Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanayin jikinki ke ba ishashiyar lafiya ce dake ba sannan kinsa bayacin abincin masu aiki cikin shagwaba tace ummi to ai itama mai aikice ummi ta girgiza mata.
mai aiki ce Amman ba kmr su take ba zeenat bana jin dadin yadda ke da mijinki kuke wa yarinyar nan "da" nakowa ne fa.
ki duba kigani haihuwa kike nema sama da sheka takwas kennan kina ganin idan ke akawa taki Yar haka zakiji dadi ? zeenat ta bata fuska tace haba ummi ya zaki hada jinina da waccen mai kama da Yar sadaka yalla idanun tamkar na mayu ummi tayi murmushi Shine kawai dalilin abinda kika tsani Yar mutane .
saboda kina ganin kmr tafiki kyau , kema fa kyakkyawace km first class zeenat tawashe baki tana dariya tace ummi shiyasa kullum nake kara sonki dayawa , dayake ance kina da kyau ba, dan haka ki dan rinka sakarwa yarinyar nan fuska ko ta sake damu zeenat .
ta dai amsawa ummi ne kawai Amman ita Sam bazata iya mu'amula da masu aikin tamkar wasu yan'uwanta ba ,km ko babu komai ita dai Tayi mugun tsanar yarinyar .

Uhmmmm. nah wa oooooo madam Zeenat fear God 😍😍😍😍😍😍


MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗





AYSHA A BAGUDO





Page 68



Zaune yake rigingine a bayan mota ,direbansa Na tukasa Ahankali.

Yayinda Kirjinsa ke cunkushe dayawan tunan tunane iri iri. Wanda zuwa yanzu yasoma suspect din wani abu ne ke shirin faruwa da rayuwarsa. Wanda a hakikanin gsky bazai iya cewa ga takamaiman abinda ke son ruguza farincikinsa ba .

Kallo daya zaka masa a yan kwanakin nan tabbatar da hakan sannan ka gane sansar damuwa dake dawainiya da rayuwarsa .

zuciyarsa ke rawa da raya masa abubuwa dayawa a game da yarinyar dake zaune agidansa .

a duk sanda zuciyarsa ta motsa game daita kirjinsa ne ke wani irin bugawa da sauri .

Yayinda , tunaninsa ke yawan barin gangar jikinsa zuwa wani bagere na daban.

, don't believe what's actually happened to my hrt yarinya tamkar wata aljana ko mayya ta tsarke min kowani shashi Na zuciya da gangar jikina ,deeni ya fadi hakan akasan zuciyarsa yana may furzar da wata iska may Tumi .

Wit that thinking har suka iso gurin aikinsa zuciyarsa fal... da damuwa .
" sule direbansa ne ya fito da sauri ya bude masa kofar motar yana may Sara masa.

, DEENI Baibi takansa ba yasoma tafiya 'cikin isa da takunsa Na takama...

Duk wani abu dayakamata DEENI yayi ranar domin barinsa aiki yakamala da komai .

Sai dai he fell some how akan aikinsa da zai barin Wanda yataso da tsananin so tun ba ,yau ba .
,amman ba yadda Ya iya da rayuwarsa dole yabar komai ya,mayye gurbin kujerar dad dinsa a halin yanzu Dan shi yafi komai mahimmanci a tare dashi .

Duk abinda yake zuciyarsa Na makale da tunanin yarinyar ,Wanda yarasa dalilin jin haka. duk yadda yaso ya yakiceta a zuciyarsa hakan yagagara domin tunaninta kokari yake ya mamaye ilahirin santsar jikinsa ,what should I do now to stop thinking about her ? Ya tmbye kansa yana mai rantse idanunshi gam.

'Yana Cikin wannan tunanin ne wayar faruk ta riske shi ,tare da katse masa damuwar dake shirin zautar dashi , Ahankali ya sauke naunauyen ajiyer zuciya tare da bude idanunshi ganin sunan dake yawo kan screen din wayar yasashi hanzarta daukar wayar hade dayin sallama .

Bangaren faruk kuwa byn deeni ya amsa sallamar deeni ,yace aboki kwana biyu shr kayi Sika's ba'a ganinka ,wayarka ma Haka .
DEENI yace kai dai bari kawai wlh abubuwa ne suka sani gaba da baya ,a en kwanakin nan amman Na kamala da komai ,sai fatan alkhari kawai ,fk yace ok kana gida ne ?

Bana nan Ina gurin aiki amman xuwa anjima kadan zandawo , kazo gobe Ina son ganinka game da aikin da ,zamuyi start .fk yayi murmushi manager da kanshi kennan ..a she zaka saduda 'cikin sauki Haka .

,wlh ban dauka zaka iya barin wannan akin naka daka kwallafawa rai ba .

mtssss DEENI ya ja tsaki dan takaicin barin aikin nasa sannan yace yanzu ma kama tayi . Shiyasa da km mahimmanci dad dina dan bazai yiwu Ina kallo wahalarsa ta tashi abanza ba ,km ko bbu komai su ya Mahmood da ya sulaiman suyimin kokari sosai akan dukiyata .

Suma zuwa yanzu suna bukatar taimako. F k ya numfasa sannan yace Haka ne ,nan dai suka shiga hirar duniya .deeni yaji dadi hirar data wanzu a tsakaninsa da amininsa Dan kashe dari ta damuwarsa ta ragu.


Ummi kishingide akan kujera a hadadden parlour ,gidan yayinda safeena ke zaune kusa da ummi tana kallon zeeyword ita kuma Zeenat tana chatting a phone dinta .

DEENI yayi sallama hade da shigowa parlour kai tsaye ya nufi kujerar da ummi take zaune ya zauna kusa da ita hade da daura kansa a kafadarta yana wani narkewa sai kace karamin yaro ummi tasa hannu ta shafi sumar kansa cike da so da kulawa tace da alamun ka kwaso gajiya gashi inason zamuyi magana mai mahimmanci dakai .

take yanayin annurin fuskarsa ta dauke , Yar fara'ar daya shigo da ita ta ragu duk da Bai san takamaiman mgnr da ummi zatayi dashi ba . amman hakan Bai hanasa cewa karki damu dani, first love bana tare da wata gajiya bara nayi freshe up na dawo muyi magana ya mike tsaye fuska nan tasa a hade ba yabo ba fallasa yana tsokanar ummi da fatar maganar da zaki min may dadi ce km wacce zata sakani farinciki.
dan nasan maganar ummina duk masu mahimmanci ne da dadi sauraro yana gama fadar haka yasoma takawa ahankali cikin sanyi ya haura upstairs.

DEENI nashiga bedroom dinsa yacire kakin jikinsa ya rataye yasaka rigar wanka yashiga bathroom ya sakar jikinsa ruwa .

byn ya fito daga wanka jallabiya fara kal... ya dauko yasanya tare da feshe ilahirin jikinsa da turare may dadin kamshi sannan ya fice daga bedroom .

ummi da zeenat har safeena duk suna nan a zaune a inda yabarsu tun kafin ya zauna safeena ta sake gaidashi ta mike tabar gurin yayinda ita kuma zeenat tashige kitchen .

Shi km ya zauna yana maida hankalinsa kacokam gurin umminsa yace ummi Gani.

tace eh naganka ai sannan ta kira sunansa deeni....Ya dago rikitattun idanushi yana dubanta dasu batare da yace mata komai ba sai dai gabadaya ya tattara ilahirin hankalinsa akanta .

cikin sanyi muryarta kasa kasa ta yadda bbu mai jinta sai DEENI din .... hakika lokacin yayi da yakamata kasan abinda kake ciki domin zaman gidan nan shr ya soma gundurata.

, zeenat ta dawo parlour'n hannuta dauke da cup din coffee ta Mika masa.

wata uwar harara ya gallamata sannan yace bazaki iya ajiyawa ba ko zaki daura min akai ne ?

zeenat tayi murmushi kawai domin ita duk abinda DEENI zai mata baya damunta sai ma sake birgeta dayake karayi.
, Ahankali ta janyo karamin stole gabansa ta ajiye masa ta sannan ta juya ta koma dakinta tacigaba dayin chatting dinta ganin kmr suna bukatar abasu guri .

ummi tacigaba a dalilin haka kaso kakara aure tun ba yanzu ba ,Ga wannan yarinyar nayi bincike akanta sosai ,irin kalar yarinyar danake son ka aura ce .

ganin maganar da umminsa ta dauko ne yasa shi mikewa tsaye hade da daukar cup din coffee, din tare da sanya hannushi ya kamo na ummi yace ummi muje dakinki .

DEENI zaune a gaban umminsa yayi shr, ya hada uban tagumi kawai yana sauraron maganar ummi ahankali tace na baka iya lokacin da naga zan iya baka akan maganar yarinyar nan Amman har yanzu ka kasa aiwatar da komai muryarta tamkar maishirin zubda kwalla tace ko so kake na mutu batare danaga kwan ka adoron duniya nan ba .
gashi yarinyar nan nablah tana da hankali da natsuwa babban abinda yakara jan hankalina gareta kyakwan tarbiyya da take da ita
ta kwanta min arai matuka fiyye da tunaninka ,dan haka kabari na dangana kaina ga iyayenta kafin mutuwata ta riske Ni .

da sauri DEENI ya zaro idanu yana girgizawa ummi kai. yayinda gumi yashiga ka karyo masa takoina ajikinsa, jin abinda umminsa tace hannuwansa duka ya daura a sama fuskarsa zuciyarsa ta taru ta hade kanta waje daya ji ya ke tamkar jinin da ruwa basa gudana ajikinsa yadda yake so ..

ahankali yaciro hanky daga aljihun gaban rigar jallabiyarsa yana goge gumin dake tsaftsafo masa .

ummi ta sake kiran sunansa DEENI ...ya amsa na'am first love idan kasan bakada abinyi da yarinyar nan kasanar dani na sallameta, taka gabanta.

Tun lokacin da ummi tafara magana deeni yake kallonta har sanda yaji tayi shr da zancenta. Jin abinda tace ne yanzu yasashi danyi murmushin gefen baki ,Wanda yafi kama Dana takaici .

muryasa kasa kasa tamkar may shirin yin rada yace ummi kina nufin auren yarinyar nan zanyi kennan?

Kwarai kuwa saboda nagaji da ganinka haka domin bansan har wani tsawon lokacin zaka dauka kafin burina yacika ba , duk sa'annin aurenka bbu wanda baida "dan" kansa, akwai mai uku mai duhu acikinsu .
tagama fadar haka ta xuba masa ido kawai tana nazarinsa sosai.
yayi shr Bai sake cewa komai ba , Amman kasan tun farko sai daka amince da yadda Na tsara kafin a kawota ?

ya daga mata kai tace to meyasa yanzu kake son min yawo da hankali kodan kaga a bukace nake da son ganin guda jininka shine ka maida zance Na wasa ?

ya hadiye abinda ya tsaya masa a makoshinsa yakamo tafin hannuta 'cikin nasa yace kiyi hakuri first love kin wuce wasa awajena duk duniya banida tamkar ki kece duniyata , na rokeki kada kiyi fushi dani.
,bacin ranki bakaramin babban tashin hankali bane atare dani.
,ya numfasa sannan yacigaba Dan girman Allah kiyi hakuri ki sallameta kawai Dan banji zan iya aurenta yarinyar nan ba.
saboda banasonta ban jin akwai halitar dana tsana kmr ta.tun zuwanta gidan first love narasa natsuwata Ni kaina ban san dalilin dayasa Na amince da zamanta a gidan nan ba.

,ummi ta hade fuska sosai tace sakar min hannu cikin sanyi jiki yasoma sakar mata hannuta kmr yadda tace .

Ummi ta xuba masa ido kawai tana dubansa Dan takaicin abinda yace , numfashi taja ta fitar sannan tace son Na lura so kake ka bata min lokaci, Amman kasan ba dole nayi maka ba tun farko kaine da kanka ka bukaci kara aure.

,km yan aiki nawa aka kawo gidan kafin ita kace basu maka ba.

da kanka ka amince da zaman yarinyar a gidan fa sannan yanzu zakace ga zance Ga mgn .amman bbu komai haka Allah yaso dani daman can bazanga jininka ina raye ba, takarasa mgnr 'tamkar mai shirin zubda sakin kwalla.

muryasa a sanyaye haba first love karkice haka ma akwai hanyoyin da dama daza mubi gurin cimma burinmu ba lallai sai ta hanyar auren yarinyar ba.
,taya za'ace kamata da matsayina da komai Na bige da auren kaskantacciya irinta . Ai da auren wlh nahakura Dana cigaba da zama da Zeenat haka koda bazamu taba haihu ba .

A fusace ummi ta katseshi ta hanyar daga masa hannu sannan tace angaya maka sbd jin dadi ne kawai , nake son kayiwa diyata kishiyar boye ,uhm kasani badan haka bane ,kai kanka kasan dalilina zanyi aikata hakan ne kawai a dalilin farincikin diyarta

Dan haka idan kai zaka iya hakura da kowani irin auren Ni bazan zauna ba ,nan gaba diyarta tashiga tashin hankali akan rashin haihuwa ba .

Ok first love yanzu abinda za'a yi ya, sunkuyar da kansa kasa sosai saboda jin kunyar abinda zai ce. cikin wata irin raunanniyyar murya yace first love me zai hana tacigaba da zama agidan a matsayin mamata kawai batare da an daura aure tsakaninmu ba.


ummi ta tsare shi da idanunta 'tana kallonsa dashi sannan tana mamaki jin furucinsa . tamkar wani mai tabin hankali . Ahankali ta dinga aiyana
kode dan nata yasoma shayeshaye ne batare da sanin ba.

"inda wani ne yatareta da wannan banzan mgnr da deeni yasanar mata da bakinshi ,to wlh da kotu ce zata rabata da duk Wanda ya fada mata hakan. Amman sai gashi, da kansa yake kokarin fayace mata ya gwammaci aikata lafin zina akan , yayi auren sunna da yarinyar .

Gumi yakaryowa ummi ta mike tsaye tana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun ...'tana
ta sake kallonshi da jin takaici acikin ranta .

ganin irin kallon da umminsa ke jifanshi dashi ne yasashi shan jinin jikinsa tare da sanin ya tafka babban kuskure daya sake ya fada mata irin wannan mgnr.

Duke kansa yake a kasa yana ladamar abinda ya fadawa ummi Wanda har Ga Allah ba nufinsa shi kennan ba" shi dai yafada ne kawai Dan yarasa yadda zaiyi da ummi .

Tsawon lokaci ,ummi Na tsaye 'tana binsa da kallon mamaki kana tace wlh azim DEENI you really gave me double surprise .
sannan km bani kunya daman can abinda ka ke aikatawa da yaran mutane a gari kennan....bansani ba?

shine Dan rashin tsoron Allah yanzu kake kokarin ka fahimtar dani halin ka na boye.

Da sauri DEENI ya dago yana kallon ummi da rikitattun idanushi dasuka gama rikewa suka dawo jawur tare da matso kusa da ummi sosai, yana may girgiza mata kanshi tamkar wani karamin yaro.


Ummi tasa hannu ta dakatar dashi .. kar ka kuskura kakaraso gareni deeni fatana Allah Ya shirya min kai shirin addinin Muslinci first love Dan Allah kiyi hakuri wlh ba hali bane nida katashi kabar min dakina kawai bana son ganinka a halin yanzu.

ayau naji kunyar kasancewata uwa agareka ,deeni ban dauka haka zuciyarka ta gurbace ba mayagun laifuka ba .
Kullun nake yabonka 'cikin kawayena da dangina .
,dana kimtsasaine kamule may daraja a 'cikin al,umma ashe bansani ba yaudarar zuciyata da mutane kawai nakeyi da kyawawan halinka .

Deeni bai daddara da kashedin umminsa garesa ba .
" yacigaba da karaso inda ummi take yace dan Allah first love ki yarda dani karki min mummunar fahimta wlh bantaba aikata makamanci abinda na fada ba, baya ga mamata ta sunna. Amman Ina neman afuwarki game da abinda nace.

ummi ta sauke ajiyar zuciya Ahankali 'tana godiya ga Allah duk tasan ba halinsa bane .Dan Tasha jin yadda mutane da dama suke yabonsa akan kyawawan halinsa duk .
tasan irin kalar tarbiyar da tabawa "dan" nata.sake sauke ajiyar zuciya Tayi ,Dan tasan ba'a shedar Dan ,yau .

Ya kamo tafin hannuta wannan karon bata hanashi ba ,ya sake cewa Dan girman Allah first kiyi hakuri nayi nadamar fadar haka kinji .Ya fadi hakan yana langwabar da kansa ,alamun Tayi hakuri.

hakan da yayi ne Yasa taji tausayinsa aranta yana sonta baya son ganinta 'cikin fushi da rashin hankali Dan haka ummi tace to Shikenan naji Allah Ya sake Kare min kai .
Take , yaji hankalinsa ya kwanta yayinda jijiyoyin jikinsa da suka tsaya cak suka daina aiki na w wuncin gafi suka cigaba aiki tare da sauke ajiyar zuciya.
Sannan ya numfasa tare da juyowa yasa hannu ya dauki cup coffee ya soma kurba Ahankali ahankali .
muryar ummi yaji yanzu km sai maganar auren ko Dan gaskiya yarinyar 'tana abubuwa masu mahimmanci dazai sa a hada zuri'a daita .

A frigice DEENI yazaro idannu waje coffee daya kurba bai san lokacin daya hadiye da karfi ba.
" ai ko ya sarke shi take yafara Tari kmr ransa zai fita ummi sai faman sannu take jero masa da kyar aka samu tarin ya tsaya ya dago rikitattun idanunshi da suka gama canza kala ya saukesu bisa fuskar umminsa .

yanzu ummi bazata rabashi da zance auren yarinyar nan ba ya fadi haka a kasan ransa yayi shr can kuma yafara magana ahankali yace ummi duk wayannan ababen da kika lisafa akan yarinyar nan nifa ba ko daya da yayi min bawai na kushe zabinki bane " Amman zan aureta da zumar samun ya'ya daga gareta.
Dan a halin yanzu gara na zauna da zeenat kadai na karasa rayuwata daita , yakarasa fadar kmr zai yi kuka .

ummi ta gyra zamanta ta riko hannushi tana sauke numfashi ka amince aje ga iyayenta kennan ?
muryasa a sukwane yace uhm Na amince zan aureta Amman ba Sai kinje da kanki nemar min AUREN SIRRI ba... da kaina zandangana Ga iyayenta tunda oready kina da address din gidansu .

Yacigaba a gsky first love zan dai aureta yarinyar ne kawai badan Ina so ba Sai Dan farincikinki .
km taza zauna matsayin matata sannan ta haifa miki yaran da kike kwadayi samu daga gareta batare da ita kanta tasan da zaman nine mijinta ba Dan sanin nine mijinta zai sa naji some how..'yana gama furta haka yayi Mike yayi waje ranshi a bace zuciyarsa tamkar zata tarwatse tsabar takaici ,ummi tabi bayansa da kallo sarai taji yace a karshe sai dai bata fuskanci inda maganarsa ta dosa ba ta numfasa abinda yake nufi shiyasani damuwarta daya ce ya amince mata da auren yarinyar tunda ya amince ,mgn takare .







MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO




*Assalamu alaikum warahmatul Allah Ina wa duk masoya wannan labari Na auren sirri fatan alkhari .yayinda duk wani korafe korafenku yake isowa gareni kai tsaye batare da bata lokaci ba say day yana da kyau mu kula mu gane wani abu shi manufar rubuta labari karan kanshi ba wai dan nishatarwa bane da biyyyewa son ranmu . Muna yi ne dan fadakarwa da wa,azantarwa Ga al,ummu ta hanyar da mutun zai samu damar ya gyara kuskurensa .da km Wanda yake da akidar aikata mummunar aiki nasan dawaya masu kawo korafinsu masoya bagudo ne, domin kuwa kaunace Silar damuwarku har takai ga korafinku ya iso har inda nake .bazan iya misalta muku tarin kaunata gareku ba. amman ina son Kusan wani abu kuna 'cikin zuciyar bagudo . Bagudo ni'feyi ju km inshallahu Muna taren tare har abada*🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻


Page 69



Kai tsaye dakinsa ya nufa ya fada kan royal bed dinshi ya kwanta flat yana fidda numfashi ahankali. yayinda , kyawawan idanunshi suka gama rikidewa tamkar garwashi tsabar tashin hankali dayake ciki.
why ...why ummi why did you want's to do this to me?
,meyasa zakiyi min Haka ummi ?
Meyasa kike kokarin son cusawa zuciyarta abinda bata so ?

,bana son yarinyar nan , Bana kaunar ganinta asalima Na tsani kusancina daita domin hakan na jifani 'cikin tsananin tunani da rasa natsuwata.
" bazan iya bijere miki ba ummi ,to meyasa kike so ki tursasani yin AUREN SIRRI da kaskantacciya macce?

tsawon lokaci ya dauka yana kwance idanunshi na kallon celing dakin gabadaya tunaninsa a halin yanzu ya ta,allaka ne akan abinda ummi take son ya aikata .
,yana son umminsa bayason abinda zai disashe farincikinta ballanantana har yakai shi Ga bijirewa
umarnita.bacin ran umminsa ,babban tashin hankalisa ne,a gareshi bancin haka da Babu abinda zai kaishi auran wannan yarinyar may idanuwa tamkar Na mage .
" mtssss yaja tsaki a ranshi Dan duk wannan zance dayake yi yana yinsa ne a zuci .

ahankali ya runtse rikitattun idanunshi banda yana jin bacci Sai Dan yana bukatar maido da natsuwatsa dake kokarin barin gangar jikinsa .



Bangaren nablah kuwa gabadaya duk wata surar dake jikinta ta sauya , ta murje ta sake yin kyau daita Sai dai walwalarta da kuzarinta sunka ragu.
sakamakon matsi da takurar da Zeenat din ke yawan yi mata, Wanda ita kanta tarasa dalilin hakan .
km kwata kwata bata dauki takurar da Zeenat din kemata amatsayin wani aibu ba .

Baya ga tunaninta Haka wasu daga 'cikin masu arziki da manyan masu hannu da shuni sukeyiwa marasa shi km marasa galihu irinta .

Duk da yawan takurar da Zeenat din ke mata hakan bai hanata samun farinciki da walwala daga gurinsu laraba da safeena ba . Dan haka ta tattara Zeenat takurarta ta watsar a gefe tacigaba da abinda yakawota iyakarta daita aiki Wanda tasan dolenta ne Tayi shi Dan abinda tazo yi kennan .


Ranar Saturday ' nablah na zaune ita da safeena a main parlour din gidan sanye take 'cikin doguwar rigar material may ratsin pink and popul yayinda jikinta ke rufe da dan karamin hijab kmr koda yaushe.

babu kwaliyar komai a fuskarta kasancewarta ba ma,aboyaciyar son kwalliya bace da kalekalen zamani, sai Dan Whit lip's din data shafawa lebenta.

,rashin kwalliyarta bai hana ainihin sihirtaccen kyawunta fitowa ba.haka ma kayataccen fatar jikinta choculate colour ta kwance luf. luf..koda take sanye 'cikin ' hijab kyawunta bai boyuwa ba..
Sai dai fuskarta Tayi fayau ..wanda ya nuna alamun rama atattare daita km hakan ya sake fidda asalin siffar halittata kyawun jikinta .

Yayinda kallo daya zakayi mata kaji farar daya tashiga ranka Wanda dama tun asali Haka yanayinta yake 'tana da saurin shiga rai duk Wanda ya daura idanushi kanta , da wuya kangata kaji bata tashiga ranka ba .

bbu kowa a gidan daga ita Sai safeena shiyasa ma ta samu dama ta dan sake ta zauna a parlour Dan bata manta gargadin da matar gidan Tayi mata ba .


Ahankali suke hirarsu 'cikin harshen turanci ita da safeena 'gefe daya km hankalinsu nakan TV .


Salamarsa ce da wani wanda batasan ko waye ba ,ta doki dodon kunneta Wanda hakan yayi daidai da faduwar da gaban yayi , Wanda km tarasa dalili .
dan Kusan duk sanda zata gansa ko

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment