Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rungumo kafafunta please ummi karki ce hk kice komai mu kice rayuwarmu kece farincikinmu kece jigon komai agurinmu karkiyi mana hk ummi yana mgn yana kuka yana rokonta tayi hakuri tayi masa aikin gafara ko a'lamura zasu daidaita gareshi.

gabadaya jikin ummi yayi tsanyi zuciyarta tayi rauni tausanyi dan nata ya huda kirjinta.
take komai ya kwance mata ita kanta bata kaunar abinda zai nisantata dashi shi kadai gareta sai marainiyar Allah zeenat .
Tana tsananin son deeni Amman soyayyar zeenat dinta daban ce kasancewar kaunar dake tsakaninta da mahaifiyarta .
tsawon lokaci suka dauka ahaka deeni nacigaba da kuka yana bata hakuri.
da kyar yasamu ya shawo kanta hannuta na rawa ta daura bisa kanshi ta shafa sumar kanshi Kana ta zauna ya daura kanshi bisa cinyarta yana kuka yana bata hkr .
yayinda ita km ta cigaba da shafa sumar kanshi muryarta a matuKar sanyaye tace is OK son kukan ya isa hk komai ya wuce Allah yayi maka albarka Allah sanya albarka arayuwarka data iyalinka gabadaya.
bai samun damar amsa mata ba sbd kukan dayake.
shi kanshi yayi muguwar nadamar abinda yayiwa mahaifiyarsa mafi soyuwa azuciyarsa... Ka tashi ka zauna akan kujera deeni ya tsinci muryar mahaifiyarsa..
ya dago kanshi yana dubanta yana girgiza mata Kai first love barni anan .
ya sake gyara zamansa agabanta suna fuskanta juna.
ummi ta numfasa tana dubansa gabadaya duk ya rame yayi dogon wuya data tuno dalilin abinda yasakashi dawowa hk tayi saurin runtse idanunta gam tana kukan zuci da blaming din Kanta.
itace silar fadawarsa cikin Matsala yana zaman zamansa da matarsa.. Da kyar ta bude idanunta tace ina zeenat dina take yanzu tana gidanka ne?


Ya girgiza mata kanshi sannan yace dukansu basa gidana.
Gabanta ya buga yashiga dukan uku uku bakinta na rawa tace ina zeenat Dina take ?
Tana gidan babanta....... ummi tayi dif kirjinta na wani irin lugude wasu sabbin hawaye suka zubo mata tasoma magana cikin harshen indiyanci , akan zeenat ta gujeta ta daina sonta sbd kuskurenta nason ganin rayuwarta ta inganta agidan danta. kuka take sosai tana daura laifin komai akanta.
deeni na rarrashinta da goge mata hawayen idanunta first love ki daina kuka yanzu zanje na dauko miki zeenat dinki bake kadai kika tsinci kanki cikin damuwar da tashin hankalin rashinta ba.
ni kaina nayi nadamar ramuwar gyayar da nayi niyyar mata yacigaba da gogewa ummi hawayenta .
ita km sai girgiza masa Kai take muryata na rawa tace kaje deeni ka... Kawo min zeenat a duk inda take ko zuciyata da ruhina za samu salama. sai da ya sake goge mata hawayen idanunta sannan ya Mike jikinsa a sanyaye ya juya yasoma tafiya hard ya kawo bakin kofa yana daura hannushi kan handle yaji an murda kofar.
ya dan dakata .. ahankali aka bude kofar.... Zeenat yagani tsaye sanye da doguwar riga da hijab lulube har kasa .
ido cikin ido suke kallon junansu kowace da abinda zuciyasa ke sakawa akan dan uwansa.
ahankali ta raba ta gefenshi ta wuce shi batare da tace masa uffan ba .
ya meida kofar ya Rufe ya biyo bayanta ummi na arba da zeenat ta Mike zumbur jikinta na rawa bakinta na rawa gurin fadar ma..ma... na tana me ware mata hannunta duka alamun tazo gareta zeenat ta fashe da kuka takasara tare da shigewa jikin ummi.. Ummi ta rungumeta ajikinta tana kuka.
a she tunani bai zama gaskiya a she zaki kawo kanki gareni byn duk abinda na miki? Gabadaya na ji kunyarki zeenat .
naji kunya akan yadda fasaha ta dauke min na kulla miki gadar zare da hannuna akamiki kishiya batare da saninki ba. ...
ummi ki daina kuka bazan iya barinki ba ummi dake kadai nasaba arayuwa bansan dadi uwa ba sai ke ummi.
ban rayu da mahaifiya ba sake ummina Kin nuna min gata fiyye "dan" cikinki ummi duk inda zanje nayi rayuwa aikin banza ne idan bana tare da ke.. dan bazan iya jurar rashinki ba ummi. ina sonki duk duniya nan banida kmr ki hakika kin raya zumuncin dake tsakaninki da mahaifiyata.
kin duba byn mahaifiyata domin nasan ko tana Raye da wuya tamin abinda kika min kin nuna min gata kinsa ban Yi kukan maraici ba.. takarasa mgnr tana kuka ummi ta yafito deeni da hannuta yakaraso ya zauna kusa daita tayi saurin goge hawayenta kana ta kamo Tafin hannushi ka bata hkr deeni....Ka Tausayawa rayuwarta har yanzu ina jin xeenat araina tmkr fareeda.. Ita kadai ke mayemin kurbin fareeda arayuwa.
ita kadai ke dabemin kewar fareeda a duk sanda hkn yataso min .....takarasa mgnr idanunta na fidda wasu ruwan hawaye.. jikin deeni a sanyaye yace first love tun jiya nake bata hakuri kwana nayi ina kiran wayarki danata Amman akashe .fisrt love nima abin atausayamin ne .ina bukatar tausayawarku ke da zeenat....
Nasani... Nasani deeni Amman Kasan mace tafi bukatar tausayawa akan namiji.
ummi ta hade hannusu gurin daya ta damke cikin Nata sosai .
atake zuciyoyinsu ya buga sbd tuno da rana da suka mallaki junansu amatsayin ma'aurata ranar da ummi tabasu amanar junansu tare da tabbatar musu da su din yan'uwan juna ne mafi kusanci da juna .
atare suka dago suna kallon juna kowanensu zuciyarsa cike da tausayawa...
muryarsa a raunane yace am very sorry zeenat.. I Din mean to hot you .
ummi ta saka baki kiyi hkr diyata... Duk nice silar cutuwarki denni bashida laifi komai. Ki daura laifi gareni zeenst nice na miki laifi bashi ba.
zeenat tashiga girgiza kanta tasa hannuta daya tana gogewa ummi hawaye muryarta raunane tace ummina na yafe miki ...nasan duk abinda kikayi kiyi ne sbd ni... Nasan ko diyar da kika haifa acikin ki irin kulawar dazaki bata Kennan .
ummi ki manta da wani abu makamancin wannan ya taba faruwa arayuwarmu wallahi wallahi ummi na yafe komai .
shima yaya na yafe mishi duniya da lahira Amman ummi akwai wani hanzari ba gudu ba.
Dan Allah kicewa yaya ya sawake min aurensa dake kaina tunda ni baya sona baya son farincikina.
bansan wani irin kiyayya yaya yake min ba wanda ya manta kowa da komai ya manta da irin rayuwar da muka gudanar a farkon aurenmu ya tsugunawa wata Mace agabana yana rokon taso shi ummi....
Idan har nacigaba da rayuwa aure dashi wlh ban kyautawa kaina ba ...
amman dan hakuri na Hakura da komai na dauki kaddarata nima zanje gaba nacigaba da rayuwata.....
Deeni yayi sororo tare da tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta cike da mamaki abinda tace.
ummi tayi gyaran murya tace mamana bazan takuraki ba sbd tun farko aurnku ma ban takuraki ba ballananta yanzu Amman da zakiyi hkr ki rungumi kaddararki dana nafi kowa dake cikin duniyar jin dadi.
burina ba wuce naganku kuna rayuwa tare ba . abinda bakusani ba batun yanzu nake son ganinku cikin inuwa daya ba.
Amman sbd sanin halin deeni danayi yasa naki hadaku tun farko ko lokacin dayazo min da zance aurenki naji matukar dadi Amman ganin ba sonki yake ba alokacin kawai yana son yin auren ne dan na matsa masa yasa naki amincewa .
Amman kikace kinji kin gani zaki iya...

Ahankali ummi ta meda idanunta kan deeni bazan takurata mata ba idan kaji kana bukatar matarka Kanason cigaba da zama daita.
kasan yadda zaka Shawo kanta idan km kasan bakada bukatarta arayuwarka sakar min abata.
domin abinda wani yagaji dashi yaga yayi masa tsufa shi wani yake so da dauki ganin ya mallaka.
deeni ya runtse idanunshi da sauri sbd jin haushi da takaicin zance ummi.
Ummi na mgn fadar hk ta Mike tsaye tabar gurin ta nufi dakinta tana goge hawaye .
bathroom tashiga ta zauna kawai tarasa abinda ke mata dadi.

zeenat ma zame hannuta tayi cikin nashi yana kallonta Tabi byn ummi.
a sikwane Yabi bayanta da wani irin kallo .

tana shiga dakin ummi ta fashe da wani sabon kukan sbd har lokacin tana jin mugun kaunar mijinta.
sonshi acikin jinin jikinta yake .rabuwa dashi babban tashin hankali ne gareta Amman zata dakewa zuciyarta ko zata samawar ruhinta salama sosai take kuka tana tuna rayuwarta acikin dakin datake yanzu.
da yadda abubuwa suka dinga gudana daya byn daya suna wucewa da yadda ta rayu da matsanancin kaunarsa batare daya Sani ba.
da yadda ya dinga jiyar daita dadin aure ta dinga jin dama lokacin zai dawo mata da ta sake sabuwar rayuwar me inganci.
ashe daman zai kara aure arayuwarsa shi yasa lokacin datace yayi mata alkwarin bazai mata kishiya ba yace a'a zeenat bani ne da rayuwata ba.
ban isa Na tsarawa kaina rayuwa ba.
Aure nufi ne na Allah idan Allah ya kaddaromin sai nayi.
kedai ki tabbatar da kin tsare min hakina .
babu mamaki idan kika tsaremin hakkina dake kanki ta yuwu gaba naki kara aure .
duk da babu yadda Allah baya juya lamarinsa.
tuno wannan zance nasa ya sake haukatata ta dinga kuka tana datasani arayuwarta.......
ahankali ta mike tsaye tana safa da marwa ...motsin turo kofar dakin taji anyi tayi saurin goge hawayen dake tsiyayowa daga idanunta batare data juyo ba.
ahankali taji an meda kofar an rufe alamun an shigo dakin.
jingina bayansa yayi da jikin kofor tare da rungume dukka hannuwasa akirjinsa.
ya tsurawa bayanta idanu kawai yana kallonta yayinda ahankali ya dinga jin wani irin tausayinta yana ratsa kowani shashi na gangar jikinsa hakika bata cancanci wulakaci ko sabanin hk daga gareshi ba a kullun yana yabawa da tarin kaunarsa gareshi.
cikin wani irin sayin Jiki yakaraso gareta ya rungumeta ajikinsa ta baya yana me juyo daita suna fuskatar junansu.
atare suka sauke ajiyar zuciya .
ya tallabo fuskarta da hannuwashi yana Kare mata kallo ya bakinsa ya tsotse bakinta muryarsa a matukar raunane yace ki bini mu koma gida zeenat mukarashe rayuwar aurenmu tare.

nifa bazan koma ba domin bazan iya cigaba da rayuwa dakai ba...... Daga yanzu kasawa ranka mata daya kacal gareka..no... no.. don't do this to me zeenat . kiyi hakuri please kishirya yanzu mu wuce tare.
ta girgiza masa Kai alamun bata komawa gidansa yin duniya yayi daita Amman taki amincewa ta bisa..

hk yagaji ya Hakura yabar gadan. Kai tsaye gidan big dady ya nufa ya duba yaransa ita kam nablah bai samu damar ganinta ba sbd taki yarda sukaga juna.


Hk ya koma gida ya shirya zuwa office.
koda ya dawo daga office gidan ummi ya nufa rarrashin duniya yayiwa zeenat amman tace Sam ya barta lokacin data aureshi bai matsawa rayuwarta ta aureshi ba Dan hk yanzu bata Yin auren ya sallameta kawai ta aure wani .
kmr ya mutu hk ya dinga ji alokacin datake fada masa hk..
a matukar fasace ya fito tmkr zai tashi sama .
ko gidan Big dady bai je dubo nablah ba. Ya wuce gidansa
dan yasan haukanta ya zarta na zeenat.
sai dai gabadaya bai da salamar zuciya .
Daren ranar da kyar yasamu bacci barawo ya samu nasarar daukarsa cike da matsanancin damuwa.


washegari zeenat gabadaya akwance take ta zube tayi wata muguwar Rama sallah kadai ke tadata koda ko abinci ta manta rabon data sakawa cikinta ummi tayi ta matsa akan ta saki ranta taci abinci Amman furrrrrrr taki.






Gabadaya komai ya cukudewa deeni guri daya takowani bangare babu sauki da sausauci gida da office baida natsuwa tafiya kawai yake Amman zuciyarsa tap take da damuwa da tsantsar tashin hankali da tunani mara misaltuwa.
daga office kai tsaye gidan ummi ya nufa yashigo gidan bakinsa dauke da sallama ummi kadai ya tarar tana zaune ta amsa masa tana kallonsa.
dan ramar tasa ta yau tafi ta kullun nunawa ahankali ya zauna tare da ajiye jakar system dinshi yace first love mun yini lfy.
lfy lau son ya aiki .
yayi dan jim sannan yace alhamdullahi kusan minti goma yayi zaune baiji motsin zeenat ba wanda abinda yasani ne matsawar ummi na guri dole ka isketa kusa daita.
jikinsa a sanyaye ya fito da system dinsa cikin wata karamar bakar jaka yasoma dudubawa yana son karasa tura sakwanni .muryarsa akasalance yace first love ina zeenat?
Ya fadi hk batare da dago ba.
Ta mike tsaye tare da bashi amsa tana sama yanzu ta tashi .
OK turo min ita first love .

koda ummi tasanar mata da sakonshi bata mutsa ba taxo a parlour ta sameshi zaune kan daya daga cikin kayatattun kujerun parlour'n ummi na alfarma system dinsa akan center tablet agabanshi yana latse latse jikinsa sanye cikin wani farin yadin volya fari kal me shegen kyau hasken yadin da kyawunsa, su suka tona asirin tsadarta kashim turaren nan nasa na yau da kullun yana nan. yacika gurin batare daya dago ya dubeta ba ya nuna mata kujerar zama da hannusa cikin harshen turanci yace have a sit.
ba mutsu jikinta a matukar sanyaye ta zauna kusan minti goma bai ce daita komai ba yanata danne dannesa ta dago idanunta tana duban agogon dake manne a parlour muryarta a sarke cike da matsanacin tsoro tace nifa gsky ina son komawa daki dan ina da abin Yi.
ya dago rikitattun idanunshi ya dubeta..ya lashin lips dinsa na kasa kana yace Kibani minti biyar local in kammala muhinman aikina.
Taja numfashi hade da kawar da kanta gefe .

ahankali ta sake kallon agogon minti biyar din tacika tana shirin sake yin mgn taga ya ture system din dake gabansa ya mike ahankali ya zagayo gefen datake zaune kafafunsa babu takalmi ya janyo wata yar karamar akujerar stood dake daf daita ya zauna ya rusuno sosai kusa daita har suna jiyo numfashin junansu.
Muzeenat........ ya Kira sunanta cikin laulausar muryarsa .
ta tsuke fuskasta sosai batare data amsa masa ba .
bai wani damu da yanayin yadda tayi ba yacigaba da mgnrsa.
muzeenat meyasa kika Xabi rabuwa Dani ki auri wani?


alhali nasan kina mugu mugun sona?


da sauri ta dago idanunta ta sauke cikin nasa gabanta ya buga da karfi take ta kawar da idanunta tace daba lokacin ban san ciwon kaina ba Amman yanzu gsky bana wani sonka.
Uhmmmmm ya sauke numfashi tare da yin murmushin yake.
nasan kin fada ne kawai sbd girman laifi da kike tunanin miki Amman in da gaske kin daina sona ki dubi kwayar idanuna ki tabbatar min da ba kya Sona ......
cike da rashin tsoro wanda duk daurace kawai ta aro tasanyawa jikinta ta Kalli cikin idanunshi tace yaya deeni na daina sonka.
bana kau... Yayi saurin katseta ta hanyar daga mata hannu tare da runtse idanunshi gam zuciyarsa na wani irin harbawa da suya muryasa a raunane tamkar zaiyi kuka yace naji na yarda kin daina sona Amman ki duba wasu abubuwa kafin kiyi tunanin barina na farko Ki duba rayuwar ummi bazata taba jin dadin rabuwarmu dake.
sannan mutane zasu zagene idan nabarki wasu ma sai Sun tsnemin akanki.
kiyi hkr ki dawo mukarasa rayuwarmu tare mu ingantata tare gidana bazai Yi hasken da nake bukata ba matsawar ba kya cikinsa .

zaman gidaka din me zanyi yaya?
ni ba da "da" ba ba samun kulawa daga gareka ba.
Ince ana hakurin zaman auren ne idan har ya'ya sunshiga tsakani.
, to ni banida ko daya atare da Kai gara kawai kowa ya Hakura .
na Kara gaba ko nima zan samu farincikin dana rasa agurinka takarasa fadar hk tana meda kukan dayaso kufce mata.

Zeenat zaki haihuwa Dani Jikina nabani zaki haihu Dani...

Zan haihuwa man nima na San da hk Amman bada Kai ba.
yanzu kinfi son kije ki aure wani ki haihu dashi bani ba..

Kina son kibarni kiyi rayuwa da wani na alhalin ina Raye?

OK kai kai ka iya aurenka a boye har da haihuwa ina Raye.
OK a she fa nice bazan iya yin hk ba Ko?

tabbas bazan iya aikata hkn ba alhalin da aurenka a kaina .
Amman ai zan iya rabuwa da Kai matsawar bana sonka?


ya sake runtse idanunshi gam sbd radadin furucinta dan ya tsani jin kalmar bata sonshi daga bakinta .

sai daya furzar da iska me gyaraye da zafi zafi kishi sannan yace dake zan gama rayuwata zeenat kece uwargidana anan Duniya km ina fatan ko alahira ki zama shugaban matana a aljanna .
ina bukatar mucigaba da rayuwa tare ke kadai kika kasan halina kika San yadda kike bi Dani .
duk wata Mace da zan kasance Daita abayanki take .
ki rigada kin sha gabanta takowani bangareni ta tabe baki wannan km matsalarkace.
matsalata ni yanzu nabarka nayi nisa dakai nayi maka Nisan da bazaka taba Kamoni ba.
ya kamo tafin hannuta cikin nashi yana murzawa cike tasasawa yace muzeenat dan Allah ki taimake ni.. wlh bazan iya rabuwa dake ba sbd ina sonki............... haka zaki tafi ki aure wani ki barni?
karka soma furtamin wannan kalmar yaya naso ka furta min ita tun ba yau ba Amman sai tsintarshi nayi abakinka durkushe gaban wata kana rokonta tasoka kana furta mata wannan kalmar dana fi son ji daga gareka ,batare da kayi alakari da ina gurin ba...
kiyi hkr ki dawo dakinki mucigaba da rayuwarmu Wlh bazan iya barinki ba sbd ina sonki.
Kabar soyayyarka zeenat tace batayi.
ka kara akan wanda kakewa na..blah wlh na yafe mata Kai dan wlh yanzu banasonka tuni ka Gama fice min arai gabadaya ya marairaice mata yana mammtsa tafin hannuta taga yana neman zube mata tun kafin yakarasa kasa tayi saurin tareshi tana juya masa Kai. kibarni zeenat sbd naga durkusawa nablah danayi agabanki shi yafi tsaya miki arai kibari kema namiki ko zuciyarki zata rage radadin datake miki akaina.
Wasu hawaye masu ciwo da radadi suka shiga zubo mata .
Kanta Kawai take girgiza Masa uhmmmmm uhmmmmm bazan taba lamuncewa da hkn ba yaya.... Bazan lamunci ganinka durkushe agabana ba........ Ni ni dai kawai aurenka yarigada ya fice min rai yayi wata irin zabura ya Mike tsaye wanda hakan yasa hantar cikinta kadawa.yashiga zariya adakin gumi na tsaftsafo masa ya dumkule hannushi guri daya ya cure sannan ya naushi iska.
yajuya ahankali jikinsa na wani irin kirrma ya dauki naurarsa me kwalkwaluwa bai sake cewa daita komai ba ya fice daga gidan..

nan ta zube kasa tana rusa wani irin kuka Amman bataji zata km zama dashi matsayin mijinta... Da daddare suna zaune ita da ummi .
ummi ke tmbyarta yadda sukayi da deeni bata boye mata komai ba tasanar Mata yadda sukayi dashi ummi tace mamana kiyi hakuri ki koma dakinki Allah ummi bazan iya cigaba da zama dashi bane .
Allah ya hada kowa da rabonsa ummi agabaki agabana agaban big dady yaya ya tsugunna gaban karamar yarinya yana kuka tasoshi... Alhalin nida muka dauki sama shekaru takwas da aure bai taba mafarkin furtamin ba....

niko me zai saka nacigaba da zaman aure dashi yaje can Allah yabasu zaman lfy da matarsa nima Allah yabani nawa mijin ummi ta goge hawayen dasuka zubomata a boye....


Duk wannan gurmin da ake nablah na gidan big dady batasan komai ba . kwana biyu nablah takoma gidan deeni wanda da kyar big dady yasamu ya Shawo kanta ta amince ta koma gidan da Zumar taje tashirya ranar lahadi zasuje gidansu gurin mahaifinta har shi.
Amman tana komawa gidan tana ganinsa ta tada balli ta sake tuburewa ta haukace masa agida tana kuka tace ko sama da kasa zata hade ko duniya zata nade koda zan rasa raina baxan taba zama agidan nan ba wallah kaji na rantse sai na barmaka gidanka km na fasa bar maka daya daga cikin ya'yana domin nawa ne ni kadai.
km da ya'yana zan tafi tunda ban yayesu ba .
ta tubure masa sosai deeni ya riko hannuta. tayi wani irin ihu hade da fixge hannuta cikin nasa ta kwasa aguje ta nufi hanyar get......... Zeenat dake cikin dakinta wanda zuwan Kennan kwasar abubuwanta na bukata ta fito sbd hayaniyar da tasoma cika gidan .

Deeni Wanda ranshi Yayi mugu mugun baci a matukar harzuke ya bi bayanta abinka ga dogon mutun tattaki yayi cikin sauri zaraf ya damkota xuwa gareshi tun bata karasa zuwa bakin get ba.
tirtirjewa tasoma Yi tana ya saketa Amman yaki sakinta sai daya shigo daita cikin gidan .
xeenat wace takarasa saukowa tabisu da kallo zuciyarta na tsananta bugawa .

ranshi a bace yasoma yaryarfa mata maruka masu rai da lafiya zuciyarsa na wani irin zafi da tafarfasa ya zaunar daita ta Mike tsaye zumbur tana watsa masa wani mugun kallo ka mareni an mareki .
ko zaki rama ne?


ahankali zeenat ta Juya ta tabar gurin ta nufi dakinta .
Dan yanayin yadda tagansu .
Ya taba zuciyarta har yasa ta dinga jin zuciyarta na wani irin suya kirjinta ya dinga bugawa da sauri da sauri ahankali tasoma karanto duk wata adduar datazo bakinta domin samun sausauci dan har lokacin babu abinda ya ragu a zuciyarta a game da kishin mijinta.

Nace zaki ramane ya sake ta dauketa da wani gigitaccen Marin dayasa har "dan" dake cikinta yayi wani irin juyawa da sauri ahaukace take saki wani ihun tana dubansa da mamaki deeni kasake Marina ta fadi hk tana nuna kanta.
Suna nan tsaye zeenat ta sauko ta raba ta gefensu ta wuce abinta.

Wlh sai Allah ya saka min .

Bai sanda haushin kalmarta da ganin zeenat ta fice yasake yarfa mata wani Marin ba yana nunata da yatsansa Muryasa a matukar harzuke ya bude bakinsa ya Kira sunanta nabeelah....

wace irin halitar mutun ce ke da baki da tausayi ?


wacce irin zuciya gareki da babu imani cikinta ?


wace irin zuciya gareki da baki yafiya?

kina son ki kasheni ne ....?
sai ga kwalla yasoma saukowa daga idanunshi da sauri ya juya mata baya yasoma mgn cike da sanyi murya matsayina da mukamina da shekaruna wanda akalla da nasamu haihuwa arayuwata da wuri da yanzu kusan ina da kamarki...
Amman duk na karyar da matsayina da girmana na durkusa miki gaban mahaifiyata gaban Matata sbd kawai nasan a miki ba daidai ba arayuwarki .
Amman duk kika kunyarta dasu.
muryata a hassale tace ai duk kaine kaja ya Ciro hanky acikin aljihun gaban rigarsa ya goge hawayensa ya juyo ahankali idanunsu suka sarke cikin juna kowanesu sai da zuciyarsa ta buga da mugun karfi gaske kawai taji ya rungumeta ajikinshi nabeeah ki taimakeni a sanda na durkusa miki ban damu da yanayin da kowa yagani ba nablah idan kin cire soyayyar Allah da manxonsa da mahaifiyata kece kike bayanta Dan Allah nablah ki taimakeni zan rike ki amana zan rikeki da kyau ki bani dama nayi miki alkwarin zan zama tmkr bawanki ta fixge jikinta daga nashi ni kabarni please nifa gsky bana jin zan cigaba da rayuwata da kai wani irin duba yake mata yana jin yadda kaunarta ke sake huda masa zuciya da bawa kowani shashi na gangar jikinsa.. Shr yayi kawai yana kallonta kafin daga bisani ya daga waya yakira sule direbansa byn yazo yace Kaita gidansu .
wani duba tayi masa kana tace ka bani ya'yana Dan wlh bazan barsu ba. Ai kinsa inda suke kije ki daukesu. Ka dai je ka dauko min su
banza yayi mata yayi tmkr bai ji abinda tace ba yana aika mata da kallon bata isa ba . ganin bashi da niyar bata yaranta yasa ta Mike ta fice abunta.
Sam bata ji wani tausayinsa ko kadan acikin ranta ba........



shi kuwa tana fita yashiga sintiri acikin parlour'n tsananin damuwa tayi masa yawa yarasa yadda zaiyi duk yadda yazaci zai shawo kan nablah da zeenat . abin yaci tura sai dai baya jin zai iya Hakura dasu.
hanyar dakinsa ya nufa. Cikin sauri ya kira wani direbansa yasa takalmi da hula ya dibi kudi masu yawa ya zuba cikin aljihun ya fita...........




Mmn sudai ce
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
AUREN SIRRI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—







AYSHA A BAGUDO


🌈kainuwa writers association

(united we stand and succed our ambition is to entertain &motivate the mind of readers)


https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

page 107




Kai tsaye gidan big dady deeni ya nufa jikinsa har tsuma yake

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment