Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rage rawar kai dan idan ya fahimci haka zaki sha wulakancin, da karshe km mutuncinki ya zube a gurinsa.

ga zaton ummi zata ji zeenat din tace ta hakura da auren DEENi din ne Amman sai ganinta tayi ta duro daga kan gado ta zube gabanta durkushe.
, taji tace idan dai har kin amince ummi inshallahu bbu abinda zai faru .

Ummi tayi shr ta tsura mata idanu tana kallonta ummi tace kina nufin kin amince zaki auri DEENi kennan ? Zeenat tayi shi shr takasa cewa komai ba sai karyar da wuya datayi , ummi ta sake duban tace ke..bafa zan yarda da auren nan ba . take zeenat ta fashe da wani irin kuka tana bawa ummi hakuri ta amince dan Allah abin ma ya daina bawa ummi mamaki , yadawo bata tsoro ,.
Cikin kuka zeenat ,tace ai shi yace yana sona " to ta yaya ke zakice A'a ummi tabita da wani irin kallo tausayi , aranta kuma tace ya'yan yanzu sam basu da kunya . wani irin son zeenat din ne taji yana ratsa ko wani part na jikinta.
ga tarin tausayin yarinyar dake matukar damunta ,Amman hakan ba zai sa taji zata iya amincewa da muradinsu ba .
ta kau da tausayin yarinyar a ranta ta hade fuskarta tamau ,sannan tace ke dan ubanki akan na hana aurenki DEENi ne zaki ,ta sani gaba da kuka "dan bakisan ciwon kakin ba ,danma ke shashace ko shi dayace yana son naki" bawai damuwa yayi dake ba.
tunda har zuwa yanzu bai kawo kansa gareki ba.
sai kece zaki wani damu mutane da kuka akanshi ,cikin wani irin sabon kukan zeenat tace bagashi ke yayi miki maganar ba .
Ummi tace OK dan yayi min maganar shine may . ni zai aura ko ke ,da kyar ta iya sausauta kukanta sannan tace ummi dan Allah ki amince mana tunda day har shi ya furta da kanshi".
ummi taja tsaki ta mike tsaye tace ni masa, ban waje tun banyi ball dake ba shashar bazan kawai.ta wuce parlour
tavarta zeenat nan durkushe.
aiko zeenat naganin haka ta fashe da wani kukan har da shesheka .

Da daddare misalin karfe tara ,DEENi zaune a parlour shida ummi suna kallo Amman jifa jifa take sako masa hirar duniya " shi dai jinta kawai yake , yayi tamkar bbu abinda ke damunsa Amman shi kadai yasan abinda yake ji aransa' zeenat ta hado masa coffee tazo har inda yake zaune ta ajiye masa nan kusa dashi ta juya zata bar gurin ko kallo bata ishe shi ba ballanantana yasan ko ita wacce, hakan da yayi ne yasa ummi taji ba'adadi aranta . muryasa a kwasashe yace ke.....ta juyo ahankali hade da zuba masa idanunta shima ita yake kallo da ritattun idanunsa ,yace dawo ki dauki abinki konace miki ina bukatane" da sauri ta zeenat ta girgiza kai, ya kau fuskarsa kmr bashi yayi maganar ba .
bai sake cewa komai ba ,km bai kalli inda ummi ke zaune ba, ya mike kan three site yayi kwanciyarsa " aransa yace akanki zan dinga huci takaici abinda ummi tamin" tunda tace bazata auramin ke ba.
nima na hakura da auren naki" sai ta jikaki tay tasha .
kunya ne hade da tsoro suka taru sukama zeenat rubdugu , taji gabadaya kakafunta sun Gaza daukarta " ana cikin haka shemah tashigo da sallamarta "kai tsaye wajen ummi ta nufa ta zauna tana gaishe da ummi "ta amsata cikin sakin fuska , .
,sai sannan ta juyo tana kallon inda zeenat ke tsaye kikam tamkar an dasata' km sai a lokacin idanun shemah yaKai ga DEENi,dake kwance idanunshi a lumshe. itama idanu ta zuba masa tana kallonsa , tana jin wani irin ajikinta yayinda gefe daya zuciyarta ke wani irin dokawa da sau da sauri " shi km kwata kwata bai ma san Allah yayi ruwan mutun a gurinba " ahankali ya mike tsaye yana wa ummi sai da safe "a ciki ta amsa masa dan takaici abinda yayiwa zeenat " suna hada ido da ummi yasakar mata murmushin gefen baki hade da yakashe mata idanunsa daya wanda ita kadai tagani " da sauri ya haye step ,.
yana barin wajen atare suka sauke ajiyar zuciya daga zeenat din har shemah " .
dan har gara shemah ma akan zeenat din dan ita gabadaya a frigice take "idanunta ta dan juya da niyar satar kallon inda ummi take , ai ko take suka hada ido daita ummi kalli zeenat din tana watsa mata harara dan gabadaya tagama bata haushi .

yana shiga dakinsa ya fada kan bed dinsa ya jawo system dinsa kennan idanunsa yaKai ga phone dinshi dayaga almost 12 miss cul da sauri yasa hannu ya dauki wayar yayi dealing number daya Gani bugu daya biyu "fk ya dauka yace ka kyauta angon zeenat" bukatarka ,ta biya ai dole kashare mutane. DEENi yaja tsaki mtssss sannan yace dan Allah ni rabani da wannan zancen naka na banza" haka kurum kasa mutun a one chance,.
gashi kaja wa mutun wulakancin kawai ,fk yace wulakancin Kuma a gurinwa DEENi ya tabe baki tamkar fk din na ganinsa sannan yace a gurin ummi mana.
to meyya faru inji cewar fk.
sai da DEENi ya jima bai yi magana ba kafin daga baya ,yaja wani irin numfashi yace ummi fa taki amincewa da shawarka ,sai ma wani yawo ake min da hankali kmr za'a bani gold.
fk ya kwashe da dariya yace mutumina kodai ka zurma ne, irin wannan jin haushi haka.
DEENi yace kai nifa na hakura da yarinyar nan wlh ,dan gaskiya bazan jura wannan wulakancin ba .
ga mata nan dayawa a waje suna bina kmr su lashe ne " fk yace tsaya ranka ya dade ba haka za'a yi ba, bari zamu samu big dady da zance nasan komai zaizo da sauki .
ko Kuma kai me zai hana kasa zeenat din da kanka.
DEENi ya sake jan tsaki yace maganar bazan kennan ai inda takaicin yake kennan haba ai kauyancine a wajena na tsaya ina gayawa wannan yar karamar yarinyar kalmar so .
fk yace kaji irin ta ko kana son yarinya Amman girman kanka na neman cutar dakai "DEENi ya katseshi " hade da cewa kai fa dan matsala ne , nasha gaya maka ka daina cewa ina son yarinyar nan, zan dai aureta ne kawai fk yace Shikenan ajiye wannan zance.
bari gobe inshaallahu zanzo muje gurin big dady DEENi baice komai ba ya katse wayarsa .



MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO


Page 11-12


Washegari bai tashi da wuri ba sai wajejen shabiyu na safe yatashi. yashiga, bathroom byn ya fito ne yayi tsaye gaban mirrow yana kallon every part of him ,tsawon lokacin yana tsaye yana kallon kansa ta mirrow kafin daga baya ya janyo wata karamar stood dake gefe ya zauna .
hannushi ya dora a saman fadaden kirjinsa yana shafa kwantaccen gashin kirjinsa hade da lumshe idanunsa "shi kansa yasan duk matar data mallakesa matsayin mijinta bakaramin Lucky Tayi ba .

cikin sanyi jiki tamkar macce yasoma shafe jikinsa da body lotion " DEENi na kashewa kanshi kudi fiyye da tunanin may karatu ,
mikewa yayi cikin tafiyarsa ta kasaita ya nufi cikin bedroom din shi dan saka kayan " har ya nufi kofar dazata kaishi parlour" sai ya tuna ana jiransa dan haka yaja tsaki mtssss sannan ya nufe kofar bedroom dinshi byn yashige tare da cewa koma waye zai tafi idan yagaji da zama dan yanzu baida lokacin kowa .


Shiryawa yayi cikin wasu hadadun kananan kaya wando blue jeans da riga longslive" wani irin kyau Allah yayi masa na daukar hankali" ya isa kan durowa ya kwashi wayoyinsa ya zuba cikin aljihun wandonsa "ya sanya takalmansa mai sawun ciki ya zura hannushi daya cikin dayan aljihun .


Shemah ce zaune a parlour DEENi take zaman jiransa "wacce tun karfe tara na safiyar ranar ta dako samamko son ganin DEENI din.

da farko bedroom din ummi ta nufa , sanin datayi dole zai shigo gurin ummi ,ganin har ummi tagama abinda take tadawo main parlour dinta yasa itama tabiyo bayanta , .
Ganin tagaji da zama kusan 1 hour tana zaune zaman jiransa Amman bata ga alamun. fitowarsa ba yasa tacewa ummi dan Allah takira mata shi .

Ummi takirasa tasanar dashi bai ce da ummi komai ba dan kusan da haushi yatashi . Ita Kuma ganin yayi shr yasa tace mata taje part dinsa .


Koda ya yafito falonsa yaga mutun zaune shi duk tunaninsa FK ne ko cikin abokan aikinsa kallo daya Yayi mata ya dauke idanunsa daga kanta "yi yayi tamkar bai ganta ya nufi hanyar fita. ta taso da sauri tana kiran sunanshi " cigaba yayi da tafiyarsa danshi a ganinsa bai ga abinda zai sa ya tsaya ba ,.
ganin saurin bazai mata ba , dan haka ta kara da dan gudu da sassarfa har ta cimmasa ,a daidai cona da zata kai mutun main parlour din gidan tasha gabansa da sauri tana sauke ajiyar zuciya hade da cewa dan Allah yaya katsaya magana nake son yi dakai .
dubanta yayi tamkar bazaiyi magana sai Kuma yace meyye matsalarki dani ? Dan ji Yayi kmr ya dauketa da maruka " Kalmar daya fada ne yasa taji zuciyarta ta tsinke " Tayi wani irin tsalle kmr zata tafasa kirjinta ,.
Tayi shiru tana tattaro kalmar dazatayi amfani wajen fahimtar dashi abinda ke ranta .
cikin sanyi murya yace ina zaton kin manta ko ni wanene shiyasa kika tareni , sai da ta saita kanta sosai, ta'aro jarumta takara akan wanda take da" sannan tasamu kwarin gwiwa. cikin marairaicewa murya irin ta masu neman taimako tace dan Allah yaya" kadan bani aron lokacin uziri ne dani.
yamata wani irin duban dayasa yanhanji cikinta kadawa sannan yace uhmm ina jinki kuma ki tabbatar da uzirinnaki mai ma'ana ne .
"da idanunta ta amsa masa dan gabadaya ilahirin jikinta kirma yake tsabar rudewa datayi har wani gumi take fitarwa na wahala.
tun ba yau ba DEENi yasan shemah nason furta wani abu gareshi Amman rashin ganin fuskarsa yasa taki tunkarsa shi bema san dalilinsa na tsayawa ba .
Shi kansa yasan dole wannan ranar zata zo komai daren dadewa ".

ahankali take sauke ajiyar zuciya saboda fargaban da tashin hankali , abinda zai biyo baya " numfashi taja hade dayin kasa da kanta dan sam bazata iya kallon kwayar idanunshi a wannan lokacin .
Ahankali tasoma magana muryata kasa kasa cikin in...inna ,tace daman ..daman..ina son sanar dakai " ina..ina so.....da hannushi ya dakatar daita" tun bata kai ga karasa maganarta ba tare da buga mata wata irin razananniyar tsawa wanda yasa ba shemah ba ,har zeenat dake kokarin fitowa daga dakin ummi zuwa parlour "ta koma cikin daki da sauri " ta manne da jikin kofar hade da cewa wayyo... Allahna me Kuma yasame sa haka cikin tashin hankali ta sake mannewa da jikin kofar . , hatta ummi dake zaune a falo say da taji amon muryasa ,wani irin kallo yake jifarta dashi yace kina.... me uhmm repeat what u say , lip's dinshi cikin bakinsa yana cizawa sannna yace what ar u try to say ,ya sake jiho mata wata tambaya, still shr kake jin shemah ba bakin magana Amman gabadaya ilahirin jikinta ya dauki kirma .
Cikin isa da takama yace u better keep what'ever you won't say before I sikater you now jikin shemah yacigaba rawa kafafuwanta suka Gaza daukarta dana sani kuwa tayishi yafi cikin buhu , ya tsareta da mayatattun idanunsa " murya a kwasashe yace na sake jin kin Kuma furtamin wannan bazar kalmar wlh azim zakiga yadda zanyi da namanki stupid girl kawai.
ya ja tsaki ya wuce abinsa ta tsaya nan tana bin bayansa da kallo ranta a bace batasan lokacin da Hawaye yasoma zubo mata tana tunanin yaushe ne zata daina kuka akan son DEENi mutumin da take matukar so tamkar ranta mutumin da mata ke rububin son shi mutumin dayake jama mata aji ga shegen kyau da kwarjini " nan ta zube kasa ta risgar kuka ahankali hade da sa hunnta duka ta toshe bakinta dasu .

Zeenat dake tsaye jikin byn kofar dakin ,banda kirma bbu abinda jikinta keyi , tsabar frigice jin abinda shemah ke kokarin yi' domin taji duk abinda ya faru tsakanin yaya DEENi da shemah tsabar tsoro ne ya hanata fitowa ,wani irin kishi ne taji yana taso mata tun daga kan tsintsiyar kafarta yana bin ilahirin jikinta hade da kashe mata duk wani gabobin dake jikinta , taji a ranta da tana iya fitowa,. tabbas da ita kadai tasan yadda zatayi da shemah, tsinuwa kuwa iri iri bbu wanda zeenat bata aikawa shemah ba .

, ahankali zeenat ta sulale kasa ta dora hannuwanta duka bisa kanta.cikin kuka take cewa Shikenan ummi tacuce ni zata kai ni tabaro "gashi taki yarda da aurena ,da yaya DEENi ga wasu can suna neman farautarsa .
,ba tasan tana shirin jefa diyarta cikin halaka bane akan tilon danta.
dan ita yanzu ji take zata iya yin komai akan DEENI .
Ahankali Tace ita yanzu yazatayi da ranta , idan Kuma yace hakura daita fa ? Taji gabanta fadi
Da sauri tasoma girgiza kanta tace hakan ma bazai taba faruwa ba inshallahu sai ta aure yaya DEENi mijinta ne ita kadai , .
dan ita yanzu wani irin son DEENi din ne yashigeta na farat daya ,kmr kar taji ya furta yana sonta ...itama taji tana maseefar kaunarsa , Ita taji ta Gani zata iya rayuwa dashi akowani irin hali.
kawai,a hankali ta sake ta saki wani irin marayar kuka mai ban tausayi tana furta ummi karkimin haka dan Allah ..kar min haka ummi ke uwace gareni har da rabi .
dan Allah karki rabani yaya DEENi wlh zan iya zama dashi a haka , duk munin halinsa ina son shi " tunda harshi ne ya furta yana sona ...
gabadaya ta rikece da wani sabon kuka tana sambatu .
kuka tayi sosai har da shesheka ahankali ta sauko da hannuta bisa kirjinta" ta dafe kirjinta dataji yana mata wani irin ciwo zuciyarta na dokowa da sauri da sauri zeenat ta runtse idanunta dan ita kadai tasan yadda take ji.....

ta ciki dakin zeenat ke rizgar nata kukan ,yayinda shemah da ke waje durkushe ta nata .


Taku yake cikin izza da jin kai da jin shi wani ne yake takunsa har yakaraso ya zauna kujerar da umminsa ke zaune ya dora kansa kan cinyarta "ita Kuma ta'ajiye jaridar dake hannuta tun soma jin amon muryasa ta daina karatu datake "ya sakar mata murmushi gafen baki tamkar bbu abinda ke damunsa ,yace gud morning my first lov ....
ta daura hannuta bisa sumar kansa tare da fadin morning my son yakatashi lfy , ya dan tabe baki sannan yace nut bad ....
tace ya'akayi ne son me kakeson cine akwai dinshi iri iri akan darning wanda orready zeenat tashirya komai .
turo baki yayi cike shagwaba har zaiyi magana " kome ya tuna sai Kuma ya fasa cewa komai " ummi ta tsurawa fusharshi idanu tace kayi shr ya lumshe idanunsa muje kayi breakfast din ina lura da kai tunda kasoma zancen yarinyar nan bakason zama ma a gidan ballanantana Kaci abinci ahankali ya ware idanunshi akan umminsa sannan yace first lov na koshi fita ma zanyi yanzu ....



MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO


Page 13-14



Bangane fita zakayi ba byn ko breakfast bakayi ba ina fa hankalce dakai fa duk kwanakin nan bakason cin abinci,
ina zaka ma tukun danaji kace fita zakayi naga week end ce yau .ta hade fuska ta mau hade da zuba masa idanunta.
Ya dan yi murmushi gefen baki har dimple dinsa ya lotsa" kyaunsa ya sake bayyana" ya mike daga kan cinyarta ya zauna sosai shima yana kallon yanayin umminsa" yana jin yadda soyayyar Ummi nasa fiyye da komai nasa "yana sonta baya son damuwarta itace duniyarsa sannan itace ke tattare da duk wani farincikinsa tana tsantsar " son shi da nuna masa duk wata kulawar da uwa kadai zata iya yin haka .

Hannuta yakamo duka cikin nasa ganin yadda ta damu muryasa a sanyaye kmr koda yaushe yace am so sorry my first lov muje zanci tayi murmushi tace kai ko hade da dan dungure masa kai "dan bazata iya fushi dashi "shi kadai Allah yabata " batada. Kmr sa duk duniya . Cikin dan daga murya Ummi tayi kiran zeenat .
DEENi ya yamutsa fuskar sannan ya langwabar da kai yace kibarta kawai "first lov .
ki zuba min da kanki nafi son naci dagareki dan ma banson wahalar dake ne ma da sabon girki zaki min yakarasa fadar maganar cike da shagwaba " ummi ta dubesa ta sake yin dariya tace Allah yashirya min kai yace Ameen yana kashe mata idansa .

byn yagama cin abinci duk da bawani abin kirki yaci ba "Amman hakan yatiwa ummi dadi ko bakomai ya dan saki ranshi ba kmr kwanaki ba" wayarsa ce ta sake karade parlour da kara wanda tun soma cin abincinsa yake jin kukanta "Amma ya" share.
ahankali yasa hannu ya dauki wayar yana kallon screen din " sunan FK yagani rubuce yana wayo "tabe baki Yayi kana ya manna wayar da kunnenshi , , FK najin alamun an daga wayar yace Yayi angon zeenat da girma "kujerarka . DEENi yaja tsaki yace ya'akayi ne" sarkin matsala.

bangaren FK kuwa shekewa Yayi da dariya sannan yace ina waje ina jiranka fa dan banson nashigo muyi westing time dan nasan halinka da son jikin tsiya " shima DEENi bay wani damu da shigorwasa ba dan baya son ummi tasan inda zashi ,

'Umminsa yake kallo har sanda yagama" waya sannan yace mata shi zai fita sai ya dawo tayi masa a dawo lfy " mikewa Yayi tsam cikin tafiyarsa ta kaisata ya nufi hanyar kofar fita ya daura hannushi kan handle ummi takira sunansa ya juyo yana dubanta tace kar kade fa yayi murmushi yace love you mum ya murda kofar ya fice .

Tsaye ya iske FK shi kadai jingine da jikin motar DEENI hannuwansa rungumeta da kirjinsa DEENi ya Mika masa suka gaisa sannan suka wuce kai tsaye gidan big dady.

FK na gaba DEENi na biye dashi a baya har suka karasa cikin gidan suka nufin inda suka san zasu tarar da big dady .

zaune suka hango tsohon mai tarin shekaru da dattako,sai dai" ya dan manyanta kadan domin shine "dan" Muhammad bello khaliyal na farko Kuma shi ke yanke hukunci ga duk abinda yataso dangane da komai" na cikin family .

Zaune yake idanunshi manner da medical glass "da Gani kasan nakara lafiyar ido ne.
suka karaso inda yake da sallarmasu ,da fararsa yake dubansu.
ya ajiye jaridar daily trust din dake hannushi gefe cikin sakin" fuskarsa dauke da murmushi ya amsa sallamar sannan suka gaidashi ya amsa yana tambaye aikinsu" suka ce alhmd .
shr yabiyo baya tsawon lokacin kafin da tsohon ya dago ya sake dubansu.
da fk, suka hada ido dan DEENi tun byn gaisuwar da Yayi masa Yayi kasa da kansa yana kallon yatsun kafarsa" tsai Yayi yana nazarinsu duka sannan yace lfy dai naganku haka duk da yana ganinsu koda yaushe "amman wannan zuwan nasu da dan banbanci "sai daya sake maimaitawa, tambayarsa sannan fk Yayi gyaran murya yasoma yi masa bayanin abinda ke tafi dasu.
Sannan yakara danashi maganar tsakaninsa shemah .
big dady yaji dadi Sosai matuka da jin haka duk da yasan kusan irin aure da akeyi kennan a family din .
Amman duk da haka yaji dadi fiyye da kowani aure da'akeyi family din.
Yana murmushi yace har kun daidaita junan ku kennan ?
fk Yayi tsuru tsuru yana kallon big dady" yayinda shi DEENi har zuwa yanzu kansa na soke a kasa" yana jin duk abinda big dady ke cewa. take yaji karfin gwiwarsa tayi kasa big dady yace uhmm kun gama daidaita kanku ?
still fk ne ya sake bashi amsa yace A'a sai dai shi DEENi ya sanarwa umminsa" amman bata amince da abun ba.
big dady ya kira sunansu daya byn daya, a tare suka dago, suka zubawa masa ido.
big dady yace kuje ku nemi amincewarsu ku daidaita tsakaninku inyaso sai asan abin yi

DEENi zaune tamkar an dasa shi ji yayi kmr kasa ya tsage ya shige ciki haka yaji " dan wani irin kunya yaji tamasa rubdugu dan haka da kyar yasamu ya iya Mikewa tsaye suka bar part din jikisu duk a sanyaye barin ma fk da bai taba tunanin haka ba .

Suna fitowa daga part din big dady" DEENi yasoma zagin fk yana bude masa wuta , yace daman ka kawo ne a sake nuna min iyakata ?
,fk yace haba DEENi ka natsu mana musan abinyi "wlh ko ni kaina bansa haka zata faru ba dan Allah kayi hakuri ka sausauta wlh na dauka komai zai zo da sauki shiya gaji nace muje . wani irin duba DEENi ke jifansa dashi " DEENI yace ok wani sabon rainin wayon zaka sake kawo min .
gabadaya fk yakasa cigaba da magana illa idanu daya zubawa DEENi yanzu yace son zeenat yake" yace masa sam ba haka ba .
DEENi ya tsaya sosai suna kallon juna shi da kf .
a fusace yace kasan Allah kasan yadda zakayi da haukar, damuwar da kaman nami dan ban ai keka kabani irin wannan gurbataccen shawar ba.
Gabada ka rusa min komai , fk dayaga hassala shima jin zantuttukan da DEENi ke furtawa .
A harzuke yace ai bani nace kazo min da shawarar taka ba " iya abinda naga zan iyayi ne" na sanar maka.
Kai tsaye ka fito kace daman can

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment