Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cin jagwalgwalon abincinta wlh nablah ta dago shanyayun idanunta da niyar kalonsa sbd yadda taji tana sakin maganganu karaf idanunsu suka sarke cikin juna ya watsa mata wani matsiyacin kallo wanda yasa ta dauke idanunta da sauri yayinda zuciyarta tashiga dokawa .

wannan km son ranka ka fada kawai dan kaji dadin bakinka amman mgnr jagwalgwalon abinci take dafawa karya ne wannan domin bbu Inda girki nablah bazai shiga ba a duk fadin Africa.
cin jagwalgwalon abinci km sai dai kar a km domin yanzu kasoma .

dan Allah rabudashi kinji nabla tashi maza kije ki samar masa wani abu me sauki .

Nablah ta Mike tsaye amman gabadaya ilahirin jikinta bbu Inda baiyi sanyi ba ..ita kanta ba,a son ranta take masa wasu abubuwan ba darajar ummi kawai yake ci agurinta .
A sanyaye ta nufi kitchen "ahankali yabi bayanta da kallo yana tabe baki tunda daman ta gababshi zata wuce km shi yakan so yaga yadda take tafiya kmr an tsamota 'cikin ruwan tsanyi .
"yana juyowa idanushi karaf 'cikin Na umminsa sukayi four eyes .. yayi saurin dauke idanunshi . waskewa yayi tare da sosa byn keyarsa alamun kunya sai dai ya sake hade ran nan nashi tamkar yana filln daga ..uhm kawai ummi tayi tana murmushi da girgirza Kai..


nablah ta dade tsaye a kitchen tana saka da warwara abinda zata daura mishi may sauki wanda bazai dauki lokaci ba.
zuwa can ta yanke shawarar dafa masa jollouf din cuscus .

ta hada masa haddadiyar jollouf din cuscus Wanda ta wadatu da kayan hadi carrot green beans da piece koda da hanta a mamadin nama kamshin Curry da tyme ne kadai ke tashi ta barwa laraba gyaran kitchen din ta zubo masa cuscus din shake da plet ta fito hannuta rike da plet .


Tun daya jin motsin tahowarta gabadaya Hankalinsa yakarkata gareta Wanda shi kansa Bai San dalilin dayasa yake jin hk a tare dashi ba.

har takaraso ta janyo wata Yar karamar stood ta ajiye masa plet din abinci akai hankalinsa Na kanta ahankali ta juya zata koma kitchen taji sautin muryarsa ke.......
Ta juyo tare da dan tsayawa darajar ummi dake zaune a gurin.
zoki kwashe wannan banzar abincin da kika ajiye ance miki Ni jaki ne ?

A ranta ko tace Ai kamafi jaki hauka agurina .
ya buga mata wata razananniyar tsawa tsayuwar uwar me kikewa mutane ?

zuciyar tamkar zata tarwatse tsabar takaici da tashin hankali a kufule takaraso tasoma kokarin daukar plet din ummi tace barshi nablah yi tafiyarki kawai .

ta juya ...Ta koma kitchen Inda ta iske laraba tana aikin gyara kitchen tasaka hannuta tare sukayi komai sunayi suna hira ..... .

Tsawon lokaci ya dauka zaune yana operating din phone dinsa batare ko kallon arziki yayiwa abinci ba.
hakan kuwa yayi mugun batawa ummi rai" tare da hassalata .
dan duk da tsananin son da takewa tilon "dan" nata hakan bazai sa taga yayi ba daidai ba ta kasa yimasa mgn .
Dan hk a kufule tace wannan km wani sabon salon wulakanci ne hk ?
Ya dago yana kallon umminsa tare dage mata girarsa daya alamun tmby ?
minti biyu kacal Na baka ka fara cin abinci nan tun kafin raina, bai Kai Ga baci ba.
abinda ya tsani ji da gani kennan bacin ran umminsa .
km yakasance shine zaiyi dalilin shigarta halin damuwa .
dan hk bbu wani ja inja ko bata lokaci yasoma tsakurar abinci yana ci tamkar yana cin magani ba dan rashin dadin abincin ba sai dan tsagwaron wulakanci irin nasa.

Nablah na kitchen taji ummi Na kiranta da sauri ta amsa tare da barin abinda take ta fito.
,yauwa nablah jeki dakina dan Allah kicewa safeena tabaki jakata ki kawo min kinji.
ta juya kennan taji sautin muryarsa ke....dawo ki kwashe wayan nan abubuwan ..dole ta sake juyowa takaraso Inda yake duk ilahirin jikinta rawa yake.
wani irin abu taji ya dunkule mata a kahon zuciyarta ,ahankali tasoma kokari hada kayan abinci data kawo masa wanda bawani cin arziki yayi ba .
ummi ta dakatar daita ta hanyar cewa barshi nablah karki hada komai agurin nan .

Sannan tayi facing din DEENI da kyau tana harararsa kana tace kabari laraba tazo ta shige dasu .
aikin nablah a gidan nan girki ne kawai .

Sai daya yatsina fuska tare da tabe bakinsa tukun yace Ok Ai duk daya ne first lov Dan aiki Dan aiki ne, bbu wani bambanci da may girki da may shara da sauran ayyukan gida duk dai Yan aiki ne ..

Duk Yan akine Amman ita wannan nata aikin may lasisi ne wanda kasan da hk ko kana daja ne?
uhmmmm first lov Ni Na isa Naja dake ..ok
Yi tafiyar ki kinji nablah ..




Karfe biyar daidai matar gidan tashigo gidan agajiye fuskarta cike da izza da Mulki da nuna isa .
ta zauna tare da Kiran washi Allahna sannan tace ummi sannuku da gida .
ummi ta dubeta tana murmushi may cike da nuna tsansar kulawa da soyayya kana tace yauwa mamana ya gajiya da karatu ?

Kai ummi wlh karatu nan kwata kwata bbu sauki. 'cikin hk nablah ta fito daga kitchen takaraso har inda Zeenat ke zaune tayi mata sannu da zuwa tare da tmbyrta abinda za'a daura Na dare .

Sai data yamutsa fuskarta sannan tace daga dawowata zaki zo min da wani mgnr abinci tun mutun bai gama huta wa ba tamkar wasu mayunwata mtssss taja tsaki.
Ita dai nablah dake tsaye bata sake cewa komai. sai ma ummi ce, tace haba mamana ki dinga bin yarinyar nan ahankali fa kinsa bawai ta taba zuwa aikatau bane wannan shine first time dinta .
to ai tace ummi daga sannu da zuwa sai mgnr abinci .
to ya isa hk wannnan duk ba laifi bane dan ta tmby. Ni dai dan Allah ki dinga sausautawa yarinyar nan yanzu dai gaya mata abinda zatayi.
inji cewar ummi "
sai da Zeenat ta sake yatsina fuska sannan tace paten doya zakiyi min .
..muryar nablah a sanyaye ta amsa da to aunty.
Amman banason yayi kauri yayi ruwa ruwa ..takarasa fadar hk tana duban sashin da ummi take ummi ku mezaku ci ?
Duk abinda mamana zataci .

Zeenat Tayi murmushi tare da cewa Ok amman shi my hrt ki mishi poundo yam da miyar ugu sauran ki yiwa mutane shirme .

Hk nablah ta sake koma kitchen Wanda zuwa lokaci har laraba ta kammalawa da gyaran kitchen din ta fita zuwa wani aikin Na daban.

ahankali take bare doyar zuciyarta tamkar zata buga tsabar bakinciki zamanta ciki gidan ta hada source Na asaro.


Kusan awa biyu da shigar nabla kitchen.
' sai Ga Zeenat tashigo da waya a hannuta tana yatsina fuska da baki sannan tace wai har yanzu akin kikeyi baki gama ba?

nablah da ranta yake a bace matuka .
a dakile tace eh aunty sauran kadan Zeenat taja ta tsaya tana rike da wayarta har lokaci ita dai nabla dataga tana aikin dadaddana waya wanda batasan abinda take yi ba.
km kusan duk sanda take girki a kitchen sai tashigo tayi mata tsaye a ka da waya a hannuta.


byn ta fita ne sai ga laraba tashigo tace nablah ....
Ta juyo tana dubanta batare da ta amsawa laraba.
kinsa me aunty take miki Inda tashigo kina girki . nablah ta girgirza mata kanta ahankali alamun batasani ba .
to wlh video take miki .

Nablah ta Dan tsorata da mgnr har idanuta suka Dan fito waje video km name?
oho Nima bansani ba wlh amman nima hk take min lokaci da nake mata girki.
bangane video ba to tayi me dashi ... ?
nablah ta sake tmbyr laraba .
uhm kawayenta take turawa idan kin yi mistake sai kawayenta suzo har gida su zageki tasssss nima hk ta min kwanaki kafin kizo takira kawayenta sukazo suka minrashin mutunci da zagi iri iri bbu halin ramawa ... .
"nablah nagama jin karshen zance laraba taja tsaki tana jin jina girman al,amarin Zeenat.
sannan tace wanna km iskancin sai dai suyi miki shi Amman Ni ....ta nuna kirjinta da dan yatsanta daya .
wlh bazan dauka ba sai dai hakan yayi sanadiyar barina gidan nan daman km hk nake so.
laraba ta kwashe da dariya nablah kennan Ga tsoro Ga ban tsoro .nan dai suka bar zance suka shiga wata hirar har zuwa sanda nablah ta sauke girki tare da shirya dinning .
sannan ta nufi dakinta bata km fitowa ba har sai data daidaici lokacin dayakama tayi serving Nasu abinci.

sannan ta fito jikinta sanye da doguwar rigar wace ta kama jikinta sosai.
Wanda daga samanta kana hango tundun nonuwanta yayinda kasan rigar keda Shep din flay ta nade kanta da dan karami 'bakin mayafin ganin darene hakan datayi , ya sake fito da ainihin sihirtaccen siffar kyawun ajikinta.

ahankali take daga kafafunta 'cikin takunta may matukar daukar hankali kmr koda yaushe .. takaraso dinning area .
sai dai me kawai ganinsu Tayi zaune tuni sunyi nisa 'cikin cin abinci Amman Banda oga deeni Dan Haka ta juya zata wuce taji Zeenat takirata da sunan datafi tsana a rayuwarta ke..... nablah ta dawo ahankali ta tsaya batare da tace komai ba .Kusan minti Goma tana nan tsaye amman kwata kwata Zeenat bata da niyar cewa mata komai.
sai byn data gama cin abinci ne tukun ta dago fuskarta a tsine tana duban nabla dasu .
hk nace kimin asaro bance miki may ruwa ruwa nake so ba .
mamaki da al,ajabi kalar iskancinta ne ya mamaye zuciyata .amman a dake tacigaba da tsayuwa a gurin sbd bata da halin tafiya taja mata kan wani sabon tashin hankali.
magi nawa ma kika saka acikin abinci ?
nabla tace daidai Wanda zaiji.
nifa banason albarzazanci a gidana akaida magi shida a pot daya ya isa .
jiki a sanyaye nablah tace to shikennan zan kiyaye inshallahu,karma ki kiyaye taja tsaki Zeenat nagama fadar hk ta Mike tsaye tana kakkabe jikinta tabar gurin .
ba nablah dake tsaye ba hatta ummi bataji dadin abinda Zeenat din tayiwa yarinyar ba.
amman taki saka musu baki dan batason tana yawan shiga tsakaninsu tunda tare zata barsu ..

da kyar nablah ta daga kafafunta .takarasa ficewa daga gurin ta nufi BQ ta zagaya Inda Anan dakin laraba yake da fara,a laraba ta tarbeta tana dariya sai yau Allah yayi zaki zo min ?
Murmushi nablah Tayi wanda har wushiryarta ya bayyana ta gaida laraba hirarsu suka Shagayi sosai dan ba ita tabar part din laraba ba.
sai wajen takwas da rabi Na dare tare suka ci abinci da laraba sannan ta baro part din .

Tafiya take sannu ahankali 'cikin sanyin jiki da natsuwa ,ahankali iskar damuna ke kadata kasancewar lokacin ruwa da'ake ciki Wanda kusan yanayin garin Lagos kennan, basu rabo da ruwa sama kasancewar basu da rani da damuna koda yaushe 'cikin ruwa sama suke .

Daidai ta kawo wajen parking space ta jiyo motsi ta dan jiyo ahankali idanunta suka sauka akan fahad abokin deeni kawai ta kauda kanta ta juya tacigaba da da tafiyarta a tunanita Bai ganta ba.
" kawai ta tsinci muryarsa haba Yan mata irin wannan shan kamshin hk Ai akalla ko gaisawa munyi,duk da cewa zuwan nan danke nayi , inji cewar fahad Wanda oready tuni har yasha gabanta.

Take kirjinta yashiga dukan uku uku fatanta kada Allah Yasa ya furta mata kalmar so...dan ita tsoron kalma take
Km bata jin har 'cikin zuciyarta lokacin yin soyayyarta yayi.
domin tafi son ko zatayi soyayya sai ta kammala da karatunta so that sai tasamu daidai da matsayinta .
dan hk a gaugauce zuciyarta cike matsanancin tsoro tace Ina yini .
lfy lau nablah ya gida da aiki?

Kanta ta dago da sauri tana dubansa jin ya ambaci sunanta dan batayi tunanin yasan da zamanta a gidan ba . ballanantana har yakai ga sanin sunanta . yacigaba Ina son ganinki km sbd ke naxo gidan nan zuciyarta ta sake bugawa da karfin gaske..
Ahankali Ta maimaita abinda yace Tare da dan ware shanyayun idanunta akansa .
yace uhm amman idan nagama da DEENI zansa a min kiranki da fatan ba zaki ki zuwa ba.
fuskarta a daure tace Allah yabani iko tana gama fadar hk da sauri ta juya tasoma kokarin barin gurin dan ganin DEENI dake tahowa Inda suke tsaye .
duk da saurin datake hakan Bai hanata jin sautin muryoyinsu ba kasancewar sun biyota a bayanta ne..

Fahad deeni yakira sunanshi a kausashe kafita daga idanuna Na rufe meyasa baka jin shawara ne shege kawai may shegen daurin kan tsiya..

Fahad ya kwashe da dariya sannan yace Kai km meyesa kacika girman kan tsiya da kafiyar maseefa Allah bai haramta min yarinya ba amman Kai kana neman ka rabani da soyayyata.

Na dade da kamuwa da matsanancin kaunar yarinyar nan amman kwata kwata ka kasa ka tsare ka hanani fahimtar daita .
meyasa zaka hanani isar da sakon zuciyata gareta ?

Ok hk kace ?
DEENI yakarasa fadar hk cike da huci yana kallon tsakiyar idanun fahad..

Yes hk nace idan km kaima kana sonta ne kafito ka kasanar sai Na janye maka dan bazan taba iya cigaba da son abinda kake so ba.

bawai ka dinga kokari hanani isar da sakon abinda zuciyata ta kamu da matsanancin so ba
Kasan Ni ..kasan halina km kasan koni waye idan ba son yarinyar nan nake da gaske ba bazan takura kaina akanta ba .

Wulakance DEENI yake masa wani irin duba cike da tsansar tashin hankali yayinda gabadaya yanayinsa yagama sauyawa.
akansa zuciyarsa yace wannan wace irin maseefa ce hk .
Tun bai gama da matsalar kB .
Ga fahad wanda shi ya dan kwana biyu dayi masa zance yarinyar.

Ahankali Fahad yace deeni kana son yarinyar nan fiyye da yadda nake sonta wlh .
idan har kasan kana sonta zan janye amman muddin baka sonta to kabari na shiga sawun manemanta kawai .
Kai wlh Azimi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba wlh son yarinyar nan kake yi km so may tsanani fahad yakarasa fadar hk yana share gumin daya fufeshi duk da isakar dake kadawa .

Sai DEENI daya furzar da wata iska ta bakinsa may dumi sannan a zafafe yasoma managa muryarsa cike tashin hankali billahi azim fahad zaka jawowa kanka maseefa ne kawai .
km hakan zai iyayin sanadin da zamu samu mugun matsala may girman gaske da kai idan ka sake furta kalmar....




MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO




*Uhmmmm uhmmmm abin 'cikin kwai Ina jinjina gareku members Na AUREN SIRRI fans hadin kanku tattare da zaman lfyrku yana matukar birgeni Ina matukar alfahari daku wannan shafin sadaukarwa ne gareku kuyi duk yadda kuke so dashi Allah yabar zumuncin dake tsakaninmu har ila yaumul kiyamati ina addu'ar kar Allah Yasa zumuncin nan ya tsaya iya social Media kawai*


Page 76


Idan ka sake furta kalmar Cewa Ina son yarinyar nan wlh zan bata maka rai fahad ,
narasa Inda zan ajiye soyayyarta sai gun house girl dina ?
kuka fa... amman wlh ka cuceni kasan cewa Ina da tarin dukiyar da ni kaina bansan adadinsu ba.
km ta ishe nazabi duk kallar mace datayi min a 'cikin duniyar "ya "ko ta gidan uba wace km ko a wani kasa take ba wai wannan bazar house girl din ba .
Kai bama Ni ba ya nuna kirjinshi da yatsansa ko wanda nake tare dashi yafi karfin yayi soyayya da house girl .


Muddin har zaka cigaba da kudirinka akan yarinyar nan to wlh kaji narantse maka kana daidai ne da raba abotarmu tare da duk wata halaka dake tsakaninmu .

yana karasa fadar hk yayi gaba 'cikin matsanancin fushi da Bai San dalili yinsa ba hk zalika baisan meyesa duk sanda yaga yarinyar da wani nmj ba wani ya nuna alamun yana sonta hankalinsa ke mugun tashi ba .

Ko 'cikin parlour ma rigima ce sosai suka dinga yi da DEENI da fahad akan nablah har ummi ta tmbye fahad din abinda ya hadasu.
Bai tsaya boye mata komai ba ya sanarmata .

ka kyale wannan rigimamme kaji kayi abinda yakawoka kasan halin deeni sarai ba sai Na tsaya gaya maka ba ummi tacigaba nablah takai mace da kowani da namiji zai so.
Domin Tana da halayya nagari da za'a so mace domin su.

dadi ya rufe xuciyar fahad sosai jin abinda ummi tace yayinda deeni ya dago sukayi four eyes ya watsamasa wata uwar Harara tare da jan tsaki .

Banda wani uziri may karfi to wlh koni zan iya shege maka gaba akan neman aurenta dan takai mace iya mace.
sai dai kashi...akwai wani sirrin boye dake tattare da yarinyar wanda zai yi maka nakasu.
ummi takarasa mgnrta Tana sauke numfashi .

Ahankali Fahad ya furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun wayyo Allahna tare da dafe daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da hannuwanshi duka. alamun zuciyarsa bata ji dadin zance ummi na karshe ba .

DEENI dake rike da wayarsa yana aikin chatting yayi musu banza yacigaba da abinda yake .
dan tunda ummi tasaka baki 'cikin mgnr Bai sake cewa komai ba sai ma kokuwa dayake faman aikinyi da numfashinsa dake neman barin gangar jikinsa.

Gabadaya hankalin da yanayin fahad ya canza take ya koma kalar tausayi .
Yayinda zuciyarsa ke wani dokawa da sauri a frigice yace dan girman Allah ummi kitaimakamin kiyi wani abu akai wlh nayi mugun kamuwa da mugun son yarinyar tun farkon ganina daita.
Ina ji a raina matsawar bata kassnce matsayin matata ba zan shiga wani hali.


a hassale DEENI yabar abinda yake ya sake dagowa yadakatar dashi yana huci kana yace Kai wani irin jaki ne kai ?
Dabaka fahimta" da wani irin yare kake son A sake maka bayani akan yarinyar nan.
Ni kaina hanya may bullewa na gayama akanta shine karabu da soyayyar yarinyar nan amman kake ci min fuska to wlh kayi Na farko kayi Na karshe duk lokaci daka sake cewa kana son wacce yarinyar sai Na fasa maka baki . ba fahad ba hatta ummi sai da karshen mgnr deeni tasakata dry .aiko fahad ya dinga dariya yana fadin DEENI rikicin gangan .
fahad yace wlh baka isa ba tunda Kai ba sonta kake yi ba .
ta ya'ya Ni zaka hanani km wlh bazan barta ba sai Inda karfina yakare tunda ba matar wani aure bace .
zan jirata har sanda sirrin boyen zai tashi daga kanta a zafafe deeni ya Mike tamkar wani mayunwacin zaki bazoto fahad ya ji an damki makoshinsa .

Ummi ta Mike a frigice Tayi kansu sbd tasan halin zuciya irinta danta .
Meyye hk deeni daga wasa zaka maida mgn fada..barshi first lov wlh bbu wasa acikin wannan mgnr sannan
Ya tsare fahad da idanunshi ka sake maimaita abinda kace dan ubanka wlh sai dai uwarka ta sake haifo wani bakai ba .

Idanuwan fahad sukayo waje sbd mugun shakar da deeni yayi masa ummi shiga tsakaninsu Sosai tana ka sake nace deeni ko bakaji ne.
shi kuwa shr yayi yana damke da wuyan fahad da iyakacin karfinsa.

kokari fahad yake ya kwace wuyanshi amman Ina yakasa dan bakaramin riko deeni yayi masa ba ,sai zufa ne kawai ke keto masa takoina ajikinsa duk da sanyi AC dake aiki a parlour hkn Bai hana jikinshi yin sharkaf da ruwa ba .
so yake yayi magana Amman ina ya kasa dan bazai iya ba ko yace zaiyi mgnr muryarsa bazata fito ba dan hk yasoma mutsumutsun kwace kanshi sai da ummi tashiga tsakaninsu Sosai sannan da kyar da yataimaka Allah ummi tasamu DEENI ya saki wuyan fahad.

aiko yana sakinsa Tari ya sarke makoshin fahad Ya dingayi Tari yana damke da wuyansa da kyar ummi tasamu ta zaunar dashi Tana yi masa sannu tare da kawo masa ruwa .

DEENI ya zauna yana sakin numfashi sama sama tare da furzar da wata iska may zafi ta bakinsa .
Ahankali ya runtse rikitattun Idanunshi gam ji yake tamkar numfashinsa zai bar gangar jikinsa ne sbd wani irin radadin azabar daya caki tsakiyar zuciyarsa lokacin da fahad din ke furta kalmar yana son yarinyar.
fada ummi ta dinga yiwa deeni sosai tare da ce masa Inda ya sake yiwa fahad wani abu wlh zai hadu da fushinta .

Jin abinda umminsa tace ne yasa ya dinga karanto duk wata addu'a dayasan zata sanyaya masa rai .
Wlh deeni batason jin wani sabani yashiga tsakaninka da fahad akan wannan zance .
Sannan ta jiyo Inda fahad ke zaune wanda zuwa lokacin gabadaya yafita daga haiyacinsa sai numfashi yake saukewa ahankali ahankali yana rike da wuyansa dake masa wani irin radadin azaba .

tace Dan girman Allah kayi hkr fahad kaji kasan halin abokin naka rigimamme ne na bugawa ajarida banason dan Karami abun nan yazama silar lalacewar abotarku kaji dana .

bbu komai ummi komai Ya wuce amman ummi shi meyasa zai hanani son yarinyar byn ya tabbatar min da ba sonta yake ba .

Kai dai kabar zance kawai bakomai bane sai fitina irintasa .
nan dai ummi Tayi tayiwa deeni fada daga karshe ta hade su gabadaya tayi musu fada sosai 'sannnan tabar parlour tanawa tilon Dan nata addu'a.

cikin hk Zeenat takaraso parlour ta taddasu jikinta sanye cikin doguwar rigar may mugun kyau da tsansi sai daukar hankali take kmr koda yaushe dan Tana kaunar sanya dagayen riguna Sosai.

A mutunce suka gaisa da fahad ta juya Ga mijinta wanda tun shigorta idanunta da hankalinta ke kansa Tana nazarin yanayinsa .
ganin yadda fuskarshi da yanayinsa suka sauya yasa takaraso kusa dashi da sauri tare da kamo tafin hannushi'cikin nata Tana murzawa Tana kallonsa tare da tmbyrsa my hrt meyesa Meka hk?

dan gabadaya itama tsintar kanta Tayi 'cikin damuwa da tashin hankali ganin halin dayake ciki hakan km ya mantar daita komai ciki har fahad dake zaune yana bin deeni da kallon mamaki wai yau shi deeni ya rufe ido kan mace yayi masa rashin mutunci..

Kokarin shegewa jikinsa take Tana sake tmbyrsa abinda ke damunsa ahankali ya dago rikitattun Idanunshi ya xuba mata yana kallon kwayar idanunta ganin yadda tadamu da son sanin abinda ke damunsa .

Ahankali Idanunshi ke bin koina ajikinta batare da yace mata komai irin shigar datayi ta daukar hankali yasa shi damke hannuta Sosai 'cikin nashi sannan ya Mike tsaye manne daita a gefen jikinsa .
yayi hanyar dakinshi daita.
Muryarsa a kausashe yace Kai km Malam idan ka gaji da zama kofa a bude take kana iya wucewa yacigaba da tafiyarsa yabar fahad a gurin yana binsa da kallon mamaki.


Kwance nabla take akan gadonta sai faman juyi da tunanin DEENI take wannan wani irin nau,in jinsin mutun ne shi kwata kwata kowa ba abakin komai yake a gurinsa ba .
takama gadara sunyi masa yawa to ko dukiyarsa ke rudarsa ko kyawun dayake ganin yana dashi ne ?
Haushi da takaicinsa ne suka taru suka lullube ruhinta yayinda zuciyarta ke mata wani irin radadi da zafi

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment