Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Deeni su kamani, dariya sukayi gaba d'ayan su, Nablah ta mik'e zata shiga d'aki .

Deeni ya sauko, ko kallon inda yake batayi ba, ta taci ga tafiyarta , shiko ya zuba mata rikitattun idanuwanshi, yana jin wani mugun dad'i yana ratsa shi, sosai ya shagala da kallan ta Ummi tayi gyaran murya.

Sai lokacin ya dawo hankalinsa, k'eyarsa ya shafa, yana murmushi ya kalli Ummi, dariya Ummi tayi tace " oh ni Oga Deeni, waskewa Yayi Yan dariya yana k'ara shafa kanshi Ummi ta kalle shi tace " yawwa gobe zan koma gida na, kuma da Nablah zan tafi, nan da fara'ar dake fuskarshi ta d'auke, .
Ummi ta lura da hakan amma tayi kamar bata san yanayi ba, yace" Ummi ni dai gaskiya a'a ban bada izini ba, ya fad'a kamar zaiyi kuka, dariya Ummi tayi tace " izini manya, yaushe har ta zama cikekkiyar matarka harda kake maganar izini?


Dariya shima yayi yace " Ummi mata ai duk mata ce, yadda hak'k'in 'yarki ke kaina itama haka nata yake kaina, sosai Ummi tayi murmushi irin Nasu Na manya kana tace " aini 'yata gani akayi akace ana so, dana hana ma mutum kamar yayi kuka,da hauka ita waccen binka ma narink'a da ita kana cewa a'a, kasan kuwa Bahaushe yace " Matar shige bata darajara, dariya shima yayi sosai yace " wata mata shigen ba.
amma banda wata, ya fad'a yana mik'ewa, gaba d'ayan su dariya suke yace " ni dai ban bada izinin akai min mata da "dana "ko ina ba.


Washe gari Deeni zai fita office yaje gaida Ummi, bayan sun gama gaisawa ta k'ara yi masa maganar tafiya da Nablah, yace a'a, Ummi tace " ai dama ni na aura maka matar to yanzu nafasa zan tafi da kayata ta fad'a tana dariya, cikin wasa da dariya suka rabu, dakin Nablah ya shiga ya iske ta tayi wanka ta shirya tsaf, ta shirya kayanta, dariya abin ya bawa Deeni amma ya kanne ya b'ata rai yace " ina zaki?


Cikin zumud'i tace " gidan mu, cikin jikinta yabi da kallo yaga yadda yayi mata d'as abin sha'awa, matsowa yayi gaf da ita ta yadda kowa yana jin bugawar k'irjin kowa, cikin kasalalliyar murya yace " da izinin wa zaki fita?

Saboda ya takureta sosai ta kasa magana, yace" to babu inda zaki, ban baki izinin fita ko k'ofar gida ba, bakin ta dake motsi yana san yin magana amma ta kasa yabi da kallo, yawonsa ne ya tsinke, k'utt ya had'iyi yawun, bakin ta ya had'e da nata ya shiga tsotsa kamar ba gobe..


Kiciniyar kwace kanta ta shiga yi amma ta kasa, idonsa ma ya lumshe yana ci gaba da abinda yake, kuka ta sakar masa, auko da sauri ya sake ta, yaci gaba da kallonta, tafiya yayi har yakai bakin k'ofa ya juyo yace " ban baki izinin fita ba, yasa kai ya fice.


A gajiye ya dawo daga wajen aiki, a parlor ya zube, cikin kwalliya Zeenart ta fito ta tare shi, tana ta zuba masa shagwab'a, shiko gaba d'aya hankalinsa yana wajen Nablah, shiru baiji motsin taba, a hankali ya mik'e yace " bari nayi wanka, ya fara taka step din, M heart nazo nayi maka?


Murmushi ya sakar mata yace " no yanzu zan fito, d'akin Nablah direct ya wuce, babu ita balle kayan ta, babu komai nata, cikin firgici ya fito bibbiyu yake taka step d'in, sai da ya saita kansa sannan ya sauka, kallon Zeenart yayi yaji bazai iya tambayar ta Nablah kai tsaye ba, dan haka yace " my love kicewa wannan yarinyar ta dafa min coffee, " wa wai Nablah ai Ummi ta tafi da ita, a firgice yace " what!?


"Da izinin wa? ba nace ban bada izini?

Wani irin kallo Zeenart take yi masa tace " izini kuma, sai kace matar ka?


Sai lokacin yasan yana nema ya kofsa, nutsuwarsa ya tattaro ya saita kansa yace " Ok badamuwa, jeki dafa man, yana ganin ta shiga kitchen yayi wuf ya fita, gidan Ummi ya nufa, yana shiga ya iske ta a parlor kansa ya shafa yace " Ummi ina Nablah, hankalin Ummi kwance tace " nasa driver ya kai ta gidan su, amma ba kwana zatay...... what Ummi gidan su fa kika ce?


Kanta ta d'ago ta kalle shi taga duk ya birkice, ya fita hankalinsa.



No editing please 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 bana 'cikin natsuwa pray for me



MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO




Dedicated to
HAUWA A USMAN
( JIDDARH)



Page 95

Kanta ta dago ta kalleshi taga duk ya birkice ya fita haiyacinsa ta hadiye abinda taji ya tasomata ya tsaya mata a kirji. sannan ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tace eh gidansu nace direba yakaita taga iyayenta kmr yadda nayi mata alkwarin .Amman
ummi Na dauka sai xuwa wani lokaci zata tafi yasoma mgn muryasa cike da zafin zuciya haba first love yazaki bari yarinya ta tafi wannan hargitsartsiyar unguwar tasu me cike da dowatsu alhalin kinsa halin datake ciki yakarasa fadar mgr muryarsa kmr zaiyi kuka .
Da kake wani fushin da daukar zabi akan yarinyar mutane .

diyata ce nablah ko taka?

Yadda kake tunanin kana son "dan" dazata haifa maka .
itama hk iyayenta suke sonta km suke bukatar ganinta kusa dasu dan hk kmr yadda nace maka nasa direba ya ka ita gida .
ahankali jikinsa Yayi mugun sanyi zuciyarsa tashiga harbawa da sauri da sauri ya runtse rikitattun idanunshi gam yana jin Babu dadi acikin ranshi ..
tare da kamo lips dinsa na kasa yasoma cizawa da karfi can ya bude idanunshi ya zubawa ummi dake zaune bisa gado tana kallon yaninyasa da nazarinsa .
Muryarsa a sarke yace first love to meyasa kika.
kwaso kayanta ?

Nakwashe km nayi hakane domin Na tabbatar da abinda nake zarge akanka deeni .


Wai meyasa Ku maza bakwa iya dannar xuciyarku akan abinda kuke so?

deeni tun ranar dana dawo daga india Na dira Daga airport Na tabbatar da ka kamu da matsanancin mugun son yarinyar nan nablah so km bana wasa ba , sosai ka nitse 'cikin kogin sonta .
" deeni kafi son yarinyar nan fiyye da zeenat sannan km kana yiwa yarinyar nan wani irin mahaukacin so .

Da wani irin mugun sauri ya dago da rikitattun idanunsa ya zubawa ummi sosai yana mata wani irin kallo me tsoratarwa sannan da mamakin mgnrta saman fuskarshi .

Eh deeni bazakataba Gane hakan ba sai lokacin Yayi .
Amman ka rigada ka fada son yarinyar nan tunda har ka iya marin zeenat agabana akanta batare ko shakkata ba .
km ka rungumi matarka agabana deeni ka kwantar daita akan kirjinka hkn ya tabbatar min da bakaramin so kake yiwa nablah ba.

ni dai koda zamanku zai daure daita fatana dan Allah dan annabi kayiwa diyata zeenat adalci karkaga wannan itace uwar ya'yanka itace me haihuwa sannan ka wulakanta min zeenat ko byn raina banason ka wulakanta min ita .
dan hk ka natsu ka kwantar da hankalinka da kyau akan 'cikin jikin nablah Allah ne yabaka 'cikin jikinta km shine me tsare bayinsa .
" inshallahu da kariyarsa nablah zata haifamaka abinda ke 'cikin ta.

A hassale muryarsa Na rawa yace ni duk ba wannan ba tunda nace kartaje ba sai a hakura ba idan lokaci hk Yayi da kaina zan kaita uhmmmm sannu ubanta mlm salisu .......

yau wata nawa rabon yarinyar nan da iyayenta kada ka mata ita kanta nablah bazataso zama tare da iyayenta ba a halin datake ciki .
Km ma Muyi daita yau din nan zata dawo .... zuciyarsa a hassale km muryarsa can kasa kasa yace first love nidai gsky banso tafiyarta ba. sannan km mgnr wai Ina son yarinyar nan komai komai.... shima ba hk bane first love domin ni nasan zuciyata nasan abinda take so da wanda bata so . banasonta yarinya idan har. Na afka sonta ta yaya bazan gane ba yakarasa fadar mgnr tare da juyawa fuuuuuu yasoma tafiya ranshi abace ya bar gidan ummi tayi murmushi irin Nasu Na manya deeni kennan ne rikicin gangan Allah Yayi maka albarka tare da sanyaya maka zuciyarka ..


Hayaniyace ta kure 'cikin gidan mlm salisu da murna da kururuwar ganin nablah gabadaya duk wanda ya kalli fuskokin ahalin gidan murna suke da farincikin ganinta ..

Mama tashiga nan nan da diyarta kanneta zagaye daita kowannesu Na murna ganinta hatta aunty Salma tazo da murnata wace ummi ce tasanar mata da zuwan Nablah din . gabadayansu ,suka saka nablah a tsakiyar su .suna murna da jin dadi ganinta .
nuratu ta kalli nablah da kyau .
Kai Alhamdulilllahi yau dai zamu huta da shan zagi gurin baba.
Na aunty Salma ta tsiyar masa da "ya" nablah tayi murmushi wanda ke karawa fuskarta kyau da annuri tare da cewa banana kennan.
nayi kewarsa nima sosai fiyye da tunaninku ..

uhm kalli yadda kika dawo Nablah kinyi kyau dake kikayi fresh sosai gadabaya fatar jikinki ta sauya wlh gurin nan ya amsheki inji cewar nuratu ..
Allah ko nablah tace hk tana murmushi sannan tacigaba duk wannan kyawun da fresh din danayi wlh nafi son gidanmu koda kuwa za'a kwana bamu ci ba Amman dai zan koma sbd wani dalili nawa .. aunty Salma tayi saurin cewa wlh bada hannuna ba 'cikin komawarki .
Ni dai tunda kin dawo Na auna arziki Na huta da fadan baba wlh har fargaba zuwa gidan nan nake .
Tun tafiyarki nake 'cikin tashin hankali boye miki kawai nakeyi sbd kwanciyar naki hankalin Amman mgnr gsky Na tsorata da al'amarin baba.. nan nuratu tashiga zaiyanewa nablah labarin duk abinda ya faru da yadda aunty Salma ke shiri idan zatazo gida .
aiko gabadayansu suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya .

Maman da tun sanda suka fara hirasu da nuratu da Salma ba tsoma musu baki ba sai yanzu tace uhmmmm nablah bana jin babanki zai yarda ki sake barin gidan nan ballanantana har ki koma wani aiki.
ni kaina wlh yanzu banaso komarwaki .
dan hk bbu inda zaki ki zauna kema 'cikin yan'uwanki zan fi samun kwanciyar hankali .
Aunty Salmah tace wlh zanceki gaskiya ne mama Amman kubari baban yazo tukun nasan da zarar yasanar mata da abinda ya zartar akanta zata natsu ... ko babu wannan dalilin bazata koma koina ba inji cewar mama .
murmushi takaici nablah tayi tare da cewa Mama kennan Allah Ni dai zan koma wlh Amman Na da wata uku zan dawo gabadaya gareku.
mama dan Allah kada kice a'a ta karasa mgnr tana marairaice muryar .
uhmmmm mama ta sauke ajiyar zuciya to shikennan Amman kibari babanki yazo kiji me zaice.
Take sukar bar zance suka shiga wata hirar daban .
karfe hudu daidai sai Ga direban ummi ya dawo daukar nablah Amman nablah ta fita da kanta tace ba yau zata koma ba sai zuwa jibi ko gata. da zai wuce aunty Salma ta bishi Dan ya rage mata hanya .



Da daddare byn sallar isha'i mlm salisu yashigo gidan da sallama a bakinsa hannushi rike da wata bakar leda yana shiga dogon parlour gidan.
idanunshi suka sauka kan diyarsa nablah dake sanye da hijab ajikinta wanda tun safe datazo gidan bataci re ba tana kwakume dashi abinda Yasa ma mama bata mata maganar ta cire ba sbd tasan tun asali hk take mayar hijabi ce ita ko bacci zatayi bata cirewa ..

Ahankali mlm salisu yakarasa shigowa ciki tare da cewa wanake ganin hk kmr nablah agidan nan ?

Nuratu ta tashi da sauri jikinta a sanyaye ta karbi ledar hannushi ta ajiye a gefe tana mishi sannu da zuwa .
Bai kulata ba sbd hankalinsa dake kan nablah ..tsam itama nablah tayi da ranta tare da shan jinin jikinta sbd ganin irin kallon da mahaifin nata ke jifanta dashi .
jikinta a matukar sanyaye ta bude bakinta da kyar gurin cewa sannu da zuwa baba ..

uhmmmm yauwa Yan neman abun duniya da fatan dai kin samo masu yawa ?
Nablah tayi tsit ta sake sha jinin jikinta ai nasan duk inda kika je zaki dawo , indai nine ubanki ba shegiya bace ke.....
yakarasa mgnr yana nunata da yatsa hannushi haba haba baban Salma tun...ke ...nasakaki cikin maganata ? Ya katse mama Yacigaba da mgnrsa .
Da "yata" nabeelah nake mgn ba da saratu ba .
dan hk banason jin bakinki cikin manta .
,ai duk da hadin bakinki yaran nan suke yi duk isakanci da sukaga dama.
basu dauke ni abakin komai ba km wlh duk lalacewata ni nan nine ubansu dole km akirasu da sunana sai dai mutun ya gudu bazan fasa mgn ba da cin uwar yarinya tsit kake jin gurin tamkar babu wasu halittu acikin parlour ..mlm salisu yacigaba har ni ubanki zance miki banason abu kice sai kinyi dole .


Ni talakane me wadatar zuci banida karfin daukar nauyin karatunki Amman kice dole sai kinyi .
Yanzu Ina kudin da kika samo a yawon duniyar da kike je dan nasan ba aiki kikaje ba?
duba Ga yanayin sauywar da jikinki Yayi Amman bbu komai hkn ma daidai ne a gurina kinyi son ranki nima nayi son zuciyarta akanki yakarasa fadar Haka tare da shigewa 'cikin dakinsa Bai sake cewa komai ba.


jikin mama Na rawa tace kungani ko.
Kunga irin abinda nake gudar muku kennan Amman bakwa jin magana..

Maza maza ki tashi kibishi dakinsa ki bashi hakuri ..

Jikin nablah a matukar sanyaya ta Mike tsaye ta karasa 'bakin kofar dakinsa ta dan yaye labulen dakin babanta.


Ta hangoshi zaune shr yasa hannushi daya ya tallabe habarsa dashi tashigo ahankali ta durkusa da kyar tayi neldwon 'agabanshi muryarta Na rawa tace dan girman Allah babana kayi hakuri Allah bazan sake ba km wlh tsakani da Allah aiki naje baba ba yawon duniya ba .
Duk da nasamu abinda Na fita nema Amman banida natsuwar zuciya sakamakon bijirewa mgnrka danayi .
Amman kayi hakuri baba takarasa mgnrta hawaye Na bin kuncinta ..

Mlm salisu ya sauke naunauyen ajiyar zuciya yana duban nablah diyarsa wacce yafi so da kauna duk a 'cikin ya'yansa komai nashi ta dauko basu da bambanci komai sai dai kasacewarta macce muryara a sanyaye byn Yayi gyaran murya yace shikennan nablah Allah kyauta km alhamdulilllahi tunda Allah Ya dawo min dake lfy bbu abinda ya sameki ai Na auna arziki.
kukan nablah ya tsananta yayinda a ranta km tace wayyyyyoo babana akwai abinda yasameni har Yayi min nakasu a rayuwata ..

kibar kukan hk Na hakura km na yafe miki Allah Yayi miki albarka sai dai wani hanzari ba gudu ba nima nayi miki abinda bazaki ji dadinsa ba ..
Domin kuwa byn tafiyar ki bbu dadewa wani mutumin kirki yazo neman aurenki nan dai mlm salisu yayiwa nablah bayanin abinda ya faru byn tafiyarta tun daga farko har karshe ..

Nablah Ta dago shanyayyun idanunta afrigice tana kallon mahaifinta dasu .
Shima ya dago yana nazarinta tare da daga mata kanshi alamun gaskiya ya sanar mata .
Ya numfasa kana yacigaba haushin abinda kika min da kaicinsa da km kimar mutumin Yasa Na aikata Haka ..
nablah wannan mutumin dana aura miki mutumin kirki ne me mutunci da girmama babba. bakiga yadda yake hidima damu ba ke kanki kinsan rayuwar gidan Na tausaya da al'amuran cikinsa gabadaya .
yanzu Hk shine ya hanani wanki hular da nakeyi ada ya samomin aiki me daraja acikin apapa..

bbu abinda zancewa wannan mutumin sai Allah Yayi masa albarka km ya albarkaci aurenki dashi ..
yanzu tunda kin dawo zan nemeshi nasanar masa ya turo iyayensa gareni domin nasan nasabarsa da inda yake zaune ..
sosai nablah ke resgar kukanta har da shesheka tana jin wanin irin zafi 'cikin ranta meyasa abubuwa suke zuwa mata hk?
daga wannan sai wannan tasan shikennan shirin karatunta ya rushe kennan har abada tarasa burin zuciyarta da farincikin rayuwarta .
yau tazo mata da abubuwa iri iri masu daci da muni.
rasa karatunta 'cikin jikinta ...auren da babanta ya daura mata batare da amincewarta ba ..

nabeelah mlm salisu yakira sunanta kinyi shr kina kuka bakice min komai ba.
ko zaki butulcewa zabin dana miki ne?

Ta sinkuyar da kanta kasa sosai tana sake fashewa da wani sabon kukan me cin rai da taba zuciya tare da girgiza masa kanta ...

Kin amince da auren dana daura miki ?

Ta girgiza masa Kanta batare da tace komai ba alamun ta amince yauwa diyar albarka nasan daman baki da damuwa ta nan, ko wancen karo ma dakika bijeremin nasan sharrin Salma ne da makircinta Amman nasan ba halin diyata bane ..
sai da mlm salisu ya dasa aya sannan nablah tace baba ... muryarta Na rawa rawa ..Ina neman alfarma guda daya agurinka dan Allah kayi hakuri kabani nan da wata uku , Ina son nakoma gurin aikin nan nawa Dan akwai abinda zan karasa musu wanda ya zama lallai sai nice zanyi da zarar nagama inshallahu zan dawo sai natare....
mlm salisu ya girgiza Kai yana mata wani irin duba kana yace Aa nabeela bazan iya sake barinki zuwa wani guri ba me kike son mutane suce akaina ..?
nazama uban banza kennan agareki koda bbu auren kowa akanki Nablah bazan km yarda da komawarki ba ballanantana yanzu danasan da auren wani akanki .
Me kike tunani mijin naki zaice akai idan yaji labarin kinzo kin koma ?

Muryarta cike da kuka tace Baba tunda yasan banana km Bai San da dawowata ba kawai kada kasanar masa Na dawo .
Aa nabeela kiji mgnta sannan kiyi abinda nake so ko al'amuran ki zasu daidaita arayuwa . gabadaya yanzu kin sauya halayenki dana sanki dasu domin ada kin kasance me biyayya gareni sannan km baki jayyaya ko yi min musu akan duk wani abu danace sabanin yanzu .

Sosai tashiga yiwa mlm salisu magiya da rokonshi tana kuka Amman yace sam Bai yarda ba.
bbu abinda nablah bata fadawa mlm salisu ba akan yabarta ta koma .
bafa zan barki ba nabeelah ki sake komawa ba.
gara ma ki hakura kiyi zaman aurenki shiyafiyye miki alkhari akan wannan aikin .
km inshallahu idan kika bi umarnina zakiga daidai arayuwarki .

Muryarta a shake sbd da kukan da tayi tace shikennan baba Na hakura yayinda km acikin zuciyata ba Haka bane ta dai fadi Haka ne kawai . ta yaya ma zata zauna ta haifi 'cikin shege a gidan ubanta.wazata tace Yayi mata ?
Kai ina...zamanta ma bazai yuwa ba duk da tana son zama 'cikin alhalinta .

Alhamdulilllahi kisoma shirinki daga wannan lokacin zuwa kowani lokacin zaki iya tarewa agidan mijinki....yana karasa fadar hk
ya Mike tsaye tsaye yasoma kokarin cire babbar Rigarsa ya rataye .


Jikinta a sanyaye ta fito Daga dakin mahaifinta


Byn fitarta mlm salisu ya dade zaune yana tunani akan lamarin nablah . gabadaya mlm salisu Yayi deciding akan abinda Yayi mata ko zai amince da bukatar ta ko bbu Nablah me biyayya ce agareshi.
yashiga damuwar sosai akan ganin yanayin diyarsa km abar kaunarsa ahankali ya dinga jin acikin tanaji yanaji babu dadi .
Sannan kwata kwata Bai ji dadin ganinta 'cikin halin damuwa ba. yakasa yin komai ko abincin da aka kawo masa tunani Bai barshi ya iya ci ba ..


Daren ranar nablah Na kwance akan gadon mahaifiyarta juyi kawai takeyi tare da tuhumar kanta akan abinda take son aikatawa kanta.
batasan dalili ba .
Sannan batasan abinda yasa ba Amman ji kawai take zuciyarta Na ingizata ta gudu kawai ta bar gidan ta koma ta haifi abinda ke jikinta tunda tasamu wanda zai amsa km ya fita bukatar abinda ke cikinta . take km ta tsinci kanta 'cikin wata irin faduwar gaba sakamakon tuno deeni da al'amuransa datayi .
Wani irin kewarsa taji ta tsarga mata tare da mamaye zuciyata da gangar jikinta duk ta inda ta motsa sai taji hannushi Na yawo a tsantsar jikinta .sosai ta dinga sauyi atare daita agame dashi .
Ta dinga jinshi har acikin jinin jikinta da gangan jikinta zuciyarta tashiga harbawa ahankali tana aiyana mata abubuwa masu tarin ,yawa akansa.. da kyar nablah ta rentse shanyayyun idanunta tana saka da warwara a zuciyarta akan zamanta gidansu da 'cikin wata bakwai da satinnai ..ajikinta.
tasan muddin mahaifinta yasan da zaman 'cikin jikinta kashinta ne kawai bazai yi ba da duka .akaron banza ma ,zance idan yakamaka kana sai Yayi matun mugun duka tana kallon yadda yake dukan nuratu akan tara samari Ina ga ita me dungurungun ......
Idanunta suka bushe takasa runtsawa 'cikin Haka nuratu tashigo dakin hannuta rike da waya tana chatting ta zauna agefen nablah. sanyayyiyar ajiye zuciya Nablah ta sauke da karfi gaske har nuratu ta juyo 'cikin sanyi jiki tana duban yanayinta kana tace wai ke meke damunki ne duk kin wani takurawa kanki akan maganar baba?
idan baki son auren dayayi miki kigamasa man bawai ki zauna kina damun ruhinki da tunani banza ba .
Itama nablah juyowa tayi sosai tana kallon nuratu takasa ce mata komai ..

Nablah ....nuratu takira sunanta .
muryata a sanyaye ta amsa da Na'am. Ta amsa muryarta Na rawa .

meyasa. kike son komawa gidan aikin nan byn kinsamu abinda
yakai ki ?

Kuma wani abu ne zai sake maida ke ?

,aganina ki hakura kawai da duk ma abinda zakiyi ki zauna acikin mu wlh lokacin da baki nan nasha mafarki dake kina 'cikin wani halin tashin hankali shiyasa ni yanzu a gaskiya bana son ki sake yin nisa damu .
duk da jikinki ya nuna baki 'cikin damuwa da wahala Amman wlh hankalina Bai kwanta da wannan aikin naki ba.

, Nablah ta fara kwalla idanunta suka cicciko taf da ruwan hawaye xuciyarta na sake karyewa .
muryarta a sanyaye km cike da raunin hawaye tace aunty nuratu bazaki gane abinda zai maidani gurin aikin nan ba kona gaya miki .
sannan km batun mafarkinki gaskiya ne domin Ina 'cikin tashin hankali da garare rayuwa wanda Yasa bana jin zan iya cigaba da zama a tsakaninku acikin wannan yanayi .
,dan hk Na yanke shawarar gobe zan yi tafiyata Amman dan Allah kada ma ki gayawa kowa dan bama zan koma gidan aikin ba .
A frigice nuratu ta ajiye wayar hannuta tana fuskarta nablah dake kwance tana matso ruwan hawaye idanunta.
kina nufi duniya zaki shiga ko me ?

Niidai kiyi min addu'a kawai domin rayuwata tana 'cikin tasko wanda bansa ranar dazan fita ciki ba Nablah takarasa mgnr hawaye nabin gefen idanunta.

Me Yayi zafi hk indai akan auren da baba ya daura miki ne Ai gara kiyi zamanki idan yaso kice masa
baki so .
Amman zance guduwa ma kada ki farashi domin sunanki zaki bata .
Uhmmmm aunty nuratu wlh ba a dalilin auren da baba Yayi min bane .
Kawai dai akwai wani sirri dake tattare dani ne.
Km shi zai hanani zama tare daku a halin danake ciki .
wani sirri ne wannan da har da bazaki iya gaya min shi ba Ina matsayin yaruwarki ?

Nablah tayi shr zuciyarta

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment