Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata alamun tsoro ko fargaba ba nablah tace zanyi ..
Ok minti biyu kacal nabaki "naganki a kitchen "idan kika kuskura kika bata min lokaci zakiga yadda zan ci ubanki a gidan nan " tana gama fadar haka
ta juya fuuuuuu tasoma tafiya tana kunfar baki.

"Nablah tayi zuru kawai tare da bin bayan Zeenat da wani irin kallon mamaki da alajabi abinda tayi mata.

dan ko kusa batayi tsammani zata fuskanci irin wannan babbar wulakancin ba mai cike da al,mara .

Yau itace aka aiki tajawo aka zagin mahaifinta..abanza uban ta fa aka zaga ,ta furta akan akasan ranta, wato silar ainkinta ne jawo a dinga wulakanta mata uba Haka km ma har da kiranta da sunan baiwa...baiwa fa takirani dashi ta sake maimaita sunan a filli gabadaya abin yazo mata wani iri km abazata" tamkar ba gaske ba.
Anya kuwa rayuwar zata yuwu a Haka tun ba,aje koina ba an fara da zagar mata mahaifnta.
" Anya kuwa zan iya daukar wannan kalar kaskancin da iskanci kuwa ,abinda ta tmbyi kanta da kanta Keenan?

,'ahankali ta furzar da iska ta bakinta tana furta wlh da sake Dan zan iya daukar komai na kunci rayuwa Amman Banda zagar min iyaye .

,

, Mtssss taja tsaki itama tana harara kofar da Zeenat tabi .cikin sanyi jiki ta nufi kitchen .

Ko minti biyu batayi da daura ruwan abincin dare ba Zeenat takaraso ta tsaya a bakin kitchen din tana kiran.. ke....ke.. nablah dake tsaye tana jin Tayi banza daita duk da tasan daita take sannan km taki juyowa ...
Sai ma cigaba da aikinta Tayi.

Sai da Zeenat ta sake maimaita kiranta sannan nablah da ke ..Kusan Sau uku sannan nablah ta juyo a danketa tana kallon cikin idanunta Zeenat .

Zeenat tace ,Yar iska yarinya kawai kina jin mutane suna kiranki Amman dan dakikanci irin naki kika yi shr..ko

nablah ta hadiye bacin ran dataji yana taso mata tun daga tsintsiyar kafafunta ,sannan tace kiyi hakuri basan dani kike ba" sbd ita kalmar ke.. din da kika ce bata daga cikinta sunan nablah....


. eyyyye Zeenat ta fadi Haka tare da ta ware ido tana kallon nablah da mamaki ni zaki kawa rainin hankali , nablah tace kiyi hakuri aunty barainin sense bane a zafafe Zeenat tace yi min shr stupid girl kawai ni zaki kalla kicewa ba sunanki ke ba.... Dan bakida mutunci , to kisani ni daga yau da sunan ke ... zan dinga kiraki ,Dan Allah idan nakiraki dan ubanki karki amsa kiga yadda zanyi dake a cikin gidan nan .. .

nablah ta datse lip's din bakinta na kasa da karfi gaske jin zafin abinda Zeenat tace mata , kusan minti biyu tsakani nablah ta sake duban inda Zeenat ke tsaye har lokaci gabadaya gabobin jikinta sun sage muryarta cike da rauni km Haka kawai ta tsinci kanta da cewa kiyi hakuri aunty .da hannu Zeenat ta katseta .. yimin shr Dan Allah dan bana son sake jin ko muryarki ne .. km ki sauke pot dinan ki daura min indomi yanzu yanzu taja tsaki tare barin kitchen din.

cike da mamaki yarinyar Zeenat takarasa ta zauna ranta a abace wahake take fidda numfashi dan kwata kwata bata taba jin tsanar mai aikinta irin yadda take jin haushin nablah .

Gashin yarinyar kmr bata da wani alamun tsoro atare atare daita .

Cikin mintinan da basu wuce biyar ba ta sauke indomi ta yuye a plate sannan ta sake maida pot din abinci dare kan gas .

zaune ta sameta ta hankice a parlour sai faman cika take tana batsewa tare da hura hanci 'tana kada kafa daya ..

ahankali nablah ta ajiye mata plate din indomi agabanta akan center table tare da kwalbar vitermilk kana ta juya ,tabar parlour .
,banda tunanin da mamaki Zeenat bbu abinda nablah keyi .

ko meyasa ita takasance irin haka ba kmr ummi ba ,mai matsananin son mutane da kyautata musu" km tana lura da irin yadda ummi din ke matukar bawa duk wasu mutane dake shigowa cikin gidan, kulawa ta musamman " sabanin ita wannan bazanr matar mai kama da mutane China .

, 'Ahankali nablah tacigaba da aikinta na zagin Zeenat din aranta sai data gyara koina tsab .

sannan taje tambaye Zeenat din ko akwai wani sauran aikin da zatayi Dan gujewa cin mutuncinta .

,a yatsine Zeenat din ta dago fuskarta tamkar hadari sannan tayi mata nuni da hannuta alamun zata iya wucewa kawai .

jikinta a mace tabar gurin , da kyar ta dinga daga kafafuwanta tsabar gajiya datayi , yayinda idanunta suka ciciko da Hawayen batayi kokarin hana hawayen idanunta zubowa ba,sbd tashin hankali take ciki da wutar dake ruruwa a zuciyarta tana tafe tana kukan zuci yayinda hawayen idanunta ke sake cigaba da bin fuskarta...

ahankali ta hau step daidai conar da zata kaita dakinta.
anan suka kusan cin karo da deeni da ba dan Allah yakiyaye da sai daita tajita a faffadan kirjinsa . sakamakon hannunta duka biyu datasa tana goge Hawayen idanunta ..

daddaden kamshin turarensa ne ya doki hancinta a frigice tayi sauri janye jikina..
Ta makale jikin bango batare da tasan Tayi hakan ba , jikinta ya dauki rawa kirrrrrrma hawaye km sharrrrrrr suna sake bin fuskarta ido cikin ido suke kallon juna ,itace ta soma janye idanunta ta ta runtse gam tana jinra kawai taji saukar mari ..
, tsayawa yayi cak Shima yana karemata kallo up and down .

A tsorace tasa tafin hannunta duka ta rufe fuskarta dashi.. kijinta na sake daukar kirrrrrrma .

'Ahankali ya ja wani irin mugun tsaki mtsssssss wanda hakan ya sake jefe zuciyar nabla shiga cikin rudani .

, yana tsananin jin haushi yadda yarinyar ke behaviors kmr wata dakiykiya ..
harara ya zabga mata kana ya sake jan tsaki sannan ya yasoma taka step . tana jin takunsa har sai da yakurewa step din Sosai sannan ta bude idanunta da sauri ta fada dakinta tare dannawa kofar key ..

.ta fada kan gado takarasa fashewa da wani sabon kuka.... Mai cin rai blaming kanta kawai take ta yadda tayi sanadin jefa kanta cikin meyakawoni matsala.
, meyakawoni cikin wannan gidan ?

meyasa na kawo kaina cikin halaka irin haka ?
anya kuwa nayiwa kaina adalci Dana zabarwa kaina irin wannan rayuwar ,mai cike da kaskancin da wahala ..
Anya kuwa zan iya cigaba da yin wannan aikin kuwa ? Haka ta dinga jerowa kanta tambayar iri iri batare da tasan abinda yakamata Tayi ba ..
yanzu irin rayuwar da zanyi kennan?
..Ta sake jeho kanta tmby.
agigice tatashi zaune ta jingina bayanta da jikin gadon dakin tare da zubawa celling dakin Ido tana tunanin abinda yakamata tayi "shr yabiyo baya na wani dan lokaci .

tuno auntynta datayi ne yasa tayi saurin sauke ajiyar zuciya, Dan tasan ita kadai ce zata iya fidda ita a wannan halin wulakancin datake ciki , batare wata matsala ba. ai aikin bai zama dole ba , da sauri ta hau goge Hawayen fuskarta tace zan kwantar da hankalina na zuwa wani lokaci "kafin nasamu yin waya da auntyna . ahankali ta Mike tashiga bayi ta dauro alwala sallar magrib koda ta idar ma bata tashi ba sai datayi isha'i a gurin .
, bata bi takan komai ba dan ko abinci bataji zata iya zuwa ta sakawa cikinta ba .
ballallantana ta hadu da hawan jini ,da ciwon ulcer wato deeni da Zeenat .

,Ta kwanta anan ta dunkule jikinta cikin hijab tare da lumshe idanunta kawai" duk da ba wani bacci takeji ba, ahankali tarinka jin yadda zuciyata tasoma beating dip....dip.... kafin daga baya tashigayi da sauri da sauri sakamakon tunowa da Mr horo datayi ...
"Tarasa dalilin dayasa duk sanda tayi arba dashi ko ta tuno shi take shiga cikin tashin hankali, ba.
, addu'a tasoma aciki. zuciyarta ya Allah...ya Allah kamin tsari dashi da duk wani wani shirin dake tattare dashi . Allah idan zama acikin gidan nan alkhari ne a rayuwarta Allah kasamun natsuwa da hakuri zama da matar gidan .
,idan km bbu alkhari Allah ka fidda cikin kowace irin maseefa cikin sauki . haka tayi tayi yan addu'oita , har taji zuciyarta ta dan samu natsuwa daga tashin hankali data shiga na wuncin gadi ,daga karshe bacci mai nauyi yayi gabadaita.


Acan kasa kuwa DEENI ne kwance akan thrre sites hannunsa rike da remut yayinda zeenat ke zaune a gefenshi suna hira ,rashin ganin nablah yasa duk ummi ta damu har . takai ga tambayar zeenat ita , ummi tace ni kuwa ina yarinyar nablah take ne har yanzu banga saukowarta ba ko lafiya?deeni dake zaune yaji gabansa ya fadi zuciyarsa tashiga harbawa .

" zeenat ta Dan yatsina fuska kana tace wa ummi . ai tun dazu kafin ki dawo ta sauko taci abincinta ta koma dakinta dayake fita ummi tayi ,yau . Ummi ok na jita shr ne .sannan tacigaba yabon nablah yarinya mai hankali wlh .
Zeenat taji magannun ummi na neman saka mata ciwon kai ,ta barta da karyar data ,sharara mata ta ba gaira ba dalili .

Zeenat ta Mike tsaye tsam tare da yiwa ummi sai da safe Dan itama yau bacci take son yi da wuri sbd tana da lecture karfe goma daidai na safe .. .
ita data shiga dakinta da niyar samun natsuwa Amman zuciyar tashigo mata da tunani iri iri ciki kuwa har da maganar haihuwar da bata km samu ba har yanzu wanda shine jigon rayuwarta a gidan mijinta ..

'Byn tafiyar Zeenat ummi dago Ahankali tana duban deeni tare da kiran sunanshi..
DEENI dake kwance ya amsa hade da dan mikewa zaune ya mai da hankalikasa kacokan a kan umminsa .

Ummi ta numfasa sannan tacigaba deeni naji kamin shr game da zance yarinyar nan mai aiki... , gabansa ya yanke ya fadi rasssssss ...jin abinda ummi tace "ya zubawa ummi ido kawai yayi shr yarasa me zai ce mata " saima shiga wani yanayi da yayi .'ahankali
ya runtse idanunshi yana Jin tamkar ummi ta watsa masa ruwan zafi yake ji da wannan maganar yarinyar datayi masa.
dan zuwa yanzu ya dauka ummi tabar zance ne kwata kwata ganin bata sake mishi maganarta ba .
"ummi tace kamin shr DEENI idan kasan baka shirya yin komai ba akai mezai hanna ni kabarni na aiwatar da komai domin nasan abinda zanyi ..
"ahankali deeni ya bude rikitattun idanunshi ya zubawa ummi su kawai yana kallonta ,kada masa kanta tayi alamun abinda ta fada din haka take nufi .
yace first lov kiyi hakuri Dan Allah zansan abin yi Amman dan Allah kidan karamin lokaci kadan kinji first lov .
Ummi tayi shr can Kuma tace shikenan Ni daita burina bai wuce nasamu abinda nake fatan samu daga yarinya ba .. tan Ga fadar Haka ta mike tana mishi sai da safe .

,Karfe shadaya daidai deeni Yashiga dakin Zeenat byn ya gama shirin bacci cikin wasu ratsasun kayan bacci.m masu matukar kyau.

batasan shigowarsa ba tana can duniyar tunani "ahankali DEENI yakaraso har inda take tare da ya kamo tafin hannuta cikin nasa Yana murzawa sannan ta juyo 'ahankali tana sauke naunauyen ajiyar zuciya.

ya tsareta da idanunshi kawai sannan yace meke damunki Zeenat ?
Ke ke nan kullun bakya gajiya ,ki raba kanki da wannan tunani ,kisani tunani shine abu mafi sauki dake saurin nakasa rayuwar Dan Adama Amman ke kin maidashi abincin cinki kullun ..,kinsa Allah ba tunaninki ke damuna ba ,halin da first lov zata shiga sanadin wani abu ya sameki nake .idan akwai abinda kika san yana dumunki please tell me...
tayi shr kawai tana kallonsa sun dade a haka suna kallon junansu sannan , ko me ta tuna Kuma ta sakar masa murmushi karfin hali ta matse hannushi cikin nata gam tare da lumshe masa idanunta ta girgiza masa kai alamun bbu komai .

Deeni yace I you sure bbu komai" ta dage masa girarta daya kmr yadda yake mata shima, har taso tabashi dariya yayi murmushi tare kwantowa jikinta ya rungumeta ajikinsa tsam tsam Yana aika mata da sakwanninsa masu matukar birkita mata kwalkwaluwa .. hannuwansa duka yasa ya zagaye kugunta dashi ,Haka kawai Yashiga aiyanata yarinyar, 'ahankali ya sake narke mata ajiki yana duk inda hannushi yaci karo dashi itama cikin kwarewa tasoma romancing dinshi .
ranar dai kwana sukayi suna jiyar da kansu dadi deeni yayi Tayi batare gajiya ba .
Iya murzuwa Zeenat Tayi shi a hannun DEENI har kai saka masa kuka sannan yabarta ya Mike Yana mata korafin tacika ragunwaci.
ita batace masa komai ba . washegari gari ma da kyar tasoma tashi yayinda da kyar ta dinga kafafunta, bayi tashiga ta gasa jikinta da ruwan zafi .

baita tabar gidan ba Sai wuraren 9 AM .. ..




MMN SUDAIS CE
[7/12, 7:08 AM] 0mmer Farouk: 💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗





AYSHA A BAGUDO





Page 64



Tun byn fitar Zeenat nablah ke faman aikin gyaran gidan batare da samu damar zama ta huta ba.
,duk da matar gidan bata nan hakan bai hanata yin kokarin taga ta kammala da aikin ba .


Tana tsaye a kitchen din yayinda hannuta ke kai kawon gogen kayan kitchen din Wanda ya zame mata dole kullun garin Allah Ya waye sai tayi.

laraba ce tashigo kitchen din tana yimata sannu tare da sanya hannu tasoma kokarin taimakawa nabla da wasu ayyukan .

Nablah Tayi murmushi dama kinbarshi aunty yanzu zan gama ai"

Karki damu sis nima zaune nake bana aikin komai shiyasa kikaga naxo .
gashi km Naga kmr aikin Yayi miki yawa dan nasan yadda yanayin aikin gidan nan yake da cin rai km bai karewa.
" Dan ma Allah taimaka madam batanan da yanzu tasa jininki ya hau kilometers duhu.

,Dan har gara hjy da mai gidan akanta " Dan shi maigidan kwata kwata baya shiga harkar mutune yayinda ita hjy wani lokacin takan tausayawa mutun.

nablah tace Haka ne .laraba tacigaba
amman ita madam Komai zata saka mutun Sai ta nuna maka iko da isa " Ga zagin rashin mutunci , tamkar ta haifi mutane , km duk irin aikin da zakiyi mata idan bai gamsar daita a banza yake a gurinta .

nablah Tayi shr kawai tana sauraronta batare da tace mata ba , komai Sai ma maida hankalinta datayi kan aikinta.

laraba ta sake cigaba kinsa Allah ko abinci kika dafa wannan matar , muddin baiyi mata ba wlh dole ki sake yin wani .


Nablah dake tsaye 'tana aikinta , tace nifa Ina ganin kmr mdm din nan taki , kwarkwar ce.......

"Haba aiko laraba ta kwashe da wata muguwar dariya , kai gsky nablah baki da kirki wlh madam din ce kwarkwar tana mai sake kwashewa da dariya .

nablah ta bar abinda take ta juyo Sosai tana duban inda laraba take .

Kinsa Allah wlh Ni kallon kwarkwar nakewa matar nan sbd wasu abubuwa dana Ga tana yi Na marasa hankali.

" nan dai sukai ta hirarsu tare da zagin Zeenat din ,.
nablah har da cewa Allah Yasa ogon madam yakarowa mdm amarya labara Tayi saurin kai hannuta ta toshe wa nablah baki ,tare da leka parlour sakamakon jin kmr motsin mutun .
"ganin bbu alamun kowa ne yasa ta dawo ta tsaya kusa da nablah .

"ai inaganin abinda mdm din tafi tsana kennan a rayuwarta .
"kishiya.... uhm zata iya yin komai akan mijinta. ba kya ganin ko inda mijinta yake bata son ana zuwa ,ke ko kananan kaya kika saka wlh Sai takawa mutun miki birki da guzirin Harare da zagin .

,kinji ba , ai abinda yasa kikaji nace miki , Ina mata kallon kwarkwar ,Dan some time sai inga kmr tana hararata byn ban mata komai ba inji cewar nablah.

Laraba ta numfasa sannan tace shiyasa lamarin zaman gidan Sai kin kara da hakuri. nabla ta sauke naunauyen ajiye zuciya sannan tace indai hakan kike fama da matar nan Na jinjina miki dan gsky kinyi kokari wlh.

, ai a Haka ma bakiga komai ba indai mdm ce inji cewar laraba , Dan naga kmr ke kina da wani matsayi a gidan" tunda har an barki kina ganin mai gidan ,gashi km har special room aka baki a sama.

" Mtssss nablah taja wata muguwar tsaki matsayi ko walaha byn bakada wata darajar a idanun masu gidan. "nabla ta sake yin kasa kasa da muryarta Dan kar wani yajiyo abinda zata ce sannan tacigaba abinda zan fada din nan Dan Allah bana son ki fadawa kowa" Amman Allah nayi mugun tsanar mdm Zeenat din nan byn Haka km Ina fatan Allah Yasa mijinta ya kara aure.
, Dan kawai nayi kallon irin kalar haukar da zatayi koda yake ma ,may be by the time din da zai kara auren ma ,na dade da barin gidan Dan bana jin zan dau wani lokaci a gidan nan .
, laraba tayi saurin marairaice fuska haba nabla Dan Allah kada kiyi Haka ,Karki tafi ki barni na rigada na saba dake banzan so ki tafi kibarni ba .hakuri kawai zakiyi da halinta ,kiyi abinda yakawo ki.

laraba da nabla suka cigaba da aikinsu suna hira sama sama laraba Na sake cigaba dabawa nablah labarin gidan dama estate din gabadaya ,Da yake ita tana fita sosai .
nabla sai murmushi take km tana kwadayin fita taga yanayin estate din Dan tun zuwanta gidan ko get bata sake lekawa ba .


Washegari gabadaya da gyre gyre aka tashi dashi a gidan.
koina ka kalla a hargitse yake saboda wani gyara da za'a a sama da km zuwan bakuwar daza suyi daga kasar India, kmr yadda nabla taji zeenat nafawa wata friend dinta datazo .

kai kawo nablah ta dinga yi tsakanin upstairs da downstairs , kallo daya zakamata ka gane tsansar yadda ta fita haiyacinta tsabar gajiyar dake tattare daita dole ma kaji ta baka tausayi .

tsaye take kusa da zeenat ta takure jikinta waje daya , byn ta gama waken kayan da Zeenat din tayi amfani dasu ,banda harara da kallon banza bbu abinda take jiho mata .

,A zafafe Zeenat din ta kallo inda nablah ke tsaye kinzo kin wani tsayamin a kai kmr zaki tsotsemin jinin jiki ki dauki plastic ki kawai my hrt.. takarasa fadar Haka tana watsawa nablah wanimugun harara .

Nablah tasa 'hannu kennan zata dauka sai ga laraba tashigo kitchen wasu kayan wando jeans da Riga Tayi gurin frij .

zeenat ta kallite ta kalli kayan jikin laraba sannan ta watsa mata wata uwar harara ,har nablah ta ji hantar cikinta sun cure gurin daya .

Fuskarta a yatsine Tace meyye haka kuma laraba ...kinsa bana son wannan iskanci a gidana .
bama na hanaki saka irin wayan nan kayan ba?

Nablah ta dago ta dubi aunty laraba jens ne a jikinta sai riga iya gwiwa .

ok karuwanci kika zo yimin a gida ko me?
, da sauri laraba tasoma bata hakuri .
dan Allah madam kiyi hakuri wlh bazan sake sanya su ba wannan mistake ne .
,da hannuta mdm Zeenat ta dakarta da ita ya isa bana son jin komai daga yanzu ma na kashe sa irin iriin wayandanan kaya muddin kina son zamanki ya daure dani. sannan ta kallo inda nablah tsaye har lokacin bataje inda ta aiketa ba ,tsawa ta buga mata ke kuma tsayuwar uban me kikewa mutane da bazaki wuce ba kin wani tsareni da shegun idanuki masu kama dana mayu.. bazaki wuce inda na aike ki ba.

Duk da nablah taji maseefar tsoron yadda taga Zeenat Tayi Amman hakan bai sa ta nuna ta fito da tsoronta filli ba a dake sannan km fuskarta a hade ta bar kitchen din hade da tausayawa kai banta.

Domin bata ganin laifi Zeenat sai nata domin ita takawo kanta da kanta cikin wannan maseefa.

Ta Dan tsaya kafin takarasa parlour mai gidan Tasa 'hijab dinta tana goge hawayen daya yasoma bin kuncinta dan iri irin abinda zeenat takeyi musu yana taba mata zuciya sosai .

'cikin sanyin jiki tasoma tafiya har ta iso parlour da mai gidan yake tare da bakinsa da sallamarta tashigo. muryata fal cike da tsoro da fargaba.

kallo daya DEENI yayi mata ya dauke idanunsa sai abokansa guda biyu ne suka amsa mata sallamar.

, ahankali cikin tafiyarta mai daukar hankalin ga duk wanda ya kalleta , ta karaso ciki sosai , ta tsugunna ta ajiye plastic din da cup's .

Banda kallon kasa ido bbu abinda DEENI yake mata ,'ahankali tare da natsuwa ta soma tsiyaya musu coffee .
cikin wata kwasatsiyar murya taji ance ke zaman me kikeyiwa mutane anan .... oya live this place now...

Gabanta ya dukan uku uku ,cikin tsananin tsoro hade da tashin hankali ta Mike tsaye , jikinta ,har rawa rawa yake tasoma kokarin daga kafafunta yayinda idanunta suka ciciko da hawaye tafff, ta bar parlour, daidai bakin kofar main parlour ta kusan ci karo da zeenat da sauri taja da

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment