Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nake yi ba .

fk ya sake dubanshi sannan yace dan rainin wayo kawai "kar ka mai dani tamkar wanda bai san komai ba mana .
,tunda har ita zuciyartaka ta iya amincewa daita, har kaji zaka iya aurenta definitely kana sonta" ko yaya ne" .
,. Amman maganar kace baka sonta,wanna ma ba gaskiya bane .

deeni yaja tsaki hade da furzar da iska ta bakinsa" sannan yace matsalata dakai kennan rashin saurin fahimta .

fk yace ta yaya kake so na fahimci wannan shime ?
Alhalin ga zahirin gaskiya nan Ina Gani.

" idan son da kake mata ne ,na fahimta wannan.
,Amman kace wai kai baka sonta km kake kokarin aurenta , wannan ne fa bazan taba fahimta ba.sai dai kayi hakuri ,

DEENI ya sake furzar da huci may zafi ranshi yasoma baci muryasa a sarke" yace da alamun kana son mu samu matsala dakai fa" muddin baka daina cewa Ina son yarinyar nan ba .

Idan km kafin son haka ya daga kafadarsa alamun Shikenan ,.
parlour ya dauki shr na wani "dan lokaci, yayinda deeni ya jingina bayansa da kujera da yake zaune, hade da soma jijiga kafarsa daya a tile's din dakin .
" runtse idanunshi Yayi dan jin daci abinda fk din yace"
'ta yaya ma " zai nace akan lallai yana son yarinyar byn shi yasan auren kawai yake da bukatar yi" bawata ,aba soyayya ba ...

maganar fk ce ta daki dodon kunnenshi" to yanzu meyye solution akan maganar, tunda yarinya ta rigada ta amince ?


Ahankali ya bude rikitattun idanunshi ya sauke su ,akan fuskar fk sannan yayi magana cikin sanyi tamkar wanda aka takura masa dole. Yace karkadamu zan samu yaya mahamud ,Ai ka gama may wuyar " tare da maida idanunshi ya sake lumshe su tamkar dai yadda yayi dazu .

girgiza kai kawai fk yayi. shi wannan fa bazai taba canzawa ba .

halinsa, na nan kmr dai yadda yasan shi" haka km yataso da murdanden ra'ayi " shi komai baya so ,matsawar ba ra'ayin bane fk ya fadi haka haka kasan ransa,,.

Ganin da fk yayi DEENi ya bawa banza ajiyarsa yasa shima ya mike yayi masa sallama yayi ficewarsa .


Daga gurin DEENi kai tsaye fk part dinsu shemah yayi ,ba bata lokaci yasamu yaro ya tura ayi masa kiranta.
dan ya kudirtawa ransa ,yau ce, ranar da zai isar da sakon zuciyarsa gareta .
domin yagaji da cutar da kansa .

tafito sanye cikin doguwar rigar material puppy colour mai shegen kyau hade da yane kanta da karamin mayafe baki,

ahankali take isowa gareshi duk step daya da tayi Sai kirjinta ya motsa sakamakon dukiyar fulani dake gareta.
tun fitowarta , ya zubawa kirjinta idanunshi kyam ko kyafta ido bai yi .
yana kallon yadda albarkatun kirjinta ke motsawa, a duk takun datayi lumshe idanunsa shi yayi na wani lokacin ,sannan ya sake budesu ahankali. mutuwar tsaye yayi a gurin " har takaraso inda yake tayi sallama.
bai dauke idanunshi "akanta ba .Sai ma cigaba da yayi" da binta da wani irin mayataccen kallo wanda yasa shemah tasha jinin jikinta.
Ganin irin duban da take masa ne yasa yayi saurin ,sauke idanunshi,tare da sakin ajiyar zuciya, ta gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska, yana sake bin koina na jikinta da kallo dan tayi masa kyau matuka ,rigar jikinta irin mai flay din nan ce daga kasa, Sai dai taka mata a samata sosai.
cikin sanyi murya tace yaya faruk Gani , Yace Ai naganki .

,yayi shr yana tunanin ta inda zai soma ,itama shr tayi Sai dai,haka kawai ta tsinci kanta da jin ,faduwar gaba. haka nan kallon da yaya faruk din kema ,yasa taji wani iri ajikinta ,dan haka ,ta sunkuyar da kanta kasa kawai tana Jira daga gareshi.
,can ya numfasa,hade da jin kwarin gwiwa yazo masa ,ya danyi gyaran murya" tukun yace daman nazo ne na fayace miki abinda na dade Ina boyewa akanki , .
Take taji gabanta yashiga faduwa ,ta dan dago kadan ,taga ita yake kallo , ahankali tace akan mefa?
Sannan ta km maida kanta kasa tana jin yadda gabanta ke lugude faduwa.
Yayi murmushi yana cigaba da kallonta, cikin natsuwa da jarumta.
yasanar mata da komai .

tun da yasoma maganar sa tayi shr kawai hade da sake sunkuyar da kanta kasa, sosai badan tana jin dadin sauraron abinda yake kokarin fahimtar daita bane ,taji hankalinta ya yayi matukar tashi dan haka , ahankali ta dago kanta , ta zuba masa idanunta , Sai data tabbatar daya gama fadar abinda yakawoshi, a dan frigice tace ,dan Allah yaya kayi hakuri wlh akwai wanda zuciyata ta dade da kamuwa da soyayyarsa , Amman kayi hakuri idan maganata ta bata maka rai ,yace Ina fa za bata min rai Ai iya gaskiyar ki kika fada Sai dai ki sani zuciyata bazata iya wannan hakuri dake bani ba, Sai dai zan baki lokaci kiyi tunani akai , tace tunanin me km zanyi?byn na fada gsky nifa bawani tunanin dazanyi ka dai yi hakuri kawai ka nemi wata.
,ta juya ta wuce tabar sa nan tsaye .
,da mamaki yabi bayanta da kallo ya dauki lokacin tsaye a gurin batare da yasan abinda zaiyi ba , Ganin tsayuwa nasa bata da wani amfani yasa yasoma kokarin daga kafafunsa da suka masa mugun nauyi.
, ahankali yake daga kafafunsa yana saka da warwara" da tunanin makomasarsa a gurinta .
,a fusace shemah tashiga part dinsu tana zuba tsaki da zage zage iri iri har mmnta ta tambayeta abinda yasameta tace mata bakomai.

Byn kwana biyu

Da misalin karfe takwas na dare fk ya km samu shemah da zance ,shi fa bai ji zai iya wani hakura daita ka " kawai tayi hakuri ta amincewa aurensa .
,tace ni dai dan Allah yaya kayi hakuri karabudani, wlh da bbu wanda nake so ne ,zan iya aurenka dan kaima baka rasa komai da zankika ba .
kadai yi hakuri kawai .

al'amarin dayayi matukar dagawa fk hankali kennan ,yayi shr kawai yana kallon yanayinta tare da nazarin kalamanta masu kokarin tarwatsa masa zuciyar rasa "
yarasa yadda zaiyi daita, can dabara tazo masa, dan haka ya tsareta da idanunshi Yace ke banso iskanci da rainin hankali fa" ni zaki cewa kina da wanda kike so byn Banga uban da kike saurara ba.
,lafazinsa yayi,
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO



Page 23-24





Ni dan girman Allah kabarni na wuce tun kafin laifina ya Karu.

,Murmushi karfin hali kawai yayi ,tare da nuna mata hanya da hannushi alamun ta wuce din.

, kasa tafiya tayi " sakamakon idanushi da taji yana mata yawo a gangar ajikinta . Gabadaya taji tamkar ya daureta ne .
takasa kwakwaran motsi" jikinta yayi bala'in yin sanyi.
,taji ina ma zuciyarta na da yanci da bata kamu da soyayyayar deeni ba.

Da bbu shakka zata iya hakura da kamil tunda shima yana da nashi kyawun daidai gwargwado .

Yayi shr kawai yana kallonta" kaunarta ce ke tasomasa tare da nukurkusan zuciyarsa.
,ya dinga jin tamkar ya halaka kanshi lokacin daya tsinci idanun deeni akan su.
ya dinga kallonta "yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa " da gske dai yana shirin yarasata kennan ,rashima na har abada.
km ta haramta ta zama matarsa wani irin zugi zuciyarsa keyi ahankali
Yakira sunanta..Zeenat kina son deeni sosai ko ? Cikin sanyi
ta dago kanunun idanunta ta kalleshi dasu "sannan tace , wannan wace irin tmby ce ? Yace amsa kawai nake bukata ,tace to bana son shi shikennan.
Karkimin karya mana Kina son shi kalli...kalli yadda yanayinki ya canza jikinki har rawa yake saboda kin ganshi .
ya tabbata kennan baki sona ,rainamin hankali kawai kika dinyi .


A fusace Zeenat tace Nifa karka zageni da laifi da bansan na aikata ba. mgnr ina sonshi ko bana sonshi ma duk bata taso ba .

kai kanka kasan bantaba amsa maka da Ina sonka ba.
ballanantana kace yaudararka nayi ka dai yi hakuri Allah ya hada kowa da rabonsa , yace ok yanzun duk tarin son da na miki yazama tarihi kennan ?
Ta zuba mishi ido kawai dan tasan duk abinda zata gaya masa ahalin yanzu ba fahinmta zai yi ba shiyasa tayi shr taki cewa komai
Ahankali Ya girgiza kanshi kawai batare da sake cewa mata komai ba ya juya yasoma tafiya.

, Tayi jim jikinta ya mata tsanyi ,bata ji dadin yadda taga reaction dinsa ba .
tasan kwata kwata bata kyautawa masa ba. Amman ba yadda taiya da zuciyarta " DEENi shine muradin ranta .
raba zuciyarta dashi tamkar barazana ce ga rayuwarta.
Duk da taji ba dadi ba hakan bai sa taji tausayinsa yashigeta har taji zata iya hakura da auren DEENi . Dan haka ko ajikinta ta wuce.

Jikinta a sanyaye yashigo part dinsu hankalinta a tashe
Tana shiga daki Ta daure fuskarta "ganin ya shigo dan a zatonta yana shigowa zai zabgamata mari.
sanye yake da t shirt din su na sojoji da wando.

Tana jinshi yacewa Ummi shi ya wuce sai da safe "Ummi tace can zaka kwana ne yau ?
yace eh "akwai abinda zai maidani tace to Allah ya tsare min kai ya km bada sa'a ,ka yawaita addu'a dan Allah yace Ina yi sai dai zan kara kulawa .
ya sake wuce zeenat zaune ko kallon inda take baiyi ba .

bayansa tabi da kallo tana jin wata irin masefaffiyar kaunarsa nabin jininta, hade da ratsa kowani part na jikinta.
, aranta tace attajirina kennan ,miskilili zaki maza .
nan ya fita yabarta da dadeden kamshinsa tare da fargaba.
sai dai, da ganin yanayinsa yana cikin tsananin fushi .

da misalin karfe tara dare tana kwance akan gado" juyi kawai take, yayinda zuciyarta ke nazari akan irin kallon da yaya deeni yayi mata, dazu sakamakon ganin da yayi mata tare da kamil .

ta ji tamkar takirashi tabashi hakuri amman tsananin tsoransa ya hanata aikata hakan , zuciyarta ce ta bata shawara kan tura masa text ba sai takirashi ba .
dan haka ahankali ta mirgina ta janyo wayar Ummi dake kan bedside .
ta soma rubuta masa text da niyar turawa masa " sai km taji zuciyata na gargadinta akan kar ta sake ta tura masa text din . Tayi tana tunanin ,ta tura ne ko ta share
Tayi haka ya yafi sau goma kafin daga karshe tayi jahadi ta tura masa .

Yaya dan Allah kayi hakuri idan na bata maka rai dazu wlh bazan sake ba ... daga zeenat


Byn ta tura sakon ne ta goge "sannan takoma ta kwanta lamo tana jin yadda kirjinta ke tsarkewa ,ahankali ta lumshe" idanunta ,xuciyarta ke beating tare da yi mata fadar abinda ta aikata .
ita kanta tasan tayi babban kuskure sosai wajen tura masa text ,dan tasha jin yadda yake yawan yi complain akan tura masa sako ko kiran wayarsa yayinda yake kan aiki ,
Sai dashi duk lokacin daya gadama zai kiraka idan km baka dauka ba yazama matsala .
dan haka tayi shr kawai tana fidda numfashi sama sama .

Tsawon lokaci tana kwance "tana tunanin abinda zai biyo baya idan yaga sakonta , addu'a take Allah yasa ba karawa kanta laifi tayi ba agurinsa .

take tsoro da fargaba suka taru suka dira mata " alokaci daya.
Idanunta a lumshe har lokacin tana saka da warwara deeni dan ra'ayi baka masa dole ballanantana ta tursashi .

can taji alamun shigowar sako a zaburi ta mike" ta rarumi wayar jikinta har rawa yake .
idanunta ne suka ci karo da reply dinsa .
hankalinta a tashe tasoma karanta text din .


Ke ... Banida lokacin karanta wannan shirmen naki na baza , aikina yana da mahimmanci a wajena banida lokacin hada aikina da zantuttukan marasa ma'ana dan haka ki kiyaye gaba ..


Tana gama karantawa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta sulale takoma ta kwanta tare da lumshe idanunta.
Tabbas tasan ta daukarwa kanta abinda yafi karfinta .
tayi shr ,tana son tayi nazari akan kalamansa tasan dai yakaranta sakonta sarai .

tsabar rainin wayo ne da miskilanci irin nasa .
yasa ya nuna kmr bai da lokacinta .
tayi juyi tana mai tausayawa kanta na nacewa auren DEENi.
yanzu Gabadaya son aurensa ya sire mata ya fita akanta.
, tsoro aurensa take km sai yanzu maganganun Ummi ke sake shigarta .
Inda tace zeenat ,kin fahimtata ne kawai deeni dana ne dana haifa a cikina.
baki fini sonshi ba sanin halin miskilancinsa da girman kai irin nasa yasa kikaga naki amincewa da aurenku wahala kawai zakisha a hannushi .
, gara yaje waje can ya nemo matarsa.

batayi aune ba taji saukar hawaye nabin kuncinta" bata hana su zubowa ba ,domin ita kanta zata fi so ta zubar dasu ,kodan samun natsuwarta.
Km ko ba komai hakan zaisa taji sanyi da ragewa kanta radadin abinda ke nukurkusan ruhinta.

Jikinta yayi matukar yin tsanyi ahankali tasoma sambatu ..
Wayo Allahna... ni zeenat yaya zanyi da zuciyata data ta makance akan kaunarka.

Ina sonka yaya deeni har bansan yadda zan misalta tarin soyayyata gareka ba.
kaunarka ajinina da ruhina yake .
daita Allah ya hallice . bazan iya daina sonka ba muddin rai .
koda baka sona ni Ina sonka km zan iya jurar komai akanka ,raba zuciyata da soyayyarka tamkar rasa numfashina ne .
Haka tayi surutai har sanda Tajiyo motsen shigowar Ummi .
tayi shr tare da saurin juya mata baya.
tana cigaba kukanta, kasa kasa batare Ummi ta Gane halin da take ciki ba .
Zuciyarta ke mata wani irin ciwo da radadi mai zafi .


Washegari ma sukusuku ta tashi tamkar wace batada lfy ta rame sosai " idanunta a kumbure kallo daya Ummi tayi mata ,ta Gane kuka tayi .
km daman tana lura daita jiya bawani baccin kirki tayi ba .
taji wani irin tausayinta ya tsarga mata har cikin zuciyarta "dan tasan tunda ta kwallafawa ranta auren DEENi , ta hadu da babban aiki .
km sai ta hadu da abinda yafi haka.a addu'a dai zata cigaba dayi musu Allah ya kauda fitana atsakaninsu.

Ahankali Ummi takira sunanta ...ta dago da kumburarun idanunta tana kallon Ummi dasu batare da tace mata komai ba byn gaisuwar datayi mata .
,Ummi tace meke damunki ne zeenat naga duk idanunki duk sun kunbura" sai naga ma kmr kuka kikayi .

Zeenat ta danyi murmushi dole sannan tace kai Ummi bbu komai fa, idanuna kemin ciwo ,km jiya da ciwon kai na kwana .
ta fadi hakan da hankalin Ummi ya kwanta .

Ummi tayi shr kusan minti goma tana kallonta sai da tagama nazarinta tsab sannan ta numfasa tace shikennan Allah ya sawake kinsha magani ?
Zeenat ta girgiza kai kawai.
Ummi tace maza ki tashi kije daki ki dauko magani kisha.
a sanyaye ta mike jikinta babu kwari tace to ...
tare da shigewa kitchen dan bataji zata iya shan wani magani a halin datake ciki yanzu ,dan tasan ko tasha bazai taba yi mata maganin damuwarta.

kusan duk dare sai bacci ya katse mata sakamakon tunanin DEENI da hali ko in kula da yake nuna mata .
, shi sam mutun ne da babu ruwanshi da wani damuwa harakar gabansa kawai yakeyi hankalinsa kwance .


tayi shr cikin zullumi irin zaman da zatayi da DEENi,a zahirin ce tagama duk wani tunani da zatayi akansa ,amman sam bata hango wani jin dadi ko kulawa da za samu aurenta dashi ba .


Sai yanzun take gane manufar Ummi" tana guje mata wahala ne yayinda ita km ta kasa fahimtar hska . gashi yanzu lokaci ya kure mata bata da daman tace ta fasa .


Misalin karfe takwas na dare .
kwance take a parlour kan doguwar kujerar three site .
hannuta rike da wayar Ummi ta juyata idanunta kuru akan TV .zaka dauka ko kallo take .
amman a hakikanin gaskiya kallo daya zaka mata ka gane Gabadaya hankali bai gurin TV .
tana can ta lula cikin duniyar tunani tunani .

, kamshin turarensa ne ya ankarar daita ,take tayi firgigib da dawo duniyar kasa dan tasan tunda Tajiyo kamshinsa yana kusa kennan dan haka ahankali ta dan juyo tsaitin datake jiyo kamshin nasa , ahankali idanunta suka cin karo da kyakkyawan fuskarsa ko kallonta inda take baiyi ba , yakarasa shigowa parlour fuskar nan tashi a daure tamkar zaki .

,take taji zuciyarta ta tsinke tasoma rawa wata irin zazzafar kaunarshi ce ta dinga taso mata tamkar ta tarwatsa mata zuciya , lokacin data daura idanunta kansa.

kamshin turarensa ya addabi hancinta ji take kmr tajita a kusa dashi .
sallama Yayi aciki.
ta amsa tare da sunkuyar da kanta kasa har ya wuceta yasoma taka step bata dago da kanta ba, sai da tabbatar da tadaina jin motsen takunsa" sannan ta dago tana sauke ajiyar zuciya tare dafe kirjinta tace wayoooo Allah kirjina .
dan ita kadai tasan yadda ta dinga ji .
can taji sautin shigowar sako a wayar Ummi " ,sharewa tayi tunaninta ko yan network ne.
Dan haka ta maida hankalinta kan shirin da'ake gabatarwa a TV.
minti biyar tsakani taji wayar ta dauki kara ta dauki wayar tana dubawa .
Wata bakuwar number tagani" yana yawo akan screen din .
Dan haka ta manna wayar a kunneta tare yin sallama .
muryar da tafi so da tsoro ne "ta daki dodon kunneta hakan yasa jikinta ya sake daukar rawa gabanta yashiga faduwa da sauri .

,yace ke dan iskanci da rainin wayo bakiga sako na bane ?
Muryarta A sanyaye tace ban gani ba Amman kayi hakuri dan Allah tsaki yaja tare da kashe wayarsa .
Da sauri tashiga in box din tasoma duba sakon

Kisame ni a dakina yanzu " abinda tagani kennan .


,take gabanta yacigaba da faduwa , duk da tana cikin fargaba hakan bai hanata ,mutunta kanta
da son janyowa kanta martabarta ta Diya mace .
Sai da ta dauki mintina tukun ta mike cikin sanyin jiki ta nufi dakin shi .
tsaye take akan kafafunta a bakin kofar dakinsa zuciyarta na dokawa .
tsoro taji yana shigarta sai ta daura hannuta kan handle din kofar .
sai tacire hannuta da sauri .
,da kyar tasamu tattaro duk wani kuzarin dake jikinta .
,karfin hali tayi wanje murda handle din kofar da iya karfinta tashiga parlour'n da sallamarta .

shr parlour bakajin komai sai karar TV tsayawa tayi tana jirashi kusan 5 minti bata ga alamunsa ba ko jin motsensa batayi ba . dan haka ta yanke shawarar shiga Bedroom dinsa.
tana shiga dakin gabanta ya tsananta faduwa , cikin sanyin murya ta sake yin sallama .ya amsa da kyar km a ciki .

Zaune taganshi yana operating system sanye cikon wando three counter da pure whit singlet , ahankali take takowa har inda yake yayinda kanta ke sunkuye .
tsugunnawa tayi a gabansa muryata na rawa tace Gani Yaya .


GA TSARABARKU TA KANO BA YAWA KUYI MANAGE 😃😃😃



MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO


Page 25- 26

Bai ko kalli inda take ba hasali ma operating din system dinsa yacigaba dayi.
" tayi kusan minti goma tsugunne a gabansa batare daya dago idanunshi ya kalleta ba .

Shr Tayi tare da" sunkuyar da kanta kasa .
Yayinda zuciyarta ke tsananta bugawa .

cikin daddaden muryarsa may cike da dadin sauraro "fiyye da komai datafi kauna .

Yace tun yaushe kike tare da wance sakaran Dana ganku shekaranjiya ?

Batasan sanda ta zauna ba ,dan tsabar frigice da tsoron daya shigeta na lokaci guda .

,zuciyarta ce tasoma rawa...rawa tare dokawa .tarasa yadda me za tace.
cikin ya'n sakanni nan hankalinta yayi matukar mugun tashi. kwakwaluwarta "tashiga tariyo mata abinda ya faru a shekaranjiya din .

gabadaya tagama
frigita da tmbyr daya jiho mata, tunaninta ya ta'alaka ne akan ya manta da abinda yagani din .
dan ganin ya share Bai nuna koda a fuskarsa ba .
da kyar ta iya bude bakita tare da son nuna masa , itama batasan inda zancesa ya nufa ba.
, muryarta cike da rudani tace wa kenan ?

Sai Lokacin ne ya dago rikitattun idanunshi ya dubeta dasu .
,tare da zabgamata wata uwar harara .
cikin sanyayyayiyar muryarsa, ta isa ya sake yin magana Yace wawa ..... .ni zaki waskewa ya nuna kirjinsa da yatsansa
bakaramin laifi zaki karawa kanki wajen nuna min bakisan abinda nake nufi ba .

Domin bana bukatar
rainin hankali ko karyata min abinda idanuna suka gane me .

Amsa tmbyta kawai nake da bukata .

take muryarta tasoma rawa alamun kuka keson kufce mata.
,ahankali ya daura yatsan hannunshi akan lip's dinshi " shiiiiiiiiiii....... karki kuskura naga Tear's dinki ko rawar murya .
dan banida bukatar su .
I said tun yaushe kuke tare , that's ol ....
A boye ya dinga sauke ajiyar zuciya sannan ya"
yacigaba ko duk dadewarku bakisan tun lokacin da kuke tare ba ?

Lokacin daya taji maganarsa na neman birkita mata Brain dinta. to up side down" wani irin rudewa da gigicewa ta sake yi .

Ba bakinta kadai ke rawa ba ,yanzu kam har gangar jikinta rawa yake .

Ta dawo tamkar wata zautacciya Da kyar tasamu ta iya hadeye abinda taji ya tsaya mata a makoshi .
tare da zubda hawayen da suka taru a idanunta, cikin rawar murya tace shekara biyu kennan.
Tana gama fadar haka
, tayi saurin sunkuyar da kanta kasa dan gudun jin saukar mari .

yayinda hawayen tausayin kanta suka cigaba da bin kuncinta.

a hankali ya dinga girgiza kanshi shekara biyu kennan ya sake maimaitawa kansa.
Cikin sanyi ya maida jikinsa" ya kwanta rigingine ya Kuma cigaba da operating din system dinsa batare da ya sake ce mata komai ba .
,Take yaji zuciyarsa ya dauki beating ,wanda yarasa dalilin jin haka .

Kusan minti shabiyar kennan idanunshi na kan system dinshi yana cigaba da aikinsa .
, wanda

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment