Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

��ࡱ�>�� )i������������� �

� �

������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������e�

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~�Root Entry�������� �FjWordDocument����X(0Table��������*Data
�������������������� P���"KSKS�X(�n�������pp����]q� ��
��$u�'*p������Q�qQqQq�q �>`��>Normal$a$KHOJPJaJ�n��z̝@�����(�J�������'�V}�����������,,OFc�vF�>�b��J���@�Xvl:�� ����
��I�o$z������(x&�`�x��$�����
v?�l2rt�~��� 63�P\���
�� � �E r �{ �� �� �� �� �
HO
�v
\|
��

��
��
�G �y 6 4� �� � � . �f �� [1/27, 4:03 PM] Oum�ahira: =؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�
��� *RAYUWAR MADINA* =ا�
=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
� �� _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>���*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <��

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ت�)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

� � �� *P.W.A
'�*





*CONTINUE... STORY OF MEEMA FARUKH*




*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga �an uwana Mata waWanda suka fuskanci u�uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana �arshen wahalar rayuwa._




















______________ *EPISODE 1*
_____ *ZARIA CITY*
�aramar �auye mae cike da albarkatu kala-kala, yanki ne da ake shuke-shuken kayan gona waWanda ake samun iri masu ban sha'awa da burgewa, wanda hakan ne ya zamewa �auyen abun dogaro kuma sana'a a gare su, da noma suke ci suke sha kuma suke siyarwa a garuruwa mabambanta saboda Allah ya basu wadataccen fili mae kyau; ga kuma �orama da ke fitar da ruwa sosai, da lokacin damina da lokacin rani gaba Waya idan suka yi shuka suna ganin albarkan abun sosai. Sai dai kuma wannan �auye tana Waya daga cikin �auyukan da har yanzu basu waye ba a cikin al'umma, al'adun su sun sha bamban da sauran na mutane, har yanzu kansu a duhu yake wanda su sun Wauki wasu al'adu tamkar addini a wajen su, karatun Boko ma har yanzu basu wani yarda dashi ba, iyakan su karatun Arabia da suke yi a zaure, da zaran kuma kayi sauka shikenan sai kuma ka ci gaba da sana'a ko kuma a aurar da kai, shiyasa su a tsarin su Mace tana kai wa shekaru 13 suke kaita Wakin Mijin ta

A cikin �auyen akwai wani babban gida wanda a gaba Waya cikin �auyen shi ne Babba domin babu kamar shi, gida ne babba da sassa kusan goma sha biyar a ciki, kuma duk wannan gidan ahali Waya ne domin Mutum Waya ya haifi yaran gidan, waWanda su kuma sun yi aure a cikin gidan sannan suka hayayyafa. Sai dai a yanzu Allah ya yi wa Malam Umaru rasuwa wanda ya kasance shi ne Kakanmu kuma mai Ahalin nan gaba Waya, tare da Matarsa guda Waya mai suna FaWime da ta haifa mishi Yaransu goma sha uku cif, kuma gaba Waya babu wanda ya rasu face Mutum Waya, wanda shi ne Wa na uku a cikin yaran gidan, Malam Sule. Ya rasu tun da �uruciyarsa, ya bar yara guda biyu dukka Mata, yayinda Matarsa ta fita tayi aure a cikin Zaria

Yanzu haka Babban Wan Malam Umaru shi ke jagorantar gaba Waya Ahalin nan, Malam Abubakar. Muna kiran shi Baban Sasa; wanda shi ne Babba sannan kuma ya fi kowa iyalai a gidan. Matansa su huWu ne ko wacce da nata zugan Yaran, wasu sun yi aure wasu kuma suna nan sun fantsama �auyaku suna sana'a

Sai kuma mai bin masa Malam Ali; da muke kiran shi da Baffa, shi kuma Matan shi biyu ne da nashi zugan Yaran shima, domin shima Allah ya albarkace shi da yara da yawa

Sai Malam Sule wanda ya rasu da jimawa, kamar yanda na faWa muku Yaran sa biyu ne tal a duniya, kuma shi ne Mahaifina

Sai sauran waWanda yawancin su Mata ne suna aure a sauran yankuna na �auyakun, wasu kuma sun samu ci gaba suna aure a cikin birnin Zarian. A ta�aice dai Iyayenmu Maza a gidan su takwas ne, sai Mata su biyar kuma kowanne Allah ya albarkace su da Yara da dama. Duk da akwai wayewa yanzu sosai a cikin rayuwarmu amma har yanzu muna da al'adun da muka kasa barin shi, duk wani ci gaba bamu yarda mu watsar da al'adun nan ba sabida muna ganin shi ne tushenmu tun iyaye da kakanni, idan za'a yi wa yarinya aure Iyayenmu da kansu suke zaSa mana Mijin aure, sannan kuma dole ne ko wacce Mace sai an yi mata kaciya. Eh kaciya, su Iyayenmu sun mayar da al'adunmu ba namiji kaWai ake yi wa kaciya ba har da Mata, kuma har yanzu suna nan a kan bakansu sun �i dena wannan al'adan sabida sun Wauke shi da matu�ar muhimmanci. Suna ganin ta wannan hanyar ce zasu natsar da �a�ansu Mata wajen kamewa da ri�e budurcin su har sai sun yi aure, kuma suna ganin hakan na �ara wa Mijin jin daWin Matarsa wajen kwanciyar Aure; ko kuma taimakawa wajen samun ciki da sau�i. Wannan al'ada an la�anta shi da auren wuri kuma duk mutanen da ke cikin wannan �auyen zaka tarar Mace ba'a Wauke ta a bakin komai ba kuma bata da daraja ko kaWan, suna yin wannan kaciyar ne da zaran Mace takai shekara goma sha Waya sannan sai ayi mata, bayan shekaru biyu kuma sai a aurar da ita, duk da a yanzu ya sha bamban da rayuwar baya, ada can ana yi wa yarinya kaciya ne da zaran takai shekaru biyar a duniya, amma yanzu kai ya waye an samu ci gaba dole sai yarinya takai shekaru 11 sannan za'a yi mata

Duk yadda Mutum ya so ya dubi al'ada; ba ta wani Sangare da ya cancanta sam. Cin zarafi ne na Wan Adam da bai cancanta sam ya zama yana wakana koda a kan kowa ba, domin wannan Wabi'a na sanya wa Mata da aka yi musu kaciya; zasu kamu da matsaloli da suka shafi lafiyar Mace (mental and physical health challenges) a gaskiya ba Macen da ya kamata ayi mata kaciya. Haka wannan al'umma suke ala�anta kaciyar Mata da addini, musamman addinin musulunci. Haka ma a wasu �asashe da dama suna amfani da addini domin yi wa Mata kaciya; kuma suna kafa hujjarsu mara tushe a kan wannan aika-aikan, duk da cewa basu da hujja kuma basu da takamaiman inda zasu kama a cikin Al'�ur'ani ko hadisan Manzon Allah. Wannan na faruwa ne saboda rashin cikakken ilimin addini da kuma mabiya da basu san al�iblan su ba, wanda ya kasance abun da suke aikata wa Mace daban da abun da yakamata su cire mata, sam kaciya bata dace da Mace ba, hanyar da suka dauko ba shine wanda ya dace ba, a ganin su daidai ne. A dalilin haka wannan al'ada ta samu shiga sosai a wannan �auyen, kuma babu wanda ya isa ya tsallake wa hakan.





P+P+P+P+P+P+P+P+

_____Kamar yanda kowacce shekara ake samun waWanda ake musu wannan kaciyar, hakan ta kasance a cikin wannan �auyen. Mata da yawa waWanda aka shirya domin aiwatar musu da wannan al'adan a gobe juma'a

Inda a babban gida kamar yanda muke kiran sunan gidan mu, Mata shida su ne waWanda za'a yi wa kaciyar suma, shiyasa kowacce Uwa take tausayin Wiyarta sabida abun da zai faru gobe, suna ganin daga yau kuma Wiyar su ta zama babbar Mace, ta tashi a �aramar yarinya, da zaran an yi kuma sai maganar aure da zai fara tashi, inda za'a zaSawa kowacce Mace Mijin da zata aura, wannan dalilin ne yasa Idan ka shiga babban gida zaka ga kowa jigum haka suke zaune duk babu karsashi a jikin su, musamman ma Yaran da su za'a yi wa kaciyar kana kallon fuskokin su zaka ga rashin walwala a tattare da su, ko kaWan ba sa �aunar gobe tayi sabida azaban da zasu sha.
�an uwanmu suna bamu labarin wahalar da ake sha, mu ma kanmu muna gani, amma kuma wacce ta tsallake shikenan, bamu da yadda zamu yi dole ne mu fuskanci wannan ranan kamar yanda �an uwan mu suka fuskanta a rayuwar su.

Da yammacin ranan ne Baban Sasa ya yiwa �an uwan shi kira suka zauna suna tattaunawa a kan gudanar da al'adar tasu a gobe, wanda a cikin jawabin Baban Sasan ne yake cewa, "tunda yanzu Madina ta kawo girma itama, babu wani sa'ar ta a cikin gidan nan sauran duk yara ne, to, sai a haWa ta da sauran Yayyinta da za'a yi musu kaciya gobe itama ayi mata, ai ina ga babu matsala tunda da shekara Waya suka girme ta, kunga mun huta ma."

Jin zancen Baban Sasa babu wanda ya musa, kowa ya ga dacewar hakan, sai kaWa kai suke yi suna cewa, "�warai kuwa hakan ya kamata, ai itama tana da girman jiki ta kamo su a girma, babu wanda zai ce sun girme ta, za'a haWa su kawai ayi musu."

Ana haka sai gani na shigo cikin falon ri�e da kwanon sha da aka aiko Ni in kawo musu farau-farau. A hankali na ajiye kwanon shan tare da dur�ushewa na soma gaishe su cikin girmamawa irin nawa, sannan na isar da sa�on kamar yanda Matar Baban Sasa ta aiko Ni, Matarsa ta farko wacce muke kira da Inna Lami

"Yauwa Madina, ajiye." Cewar Baffa da yayi maganar yana kallo na, domin a cikin su duk shi ne wanda yake da sakin fuska da wasa da Yara sosai

Har na mi�e Baban Sasa ya tsayar da Ni yana cewa, "zauna Madina akwai maganar da zamu yi da ke."

Hakan yasa na samu wuri na zauna a saman �afafu na yayinda kaina ke �asa na kasa Wagowa. Baban Sasa ya soma sanar min da hukuncin da suka yanke a kaina wanda lokaci Waya na Wago kai ina kallon su Waya bayan Waya, duk da ba wani wayau ne da Ni ba domin a lokacin shekaruna goma ne cif; amma kuma ina sane da wannan Shegiyar al'adan tamu wacce ina Waya daga cikin waWanda suke matu�ar tsoron zuwan wannan rana a gare mu, musamman yanda naga Yayata ta sha wahala a lokacin da aka yi mata, tayi ciwo sosai kuma ta sanar min akwai wahala sosai, daga �arshe dai Allah ya bata lafiya har aka yi auren ta, yanzu shekara Waya kenan kuma har da �arta guda Waya da ta haifa ko kwana hamsin ba'a yi ba. Jin cewa da Ni za'a yi kaciyar gobe zuciyata tuni ta cika da tsoro wanda ya kasa Soyuwa a kan kyakkyawar farar fuskata da take Wan tsut da ita, kullum a rame kamar ba na cin abinci, to kusan haka ne tunda dama rayuwar gidan yana matu�ar min wahala kasancewata marainiya babu Mahaifina, sannan kuma mahaifiyata ta fita tayi aure a can cikin Zaria anguwan �aya, shiyasa muke matukar shan wahala Ni da Yayata Haula, sai dai kuma yanzu ita tayi aure ta huta ba kamar Ni ba, kullum kamar Ni ce jakar gida ko wacce Mace Ni take sakawa aiki, babu damar aga wul�awa ta sai Waya daga cikin matan gidan sun kira Ni sun saka Ni aiki, da su saka yaran su sun gummaci su sanya Ni, shiyasa a kodayaushe bani da lokacin kaina kullum cikin bautar Matan gidan nake yi, kuma dole inyi tunda bani da �yuya ko kaWan, idan ma ban yi ba abincin da ake bani sai dai in rasa domin babu wacce zata bani ban yi mata aiki ba, shiyasa na zama tamkar Almajira a gidan kamar ba �ar gidan ba, idan aka yi min wani abu sabo sai dai idan Baffa ne, ko kuma Baban Sasa wanda yake haWa kowa na gidan da sallah yayi musu sabon kaya, to idan ba sallah ba Ni ba na samun me min komai koda biki ake yi a gidan namu, babu me min anko ko ya siyan min sabbin kaya, sauran yaran kuwa iyayen su mata suke siyan musu duk abin da suke so tunda duk suna sana'a suna samu, kasancewar rayuwar gidan mu yawanci matan su suke yiwa kansu hidima na yau da kullum, iyayen mu maza basu saba ba kuma baza su taSa yi ba sai idan sun ga dama, yana Waya daga cikin u�uban rayuwar da Matan cikin �auyen namu suke sha, har yanzu kai ya �i wayewa. A gaskiya na shiga tashin hankali jin cewa har da Ni za'a yiwa kaciya, na ruWe sosai sai dai na kasa yin magana sabida kasancewar Baban Sasa ne mai maganar, domin shi ba ya Waukar raini kuma ba ya so yana magana ana katse shi, yana da son girma sosai duk abin da ya gindaya to babu me iya tsallakewa. Hakan yasa ya bani umarnin, "in je gidan Yayata in kira ta." Babu musu na mi�e na fita jikina na rawa kamar mazari, har ina jin tamkar �afafuwana baza su iya Wauka ta ba, duk yanda na so na daure kar na fitar da halin da nake ciki amma hakan ya faskara, tuni hawaye sun soma sauka a kan dandamalin fuskata sai shatata suke yi kamar an kunna famfo, dole na mi�a hanya na fice daga gidan namu na doshi gidan Yayata da babu nisa sosai, tunda naga na fita cikin jama'a sai na soma kuka wi-wi kamar ana yankan naman jiki na, har ba na iya ganin gabana a yanda nake tafiya a haka nakai �ofar gidan da Yayata take Aure. Gidan ba wani babban gida bane kuma su uku suke zaune, daga surukar su sai Wan Mijin Yayata; da Matarsa shima da yara biyu. Ina shiga babu kowa a tsakar gidan sai na nufi kaina tsaye Wakin Yayata, ina shiga Wakin kuka na ya janyo hankalin ta da har barci ya soma fizgar ta, tana rungume da jaririyar �arta me sunan Umman mu, Asiya, mu kuma muna kiranta da Ihsan

Yayata hankalin ta ya tashi ganin yanda na shigo mata ina kuka, shiyasa nan da nan ta ruWe ta soma tambaya na, "Madina lafiya mene ne? Me aka yi miki? FaWa min inji?" Dukka ta rungumo Ni jikinta tana kallon fuskata; yayinda ita nata fuskar cike da damuwa tsantsa

Ni kuma kukan nake yi na kasa denawa. Dole ta zauna bani ha�uri har nayi shiru sannan ta sake tambayata? A nan na bata labarin komai har da kiran da Baban Sasa yake mata

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..." Salati kawai take rafkawa lokaci Waya ta sake rikicewa wanda har hawaye ne suka soma sintiri a kan fuskarta me kama da nawa sak, cikin tsantsan tashin hankali tace, "yanzu kina nufin da ke za'a yi wa kaciya a gobe?"

Shashshe�a na soma yi ina gyaWa mata kai a hankali, yayinda wani kukan ya sake taho min sai na faWa jikinta ina cewa, "shikenan Yaya Haula nima zan fuskanci wannan u�uban rayuwar da ku ka sha? Ni yanzu ya zan yi wlh bazan iya jurewa ba, idan aka yi min mutuwa zan yi, don Allah ki kai Ni wajen Ummana ba na so ayi min, ki ce musu ba na so."

Haula ta kasa magana illa sake rungume Ni da tayi tana kukan itama sosai cike da tausayina, ta san kuma aikin gama ya rigada ya gama dama wannan ranan take gudun zuwan ta, tana tausayin �anwarta musamman kasancewar ta me rauni sosai, tana gudun zuwan wannan ranan ga �anwarta, amma babu yanda zasu yi dole ne itama sai an yi mata. Ta kasa rarrashina yayinda Ni kuma nake ta sambatu ina kuka ina faWa mata, "Ni ba na so." Ri�o kaina tayi tana Wago Ni tare da kallon fuskata da nake ta shatatar ruwan hawaye, haka itama nata tuni idanuwanta sun yi jawur tace, "haka nan za ki yi hakuri Madina babu yacce zamu yi, wannan al'adan dole ne ayi, dama tunda kika kawo girma dole za ki fuskanci wannan rayuwar, ko ba'a yi miki yanzu ba a nan gaba za'a yi miki, domin baza a taSa aurar da ke ba sai an cika wannan al'adan, kiyi ha�uri kinji babu yadda zamu yi. Tashi mu je kar su ji Ni shiru ya zame min laifi." Ta �are maganar tana cire hannunta daga kaina, yayinda ta bi Ni da kallo ganin yanda na ci gaba da kukan ban fasa ba, "kiyi ha�uri Madina kiyi shiru, kukan nan be da amfani kar ki sakawa kan ki wani ciwon, ki share hawayen ki mu tafi, bari in goya Ihsan." Sai ta tashi ta saSa Ihsan Win da ke faman sharan barcin ta hankali kwance, sai da ta gama goya ta sannan ta yafa mayafi ta kalle Ni tace, "mu je, ki dena kukan nan nace kar mu je a ganki a haka."

Kai kawai na gyaWa mata ba don zan dena ba, domin kukan ma na kasa tsayar dashi sai shashshe�a nake yi yayinda wasu sabbin hawayen suke ta kwaranya a kan fuskata, sai saka hannu nake yi ina sharewa amma hakan babu amfani. Hannuna ta ri�e muka fita a gidan tunda babu kowa bare tace musu, "zata je ta dawo."

Muna shiga zauren gidan mu; ta sake share min fuska domin kar a gane nayi kuka, amma kuma duk da haka ana kallo na za'a san kuka nayi, yanda idanuwana nan da nan suka tashi suka yi girma sosai suka yi ja, dama ga su manya ne sai suka sake luhu-luhu, sai jan majina nake yi ina shashshe�a. Kai tsaye falon Baban Sasa muka wuce ba tare da mun shiga cikin gidan ba, tunda sashin shi daban ne ba sai ka shiga ainihin sasukan gidan ba, sai dai idan ka haWu da mutane a hanya amma babu me ganin ka, tunda gidan yawa ne baza ka rasa yara suna wasa ba. A bakin �ofan Yaya Haula tayi sallama ta shiga ri�e da hannuna, hakan yasa na sauke kai �asa kar ma su gane a halin da nake ciki, har yanzu jan ajiyan zuciya nake yi na kasa denawa. Zama muka yi a wuri Waya inda ita Yaya Haulan ta soma gaishe su cikin girmamawa

Suka amsa ta cike da kulawa wanda har Baffa yake cewa, "Ina Ihsan Win; ba dai tayi barci ba?"

"Eh Baffa tayi barci."

"Ayya uwar son jiki; ai na kula yarinyar irin Uwarta Madina ce, Allah ya raya ta." YafaWa cikin murmushi da wasa a fuskarsa

Tsirarun mutanen wurin suka amsa da Amin har da Yaya Haula, kana ta �ara da faWin, "Baba gani an ce kuna kira na."

"Eh Haulatu. Maganar �ar uwanki ne da muka yanke hukunci a kanta, gobe da ita za'a yi wa Yaran gidan nan kaciya sabida a huta, to ke �ar uwanta ne shiyasa muka kira ki mu sanar miki, sannan ki buga waya ki sanar da matafiyarku halin da ake ciki."

Cike da sanyin murya Haula tace, "to Baba." Batare da ta sake furta komai ba bare tayi gardama

Sai ya bata umarnin tafiya, shiyasa ta tashi zata fice. Nima hakan yasa na mi�e na bi bayan ta, yanda zuciyar Yaya Haula gaba Waya babu daWi ta kasa rarrashina saboda tunda muka fito na fashe mata da kuka, dole ta ja hannuna muka wuce gidan ta, ta zaunar dani tana ta faman rarrashina, ita kanta karfin hali ne irin nata amma ba wai farin ciki take yi ba, bata san ma ta hanyar da zata sanar da mahaifiyarmu ba sabida a yanzu bata da waya ta lalace, shiyasa ta yanke shawaran goben nan zata nufi can anguwan �aya ta sanar mata, ko hakan zai taimaka ita Umman tamu ta zo ta basu ha�uri a �yale Ni zuwa nan gaba, tabbas da cutuwa ace kamata za'a yiwa kaciya, su kansu da aka yi musu da shekarun su ya fi nawa sun sha ba�ar wahala bare Ni, shiyasa take matu�ar tausayi na. Ni kuma duk rarrashin da tayi min na �i yin shiru, Ni gani nake yi kamar idan aka yi min shikenan mutuwa zan yi, rayuwata ta gama yawo, bazan sake ganin Ummata ba, itama Yayata zan rabu da ita

Ana haka sai ga surukarta ta shigo gidan, jin kukana shi ne ta shigo Wakin tana tambayar ba'asi?

A nan Yayata ta sanar mata komai abun da ke faruwa

Sai tace, "oh! ke kuma Madina mene ne na tayar da hankali bayan kin san kowacce Mace da haka ta saba? Haka nan za ki yi ha�uri idan an yi miki yanzu ai kin huta, Haula sai ki rarrashe ta tunda ita yarinya ce dole sai ana tausan ta, Allah yasa ayi a Sa'a."

"Amin Mama." A cewar Haulan

Inda ita kuma Maman ta fice tana sake tausa na

Ni kuwa ina jikin Yaya Haula ina ta �ananun kukana na kasa yin shiru, �arshe har aka kira sallan magriba kafin na tafi gida, shima sai da ta bani abinci na ci da�yar domin na kasa cin komai, haka ta lallaSa Ni sannan ta tura Ni gida

A lokacin da na isa gida har maganar ta zagaya ko ina, cewa dani za'a yi kaciyar gobe, masu tausayi na nayi waWanda kuma basu damu ba takan �a�an su suke yi, babu ruwan su da Ni tunda su ma abun ya shafi �a�an su. Haka na wuce Wakin mu da muke kwana dukka �an matan gidan sa'anni na duk da ni ce �aramar su, babu mai walwala a cikin mu gaba Waya, dama Ni ce to yanzu an ce har da Ni za'a yi, shiyasa nima na bi ayarin su. Tunda nayi sallah na haWa da magriba da isha'i na kwanta a tsumman katifana na kasa tashi bare in fita, ina jin hayaniyar �an gidan amma na kasa fita bare ayi dani, yawanci su ma sauran suna zaune a Wakin, wasu kuma sun wuce Wakin iyayen su suna can ana rarrashin su, Ni kuwa ba mai rarrashina, ina jin sanda samarin gidan suka dawo suma ake basu labarin ai har da Ni za'a yiwa kaciya, wasu sun tausaya min a ciki, wasu kuma suna cewa, "haba har dani memakon a bari sai wata shekaran? Ai nayi �an�anta tunda su Fa'iza sun girme Ni." Yawanci maganganun da suke tayi kenan, Ni kuma jin hakan ke �ara raunata min zuciya, sai kawai hawaye suyi ta zuba min ina danne baki kar kukana ya fita; ya zame min wani bala'in. wayyo Allah! ya zan yi da rayuwata? Shikenan gobe zan fuskanci wata rayuwa? A ha�i�anin gaskiya ba na �aunar wannan kaciyar, ina matu�ar tsoro amma babu yadda zan yi, bazan iya tsira ba. A haka na kwana a cikin zullumi, ko in ce muka kwana dukkan mu, barci na ragagge ne a wannan ranan da nayi; cike da tsoro da zullumin zuwan goben.


_Labarin zai zo muku a duk sati sau uku a rana ne, every Juma'a; Saturday and Sunday, please babu �orafin hakan don Allah. WaWanda suke son magana dani kai tsaye a WhatsApp zasu same Ni a kan wannan numban 07065334256. Nagode Masoyana._
[1/27, 4:05 PM] Oum�ahira: =؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�
*RAYUWAR MADINA* =ا�
=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�=؎�


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>���*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <��

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ت�)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A
'�*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga �an uwana Mata waWanda suka fuskanci u�uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana �arshen wahalar rayuwa._
















______________ *EPISODE 2*
_____Washe gari Yaya Haula ta sanar da Mijinta sa�on Baban Sasa, ta CE mishi, "zata je ta sanar da Umman su." Shiyasa ya barta ta tafi kusan �arfe goma na safe, tafiyar awa Waya da rabi ne ya kaita cikin Zaria anguwan da Umman su take Aure

Dayake yau Asabar ne tana gida ita da yaranta, Mijinta ne kawai ya fita �wadugon sa da ya saba, ba wani me shi bane tunda kullum sai ya fita sannan zai samu wanda zasu ci a rana, shiyasa Umman namu take aikatau a wani gida da ke kusa da su, Matar tsohuwa ce sai jikokin ta da take zaune da su, shiyasa aka sama mata me aiki tana rage mata wasu abubuwa, to a nan ne su Umman mu suke samun na rufawa kansu asiri, ga Yaranta Hassana da Hussaina da ta haifa sun girma sosai, domin yanzu shekarun su kusan bakwai ne, tunda tun sanda Baban mu ya rasu ta koma �auyen su, sai tayi aure babu jimawa, to daga kan su Hassanan ne bata sake haihuwa ba duk da tayi Sarin wasu �an biyun

Umman mu tayi mamakin ganin Yaya Haula da safen nan, shiyasa ko zama bata yi ba ta soma tambayar ta hankalin ta duk a tashe saboda gani take yi kamar babu lafiya, musamman yadda ta ga fuskar Yaya Haulan ta koma

Yaya Haula bata ce komai ba sai da ta zauna sannan ta gaishe ta, �an biyu ma suka gaishe ta; ta amsa su tana musu murmushi

Sai Umma ta cewa Hassana, "ta tashi ta Wauko mata kofi ta zuba wa Yayar su koko."

Hakan yasa Hassanan ta mi�e ta je ta Wauko ta kawo

Umma ta amsa ta zuba mata, ta tura mata da raguwar �osan da ke gabanta tace, "ga shi ki ci, sauko min takwaran tawa."

Babu musu ta

Please Login or Register in order to submit comment