Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gurin. Kuka take sosai tana nadamar abinda ta aikatawa rayuwa ta rarrafa zuwa inda ummi ke zaune tana goge hawaye.
ta daura kanta bisa cinyoyin ummi.. Ummi kiyi hkr kiyi hkr ummina ki yafemin ki min aikin gafara bisa furuncina gareki bazan taba yin fushi dake ba ummina nasan ni na cuci kaina bakece kika cuceni ba nasan kinyi hk ne sbd daurewar faruncikina a gidan yaya bazan taba butulce miki ba ummi duk duniya banida wacce tafiki ...Tana kuka take mgn ummi ina neman alfarma agurinki ki taimakamin kisa deeni ya sauwakemin aurenshi dake kaina na hutawa rayuwata da ganin bakin ciki.
ummi tashiga girgiza mata kai tana kuka.. ummi bazan iya ganin da jurar kallon yaya tare da wata ba .
zuciyata ummi zata tarwatse zan mutu.... Mutuwa zanyi ummi muryata cike da kuka takarasa mgnr...haidar da anan har junior da suke zagaye da ummi suka shiga goge mata hawayen dake tsiyaya da hannusu....


Yaran kamar wasu manya suka rungume ta, suna kuka, itako Nablah da gudu kamar zararriya ta sauko daga sama tayi hanyar fita, kota kan yaran bata bi ba balle kayan ta, cikin zafin nama Deeni yayi kanta ya manta da jama'ar dake falon, rik'o ta yayi gam a jikin sa, yace " pls Nablah karkiyi min haka, karki guje ni, kar ki hukuntani da laifin da ba nawa ba, wallahi kece rayuwata idan kika barni mutuwa zanyi, matuk'ar bakya kusa dani Nablah rayuwa ta bata da wani amfani, ke haske ce a gare ni, pls karki min haka, ya k'arasa maganar hawaye nabin fuskarsa, da k'arfi ta hankad'e shi ta kalleshi ido cikin ido ta nuna masa yatsa tace " don't, don't ever touch me again, I hate you Deeni, you are monster, you are cheater,you are liar, deceiver, I don't want to see you again in my future life.
, ka yaudare ni, na yarda dakai, na d'auka kafi kowa so na, da tausayi na, ashe kai mugu ne, I can believe it, Deeni kaine kayi man haka. Duk yaran suka taso suka bar jikin zeenat suka rungumeta a fusace ta cire su daga jikinta. Tana cigaba da mgn.

Yara gasu nan, dama sune burinka, to Allah ya cika maka, ka rik'e kayanka, Deeni yace " pls Nablah you are my life, don't live me, murmushi tayi cikin kuka tace " ur life, kanka kawai ka sani, ta juya zata fita, da sauri yace " a matsayi na mijinki ban baki izinin fita ba, juyowa tayi ta tako gaf dashi tace " miji!!! , ta nuna shi tace " wai kai kana tak'amar miji, gaya man meye miji meye aure?

"Sannan ka sanar dani hakki na d'aya dakataba sauke min, bayan biyan buk'atar kanka, kai yanzu baka ji kunyar kiran kanka mijin Nablah ba, yanzu .
Deeni shi kanshi mahaifina kaji kunyar sa, bai sanka ba, bai san daga inda ka fito ba ya d'auki 'yarsa ya baka, ya baka yarda da amana, nasan mahaifina ba dan matsayinka ya bakani.
dan nasan baima san waye kai ba, balle yasan abinda ka mallaka, Deeni daga ni har mahaifi na ka cuce mu, ka yaudare mu, amma ba komai Allah na nan, ta juya saitin zuciyar sa ya dafe, yana kuka sosai kamar k'aramin yaro ya matso inda take, yace " wallahi Nablah ina sanki fiye da komai da kowa a duniya you are my first love, I love you so much, wallahi Nablah idan kika barni zuciya ta bugawa zata yi, mutuwa zanyi Nablah, rayuwata bata da wani amfani matuk'ar bakya tare dani.


Wani irin mahaucin kuka Zeenat ta saka tabar jikin Ummi tace " Ummi kinga abinda kika jawo min ko? Ina zaman lafiya da miji na kin d'auko min bala'i tunda nake da Deeni bai taba'a furta kallar koda yana so na ba , balle yace he love me so much, Deeni bai tab'a gaya min kalaman soyayya ba, Ummi alhakin Nablah ne zai kamaki, shiyasa Allah ya jarrabi Deeni da sonta fiye dani, koma ince fiye da kowa harke tunda kema da kunnanki kinji abinda yake cewa akan ta, Ummi kinga yadda tunaninki ya cutarda mu, ta k'ara fashewa da wani mahaukacin kuka.


Shidai Big Dady kallan su kawai yake ya rasa abinyi, nablah tasoma daga kafafunta Deeni yace" pls ku taimka kuyi mata magana kusa baki karta tafi ta barni, wallahi ita ce rayuwa ta, kafin kowa yayi magana Nablah tace" wallahi ko mutuwa zakayi deeni sai na barka, kai koda gawarka kace a gaba na zan saka k'afa na tsallake ta, tasa hannu ta share hawayen dake zubo mata tace " akan me zakayi *AUREN SIRRI* dani,.

shi ban kai maccen da za'ayi Auren bainar nasi dani bane komai?

Kai ya girgiza mata yana kuka kamar wani k'aramin yaro, tace" san kai ne yasa kayi min haka, ka aure ni, ban sani ba, ka rink'a kusantata ba tare dana sani ba , harka yi min ciki, ka k'ara lallab'owa ka d'irka min wani ciki, yanzu ma in banda Allah ya toni asirinka da sai dai kayi tayi man haka, ina haihuwa ka yanke min jin dadi kanannaye komai na rayuwata ta fashe da wani sabon kuka tace " Allah ya isa Deeni, Ubangiji ya saka min, & I will never for gv u, ta jiya zata fice sosai Deeni ke kuka ya durk'usa gwiwa bibbiyu a gaban Nablah yana kuka wiwi yana rok'onta karta barshi.


Zeenat ma kukan bak'in ciki take, a gabanta mijinta yake durk'usawa agaban macen da bata kaita komai ba yake rok'onta ta so shi, zuciyar Ummi kuwa kamar zata tsage don bak'in ciki da takaici, ji take kamar ta d'ora hannu aka ta fasa ihu, ta gwammaci mutuwarta da ganin wannan rana, Deeninta ...tilon danta mai kyau,da tarin ilimi,da aji, gata, ga naira, yau shine yake rusa kuka durkushe a gaban mace yana rok'on soyayyarta, a gabanta kuma ba Zeenat d'inta ba.


Deeni na dafe da zuciyar sa, yana kuka a gaban Nablah, ganin zata fita ne, kuma babu wanda ke da niyyar yi mata magana kan ta tsaya.
ya sashi cewa " idan kika fita nabeelah ban yafe miki ba, Allah ya isa, ci gaba tayi da tafiyar ta,batare data juyo ba yaran ma suka bayanta suna kuka.
murmushi irin na manya Big Dady yayi sannan ya kira sunanta NABEELAH!, cak ta tsaya ba tare data jiyo ba, yace " zo nan, diyata a hankali ta jiyo ahankali tazo gabansa ta durk'usa, sai kuma ta fashe da kuka, da rarrafe Deeni ya rarrafo zuwa inda take yazo gabanta yace " please my heart kice kin fasa bari na, yayi maganar kamar wani zararre, Big Dady ne ya daka masa tsawa yace "deeni ka shiga hankalinka, sannan ya juya ya dauki waya yakira Ammar yace " kasanar da Family gabadaya cewar akwai meeting, nan da 1hr maza da mata har wad'anda ke gidan miji ka kira su ka sanar dasu, Big Dady ya kalli Nablah yace " jeki d'auko hijab d'inki, ba musu ta shiga d'aki ta kintsa kanta sosai sannan ta fito, Big Dady ya kalli su Ummi da Deeni yace " nan da 1hrs ku hallara,r ya kalli Nablah yace " muje, da sauri Deeni ya mik'e yace " nima zan bita, wani wulak'antaccen kallon Big Dady ya watsa mai wanda yasa shi ya shiga hankalinsa dole, Anan, Haidar, Junior gaba d'aya suka rik'e Nablah suka saki kuka mai ban tausayi, Big Dady ya kalli Ummi yace " jebi yara abin tausayi dan Allah, wallahi hakkin yaran nan kad'ai ya isheki, kodan gashi nan ma kin fara gani, Big Dady ya rik'e hannun Anan, ya kalli Ammar yace " rik'e Babanka, Ammar yayi murmushi ya d'auki Haidar, da junior big dady ya d'auki Anan, suka tafi gidan Big Dady. Har nablah.


Meeting room


A babban falon Big Dady kowa ya hallara manya da yara, maza da mata, ciki kuwa harda FK, gefe ga Deeni sai Zeenat dake ta faman kuka, kusa da Ummi, Nablah ma har lokacin kukan take, yaranta na nanik'e da ita, Big Dady yayi gyaran murya, ya kalli Fk yace " bud'e mana taro da addu'a, bayan an kammala ne Big Dady ya kalli Deeni yace " maimaita abinda ya faru, ba tare da tsoro ko wani fargaba ba Deeni yashiga zayyana duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe, kmr yadda ya sanawar da big dady kowa a wajen ya hau kallon Ummi yana mamaki, had'i da yin sallallami, gyaran murya Big Dady ya kuma yi sannan ya kalli Ummi yace "


Yanzu ke fisabilillahi kinyiwa yarinyar nan Nablah adalci, idan 'yarki aka yiwa haka ya zaki ji, wanne irin mataki zaki d'auki, ki duba yadda kika tauyewa yaran nan hakki akan farin cikin ki keda 'yarki, a ganinki kinyi dai-dai, ke yanzu ko tausayinsu baki ji bA.
, baki kunyar mahaliccinki, haba fadeela gaskiya baki kyauta ba, shiyasa Allah ya nuna miki baki isa komai ba, ya fifita yarinyar a zuciyar Deeni fiyye da taki 'yar, mai gatan, shiyasa Allah ya nuna miki ikonsa yasawa Deeni matsananciyar soyayyar Nablah, ta yadda bazai iya daurewa ko yi miki biyayya ba, a gabanki, akan idonki ya durk'usa a gaban ta yana kuka akan ta so shi, wannan kad'ai ya isheki izzina, da kuma darasi ga masu halin san kai irin naki, ki dubi yaran nan ya nuna su Haidar yace " idan suka girma suka ji abinda kikayi musu, da mahaifiyarsu kina ganin zasu k'aunace ki, ke ko tausayinsu baki ji, baki tausayin yarinyar nan k'arama yarinya kmr wannan dan nasan batafi 18yrs ba, kinga yadda Ubangiji ya nuna buyawarsa akanta ya hana 'yarta ki haihuwa da Deenin.


"Ni nasan bazaki tab'a yarda ayiwa 'yarki haka ba, idan ko akayi mata sai inda k'arfin ki ya k'are, gaskiya kina da san kanki, baki da adalci, wallahi ki nutsu ki koma ga Allah, ki nami yafiyar yaran nan, kinga dai yadda Allah ya saukar da aya a kanki wannan kad'ai ya isa ki gane kuskuren ki.


Kinga dai yadda ke da kanki kika had'a muku GADAR ZARE, keda 'yar taki, kika yiwa 'yarki kishiya abinda tafi tsana arayuwarta, kuma bata tashi sani ba sai da kishiyar ta zama dole k'anwar nak'i, dan ko ba'a zauna da ita ba dole a zauna da 'ya'yanta tunda ga tanan nan ma wani tsohon cikin, kinga keda kanki kinyi mata illar da harta mutu bazata manta ba, wannan kad'ai ya isa kusan komai na Allah ne, shike yin abinda yaso akan wanda yaso, a kuma inda yaso, dan haka mutane mudaina gaggawa a rayuwar mu.



Sosai Big Dady yayi musu fad'a gaba d'ayansu ya had'a dayi musu nasiha mai ratsa jiki, sannan ya sallami kowa, duk wainar nan nan da ake toyawa inna bata sani ba, dan idan ta sani ba zaman lafiya shiyasa Big Dady ya hana a fad'a mata, yace " Deeni ya tsaya,



MAMAN SUDAIS
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

Dedicated to
Hauwa A Usman
jiddarh




Kainuwa writers association
(united we stand and suceed our ambition is to entertain & motovite the mind of readers)


https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

Page 106


Byn kowa ya watse. parloun'n ya dauki shr na tsawon wani lokaci big dady ya dinga kallon deeni yana mamakin reaction dinsa na dazu daya dinga Yi akan yarinyar.
"ahankali Big dady ya cigaba da kallonsa tmkr wani sabon Halitta agabansa.
sakamakon yadda cikin kankanin lokaci gabadaya kamaninsa suka sauya ya dawo wani irin mutun Abin tausayi.
Ahankali big dady yake kalleshi tare da nazarinsa Kana ya numfasa muryarsa a matukar raunane irin ta Manya ya kira sunan shi..... deeni ya dago rikitattun idanunshi da suka gama canza kala tsabar rudani da tashin hankalin da yake ciki .
ya zubawa big dady su yana kallonsa batare da yace uffan ba.
" sai ma hadiye abinda ya tsaya masa amakoshi yayi yana maida hankalinsa sosai gurin sauraron abinda big dady zai ce .

Big dady ya sake fuskantarshi da kyau sannan yace nasuruldeeni na fuskacin kana matsanancin son yarinyar nan nabeelah kana mata mahaukacin so fiyye da tunanin me tunani wannan kalubali ne agareka sannan km babban yakine akanka daka San yadda zaka shawo hankalin yarinyar nan cikin sauki.
sbd daganin yarinyar tana da kafiya da taurin Kai da taurin zuciya sai kayi mugu mugun aiki da km yaki sannan Zaka samu ka shawo kanta da hankalinta.
" musamma sbd abinda akayiwa yarinyar wanda kowace Mace akayiwa hk zata iya yin hauka fiyye danata .
na Lura sosai kafi son yarinyar akan zeenat duba da yadda ka dinga yi wasu abubuwa agabanmu gabadaya idanunka sun Rufe deeni akanta.
so nidai abinda zance anan bai wuce nace kayiwa Allah kayi aldalci atsakaninsu deeni.

kayi adalci atsakanin matanka kada ka taba fifita daya akan daya karka sake kabari daya tagane kafin son daya akanta .
duk wacce Kake so axuciyarka kabarwa ranka yazama sirrin zuciyarka .
daman dole ne sai kasamu wacce zakaji kafi so atsakanin matanka .
Amman karkar kuskura ka bayyanawa kowace daga cikinsu.
kabarwa zuciyarka kayi adalci kaji tsoron Allah karike matanka amana dan karkaga nabeelah ce me haihuwa uwar ya'yanka kace zaka wulakanta zeenat sannan kada kaga zeenat yar'uwarka ce ka biyewa mahaifiyarka.
ku taru ku wulakanta nabeelah..
sosai big dady ya dinga masa Nasiha me ratsa jiki da huda zuciya dasa zuciya nadamar abinda ta aikata. Sannan zance ita yarinyar nan nabeelah kabarta anan tukun kafi asan abin Yi. ya daga kanshi alamun yaji.
byn big dady yagama dashi yace idan ya fita ya turo masa zeenat. Jikinsa a matukar sanyaye ya mike tsaye da kyar yana yiwa big dady sallama hade da godiya...


Byn ya fito ya iske zeenat zaune a karamin parlour'n gidan ya zauna kusa Daita sosai yana jin wani irin matsanancin tausayinta yayinda sound din kukanta ke taba zuciyarsa. "gabadaya nadamar abinda ya aikata agabanta yakeyi.
hakika bata cancanci hk daga gareshi ba kodan duba da yadda take matukar kaunarshi fiyye da komai arayuwata . cikin sayin jiki ya kamo tafin hannuta cikin nashi yasoma murzawa ahankali ahankali kafin yace wani Abu.
Da sauri ta zame hannuta cikin nashi tare da juyar da kanta alamun bata son ganinsa .
yaja numfashi da karfi ya fetsar yana tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta cike da tausayawa.
sannan ya bude bakinsa da kyar ya kira sunanta complete Name dinta muzeenat, ..............
zeenat taki juyowa ta kalli inda yake ballanta yasa rai da samun amasart.
sai ma jijjiga kafar daya da take tana cizan lips dinta.
Miryarsa a raunane ya sake kiran sunanta My Zeenat am sorry.... am very sorry for what I did...nasan ban kyauta miki ba .
sannan baki cancanci hk agurina ba.
" tabbas naso na kuntatawa rayuwarki alokacin da kikayita zubar min da cikina arariya ....Amman bata wannan hanyar ba.
Ko auren sirrin dana Yi da nablah ba'a son Raina nayi ba.
Umarnin first love nabi wanda alokacin gabadaya daurewar farincikinki take nema agidana .amman kiyi please ki yafemin bisa biyyewa first love danayi gurin boye miki..
duk wannan bayanani dayake mata bata juyo ta kalleshi ba har yagaji ya Mike da niyar wucewa tare da Sanar mata da sakon Big dady.

zeenat wacce taci kuka tkmr zata bar duniya idanun nan nata suka sake kankancewa sukayi sumtuma sumtuma sukayi jawur dasu . tashiga dakin da big dady yake zaune zaman jiranta.
wasu hawayen bakin ciki da takaicin abinda mijinta yayi dazu yashiga silalo mata bisa kuncinta.
ahankalin tasamu gurin nesa kadan ta zauna tana fuskantar big dady sosai .
wani irin tausayinta gyaraye da tsantsar kaunarta ke ratsashi. hakika yasan anyi mata laifi me girma...Wanda ta cancanci atausayawa rayuwarta da komanta. an tauye mata hakinta... anci zarafinta da mutuncinta.
an hukuntata da hukunci me radadi da ciwo da wuyar mantawa.
ya ja numfashi da kyar ya fetsar idanunshi kyam akanta yana nazarinta sannan ahankali yasoma da yimata nasiha akan yarda da kaddara .....
muzeenat kiyi hakuri da yadda kika tsinci kanki. ki yarda da yadda kaddaraki tazo miki.
wannan Abu ba daga umminki bane ba daga nasuruldeeni bane ba daga ita yarinyar bane daga Allah ne .
wannan hukuncin Allah ne ,ya zarta akanki.
" kada kiyi jayayya da ikon Allah.
kada kiyi fushi da abinda mahalinciki Allah ya zarta akanki .
"sannan rabon yayan nan ya rigada ya rantse muzeenat sai Sun xo duniya.
in ma ba haifesu ta hanyar sunnan aure ba sai sun zo duniya ,tunda Allah yarigada ya Kaddara akwai rabon ya'ya atsakain nabeelah da nasuruldeeni sai an haifesu kota hanyar shegu ne, musamm ma idan kikayi duba da yadda Allah ya nuna ikonsa acikin shekara daya Allah yabashi yaya har uku sannan ga wani cikin wanda Allah Kadai yasan abinda zata haifa.. wasu zafafan hawaye masu ciwo da taba xuciyar ma,aboci tausayi suka shiga gangaro mata a fuska ..
zeenat ta dafe kanta datake jin yana mata wani irin sara da mugu mugun ciwo.
cikin wani irin matsanancin kuka tashiga girgiza kanta yayinda aranta ta dinga furta kalmar Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un ...yaushe ni muzeenat zan samu sauyin rayuwa me dadi irin na kowace mace agidan aurenta?
.. Big dady ya numfasa kana yacigaba muzeenat ki natsu ki sanyawa zuciyarki salama akan lamarin nan sbd idan kin matsa dayawa rabo zai iya kasheki, ki mutu kibarsu, su cigaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali .
Dan hk ina son kiyi hakuri ki Karbi wannan kaddarar data zo miki da hannu biyu biyu.
" ki rungume kaddarki muzeenat km da alamun yarinyar zata biki yadda ya dace .
zata miki biyayya kada ki zubda girmanki a idanunta itama Sosai yayi mata nasiha me ratsa jiki da sanyaya zuciya tunda big dady yasoma mgn bata dago kanta ta dubeshi ba .
Sai kuka datake kawai tana sake nadama abinda ta shuka arayuwarta.
wanda shi yajefa rayuwarta takasance hk.take wasu wurare suka dinga budewa jikinta suna karbar kaddarar tada fada mata. wani irin tsoron Allah ne ya sake shigarta..



Kafin kace me tunin zance ummi yakarade ilahirin estate din .
"masu zaginta nayi masu side dinta nayi kowa da yadda yake fadan albarkacin bakinsa akanta .
wayanda basa side dinta kuwa suka dinga Yi daita suna zaginta.
Tare da tsananin mamakin sonkai irin nata da butulci da cin amana da yaudara da haincin irin nata.
Sosai suke mamakinta . wannan wani irin sonkai ne daita?
kwata kwata batayi adalci ba.


Daga gidan big dady kai tsaye zeenat gidan babanta wasu daga cikin yan'uwaa suka nufa daita.
yayinda nablah ke gidan big dady Dan koda big dady ya gwada Yi mata Zance takoma gidan mijinta kafin asan abinyi.
kin yarda tayi, ta koma gidan deeni...

Daren Rana banda kuka babu abinda zeenat keyi wanda daga karshe ta yanke shawarar kaiwa Allah kukanta.
,ta Mike taje tayo alwala tashiga jero nafilloli tana kuka tana neman sausauci agurin Allah, ya kawo mata sauki cikin lamarinta .
byn ta idar ta Dade zaune hannuta rike da carbi tana lazimi .
kwata kwata takasa runtsawa sakamakon tuno ummi datayi tasan duk inda ummi take tana can cikin tashin hankali da kuncin zuciya .
tasan ummi bazata taba iya runtsawa ba.
Tasan yadda ummi ke matsanacin sonta da kaunarta fiyye da komai aduniyarta .
wasu zafafan hawaye masu ciwo suka shiga silalomata.
tana nan zaune tana ambaton Sunan Allah har sanda aka Kira asalatu bata runtsa ba addua Kawai take...


Sosai ummi tashiga tashin hankalin rashin zeenat tashiga uku tarasa abinda ke mata dadi ta rame acikin kwana daya kacal .
abun Duniya duk yabi ya dameta gabadaya yanzu kunyar dangin take ji.
da gudun shiga tsakaninsu sbd duk magangun da suke fada yana dawo wa kunneta hankalinta yayi mugu mugun tashi tarasa inda zata saka ranta taji dadin arayuwarta.
bata da kowa akasar Nigeria sama da zeenat da deeni suka gareta.
idan har zasu iya gujemata zamanta bashida amfani akasar.

Ahankali ta mike tsaye jikinta kasalance ta shiga tsintiri adakinta na ainihin gidanta.
Kafin daga baya ta nufi inda ta,ajiye wayarta takira Wanda ke mata biza zuwa kasar haihuwarta.
byn tagama wayar ta dauko yar karamar jakar matafiya tasoma shirya kayanta ciki tana hawaye tana jin wani irin radadi da kewar tilon danta deeni da zeenat aranta .
Tsab tagama shirya komai..
Itama tunda rigimar nan ya faru bata samu ta runtsa ba har zuwa yau din nan .

Washegari tana idar da sallah asuba ta dauki Jakarta da niyar barin kasar gabadaya.
ahankali take saukowa daga matattakalan gidan xuwa parlour'n kasa taji motsen alamun bude kofar cak ta tsaya da tafiyar datake jikinta ya dauki kirrrrrma...abinka ga jikin girma kadan ya rage batayi kasa ba.
Km har lokacin danunta na kallon kofar shigowa.
tilon danta deeni taga Yana kokarin sanyo Kai cikin gidan. Ahankali karasa yashigowa jikinsa sanye da farar jallabiya fara kal da alamun daga masjid yake.
Take wani irin sanyin dadi ya zirayarci ilahirin jikinta da zuciyarta.ta dinga jinta wani Iri wani iri.
Amman ta kauwar da kanta da abinda take ji tacigaba da saukowa ahankali jikinta naciga da rawa wanda har yar karamar Jakarta hannuta rawa yake.
gaban deeni ya buga da matsanancin karfi ganin umminsa rike da jakar matafiya .
Wanda duk sanda kaganta da ire iren jakunkunan Kasan tafiya zatayi.
har tazo ta gifta ta kusa dashi idanunshi akanta yana kallonta da mamaki a saman fuskarsa.
ganin tana shirin bude kofar yasa da sauri ya riko jakar hannuta Jikinsa na wani irin rawa ..muryarsa cike da in... Inna... yace u'm.... ummi ina km zaki tafi hk ?
Meyasa ummi zaki mana hk ?
ummi please.......

ummi kada kiyi hk Dan girman Allah kiyi hakuri ki yafemin ya zare Jakar hannuta ya ajiye agefe daya tare da tsungunawa agabanta gwaiwa biyu biyu ya daura tafin hannusa duka bisa kafafunta please ummina kiyi min afuwa bisa ga laifin abinda na aikata miki bazan sake ba.
na tuba ummi nabi Allah da manzonsa na biki. ummi karki kujemu.idan kika gujemu rayuwarmu zata tagyara zamu shiga wani hali dagani har zeenat dinki......
ahankali ta zare kafafunta zuciyar na wani irin bugawa jikinta yayi sanyi.
Take zuciyarta tashiga shawagin barin tilon danta da diyarta zeenat .. Taku daya tayi zuwa biyu taja ta tsaya hade da juya masa baya tana jin wani irin matsanacin kunyar deeni .har zeenat ahalin yanzu kunyar hada ido
take dasu.
Batason km hada idanunta danasu.
tarasa ina MA zataje ta saka ranta taji dadi da
wa zatayi hirar ta rage zugin da zuciyar ke Yi akan abinda ya faru zeenat kadai gareta diya Mace gashi itama tagujeta ta juyawa rayuwarta baya akan abinda ya faru...
Jikinsa na rawa da rarrafe ya samu ya matso inda take.
yace kiyi hkr ummina karki tafi ki barmu bamuda kowa a nan sai ke idan kikabarmu yaya kike son rayuwarmu takasance?
Ummi taja naunauyen ajiyar zuciya da numfashi ta sauke da kyar.
Kana tayi dauriyar juyowa tana kallonsa duk da har lokacin zuciyarta cike take tab da jin kunyarsa da kunyar abinda yayi mata gaban big dady da gaban dandazon daginsa sbd common Mace.... Mace ma wace itace da kanta ta tsaya tsayin daka ta aura masa ita ,yana kukan bai sonta....
"muryarta a dake tace Ai wannaN bakomai bane idan na barka deeni.. karka manta yanzu kana da madadina wacce tafi agurinka .
har kake kokarin yimin tawaye akanta you give me double surprise deeni akan Macen da nice na tirsasaka ka aureta ba dan kana sonta ba..
ni... ni deeni ta nuna kirjinta da dan yatsanta Amman babu komai karku damu duniya ce.
sai dai kasani ayau din nan zanbar muku kasarku da danginku gabadaya na koma tawa kasar .
dama dan wa Nike zaune?
Dan kai da zeenat ne Amman ayau kun nuna min ni din bakowa bace agareku km nasan ko babu ni arayuwarku zaku cigaba da rayuwarku yadda kuke so.... Takarasa fadar hk tana kuku .
deeni ya rude ya gigice hankalinsa yayi mugu mugun tashi ya sake

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment