Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kana son yarinyar" bancin haka daga baka shawarar , meye naka na damuwa daita .
DEENi bai san sanda ya dunkule hannushi" zai kaiwa fk naushi a baki ba.
Take fk ya goce yana kallonsa gabadaya yanayinsa yagama canzawa sai huci yake kmr mayuncin zaki .
Fk yace wai meke samunka ne ?
kodai kasha wani abu ne yau , a fusace DEENi yace wuta nasha ba wani abu .
Sai daya furzar da huci mai zafi sannan yace kasan Allah sai dai kasan yadda zakayi da tashin hankali daka jefani ciki .

fk yace idan ba haka ba Kuma fa "DEENi Yayi kyacci yace I will finish you.... ya wuce fuuuuuu kmr wani zaki .fk yabi bayansa da sauri yana kiran sunanshi yayi banza dashi yacigaba da tafiyarsa da sassarfa har yacimasa ya ruko hannushi "da sauri DEENi ya juyo, ya bige masa hannu " fk yace haba DEENi meyasa kake daukar komai da zafi ? DEENi yace da fetir ne kasan Allah idan har kana son zaman lafiyarka dani " wlh ka nemo solution ya wuce nan yabashi .


Cikin tsanyi jiki zeenat ta mike tsaye byn taci kukanta ta koshi . bathroom tashiga ta wanke fuskarta tukun sannan ta fito' ta murda handle din kofar ' daidai lokacin da shemah ta mike tsaye itama " tasa byn hannuta tana goge fuskarta " yayinda wasu ke sake silalowa" wani irin kallon zeenat ke binta dashi ,kmr takasheta haka take ji wanda kallo daya shemah tayi mata "tarasa dalilin dayasa zeenat ke mata irin wannan kallon haka .

Zeenat tace munafuka ashe zuwan dakike mana gidan" ba dan Allah kikeyi ba.
Shemah tace lfyr kuwa , bangane nufinki ba.

zeenat tace zaki gane manufakar banza kawai daga karki sake shigo mana gida tunda kinada manufarki ta zuwa .

jin haka yayi mugun hassala shemah, gashi daman tana tare da haushin abinda DEENi Yayi mata , hannuta tacire ta dauke zeenat da wani mari wanda ya frigita zeenat .
ai kafin ta sauke hannun zeenat bata tsaya wata wata ba" ta damki makonshi shemah tace ni kika mara.. kika mareni daga bazaki sake marin wata ba ,wani irin nishi shemah ke fitarwa tana mutsu mutsun kwatar kanta har hawayen wahala take fitarwa ,zeenat tace ba kukan soyayya kikeyi ba zan aikaki abarzahu inyaso kya ji dadi yin kukan da tushe .
Km still tana damke da makoshinta " tace nufinki kice kina son yaya DEENi ko .

Wlh yarinya karyar tasha karya " da kyar shemah tasamu tasa iya karfinta ta kwace kanta daga rikon da zeenat ta mata .
Take suka suma kwokuwa da juna gabadaya hayaniryasu ta cika gidan ,a tsorace ummi takaraso gurinsu ta shiga tsakanin" zeenat da shemah wacce har shedewa take saboda kukan dayaci karfinta gabadayansu fuskarsu tayi jazir,.
zeenat na kuka shemah na kuka cikin fushi da bacin rai ummi ke tambayar su abinda ya hadasu fada amman cikin bbu wanda yabata amsa har sanda " DEENi yashigo gidan ya samesu tsaye cirko cirko , yaja ya tsaya yana jan tsaki dan tun shigowarsa yake jin hayaniryasu yanzu ma ganin ummi ne yasa ya tsaya , da kallo yabisu dashi " ummi na ganinsa tace yauwa gara ma daka shigo , ta sanar masa abinda faru ummi nagama fada masa takama gabanta .

ai yana gama jin abinda umminsa tace ya fara dauke zeenat da wani mahaukacin ,mari dayasa taji dan guntun fitsarin dake makale da mararta zubowa , itama shemah bata nata sannan ya gwara kansu gabadaya waje daya jikake gum....... Bbu wacce tayi kokarin yin kuka cikinsu dan sunan halinsa sarai bakaramin aikinsa bane ya hada musu da punishment.

tsawa ya daka musu yace kowace ta takama gabanta tun bai sabauta musu jiki ba , hade da cewa yan iskan yaran kawai .

