Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutun zai iya dauka aikin ne kawai a gabansa"
amman a zahirin gaskiya hankalinsa ya rabu gida biyu ne . kan aikinsa da nazarinta yanayinta " maganarta ba iya kunnenshi kadai ta tsaya ba " har gangar jikinsa takaiwa farmaki . ahankali ya dinga furzar da iskar mai zafi daga bakinsa . gashi dai magana yake son yi amman taki fitowa sakamakon zuciyarsa dake bugawa .
,da kyar yasamu iya bude bakinsa .
yace kina nufin shima sonki yake yi kennan ?

Tsoro da faduwar gaba ne suka taru suka mamaye zuciyarta.
cikin in..inna ..tace wai wai haka yace "amman , dan Allah kayi hakuri .

da sauri DEENi dake rigingine ya mike zaune cikin daga murya yace mene ? Nayi hakuri ubanki "
Da sadakin nawa akanki idan da kuna kula juna ,I don't care .
Amman yanzu iskanci ne yasa kika, cigaba sauraran wancen sakaran dan tsabar kin raina min hankali.

Bakinta na rawa tace Ai shima yasani" shiyasa ma yace ya hakura dani .
, ok da shi m...
sai km yayi shr yakoma ya kwanta . hade da runtse idanunshi . Lips dinshi na kasa yakamo yana cizawa a hankali ahankali " cikin zafin rai da kunar zuciya ya nuna mata kofa da yatsansa alamun ta bar masa dakin .

,kasa Mikewa tayi tsabar tsoro gabanta yacigaba da faduwa ,muryarta na rawa" ta sake yunkurin bashi hakuri dan Allah yaya kayi hakuri wlh mun rabu dashi tun ba ya...

Wata irin tsawa ya daka mata take maganar ta makale "tun batakai ga karasa yin ta ba .
wanda hakan yasa ta mike tsaye da sauri batare da tashirya yin hakan ba.
jikinta yacigaba da kirma .
Ahankali ya bude rikitattun idanunshi "kasa kasa yake kallonta ji yake tamkar ya tashi ya shakota" tare da yaryarfa mata maruka" ko zai dan samu ya ragewa kansa tension din daya addabe shi tun shekaranjiya.
amman ina baya ji zai iyayi haka.
kodan "
,sanin halin Umminsa.
yasa muddin yayi haka ranta zai baci ,hakan kadai ne yasashi kasa aiwatar da komai akanta.

idanunshi ya watsa mata yana mai sake kafeta dasu wani irin kwarjini ya sake yi mata wanda hakan shi ya kawo katsewar duk wani kuzarin dake tattare daita .
Muryasa a sarke yace live dis room now before I skater you .Ai Bai kai ga rufe bakinshi ta kwasa "
da sauri ta soma kokarin barin dakin.
Hade da tabe baki a ranta Tace matsefafe banza kawai "anya zan iya daukar wulakancin nan naka kuwa ?
ta fice tana goge gumi duk da ba lokacin zafi bane jikinta sharkaf yake da gumi .
Tana fita ta dinga fidda numfashi sama sama tamkar mai cutar asma.
sai data goge gumin daya cigaba tsatsafo mata sannan ta shiga daki .
Zaune ta samu Ummi. Tana balle magani zata sha .
Ummi tabita da wani irin kallo tace ke km daga ina haka ? Tace yaya DEENi ne yakirani" Ummi tace yashigo ne ta girgiza mata kai" kawai " alamun Eh " to yana ganki duk a frigice kmr wacce tayi gudun tsire ,ko wani abun yayi miki.
zeenat tayi narainarai da idanuwa tace A'a Ba abinda ya min .
Ummi ta sake dubanta hade da tabe baki tace ke kika sani ma idan wani abun yayi miki .

,ba kinki tsayawa waje daya ba, sai wani rawar jiki kike yi akansa dan tsabar sakarci irin naki .

Zeenat dake tsaye tana duban Ummi taji tamkar ta zubda kwalla dan jin takaicin abinda Ummi tace mata .
, Tace to ni yanzu Ummi wani rawar kai nayi km ? tmbyta abu kawai yayi fa.
Tace to me Yace miki ko abinci zai ci zeenat ta sake girgizawa Ummi kai.
, baki da bakin ne da zaki dinga amsa minb da ka. cikin rawar murya zeenat tace Allah Ummi tmbyta kawai yayi.
tmby ce kawai zai saki kiyi hujiga hujiga haka kmr an kwatoki a bakin kura .
Ki sanar dani idan wani abu yayi miki.
Tukun na ma , how many hours dana dawo parlour na iske baki nan . Km nasan tun lokacin Kina dakinsa dubi yadda kike fidda gumi dan Allah .
a sanyaye zeenat din Tace to ni Ummi me kike so nace byn .....
sai km hawaye ya balle mata shar shar.
yasoma bin fuskarta . Tayi saurin tare da
sanya byn hannuta tana goge hawayen wasu na sake silalo mata.
Ummi ta zuba mata idanu kawai tana kallonta tare da nazarinta tabbas tasan duk yadda akayi akwai abinda deeni ,yayi mata .
Amman dan sakarci da kafiya irin tata gashi tski fadar gaskiya.
sai da ummi ta numfasa sannan ,tace meyye km na kuka ke da kika ce ba abinda aka miki .
,bakiyi kuka a can inda aka ritsa ki ba sai a nan ,dan kin rai nani ko..

kasa cewa komai zeenat din tayi illa sanya kai datayi cikin bathroom, tashige abunta tana kuka kasa kasa , abubuwan sun taru sun cakude mata .
goma da ashirin ga rashin samun kulawar DEENi gareta .
ga damuwar Ummi akan ta nacewa DEENI .

cikin dare ma sam kasa bacci tayi .
Sai faman juyi kawai take akan gado tare da tunanin iri iri ta jima kwance batare da bacci yayi nasarar dauketa ba .
Wani tunanin ne yazo gara ta tashi takai kukanta gurin mai duka.
dan haka ta mike cikin sanyi jiki " taje tayo alwala .


sallah nafila ta dingayi ba kaukautawa tare da neman zabbi Allah akan aureta da DEENi.

dan ita kanta tasan zuwa yanzu tabbas tayi kuskuren saurin amincewa da aurensa datayi .

Domin shine musababbabin abinda yasa wulakancinsa ya sake nunkuwa gareta. wanda ita kanta tasan hukuncita abinda yafi dacewa daita kennan .
na saurin amincewa datayi da auren DEENi cikin gaggawa batare da ta neman zabin Allah ba .

hankalinta kan tashi.
a duk sanda ta tuna da maganganu ummi. A Ranta tace anya kuwa bazan hakura da auren nan na DEENi na hutawa rayuwata ba .
wai ace mijin da zaka aura ne" ya zame maka tamkar wani ma'alaikan daukar rai ko wani dodo .
Kuka take sosai tana , addu'a neman Zabin Allah a game da auranta dashi .


darajar nafilar data kwana tana yi ne .
yasa washegari ta tashi sakayau daita cikin nishadi da farinciki "
ba kmr ko wace safiya ba .
duk da bata da wani kuzari da walwala. Amman hakan bai hana jin dadi ba.

kitchen ta nufa kai tsaye dan hada masa breakfast kasancewa weekend ce .


" byn wasu yan mintina ta kamla da komai na break tashirya dining . Cikin haka ummi ta iso parlour ta zauna kan dinning table tana yi mata sannu , murmushi tayi tare da koma kusa ummi ta zauna" ta sheida mata ta gama komai .
tana jinsa yashigo yana gaida ummi fuskasa a daure kmr kullum.
Sanye yake cikin dark blue t shirt da wando jeans . ummi ta amsa masa cike da fara'a ka tashi lfy ya dan saki fuska kadan Yace lfy lau na tashi first lov kujera ya zauna . a tsorace itama zeenat din ta gaishe shi ,ya amsa mata a ciki batare daya kalli inda take ba.

,ummi Tace ya..ya .ayi serve din ka ne ? Ya hade rai yaki yin magana .
da kai fa nake a zubo maka abinci ne ta sake maimaita wa ?
Ya dan dubi ummi a shagwabe Yace bana ci.

ummi ta Gane tmbyrta da tayi masa ce ta hassala shi .
dan haka sake bi takansa ba da kanta ,ta zuba mishi komai da'aka girka ta turo plate din gabansa ,tare da dungure masa kai " gashi nan miskilili sarkin zuciya Yace to ni ta yaya za'a tmbye ni ko zanci abinci " byn ansa zanci din "
ummi tayi murmushinsu irin na manya Tace uhmmmm DEENi kennan halinka sai kai "Allah ya canza maka wannan budadden halin naka " Ameen yace tare da kai spoon bakinsa .

parlour ya dauki shr baka jin motsin komai baya ga karar spoon din zeenat .
juyawa spoon din kawai take takasa kai ko loma daya bakinta sakamakon cika wajen da DEENi yayi" duk da tasan hankalinsa da idanunshi ba'akanta suke ba .
tayi shr ta fada cikin duniyar tunanin abinda ya shafeta km yafi damunta.
Wanda a halin yanzun Bai wuce aurenta da DEENi ba .
domin kuwa tana matukar jin tsoron zama dashi ba dan komai ba sai dan tsoron azabar da zai dinga gana mata a gidansa.
hankalinta kan tashi a duk sanda ta tuna da hakan.
Ahankali Ummi ta ajiye spoon din hannuta tare da zuba mata ido kawai tana binta da kallo tarasa meke damun Brain dinta a cikin kwanakin nan .
kusan minti goma ta dauka tana kallonta batare da ita zeenat din tasani ba .

Zeenat .....ummi takira sunanta a frigice ta juyo tana kallon ummi ,ci abinci abinda ummi ta iya cewa kennan .
DEENi dake zaune haushi kmr ya kashe shi tsaki ya dan ja ,ummi ta juyo bangaren sa Tace lfy kai km ?
Fuskarsa a dakune Yace babu , Sai da taga Ummi ta sake dubeta sannan tasoma cin abincin , shima bawani sosai .




Byn sati biyu

Shirye shiryen bikinsu zeenat aka soma sosai ba kama hannu yaro.

,anshirya komai na al'adar hausa kmr sabbabin dinkuna da gyaran jiki komai km tare akeyi musu ita da shemah km iri daya.
musamman ummi ta dauko kwararriyar mai gyaran jikin daga india domin ta gyara mata tilor diyarta da kyau.
duk wani gata da uwa zata yiwa diyarta "ummi tayiwa zeenat shi .
shima mahaifin zeenat din yayi iya bakin kokarin Sosai .

a nyi kamu amare idan aka feshe su da turare masu dadin kamshi na mutune India wanda duk wacce ummi ta dauko ta gyara zeenat din ce tazo dashi.
Anyi musu murzar lalle da kitso .
amman ansha fama da zeenat gurinyin kitso dan cewa tayi ita sam na attachment ,zatayi .
sai da ummi ta bude mata wuta sosai tare da cewa ,zata sanarwa DEENi tukun ta natsu .

Sau ran kwana biyu daurin aure mutane India suka iso , kusan mutum ashirin maza da mata sosai aka shiga hidimar da ,baki.ummi taji dadi Sosai dan kusan duk shakikanta ne suka zo wanda km shine zuwansu na farko Nigeria idan .

,gabadaya gidan nasu cike yake da baki dan haka ba kasafai zeenat din take zama a part dinsu ba ,tana can gidansu shemah .

Zeenat Tace dan Maryam muje kirani part dinmu ina son naga ummi yau duk banganta ba .
, Maryam Tace gaskiya na gaji da yawa wlh kije kawai . zeenat ta ja saki Tace dan Allah muje kiraki ni yanzu zamudawo.
shemah dake kwance ta mike zaune tace muje na rakaki kinsa halin Maryam da maseefar son jikin tsiya.
, Mikewa sukayi har sun fito sai ga Maryam Tace wlh baza kubarni ni kadai ba , zeenat tace ke km kika sani " idan zaki muje .
Tare , suka nufo part dinsu zeenat.
tafe suke suna hira irin tasu ta amare daga nisa zeenat ta hango motar DEENI parke a kofar part dinsu "daga gefe .
" can baya km motar fk ce sai wata motar daban wanda batasan ko ta waye ba .

Jingine yake jikin motar shi yana amsa waya sanye cikin English wear's black jeans da rigar ashi colour "mai gajeren hannu wanda ta fidda ainihin kyaunsa da gargasan gashin jikinsa dake kwance kan Gabar hannushi .
idanunta fes akanshi tana binshi da wani irin kallo saboda yadda taga yakara yi mata kyau. fuskasa har wani shekin annuri take fitarwa kmr ance ya dago idanunshi suka hada idanu.
da sauri ta dauke idanunta wani abu ta dinga ji yana tsirga mata ajikita. sai taga ya fita daban cikinsu fk duk da bawani kallonsa tayi sosai ba .
ta sake dago idanunta da niyar sata kallonsa suka sake hada ido harara ya sakar mata , kallo daya ya sake yi mata ya kau da fuskarsa gefe yacigaba da wayarsa a kallo dayan da Yayi mata yane yadda jikinta ya tsanyi .

kai tsaye zeenat taja hannun Maryam wacce tafi kusa daita ta juya da sauri ta karya cona itama shemah ganin haka yasa tabiyo bayansu da sauri tana jin fk na kiranta . shemah Tace yazaki biyo damu tana km.
zeenat Tace bbu komai mu bi nan di yafi sauki .


ta bayan part dinmsu suka shiga , da ummi tasoma cin karo ta rungume tana sakin ajiyar ,ummi tace meyye haka ?muryata kmr mai shirin yin kuka take Haba ummi yau fa duk banganki ba ,baki ga har wata rama nayi ba " tayi murmushi tace lallai kam kin rame dan ga natsuwa nan suna bikin dariya mutane dake tare da ummi suka shiga yi .
Ummi tayi gaba zeenat nabiye daita tana zuba mata shagwaba.
shape shape tayi abinda zatayi suka bar gidan .


Ranar daurin auren da safe ta nufo gidansu dan dauka kayanta dazata saka .
wanda ta manta bata hadu dashi ba cikin kaya .
,tafe take tana sauri . yayinda su ya faruk da abonkan DEENi ke tsaye duk cikin shirinsu na zuwa daurin aure .
amman banda DEENi wanda dagani shi suke Jira .
Wani irin kunya ce taji takamata dan haka ta dan janyo gefen mayafinta ta rufe fuskarta ,tana jin yaya faruk nacewa amaryamu ki bude idanunta kada ki fadi mana .
amman ina ko waiwayo batayi ba tacigaba da tafiyarta ta kofar baya tabi yauma.
tashigo dogon parlour'nsu ta baya kennan tasoma jiyo kamshin turarensa kafin tayi kokarin bude fuskarta taji sunyi karo da mutun .
da sauri takarasa bude fuskarta "yaya DEENi ne wanda zai fito har wayar dake hannushi ta fadi .
,gabanta ne yayi wani irin faduwa dan har wani juya juya ta dinga ji da sauri ta tsugunna dan miko masa shima ya tsugunna da zai dauka a tare hannunsu yakai kan wayar ,wani irin shock ne yajata " wanda baita kadai ba har shi DEENi yaji abinda taji.

Wani iri shima yaji ajikinsa tamkar an jona masa lantarkin .
. Shine yasoma kokarin janye hannushi daga kan nata ,ahankali ta Miko masa wayar batare da ta mike ba hade da cewa kayi hakuri dan Allah .

komai Bai iya cewa ba baya ga amsar wayar da Yayi ya barta nan tsugunne.

Bayansa tabi da kallo yayi matukar yi mata kyau har batasan yadda zata misalta ba sanye yake cikin shadda fara kal sai kamshin yake zubawa .
gabadaya kamshin turarensa ya gyaraye dogon parlour'n .
Ahankali zuciyarta tasoma bugawa tamkar zata basa kirjinta ..
girgiza kai kawai tayi dan batasan wani irin aure take shirin yi ba haka ta juya cikin sanyi jiki tabar gurin tana shiga ciki.m mutane akama kiranta da amarya amarya kinsha kamshi ita dai bata iya cewa komai ba dan gabadaya jikinta a sanyaye yake .






MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO



Page 27-28

Part din cike yake da abonkan arzikin da en'uwa ,Ummi
Jikinta a sanyaye ta dinga ratsa mutane dake ,zaune a parlour ' har ta iso dakin ummi , da idanun take bin en dakin da kallo .
kozata ga ummi ganin bata alamunta bane , yasa tmbye matar uncle din Inda ummi take.
tace yanzu tashiga bathroom .
Ahankali ta fidda numfashi tare sauke ajiyar zuciya .
cikin haka ummi ta fito tana ganin zeenat din.
ta bata fuskarta "ta zauna tana dubanta"

gefen ummi zeenat tasamu ta zauna fuskarta dauke da murmushi wanda da Gani na karfin hali ne .

Cikin kasa da murya ummi tace yana ganki haka ina kayanki ?

Cikin sanyi jiki zeenat tace shi nazo dauka .

,ummi tace ke dai kin cika shiririta wlh "
komai baza kiyi shi cikin sauri da kazar kazar ba kin dinga jan jiki kennan ,kmr wata mage .

Alhalin kin san halin wanda zaki aura " dan oya oya ne .

jin haka yasa jikin zeenat din sake yin sanye, tare jin wata irin faduwar gaba " zuciyar ta dinga dokawa da sauri tamkar baso kirjinta.
ahankali tasa hannuta ta kamo na ummi
cikin nata jikinta har rawa yake hade da rage murya tamkar mai shirin zubda kwalla tace dan Allah ummi kiyi hakuri kinji karkiyi fushi dani ,zan canza inshallahu Amman " kimin addu'a .
wlh tun sanda aka samo shirin bikin nan nake jin faduwar gaba wanda narasa dalili .
ummi ta tayi shr tare da zuba mata idanu kawai tana kallonta .
tausayinta ne ya sake kamata , ,duk sai taga takara ramewa ba kmr kwanaki ba hakan yasa taji ba dadi aranta.
, ahankali ummi ta mike tare da riko hannuta tayi cikin , bedroom daita. En dakin suka bisu da kallon sha'awa duk da basu ji maganarsu ba Amman sun birgesu .

,Har suka shigo bedroom din Ummi na rike da hannuta Ta zauna daita tana rarrashita kan ta kwantar da hankalinta fargaban aurene kawai ke sata jin faduwar gaba Amman bbu abinda zai faru inshallahu "
Ummi da kanta ta shirya diyatata cikin wata arniyarta geziner ligth blue sai daukar ido take da kamshi tare da fesheta da turaruka kala kala masu sanyi kamshin take zeenat ta fito amarya sak .tayi kyau sosai
Ummi ,ta dauki waya tayi mata hotuna sannan takira Maryam tace tazo ta tafi daita din .



Kwanciyar tayi flat a kan gadon su shemah tana kallo da sauraran duk abinda ke faruwa .
a cikin dakin dake cike da en mata da kawaye

abinka ga mai yawan kawaye " da mutane kala daban daban " yasa dayawa wayan dake cikin dakin kawayen zeenat din ne .
gyara kwanciyarta tayi idanunta na kallon celling dakin hannuwanta duk rungume da kirjinta yayainda zuciyarta ke cigaba tsalle tamkar zata fasa kirjinta ta fito waje.

ahankali ta runtse idanunta sanyi taji yana ratsa koina a jikinta duk da tarin fargaban dake tattare daita hakan bai hanata jin jikinta yayi mata nauyi ba .
Tana ji ajikinta burinta da dokin son auren DEENi .
duk babu shi ahalin yanzu sakamakon fargaba da tsoron kasancewa tare dashi a muhalli daya .
Ta dauki lokacin mai tsawo kwance yayinda ta dinga jin wani iri ajikinta .
Bugun zuciyata na sake karuwa.
ta dinga kokarin ganinta ta cire damuwar dake damunta wanda a zahirance ita ta daurawa kanta .
har yanzu da take kwance jikinta a sanyaye yake takasa tabuka komai.
idanunta ta runtse tana cigaba da sauraron hirar dasuke sama sama .



10:30


Karfe goma da rabi daidai na ranar lahadi Allah ya cika alkawarinsa domin dimbin, jama'a sun shaida daurin auren NASURULDEENI ALIYU BELLO da MUZEENAT HABIB BELLO" daurin auren daya tara manya attajirai da kusoshin gwanati hade da maikata
bakaramin farinciki family din muhd bello suka yi ba ganin sun kara karfafa zumunci a atsakaninsu, .
dan haka farincikisu ya sake karuwa takoina ka juya , family din murna ne cunkushe a fuskokinsu



Zeenat dake kwance har lokacin tana saka da warwara still jikinta a sanyaye yake takasa kwakwaran motse .
zuciyarta fall da fargaba musamman lokacin da taji hayaniyar mutane ta cika gidan alamun an daura aure, en'uwa nata shigowa ana gaisawa , ajiyar zuciya dumin hawaye taji yana bin kuncinta shikennan ta faru takare tana matukar son deeni Amman tana jin tsoron zama dashi hayaniyar mutane take sake jiyowa hakan yasa jikinta ya dauki kirma,kirrrrrr... sam ko kadan bbu wanda ya lura da yanayinta.
Sai ma tashi sukayi suka fita waje km har sanda suka fito tsakar gidan suna ta daukar hotuna bbu wanda ya lura da yanayin da suka barta .
" Maryam ce data karaso wajensu taga suna ta hotuna bbu ita yasa tashiga dakin dan dubota dan kusan tana lura daita tun jiya tamkar mara lfy .

kwance ta tadda ita tana fidda numfashi sama sama .
Da sauri ta karasa inda take bbu abinda jikinta keyi sai fidda hucin zafi, a rude ta dinga takiran sunanta zeenat ... zeenat daman bakida lfy ne?

Kai kawai ta iya girgiza mata alamun eh da sauri Maryam ta mike ta nufi part din ummi tasanar mata .
tare suka dawo gurinta da wasu en'uwa ummi guda biyu .
zuwa yanzu jikinta ya tsananta zafi tare da karkarwa .
ban da salati bbu abinda ummi keyi da sauri takarasa kusa da zeenat din ta zauna tare da riko hannuta" may zan Gani , haka ni fadeela ?
, zeenat kina son ki kashe min kanki ne ?
Ko yaya ,
Alhalin kinsa ke kadai gareni duk duniyan nan km ke kadai debimin kewar er'uwarta dana rasa , bazan iya jurar rashinki ba dan Allah ki tausayi min mamana.
sai km hawaye shar shar daga idanun ummi sosai Ummi ke zubda kwallar tausayi diyarta ganin yadda ta fita haiyacinta cikin lokaci daya .
Ummi tace zahra kamama min ita dan Allah .
su aunty suka mata zeenat sukayi part din Ummi daita .


kai tsaye dakin DEENi ummi tabada umarnin a wuce daita.batare da bata lokaci ba ummi
takira family doctor dinsu .
sannan takira DEENi tace yasameta a dakinshi yanzu yanzu .


Doctor bai dauki

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment