa Munayferh!, Wani 6angare na Zuciyar sa kuwa Tunani yake yanda Za'ayi ya Gujewa Ni'imar Munayferh, kuma Ya zama Dole Ya Aikata Hakan Tunda Hakan Shine Farin Cikin Mahaifiyarsa Kuma ya Riga da ya dau mata Alqawari.

****

Ni Kuwa ina Komawa na Sami Gefen kakus na Zauna Shuruu ina Zare ido kaman Manafuqah Saboda Sosai kalamansa Suka Saukar Mn da wani irin kasala hadida Bugun Zuciya.


Kakus Ce ta dan dubeni Tace "Ke ina Suke"


Hararar ta nayi Hadi da Turo baki Cikin son Tattaro Natsuwata nace

"Ki nemi 'Ke' A chan KARACHI Ko SINDH Amma ba nan ba don Banga Mai kamarshi Anan ba"


Abba ya dan Harareni ,Yana Fadin "Angel Dina Zan zaneki Fa"


Ita kuwa Kakus Dakuwa tamin tana mai fadin "Kinci Gidanku"


Dariyar Qarfin hali nayi ,Tareda Nuna kaina da 'dan yatsa nace

"Abbie na, Ni ...Ni!..Munayferh kakarka ,'Yarka, kuma Matar 'danka Ni zaka Daka!, Heyye Lallai duniya tazo qarshe ...... Ke kuma kakus Ki kama Bakinki karkiyi Sa6o Dan naga Alama Tsufan nan Ya fara ta6a mana kwakwalwarki.... Idan naci Gidan Mu Ai ba kanta kenan!, dan Gabaki dayan Ku babu Wanda zan bari ya tsira"


Haka Muka Cigaba Da hira Cikin Raha ,Har InnaRabi ta Shigo Parlon Riqeda Tray mai dauke da fruits.


Ta Ajiye Tray din Saman Center Table Sannan ta Samu Gefe ta Zanna .


Kallonta Nayi ,Sai a yanzu na tuna da Su Aaryaan da Aka Aika na kira su Suka qi Fitowa!, Gaba daya na kosa naji hukuncin da Za'a yanke Msu๐Ÿ˜.


Kallon Abba nayi Cikin marairaicewa nace
"Abbie na!, kace InnaRabi ta Dubo mana su YaaAary Tun dazu ko lafiya" na Qarashe magana tareda Yatsine Fuska.


Harara InnaRabi ta Watso mn "Ehh Tunda Gani Galatian Mai Kafar Shige kororo, ke Bakida Qafa ne?"

Turo baki nayi Cikin Muryan Shagwa6a nace "Abbie na kaji Abinda take Fadi ko?, Harda Harara na Fa , Wayyo Abbie Gaba daya Matanka Sun Tsaneni, basu so na, Basu qaunata, kullum burinsu bai wuce Su 6ata mn ba, Don Sunga Babu Ubana A Gidan Kenan, Na tabbata da Daddy na Gidan nan Bazata Ta6a iya Duban Cikin Idanuna Ta Yarfa mn Maganganu Son Ranta ba!,Allah Sarki daddy na, Allah ya kare mana Kai a duk inda kake,Allah ya sanya maka Aminci da Salama A duk inda kake ya bayyana mana ka Cikin Qoshin lafiya da kwanciyar Hankali" na qarasa Cikin Rauni tareda Kwantar da kaina bisa Kafadan kakus dake kusa dani tareda Lumshe idanu, Hannu tasa ta Qarasa Rungumoni Jikinta Cikin Mutuwar Jiki ,magana take sonyi Amma ta kasa ko Bude Bakinta Ahankali Hawaye Suka zubo daga Cikin idanunta Cikin karaya ,Dan maganganun da nayi ya tuna mata 'dan Autan ta.

Ita kuwa InnaRabi Murmushin Mugunta tayi a ranta tace


~Baku Fara Kuka ba, Sai nan da Wata daya idan mun Fara gana Mshi azaba~

(TOFA)

Shi kuwa Abba Cikin Bada Umurni Fuska daure ya Nuna mata Hanya tareda Cewa "Banson Shashanci Rabi Tashi kirasu ,Na baki nan DA...."


Sallamarsu ce t Katseshi, daga fadan da ya fara

Ummah CE ta fara shigowa ,Sannan. aaryaan Gaba daya Sunyi Zuru Zuru ,Idanunsu Jazir ,Kallo daya Zakayi msu ka fahimce hakan Barin ma Aaryaan mai Kumburarren Fuskan da tasha Mari Ga Yaqushin Da yasha Jiya dadaddare Wajen Munayferh.



Karasowa yayi ya duqa har qasa ya Gaida Abba da kakus a mutunce Sannan ya Juya ga InnaRabi yayi mata kallon Uku saura kobo A hankali kaman An tilasta Shi yace ''Sannu"


Iya Hasala ta Hasale ,Ganin yanda ya Gaidatan ,Gashi ko kallonsu Abba baiyi ba Bare yasani.

Daga nan dakin ya dau ki shuru, bakajin sautin komai Sai na television Dnda Ke ta faman Aiki.



Nikuwa tunda ya shigo na qura mshi ido Cikin nazari Inason Gano Dalilin kumburewan Fuskarsa Daga Fitarta Zuwa yanzu, Kasa haquri nayi ,Cikin Kulawa na taso har inda yake Duqe Gefen Qafar Abba, na Zauna kusa dashi


Gaba dayan su ido Suka zuba mn Suna Son ganin Abinda nake shirin yi!, ita kuwa UmmA Tsura mn ido tayi Tana kallon yanda na tako Cikin tafiya a warware.


Zama nayi kusada Shi A hankali na kai hannu na Bisa kuncinsa da yayi rudu Rudu

"Yayan Hafsah, Ummace ta mareka ko" Shuru yayi Bai tanka mn ba kansa a qasa,Haka kuma Gaba dayansu ido Suka zuba mana Sun Kasa fadin komai .


Cigaba nayi da cewa

"Nasan itace ,Hakan na nufin Taji duk Abinda muka fada..." Da sauri ya dago ya dubeni hadida Watsa mn Harara.


Tabe baki nayi na juyar dakai Gefe ina Harara qasa qasa

Cikin Sanyi Abba yace

"Angel tashi ki koma inda Kika Taso"


Babu musu na miqe na koma inda Kakus ke zaune , Na Zanna tareda Dora kaina bisa Kafadan Ta Zuciyata na suya.


Cikin Qaguwa Aaryaan yace "Dad Ance kana kiran mu "

Gyaran Murya yayi Cikin zafi ya fara magana

"Aaryaan Ashe Bazan iya damqa maka Amana Ka Riqe mn Cikin Aminci da Salama ba?, Ashe Zaka iya Cin Amanar 'dan Uwana ?, Aaryaan yaushe ka zama haka?, Yaushe ka Zama Ragon Namiji Mara Jarumta ?, Eh mana Ragon Namiji Shine mutuminda Zai daga Hannu ya daki Matarsa ta dalilin Kuskuren da ta Aikata"


"Kayi Haquri Abba... Ban Fahimci inda Maganar ka ta Dosa ba Wani Abun tace nayi mata?"


Aaryaan ya fada Cikin Rashin Fahimta.


Kakus ta dauki pillon dake Kusada ita ta jefa mshi
"Ja'iri taya zaka Fahimci Abinda Kayi mata Tunda ka rigada Ka Aikata?"



Damm Gabansa yayi wani Irin mugawa ,Kardai Munayferh ta gaya Msu komai bai Ida Tunani ba yaji kakus na cewa na maimaita Abinda na fada dazun.


Cikin Sanyi na dago kaina daga kafadarta , na Dubi Umma Dake zaune Kusada InnaRabi ,Gana daya ilahirin Jikinta babu inda baya Rawa ,Na kuma kai Duba na Ga Aaryaan da kansa ke Sunkuye


"Ranar da Aka kaini Gidansa Umma ta kirashi A waya Sai...."


Sai nayi shuru na kasa karasaWa ,Karo na farko na danaji kunyar Kai Qarar Umman.


"Sai Akayi ya?, "
inji Abba


"Sai....Ta zageni!, Nima na Rama Shine ya Mareni harda Shaqeni ,Saida na Suma Sannan kuma ya mn...."


"Shaant Reho!"(Yi mn Shuru ) Aaryaan ya fada Cikin Daka Tsawa tareda Nufoni kaman Zai dakeni nqame Kakus na kumayi jiki na Rawa.

Shima daka mshi Tsawa Abba yayi ,Hakan yasa ya koma ya zauna Yana Huci jikina Rawar jiki Yasan qaramin Aiki na bne na fada musu Ya mn Fyade.


Gaba daya kasa magana Sukayi Suka zura mshi idanu Suna Jiran hukuncin da zai yanke, Umma kam tuni ta Gama jiqewa Sharqab da zufa

Abba kuwa Jin Abinda na Aikata Yasa Shi yin Shuru Cikin nazari, ya Saba Goya mn baya Akan Abinda nake Aikatawa mai kyau da mare kyau ,yasan Tabbas Abinda Na Aikata Yau Ba Abune mai kyau ba, Kuma ya kamata Aaryaan din ya dau hukunci Tunda Ai Uwa ba tafi Uwa ba, Koshi Akayiwa Hakan Sai inda qarfinshi ya qare ,Umma kuma Ita tajawa kanta meye na kiran Munayferh tana Zaginta?, Akan me ?,Inma Akwai mai Laifi To Umma ce tunda itace ta kasa Riqe Girmanta .

Cikin Haushi kuma Cikin kaushin Murya Abba ya fara magana


"Haleemah wato ni ban isa dake ba ko?, Ban kai na baki Umurni kibi ba ko?, Sa'adiyyah Bansan Cewa kinfi karfina ba Ashe ban isa dake ba bansan Cewa kinfi karfin ki mn biyayya ba!, So nawa zan Gaya mki Ki fita harkar Yarinyar nan ,So nawa Zan gaya mki Ki daina Samata ido a lamuranta?, Ke ko kunya Bakiji Kici mata Mutunci ta Rama har ta kuma kawo qararki ,Ya kamata kiyiwa kanki fada ,Yanzu Munayferh ba Matsayin 'ya kadai take a wajen ki ba, 'ya da suruka ce A Wajen ki!, ya kamata kiyi Wa kanki fada ki kori duk Tsanar dake tsakaninki da ita ki Rungume ta a matsayin Suruka hakan kadai zaifi zama mki Alkhayri A wajena, kuma maganar rama Zagin da tayi Banida ta cewa dan Ke kika jawo tunda fari da kin Kama Girmanki da Hakan bata faru ba....kai kuma Aaryaan kana wani sussun dakai kaman Munafiqi ,meye na Shaqe 'Yar mutane Akan ta fadi Gaskiya?, Idan kasheta fa?, Me zaka Fada mn?, Zanyi maka Uzuri Saboda Yanayin Zuciyar da kake dashi ,Amma daga Yau ko harararta kayi mata naji labari sai na dauki mummunan mataki Akanka Shashasha kawai, ita Munayferh ba Hukuncin Duka da Fada take buqata ba ,Aduk lokacin da tayi kuskure kamata yayi a zaunar da ita a Nuna mata kuskurenta ,Ba wai a dauki matakin Duka ba, Sabo da Duka na Janyo bushewar Zuciya, idan mutum ya Saba da Duka zai zama baya tsoron Dukan Kuma Zuciyar shi qara bushewa zata dinga yi Ya zama Baya Shakkar Aikata Abinda Ake Dukanshi Akai, ya kamata ka kiyaye!, Yanzu kai ba Yaro bane!, kanada mata har Biyu, ko dai haka kake dukar dayan matar taka Idan tayi maka Laifi?"


Ya fada yana kallon Aaryaan da ya Sunne kai yana sauraronshi ,Ahankali ya Juya kai Alamar A'a

Abba ya cigaba

"Auho wato 'yata ka Raina kenan, don ka Ganta 'Yar qarama?, ka Gujewa Ranar da Zata Zame maka Babbar Alhaki...."
Ya kuma juyawa Gareni nima kallonsa nakeyi Cikin Sanyin Jiki

"Ke kuma Munayferh, Meyasa baki jin magana ne?, Meyasa Zaki Daga Murya Ki Zagi mata ta?, hakan na nufin nima Wata ran Zaki iya Bude baki yi Zageni kenan!, Kisani Yanzu ba matsayin Uwar Riqo take Wajen ki ba, Matsayin Uwar miji take, kuma ya kamata Ki San Abinda Kikeyi ,daga yau kar in sake Ganin Kin Dagawa Uwar mijinki murya ba, Inba so kike Raina ya 6ace Nima na Zaneki ba,kome tayi mki ki Kirani a waya ki sanar Dani, zan dau mataki Akanta, Munayferh karki watsa mn Qasa a ido Yin hakan zai haddasa Tarwatsewan Qaunar dake tsakanina dake, Ayau kin 6ata mn Rai, Kin haddasa Abubuwa da dama Cikin Raina " ya qarashe magana Cikin Raunanniyar Murya.



Kuka na saki Mara Sauti,Tunda nake Abba Goya mn baya yake aduk lamurana ,Ya saba Ganin Muna Kace nace da Umma ya Goya mn baya koda kuwa nice banida Gaskiya, Tunda nake bai ta6a daga mn yatsa ba bare akaiga Fada , Danasan Haka Zancen Zata juye kaina da ban Kawo qara ba, da dakaina na dau mataki Amma a juri zuwa Rafi Zasu Gane Aurensu ne! Daga su har Abban, Munayferh Suka Ta6o bana barin bashi Zuwa ma mutum Cikin barci Shine mafi qanqanta daga Cikin Aikina.


Cikin Sanyi da Rawar murya Aaryaan ya Fara bada Haquri ,Umma ma Haqurin Ta bada ,Ni kuwa miqewa nayi batareda na bada Haqurin ba, Kuka nake Sosai Cikin tsananin Tsoro na fara takawa hankali Gudun kar na Fama Ciwo na, ina Cije lips tareda Matse ido, nayi hanyar Fita.


Gaba daya Suka Bini da ido, Umma ,InnaRabi Da kakus Kuwa sun Fahimci Abin ,Sun San da Adaa ne da tuni na Fice da Gudu ina kuka,


Abba kuwa bai kawo komai a ransa ba, yafi danganta hakan da Tsoron fadan da yayi mn

Please Login or Register in order to submit comment