Dakinsa ya wuce yasoma zariya daga farkon daki zuwa karshe hannuwansa duka yasa yana balbale botura rigarsa" wani irin zafi yake ji a zuciyarsa tamkar ana zuba masa barkono , gumi ke tsatsafo masa takoina kmr ba dazu yayi wanka ba " sai daya balle botura rigar ya cire yayi jifa daita ya fada kan bed idanunshi na kallon sama celling dakin ahankali .
Ahankali yasoma runtse idanunshi har ya rufesu ruf gabadaya tunani mafuta kawai yake tabbas indai sai ya tunkari yarinyar nan da sunan yana sonta to wlh ya hakura daita har abada kai auran ma yafasa gabadaya .


MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO



Page 15-16


Tare zeenat suka jero da shemah" suna kuka saboda marin da yaya DEENi yayi musu yashigi kowannesu" amman hakan bai hana zeenat aikawa shemah da zagi iri iri ba" har suka karaso parlour" inda ummi ke zaune tayi xuru ...hade da zubawa sarautar Allah ido abin ya faru Yayi maseefar girgiza zuciyarta . kirasu ummi tayi tana sake tambayar su" abinda ya hada su fada haka" alhalin da can ba haka sukeyi ba,.
shemah ce tasoma magana cikin kuka Allah ummi ni bansan nayi mata wanj abu ba" kawai ganinta nayi tafito daga daki" tana wasu abubuwa ,daga nan Kuma sai ta hau ni da zagi ,.
zeenat zatayi magana ummi "ta katseta tace ya isa banson jin komai daga bakinki .
dan ta fara zargin wani abu dangane da abinda ya faru yanzu " ummi tayi musu fada sosai da nasiha mai ratsa jiki .
tace karta sake ganin sunyi fada da juna , shemah ce kawai ta iya amsawa tayi wa Ummi sallama ta wuce Amman it's zeenat kishi tattare da kunar zuci suka taru suka tsaya mata a kirjinta hakan yasa takasa cewa komai .

Ko byn fitar shemah ma "zeenat tsaye tayi tacigaba da kukanta tana jin haushin ummi data hanata yin magana ,alhalin gaskiya tana Gani .
yatsun DEENI ne kwance a gefen fuskarta wanda ya haddasa wajen dan tasawa , dan gabadaya fuskarta ta canza kala tayi jazir ".
tun Ummi naji haushin kukanta nata har ta dawo tausaya mata dan tasan , ta daukar kanta wahala ne in dai akan DEENi ne .
Ummi na kallon yatsun DEENi kwance a fuskarta take taji wani abu ya tsarga mata " har cikin zuciyarta taji kmr ta zubda hawayen takaici kiran sunanta tayi hade da nuna mata guri zama kusa daita.
cikin sanyi jiki zeenat ke daga kafafunta inda take tsaye har ta isa inda Ummi ke zaune ta zauna "kmr yadda ummi ta umarceta ,

Ummi ta zuba mata idanu kawai tana kallonta dan abun nata na neman fin karfinta "tsawon lokacin zeenat tana risgar kukanta ,batare da ummi tace mata komai ba ,
sai da ummi ta gama nazarinta tsab sannan tace duk wannan kukan na meye haka ?

Kar kice min duk akan son DEENI kike neman yin fada da er'uwarki . Saboda Allah Ke ko kunya abinda kika aikata baki ji ba .
" zeenat tayi shr takasa cewa komai dan ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta, .
Ummi tace meyasa zeenat , meyasa bakya jin maganata ne ,irin abinda zaki min kennan ko wannan shine kalar tarbiyar dana baki uhmm ?
kina ganin haka kawai zanki amincewa da auranki da DEENI " kiyi tunanin mana .
koda yake baki san ciwon kanki ba shiyasa.
' ballanantana" kisan gata neke miki .

mutumin da bai san da zamanki ba, bai damu dake ba" ko kallon arziki baki isheshi ba" shine zaki zauna kina westing din hawayenki akansa takarasa fadar maganar tana takaicin zeenat,.
" Ummi ta sake maida dubanta sosai gareta tana mamakin yadda zeenat din ta canza cikin lokacin kadan . Alhalin ita duk iya lokacin ta dauka tare da yarinyar bata taba ganin irin haka atattare daita ba
cikin kuka zeenat tace ummi kinki amincewa da aurenmu yaya DEENi .
ai gashi nan ai ...... sai km tayi shr" dan jin kunyar abinda take kokarin son fadi "dan haka tacigaba da sheshekar kukanta,.

" Ummi tace uhm Ina jinki kikarasa mana , tace wlh wlh idan kika kuskura" kika bari yasan kina wannan" haukar akansa " kin shiga uku da wulakanciinsa " .

zeenat ta zube nan kasa tana kuka hade da kamo kafafun Ummi .
tace dan Allah Ummi ki Amince da maganar yaya kinji "wlh ni Ina sonshi a haka " kiyi mana addu'a kawai" bbu abinda zai faru inshallahu .
Ummi ta sake zuba mata idanun tana kallon sarautar Allah, da rashin kunya irin ta Zeenat , su fa daman yayan zamanin nan ba wata kunyace ta ishe su ba .

,ummi tace" da bai ce yana sonki ba fa ?
Ta jeho mata tmyr " data girgiza zuciyar Zeenat " din" tayi kasa da kanta tana zubda kwalla ita fa ganinta bbu abinda tayi .
a ranta ko cewa tayi ai shima yana sona tunda ya iya furtawa .

Ummi ta sake kiran sunanta tace zeenat idan bakiji kunyata" ta matsayina ta mahaifiyarki ba " ,
Ai kya ji kunyata ta ummin DEENI .
amman tunda kin nacewa auren DEENi km kinji" kin Gani to wlh duk abinda kika Gani Shikenan , .
da ma sharadi kozan amince da auranki dashi .
Banda zuwa kawo kara kum duk abinda yabiyo baya babu ruwana ciki sai dai ki haye abinki tunda shi kika zaba .
da sauri zeenat tace to....ummin indai kin amince bbu ma abinda zai faru sai alkhari .
Wani irin kallo Ummi tabita dashi wanda da Gani kasan na tausayi ne.
Dan yanzu ta daina mamakin duk abinda zatayi .
da murna ta tashi ta koma bedroom tayi kwanciyarta tana jin dadi Ummi ta amince da aurenta da yaya DEENi . idanunta ta lumshe" tana jin Yadda soyayyar DEENi ke sake huda zuciyarta .

Yinin ranar da murna zeenat tayi shi cike da tsantsar farinciki ga tarin tunanin DEENi dake sake mamaye kowane part na jikinta yau tazo mata da abubuwa masu yawa bacin rai da farinciki .
duk abinda takeyi Ummi na hankalce daita . kallonta kawai take tana binta da idanu .

Washegari zeenat" ta zaci ummi zata sanarwa yaya DEENi cewa ta amince" sai kurum taji ummi ta share da zance gabadaya , koda dai da wuri yake fita ,.

wasa wasa ummin ta share da maganar kwata kwata garakar gabanta kawai take , .
tana jin lokacin da dama idan yaya DEENi ya dauko mata maganar zata katse shi tace kar ya dameta ya rabu daita .

sai dai abun yana damun zeenat matuka yadda kullum yaya DEENi ke sake daure mata fuska da wulakanci iri iri. Amman takan masa uziri ganinta killa sai lokacin da ummi ta amince masa ' sannan zai daina nuna ko in kula dayake ,mata.

shi kansa yaya DEENi baisan cewar zeenat din tasan da zance ba. kullum dai ya shigo wajen ummi sai yayi mata nacin ,shifa yana nan yana Jirata.
ita km tace kar ya dameta bayace yafi son Yar jami'a ba .
"to yaje ya nema Amman ita sam bazata bashi diyarta ba , .

yana fita zeenat ta matso sosai kusa da ummi tace ummi dan Allah bakince ,kin hakura ki amince tunda na yarda ba .

sai ummi ta dube tana watsa mata harara tace sakariya bazan kawai".
kalli fa ko kallo arziki baki isheshi ba .Amman duk kinbi jin tsamgwami kanki .dan fitina tsiya da jaraba , .
ni duk abinda nake Ina yi ne "dan Kare matuncinki , ba dan Ina kin aurenki da DEENi bane .


tunda yashiga dakinsa bai sake fitowa ba" sai dai yatashi" yayi sallah kawai yakoma gado .
yasawa ranshi, cewa ya hakura daita kwata kwata dan baiga dalilin da zai sa shi ya dinga batawa kansa lokaci ba .



Kwance yake akan makeken royal bed dinshi ya rufe kanshi cikin alky blanket mai matukar taushi ,.
bacci yake Sosai hankalinsa kwance ya rufe koina na jikinsa banda fuskarsa saboda yanayin unguwar su mai dauke da sanyin ni'ima ,.

ahankali ta bude Kofar dakin" kwance ta ganshi, yana sharar baccinsa ,sai yanzu hankalinta ya kwanta gangar jikinta yasamu natsuwa , kusan kwana biyu kennnn rabon data sashi a idanunta,.

ahankali take daga kafafunta har ta isa inda yake,. kwance
idanunta ta zuba masa" tana kare ma kwakkywan fuskasa kallo yadda tayi kyau tana fidda annuri na musamman .
Ahankali ta lumshe idanunta " tana jin wani irin tsanyi nabi jijiyoyon jikinta.
Ahankali ta bude idannuta suka sake sauka akan beautiful face dinshi ,.
fuskarsa ta kurawa ido har wani kyalli kyallin kyauwu take fitarwa , cikin rawar hannu takai hannuta gefen fuskasa ta dan tashafo . wani irin taushi taji wanda ya sake dulmiyar daita a duniyar kaunarsa .
Take taji koina na jikinta ya mutu sai wani yammmmuu take ji.
ita kanta tarasa dalilin dayasa take jin haka ajikinta .
ganin bacci yake sosai yasa ta juya ahankali tabar dakin cike da shaukin soyayyar DEENi dama Ummi ce "tace ta dubashi dan har lokacin fitarsa aiki na neman wuce .

Koda ta sanar da Ummi cewar bacci yake har yanzu, yasa ummi ta nufi dakin" dakanta kusa dashi taje" kai DEENI sai data kira sunanshi" kusan sau biyu" sannan ya dan bude gengerous eyes dinshi ya kalleta dashi "tace lafiyarka da har yanzu dabaka tashi ba , .
tacikin blanket din ya dan yi Mika hade da salati sannna ya dan gyara kwanciyarsa yace lfy first lov ,natashi har nayi sallah " to bazaka aiki bane yace zani.

Ummi tace Ina jiranka idan kagama.
ya amsa mata da kai kawai .
a hankali ya zame jikinsa daga cikin blanket din , daga sai dan gareni wando Mika ya sake yi yasa hannunsa ya gyara jijiyarsa dake mike .
Sannan ya shiga bathroom,.
duk da yamakara hakan bai sashin yin sauri ba, wanda normally haka yake da sanyi jiki .
wanka yayi, ya fito. ya shirya cikin kakinsa da suka dace da surar jikinsa, har ya murda handle din kofar "dazata Kai shi parlour ya tuna Yayi mantuwar wasu files a dakin baccins" dan haka yakoma ciki daukowa .

Tsaye take a bakin kofar dakinsa tafi kusan minti biyar a wajen tana saka dawarwara yadda zata sake shiga Bedroom din sa.
ummi ce tasake aikota .
Ta dubashi dan taji shr har yanzu .
tana son tayi nocking Amman tsoro da fargabane suka hanata .
daidai wannan lokacin DEENI ke shirin fitowa daga part dinsa . ta daura hannuta kan handle din kofar.
ai agigice cikin matsanancin tsoro tasaki wani irin kara da tasa DEENI , tushe kunnuwanshi " da duka hannushi "ai batasan sanda ta fada saman fadaden kirjinsa ba .
hade da runtse idanunta gam dan tsabar jin tsoro , batasa abinda zai mata ba Jira kawai take taji saukar mari dan gabadaya tagama frigicewa.
Amman abin mamaki sai taji sabanin haka.s shiyasa tasaki jiki ta sake narkewa a fadadden kirjinsa tana shakar dadeden kamshin turarenn jikinsa mai birkita mata tunani "a duk sanda ta Shaka .

wani irin ya dinga ji ajikinsa, yrrrrrrrrrrrrr.... yrrrrrrrrrrrrr abinda bai taba faruwa dashi ba kennan" jikinsa ya hadu da wata macce" shi tunda yake ma ko hannun macce bai ta ba rikewa ba ballanantana yakai ga hada jiki .
Ya dinga jin wani irin wani irin a gangar ajikinsa.
gabadaya tsigar jikinsa suka mike tsaye , yaji da zai iya " rungume zai yi kawai zaiyi .
ko zai ragewa zuciyarsa radadi da ciwon dayake ji.
Amman Ina... Sam bazai taba iya aikata hakan ba .
ganin yadda tayi lamo ajikinsa ne yasa, cikin takaici ya bambareta daga kirjinsa cikin tsanyi jiki,
tsayuwa ce ta gareta , zuciyarta ke neman tarwatse tsabar tsoro da rikincin data tsinci kanta ciki.
,ko ta kanta bai bi ba ya tsuke fuska yana kallonta ,itama idannuta ta zuba masa ko kiftawa batayi.
ga wani irin tsoransa dake lugudar zuciyarta.

ahankali muryasa a sanyaye yace malama ki daina min "irin wannan kallon na munafurci .
in ba haka na kwakule idanun rashin kunya tsaki yaja hade da bin gefenta yazagayeta ya wuce kai tsaye part din umminsa yashiga" sai dai bai ganta ba,.
dan haka ya wuce main parlour 'dan yasan tunda bata dakinta, tana can .

zaune yasameta tana yin breakfast fuskarsa a dan sake yakarasa har kusa daita ya zauna yace gud morning my first lov, ta dubeshi fuskarta dauke da murmushi tace morning dear ,kata tashi lfy girarsa ya dage mata.

cikin tsnayin jiki zeenat takaraso wajen, kallo daya DEENi Yayi mata yasa ta canza hanya batare da ta sake kallonsa , kan wasu kujeru dake ajiye a gefe ummi tabishi da kallo batare da tace masa komai ba " da kanta tayi savice , din shi ,shi km sai wani zuba mata shawaba yake , .
coffee kawai ya iya yasha, ya mike tsaye cikin hanzari sakamakon wayarsa data dauki kara yana dubawa yaga ogansa ne daga wajen aiki .
dan haka yayiwa umminsa sallama da hannushi ya fice wayar manne da kunnenshi .

Zeenat data zuba tagumi ,Da hannu biyu tabi bayansa da kallo har yabar gurin idanunta na kansa , itama ummi data dauke idanunta daga kan DEENI "zuru tayi tana kallon Zeenat din , tana girgiza kanta .
waskewa zeenat tayi hade da sakarwa ummi murmushin dole ummi tayi mata dakuwa da hannu .


Byn DEENi ya gama amsa wayar oganshi ne yana zaune cikin mota wayar fk yashigo " yasa hannu ya dauki wayar ya duba ganin fk ne yasa ya maida wayar ,mazauninta .
Yakirasa yafi sau gomasha daya Amman yaki pic sai a karo na shabiyu ne ya danna wani abu "sai ga muryar fk radau yakarade koina a motar , hello.... hello DEENi kana jina ....
Yayi shr yaki yin magana,sai ma cigaba da yayi " da direving dinshi .
fk yace haba DEENi ya kana jin zaka min shr. "duk fa" maganar bata kai haka.
afusace DEENi ya katse shi yace maganar tafi haka har ta zarce haka a waje na.
km wlh wlh karka kuskura, ka tako inda nake da sunan kasan ni ai bansa cewar da kungurumin ,dan iska nake zaune ba.
fk yayi murmushi yace Allah dai ya huci zuciyarka ,dan shi.
bai fiyye fushi ba" kwata kwata ma bayason duk wani abinda zai kawo masa tashin hankali .
dan haka yayi tabawa DEENi hakuri hade da bashi baki .
DEENi yaja numfashi ya sauke ajiyar zuciya . hakan yasa fk ya gane cewar ya sauko kennan fk yace to yanzu yazamuyi da maganar da big dady yace.
DEENi ya tabe baki yace ya dai zakayi dan ni tuni na hakura da wannan yarinyar , karma ka km yimin wannan bazar zance.
daidai da yakaraso wajen aiki ,ya katse wayar fk batare daya tsaya ji mai fk din zai km ce masa ba .



MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO



Page 17-18


Wata daya kennan fk yaji "shiru DEENi bai km yimasa zance maganarsa da Zeenat ba musamman" yazo gurinsa dan zance daman Kuma sun dade basu ga juna ba" sai dai sukan yi waya lokaci zuwa , lokaci dama ya kirashi a waya cewa yana nan zuwa .


Byn sun gaisa fk yace friend har yanzu ban sake jin batunka da yarinyar nan ba .
deeni ya gyara zama ,hade da yaja tsaki sannan ya lumshe idanunsa dan takaici da Haushi maganar .
ya zubawa fk ido yana kallonsa kawai domin rasa me zaice masa Yayi ,tsawon lokacin suna zaune a haka sannan fk yace friend hakuri zakayi dan Allah ba wai Ina son dawo maka da hannun agogo baya bane .

Amman idan maganar danayi akan Zeenat ya bata maka rai, kayi hakuri.

ahankali deeni ya furzar da iska mai dumi ya miko hannushi ya dafa gwiwar fk , Friend ban tasamun abinda ya bani matsala kmr maganar yarinyar nan" abin haushi duk lokacin da nayi kudirin hakura daita sai nakasa .

Kullum addu'a ta Allah yaye min ita daga raina Amman abin ya faskara ko son yarinyar ne yakamani "oho " fk yayi murmushi yace lallai sonta kakeyi Allah yasa itama ta soka haka .

DEENi ya gintse fuska yace Ina ruwana daita first lov ce kawai damuwata ,data amince da yanzu an wuce gurin Amman tsohuwar nan sai cewa take zan cuci Yar mutane ita bazata bani Yarinyar karama ba inzo Ina bata wahala fk yace sanin halin ka tayi dan kai din bana wasa bane kana raina yarinyar ne dayawa shiyasa ummi batason aura maka ita wani lokacin sai inga kmr da gaskiya ummi DEENI yayi masa wani kallo dan ni bason iskanci idan abinda yakawo kennan kana iya tafiya .

Fk yace zanje in sameta da kaina kar damu .
deeni yace dama kabar ta kawai dan ko kaje ba amincewa zatayi ba.
nasan halin first lov , da zata yarda da tunin ta amince .
na dai fada mata cewar ni na hakura dayin auren gabadaya" inda tagaji da zamana haka tasan abinyi .

Fk yayi ta dariya tare da xolayar DEENI" friend ka dai shiga da yawa da ka'ajiye duk wani girman kai ,ka dinga kiran yarinyar kana janta ajiki ,idan ummi taga haka zatafi yarda da gaske kakeyi "Amman kai kullum fuskarka a hade kmr hadari .


DEENi ya tabe baki, kasan Allah bazan taba iya kiran ko wace irin yarinyar bace, da sunnan zance koba Zeenat ba. kai ma abinda kariga kasani ne "bansa ta Ina zan soma ba ,nifa bana kawo Zeenat a raina ,in dai first lov ta yarda " to tayi hakuri ta aureni kawai dan ni banda wani lokacin ya mace . dan ma taji dadi ta samu miji irina ,yakarasa fadar maganar yana jan tsaki fk yayi dariya yace friend banda yabon kai fa , DEENI ya dan yi murmushi gefen baki har dimple dinsa ya lotsa kai ma kasan gaskiya fada ne dai

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment