Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsam ajikinshi yana cigaba da wasa da kirjinta .



Washegari DEENI yashigo dakin datake .

sanye 'cikin wasu hadadun suit light blue sunyi maseefar yimasa kyau "kyawun haibarsa da nagartaccen annurin fuskar nan tashi Na nan bbu abinda ya canza agareshi ,sai ma wani kyawun da kwarjin dataga ya sake yi mata ba kmr jiya ba .
* fuskar nan tashi a daure tamau tamkar yadda tasoma ganinsa tun farkon zuwanta gidansa matsayin me aiki .

Kallon ido cikin ido suke yiwa junansu , kowannesu sai da tsigar jikinsa ya tashi nablah tayi sauri janye shanyayyun idanunta Daga kallon rikitattun nasa ido, tun bai km mata wata fassara ba ..

Bakinta yayi mata nauyi tamarasa me yakamata ta farayi ,gaishe da shi zatayi ko kwalleshi zatayi yacigaba da tsayuwarsa ?

Mgnrsa ce takatse mata tunani da muryarsa me saka mara jin mgn natsuwa ,ta daki dodon kunneta Gabanta yabada darammmm yayinda zuciyarta tashiga harbawa da sauri... ta dago shanyayyun fuskarta tana sake kallonsa .

Zaman me kike yiwa mutane dabazaki shirya ba alhalin kinsa kina da zuwa karbar sakamakon...

Zuciyarta tacigaba harbawa da sauri da sauri jin abinda yace .

Bakin Na rawa muryarta da in ..inna..tace wani sakamakon zanje karba ?

Yace bansani ba minti biyu nabaki ki shirya ..

Wlh Ni bbu wani hospital da zanje garama kayi tafiyarka Inda zaka ya fiyye maka alkhari .

Ke banson iskanci ko sa,an wasanki ne da Ina mgn kina maida min martani ban darajar mahaifiyata ke har isa Na tsaya Ina bata lokacin akanki ,taimaka miki kawai za'ayi badan kinsa ba . Ta dinga kallonsa tana mamakin wani irin mutun ce shi da canza yanayi baya mishi wahala yanzun nan zaka ganshi tamkar mutumin kirki anjima zakaga ya sauya ..

Miryarta 'Cike da in inna ..tace to..to.ni Na gode bana son taimakon naku ko dole sai an taimaka min ..bata ankara ba taji ya buge mata bakinta , hannu tasaka da sauri ta dafe bakin nata saboda zafin dataji ya ratsata fiyye da tunanin me karatu kafin kace me tuni hawaye sun fara gudu bisa kuncinta.

Yaja siririn tsaki yana hararrata sannan ya raba ta gefen ta zai wuce kana Yace minti biyu kacal nabaki ki shirya ki sameni a parlour ..

Muryarta can kasa kasa ta yadda tasan ba zaiji ba tace wlh Allah Ya isa bazanta taba yafe maka ba ....tsayawa yayi cak Daga tafiyar dayake dan jin abinda tace hakika kunnenshi bai ji masa karya ba.
Allah Ya isa tayi masa DEENI ya fada yana juyowa ....sai dai Ina..tuni tayi nisa tashige bathroom .. ahankali yakaraso yana murder handle din kofar yajita gammm.. Yace zamu muhade ne zaki gane bakida kunya yarinyar tana jin motsin tafiyarsa tayi saurin bude kofar tana kallon bayansa kmr ance ya juyo suka hada ido tamasa gwalo da harshenta tare da saka hannuta bisa idanunta ..

Ta sake koma 'cikin bathroom din da sauri ta kulle ..

Samun kansa yayi da sakin murmushi tunda yake a rayuwarsa bai taba haduwa da wawiya yarinyar irinta ba ,ya sake sakin wani murmushi Wanda shi kansa baima San yanayi ba ..

Nablah naganin ya fita daga dakin ta fito ta shirya kanta 'cikin wata doguwar rigar Wanda DEENI ne ya siyo mata shi a shopping sanda ya dauko Daga gida .
sosai tayi kyau ta dauki daya Daga 'cikin turarensa ta fashe ilahirin jikinta dashi sannan ta saukowa jikinta a sanyaye cike da jin tsoron abinda zai biyo baya ..

zaune ta ganshi ya harde a kan kujera tare da tsurawa hanyar step idanunsa.
tuni gabanta nablah yashiga faduwa da kyar ta iya karasa saukowa hannuta dafe da kirjinta tana sakin numfashi ga wani azababen faduwar gaba daya tasomata .
bai dauke rikitattun idanunsa akanta ba har sanda takarada saukowa hawaye ke neman kwace mata ahankali tayi saurin maidasu sbd irin kallon dayake aikomata dashi.

oh my God bazanyi kuka ba nablah kada kiyi kuka ki daure idan DEENI yaga hawayenki zai rainiki ,hawaye kadan ya fito daga idanunta tasa yatsanta tare da dauke Hawayen ...sai data daidai kanta sannan taje Inda yake zaune ..

Xumbur DEENI ya Mike zaune yana dubanta karki sake karawa kanki laifi ta hanyar bata min lokacin ..wuce muje ya nuna mata hanya da hannunshi hk ta shige gaba tasoma tafiya tamkar wace kwai ya fashewa aciki shi km yana biye daita abaya daidai bakin Glass din kofar fita.
taja ta tsaya sbd batasan yadda za'tayi ba yakaraso tare da daura yatsun hannushi saman glass din kofar.
ta bude ...suka fice ta maida kanta ta rufe ...


Tunda motar DEENI ta kunna kai 'cikin harabar hospital din nablah tasoma zare ido tana jin yadda zuciyarta ke tsalle tamkar zata fasa kirjinta ta fito DEENI ne yasoma fitowa tare da bude mata motar da kansa ..



Zaune suke a gaba doctor saira DEENI ya sauraron bayanin doctor wani irin yanayi mara misaltuwa ya tsinci kanshi ciki abubuwa masu yawa da mahimmanci sun same shi a arayuwa, Amman bai kai wannan matsayi da mahimmanci ba .
Yama rasa takamaiman me zai yi ahalin dayake ciki.
, farinciki ganin wannan rana ko kuma kukan murna ?
Wanne ya dace a gareshi a irin wannan ranar me tattare da farinciki ?
rike yake da farar takarda a hannusa har lokacin yana karanta abinda ke ji .

ahankali ya maida idanunshi kan nablah dake zaune tamkar andasa wacce gabadaya jikinta kirrrrrrma yake . tun sanda doctor tasoma mgn yayi shr tare da tsura mata rikitattun idanunsa dan son ganin wani irin reaction zatayi.

Murya doctor saira ta daki dodon kunneta Gabanta yabada darammmm tsabar frigice datake ciki.
Ki karbi takardar kikaranta abinda kika kasa yarda dashi tun jiya kennan ciki gareki har tsawon wata hudu...

Cike da tashin hankali DEENI ya riko hannun tare da saka mata farar takardar a tafin hannunta ,jikinta Na rawa rawa tasoma karanta abinda ke jiki . 'Cikin tuttukin bakinciki da tashin hankali hade zafin nama ta zabura zata Mike tsaye DEENI ya riko hannun tare maidaita da sauri yana cewa wani irin iskanci ne hk ?

Kada ka sake dangantani da wannan kalmar dan Ni ba Yar iska bace Ga katuwar Yar iska nan a gabanka kana kallo tana min sharri .tasoma yayyaga result din ta sake zabura ta Mike tsaye tana me watsawa doctor saira takardar ajikinta tana huci ...

doctor saira ta dinga kallon piece din takardar dake watse a jikinta tana kallon nablah tare da mamaki yarinyar ...

Yes .... wallahi wallahi wallahi idan kika km cewa ciki gareni sai Na tsinka miki mari , ko kwalkwaluwarki zata dawo jikinki ..Tana me nunata da ,dan yatsanta ke ba aikin likita yakamaceki ba kwasar bolar titi shi yafi dacewa dake ..

haba kunjimin mata da jaraba tsiya kin bi kin dameni da zance wani ciki...ciki gareni alhalin ba hakane bane .

Idan ma har ciki gareni sai dai ubanki ne Yayi min.
Doctor saira ta Mike tsaye a fusace tana duban nablah a xuciye ta Ciro hannunta zata tsinkawa nablah wani mahaukacin mari ..zaraf DEENI ya riko hannunta tare da cewa kar ki sake doctor.....


Barta ...DEENI barta ta mareni a tunaninki idan kike mareni bazan rama bane ko me?

shiiiiii haba duk kin bi kin cikawa mutane kunne da hayaniyar banza .. wannan ai haukan karya kike yi da borin kunya..Ya karasa fadar hkn yana sakarwa doctor saira hannu .

Idan ita doctor tayi miki karya result din shim a karya ne Yayi miki...?

Doctor saira da ranta yaga baci a fusace tace Ka dawo daita nan da wata biyu ta ganewa kanta abinda ke cikinta ko zata dawo 'cikin Hankalinta stupid girl kawai .. kina Yar yarinyar ki dake kinsa yadda akeyin 'cikin idan banda ke dakikiya ce ai yakamata kinsa ciki gareki when last da kikaga period dinki ?


Wani zufa ne ke karyawo nablah takoina ajikinta tayi shr tana tunani rabonta da ganin period dinta .
A atsorace jikinta a sanyaye ta dagawa doctor saira yatsunta uku alamun wata uku kennan.

Ok wannan shine step Na farko da mace zata gane tana da shigar ciki Amman dayake mahaukaciya ce ke kika kasa gane hkn ...

Jiikin nablah yashiga kirrrrrrma har da karkarwa takoma ta jingina da jikin bango office tana duban daya byn daya kallon DEENI da doctor take tamkar wasu halitta Na daban da bata ganin irinsu ba.

sosai jikinta ke cigaba kirrrrrrma nan ko doctor saira tasamu abinyi tashiga xuba zance tana sakin maganganu marasa dadi Ga nablal gara tun lokaci bai kure miki ba kije ki nemo Wanda yayi miki ciki ...ZUCIYAR nablah ta cika da damuwa ta tsaya cak...Ta daina aiki Na wuncin gadi kafin Daga baya tacigaba da bugawa da sauri da sauri ji take maganganu doctor saira ba a iya kunneta kadai suka tsaya ba har 'cikin zuciyarta take jin komai sbd dacin kalmar doctor gareta..

kuka ta saki mai cin rai da ban tausayi muryarta cike da kuka da tashin hankali ta shiga furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun meke shirin faruwa dani ?

Yayinda doctor saira tacigaba da surutai kusan yadda wasu doctor suke ballanantana idan sunji ciki bbu aure ..

ba yanzu ne zakiyi kuka ba sai ma kin rasa Wanda zai karbi wannan shegen 'cikin n.....wata irin razananniyar tsawa DEENI ya bugawa doctor yana aika mata da wani irin mugun kallon me tattare da tsana Wanda yasa take tashiga hankalinta ..a hassale yasoma mgn 'cikin tashin hankali meyesa wasu Daga 'cikin likitoci basu da imani ne ?

Dame kike son taji ?

Wlh idan wani abu yasameta sakamakon wannan zantuttukan naki marasa ma'ana, bazan barki ba ..

Tsaye nablah take ajikin bagon tana fezgo numfashi da kyar tamkar me cutar Asma tana fesarwa tare da duban DEENi rasa Inda zata nufa ne yasa ta nufo Inda DEENi ke tsaye yana dubanta
'Cike da tashin hankali da frigice ta matso kusa dashi sosai ta riko tafin hannushi 'cikin nata .
tana kallon fuskarshi takasa mgn so take ya karyata mata abinda taji doctor tace yazama ba gsky bane karya ne ko result din banata bane .

kallon kwaryar idanunta yake yana mai jin tsananin tausayinta har 'cikin ransa gabadaya duniya ta cukude masa waje daya bai taba sanin hk tashin hankali irin wannan dayake ciki yake da muni ba .

Sosai take kuka har daNa fitar hankali ita kanta bai taba tunanin rayuwarta zata kasance 'cikin wannan maseefa me cike da rudani ba rawar da jikinta keyi yasa .. kafafunta suka Gaza daukarta tayi kasa luuuuuuuu DEENI Yayi saurin tarota ta fada jikinsa ya rungumeta tsma ajikinshi gabadaya halin tashin hankali daya ganta ciki yasa shi mantawa ko waye shi da km Inda yake .
can km ta fexge jikinta Daga nashi da iyakacin karfinta .

tayi zaman dirshan a kasa tana tattara kan takardar data yayyaga Domin sake karanta abinda ke jiki .. Amman Ina aikin gama yarigada yagama ..ba dama .
dan bbu komai dazata iya Gani ballanantana har takaranta .

tashiga kuka tana sambatu iri waye yayi min hk ?

Wani mara imani ne da tausayin ,yayi min ciki ?

Wani la'ananne Wanda bazai taba gama wa da duniya lfy ba Yayi min wannan cin zarafin ?

Kuka take tana buga kasa da tafin hannunta tamkar wata zautacciya.

ba DEENi dake ake tsinewa ba hatta doctor saira sai data dawo tana tausayawa yarinyar ganin bil hakkin batasan da zaman 'cikin jikinta ba ..

DEENi yasoma matsowa zuwa Inda take zaune tana kukanta me cin rai daban tausayi tayi sauri dakatar dashi kar ka motso Inda nake tasoma ja da baya tamkar taga wani abun gudu Bai saurareta ba yacigaba da binta ya fixgota tare da Rungumeta ajikinsa yana fexgar numfashi ...
,




MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO




Page 86


Runtse idanunta tayi gammm..... wasu zafafan hawaye Na tsiyaya akan kuncinta karo Na farko data ji wata mummunar qiyayyar wanda yayi mata wannan aika aikan ya shiga zuciyarta daram ya zauna tare da huda duk wasu gabobi da jijiyon dake aiki acikin a sansar aikinta.
,koda kuwa ba halitar bil Adama bane ,wato aljani .. kuka take sosai har dana fitar hankali


Kokarin zamewa take daga gangar jikinsa duk da yadda take jin kanta ajikinshi amman takasa raba kanta dashi dan sake rungumeta deeni yayi tsam ajikinshi yana fidda numfashin ,'cikin wani irin matsanancin kuka tafara mgn da muryarta da soma dashewa ni ka sakar min jiki ...

kabarni nace ...

Kabarni Naji da maseefar data sameni....

Ni nablah ke dauke da 'cikin shege yau ... DEENI yashiga girgirza mata kanshi batare dayasan ya aikata hkn ba ...

Kana jin abinda doctor tace ciki gareni fa har Na tsawon wata hudu amman kake rungume dani ajikinka ...takarasa fadar hkn tare da fashewa da wani sabon kuka me cike da cin rai da girgirza zuciyar ma'aboci sauraro...

ahankali DEENI ya sausauta rungumar da Yayi mata ajikinshi yayinda jikinta ya sake daukar kirrrrrrma sun kusan minti ashirin a haka , kafin daga baya ya dagota cike da kulawa ya tsura mata rikitattun idanunsa ,yana kallonta. da kallon yanayin tashin hankali datake ciki .

,rasa yadda zaiyi da rayuwarsa ,yasashi cigaba da kallon cikin kwaryar idanunta kawai.s sannan ya hadeye abinda yaji ya tsaya masa a makoshinsa .

yayinda doctor saira ke tsaye tana kallonsu tamkar wasu jaruman shirin fillm .gabadaya al'amarin Nasu ya zauta hankalinta tare da girmama tunanita .
"Barinma Yadda taga deeni ya rude da gigicewa akan yarinyar ko shine Wanda Yayi mata 'cikin wa tunaninta iyakacin abinda zai yi kennan..

Ahankali yacigaba da kallon yadda kukan ke galabaitar daita .
"tayi mugun fita haiyacinta.
Ahankali yasa hannushi ya kamo tafin hannuta 'cikin nashi yana shafawa da baya hannushi ahankali 'cikin sarkewar murya yakira sunanta da sanyyayiyar muryasa .
da kyar ta bude shanyayyun idanunta ta xubasu 'cikin nashi batare data amsa masa ba.

,Ya lura gabadaya jikinta a sanyaye yake ko dan yatsanta bata iya motsawa,kokarin son dagota yayi ta zame jikinta daga gareshi..

kabarni DEENI bazan iya tashi ba.... ta sake tsananta kukanta me tsuma zuciya .

Muryarta a sanyaye ta dinga furta kalmar...wayyohhhyyy Allahna.
.

wayyohhhyyy Na shiga uku ..waye Wanda yayi min wannan cikin da bai kasheni gabadaya Na huta daganin wannan ranar me tattare da bakin ciki rayuwa ba?
... wayyo Ni nablah me zancewa mahaifina dayace kada nazo aikatau ..?

Me zancewa yan'uwana da suka tattara dukkan wata yardarsu da amanarsu gareni" tare da amincewa dani ,?


Wayoyyy wayyyyyoo Ni nablah wazan ce yayi min ciki......? Kuka take hade da sambatu iri iri .

,tausayinta ya sake kama doctor saira ya mamaye zuciyata sosai har batasan sanda hawayen tausayin yarinyar yashiga tsiyayo mata ba .
, ahankali ta zare dan siririn medical glass din dake manne da fararen idanunta ta goge Hawayen dake tsiyayo mata tare da maida medical glass dinta tana cigaba da kallonsu , ...


Mikewa nablah tayi da kyar tana layi... yayinda gafe daya km tasoma ganin juwa juya.
batare data juyo ta hankalta da irin kallon tausayin da doctor saira ke mata ba.
" ta fara tafiya cike da damuwa da rudanin rayuwa....

DEENI ya zabura ya Mike tsaye ya biyo bayanta da sauri yana Kiran sunanta tare da kokarin dawo daita amman taki sauraronsa ,sai ma fizge jikinta datayi daga nashi tacigaba da "Daga kafafunta da kyar ..

tafiya daya biyu zuwa uku tayi DEENI yayi nasarar sake damkota gareshi Ina zaki a hk...?


Ki natsu man musan abinda yakamata a yi duk wannan kukan naki bashi ba sulotion atare dake .....

zubewa tayi ajikinsa tare da sakin wani irin gigitaccen kuka.
ahankali tasa hannuta ta dafe daidai tsaitin zuciyarta datake jin yana mata zafi tamkar zata tarwatse..
" ta manne ajikinshi tana sakin numfashi da kyar tare da lumshe shanyayyun idanunta hawayenta Na tsananta zubowa, yayinda zuciyarta ke dada karyewa sbd mummunar halin data tsinci kanta ciki ..


Ahankali ta bude shanyayyun idanunta data lumshe ,tasoma ganin dakin Na jujjuyawa daita ...juwa take Gani sosai Domin zuwa lokacin bata ganin komai dake 'cikin dakin hatta bakin dake cikin idanunta yasoma yin sama da kasa alamun juyewa .

DEENI ya dake rungume daita a jikinshi yana kallon yadda idanunta ke son kakkafewa Yayi saurin yin kasa daita , kafin ya ankare tuni ta saki wata irin naunauyen ajiyar zuciya me karfi gaske .

Yayi saurin saka hannunshi duka yana jijiga fuskarta da iyakacin katfinsa tare da Kiran sunata a rude na..bee..lah.. na..bee..lah dan girman Allah Kada ki min Haka please.... ki natsu musan abin yi tukun yana cigaba da girgirzata Can yaji gabadaya takarasa sakewa ajikinshi .....ya tsayawa cak ..... yana dubanta da rikitattun idanunsa....

Gani Yayi bata numfashi ya dago fuskarta da sauri yana dubanta sannan a rude yasa byn hannushi a hancinta .

Amman kwata kwata bai ji wata alamun
numfashi a atare daita ba .

'Cikin wani irin tashin hankali da matsanancin fargaba ya Mike tsaye daita.
Yayinda , jikinshi ya dauki wani rawa yana Kiran sunnan doctor .......

kai tsaye kan dan madaidaicin gadon marasa lfy ya nufa ya kwantar daita yana sake Kiran sunan Doctor.

,yayinda doctor saira itama tazagayo daga inda take tsaye.
da mugun saurinta tare da kallon abin mamaki yadda DEENI ke sake ya rudewa akan wannan yarinyar dabata gama Sanin kowacece gareshi ba .

da dan hanzarinta takaraso inda nablah ke kwance tamkar wata matacciyar gawa dan bbu inda ke motsi a sansar jikinta..

Cike da natsuwa doctor saira tasoma dubata suma tayi doctor saira ta fadi hk tana duban Inda DEENI ke tsaye rike da hannun nablah yana mammatsawa ko zata dawo haiyacinta..

suma ... DEENI ya furta hkn da karfi jikinshi Na sake daukar rawa duk jikinshi bbu inda baya tsatsafowa da ruwa gumi tsabar tension din dake zariya a gabobin jikinsa.

,Ok please doctor taimaka min kibata taimakon gaugauta please.

Abinda nake kokarin son yi kennan ..

DEENI ya saki yatsun Hannu nablah da kyar .

ya shiga zariya acikin makeken office din yana furta duk wata addu'a dayasani Dan neman sausauci a gurin Allah.

da taimakon Allah dana doctor saira aka samu numfashi nablah ya dawo daidai yasoma sauka ahankali ..

doctor saira ta sauke ajiyar zuciya ganin numfashin nablah ya dawo daidai ,shima DEENI sai lokacin hankalinsa ya dan kwanta ..

Doctor tace muje mr DEENI Ina son magana da kai, ya gyada mata kanshi kawai batare yace mata komai ba sai ma zuwa yayi ya zauna kan kujera yana furzar da huci me gauraye da tashin hankali.

Doctor saira ta zagaya ta zauna tana dubansa Na wasu Yan dakiku sannan ta saki numfashi kana tace .
"yanzu Mr DEENI yakake ganin za'a bulowa Lamarin yarinyar, kaga dai yadda ta daga hankalinta akan 'cikin jikinta ?

Jikinsa a matukar sanyaye yayinda gabadaya yanayinsa ya sauya 'cikin lokaci daya da kyar ya iya bude bakinsa gurin cewa ki barni daita kawai zansan yadda zanyi handover din koma ta yadda komai zaizo da sauki .

Wlh yarinyar tayi matukar tabani tausayi sosai yanzu kowaye mutumin da Yayi mata 'cikin ?

Nima abinda nake son sani kennan DEENI yabata amsa da hkn.

A gsky idan ba,zaka damu ba zanso nashiga 'cikin lamarin binciken Wanda Yayi mata 'cikin jikinta ...Wannan ba damuwarki bane ba km hurunmin ki bane da son sani Wanda Yayi mata ciki DEENI ya katseta ta hanyar ce mata hk ...

A dan kausashe yacigaba da kaina zan nemo duk Wanda Yayi mata hkn sannan Na zartar da hukuncina akansa ..

Ok hk ma Yayi
Amman kasoma da rarrashin ita yarinyar firstly ko zata tuna Wanda Yayi mata haka kafin ka zartar da komai.

Yace uhm alamun yaji ....

Cike da natsuwa Ta tsura masa ido kawai tana sake dubansa da nazarinsa sosai kana tace dan Allah in maka wata tambaya Inda bazaka damu ba ....

Ya dago rikitattun idanunsa ya zuba 'cikin nata kana ya sake ce mata uhmmmm...

Ina son sanin matsayin yarinyar nan a gurinka? ..Yayi tsaida da ranshi tare da yin shr yana nazarin abinda zai ,daga karshe da yace mata cousin's muke daita . Ok shiyasa naga duk hankalinka ya tashi to Allah kiyaye gaba .. doctor saira nagama fadar hk ta Mike tsaye tana gyara farar rigar jikinta ta nufi kofar fita Domin son zuwa duba peticent dinta ..



Kusan awa daya da fitar doctor saira sannan nablah ta farka ... da wani matsanancin kuka har da shesheka deeni dake tsaye akanta ya matso sosai kusa daita ..yana shafa sumar dake baje a kanta.
Ahankali ya dinga jero mata sunnu babu kwaukwautawa.
, shr kawai tayi tana kukanta batare datace masa komai ba.

Yasa hannunshi ya dagota tare da jinginar daita .sannan ya zauna kusa daita ganin yadda ranta ke a jagule da bacin ran halin datake ciki.
yasashi Mikewa tsaye 'cikin tsanyi jiki Ya nufi dan karamin fridge din doctor saira ya dauko ruwa mai tsanyi ya zuba mata a cup ya kara mata cup din a daidai lip's dinta, yashiga bata ruwan da kanshi .

Sai dai kadan Tasha ruwan ta cire bakin daga cup din tare da jan naunauyen ajiyar zuciya.. DEENI ya ajiye cup din a gefe daya , ya tsura mata idanunshi yana kallonta ji yake tamkar ya rungume ajikinshi ya rarrashita ,hk yaji ..'cikin muryarsa kasa kasa yakira sunanta tare ,
Da kamo tafin hannuta 'cikin nashi yana shafa byn hanunta da nashi hannun ahankali ..
bata amsa masa ba ,sai numfashi da take saki akai akai .

muryasa a kasalance ya sake Kiran sunanta nabeelah kallonsa tayi da shanyayyun idanunta.
ido cikin ido suke kallon junansu , gabanta yashiga faduwa da sauri Wanda Shima sai dayaji hkn atare dashi ..

wai garin Yaya hk ta faru dake ne ?

Shr tayi bbu amsa dan gabadaya wata irin kunyarsa ce ta rufeta ta kasa cewa komai sai kallon 'cikin idanunshi da take ..sai da suka dauki sama da minti goma a hakan suna kallon juna ko wannensu ya kasa dauke idanunshi daga kallon dan uwansa , km kowannesu da abinda zuciyarsa ke sakawa ...


DEENI ne Yayi karfin halin janye idanunshi daga 'cikin nata kana yace tmbyrki fa nakeyi ?

Da kyar Ta iya bude bakinta Wanda Yayi mata nauyi Ta dan turo tsukakken karamin bakinta 'cikin wata irin murya Na Wanda yaci kuka ya koshi tace wlh Allah bansan ya'akayi hk ta faru dani ba , takarasa fadir hk wasu siraren hawaye nabin gefen idanunta daya tare da sunkuyar da kanta kasa .

,dariya taso subuce masa Yayi saurin dannewa.. ai kuwa kiyi gaugawa sanin yadda akayi kikayi ciki .Ko km tuna Wanda Yayi miki ..

Ta dago da sauri tana dubansa ta km fashewa da wani gigitaccen kuka Ni wlh Allah bansan inda zan nemo Wanda Yayi min ciki nan ba tana fadar hkn ta km maida kanta ta sunkuyar .

...Ya km danne dariyarsa a karo Na biyu , to yanzu ya za'a yi kennan da

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment