Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Suka cigaba da kallon kallon da adduar samun nasara acikin zukatansu .
Suna nan tsaye tsawon minti 30 sai ga wata doctor to fito daga lab zatashiga dakin tiyarta da sauri deeni ya bita abaya yana tmbyrta halin daake ciki Amman babu wata gamsashiyar bayyani daya samu daga gareta.
sai ma dakatar dashi datayi dacewar yallabai kayi hakuri kajira mu a waje.
yace madam please kiyi min hakuri nima ina son naga halin da Matata take ciki Amman ina taki sauraronsa .
dole tasa ya juya ya koma gurin ummi suka cigaba da tsayuwa ta sake fitowa ta wuce su tashige wani office tashin hankali kam bazan iya misaltamuku irin wanda deeni da ummi suke ciki ba sai dai addua.

hankalunsa ya kai karshen tashi.
shr ba'a fito da zeenat ba, hk ma likitoci .har likacin sallah ta gabato ummi tace WA
deeni yaje yayi sallah yayi mata addua kawai hk ya tafi yin sallah jikinsa a matukar raunane.
yayinda yan'uwa kowa sai addua akeyi..

Adakin tiyata kuwa gabadaya likitoci tsaye suke akan zeenat kowanensu da kayan aiki sanye ajikinsu da handglof a duka hannayensu byn Sunyi scaning sun tabbatar da ko ya'ya nawane a cikin cikinta .
sannnan suka fara Yi mata allura take hankalinta yakarasa gushewa Duniya da abinda ke cikinta suka jujjuyawa daita, kana suka soma aikinsu cikin kwarewa da iyawa tare da adduar samun nasara koina Shiru bakajin motsin kowa cikin cikin dakin sai motsin sizos kawai da motsin mutun biyu din dake kan aiki.
suma bawai mgn sukeyi ba sai dai suyi nuni ga abinda za'a miko musu Lokacin da aka tsagata aka soma ciro yaro daya namiji kosashshen km lafiyayye yana motsi aka yanke cibinsa aka mikawa wani mutun dake tsaye gefe guda aka sake fito da wani shima namiji ne aka yanke cibi aka mikawa still mutumin dazu ganin za'a km ciro wani yasa sauran mutane suka soma kiran allahu Akbar ....babu kaukautawa aka mika masa sai dai ita wannna macece sai ta karshe baby still Macece itama take dakin ya dauki kabbara allahu Akbar...Allahhu Akbar kana aka fita da yaran dan gyarasu ummi da deeni sunyi matukar murna har sun sanarwa dagin .
suma sunyi murna da farinciki da saukar zeenat lfy an shirya yaran tsab ana murna ganinsu a hospital din.
shi kuwa deeni kwata kwata bata yaran yake ba zeenat dinsa yake son gani .
hk ma ummi doctors Suka ce karsu damu su kwantar da hankalinsu ana kimtsata tukun km har yanzu allura bata Saketa ba sai nan da wasu yan awanni .

Dakin Hutu aka kaita tana kwance tkmr wata matacciya su ummi suka Kasa hidima GA yaran tmkr basuyi dokin zuwansu duniya ba. Burunsu da faricikinsu bai wuce suga farkowar uwar garken ba.

Kusan awa biyar tsakani sannan zeenat ta farko atare ummi da deeni sukayi kanta suna Yi mata sannu, zeenat kin tashi?
Kallonsu kawai take daya byn daya aranta take wa Allah Godiya daya rabata da cikin jikinta lfy duk da batasan abinda ta haifa ba ko yana raye ko akasin hk.
jikin deeni na rawa yace ummi hado mata ordinary ruwan zafi bari na wanke mata baki shi ya tayar daita zaune ya wanke mata baki cikin wani Dan karamin kwanon siliba sannan ta Dan sha ruwan zafin kadan ummi tace mamana baki tmbye abinda kika haifa ba?

Shr zeenat tayi mata aranta Tana fargaban jin abinda zai biyo baya akan lamarin cikin data wassake taga babu ajikinata .
deeni yaje da sauri ya turo gadon da ya'yan duka hudu ke kwance kowannensu kwance cikin farin showel me Shegen kyau da tsada. zuwa gabanta ummi ta nuna mata da yatsanta kalla kiga arzikin da Allah ya bamu tana murmushin jin dadi.
xeenat dake zaune sai sake bude idanunta tayi Tana kallon beautiful baby's din da ummi ke mata nuni dasu.
ganin tayi shr taki cewa komai km still idanunta na kan yaran tana aikin kallonsu cike da mamaki yasa ummi sake maimaita mgnrta.
aiko tsabar dadi da farinciki zeenat batasan sanda kukan murna ya kufce mata ba tana sake godiya ga mahalincinta doctor suka shigo kusan su uku dakin suna ganin hk suka soma fada akan Dan me za'a Bari Tana kuka irin hk.
sai da deeni yayi musu bayani dalilin kukan nata sannan km duk suka shiga tausayawa rayuwata.
doctor byn yagama duba zeenat yace deeni yabiyo shi xuwa office Dinsa .
byn sun shiga doctor yayiwa deeni nuni daya zauna sannan km ahankali doctor yashiga yiwa deeni bayani akan matarsa tasamu matsala acikin mahaifarta mahaifar ta yadda mahaifarta bazata sake daukar ciki ba.
Har a iya tsawon rayuwarta Dan hk ma tun gurin operation din sun cire mahaifar gabadaya deeni ya runtse idanunshi jin wannan mummunar labarin can km sai GA hawaye yashiga zubo masa kana yacigaba da sauraron doctor har ya dasa aya..Allah sarki zeenat dina ya furta hk abayyane sannan km ya kudurcewa ranshi duk runtsi zai barwa kanshi wannan sirri azuciyarsa ko ummi bazai taba sanarwa ba ballantana zeenat.
Alhamdullahi ko yanzu Sun godewa Allah bisa wannan ni'imar .
Dan hk ya baro office din likita jikinsa a raunane .

Kwanan zeenat 5 a hospital suka fito suka koma masaukinsu akaciga da bata kulawa agida ita da yaranta yayinda duk sanda deeni ya kalleta sai yaji matsanancin tausayinta me gyaraye da tsantsar kaunarta na tsarga masa.
sosai suke bata kulawa shi da ummi sunyi waya da yan gida sannan hankalin kowa ya kwanta.
Cikin yaran mata guda ta dauko kamanin marigayi amna sak wato kamanin umminsa .
dayar km photocopy din zeenat ce sak tun lokacin deeni ya lakabawa me kama da amnarsa ta da small amna.
km sosai yafi jinta cikin ranshi ummi tace banda nuna son kai deeni...
first love Allah sai dai kuyi hakuri dan wallahi duk nafi jinta cikin raina thank you zeenat Allah yayi miki albarka da kika sake dawomin da amnata...
ameen my hrt ta amsa tare da yin murmushi jin dadi tana wasa da yatsun hannuta.
yau tazo mata da abubuwa masu mahinmacin da farinciki, farincikinta datarasa shekaru dayawa suna Dawo mata daki daki hakika Allah maji rokon bawansa ne km me yawon yafiya ne GA bayinsa .
ayau babu abinda zatace sai godiya ga Allah bisa tarin ni'imominsa gareta ubangijinta bai Barta hk kara zube ba duk da ita din me tarin laifi ce gareshi .alhamdullahi alhamdullahi Ta dinga furtawa a kasan xuciyarta ta bude bakinta da kyar tace my hrt gobe ne zamu Yi sati da haihuwa har yanzu bamuji sunan da yanke shawarar zaka sakawa Yara ba?

Gsky ne my hrt ina kan tunani akan hk NE shiyasa kika jini dip.
suna mgnrsu atsakaninsu cike da bawa juna kulawa.
Ummi tayi dariya irin nasu na manya tace lallai iyayen zamani kwata kwata Baku da alkunya agabana kuke zance sunan da zaku sakawa ya'yanku... Sorry first love inji cewar deeni.

my hrt zeenat takira sunan deeni wanda gabadaya idanunsa ke cikin na amna yana kallonta ko kyaftawa baya son yi . Yana jinta yayi mata shr..


My hrt ta sake maimaitawa sai wannan lokacin ya dago rikitattun idanunshi ya tsura mata yana amsa mata Amman hankalinsa still nakan babynsa muryasa ahankali ya amsa da yes dear?
Bakaji ummi bane?
Kayataccen murmushi yayi yace Kalle first love wata alkunya za'a Yi km sosai ummi taji dadin yadda abubuwa suke Gudana tsakaninsu my hrt kasanar Dani sunan da za'a kasawa baby's ya runtse idanunshi for gud 3 second kana ya bude su fess bisa nata yace nabar miki Xabi sunansu duka.
Amman banda amna ki zabar musu sunan daya dace.

ka sanar dani Zabin ka ya sake murmusawa yace uhm byn dukkan wannan kyauta da sadaukarwa da kika min yanzu har ina da wani zabi wannan damarki ce nabaki ita ki damawa kawai my hrt .
duk sunan dakika zabar musu fine zamu kirasu dashi km zai mana dadi ko first love ummi tace uhmmmmm bamuda da matsala .
zeenat ta Kalli ummi cike da jin dadin amsar data bayar deeni ya tsura mata Ido yana kallonta yana sauraron abinda zata ce suka sakarwa juna kayataccen murmushi.

aranta tace gasky Allah maji rokon bawane ya amsa mata addurta ,data Dade tanayi cewar Allah ya karkato da hankalin mijinta gareta yasota kwanton kwancin wanda take masa yaga dararjarta a idanun kowa gashi km tana ganin komai a zahirance addurta ta karbu agurin Allah.

Ahankali muryarta a sanyaye tace my hrt ummi banda amna dayar bby'n na saka mata sunan *nabeelah* cak deeni yabar abinda yake ya dago yana me sake kallon zeenat cike da mamaki da birgewa da adalci irin nata data saba Yi masa.
tabbas zuciyar tagama tsarkaka akan komai daya faru arayuwar baya. hakika ita din me adalci ce akan dukkan lamarinsa da farincikinsa.
tabbata ita din me son shi ce da son dukkannin farincikinsa.
Dan hk kulkun yake sake ganin darajarta da mutuncinta har yake ganin ita din daban take acikin mata .
ya lumshe ido yana murmushin farinciki da jin dadin abinda tayi masa sannan yana cigaba da wasa da hannu amna dake cikin hannushi.
sosai yake jin dadin karamcinta gareshi....

Tacigaba da mgn ahankali Mazan biyu daya Sunan babana habibi Dayan km sunan big dady wato Mahd zubair gabadayansu suka shiga murna deeni ya jinjinawa namijin kokarinta hakika ta kyauta sosai datayiwa big daday takwara..

AI wannan karamcin nata ya janyo mata jama'a sosai sai tururuwan zuwa kasa me tsarki ake ganin takwaran big dady wanda hatta shi kanshi big dady din ba'abarshi abaya..nablah tazo ganin takwararta ihsan daganin lfyar zeenat tanuna matukar farincikinta fiyye da tunanin me tunani Fareeda taci amnah nabeelah taci ihsan habib yaci abulkhari ,big dady yaci abulbaiti murna samun wayan nan yara baya misaltuwa ga ahlin Bello khaliyal.

Watan zeenat guda ta warke sumul tana takawa koina tmkr baita aka yiwa cs ba. Dan hk
suka tarkoto xuwa kasarsu ta gado Nigeria aiko suna dira gidan ya cika makil da dandazon dangi .

deeni ya kanaye yaran tmkr bai taba samun haihuwa ba fk yana zaune agefenshi yace kai deeni wai kai wani irin mutun ne ?

Hk akeyi Dan girman ?

Duk Ka wani kanainaye yara tun dazu ka hana jama'a dauka fk yakarasa fadar hk cike da wasa da murna.
hkn ne yasa dukansu kwashewa da dariya har nablah dake zaune kusa da zeenat tana hada mata tea me kauri gefe guda km ga lafiyayar Tuwon samoviter ne da miyar kuka wace tasha naman kaza da kayan kamshi.

Deeni ya gyara anan dake makale a saman wuyansa tana kallon baby yace sai dai fa kuyi hakuri Dan wallahi duk yadda zan bayyana muku murna da farincikin da nike ciki yanzu ba ganewa zakuyi ba.
I can't believe that those beautiful baby's here they are my children's zeenat is mother today all prays due to Allah ..nablah tace tabbas hH ne dole ne mu nuna farincikinmu Allah abin Godiya km alhamdullahi mungode masa .
ok bayan mijinki zaki bi Kennan nablah tayi murmushi wanda ya bayyana wushiryarta kana tace of course ko byn ka kake son nabi?
. fk yayi saurin girgiza kai tare da cewa rufamin asiri zancenki yayi min sauri dayawa karkisa wannan mijin naki ya hadiyi zuciya yanzu suka sake kwashewa da wata dryr.

An sha sunan yan hudu lfy akasha sosai wanda oready daman angama shirya komai kafin dawowarsu alhamdullahi duk yadda zan zayyane muku irin gagarumin taron sunan da'akayi bazai wadatar da zuciyoyin makaranta ba Amman nabar muku ku kistsima yadda zai kasance da kanku....

kowa dai yasan wacece zeenat sannan diyar ummi diyar alhaji habibu derector of land and housing na Lagos State gabadaya .
sannan km uwar gidan babban dan kasuwan nan da duniya ke yi dashi km take damawa dashi takowani bangare.


byn shekara biyar abubuwa na dadi da akasin hk sun fau ciki har da rasuwar big dady mutuwar da tayi mugu mugun taba zuciyar family Bello khaliya sunyi kukan rashinsa a doron duniya wanda bazasu taba mantawa ba.
da km haihuwar da nalah ta sake Yi na biyu duka maza aksamu fk da ya Mahmud.
Nablah yanzu tazama big madam wace take ji daita anahiyarsu ta Lagos State.
domin tazama hamshakiyar me yin business da decorations din gidaahe duk wani Hadadden gidan dake ji da kanshi.

itace kangaba gurin shiryasa tare da taimakon jarumin mijita uban ya'yanta yayinda kullun zaman lafiya ke sake wanzu atsakanin zeenat da nablah gefe guda km ga adalin mijinsu me adalci atsakaninsu baya danne hakin wata akan wata. itama zeenat kullun supermarket dinta kara tumbatsa yake har ta Kai ga sake bude wani kasancewar daman ita harkar business takara shiyasa komai yake zuwanmata Cikin sauki da nasara.

A kullun tsakanin ummi da surukarta nablah da diyarta nuni ne na alkhari akan rayuwa da Bin miji da kyautatawa akan suyi masa biyayya sbd girman hakinsa akansu iya hakuri km sunayi dashi bisa ga lamari na yawon bukuwarsa garesu.
Domin babu abinda ya ragu tmkr yanzu yake jin karfi ajikinsa, a kullun sunayi masa zance kara aure Amman yace shi sam bashida ra'ayin sama da mata biyu a duniya, idan zasu cigaba da bashi kulawa fine .
to bisa wannan dalilin Yasa har yanzu dai nablah da zeenat ne zaune cikin sabon katamfarin gidansa dake hailand.
nablah wacce take da ya'ya goma sha biyu yanzu haidar junior anan Mimi mualim nihal fk wanda suke kira da uncle da Mahmud .
muzeenat da ummu Salma sulaman sai auta hajarulaswad ,wace tasha kafirar walaha da kyar Allah ya kuburtar daita sbd matsalar datasamu adalilin saka robar nasara datayi.
ita dai nablah batasan matsalar zeenat ba ta dai ji har yanzu shr babu wani labari Amman tafi bawa zuciyarta ko dai itama tsarin iyali tayi tun byn haihuwar yan Hudu domin samun wadataccen lokacin da kulawa da me gida.

After 10 years

a wanna lokacin gabadaya yan matan gidan nasu Su anan Mimi nihar amnA da ihsan suna dakunan mazajensu har da rabo atsakani sbd auren wurin deeni yayi musu dan suna da shabakwai bakwai ..

sai dai har yanzu suna nan suna cigaba da karatunsu a jami'oi daban daban suma Manya maza masu duka nauyi haidar da junior suna kasar America sun tafi karatun digiri dinsu na farko akan tattalin arzikin Kasa .

abulkhari da abulbauti Sun kasar maleshiya abulkhari na karanta doctor abulbauti na karanta Law.
Sai ummusalma muzeenat sai auta Aswad sune suke makarantar secondary ta nan Nigerian tukyshi boarding school .

yanzu gidan sai sulaman Mahmud da uncle wanda dukansu a hannun zeenat suke duk inda kaganta zaka gansu tare da su take yawo. supermarket dinta tayi matukar samu albarka dan hk yanzu a shekarun datake dasu arbain mafi yawancin alamuranta da lokutanta da farincikinta , kan tafi ne akan abinda ya shafi lamarin umminta da ya'yanta dana ya'yan abokiyar zamanta da yan'uwnta.

supermarket dinta da gidan gonar da mahaifinta ya bude mata hidimominta kwalliyarta karatunta har yanzu bata daina ba da wasu abubuwa da suka dagancin gidan aurenta .

Yayinda kwata kwata deeni baya kaunar yaganta cikin damuwa Dan ko tagumi deeni yaga zeenat tayi cikin halin tunani yanxu ne hankalinsa zai tashi ya dinga llaminta Kennan da kalaimai masu dadi .
kaji yana cewa na faje wajen ummi tace tana gaishki .
ko yace yaje gurin amna domin gsky yana mugu Mugun son amna ,Allah ya jaraeshi da son yarinyar... Yace tace tana gaisheki, Dan dai kawai ya Nemo dalilin da hira zai Yi nisa tsakaninsu, sannan a hk sai taji itama amaryar gidan da suke zaune lfy km mutane suke ganin kmr me gidan yafi sonta akan uwar gidan tana korafi AI bashi da wani lokacin kowa da zance kowa sai na zeenat..
in ma labari ya zauna zai baka to baki sanin yadda ake sai kaji labarin yakoma Nata a hk dai zeenat ta takara fahimtar cewar shi dai namiji Mai mata biyu ko uku atsakani yake bai cika samun gwaninta mai dorewa a wurin daya ba. in dai akan adalci ne ya Tsaya ba karkata yayi ba.
Dan hk yana da kyau wata tafi wata hakuri da juriya km da Dan saurarawa miji .
Dan a samu saukin al'amura .
kan hk yasa zeenat take sake yankewa kanta hukunci kara hakuri da mijinta da abokiyar zamanta a kowani lokaci a km kowani hali .

Cikin wannan lokacin da abubuwa yayi musu dadi suka ziyarci kasar American kaiwa haidar da junior xiyara amakaranta.

km suma yaran suka biyosu masaukinsu Don Yi musu hira.
hira sosai sukayi da mahaifinsu .
tattaunawa sukayi akan karatunsu..

daga nan malesiya suka nufa gurinsu Mu'alim da abulkhari da abulbauti sannan suka dawo gida cike da tsantsar murna.


Nablah na tsaye tare da ya'yanta aswad da ummu salma tana tunani deeni ,aurenta dashi da gwagwarmayar data fuskanta matsaloli tun daga mahaifiyarsa har zuwa danginsa kafin daga baya komai yazama tahiri .
duk wayan nan matsalolin duka basa saka idanunta rufewa ta mance alkharin mijinta da abokiyar arxiki da Allah ya hadusu zama tare .
tsayuwar mijin nata akanta kwata kwata baya cikin mazajen da akecewa ba "yan "goyo bane.
Uhmmmmm tayi murnushi me kawarta da fuskasta tana tafiya zuwa part din tana zance zuci ita kam nata mijin na goyo ne bata GA komai ba sai alkharinsa har take ganin kmr dai ace shi din shi kadai halinsa ya fita daban acikin sauran maza sannan yana yin abunda yake wanke sauran laifuffukan yan'uwansa maza agurin mata.
to sai dai tace WA yan'uwanta mata cewar ai babu wani goyo ME dadi irin goyon mijinta domin kuwa shi nmj bakowa Bane face wani cikakken mutun kamilalle jarumi mai fuskantar kowane irin al'mari da karfin zuciya mai iya juyawa daga wani mataki ya koma wani batare waiwaye ba me tarar irin jarumartarsa Don zamo kariya ga nakasa dashi sanin yakamatashin shi ke sake tafiya da zuciyarta sannan yasan yadda ake saka alkhari da alkhari ita kam gani take mijinta yayi WA sauran maza zarra ta koina.
km godewa Allah abisa mallaka mata kamilanllen miji irinsa tmkr da dubu tana cikin wannan tunani taji an rungumeta ta baya ta juyo a tsanake tana me shigewa jikinsa sbd tasan sanyin idaniyanta .

*Alhamdullahi*

*Sai mun sake haduwa daku acikin sabon novel dina me suna sai ka aureni dole.... Idan Allahu ya nufa.*


*allahumma lah sahala illa maja'altahu sahala WA'anta taj'alul hazana izah shi'ita sahala*


*na gode taku har kullum yar mutun bagudo* πŸ‘‰πŸΌπŸ‘‰πŸΌ

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment