Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ya rungumeta tsam tsam ajikinsa tare da cusa kanshi cikin sumar kanta yana shakar dadeden kamshin jikinta "take yarinyar itama ta narke masa ajiki tana taba wasu part na jikinsa cikin wani irin salo a haukace tamkar wani zaki DEENI yasoma romancing din every part of her "cikin zafi zafi ya hade bakinsu waje daya yasoma tsotsa tare da lumshe rikitattun idanu.. ........ sosai yake juya yarinyar yadda ya so batare da wani abu yamasa shamaki ba.
daidai komai yagama faruwa atsakaninsu ne ya farka afrigice zaune kmr jiya yana sauke numfashi sama sama..
tare da karanto addu'ar da duk tazo bakinsa na neman tsari daga sharin shedan ,ganinsa mafarkinsa nasaba da sharin shedan dan gabadaya yarasa dalilin dayasa yatsinci kanshi cikin irin wannan yanayin mai cike daban tsoro da alajabi .. hakika shi bazai ce Ga abinda ke damunsa acikin yan kwanakin nan dayasa yake tsintar kanshi cikin irin wannan birkitaccen yanayin ba .

Tsawon lokaci ya dauka yana zaune Yayi shr kawai yana tunani.
" yayi yayi ya gane abinda ke damun rayuwarsa Amman Sam yakasa domin duk ta inda ya duba bai gano takamaiman abinda yasa yake irin wannan mafarkin ba ..... 'ahankali yasa hannushi yajanwo hanky agefen bed dinsa ya goge gumin daya rufeshi . dan duk da AC dake aiki acikin dakin bai hana Gumi tsatsafo masa ta koina ajikinsa ba .. .. sannu ahankali yakai idanunshi kan agogon bangon dake manne a dakin.
karfe biyu yagani daidai ajiyar zuciya ya sauke tare da koma yayi kwanta lamo.... yana juyi kawai batare yasan abin yi ba dan kwata kwata idanunshi ya kyan kyashe bbu alamun bacci acikinsu tunani kawai yake yana juyi. ...


Washegari

da safe byn ta idar sallar asuba bata koma bacci ba saboda tasan yanayinta domin tana komawa bacci me nauyi ne zai dauke ta.
" kowa Kuma yasan yadda baccin safe yake dan haka kishigida kawai Tayi kan pray mate .



karfe bakwai daidai ta fito daga dakin da'aka sauke ciki. shr koina babu motsen kowa ballanantana mutun ya saka ran ko akwai wani bil,adama acikin gidan kasancewar week end ce.


tafiya take 'ahankali cikin tsanyi jiki , har ta iso part din ummi takutsa kai ta shiga da sallmarta ...

nan ma shr ba motsin kowa ciki "can taji " alamun motsen ruwa a bathroom dan Haka tabbatar da ummi tana.

" bata wani tsaya batawa kanta lokaci ba ta soma yin abinda yakaita, daidai nablah tagama gyara koina ummi tafito daga bathroom..

tana ganin nablah ta saki fuskarta sosai tare da yin murmushi . nablah ta gaishe da ummi cike da girmamawa .

Ummi ta amsa tana mai Bin nablah din da wani irin kallo mai hade da mutuntaka .

Jikinta nablah a sanyaye takarasa toilet din ummi tawanke koina tasss ... sai da tabbatar data gyara duk inda aka nunamata tasss ..

Amman banda part din mai gida Dan so take sai ta gama da koina acikin gidan sannan tashiga part dinsa saboda tsaro ..

Tsaye take a bakin kofar da zata shigar daita cikin part din mai gida.. hannuta rike da handle din kofar .
"takasa murdawa tashiga a dalilin zuciyarta da tasoma wani irin harbawa da sauri .
ta dinga jin wani irin ajikinta wani irin yanayi ne na daban ta tsinci kanta ciki .
,yayinda wani part na zuciyarta ke bata umarni tashiga kawai batare da wani tsoro ko fargaban ba , a tunaninta may be ma yafita ,duk dai tasan week end ce bai zama lallai yazanmato yana ciki ba.
Amman kwata kwata fargaba datake ciki ta hanata yunkurin kusawa cikin dakin ..
,sai da ta runtse idanunta tare da tattaro jaruntar ta sanyawa gangar jikinta , sannan ta iya murda handle din a natse tashiga dakin ,da idanun take bin dakin da kallo Sha,awa.
koina tsab tsab tamkar an gyara bbu wata alamun da zai nuna mutun na rayuwa a cikin dakin , ahankali ta kamo gefen lip's din bakinta ta Dan ciza kadan kana ta soma abinda ya kaita .

Daki daya ya rage a cikin part din da bata gyara ba Dan haka ta kutsa ciki ta soma da wanke toilet ta zo kan royar bed dinshi, ahankali tasa hannuta kan blanket din dake rufe da gado da niyyar cirewa ta nike Dan kwata kwata batayi tunanin zata samu bil ,adama kwance cikinsa ba" a tsorace Tayi sauri sakin blanket din
' tana zare idanu waje tare da furta wayyo Allah nah a kasan ranta , take jikinta ya dauki kirma ta gigice tama rasa hanyar fita dan neman tsira daga cikin dakin.

tsabar rikecewa batasan sanda ta kama handle din kofar bathroom ba ta afka ciki ... Ai ko tana ganin ba kofar fita bace ta sake juyo da sauri ,bbu inda baya rawa ajikinta tare da tattara kayan moupystick dinta tabar dakin da saurin bala'i tana haki sama sama tare da fidda numfashi .

A can bakin corridor din dake tsakanin part din deeni da ummi taja ta tsaya ta sake fidda numfashi tare da addu'ar Allah yasota.. ..

shi kuwa deeni dake kwance ya sake lumshe rikitattun idanunshi kawai dan tun shigowarta dakin idanunshi ke bude ganin itace yasa shi sake lafewa jikin pillow , dan shi ko yaya akayi motse zai farka.
yadda yaga ta gigice ne ya fi tsaya masa arai .
Dan Haka a tsanake ya tmbyi kansa to me hakan yake nufi da wannan gigicewar dayaga tayi ?

tabe bakinsa yayi tare da jan tsaki sannan yacigaba da baccinsa .

Sai kusan azahar sannan yatashi ,yashiga bathroom yayi wanka hade da alwala yana fitowa ya goge jikinsa ya shafa lotion ya zira jallabiya long sleeve tare da fashe ilahirin jikinsa da turaruka masu mugun kamshi da daukar hankali....
ahankali yake saukowa daga step hannushi rike da gefen jallabiyarsa har ya iso babban falon gidan inda ya tarar da duk ahalin gidan zaune .

ya gaida ummi yayinda zeenat ta gaidashi .

nablah da tun
saukowarsa taji tana kiciniya da numfashinta dake namen barin gangar jikinta ta gaisheshi muryarta aciki.

Yana jinta Yayi banza daita tamkar bai jita ba Sai ma hankalinsa daya dauka kacokan yamayar kan ummi dake kallo, muryarsa a dake yace first lov ni zani masallaci ta juyo tana dubansa tare da ce wa To sai kadawo yarona , sa kai ya fice .

takasan idannu take kallon every step of him dab ..dab... kmr wani jinin sarauta yayinda duk takunsa daya ke daidai da bugun zuciyarta har ya bace wa ganinta idanunta nakansa km Sai lokacin tasamu natsuwar zuciyarta, dan gabadaya ilahirin jikinta bbu inda bayi sake ba .

Muryata Ummi ce tasa ta sake dawowa cikin natsuwarta . nablah ki dawo kan kujera man ki zauna kin wani je can kin rakube akasa... maza taso kidawo nan kusa dani kinji "ki saki jikinki damu nan ma tamkar gida ne , a sanyaye nablah ta Mike tayi kmr yadda ummi ta umarceta .

Ummi tacigaba da magana . kishirya zuwa anjima akwai doctor da zata zo ta miki test kinji nablah cikin sanyin muryarta tace to.....

Ummi tasa hannu ta dauki remut tana canza channel zuwa zeeword .

, zeenat ta dan juyo a wulakance tana kallon inda nablah ke zaune tare da watsa mata wata uwar harara .. bakinta ta tabe kawai cigaba da aikawa nablah da harara iri batare da tabari ummi taganta ba ita dai haka kawai take jin tsanar yarinyar har cikin ranta .

hirar ball ummi da Zeenat keyi jifa jifa har suka gangaro kan hirar duniya ummi ce ke kokarin saka nablah ciki hirartasu " yayinda ita km nablah Ido ne kawai nata ko murmushi Dan kwata kwata ita batasan ma me zata dasu ba' dan Haka tacigaba da sauraronsu har zuwa sanda mai gidan ya dawo daga masjid tare da wata mata suka shigo ..
byn sunyi shafta da wasa da dariya tare da mdm zeenat wanda hakan ya nuna alamun sun saba da junansu sosai ba tun yau ba ..
" ummi ta umarce doctor din data shiga da nablah ,hakan ce takasance domin bata tsaya wani tmbyr ummi ba Dan tasan abinda zatayi .

abinda yabawa nablah mamaki bai wuce ganin komai na aikin likitoci dake cikin dakin ba.
bbu abinda bbu har gadon kwanciyar marasa lafiya akwai shi a dakin.

, Doctor din ta umarce nablah data zauna" ta zaro sirinji acikin hand bag dinta .
ta zuki jininta wanda hakan bai sa hankalin nablah tashi ko daya ba saboda daman hakan yana daga cikin budget dinta.


byn doctor din ta dibi jininta tashiga wani daki still dai acikin dakin da suke ciki tare da bawa nablah umarnin Wuce wa.

Ta Mike jikinta bbu kwari Sai dai bbu wata alamun damuwa ko fargaba atattare daita .

direct hanyar step tabi " ta nufi dakinta" koda tashiga dakin ma rasa abinyi tayi domin kewar yan gidasu ne tattare da zuciyarta" tana ji kmr taje tasamu ummi ta roketa takirawo mata number auntyta su gaisa .

tunawa datayi Killa ma yanzu haka ummi na can tare da mutun da ko kafafunsa ta kalla zuciyata tamkar zata tarwatse takeji" yasa ta share kawai taki koma gurin ummi ..



Sannu ahankali Yau kusan kwanakin nablah goma kennan a gidan Amman bbu Wanda yayi mata bayanin komai dangane da jininta da a gwada.
duk da hakan bawai ya dameta bane illa rashin jin muryar daya daga cikin ah'linta ,tunanin hakan ne yasata .

Mikewa tsaye cikin hanzari da niyar zuwa tasamu ummi ta taimaka ta kiramata auntyta .

bude kofarta ke da wuya taga mutun tsaye abakin kofarsa yana kokarin yiwa kofar dakinsa da key .

Da sauri ta risinawa tana gaishe shi shiru yaki amsawa km bai da alamun zai amsa din sai ma dauke kansa dayayi yacigaba da abinda yake .

Jikinta yayi maseefar yin sanyi da abinda deeni yayi mata.
Dan haka 'ahankali ta dinga daga kafafunta yayinda Rainta yake a dagule tana jin wani irin ciwo mai radadi , duk da kasancewarta mai matukar hakuri da rashin sauri fushi akan abu. Amman abinda mai gidan yayi ya taba ranta .
domin a rayuwarta idan akwai abinda ta tsana da Gani bai wuce tsagwaron raini hankali da cin fuska tare da isgilanci ba dan zata iya dauka komai Banda su .

ahankali ta dinga daga kafafunta dasuka gama sagewa ta nufi hanyar da zata sadata da ummi . dan gurinta kadai take samun sausauci acikin gidan.

A tsanake yabita da Idanunshi tare da rike kungunsa da hannu daya yana bin bayata da wani irin matsiyacin kallo.
yayinda zuciyarsa ke harbawa ko kifta idanunsa bai da alamun yi " so yake ya tabbatarwa idanunsa abinda yake Gani a cikin mafarkinsa , hajabi dake sanye ajikinta bai hanashi yimata kallon kurulla ba " gabadaya idanunshi sun rufe ya shagaltu da kallon Surar jikinta a bayyane ... domin ganinta yake murarta ba tare da wani hijabi ba .

Jin yadda idanunshi ke yawo a tsantsar jikinta ne " yasa Kirjinta ke wani irin harbawa da sauri tamkar wacce ake bugawa guduma a kahon zuwa .

Yanayin sanyita da tafiyarta yasake shagaltar dashi ba dan deeni yagaji da kallonta ba ,ya dauke idanunsa akan ba Sai Dan gudun juyowarta cikin sautsayi.

What lokaci tana kan step Dan ko rabi batayi ba dan kallon da kafe dashi ne ya sayayar mata jiki tare da rage mata kuzarin jikinta .. ahankali km tasoma jin kmr takun mutun abaya daidai ta kai rabin step din cak.... taja ta tsaya tare da rabe jikinta gefe daya .
alamun tana son bawa duk wani mai son wuce dama ,duk da oready jikinta yabata alamun mutumin data baro tsaye ke saukowa sakamakon kamshin turarensa mai tada hankali da ta keji ...

shr kusan two minutes sannan yazo ya wuce ta gefenta zuciyarsa na tacigaba da harbawa .duk da Bai bari jikinsu ya tabu da juna .

Tana nan tsaye har yazo ya wuceta tare da bude wata kofa ya shiga dan kusan har yanzu bata gama sanin kan dakun nan gidan ba.


,inda tasan zata samu ummi kai tsaye ta nufa zaune suke ita da Zeenat kmr koda yaushe suna kallo TV suna hira abunsu hankali kwance. Yayinda kayan fruit ke gabansu da sallmarta takarasa inda suke sannan tasamu guri kan Tia's ta zauna tana wasa da Zara zaran yatsun hannuwanta. ummi ta juyo ahankali tana duban nablah byn ta amsa sallamarta kallonta kawai take Tare da nazarinta .

yayinda zeenat tunda ta juyo ta mata kallo daya ta dauke kanta tare da mai hankalinta kan film da,akeyi .

Sai da ummi tagama nazarinta tsab sannan ta takira sunan nablah ..

Nablah ya'akayi ne ?
Nablah tayi kasa da kanta tana cigaba da yamutsa yatsun hannuta a atsorace muryarta cike da sanyi da in...inna.. tace dan... Allah daman ina..Ina. son nayi magana ne da auntyna ta fadi hakan idanunta suna masu cikowa da hawaye. domin daukarta ko baza su kiramata auntyta bane shiyasa duk takoma wani iri .

Ummi tayi murmushi kawai Tare da sake zubawa nablah ido ganin yadda duk ta dawo kalar tausayi ..
ummi ta girgiza kanta sannan tace yanzu akan zakiyi magana da auntynki ne duk kika dawo haka tamkar zakiyi da kuka?
.. gsky nablah akwai shagwaba atare dake tasa ummi takarasa fadar haka Tare da Mika hannu ta janyo wayarta dake gefe tasoma dealing number Salmah ta Miko mata wayar tare da nunawa nablah wani daki da hannuta . Kishi Ga nan kiyi wayarki kinji diyarta .. haushi da takaici ne gabadaya suka gama turnuke zuciyar Zeenat dake zaune gurin tamkar ta tashi ta shake wuyar nablah ta dinga a zuciyarta , tarasa yadda zatayi ne kawai yasa ta dinga ja tsaki tana aiyana yadda zatayi da yarinyar..


wayar manne da kunnenta har tashiga dakin da ummi ta nuna mata ,daidai nan murya aunty Salmah ta doki dodon kunneta tun kafin nablah tayi magana aunty Salmah tace assalamu alaikum hjy anyi lafiya .
murya nablah cike da doki da shagwaba aunty ba hjy ba ce nablah ce .

Aunty Salmah tayi murmushi A'a nablah.. yana ji muryarki haka kmr kina cikin damuwa ?
Sai da nablah ta sauke ajiyar zuciya sannan tace bazaki jini cikin damuwa ba , byn kewarku ta dameni duk sai aunty Salmah gigice.
tace ko dai akwai da matsala ne a gidan?
" nablah tace uhmmmm fa ba matsalar komai.. in ma akwai matsalar nan bai wuce kewarku ba .

Nablah tacigaba aunty baki bawa mama number wayar hjyr bane kmr yadda kika ce gsky zuwa yanzu na matsu da son jin muryarta, km kmr naganni agabanta haka nake ji ,aunty Salmah tace Eh ban bata number ba nafison zuwa nan da sati biyu tukun nasan zuwa wannan lokacin kingama da sanin halin mutane gidan , ni dai abinda nake so dake ki zauna lfy da kowa Amman da kinga akwai matsi da takura just give me a cul" furrrrr zaki ga aunty ki kmr flay.

nablah ta saki sanyayyayiyar murmurshin dayasa dimple dinta lotsawa sosai wanda hakan ke sake fito da ainihin bawar kyawun da Allah yayi mata .

Ahankali " tace Allah aunty bbu matsalar komai fa aunty Salmah tace to.to. shikenan ,ki kama kanki da kyau km ki dinga saka hijab dinki duk inda zaki shiga a gidan .

Nablah tace har baccima dashi nake aunty Salmah Tayi yauwa Yar gari nablah na murmushi tasake bude baki da niyar tambayar auntyta dip ...maganar ta tsaya ...... Tana zaro Idanu waje sakamakon hasken dataga ya gwaraye dakin gabadaya duk daman can akwai wuta a dakin dan koda tashigo fan na aiki ..

kwance yake akan kujera idanunshi a lumshe yana kallonta kmr ranar farko daya soma ganinta a rayuwasa .

murya aunty Salmah taji tana cigaba da cewa lfy na jiki shr kin dauke wuta kmr NEPA.

A daburce tasoma in in na , A'a.......uhmmmm ba komai to yanaga duk kin rikece kigayamin in wani abu nablah tace Allah bbu komai aunty to kigaida hjy zan Kuma bawa mama number hjy zuwa jibi inshallahu ki kwantar da hankaliki zata kiraki, itama ta matsu taji muryar autata ,da kyar nablah dake kokuwa da numfashinta ta iya bude baki tace to aunty sannan ta kashe wayar Tare da sauke wayar daga kunnena.
har lokacin bai dauke idanunshi akanta ba wanda shi kansa basan ma Yana kallon nata ba .

Itama shanyayun idanunta ta zuba masa kawai tana kallon kwakkywar fuskarsa dam ...taji kirjinta da zuciyarta sun amsa a lokaci daya take ta soma jin tsoron yanayin irin kallon dayake mata.

,jikinta kuwa Banda kirma bbu abinda yake ,takoina gumi ya dinga tsatsafo mata ajikinta Jira kawai take taji yace arrrrrrr ta arce da gudun maseefa Amman Sai kawai taga sabanin haka, domin ko motsa bakinsa bai da alamun yi ballanantana akai gasamun fitowar kalma daya daga bakinsa Sai ma taga tabe bakinsa tare da dauke idanunshi akanta .


aransa kuwa cewa yayi munafuka kawai Tayi wani shr kmr ba yanzu tagama wage baki tana waya ba..😍😍😍
Ni dai nace uhmmmm deeni Banda kin fad ar gaskiya...nooooo


komawa yayi sosai yayi kwanciyarsa normal ganin datayi ya kina ya kwanta ne yasa tayi saurin juyawa da jikinta na rawa ta bar dakin har hijab dinta na neman hardeta kafafuwanta .

" afrigece ta dawo parlour inda ta bar su ummi .
Ummi kadai tagani zaune Banda mdm muzeenat ko Ina tashiga oho ita dai tunda tasamu ta mikawa ummi wayarta ta bawa karfa iska .

tayi shr sannan komai ta tuna ta dagamin kai ...

Koda tashiga dakin ma bayi tashiga dan jin yadda cikinta ke murdawa ,tun sanda take tsaye gaban horo dan sunnan data bashi kennan take jin yadda cikinta ya cure guri daya .

toilet tayi sosai byn tagama tashiga cikin bathtub ta kunnawa kainta" shawa ta dade kwance tana jin dadin yadda ruwan ke rasa kowani part na jikinta .

sai data soma jin kiran sallar ne a masallaci dake cikin gidan sannan tayi alwala ta fito jikinta daure da towel zigidir tayi gaban mirrow tana goge sauran wuraren dake da ruwa ajikinta yayansa take bin koina ajikinta da kallon, yadda yanayinta ya canza gabadaya 'ahankali tayi murmushi tana sake kallon kanta doguwar rigar mai dagon hannu ta zirawa jikinta tare da zira hijab dinta ta tada ikama...




MMN SUDAIS CE
[7/12, 7:08 AM] 0mmer Farouk: 💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA .A .BAGUDO



Page 63



Byn ta idar da sallah ne ta Mike 'ahankali jikinta a tsanyaye takarasa jikin window dakinta .
" ta makale hade da dan zuge labule window kadan ,ta yadda zata ji dadin hango abinda ke wakana a compound din estate din.

Tana nan tsaye tana kallon yadda motocin ke shige da fice a cikin estate din , ta zurawa waje Ido sosai kmr mai shirin hango wani abu na daban aciki estate din, yayinda take shakar wata iska ta musamman mai dadi da ratsa jiki.
wanda rabonta da jin irin haka ta dade , tun kafin shigowarta cikin gidan.

,har wani lumshe shanyayun idanunta take sakamakon farinciki data tsinci kainta ciki.

,Ta dauki tsawon lokacin makalle agurin tana shan iska "karar bude kofar dakin data ji anyi ne.
Yasa ta dan juyo da sauri hade da sakin labulen window.

ahankali nablah ta sauke idanunta fess. akan Zeenat dake tsaye kikam.. tana mazurai . take gaban nablah Yashiga faduwa da sauri a yatsine Zeenat ke watsawa nablah wani irin mugun kallon wanda ke hautsina kayan cikinta , ganin irin kallon rashin arzikin da Zeenat ke binta dashi ne . yasa nablah shan jinin jikinta.

tabe baki Zeenat tayi sannan tace Yar iskar baiwa... kawai abinda yakawo kennan , kin wani zo kin nemi waje a daki kin zauna kina tamkar boka dan tsabar munafurci , to kike so yayi miki sauran aiki da yayi saura uhm ?

Nablah tayi saurin girgiza kanta tare da cewa dan Allah aunty kiyi hakuri wlh na dauka ko mungama aikin ne.

Zeenat , ta sake watsamata wata uwar hararar hade da kallon banza.. wanda hakan ya suka sake frigita zuciyar nabla dake tsaye Amman ta dake batare da tabari Zeenat din ta gane yanayin data ciki ba .

Mtsssssss Zeenat taja tsaki tare da cewa dan Allah malam ni fito ki kije ki karasawa mutane aiki sannan km ki daura min abinci ,Yar isakar baiwa... nablah tayi shr tare da dago shanyayun idanunta tana kallon Zeenat dasu ,yayinda take jin zuciyarta tamkar zata kama da wuta tsabar takaicin sunan da Zeenat din kirata dashi .

Zeenat tace
Kin wani tsareni da idanunwa narai narai kina kallona ko baza kiyi bane ?
a tsanake batare da

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment