Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiyo sautin muryarsa Sai ,gabanta yayi mummunar faduwa.

Ahankali Ya karasa shigowa parlour gabadaya fk Na biye dashi a baya .
har zata dago idanunta da niyar kallon inda suke tafasa.
ta maida Hankalinta sosai kan TV dake aiki a parlour tare da amsa sallama aciki batare da ta dubeshi ba Shima Dan sanin mahimmancin sallamar datayi ne Yasa ta amsawa.
" Dan Tasha alwashin bazata km gaida shi ba tunda baya amsa gaisuwa.

Fk yakarasa shigowa parlour Sosai,ahankali idanunsa suka , sauka akan nablah dake zaune Kusan minti biyu ya dauka tsaye yana kallon bakuwar fuskar daya gani agidan ,yaso kwarai ya dauke kansa daga dubanta Amman ya kasa yin hakan.
,a zuciyarsa yake tasbihi Ga ubangijin halitai Dan rabon shi daganin kamilalliyar macce mai tarin kyau da kwarjini irinta ya Dade ,kai shi bai ma taba ganin ba .

Gabanta ya tsananta bugawa da sauri yayinda a 'cikin jikinta ta dinga jin ana kallonta km still har lokacin taki ta yarda ta juyo bayanta Dan tasan deeni ne tsaye .
Sai dake dubanta Wanda bata sanshi ba km tayin hakan ne sbd gujewa kanta wulakanci daga gareshi .

haka kawai taji ta takura a gurin takasa sakewa shanyayun idanunta dake kan TV ta lumshe gabadaya hankalinta baya gangar jikinta ta matsu su bar gurin ko tasamu natsuwar zuciyarta.
, Amman hakan ya gagara samuwa Sai gani tayi ma sun samu gurin sun zauna kujerar dake facing dinta suna cigaba da hirarsu.

safeena ta gaishesu suka amsa a tare amman ita nablah takasa bude bakinta ta gaidasu Sai ma mikewa datayi tsaye 'tana gyara hijab din jikinta Tayi hanyar step .

fk yabi bayanta da wani irin kallo .yana tunanin ko wacece ita a kasan ranshi.shima oga deeni tun shigowarsa zuciyarsa ke kanta Amman ganin yadda Tayi musu banza tamkar bata gansu ba.
, yasa zuciyarsa ta sosu kwarai ranshi ya dinga baci , ballanantana da yaga fk din yayi mata kuriiiii da idanu yana kare mata kallon, hakan ya sake hassala zuciyarsa ,haushinta tare da takaicinta suka taru suka mamaye ruhinsa.


'Tana shiga dakinta ta kwanta ruf da ciki 'akan gado tana sauke ajiyar zuciya wayyo.. wayyo.. Allahna wannan wacce irin maseefa ce take shirin ruguzamin rayuwa ?
meke shirin faruwa dani?

hakika wani mummunar abu Na kusanto rayuwata da Al,amurana gabadaya.
,domin yawan faduwar gabar da nakeyi ta yiwa a tun sanda nazo gidan nan wanda narasa dalilin jin hakan .
Ahankali ta dinga maganar zuci da kanta batare tasani ba .

Ahankali taji an bude kofar dakin safeena ce tashigo ahankali 'tana kiran sunanta .


Ya km Muna zaune Muna hirarmu zaki gudo daki ,kibarnk Ni kardai ?

kefa Naga alamun zaman kadaici baya damunki fa Sai ma Naga kmr baki jin dadi ..

nablah Tayi murmushi yaqe may tattare da takaici kana tace wlh bbu komai safeena km bbu abinda ke damuna , kawai dai Ina son Na dan kwanta na huta ne sbd Ina dan jin bacci ,kafin Aunty Zeenat ta dawo .

Ke dai ki fadi gsky ba wannan ne dalilin dayasa kika dawo daki ba . safeena ta fadi hakan 'tana kokarin zama gefen nablah , nifa Sai Naga kmr shigowar bros ne Yasa duk kika rikece kika kasa zama .

Nablah dake kwance taji gabanta ya sake faduwa jin abinda safeena tace dan Haka a sukwane ta Mike zaune 'tana bin safeena da wani kallon mamaki .
Muryarta a sanyaye tace ko daya ba abinda kike tunani bane ,kawai day Ina bukatar natsuwa ne.

to Dan me ma zan rikece nakasa zama Dan Naga yashigorsa .
Ni karfin shigowata daki yana da nasaba ne da banason Aunty Zeenat ta iske ne a parlour,n sbd gargadinta gareni if not me zaisa Na taso sbd wani alhalin ba zamansa nake yi a gidan ba .


Me zai sa nataso sbd wani alhalin ba zamansa nakeyi a gidan ba ...safeena ta sake maimaita mgnr nablah a ranta ,har ta bude baki da zumar zatayi magana Sai km Tayi shr sbd wayarta data dauki tsiwa, ta duba screen din wayar tana picking din call din 'tare mikewa tsaye dan barin dakin .
'Byn fitar safeena nablah tacigaba da zaman shr tare da tunani iri iri Wanda Kusan yawancin tunanin Na ahlin gidan su ne .


Bangaren faruk kuwa nablah Na karasa bacewa idanunshi ya maido da hankalinsa Ga deeni tare da tmbyrsa wacce wannan yarinyar may zafi Haka ?

Wani kallon wulakancin may tattare da haushi deeni yajuyo yana watsawa fk tare da jin takaicin tmbyr da fk din yayi masa.
, kallon gefe ido Shima fk yayi masa kana yacigaba ,dan Allah a Ina ummi tasamota ko tare da safeena suka zo ?

Deeni yayi masa banza tamkar bashi da yake ba ,kai dan banzan yaro ne wlh wani lokacin kana jin mutune kake nakkasasu. Zuciyar deeni gabadaya tagama cakudewa ta cure kanta guri daya 'ta daina kai kawo a gangar jikinsa.
tarasa sukunin kanta kai kawo tsabar takaicin fk .

Sai da fk yayi ta maimaita tmbyrsa sannan deeni ya furzar da iska may zafi ta bakinsa tare da harde hannuwansa guri daya a fadadden kirjinsa ya fara mgn 'cike da dakewa da yatsina fuska yace housemaid din ce ....

fk ya ware iduna yana kallonsa da gaske kai amman gsky yarinyar batayi kama da housemaid ba wlh. wannan Ai kamata yayi ace 'tana aji 'tana daukar darasi domin karatu ne yafi dacewa daita .
,deeni ya gyara zamansa yakoma rigingine akan kujera dayake yana sakin ajiyar zuciya tare da yin shr ....tsawon lokaci fk Na zaune har ya fidda ran deeni zai sake yin magana Sai km yaji sautin muryarsa a sanyaye ,sanadin karantu ne yakawota aiki .
Fk ya saki murmushi sannan yace ayya ..itama tasan abinda yafi dacewa daita kennan.
to me zai hana ka taimaka mata kamay daita Ga iyayenta sannan ka dauki nauyin karatun nata kmr yadda kasaba taimakawa mutane marasa galihu irinta .

Tsab deeni dake zaune yana sauraron bayanin fk yayi masa kallon baka da hankali 'cikin sarkamewar zuciya da rashin tsoro tare da jin zafi furuncinsa deeni yace baza,a takaimaka mata ba.
Yacigaba , wannan bazanr yarinyar da bata da tarbiyya zan dauki nauyin karatunta" yarinyar da kwata kwata batasan me ake Kira da respect ba kana kallon yadda ko kallon mutunci bamu isheta ba ,Ni wlh haushi ma kabani da naga yadda ka tsaya kana kallonta tare da zuzuta wani wai kyau gareta ko me mtssss yaja tsaki .

fk ya kwashe da wata uwar dariya matsalata da kai kennan idan baka son mutun ,wlh har naji yarinyar tabani tausayi .
Mtssss deeni ya sake jan tsaki .

Tabaka tausayi ko to ka dauki nauyin karatunta man ,Ai kaima Naga kana da karfin dazaka iya yin Hakan.
Fk numfasa tare cewa waneni wannan Sai Ku manya ..nan dai suka bar zance nabla suka shiga abinda yakawo fk.



Wasa wasa rayuwar deeni gabadaya tasoma canzawa 'acikin yan watanni nan.
rabonshi daya samu natsuwa da farinciki har ya manta tun kafin zuwan nablah gidan.
Dan duk sanda zai hadu da yarinyar Sai yanayinsa ya sauya hakan ma ko 'cikin baccinsa ita yake ganin zaune a gefen tare da wasu kyawawan yara tana Miko masa" masu tsantsar kyawu sosai har kagara yake gari ya waye ya daura idanunshi akanta .yanzu kam yasoma gasgata tunaninsa na mayya ce yarinyar idan kuwa ba Haka bane to 'tana da alaka da mutane boye.😍😍



Sannu ahankali sule direbansa ke jansa har xuwa , unguwar gatan kowa dake iyanu - paja .



Nisa kadan da gidan da oga deeni yabashi address sule yayi parking ahankali tare da juyowa baya yace may gida mun iso Ga gidan can ya karasa fadar Haka yana nunawa deeni gidan da yatsansa .


Deeni dake hakemce a bayan mota ya sake gyara zamansa yana karewa gidan da sule direbansa ya Nuna masa .
,tsawon lokaci deeni ya dauka yana kallon gaban gidan tare da Allah wadai da wannan aure da zaiyi.

yanzu irin gidan da zai nemi aure kennan gabadaya kofar gidan a rushe yake bbu wata ishashiyar katanga Sai dan kwanun da,aka zagaye shi dashi tsabar babu . Gabadaya unguwar a hargitse take bbu kyan Gani .

Ahankali kalaman umminsa ke dawo dashi 'cikin duniyar tunaninsa yayinda natsuwarsa ke kokarin shirin barin jikinsa domin gabadaya tunaninsa ya ta'alaka ne da yadda zai nemi auren yarinyar a gurin iyayenta. Yanzu shi wani irin aure zaiyi ?Anya kuwa zai iya auren .

Tunda sule direba yayi mgnrsa ta karshe Bai sake yunkurin cewa uffan ba Dan gudun maseefar ogan nasa ,a sukwane sule yaji sautin muryarsa 'cikin kunnenshi fita kayo min sallama da may gidan iya abinda deeni ya fada kennan yaja bakinsa yayi dif...


Sule ya kashe motar Tare da barin AC motar a kunne ,ya fito yana aikin raba Idanu ta inda zaiga yaron aike .

unguwar shr... sakamakon ruwan saman da,a kwana ana sulawa ,jifa jifa mutane ke wucewa Sai da sule Bai yi dacen samu Wanda zai aika 'cikin gidan ba .
dan Haka ya koma ya jingine jikinsa ajikin mota yana addu'ar kar Allah Yasa oga ya fusata har zuwa sanda zai samu dan aike .


Fitowar wani kyakyawan dattijo ne daga gidan yasa sule jin farinciki a ransa yayinda hankalinsa ya kwanta 💯.

Dattijon dake kokarin gefta shi yana faman xuba fada ,sule ya karaso da sauri Tare yi masa sallama yana kokarin tsugunawa dattijon yayi saurin Miko masa hannu suyi musabaha.

suka gaisa sule Na tmbyrsa ,dan Allah baba may gidan daka fito daga 'cikin sa nake nema , dattijon ya saki murmushi Tare cewa Ai nine may gidan .

Sule yayi murmushi yace yauwa daman may gidana ne yake son ganinka yana 'cikin wacce motar dattijon yabi hannun sule da kallo galleleyar motar dake parke nisa kadan dashi yabi da kallo.
Yace to to yaro bbu komai kana iya sanar may gidan naka Gani .


Sule ya juya 'cike da natsuwa ya sanar da deeni ,dake hakemce abayan mota ya ware kafafunsa yana jiran tsammani .
Ce masa yakaraso nan .

Sule sake koma yasanar da dattijon.
, dattijon Bai wani damuba yakarasa kai tsaye har inda motar take sule bude masa sashen da deeni yake ahankali idanun deeni suka sauka akan mutumin dayake kallo yanzu a gabansa tamkar an tsaga kara da yarinyar dake zaune a gidansa .


Dattijon ya Mikowa deeni hannun domin su gaisa deeni ba Dan son ranshi ba ya bashi hannun Sai dai fuskasa a dan sake ba yabo ba fallasa .

Yace idan bazaka damu ba kana iya shigowa daga ciki magana ce may mahimmanci takawo gareka .

Dattijon yace bbu wata damuwa yashigo mator batare da an rufe ba Sai da deeni ya numfasa zai mgn sai km yayi shr 'yana may toshe hancinsa da hanky sakamakon wani wari kwata daya bugu yayi nasarar shiga hancinsa .ganin Haka Yasa dattijon janyo kofar motar ya kulle .sannan DEENI yasa samu damar soma mgn.

abinda yakawo gareka Naga wata yarinyarka ne Ina son ka aura min ita bisa sharadin deeni yasa hannunshi yajanwo wata yar karamar jaka may shake da kudi , ya bude zan mallaka maka fiyye da wannan kudin ..

dattijon daya Ga jiya km yaga yau ya kalli kudi masu tarin yawa sannan ya dago ya kalli deeni yana murmushi .
Kwata kwata kasa dauke idanunshi tsohon yayi daga kallon DEENI Sai ma nazarinsa da yake .


Kusan minti goma yana nazarinsa har DEENI ya tsargu kansa sannan dattijon yace yaro kennan wacce daga 'cikin yaran nawa kake so da aure kafin aje ga mgnr kudi.
bbu wata shakka ko tsoro deeni yace nablah....

dattijon yace garama datazama nablah ce Yar albarka duk da inajin haushinta a raina amman hakan ba zai sa nakasa ji dadi aurar maka daita ba .

Deeni ya sauke naunauyen ajiyar zuciya jin abinda tsohon yace hakan ya tabbatar wa kansa samunta bbu wani shamaki sai dai yayi mamakin yadda dattijon yace yana Jin haushin diyarsa ta 'cikin .

Dattijon yacigaba Sai dai ita wannan yarinyar da kake magana akanta bata nan , asalima ban san inda take ba ahalin yanzu ,deeni numfasa sannan yace wannan ba zai zama da wata damuwa ba muddin ka amince zaka bani aurenta.
,nima tafiyace a gabana zuwa wata kasa ,dan Haka auren kawai nake da bukata a daura inyaso idan Na dawo daga tafiyar sai ayi bikin kaga itama nasan zuwa lokacin ta dawo .

Dattijon yaji dadi mgnr Sosai daman yana 'ciki da abinda Salmah Tayi masa Na daukar masa yarinya, takai gidan aikatau 'byn yace Bai amince akai masa ita aiki ko Ina ba.
,yanzu hakan ma daya fito daga gidan yana fada.
" shi da Salmah ne yake ce mata ta dawo masa da diyarsa muddin batason bacin ranta , dan shi baya wani bukatar Taje neman kudin karatu yafi son ta zauna agabansa har zuwa sanda zai aurar da abarsa .

Ahankali dattijon ya dawo daga duniyar tunani daya lula yace yaro zuwa yaushe kennan kake son auren nata .

Deeni yace idan zai yiwu ayanzu Ma zan fi so Haka dattijon yace may zai hana yiwar hakan wannan Ai abune may sauki tunda Sai ka dawo daga wata uwa duniya za'a yi bikin .

Deeni yayi shr kawai yana kallon dattijon dake zaune Kusa dashi yana kokarin amince masa batare da yasan ko shi waye ba .


'Cikin mintina da basu fi talatin ba mlm salisu ya nemo aminnansa guda hudu na nan kusa da cikon shi biyar .

Sai deeni da sule aka daura auren nabeela salisu gulunbe da nasuruldeeni aliyu khaliyal bisa Ga sadaki naira duba dari cassssssssssss. Wanda sule yakasance wakilin deeni yayinda wani aminin mlm salisu din ya zama wakilin nablah .


Sule yaji mamakin wannan auren daka daura abu kmr a al,mara to daman ogansa aure zaiyi batare da sanin kowa , to wannan wani irin aure ne Haka .

Byn angama daurin auren deeni ya mikowa mlm salisu jakar kudin amman mlm salisu yaki kabar sai ma cewa da yayi nasuru ka rike kudinka domin bbu abinda zanyi dashi .

duk da bansaka km bansan daga inda kazo neman auren diyata ba Haka kawai naji Na amince nabaka auren nablah Ni kawai abinda nake bukata daga gareka shine ,idan Allah Yasa kadawo daga tafiyar dazakayi lfy kasadani Ga danginka amman bazan karbi kudinka ba .

Wani irin kunyar dattijon ne yakama DEENI yaji tamkar kasa ta bude ya netsina ciki dan kwata kwata baiyin tunanin dattijon zaiki amsar irin wannan kudin ba .a wannan zamanin da ake ciki, na kaka nakayin.
da wuya kasamu irin dattijon duk da alamun bbu dayake hangowa atattar dashi muhalinsa kadai yaisa ya tabbatar wa mutun yadda yake gudanar da rayuwarsa.

Haka kawai deeni yasamu kanshi da kiran dattijon da baba ... dan Allah karkayi min Haka kar kace baza karba kudin nan ba

Da farko nayi tunanin bazaka amincemin da aurenta bane 'cikin wannan lokacin danafi bukata shiyasa kaji na daura sharadi akai .

Amman yanzu dattakonka gareni yafi karfin wannan kudin .
dan Haka har ga Allah Na baka wannan kudin idan ma kana bukatar wasu zan karaka maka ..

mlm salisu yace Sam bazai karba sai wani abokin mlm salisu din yasa baki sannan yasa hannu ya amshi jakar kudin Tare da sanyawa deeni albarka .

daman km yana da bukatarsu. Sukayi sallama da zumar Sai Allah Ya dawo dashi ..


Mlm salisu Yashiga gidansa cike da murna yana duban Salmah da nurat Sai mahafiyarsu dake zaune suna tattaunawa akan batun nablah din .

Yakarasa shigowa yana murmushi Tare da ajiye musu jakar kudi a gabansu ya zuge.

Kudin suka bayayyana bbu Wanda Bai ji tsoron ganin kudin ba sbd tsabar yawansu .

Mlm salisu yace
Ku duba kuga ikon Allah sanadin diyata nabla Yar albarka Na samesu suka shiga dubansa da alamun tmby a saman fuskokinsu .

, yacigaba yanzu nan Na daurawa nablah aure da wani mutumin kirki dayazo neman aurenta km shiya bani wannan kudaden da kuke Gani .

mahaiyarsu saratu wacce suke Kira mama tace wacce nabeela kake mgnr ka daurawa aure .

,Ina da wata nabeela ne byn diyata ,ita din aka daurawa aure yanzu.
gama sadakinta nan ya fidda wasu kudin .

Mama tace ,cewa zakayi kasiyar min da yarinya kawai bawai ka daura mata aure ba amman abinda zai sa hankalina ya kwanta sanin inda nablah take a halin yanzu .
Dan haka duk ma Wanda kabawa aurenta kabashi gaibu . Ka dai daura aure dashi ne Amman bashida mata .


Mlm salisu ya hade rai Ke dai kika sani Yar Bakin ciki kawai Ai ba tun yau nasan bakya son cigaba Na . Yau dai tawa ce to Na aurar daita Ga Wanda nake so km kina zaune za'a yi bikin nablah ta wuce gidan aurenta .

Duk magangun da mlm salisu ke yi mama Tayi shr batare da ta sake cewa komai ba sbd alamun da Salmah Tayi mata Na kar tayi mgn .

Ke km Salmah mlm salisu ya kanta wlh wlh kinji ransuwar muslimi kwana biyu kacal nabaki ke dawo min yarinyata may kan sa'a da kan arziki kafin nasoma cin uwarki ,dan wulakanci ke kina zaune a gidan mijinki lfy Sai tawa Yar ce ta iya zuwa neman abin duniya ke kar ma Na sake ganin kafarki a gidan nan muddin ba da nabeela bane shasha banza dabatasan ciwon kanta ba yaja tsaki yana kokarin shegewa ciki kuryar da jakar kudinsa . Gabadayansu da idanu suka bishi da shi hankalinsu ,a tashe.



Kirrrrrrrrrr... kirrrrrr ......kirrrrrrrr... karar bell ya cika koina a gidan.
nablah dake tahowa daga kan step ta hanzarta saukowa da sauri ta nufi Bakin kofa ta bude .

Kabiru may wankinsu Zeenat ta Gani tsaye a 'bakin kofa yana sakar mata murmushi itama murmushi Tayi masa tare da gaidashi.

Daidai lokacin da motar deeni tasanyo kai 'cikin estate din idanunshi suka sauka akan nablah fuskar nablah dake sakarwa kabiru murmushi .
take annurin dake fuskarsa ya dauke gabansa ya daki uku uku ya fadi yayinda zuciyarsa tashiga aikinta data saba wato dokawa da sauri har sanda sule yayi parking motar idanunshi nakansu yakasa daukewa.

mlm nablah kennan ya gida da aiki inji cewar kabiru .
Nablah tace duk lfy wlh ya naka aikin Shima ya amsa mata da lfy suka shiga hirarsu sama sama dashi sbd sun dan saba .

Kusan minti goma deeni yayi , zaune a mota ya kasa fitowa sakamakon dokawar da zuciyar takeyi da sauri ya dinga jin tamkar ana masa wanka ne da tafashashen ruwan zafi ne ajikinsa yayinda natsuwarsa ke kokarin barin gangar jikinsa take gumi ya rufe shi takoina ajikinsa .
ahankali ya ciro hanky daga aljihun gaban rigarsa ya goge gumin dake tsaftsafo masa batare da ya sauke idanunshi daga kallonsu ba har zuwa sanda yaga kbr ya Miko mata kaya a wata jaka ya juya yana sake yiwa nabla murmushi .
Wanda sauran kadan zuciyar deeni ta tarwatse tsabar frigici .
Ahankali yasoma kokarin fitowa daga mota byn sule ya bude masa .


'Tana shiga gidan taje ta, ajiye kayan a inda tasaba ganin ana ajiyewa sannan ta nufi kitchen tasoma aikin girki hade da wanke kayan da akayi amfani dasu, kasancewa yau Sunday ce.
Laraba tana church ummi kuma sun fita tare da aunty zeenat da safeena ba yadda ummi da safeena basu daita akan tazo su fita tare tace A'a saboda ita bata damu da yawan fita ba ko agidansu.

cikin sanyi jiki take aikinta da zeenat ta gama koya mata kalar abinci da mai gidan yafi son cin ne yau aka bata practices dan aga yadda kwarewarta tayi.

kamshin turaren mat Hamilton 27 datashaka ne ya haddasa mata faduwar gaba Wanda tun safe take jinta Haka .

DEENI tsaye abakin Kofa kitchen din yana aiko mata da kallon tsana byn yaje yayi freshe up .

'Cikin tsananin tsoro da fargaban abinda zata Gani ta juyo karaf idanunsu suka sarke cikin juna take zuciyoyiinsu ya bagu... gabansu Yashiga faduwa .
da sauri tayi kasa da kanta ta dinga karanto duk wata addu'a datasani na neman tsari .

Ahankali ya tabe bakinsa yakaraso cikin kitchen din Sosai .
"cikin muryasa may matukar dadi da sauraro yace ke..uban me kike Jira da har yanzu baki gama abinci ba .

wani irin shock...ne yajata ,jikinta yasoma sheking takasa furta komai ya daka mata wata irin razananniyar tsawa ke ..
Ba magana nake miki ba yakarasa maganar cikin kunar rai .

"muryarta na rawa tace dan Allah kayi hakuri wlh nakusan gamawa yace you are very stupid dake da gamawarki kina tunanin an daukeki aiki ne dan kidinga yiwa mutane iskanci da aikin ba'a kan lokacin ba.

mamaki hade da tsoro sukayi nasarar lullubeta ko kwakwarar motse gagararta yayi .

yayinda haushinta ya sake turnuke wuyan DEENI a harzuke ya fizgo hannuta yace ke me kike takama dashi ke waye ma ubanki duk fadin Africa da har zandinga miki magana kiyi banza dani tayi kokarin fizge hannuta sai dai kashi ...ta kasa abunku ga soja.
gata yarinya karfin su ba daya ba , ko namiji DEENI yarike da wuya ya iya kwatar kansa.

ranta ya baci matukar dan haka itama fusace tace dan Allah malam ka sakar min hannu .

kallon baki isa ba ya watsa mata sannan ya sake matse mata hannu Sosai yana kallonta cikin tsigar wulakancin hade da sake damke laulausar fatar hannuta.

yace ki kwace hannu mana idan kin isa , tasoma girgiza kai dan wani irin radadin azaba da takeji acikin kashin hannuta .
tayi kasa da kanta 'tana zubda hawaye tausayin kanta domin ita takawo kanta cikin wannan maseefar datake ciki.

ashe rabon wahala ne yakawota gidan batasani ba .

sai da yaga ji dan kansa sannan ya wurgar da hannuta nata da karfe ya juya cikin tafiyarsa ta kasaita da jan hankalin duk wanda ya kalleshi.

minti goma kacal na baki kigama sannan yakarasa barin kitchen.
ta durkusa kasa tare da fashewa da wani matsanancin kuka tasoma datasanin zuwanta aiki uguwar lekki ,da kyar ta iya mike.

tacigaba da aikin girkin hawaye nabin kuncinta sai da ta kammala da komai ta shirya akan dening area sannan tazo ta wuce ta gabansa yana kwance a kan three sites hannunsa dafe da kirjinsa har tayi step daya zuwa uku tajiyo shigowarsu ummi ta dawo ahankali hade dayi musu sannu da zuwa .

ummi da safeena suka bita da kallo byn ta

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment