Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

km dayan na goye abayanta tana jijiga su tana kuka su ummi da zeenat tsaye akanta sunyi cirkocirko suna dubanta .Dan gabadaya sun rasa yadda zasuyi daita tun barin deeni gidan take a Haka .
baby's din ma kuka suke sosai tamkar sun San mamansu Na 'cikin tashin hankali.

ahankali deeni yakarasa shigowa dakin sosai yana bin su ummi da kallo.
kana jikinshi narawa da zuciyarsa gurin cewa lfy ummi naganku hk ?
Ina fa lfy deeni tun safe daka bar gidan nan nake fama daita taki cin taki Sha har zuwa yanzu.
Yanzu km mun shigo dakin munganta goye da ya'yan .
da alamun shirin guduwa take ya runtse rikitattun idanushi dake cike da rudani yana ambatar sunan Allah .
ya kamota ya zauna daita ya karbi yaya duka ya kwantar dasu ya riko hannuta'cikin nashi yana kallon ummi da zeenat tare da yi musu alamar su fita.

Byn sun fita gabadayansu ya Mike yaje ya rufe dakin tare da yiwa kofar key yana dawowa ya rungumeta gam ajikinsa kusan minti goma shabiyar suka dauka haka batare da yace komai ba suna sauke naunauyen ajiyar zuciya da shakar numfashin junansu.cike da tausayinta ya zareta Daga jikinsa yaje ya hado mata tea me zafi yakawo mata ta kar Tasoma sha ahankali Dan yanzu tafi yarda dashi akan zeenat da ummi .
muryasa'cik e da fargaba yace nablah ta dago shanyayyun idanunta tana kallonsa batare da ta amsa.
Meke damunki ?
Tayi shr taciga da kurbar tea .
Ko wani abu su ummi suka miki ?
Ta girgiza masa kanta .
Ya kamo tafin hannunta wanda yake empty yasoma murzawa ahankali ahankali tare da tsareta da rikitattun idanunshi.
Muryarsa cike da laushi ya sanyaya ta sosai sannan yasoma mgn a tsanake yace ba ki min alkwarin zaki bani bby
ba?
Ba gori ba ki tuna abubuwan alkhari dana miki nablah akanki Na mari matata ta sunana akanki Na kewa mahaifiyarta gardama Ya'yanki ba'a San usilinsu ba.
ba'a San tushensu ba Amman naji nagani nace karbi 'cikin jikinki domin Na rufa miki asiri sbd kar duniya ta zage ki .

,kin tuna sanda kika yi 'cikin nan ban Kiki ba nayi rayuwa dake tamkar matata ,Na kula dake da abunda ke cikinki . please nablah kada ki canza ra'ayinki akan alkwarin dakika min akan zaki bani su . jikinsa Na rawa yacigaba da cewa wlh idan kika yarda kika amince kika bani baby's din nan nayi miki alkwarin zan mallaka miki gidan glass gabadayansa zan mallaka miki gidana dake ajawu estate zan maidake makaranta kicigaba da karantunki dakike buri .
zan taimakawa iyayenki Na canza musu rayuwa zan ingata rayuwarki data ahlinki gabadayansu .
haka ya dinga kwadaita mata abubuwan alkhari dazai mata .
nablah Ina son kisan wani abu ko matata ta sunnu bata taba zuwa sabon gidana Na glass ba Sai ke.
bantaba yin rayuwa da wata mace a duniya irin yadda nayi rayuwa dake ba .
Narasa tantancewar kaina da zuciyata shin sonki nake ko km tausayin ne ko km sabo ne Amman mutane da dama idan Na tmbyesu suna gaya min sonki nake.
which's kema kinsha gaya min haka.
Amman Ina karyata zuciyata nablah ki dubi Allah ki taimaka please ki bani yaran nan sake of me zuciyata tayi rauni dayawa gashi bata iya naci akan abu duk girma Amman yau tsawon kwana hudu Ina binki.
sanadiyar wayan nan yaran bbu abinda bazan iya miki ba arayuwa zan miki komai Na rayuwar duniya r nan .
jan jiyar dake dadin duniya zan saki daukaka acikin duniya.
bazan taba barin ki wulakanta ba.
Duk abinda deeni ya mallaka naki ne hk zuciyar deeni take ce please please nablah ki taimaka please Haka ya dinga gaya mata Ward's masu dadi da sanyaya zuciya as ended.
Ya zube kasa agabanta Yayi mata neildwon tamkar dai yadda zeenat tayi mata.
ya daura kanshi a saman cinyarta sannan ya sakala hannushi ya rungumeta gam ta baya muryarsa a raunane yace mata.
Dan girma Allah kiyi hakuri ki taimakeni ki rufa min asiri ni badan zeenat ba Dan ummi banason ki kunyata ummi sbd ta rigada tagama gayawa mutane zeenat haihu . Yanzu tunda abin yazama hk Kinfa sa kyautar mana da yaran shikennan ki ba r ya'ya kawai .
Amman Dan sbd dan kada mutane su farga su gane ba yaranmu bane .

Ki aro mana su Amman agurin ki zasu dinga kwana a lallaba mutane har ayi suna inyaso byn suna Sai a gayawa duniya da mutane abinda zeenat ta haifa sun mutu har an binnesu ke km kina iya tafiya da yaranki .
Gabanta ya fadi jikinta ya dauki rawa tace to.. to. shikennan Na yarda da wannan .
zan muku alfarma har ta wata daya a gama rurumar suna da barka Sai dai fa wlh da ya'ya zan dinga kwana kmr yadda kace.
zuciyarsa cike da farinciki samun nasara da Yayi yau yace Na amince .
to kira ummi da zeenat ka maimaita agabansu gabadayansu suka shigo dakin byn kiran da deeni Yayi musu ta waya.

Ahankali cike da natsuwa ya maimaita yadda sukayi da nablah ummi zatayi mgn da zeenat Yayi saurin yiwa ummi sigina da idonsa alamun kada suce komai take kuwa suka yi shiru.
suka hau cewa shikennan mun yarda da wannan tsarin ... gabadayansu da ummi da zeenat har deeni suka tabbatar mata da sun Yarda akan tsarin...




Uhmmmm to ko yazata kaya tsakanin deeni da zeenat har uwar gaya ummi 🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔Ku dai kucigaba da biyo Yar mutan bagudo




MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗





AYSHA A BAGUDO



Dedicated to
HAUWA A USMAN
(JIDDARH)




Page 101




Gabadayansu suka fita Daga dakin atare.
zuciyar ummi da zeenat cike da matsanancin fargaba da tsoron abinda zai biyo byn wata dayan nan da nablah tabasu.. zeenat so tayiwa ummi mgn akan hukuncin da nablah akan baby's .
Amman bakinta Yayi mata nauyi .
takasa cewa komai Sai dai ita azuciyarta taso ne ace ambar mata yaran gabadayansu ba wai aro aka basu da gindaye sharadi ..


Byn fitarsu nablah tayi kuka har da ciwon kai akan rayuwar data tsinci kanta ciki .

Me zatacewa iyayenta da danginta akan yaran ?

Wa zata ce Yayi mata cikinsu ? Sosai tayi kuka tamkar ranta zai fita ..

Ita dai duk rintsi tana son ya'yanta km duk tsananin wuya tana tare dasu km zata rayu da abunta domin sune duniyarta itace duniyarsu .



da daddare deeni yashigo dakin ta Dan dago shanyayyun idanunta ta dube shi wallahi Sai taga duk ya rame mata Yayi Dan wuya , yaja stood ya zauna yana facing dinta idanunshi akanta tayi saurin yin kasa da kanta . muryarsa a raunane.yace me Dame kike so game da suna ?
ta sake dago shanyayyun idanunta ta dubeshi dasu tana maimaita abinda yace a cikin ranta muryarta a sarke tace ni Ina ruwana da wani suna ?
Nifa babbar sunana kugama abinda zakuyi da yarana Ku dawo min da abina nakama gabana .

Ya kamo hannuta 'cikin nashi yasoma murzawa yana kallonta agalabaice kana yace Karki damu kanki Ai za a dawo miki dasu .
Amman kafin wannan lokaci Dan girma Allah ki saki ranki sosai kin dinga ci abinci kina basu nono sosai suna Sha . Yakarasa mgnr da duk kinbi kin tada hankalinki sbd yaran nan.
,uhmmmm dole ne naga kmr ana son a farmakeni akansu ne km mgnr bada nono Ai ko bakace ba dole nabasu idan ma banbasu me zanyi dashi?
numfashinsa ya sauke da kyar yana cigaba da kallonta ya km damko dayan hannuta 'cikin nashi yana murzawa ahankali ahankali yana kallonta surar jikinta nablah yakira sunanta ta kalleshi ta sauke idanunta 'cikin nashi .take gaban dukkansu ya buga da karfi .
wai bakya jin komai a game dani ne?
ya fadi hk muryarsa cike da fargaban abinda zatace .
Sai data tsuke tsukaken bakinta hade da lumshe idanunta sannan tace me kake tunanin zanji a game da kai ?
Wani abu makamancin felling akaina ko shaukin kaunata ......... Yayi mgnr yana matse hannuta sosai 'cikin nashi.ta girgiza masa kanta
uhmmmm Gsky ni bana jin wani abu makamancin hk a game da kai .
Sai dai idan Kai ne ke jin hk agame dani .
Yayi saurin lumshe rikitattun idanunshi na 2 second kana ya bude fess yana kallonta tabbas abinda ta fada masa ba gsky bane .
idan dai har shi yana jin wani abu akanta yasan dole ne itama takasance hk ..

Ya Mike yakarasa gadon da bbys dinsa ke kwance suna bacci ya sumbacesu daya byn daya Amman ya dade akan bby girl dinsa yana kallonta yana jin kaunar yarinya Na sake huda zuciyarsa komai nata irinn Na nablah ne sak.
bbu abinda ta dauko nashi Sai hasken fata koda ya dawo gurin nablah har tayi shirin bacci .
ta Dan dube shi tace kazo ka wuce bacci nake ji zan kulle kofa uhmmmm babudamuwa kina iya kullewa kawai Dan nima anan zan kwanta .

Bangane anan zaka kwana ba ? Tayi masa tmbyr a Dan hassale .
Bai ce daita komai ba ya nema guri can karshen gado ya kwanta .
Yana runtse idanushi .
tazo inda yake kwance ta tsaya akanshi .. please kazo ka bar dakin nan .
Nifa wlh bana son kebencewana da kai alhalin Kai ba muharramina bane.
fizgota taji yayi ahankali bisa kirjinsa ya rungume tsam yana sakin numafashi .
kiyi baccinki anan bbu abinda zan miki .
Muryarta a matukar tsorace tace gsky ni a'a .
ada can baya banyi komai dake ba Sai yanzu ..kina jego
Ta bude baki kennan zata sake yin mgn ya hade bakinsu guri daya yana girgiza mata kanshi da lumshe rikitattun idanunshi masu kashe mata sansar jikinta.
Dolenta tayi shr ta lafe a fadadden kirjinshi tana fidda numfashi sama sama .

Asuba ta gari tsumammu masoya ..


Ana sauran kwana biyu suna nablah zaune a gefen godo jikinta sanye 'cikin wata hadaddeyar doguwar rigar shadda har kasa wacce ummi takawo mata.
rigar shadda tayi matsefafe kyau ajikinta km dagani zatayi tsada Tasha aikin stone work sosai rigar tayi mata kyau ta karbi sihirtaccen surar jikinta me daukar hankali .
tayi kyau sosai tayi fresh Sai sheki take xubawa irin Na me jego .
Koina ya cicciko ajikinta most especially brest dinta da suka sake wani irin cikowa bam dasu sukayi mata hakeke akirjinta tamkar zasu yaga rigar dake sanye jikinta .
Sai kamshi turaren me sanyi dadi take takoina kasancewarta me tsanani tsafta da son kamshi .
deeni yashigo dakin bakinsa dauke da sallama ya ajiye wasu manya manya lailon .
ya zauna kusa daita sosai tare da cewa washhhhhh yana kallon fuskarta.
ta juyo ahankali saitin inda yake zaune idanunsu suka sarke 'cikin juna ya kashe mata idonsa daya yana kallon 'cikin kwayar idanunta da surar jikinta wani irin shock jikinsa Yayi. Kullun yaga ganta kara kyau take masa da sake shiga zuciyarsa .

take zuciyarsa tashiga harbawa da sauri akanta .
muryarsa a raunane yace ga kaya nan ki bude ki duba wanda Bai me ki ba Sai a canxo.
lumshe shanyayyun idanunta tayi batare da tace masa komai ba .
tasoma bubbude lailon din jikinta a sanyaye.
Nablah Na budewa taga wasu kwali guda uku manya Sai Dan karamin kwali guda daya ta dago shanyayyun idanunta ta kalli deeni suka hada ido ya jinjina mata Kai alamun taciga da budewa kawai taga abinda yake cikinsu
Dan har wani kamshin kwalayen keyi da lailon din gabadayan .


Manyan kwalayen tasoma budewa takarmane hadaddun aciki.
kusan kala biyar ajere aciki .
ta sake dago shanyayyun idanunta ta dubesa ya sake kashe mata idonsa daya.
Domin daman idanushi nakanta ne.
jikinta a matukar sanyaye taciga ta ajiye wannan kwalin ta bude wani vasassce flat shoes different types tagani Suma guda biyar masu shegen kyau da tsada da daukar hankalin batace komai ba ta km bude dayar kwalin kayan jewairis ne dangin kayan wuya kowane sarka sait da dankune da agogo da bangus da abin hannu Na axurfa sai sheki suke da daukar ido anyi musu ado da Stones farare yayinda kowanne jikin abin hannu an rubuta
N N da manya harafi kana Gani azahirance .. sororo tayi kawai tana kallonsa da shanyayyun idanunta jikinsa cike da shaukin kaunarta ya sake motsawa sosai har suna jin numfashin junansu da bugun zuciyoyinsu.
ya karba abin hannu ya zira mata yana murmushin gefen baki wanda Bai hade da fuskarsa gabadayan ba .yace ya kikagani ,sunyi kyau ko ?
Ta lumshe idanunta batare da tace kala ba .

Ki Bari byn suna zan kanki saudiya ki zabi design din da kikeso ayi miki Na zinari ..

Ita dai nablah har lokacin kallonsa kawai take da mamaki tamkar a mafarki wai ita yau deeni yakewa abubuwa kmr matarsa ta suna km yake bata kulawa ta musamman ita fa tasoma jin tsoron lamarinsa gsky .
Ahankali Ya soma shafa saman hannuta yana lumlumshe rikitattun idanunshi ya sake cewa ya kikagani ko kayan basu miki bane ?
Girgiza kanta kawai tayi tare da cewa Na gode Allah Ya saka da alkhari Allah yakara Budi .
km sunyi matukar yin kyau sosai ..

Murmushin ya sakar mata deeni.
fari tas yake jin zuciyarsa Sai wani murmushin farinciki yake jin yana mamaye ilahirin jikinshi .
Wannan shine karo Na farko da Yayi mata alkhari irin hk arayuwarsa km taji dadi ta yaba har tayi masa godiya da addu'a .

Ga kanshi ya bude Dan Karami kwalin ya ciro wata dankareriyar waya Samsung ya hada da layi da komai yabata murna ya rufeta sosai jikinta a mace tasa hannuta ta karba tana sake yi masa godiya . girgiza mata Kai Yayi alamun bayaso .
yadda ta nuna taji dadinta sosai aranta .
Dan hk dole shima yaji dadi ya Mike ahankali ya fita Daga dakin yanata fara'a da murna itama binsa tayi da ido tana yatsina fusaka har ya fice ya rufo mata kofar ..

ta sake dudduba kayan sosai tana yatsina fusaka tana jinjinasu a ranta tace aikin banza kawai dama kasani baka wahalar da kanka ba idan kayi da wata manufane ma .
burinku ba zai taba cika ba akaina da yarana ba .
duk 'cikin kyautar bbu abinda ya birgeta km ya dauki hankalinta kmr abun hannu hk ta dauki lokaci tayita kallonsa tana shafawa tana lumshe ido .


Ranar suna deeni ya kashe wasu irin mahaukatan kudi tamkar a kasa yake hakosu zeenat da ummi kallonsa kawai suke.
akwati day day har biyar yayiwa kowane Daga cikinsu Daga nablah har ummi da zeenat tsayawa ma fadar abinda yake 'cikin akwatin nan bata lokaci ne .
Ga key din mota da daya bawa nablah kira 4mart Yar me shegen kyaun tsiya sabon sanfiri .
ga kujerar hajji da umara ita da iyayenta sannan Ga takardun gidan shi Na glass yace yabata halak malak ko byn ranshin sannan ko bata tare dashi Na gaya ummi ta km ta amince da hkn sanda yagama zayye ne mata komai.
hakan yasata jin wani irin mugu mugun tausayinsa domin tasan duk yanayi wannan abun ne Dan ta hakura tabar masa ya'ya ta .
ita km Wlh duniya da abinda ke cikinsa zai bata bazata kyautar masa da yayanta ba .


Ta fada jikinshi sbd murna abinda Yayi mata ta rasa wace irin godiya zatayi masa .
hannunshi duka Yasa yabata kwakkywar runguma ajikinshi tare da lumshe rikitattun idanunshi.
Sbd shaukinta dayaji ya tsargamasa sakamakon jinta ajikinsa .
sai aikin cusa kanshi atsakankanin kirjinta yake xuwa wunyata yana shakar daddaden kamshin turaren jikinta dake karawa zuciyarsa shaukinta bbu abinda deeni yake banda sauke naunauyen ajiyar zuciya da hadiye miyo kasa cewa komai Yayi sai aikin shinshinata da yake yana bata hot kiss a duk inda bakinsa yaci karo dashi ajikinta rungumeta yayi tsam tsam ajikinshi yana sake sakin ajiyar zuciya tamkar wanda yake jin tsoro kar akwace masa ita.
, ahankali Ya Kai hannunshi sama 'sumar kanta yasoma shafawa xuwa bayanta ita kuwa nablah da gabadaya a sukwane take sbd jin dadin abinda Yayi mata da tausayinsa tayi lufffff acikin fadadden kirjinshi me cike da yalwar gashi tare da sa hannuwanta dukka ta zagaye bayansa tana shashafa wuyansa 'cikin salon son zautar dashi gabadaya wani bakon al'amari take ji a game dashi wanda sai yanzu takara tabbatarwa da xuciyarta da abinda ke faruwa daita wato matsanancin soyyayar deeni tayi nasarar cafkar ruhinta.
take km tausayin kanta ya rufeta sanadiyar tuno wanene shi deeni a karon kanshi .
da km matsayin matarsa wani irin azababen wutar kaunarshi ke taso mata bataki ace matsayin miji da mata suke ba.
yayinda wasu warare daban daban ajikinta ke sake budewa ajikinta suna bawa deeni muhali Na musamman yadda taji yaki sausautawa sai aikin shinshinata yaje yana sakin numafashi me gyaraye da zafi zafi me kara raunana zuciyarta akan shi.
idanunta suka cicciko da ruwan hawaye Amman ta maidasu sbd rashin sanin fassararsa garesa..


Muryarta a raunane takira sunanshi Bai amsa ba saima sake susucewa dayayi ajikinta ganin bashida niyar amsawa Yasa tasoma raba jikinta dana shi . muryarta a raunane tamkar zata fashe da kuka tace duk wannan hidimar wa ni Kadai deeni ?
Ya Daga mata Kai .
Deeni sunyi yawa wlh sun min yawa hawaye suka shiga bin kuncinta .

basuyi yawa ba nablah ki zarta hk a gurin zan iya karar da duk abinda Na mallaka akanki ..
Kin bani farinciki mara misaltuwa a rayuwa ki daina kukan nan yau ranar farinciki ce please yashiga goge mata hawayen .

dangi sunyi hidima da bby .
sosai aka sha shagalin suna.
yara sukaci sunan ummi da mahaifin deeni da sunan deeni karan kanshi.
kowa ya wadatu da kayan suna domin rabon get fast aka dinga bayawar .
mutane kuwa kmr turosu ake takoina ka kalla jama'a ne .
Fanni
Kawayen zeenat kuwa bbu mgn suncika gidan makil , da fatan baku manta da zeenat da tarin kawaye ba Sai shiga take tana canzawa . shannu goma aka yanka da raguna biyar . Haka ma kawayen ummi sun zo sosai fuskar kowa ka kalla a gurin murna yake .


Ita kam Nablah tana can dakin tayi shr ita kadai tana tunani abin arzikin da deeni yayi mata a safiyar yau din nan da irin hidimar dayake mata.

zeenat tashigo dakin hannuta rike da wata dakakiyyar shada geziner Sai sheki take tana daukar hankalin ta mikawa nablah ungo ki canza zamuyi photo .
nablah bbu mutsu tasa hannuta karba .
riga da zane ne wayanda suka sha aiki stone work ta mike jikinta a matukar sanyaye tasoma cire kayan jikinta tasaka can km Sai ga ummi da deeni sun shigo har da bby da camera man.
irin kayan dake jikin zeenat danata ,shi tagani ajikin deeni wato anko kennan Yayi musu zeenat tayi tayi ta gyarawa nablah fuskata Amman nablah taki.
Ummi ta miko mata bby boy ta karbi .
shi km deeni rike da mace zeenat rike da dayan boy din aka dinga kashe musu pic .
Sosai akayi musu hotuna wani deeni shi da nablah da baby's wani da zeenat wani km gabadayansu har ummi .

Daren ranar sunan byn kowa ya watse ya kama ganansa gida ya saura Sai Yan tsiraru abokan arziki .
deeni yashigo dakin nablah yaga har tayi bacci yaje ya tsugunna gaban gadon yaran Yayi musu addu'a sannan ya sumbucesu yazo kusa daita ya sumbaci kumatunta ya tsotsi lips dinta , ya kashe AC dake aiki acikin dakin ya fita ..Ya nufi dakin zeenat..


Byn sati biyu sosai baby's suka kara girma sakamakon kulawa kallo daya zaka musu kaji sunyi mugun shiga ranka sannan kamaninsu da mahaifinsu yana sake bayyana wani lokaci idan zeenat ta kallesu Sai taji gabanta Na faduwa har tadasa ayar tmby akansu Amman da zarar tayiwa ummi zance ummi zatace Suma halitar Allah ne km duk yadda Allah yake son bawansa yakasance hk zaiyi km halita biyu biyu Allah yake yi a duniya ..da hk ummi take dauke hankalin zeenat Daga kamanin da yaran sukayi da deeni .km sosai take son yaran take basu kulawa ..Sai dai yaran kiyiwar maseefa garesu indai ba'a gurin mamansu suke ba bbu kwanciyar hankali su dinga kuka kennan har an kaisu gurin uwarsu tukun wanda hakan Na matukar bakanta ran zeenat domin ita so take kafin lokacin da nablah zata bar gidan ta kwace yaran a hannuta ko ta karfin tsiya ne ..


Kullun deeni 'cikin tashi hankali yake akan lamarin yarinyar da shaukin tunanita domin gabadayansa yagama tabbatar wa kanshi da son yarinyar yake bil hali da gsky bbu karya juyi kawai yake akan makeken gadonsa yana tunani ta yadda zai furta wannan tsadaddiyar kalma .
Ahankali zuciyarsa ta bashi shawarar ya sanar mata kawai a wuce gurin take zuciyarsa tayi Na'am da wannan shawara ..


Washegari Ahankali nablah ta fito Daga dakin tasoma saukowa Daga kan step jinkinta rufe da wani Dan Karami 'bakin mayafin shiform.daidai ta kusan karasa saukowa tasoma jiyo kamshin turaren deeni a bayan ta Dan juyo ahankali gabanta Na wani irin bugawa .Shi din ne tagani shima yana takowa ahankali 'cikin takun nan nasa me cike da izza da kasaita byn yaje dakinta Bai ganta ba Sai yaran yagani kawai .


'Cikin sanyi muryar nan tasa me matukar kashe jiki taji yakira sunanta nabeelah tayi ki juoyawa yace please ki tsaya muyi mgn man..
Abu ne me mahimmanci yakawoni yau gareki .
ko kallonsa batayi ba tacigaba da tafiyarta ballanantana ta nuna alamun taji abinda yace shi km hakan datayi yakara narkar da zuciyarsa akanta sannan yakara jin yarinyar tagama tafiya da imaninsa wani irin sonta ke fizgarsa gareta .Haka kawai ya tsinci kanshi da binta kawai tamkar wani rakumi da akala har xuwa babban parlour'n gidan

sai alokacin ta Dan juyo tana masa wani irin matsanancin kallo sannan fuskarta a tamke tace uhm Ina jinka ..?

Abinda tayi yayi matukar mugun bashi mamaki ya km shiga tambayar kanshi da gaske kennan son yarinyar yake ?
Idan yayi laakari al'amarin.
da km yadda yazamo yanzu agabanta tamkar wani zautaccen sauna . To yanzu idan Yayi sanya rashin sanar daita abinda yakeji a game daita taje ta fada son waninsa da aurenshi akanta fa ? Ya zai ji ?

take km wani gumi yasoma sauko masa yashiga gogewa yana take km idanunshi sauya kala sbd matsanancin kishinta dayaji .



Ita kam mamaki da tsoro ne suka rufeta Na abinda ya canza shi farar daya Dan 'cikin sanyi muryar da bata San tana daita ba tace ya dai deeni ?

Kawar da komai dake 'cikin zuciyarsa yayi ya kamo hannuta yana murzawa 'cikin salonsa ya sunkuyar da kanshi kasa yana kallon agogo dake daure da tsintsiyar hannunshi Yama rasa ta Ina yakamata ya fara Bai taba tsintar kanshi da jin nauyi Dan zai fadawa mace yana sonta ba sai akanta ..
Ita kuwa nablah duk ta qagara taji abinda yake son sanar mata Dan hk ta tsareshi da shanyayyun idanunta tana kallonsa .
gabadaya abinda take ji akanshi Yasa ta manta da inda take burunta Bai wuce taji ya furta sonta yake ba ...sun jima a Haka hannusu sakale dana juna kafin ahankali Ya bude bakinsa kmr me rada

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

10 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment