Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...

*Chapter 1*

"Haba Umma, Ke ko kunya ma bakyaji ace Jiya ankawo miki Suruka Yau har kin fara nuna mata halinki, Hava Umma wannan ba ajinki bane gaskiya, kamata yayi ki gode Wa Allah ma da ya baki surruka mai hakuri Amma wlh ni babu wata tsohuwan da ta isa a kawo ni gidan danta jiya ta Sani wanki yau, inaa Allah saidai ayita ta qare Ehey" Na fada ina hararta ta qasar ido

"Ke dallah rufe ma mutane Baki, Me kika Sani a zama da uwar miji?, insha wahalan Daukan cikinsa , haihuwa da raino , Wata tazo da rana tsaka tace zata rabani da Dana?๐Ÿ˜ , Ai ko kece nasan zakiyi fiye da hakan mah"

"Mtsww" Naja tsaki tare barin wajen Har na kai bakin kofa sai na waiwayo nace

"Umma ina Rabaki,.....Ban iya waazi ba da nayi miki waazi ko Zaki gane ki fahimta zama damatar da ba zama da baiwa bane, Don kin haifeshi kin Raine shi ita ba haifan ta akayi ba?.....Ohw no wonder JJC ne ke damunki tunda baki ta6a aurar ba shiyasa kike Son shinfida tsiya da na farko ko?......abege duk ba wannan ba mah, ah no fit talk for this matter.. kije ki kar6i wankin ki kiyi da kanki,Inba haka ba ina komawa gida zan fadawa Abba," Ina dasa aya NASA kai na yi ficewa ,Na barca da Bakin cikin maganganun da na Gasa Mata,
Duk cikin 'Ya' Yanta Babu wacce take kallon ta kaitsaye ya Gasa Mata maganganu Sai Ni, Ta rasa mai yasa,bata iya maida mini martani ko ta kwa6e ni Akan Rashin kunyan da Nike mata ba, Ko Dan halaccin da iyayena suka yi Mata a lokacin da suke Raye ne oho!

Ina fita daga dakin Umma kai tsaye parlor na nufa inda na tarar da kawayen Amarya ,Na karasa inda suke fuska sake ina gaishe su.
Yasira babbar kawar Amarya ta kalleni tace "Wai ina Amarya ta shiga ne inata trying numbern ta yana Ringing amma Baa dauka ba, To nayi tunanin may be suna tare da angon ne ,kuma kinga bai kamata na takura ta ba"
Kalamanta na karshe sun bani dariya _(wato suna tare DA Ango_ ) saboda haka sai da nadan dara "hehehe aikam Suna Tare da Ango Fa, Kuje Common Room zaku ganta wankin kayan uwar angon takeyi" Ina gama fadin haka nayi gaba ina dariyar mugunta๐Ÿ˜‚

Gaba daya kallon kallo sukeyi babu mai cewa uffan Dan basu Fahimci inda maganganuna Suka nufa ba.
Suna Haka sai gata ta fito Riqe da bucket mai dauke da wankakkun kaya.
Turus tayi ganin kawayenta zaune duk sai kunya ya kamata, ita shar ta manta sun kirata sun fadamata zasu zo
Jiki a sanyaye ta ajiye bokitin wankin ta nufi inda suke zaune sun Zuba mata ido, ta kakaro murmushi tace "aah Yassy,Rukky ai banyi zaton zuwanku yanzu ba na dauka sai da rana ne"
Rukky da ta kasa hakuri tace "Amarya kece da Wanki da kanki?,"
"To laifi ne Don nayi wanki?"
Yaseera tace"Ba laifi bane,Amma wannan ai ba kayanki bane, ji uban kayan fa?,In ma naki ne daga jiya zuwa yau ai bai ci ace kin bata Uban kayan nan ba koke waye kuwa"
Cikin in ina Ramla(Amarya) tace "Eh dama kayan umman shine tace nadan wanke mata"
Rucky tace "baga kanwarshi ba?,Meyasa bata bata ta wanke ba?,Sai ke zuwan jiya,kuma kinsan yanayin jikin ki baki da lafiya akayi auren nan maimakon ta......"
Muryan Umma Sukaji abayan su tana fadin" To Sannu uwarta Sannu Mara kunya, ke har kin isa ki tako kafarki har gidan Dana kice Zaki ci min mutunci?, ko gidan ubanki ne nazo kia min haka?,Ballantana Gidan Dan da na Haifa da kaina"Sai ta tsagaita tana nunasu da yatsa manuniya tace"banason dogon magana daku domin yin hakan barazana ne a gare ku kafin in kirga Uku Ku fice min a gida Banason Sake ganin wata daga cikin ku ta tako kafafunta tazo gidannan oya Get owt of my Sight jare" Ta karasa tana nuna musu hanya
Ruky tayi Yar dariya harda tafa hannaye "Lallai tsohuwa ai ko baki kore muba fita zaayi,Allah yaso badaga gidan matsiyata muka fito ba,kowa da gidan ubanta, Mtsww aikin banza" Tana dasa aya ta dau jakarta ta fice ba tare da ta waiwayo ba, yaseera ma tabi bayanta Suka shiga motarsu Suka bar harabar gidan
Bayan fitar su Umma ta kalli Ramla tace "Tunda haka kika za6a wato kiran kawaye ana ci min mutunci to bismillah mu zuba dani dake Dan halak ka fasa " Tadaka mata tsawa
"Zaki je ki karasa aikin da nasaki ko inje inyi da kaina?"
Ramla ta share hawaye kamar tace mata eh amma bazata iya ba, Dole ta je ta karasa abinda ta umurceta tayi

Dadare 11:00pm na dare Aryaan ya Shigo da ledar kaji da fresh milk Dan jiya Umma ce ta cinye masa kazar amarcin Sa Wai yunwa takeji gaskiya kuma ita kazar take so(ohh ni 'yasu ๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ,see me see wahala yau ga uwar mijin novel me cin kazar amarcin matar danta๐Ÿ˜†)

Cikin Sanda ya Shiga gidan ya tarar babu kowa a falon sai karar TV yasan wannan aiiki nane (barin TV a kunne),Ya karasa ya kashe Tvn, ya haura sama kamar wani barawo zai bude kofan bedroom yaji an kira sunansa Ta baya" Aryaan har ka dawo?, To ina zaka da Leda haka?"..
Baki na rawa yace "Ehm dama kazace da fresh milk, Kinsan ban kawo mata jiya ba, Shine nace...."
Bai karasa ba yaji tace "Kaza da madara?, nifa?, ka barni da yunwa ka siyo ma wata gardiya kqza harda madara?,"
Sai ta fara sharar kwalla
"Daman na Sani auran nan ba alkhairi bane a gare ni shiyasa na nace akan bazaka aureta ba,Amma ka nuna min ban isa ba gashi Tun baa kai koina ba ka fara wulakantani

Aryaan ya rumtse ido cikin matsanancin 6acin rai yace " Umma ba dai akan kaza bane?,To gashi" ya bata ledar kajin bakunya ba tsoron Allah ta sa hannu ta kar6a
Yace to sai da safe ya juya zai shiga daki ya dakatar dashi " Ai ba shi kenan ba ,dama Tun dazu nake jiran dawo muyi hira"
Ya kauda zancen da cewa "Umma yaushe Zaki koma?"
Tace "Ka kosa in tafi ne?"
A ransa kaman yace eh amma sai ya girgiza kai "Aa Umma dama gani nayi an gama biki kuma..."
"Kuma na takura maka ko?" Sai ta fara sharar kawalla "Da nasan haka zaka wulakanta ni aryaanu da Ko gidan nan ban tako ba , yanzu zamani ya chanza da ke korar uwarsa a gida akan yayi mata!๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ"

Aryaan ya dafa kai "ohh my god๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ, in hira ne Umma idan nayi wanka na ci abinci zanzo"

Umma ta share kwalla tace "Muje part dina kkayi wanka sai muci Kazan nan tare nima yunwa nake ji"

Aryaan bakin ciki kaman ya kashe shi haka babu yanda ya iya ya biye mata yayi abinda take so

Ramla da ta Dade tsaye bakin kofa tanajin su ta share hawaye ,Tun ranar amarcinta ta fara fuskanta matsala da uwar miji ina ga nan gaba, jiki a sanyaye ta koma ta kwanta tana tunanin kalakala akan yanda zaman su da Umma zai kasance

Washe gari Monday Nida Hafsah muka shirya Tun Shida da rabi ko break fast bamuyi ba Saboda lecture dinda muke dashi7:00am gashi shegen lecturer ne baya daukan excuse, Gashi yana taking attendance serious

Nida Hafsah muka shiga motana naja Muka fice da gidan A hankali muna Dan ta6a hira

Hafsah tace "Sis kinji Draman DA ya faru jiya da daddare?"
Na juyo na kalleta sannan na maida hankali na ga tukin da nikeyi
Nace" bani nasha"



Shin Wai wane irin gulma hafsah ta kwaso?

Me zaku fada akan wagga uwar mijin?๐Ÿ˜‚

Please share
And
Comment




Fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ


Acigaba da wanke hannu๐Ÿ˜‚

Stay safe๐Ÿ˜€
9^Aug^August

๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...

*Chapter 2*

Tace "jiya bayan mungama kallo mun kwanta, Hayaniyan Yaya Aryaan ya tashe ni" Sai kuma tayi shuru

Nida son jin gulma balle kuma akan dodon nawa, ai tuni na bata hankali na nace "What happened Again, Me ya faru?,Fada sukayi ne?,"

Hafsah yi Yar dariya tace "Heh.. Kece idan kin kwanta barci marabar ki da gawa numfashi, ai nata tashin ki Don gudun Dama-dama, Amma kaman kara miki nauyin barcin nike, Amma fa na dauki Wasu a waya nah"

Saida na rage gudun Motar kadan kafin nace "Tell me what happened Fara fada min inyaso anjima na kalla video din"

Ta kwashe da dariya tana fadin "wlh Munayferh kin cika zakewa dayawa,ina kaiki ki bari na isa inda Nike son zuwa dake mana"

Shuru nayi mata itama daga nan bata sake fadin komai ba.
Ganin Abinnata ya fara zama rainin hankali yasa na sami gefen hanya nayi parking
Ta dago ta kalleni a razane, nima kallon ta nayi cikin maganana mai kamada An tilastamin nace "If you'r ready tell me In kin gama Jan min rai ki fada min Abinda ya faru jiya, in kin gama Sai naja mu mu tafi"
Hafsah ta dubi agogon dake manne a tsintsiyan hannunta tace "Haba Munaiferh Yanzu fa 6:45am pls ki tada Motar mu tafi kar muyi latti"

Na tabe baki dakko wayana Na fara latse latse,

Hafsah ta san halina na kafiya akan abinda nke so koda zan rasa abu mai mahinmanci agareni ne bandamu ba in dai zan sami abinda nike so bqn dqmu ba kowa ya mutu ๐Ÿ™„

Chan sai naji hafsah ta dafa ni "Sis ga videon" naji ta fada a sanyaye,

Bansan lokacin da murmushi ya kwace min ba, na karba na kalla ina jinjina karfin hankali irin na tsohuwa Umma, ina gama kallon na tura a wayata nabata wayanta ,Sannan naja Motar muka wuce babu mai magana a cikin mu
Ita hafsah tana jin haushin abinda nayi mata DA danasanin gaya min draman da tayi, gashi nasa munyi latti,Ni kam Zuciya ta Fess,Bama fargaban Rasa lectures din Nike yi ba tunanin Yanda naga ran yaa Aaryaan ya 6ace nake ko ba komai nadan ji dadin hakan, an cinye masa chicken kuma an Hana shi yin xhfsilvdativxxnkdwyogckrqakner๐Ÿฅด๐Ÿ˜œ
Dan na tabbata ba yarda zatayi ba, Bataci ba a hpkxqkgf ta? ...
Da wannan tunanin muka isa makaranta kaman kurame
Munyi Saa malamin Malam daud yana Shirin Shiga aji yana tsaye bakin kofa yana waya Da sauri na kamo hannun hafsah na bangaje Shi yayi baya Ranga ranga,Sai gashi a jikin Fareeda Shu'aib (Assistant c-rep) Gaba daya aji ya kaure da hayaniya, Masu waya na daukan su kai harda masu video live, nan take Wasu suka fara posting a kan Net with the caption
~"Yau Dubun Ks.Daud ya cika sakamakon kamashi da akayi Rungume da wata daliba a lecture theatre, Alamu dai sun nuna ba yau ya fara hakan da ita ba"~ (Kai jama'a๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ˜†),

Shi dai KS daud, bai sake sanin inda yake ba,Gani yake kaman ya kwanta a kan katifa๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

Hasken Flashes na wayoyin mutane ne ya dawo dashi hayyacin shi Sai yanzu ya lura da abinda yake faruwa

Kunya,Tsoro,kai harda Rashin gaskiya duk suka hadu suka gare mai guri daya ya duka zai kwasa littafan da ya zube wani student yayi saurin kwasan mishi harda kakkabewa yana dariya ya miqa masa, ya amsa kansa a sunkuye tareda ficewa daga lecture theatre din.
Yan aji suka dau shewa dama suna kume da Farida sakamakon cin kudin su da tayi tace wani lecturer yace sukawo kudin class list kunsan Yan 100 level da JJC Shine daga baya sukejin ai ba haka akeyi ba , ko zaa bada kudi bai wuci 5naira ko ten naira ba tunda single copy ne.

Ranar dai na zama cele Don musamman ake zuwa sit dina ana min godiya Wasu na kar6an number waya na Wasu na daukan hoto dani, ni kuma abin nema ya samu sai shan kamshi nake ina daga kai irin nayi abin arzikin nan....

Da naga zasu isheni sai na tashi nabar musu theatren Don har na farajin yunwa kunsan dai ban karya na fito ba.

Na nufi Student cafeteria na skul din nayi ordrn abinda Nike buqata ina zaune wayana ta soma ruri , Jaanaan ce . nayi takaitaccen murmushi Kafin na dauka
Nace "Hello Besty yau where are you? bazaki shigo bane?,"
Daga chan 6angaren tace "sorry babe Wlh nayi latti ne Sai 11:30 zan shigo inshaallah"
Nayi Yar dariya nace "Banza ina jiran ki nan da 15minutes kizo ina cafeteria akwai news phaa"

Dake itama gulmammiya ce iri na Kit ta kashe wayan ta Shirya 10minutes sai gata tazo ko da yike offkay gidan da take zaune babu nisa da skul din


taja kujera ta zauna kusa dani tana tambaya na miya faru tas na maida mata abinda ya faru Aikan Tasha dariya harda riqe ciki, gata dama gwanan dariyan mugunta, tace ohsht Gaskiya nayi missing Omg naso ace ina nan da tuni nima na posta Dan hegiya me kirar yahudawa,
Nima dariyan nayi nace "I Dnt even know what happened nima wlh tsautsayi ne, ture shin da nayi da niyyar mu shiga kafin ya gama waya,sai gashi ya kwaso laushi"

Jaanaan tace Ku shiga ke dawa

Nace Nida hafsah mana ai tare muka zo yau

Tace yanzu ina take ?

Nace tana baya na na Goya ta

Tadan harareni "Damn it ke dai da maganar banza kike wlh daga magana?" Ta karasa tana daukan Roban cuptail din dake gaba na.

Harararta nayi "Kwadayayya kinzo kenan "

Saida tasa cuptail din a baki ta zuka sannan tace "uhnm,Babe duk ba wannan ba ya gajiyan biki ya Amarya?"
Nace "Thank God Gajiya yabi jiki, Amarya kuma Hmmmmmmmmmm......nan na kwashe mata abinda ya faru harda Wanda nagani a video

Harna gama bata labarin batace komai ba ta daiyi tagumi tana kallo na kaman ta same TV

Ta Dan nisa tace "This is strange, Ni ban ta6a jin irin wannan labarin ba ko'a hausa novels wlh ina tausayin Mata Masu uwar miji,Su hana mutun sakat ,Da anyi magana Suce Ai su suka Haifa "

Na ta6e baki "gane min hanya ni wlh bazan auri mai uwa ba, da na auri mai uwa gara na mutu gauruwa"

Jaannan tace "Kar kice haka fa ba duka aka hadu aka zama daya ba "

Nace "ke kika San wannan ni dai na fadi nawa" haka muka cigaba da hira Har lokacin da time din next lecture yayi.

*******

Aryaan na dawowa daga masallaci Yaji motsi a kitchen yasan dai ni bazan tashi na shiga kitchen da sanyin safiya ba, kuma hafsah tana tsoron Gas bata son girki da gas ko dai Umma ne?, ya tambaye kansa, Da sauri ya karasa nan

Ramlah ya gani Sanye da Night Gown Pink ,Yadin yabi jikinta, Wani Abu yaji yana yawo a jikin shi.....(Mutum da Abinsa Anyi masa iyaka dashi๐Ÿ˜ฉ)

Jikinta ya bata ana kallon ta yasa ta waigo suka hada ido tayi Saurin kawar da kanta Daga kallon Shi.
Shima yasha jinin jikinsa yasan bai kyauta ba Abinda yayi Mata bah.

Baice komai ba, Yayi Folding hannun RigarSa ya sa hannu suka karasa girkin tare kafin suka kai dinning area zata koma ya riko hannunta ta kwace, ya qara Riko hannunta ta kwace ganin bazata saurareshi ba yasa ya Rungumo ta ya manna ta a kirjin sa...
Daidai wannan lokacin Umma ta fito daga dakin ta Rike da Gorar Fresh milk Wanda basu sha jiya ba

Daga kan da zatayi idanunta yayi gamo da mugun gani๐Ÿ˜‚.......





CHAI ,AKWAI KURA๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ


NI BAZANCE KOMAI BA๐Ÿ˜ฉ


Fahnaan๐Ÿ–‹๏ธ




Sunday 9th August


๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah๐Ÿ’”}~
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
NA
*๐ŸคFahnaan๐Ÿค*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_

ยฉ๐ŸŽ†
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* โœ๐Ÿป
_Aโ€ข Wโ€ข Aโ€ข_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…...

*Chapter 3*

Glass cup din dakedake hannunta ya ku6uce ya fadi, Nan danan ya fashe ji kake tangarararar...

Firgigit suka dawo cikin hayyacin su , Suka waiga Saitin da suka jiwo Kara,

Tsoro, Firgici, da kunya duk suka hadu suka Dabaibaye su gabaki daya

Aryaan ya sunkuyar da kai yana Dan Sosa Kai Yace "Ehm,Umma Kin tashi lafiya?"

"Ah Sannu Mara kunya, nace Sannu ba, Ai kai ne da Sannu, Ka tashi lafiya?....baka amsa ni ba nace ka tashi lafiya?, ko da yike Ba abin mamaki bane Dan in kana tare da yar boko zakayi fiye da haka mah " Ta kalleshi, Yayi tsaye yana kallon ta tace" zaka 6ace min da gani ko sai na sa6a maka"

Ya wuce sumi-Simi kaman wani Mara gaskiya.

Ta juya da kallon ta ga Ramla wacce ta kame wuri guda zazzaro Saboda tsananin tsorata da tayi "Look young lady, kar ki Ga ina Hana miki Wasu abubuwa kiyi zaton bana sonki ne ko kuma ina son takuraki, To ki bude Kunnuwanki kijini da Wannan mijin naki dakike lilliqe mawa Hoto ne dashi da babu duk daya, ina nufin ko kun kasance tare bazai iya ta6uka miki komai ba, dana nakasasshe ne baya haihuwa"
Da sauri Ramla ta dago Ta dube ta a tsorace, lokaci Guda heart Dinta yayi beating, tadafa kirji tana adduar Allah ya tasheta daga mummunar mafarkin da takeyi๐Ÿ˜ญ
Muryan Umma taji tana cewa "Gara ma Tun wuri kisan yanda zakiyi Tun bai gama dake ba,Dan ko shi bai San da lalurar nan ba"

Kasa jure maganganun Umma tayi ta haye sama da gudu tana hawaye mai sauti
Umma tabita da kallo ta kwashe da dariya "Yarinya kadan kika gani, indai ina Raye dana bazai ta6a kusantar ki ba , jibeki fa wata bunsura dake Mtsswww aikin banza"

*****
Aryaan kam ya na fita kai tsaye parking space ya nufa ya shiga mota ,ya jingina da backseat din motan yana tunanin mafita akan Wannan sarkakiyan
Shawara ce ta fado mishi ya kira Abokin Shi Hilal, Ringing daya ya daga kafin yayi magana Hilal ya rigashi "Ango kasha kamshi , Kar kace min har kun tashi"
Aryaan ya katse shi da cewa "See you ,ni fa yau idona biyu ban ritsa ba Dan bacci gagarana yayi"

Hilal yayi dariya "Ai dole ne ,An kwana ana Raya Sunnah..."
"Mtsww, Raya sunnan ko Raya tension"

"Ai dole ta baka tension, Nima Allah ya bani wata tayi wuf dani nima na raya Tension๐Ÿ˜†"

"Amma dai Anyi Soko anan, nifa ba irin wannan Tension din bane nawa, ni Tun da aka kawo min Amarya ta ko hannunta ban ta6a rikewa ba sai yau da safe .................. Nan ya labarta mishi Abinda Ya faru

Hilal yaja Dogon numfashi yace ai in Dan wannan ne ai me sauki ne " bude kunnenka kaji ya zaka yi " Nan ya fada mishi yanda zaiyi( Meye na kallo na kuma?, nifa banji abinda Abinda ya gaya mishi ba๐Ÿ˜’)

Duk suka kwashe dariya Aryaan yace"Amma fa kai Dan iska ne,duk Salon yaudara kai ka'iya, Allah ya barmun kai Buddy, "

Hilal ya amsa da Amin Suka cigaba da hirar su cikin So da kaunar juna


Karfe

Please Login or Register in order to submit comment